JAMILA 💎Labarin Jamila🖌️ Labari mai ban tausayi tare da tsantsar cin amana Na📘✍🏼 *RABI'ATU BASHIR ABDULLAHI* (Ummu Maher)Miss green💚☘️ *MATAR BASH💎* ✍🏼Marubuciyar📘📘📘 *1_UWAR GIDANA💖* *2_AUREN DOLE👰🏻‍♀* *3_FAROUK🍋* *4_INAYATULLAH🌐💠* *5RUHI D'AYA💙🤍* *6_K'ADDARAR RAYUWA Ce⛲* *7_ASANADIN ABAYAR SALLAH👘* *8 LOADING.... AKAN AIKINA👩🏻‍💼💚* *AND KNOW* *9_JAMEELA🍇🤍* ___________📖🖌️ Ina gaida sarakan surutu na Mk palace😂musamman Rafi'at/Dikko بسم الله الرحمن الرحيم 💫💫 *🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️* _*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_ *Dedicated to My Real Nimcy Luv kina wuta🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥* Ina gaida Masoyana kamar haka🖌️ Na'ima Sulaiman (Nimcy Luv❤️) Momin Shukura Momin Minal Nabila Dikko Hajara L Sadiq Queen nersmer Dr Maryam Hajiya Maryam Bintu Umar Abbale Rukayya(Gawata) Rukayya Adam marubuciyar Dr Muhseen. Sannan INA gaida Masoyana aduk inda wadand'a ban ambato sunansu ba. *TSOKACI;* Wannan labarin mallakin Ummu Maher ne ban yarda a canza min labarina ta kowacce hanya ba sai da izinina. *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫* Shãfî nã🟨1 Wasu shuke shuke ne masu kyau da k'awarta wa awajan da muke tare da kukan tsuntsaye suna sauti a hankali. "Jamila kinji irin farin cikin da na ke ji kuwa idan nazo wajen nan kuwa?" Ina manta dukkanin rayuwar da na yi matuk'ar nazo wajen nan "Jamila mutum baya zab'awa kansa rayuwar da zaiyi a gaba saboda abubuwa da yawa suna faruwa acikin rayuwarmu Wanda bamu shirya musu ba,Amman wannan yana cikin k'addarar ko wani d'an adam alokacin saka shirya da kuma lokacin da baka shirya ba." Wacce a ke kira da Jamila ta yi shiru kwalla na zuba a idonta ta kalli k'awar ta mai irin sunanta wato Jamila cikin sheshshek'ar kuka ta ce"My namesake kenan tabbas bamu ne muke zab'awa kanmu rayuwar da zamuyi ba rayuwa ce ta ke zab'a mana hak'ik'a kamar yadda bakya son tuna rayuwarki ta da nima haka ya ke a waje na."kuma na tabbata namesake labarina ya fi na ki muni nesa ba kusa ba,bana son tuna labarina ko kad'an saboda duk farin cikin dana ke ciki idan na tuno yakan sakani cikin mawuyacin hali". "Jamila inason ki bani labarinki saboda a kullum haka ki ke Ce wa labarinki yafi nawa muni yana da kyau ki bani labarinki duk da nima har yanzu baki ji labarina ba?". "Yanzu kuwa zan baki labarina idan nagama sai ki bani naki namesake sai inji na wanene yafi muni don nasan labarina yafi naki. *JIHAR KANO* Aiki muke sosai a gidan namu,nida ummana muna kitchen muna girke girke kala kala na tarar Yayanmu wato Yaya Deen,Shi d'an Yayan Mahaifina ne tun yana k'arami Mahaifinsa ya rasu shida Mahaifiyarsa a saka makon had'arin mota da ya ritsa dasu a hanyarsu ta zuwa Jigawa. Mahaifinsa ya barmasa dukiya sosai saboda yafi mahaifina kud'i,koda suka mutu sai Baba na ya d'auki Yaya Deen ya rik'esa tun yana k'arami harya girma a yanzu kuma yana England karatu. Shekararsa shida a England sai dai ayi waya dashi Amman bai tab'a zuwa ba sai a yanzun da ya gama makarantar,ni da Yaya Deen mun shak'u sosai kafin ya tafi England yadda ya ke sona nima haka nake sonshi. " Aunty Jamila ga Yaya Deen nan ya dawo". Da Sauri na fito daga kitchen d'in ina gudu don inje in shirya don ko kwalliya ban yi ba duk da na yi wanka don in rage Aiki,Umma kuwa dariya ta yi tana k'ara sa girkin don tasan yadda Y'arta ta tashak'u da Deen. Kwalliya na yi sosai da wasu English wearer's masu kyau Riga ce T_sheet da wandon jeans Wanda yasha ado da flowers masu kyau na tamke yalwataccen gashi na da Ribom daman gani y'ar kyakkyawa sai na yi kamar y'ar Baby banyi amfani da d'an kwali ba kawai na feshe jikinta da tsadadden Turare mai matuk'ar dad'i,sannan na d'auki High Hill d'ina mai matuk'ar tudu na saka koda na duba madubi ba k'ara min kyau naga na yi ba sannan Na fita. Shi kuwa Yaya Deen tunda ya shigo ya baza idanuwansa don ganin ta inda kyakkyawar k'anwar tashi zata fito,Cikin takuna mai d'aukar hankali kamar bana son taka k'asa na iso Farlon. K'amshin turare na ne ya iso tun kafin in iso,Yaya Deen ya ware min hannyensa alamun in shiga ciki,Kunya ce ta kamani don gani na ke yi da da yanzu ba d'aya bane sanda Yaya Deen ya yi tafiya shekara ta 10 yanzu 16. "Come on my lovely sister I miss u". Kawai sai na tsinci kaina a mai cemai" I miss u to Yaya Deen" cikin shagwab'a na fad'i hakan. Kawai sai na fad'a jikinsa gaba ki d'aya na zauna kan cinyarsa,Wani irin Abu yaji Wanda bai tab'a jinsa ba sai akan k'anwar tashi,ya rufe idonshi ya bud'e ya d'orashi akaina tun daga k'asa har sama ya shiga k'aremin kallo. Notice Iyaye kudinga kula da tarbiyyar y'ay'anku Ku kula da irin tufafin da zasu saka kada mu d'orawa kanmu Rayuwar Yahudawa da nasara. *Kuyi hakuri nayi tyiping kad'an* Na yi muku alk'awarin matuk'ar naga yawan Comments ya k'aru zan k'ara yawan tyiping. *_🍇🤍JÁMÉÉLÉR🤍🍇_* 💎Labarin Jamila🖌️ *Na💖* *RABI'ATU BASHIR ABDULLAHI* (Ummu Maher)Miss green💚☘️ *MATAR BASH💎* 📲MINAL MULTIMEDIA https://youtu.be/NCrdsZmuh6E Dan Allah kushiga ku danna Mana subscribe *_Dedicated to Real Nimcy Luv&Hadiza Barau gidan Iko_.* _ _*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*_ *Shãfî nã🟨2&3* Ganin irin kallon da ya ke min yasa na tashi daga zaunen da na ke ina k'ara yi mai sannu da zuwa,Har yanzu kallon mamaki ya ke bina dashi yarinyar da ya tafi ya barta tana y'ar k'arama Amman yanzu jibi yadda halittun ta suka koma. Yaya Deen Ya ce"Kai Babyn Dady gaskiya kin girma Sosai ina tunanin kayan Dana siyo miki ma baza suyi miki ba saboda na d'auka yadda ki ke Siririya yanzu ma haka ki ke Ashe ba haka ba ne.?" Shagwab'a na fara yi mai shi kuwa ya shagala wajen kallona,nima shi d'in na ke kallo yadda naga ya k'ara kyau da wani kwarjini kamar ba shi ba. Da daddare Ya kirawo mu ni da Yaya ta Safiyya sai K'anne na Twins,Raliya da Rayya,sai k'ara min k'aninmu Nasir,ko wa da tsarabarsa sai da ya gama bawa kowa sannan ya dawo kaina yana nuna min kusa dashi alamar in zauna. Bank'i ta tashi ba na zauna a d'an d'arare don duk saka kaya matsatstsu da na ke yi ban tab'a koda rik'e hannun Namiji ba ballan tana ma har in zauna Kusa dashi. Janyo wani k'aton akwati ya yi Wanda daga yadda ya janyo shi zaki tabbata ce wa akwai shi da nauyi,bud'e wa ya fara yi sannan ya turomun shi ya zuba min shanyayyun idanuwanshi. Kallon kayan na fara yi Wanda a k'iyasce za su yi kala 20 kallon kayan na fara yi sannan na kalleshi ina matuk'ar mamakin kayan ina tuno da k'awata Fatima ita ko suturar arzik'i ma ba dashi ballan tana zuwa mkrnt rayuwar Fatima tana bata tausayi duk tana gaya wa iyayenta suna taima konsu don duk Wanda ba shi dashi ka tausaya mishi kaima sai Allah ya tausaya maka. Gyaran murya ya yi ganin na yi zurfi acikin tunani na kawai sai na ji yana ce wa"My Jamy me ta faru ne naji kina tunani haba duka_duka just16 fa ba kisan rayuwa ba har yanzu shiyyasa. Godiya na ringa yi mai abisa kyautar da ya yi min,sai da na sami d'an ta yi wato Yaya Aunty Safiyya muka fara Jan akwatin. Kallona ta yi irin kallon ayar tambayar nan ta ke kallona?Amman bance da ita k'ala ba na fito daga d'akin don dama munyi nida Yaya Deen zan dawo Don ya ce min akwai maganar da ya ke son muyi. "Jamcy kamar yadda na ce miki inason muyi magana to yanzu zan fad'i miki ce wa ina sonki Jamcy tun kina cikin zaninki na ke sonki na ke k'aunarki Amman ki yi hak'uri idan na sab'a miki." Kunya ce ta kamani sosai ban iya na kalleshi ba na tashi zan fita,kawai sai naji ya janyo ni na fad'a gaba ki d'aya ajikinshi. Aunty Safiyya da ke lab'e tana video wani hawaye ne ya fara zuba a idanunta yanzu a ce duk son da ta ke yi wa Yaya Deen Amman ya b'uge da son k'anwarta. Ina baza ta tab'a yiyuwa ba Duk abinda za ta yi sai ta yi don ta raba wannan had'i,da Sauri ta juya ta shiga d'akin ta kwanta tare da Adana wayarta wata hassada ce ta ta sowa Safiyya lokaci d'aya tun suna k'anana duk inda suka shiga kafin kowa ya tanka ta sai an fara tan kani saboda halitta ta kuma gashi na fita fara'ah don ita bata da fara'ah ko d'aya. Cikin kunya na tashi daga jikinsa da Sauri na gudo daga d'akin ina cikin tafiya naji wayata ta yi k'ara number Fatima ce na gani da Sauri na yi pick d'in call d'in nata. "Fatima ganinan zuwa bari in gaya wa Mama sai Aunty Safiyya ta rakoni gidan naku". A d'aya b'an garen Fatima ta amsa da to tana sharar kwallah. Mama na samu a d'akinta tana lazimi na tsaya Ina jiran Mama ta idar da sallar,sallama ta yi sannan ta jiyo ta kalleni. " Mama yanzu Fatima ta kirawo ni tana fad'amin abin babu dad'i,wai Yanzu Aka cullo musu kayan su waje wai kud'in hayarsu ya k'are." Sallalami Mama ta yi sannan ta ce"to muje tare Harda Alhaji mu gano sannan ayi solving d'in matsalar tun yanzu." Shi kuwa Deen dariya ya yi sannan ya ce aransa Tunda na ke ban tab'a jin sha'awar wani Abu ba,koda na yi karatu a turai ban tab'a had'a jikina da wata ba Allah dai ya mallakamin k'anwata Amin. ********* Sun fito musu da kayansu waje Alokacin da Fatima ta hangomu da gudu ta rungume ni tana kuka tana nuna min su da hannu yadda suke fito musu da kayan su hakuri na fara bata,Mama kuma taje wajen Inna wato Mahaifiyar Fatima tana rarrashinta. Abbanmu ne ya je ya fara magana dasu tare da basu kud'in su, kawai muna tsaye sai muka ga suna zubawa Abbanmu kayansu Fatima a bayan Boot. Kallon su kawai na farayi ina rik'e bakina ganin yadda kullum Nigeria ta ke k'ara zuwa sahon farko wajen son kud'i da Ha'inci. Koda muka shiga mota ma hak'uri na dinga bata ina bata baki har muka je gida,Abbanmu ya yanke shawarar zasu zauna agidanmu kafin a samo musu wani gidan don ya yi Alk'awari ba zasu k'ara zama a gidan haya ba zai siya musu wani gidan. *Wacece Fatima* Fatima dai shine asalin sunanta y'an asalin k'asar Cameron ne,buzaye ne Mahaifinta da Mahaifiyarta duk buzaye ne Mijinta mai suna Suraja ya shigo Nigeria ne neman aiki koda gadi ne to shine Allah ya taimakeshi ya fara Aiki a gidan su Yaya Deen har Mahaifin Yaya Deen yarasu sannan ya koma gida anan zaman k'asar tasa wato Cameron yafi k'arfinsa,ganin haka ne ya d'ebo matarsa alokacin ba'ah haifi Fatima ba. Sun dawo Nigeria inda ya k'ara samun Aiki na gadi to da wannan ne rayuwar ta fara yimai dad'i,ana cikin haka matarsa Wacce a ke cewa Imilli ta haihu y'an biyu duk mata Amman d'ayar tazo babu rai aka saka d'ayar suna Fatima. Fatima Mahaifinta ya saka ta makrntar boko da ta islamiyya,tun Fatima tana k'arama suka had'u da Jamila a Mkrntr Islamiya sun shak'u da juna sosai har suka girma suna tare,Mahaifin Jamila yana taimakonsu sosai,har zuwa lokacin da aka nemi mahaifin Fatima aka rasa daga lolacinne kuma rayuwa ta juya musu. *Cigaban Labari* ******** Muna zuwa gida Abba ya kirawo mai gadi ya fara shiga da kayansu,Yaya Deen ne ya fito daga sashensa yasha manyan kaya ya yi kyau na kalleshi ta gefe ya nufo inda muke. "Subhana Lillahi Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un". Fatima ce ta fara fad'in haka bakinta yana kakkarwa tana nuna Yaya Deen,Ai sai gani mukayi ta sume Mana gaba ki d'aya. 🤔🤫To fa me ya sumar da Fatima kuma? Kubiyoni don jin yadda zata kaya. *Ummu Maher ce* *_🍇🤍JÁMÉÉLÉR🤍🍇_* 💎Labarin Jamila🖌️ *Na💖* *RABI'ATU BASHIR ABDULLAHI* (Ummu Maher)Miss green💚☘️ *MATAR BASH💎* 📲MINAL MULTIMEDIA https://youtu.be/NCrdsZmuh6E Dan Allah kushiga ku danna Mana subscribe *_Dedicated to Real Nimcy Luv&Hadiza Barau gidan Iko_.* _ _*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*_ *Shãfî nã🟨4&5* Salati kowa ya fara yi sannan muka nufi Fatima ni ce na fara ruk'ota tun kafin ta je k'asa ina kuka na fara girgiza Fatima. Shima Yaya Deen ya kid'ime yana mamakin sumanta kuma tana nuna sa to me ye had'insa da wannan yarinyar shi dai yasan bai tab'a ganinta ba to meye kuma na tsorata don ta ganshi?. Ruwa aka dinga yayyafawa Fatima har sai da ta tashi,Umma ta kalli Mahaifiyar Fatima ta ce"da man Tana haka ne ko kuwa yanzu ta fara?". Eh to gaskiya tana haka wani lokacin Amman sai an b'ata mata rai ina ganin ko abinda ya faru d'azu ne ya janyo wannan matsalar." D'akin mu na kai Fatima muka zauna muna hira kamar ba ita ce ta suma d'azun ba,muna cikin hirar ne Aunty Safiyya ta shigo ta ce"ke Waye ya kawo mana wannan kucakar cikin d'akinmu Salan suzo su shafa mana tsiya....." Tun kafin ta k'ara sa maganar na yi saurin ce wa"haba Aunty Safiyya me yasa ki ke haka ne?"kuma maganar talauci da ki ke yi ai Allah ne yaso ya barsu haka,irin wannan abinda ki ke yi babu dad'i fa....." Wani mari ta wanka min saida naga wucewar taurari na dafe kunci na ina kuka,Fatima ta rungume ni a k'irjin ta tana rarrashi na. Tsaki ta yi ta fita daga cikin d'akin ta barmu daga ni sai Fatima,sharemin hawaye tayi sannan ta ce"Jamila idan har zuwa gidanku zai zama...."rufe mata baki na yi Ina kuka Na ce "kiyi hak'uri ai ba Aunty Safiyya ce ta kawoki gidannan ba ballanta na ma ace? don haka ki yi hak'uri. Kafin kace me har mun cigaba da hirarmu cikin kulawa da junanmu,muna cikin hirar ne na ke tambayar ta me ya faru d'azu ta fad'i? Dariya ta yi sannan ta ce" Jamila aduk sanda kika ga na yi irin wannan ki tabbatar na ga mutumin da ba shi da gaskiya ne to anan ne zaki ga na suma". Dariya maganar ta ta bani sannan na ce yanzu Fatima yayan nawa Mara gaskiya? ki ce zamuyi fad'a da ke?". Dariya ta yi sannan ta ce a yanzu ba zaki gane duk wani abinda zan fad'a miki ba sai nan gaba idan kika gani da idaniyarki. Ban d'auki maganarta sa mahimmanci ba muka cigaba da hirarmu har muka yi bacci. Haka rayuwa ta yi ta juya mana cikin annushuwa sai dai matsalar mu d'aya Aunty Safiyya don kullum cikin k'untata mun ta ke nida Fatima. Mama har ta yi fad'an har ta gaji,a b'angaren Yaya Deen kuwa ya samu yadda ya keso ta fannin k'anwar tasa don ya lura tana sonsa sosai don duk abinda zai b'atamai rai tana matuk'ar guje masa, don haka ya ke amfani da wannan damar don koyarda Jamila wani darasi. Ta lura yana matuk'ar son tab'a jikinta wani lokacin ta yimai kunya wani lokacin kuma ta nuna mishi bata so,Amman duk da haka bai sa ya daina yi mata ba sai ma abinda ya k'aru. Akwai watarana da aka cemin in kai mi shi abinci part d'insa koda na Kai mishi a lokacin ya fito daga wanka kawai sai naji ya rungume ni ta baya ya fara k'ok'arin cire tawul d'in jikinsa da k'er na kwaci kaina na fita ina haki. Fatima kuwa duk abinda yake faruwa ta Sani Amman kullum tana cigaba da saka idanu aduk wani takun k'awarta Jamila. *Bayan wasu kwana ki* "Aunty Safiyya unguwa zaki jeni ko muzo mu raka ki nida Fatima".? Ko kallona ba ta yi ta fito ta hau motarta tayi tafi yarta ba tare da ce komai ba sai kallon banza da ta Bini dashi har ta shiga mota. Sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta kirawo Abu awaya. *wacece Abu* Abu dai wata tsohuwar mai aiki ce agidansu Jamila wacce bayan ta yi Aure ta daina Aikin ta kawo k'anwarta gidan yanzu ita ce ta ke Aiki mai suna Zinaru. Abu jininsu ya had'u da Safiyya tsab'anin Jamila da ko kusa basa shiri saboda Jamila da idonta taji suna waya da wata k'awarta akan zata raka ta wajen boka,run daganan ta fita a harkar ta. Back to story Da Sauri Abu ta iso tana haki ta ce" kai Safiyya lallai ba k'aramin so ki ke yi wa yaron nan ba kinsan kuwa jiya ma sai da na kai wata yarinya". "kai Abu kin fita surutu muyi Sauri muje mudawo saboda yanzu ma k'arya na yi wa Umma sannan nafito na ce musu zamuje oscation wani gari kuma sai dare zamu dawo sannan ta yarda. Zuwan yamma suka yiwa K'auyen tsibiri wajen wani boka mai suna Karen bana. Tun kafin su i'sa gaban Safiyya ya fara fad'uwa don gidan bokan gaba ki d'aya an saka Jan k'elle da bak'i an rufe ko'ina. Bakin Safiyya ne ya sub'uce ta yi Sallama ai kuwa ya runtuma mata arnen zagi Wanda tsabar kid'emewa sai da Safiyya ta saki fitsari ji kake tsuuuuuuuuuu...🤔🤔🤨🤨😂😂. Idan naga ruwan Comments zan cigaba da wuri,don jin bak'ar rayuwar da Safiyya ta zab'arwa rayuwarta. *Oum Maher ce* *_🍇🤍JÁMÉÉLÉR🤍🍇_* 💎Labarin Jamila🖌️ *Na💖* *RABI'ATU BASHIR ABDULLAHI* (Ummu Maher)Miss green💚☘️ *MATAR BASH💎* 📲MINAL MULTIMEDIA https://youtu.be/NCrdsZmuh6E Dan Allah kushiga ku danna Mana subscribe *_Dedicated to Real Nimcy Luv&Hadiza Barau gidan Iko_.* _ _*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION✍🏻*_ *Shãfî nã🟨6&7* .......Kallonta Abu ta yi sannan ta tsuke bakinta alamar tana san ta yi dariya kuma babu halin yin hakan,Janyo hannunta Safiyya Abu ta yi sannan suka Zauna. Safiyya sai kallon Kafirin Bokan ta ke yi tana k'en k'eminshi don duk hak'uransa sunyi wani irin yellow shar, kamar yasha d'orawa ga wani irin yawu da ke dalala a bakinshi,Uwa uba wani irin wari da ke fitowa daga Bakinsa har ma da jikinsa. Wata muguwar dariya boka ya yi sannan ya kalli Abu ya ce,Shegiya Abu da alama kina samun kud'i sosai don jiya ma kin kawo wata nan, d'anya sharaf da ita ga ta da wani maik'o da alama Amarya ce ko?koda na ji don yarinyar akwai abin harka,zanso a ce wannan ma haka ta ke don da alama ta yau har ta fi ta jiya dank'o. Bokan ya fad'i hakan yana bushewa da dariya kamar tsohon Mahaukaci,yana wangale k'azamin bakinsa. Koda Abu ta ji doguwar maganar tasa ta yi yawa sai ta fara sharhi kamar yadda ta sa ba"Boka wannan yarinyar da ka ke gani wani saurayi ta ke so ta Aura,shi kuma Saurayin k'anwarta ya ke son ya Aura,ita kuma yanzu tana son arabashi da yarinyar a Aura mishi wannan yayarta ta,ayi musu farrak'u yadda bazai k'ara kallon fuskarta ba. ......"Hhhhhhh" ya bushe da wata irin dariya sannan ya d'auko wani k'aton abu kamar jelar zalb'e Ya ajje a dai dai saitin Guiwar Safiyya sannan ya k'ara bushewa da dariya irin ta basawa d'innan. "A yadda naga al'amarin yaron yana son waccen k'anwar taki sosai don idan aka rabasu komai zai iya faruwa don bayan son da ya ke mata yana matuk'ar Sha'awar yarinyar sosai,don haka ina ganin sai dai a b'atar da ita kinga idan aka b'atar da ita shikkenan kin huta,kin yada kwallon mangoro". Da k'er Safiyya ta aro dauriya ta aza akanta jin ance Yaya Deen yana matuk'ar son K'anwarta harma da sha'awar ta,wani kishi mai zafi ya tokare mata a k'irjinta. " Boka yanzu kawai ayi musu farrak'un saboda idan an b'atar da ita wataran kuma idan suka hyi'u fa don muddin hakan ta faru to babu abinda ba zaisa in kashe Jamila ba,Amman yanzu kawai ayi musu farrak'u." Dariya ya k'ara bugawa sannan ya ce"Muguwa wato sai ki kashe ta?har kin tunomin d'an uwana dana luma mai wuk'a saboda kawai yaci bashi na bai bani kud'ina ba shine kawai na yanke shawarar kaishi bar zahu." Abu kuwa kallon Safiyya ta ke yi tana kallon boka,don bata tab'a zata Safiyya zata iya kashe mutum ba ballan tana ma ace y'ar uwarta uwa d'aya uba d'aya. "Yarinya kisha kuruminki yau yau d'innan za'a yi musu farrak'u ya ji idan bai Aureki ba zai iya mutuwa don haka ya zama lallai ya Aureki,Kuma inason yanzu ba anjima ba indai kinason burinki ya cika na zama matar waccen masoyin na ki?to sai na yi amfani da ke na d'an d'ani abinda angonki bai fara d'an d'ana ba." Kad'anne ya rage Safiyya bata kurma uban ihu a wajen ba, don jin furucin arnan bokan,Amman sanin a inda ta ke sai ta maze,Tana had'o kalamai da k'er kamar zata had'iyi zuciya ta mutu ta ce"Na amince in dai zan samu biyan buk'ata ." Ta ajje mai kud'in da ya buk'ata,shi kuwa sai murmushi ya ke yi A ta k'aice dai Boka shi ya fara sanin Safiyya a matsayin Mace,Sannan ya barbad'a mata wani abu a wajen wanda shi kad'ai ne yasan manufar hakan. Safiyya ta yi mamakin yadda har ya yi ya gama bata ta shi daga dogon baccin da ta yi ba,don yana kirawota ta nemi hankalinta tarasa,ta kalli jikinta yadda ya yi mata kaca² da jini kamar an yanka rago,da k'er ta tashi tana had'a hanya, tana kuka har ta fiyo daga cikin bukkar d'akin,ba ta ga Abu ba sai ta fara waiwaye ko zata ganta. Ganin abu ta yi ta fito daga wata bukka tana gyara d'aurin zaninta,Mamaki da furgici yasa Safiyya zubewa a wajen don k'afa funta sun kasa d'aukarta,Abu ta taho da gudu ta d'ago Safiyya suka kama ta fiya babu alamar boka babu dalilinsa a haka suka tafi har titi Safiyya tana uban tangad'i kamar y'ar maye nan kuwa tsabar wahala ce tsantsagwaro. Yanke shawarar kai Safiyya gidanta ta yi duba da yadda boka ya yi wa Safiyya fata²,Sannan ta kirawo su Umma ta shaida musu ce wa Safiyya tana gidanta wai mai mashin ne ya kad'e ta ta suma. Sun yadda sosai da Abu don shekara kusan Bakwai tana musu Aiki ba'a tab'a samun matsala ba har ta yi Aure,don haka suka d'unguma zuwa gidan Abu don duba d'iyar tasu. Ni kuwa a lokacin muna d'aki nida Fatima Umma ta shigo tana fad'a mana da hanzari muka bisu, abun mamaki har da Yaya Deen shi da basu tab'a wata doguwar magana bq don jininsu bai had'u ba,don Aunty Safiyya bata da kunya ga turb'une fuska. B'oye mamaki na na yi har muka shiga mota muka tafi dubota,Yaya Deen kuwa sai rawae jiki ya ke yi ba tare da ya kalleni ba tun da muka shiga motar,idan kuwa ada ne muddin muka fita unguwa koda dasu Umma ne haka zai juya glass d'in motar ya yi ta b'ingira dariya yana tsokana ta. Da rawar jiki ya shiga d'akin tun kafin a yi mishi iso,Ita kuwa Abu k'ara k'arfafa mishi guiwa ta ke yi wajen ce wa"Ka shi ga can ciki tana k'urya saboda iska shiyyasa da aka shigo da ita na ce a kaita cen". Wani malulun bak'in ciki ne ya ya tokareni alokacin dana ga Yaya Deen yana rik'e hannun Aunty Safiyya yana mata sannu ita kuwa sai wani kukan shagwab'a ta ke yi. Fatima kuwa kallon Auntu Safiyya ta yi ganin duk k'afar ta jini ne,Ai kuwa da sauri Abu ta rufe k'ar Safiyyar don gudun kada asirinsu ya tonu,basu san tuni Fatima ta dad'e da gano abinda ya faru Da Safiyyar ba,don Allah ya yi wa Fatima baiwar gane duk wani mutun mara gaskiya don tana shigowa ta gane don baiwar Fatima tana da yawa. Sai kuwa Yaya Deen ya ce"Umma mu tafi da ita gida don ta samu kulawa sosai don nan akwai zafi Sosai don bana son Matata ta shiga wani hali. *Kuyi hakuri kunsan bani da lfy ne na samu Miscariage so shiyyasa na yi tyiping kad'an*. *Ummu Maher* Miss green ce. Sai kuwa na jiyoshi *JÂMÊÊLÊR* Na💖 (Ummu Maher)Miss green💚 *MATAR BASH*💡 My Wattpad:Rabiatu333 🟨8&9 Wani gumi ne ya shiga karyomin ta ko INA jin furucin Yaya Deen akan Yaya ta,ga wani kishi da naji yana Neman kassarani duk kuwa akan furucin da naji Yaya Deen ya yi ne,bayan mun koma gida kuwa hankali na ne ya nemi barin jikina yadda naga Yaya Deen yana lallab'a Aunty Safiyya har da ce mata dole a yi maganin zazzab'in nan saboda kar suyi aure ta na yi,don asatinnan zai kawo kud'in saka rana Dana komai kuma ba yaso bukin ya wuce wata 1kacal. Fatima ce ta ringa tausar zuciya ta akan inyi hak'uri komai yayi farko yana da k'arshe, hakan ce kuwa ta faru dani domin a kaso 100 acikin son da na ke yiwa Yaya Deen sai naji bai fi kaso 40 ba,don arayuwa ta na tsani mutum mayaudari maci amana. Ai kuwa kwana uku da faruwar wannan al'amari naje gaida Babanmu naji yana fad'awa Mamanmu CE wa,wai jiya Yaya Deen ya kai kud'in Aure har da nasaka rana kuma nan da wata 1 za'ayi bukin,duk da gabana ya fad'i sosai da jin maganar Amman ban nuna ba ko alamu. "Fatima kinga cin amanar da akayi min ko?wai yaya ta uwa d'aya uba d'aya Amman ki duba kiga irin cin amanar da ta aikata a gareni ko?" Wallahi haryau ban San me na aikatawa Yaya Safiyya ba take nunamin muguwar tsana haka ba,a iya sanina ban tab'a k'inta ko muzanta mata ba,Amman ki duba kiga yadda ita kullum ta ke nema taci min mutunci,ta hanani farin ciki don ita ta samu farinciki. "Kiyi hakuri Jamila tabbas Yayarki taci amanarki sai dai kiyi hakuri ki fawwalawa Allah shi zai shige miki gaba aduk inda kike,kuma Allah zai fito miki da Wanda yafi Yaya Deen da komai,nidai ina rok'onki da kada ki nunawa kowa sirrin dake cikin zuciyarki,yin hakan shi zaisa kibawa Yayarki kunya." To da wannan dad'ad'an maganganun na Fatima ne zuciyata ta samu salama sosai don sai in kwana in yini banyi tunanin wani Yaya Deen ba,balle Yaya Safiya wacce ayanzu gaba ki d'aya ta zama busy saboda bikinta daya gabato,kullum suna yawo ita da Sabuwa narasa inda suke zuwa. Yadda Yaya Deen ya shareni ya fita daga rayuwata nima kuwa hakance ta faru a nawa b'angaren don ko kallonshi yanzu ba na yi,don akwai ranarda suna zaune shida Yaya Safiyya suna zance naje wucewa,ko kallonsu banyi ba na fara tafiya zan wucesu,kawai sai naji muryar Yaya Safiyya tana cewa,ke Jamila wani irin iskanci ne muna zaune Zaki wuce ba tare da kin tsaya kin gaida Yaya Deen ba,ko kuwa shima mugun halin irin naki zaki gwada mai?. Ban saurareta ba na k'ara kama hanya zan wuce tasha gabana tare da d'aga hannunta ta wanke ni da wani mahaukacin mari wanda sai Dana ga wucewar taurari ta masu haske,sannan ta nuna ni da ytsanta tace"daga yau sai yau duk ranar da kika k'ara wucewa muna zaune baki gaishe muba to wallahi na lahira ma yafi ki jin dad'i. Zuciya tace ta tsinke na kalli Yaya Deen naga ko kallo ban ishe shi ba, wani malulun bak'in ciki ya tsaya min a k'ahon zuciyata,ban k'ara magana ba na shige cikin gida ina kuka,koda Mama ta tambayeni ban bata amsa ba kawai sai na fad'a d'akinmu INA kuka mai tsuma zuciya. Fatima CE ta ringa rarrashi na,akan da na yi hak'uri kada kuma na sakata acikin raina har abin ya dameni,kuma idan nayi hak'uri ta kusa barin Gidan nan na dad'ewa ba. <★> Yau take ranar D'aurin Auren Yaya Safiyya da kuma Yaya Deen,idan ka gansu ko wannensu baki har kunne saboda murna,ya yinda ni kuma na ke cikin wani hali wani irin zazzab'i mai mugun zafi ne ya rufeni y'an buki sai sannu suke zubamin tare da tausayamin don ina shan wahala,Amman Yaya Safiyya ko kallon arzik'i ban isheta ba,saima kallon banza da take bina dashi. K'anwar Mama nace ta fad'awa Mahaifiyarmu aka kirawo min Family doctor d'inmu don yazo ya dubani,bayan ya gama dubani ne ya bani magani sannan na yi bacci,har akayi dinner aka kai amarya ban San me ke faruwa ba,domin kuwa inata bacci Fatima na kusa dani tana kallona tare da tausayamin. Sai k'arfe goma na dare na tashi,ina tashi Fatima ma ta tashi tana yimin sannu, abinci ta kawomin da ruwan tee harda maganina,sannan na tashi na rama sallolin da ake bina zuciyata tana yimin k'una yanzu shikkenan Aunty Safiyya ta Auri Yaya Deen?kuka ne naji ya kwace min Fatima ta ringa tausata har na samu na kwanta bacci. *Bayan kwana biyu* Itace kuma ranar da k'addarar Jamila ta soma. "Jamila!Jamila!!da sauri na fito daga cikin d'aki har ina had'a hanya don amsa kiran umman tawa,a farlo na sameta da wani Abu a cikin kwali Wanda ban San ko meye ba. " tashi ki shirya Fatima ta rakaki Gidan mami,don haka ake kiran Aunty Safiyya,ki kai mata wannan sak'on sannan ki tayata gyara kayan". To nace sannan na tashi zuciyata babu dad'i,don araina ban tab'a kawo zanje Gidan Aunty Safiyya da wuri ba, na samu Fatima ta fito daga wanka tana waya da Lamir,saurayinta ne Wanda suka had'u da shi ranar bikin Aunty Safiyya abokin Yaya Deen ne. Dariya nayi sannan na ce"Miss soyayya ta shi kiraka ni Gidan Aunty Safiyya,sauri tayi ta kashe wayar sannan ta ce"rufamin asiri yanzu Yaya Lamir ya CE min yana hanya sai dai idan ya tafi sai muje." "A'ah gwara ba tafi kada dare yayi idan yazo kya mik'amin gaisuwa". Kallon Gidan na farayi tun daga k'ofar gate d'in har ko'ina na Gidan, ina tuna ranar da Yaya Deen ya nunamin Gidan a wayarsa yana gayamin irin rayuwar da zamuyi a Gidan,wasu zafafan hawayene naji suna fito min har na shiga Gidan ban San na fito ba kawai sai ganina nayi a cikin Gidan. Tunda ta taho Deen ya hangota tun daga nesa tana takunta mai tattare da nitsuwa acikinsa,ya rasa me yake yi mai dad'i aduk sanda yaga Jamila sai yaji wutar sonta tare da sha'awarta Amman baya jin zai iya Gaya mata kuma aduk sanda yaganta sai yaji bazai tab'a iya yi mata magana ba. Ko kallonshi ban yi ba na yi shige wata ciki,sallama na ringayi a tsakiyar farlon babu Wanda ya amsa min,na shiga wani d'aki Wanda nake tunanin shine d'akin Aunty Safiyya,nanma babu kowa juyowar da zanyi kawai sai naga Yaya Deen daga shi sai boxer ajikinshi,hankalina ya tashi sosai na tsorata da ganin Yaya Deen a haka,ban sanda na bud'e baki zanyi ihu ba kawai saiya shek'amin wani Abu a hancina,daganan ban k'ara sanin inda nake ba... Idan kin karanta don Allah kiyi share.👏🏻 Vote Share & Comments *_JÂMÊÊLÊR_* Na💖 (Ummu Maher)Miss green💚 *MATAR BASH💡* Follow me on watt pad *Rabiatu333* 🟨10&11 Wannan ita ce rana mafi muni Dana fuskanta arayuwa ta,ranar da bazan tab'a mantawa da ita ba domin kuwa aranar ne Yaya Deen ya yimin fyed'e a gidansa kuma a d'akin Yaya ta Safiyya,kuka ne yaci k'arfin Jamila alokacin da take bawa K'awarta Jamila labarinta. "Kiyi hak'uri Namesake komai yayi farko yana da k'arshe tun kafin ki k'arasamin labarinki tausayinki ya k'ara ninkuwa a zuciyata,Amman Yaya Deen bai kyautawa rayuwarsa ba". " Hmm Jamila ki tsaya kiji k'arshen labarina domin kuwa haryanzu ban kai miki inda nakeson kaiwa ba,rayuwata cike ta da abin al'ajabi da ban mamaki,rashin tausayi,cin amana,tsantar yaudara. Fatima tayi kuka ranar kamar ranta zai fita,saboda yadda na bata labarin yadda Yaya Deen ya b'atamin rayuwa,Naso na sanar da iyaye na abinda ya faru Amman tuno abinda zai faru nayi hak'uri, na danne abinda yake cikin zuciyata,na yi jinya ta a d'aki har na warke,tun daga wannan ranar ne na shiga cikin k'unci na rame na lalace duk akan fyed'e da Yaya Deen ya yi min. Ana cikin haka ne fa na fara wani irin zazzab'in dare kullum sai na yi shi,ga tashin zuciya na shaidawa Fatima tace muje asibiti don ganin likita,har mukaje asibitin gabana yana fad'uwa don ban San me zai faru ba,ga wani irin fad'uwar gabar da na keji kiran sunan Allah na fara yi har sakamakon gwajin ya fito. Shingin kad'an in fad'i jin mummunan labarin da Likitan yake fad'amin wai inada k'ara min ciki,harda rubutamin scanning. Fatima ma kuka ta ke yi,don sai yanzu take Dana sanin b'oye maganar da sukayi ita da Aminiyarta Jamila,da k'er muka dawo gida dukkanin zuciyoyinmu kamar zasu fashe tsabar tunani da fargaba,muna shigowa Gidan da Yaya Deen muka fara cin karo alokacin da ya ke bud'ewa Aunty Safiyya mota,tana d'auke da d'an k'ara min cikinta daya fara fitowa,sai wani iyayi take koda ta hango mu nida Fatima muna tahowa saita k'ara shigewa jikin Yaya Deen tana wani shagwab'a. Kallonsu nayi cikin wata kwalla da ta fara fitowa daga idanuwa na tausayin kaina,don na lura Yaya Deen ko tunanin abinda ya yimin ba yayi,ya yi k'ibarsa ya sake wani irin fari kamar bature ko balarabe,Fatima CE ta fara wucewa ko agaishesu ba ta yi ba,ta yi wucewarta nima hakan ne a nawa b'angaren don ko kallo basu isheniba,inajin Aunty Safiyya tana tsaki tare da zagina,ni kuwa ko juyowa ban yiba nabi bayan Fatima,don jin kaina na ke yi yana juyawa tsabar damuwa,ina shiga d'akinmu na mak'ale jikin bango sai sannan wasu zafafan hawaye suka zubomin,sai asannan Fatima ta shigo tare da Mamanta. Gaba nane ya k'ara bugawa lokacin da na ji Maman Fatima tana yimin magana kamar haka. "Yanzu Jamila meye amfanin b'oye wannan maganar da ki ka yi,ni banga abin buyewa acikin wannan maganar ba,yanzu wa gari ya waya da kin fad'amin idanma ba zaki iya gayawa Mamanki ba ai da sai ki gayamin in gaya mata". Tunda ta fara yimin magana kuka kawai na ke yi don jin maganarta ta na ke yi kamar wata ta tsuniya don abinda ya faru ya Riga da ya faru don babu amfanin sake mai_mai ta ta. " yanzu lokaci ya k'ure na gayawa iyayenki,Amman babu Wanda zai fitar dake sai Allah,sai Shamsudden don koma menene shine ya janyo miki shi,don haka dole ne yanzu ya Sani ba sai an b'ata lokaci ba kamar yadda ku kayi daga farko. Haka kuwa a kayi Maman Fatima ta nemi alfarma wajen fad'awa Mamana CE wa zamu rakata unguwa, mama ta yi mana a dawo lfy. Fatima ce ta kirawo mana shi don ta tambaye shi ko yana gida ne,ya ce eh yana gida yanzu ya dawo daga kai Safiyya asibiti,Fatima ta ce mai to gasunan Amman da zai yiyu ya zauna a babban falonsa na bak'i ummanta CE ta ke son yi mai magana akan maganar abokinshi da ya ke son shi,nan da nan ya bada ammuna yana mai sake godewa Allah daba maganar da ya yi tunani ba ce don haka ya tashi ya kashewa Safiyya Ac ba ki d'aya sannan ya fita,yana Fita Safiyya ta fito cikin sand'a_sand'a ta bishi haka kawai taji bata yadda da wannan maganar ba don ta gane da Mmn fatima ya ke waya. Ummu Maher ce _*🍇JÀMÈÈLÈR*_🍇 *💖NA* _Ummu Maher(miss green💚🌱_ *MATAR BASH💡* Follow me on wattpad *Rabiatu333* 12🟨13 Sosai Umma ta yi nisa a maganar ta, tunkafin Ta k'arasa maganar da ta ke yi Yaya Deen Ya yi saurin ta shi tsaye yana muzurai k'asan zuciyarsa kuma tausayin Jamila ya ke ji Amman bazai iya zuba idanu yana ji yana gani ba mutuncinsa ya zube don haka cikin kakkausar Murya ya ce. "Gaskiya ni bansan da wannan maganar ba don ni rabona da ita tun kafin bikinmu da Safiyya,Amman na yi mamakin jin wannan zancen don Jamila ta zubarwa da su Abba mutunci...... K'arya ka ke Yaya Deen,suka jiyo muryar Jamila tana faman kuka kamar iyayenta sun mutu,Wallahi tallahi Kaine kayi min ciki domin ban tab'a aikata b'arna ba Kaine kayi min fyed'e a ranar da nazo Gidan nan Mama ta aikoni kawowa Matarka sak'o." Da k'er ta kai maganar tana numfarfashi,da sauri Umma ta rik'eta tana gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,Fatima ma tana taya ta da sauri Umma ta ruk'o hannun Jamila suka fito daga gidan. Da sauri Yaya Deen ya fito daga main farlonsa duk ya had'a gumi kana ganinsa kaga Mara gaskiya. Safiyya da ke lab'e ta ji komai don haka ta share hawayen da suka zubo mata tana sauri don ta koma d'akinta,Muryar Deen ta ji a bayan ta yana kiranta,Cak ta tsaya awajen harya k'araso ya juyo da ita yana fuskantar ta. "Yaya Deen da gaske ne Kaine ka yiwa Jamila ciki?". A bazata maganar tazo masa don haka ya fara had'a gumi yana kaicon halinsa nason zuciya da cutar k'anwarsa mafi soyuwa a rayuwarsa. Ni kuwa Ummu Maher Na ce so ko cuta.😏☹️ Da k'er ya had'e miyau d'in bakinsa wajen fara magana," Safiyya kinsan halina kinsan abinda zan Aikata wallahi ba nine na yi mata fyed'e ba,nima na yi mamakin irin sharrin da Umma ta yimin don dama matar bata kwanta min ba,tana da shishshigi sosai shiyyasa ban fiya shiga harkarta ba shiyyasa yanzu ta tsaneni tazomin da wannan zancen,Amman zanje har gida in San ta yadda zan Fara magana dasu Baba da Mama. "Amman kafin nan inason yin magana da Jamila....." "Wat wallahi baka isa kayi magana da Jamila ba su San yadda zasuyi wajen k'ara yi maka sharri to wallahi baza kaje ba,kuma tunda abin yazo da haka dole ne musan abinyi. Deen da aikin asiri ya ke Kansa har yanzu don duk abinda Madam Safiyya ta tsara agidan shi a ke yi don har mutane sun fara gane yadda Deen ya zama mijin tace. Dole yanzu Jamila tana shirya wani abin domin kuwa ni nasan ba zata zauna ta yi shiru haka ba,dole ta sanar da wannan maganar Amman nasan koda zatayi maganar to ba ayau ba sai zuwa gobe mu kuma a Daren nan zamu aikata duk wani shirinmu. Sulolo Deen ya yi kamar wani wawa yana kallon Safiyya Jan hannunsa ta yi suka shiga d'aki. Da k'er Umma ta shawo kan Jamila don ma Allah ya tai makesu da suka dawo Mama bata nan ta bada sak'o a gaya musu cewa taje dubiyar y'ar yayarta da ta haihu a kayi mata operation. Baccin wahala ne ya yi awan gaba da ita Umma da Fatima suna kallon ta suna tausayawa rayuwarta don sun San Halin Jamila ba zata tab'a k'arya ba,Fatima CE ta k'ara shaidawa Ummanta cewar tabbas Deen d'in ya aikata haka duba da irin abubuwan da ya ringa yi mata tun kafin yayi Aure da yadda Auren ya koma kan Safiyya. Sai dare sannan na tashi da wani irin mummunan mafarki wai wasu mutane suna bina. Da alama mutanen Gidan sun da d'e da bacci abin mamaki koda na duba a gogo k'arfe 9 na dare ba wani dare ne yayi sosai ba. Farlo na fito na zaunq har yanzu zuciyata babu dad'i Allah² na ke safiya ta yi don koma menene masu iya magana sunce ranar wanka ba'a b'oyen cibi. Ruwa na gani kan fridge mai sanyi da alama kuma wanine ya d'auko bai samu damar sha ba har ya yi bacci,don haka na d'auko na kafa kai a gorar ruwan sai da na shanye ruwan tas sannan na ji wani irin jiri yana d'iba ta ban Ankara ba sai da naji na fad'i saman kujerar da ke farlon. Deen da Safiyya suna d'auko Jamila suka fara tafiya akan titi suna sharara gudo,yadda Deen yasan gari shiyyasa kwata kwata baibi titi ba sai da sukayi nisa sosai,Y'an sanda kuwa masu patrol suka tsayar dasu don bin cike... *MISS GREEN ce✍🏼* _*🍇JÂMÊÊLÊR*_🍇 *💖NA* _Ummu Maher(Miss green💚🌱_ *MATAR BASH💡* Follow me on wattpad *Rabiatu333* 14🟨15 .......A matuk'ar tsorace Deen da Safiyya suka kalli junansu ganin y'an sanda sunyi cirko cirko agabansu hanjin cikinsu ya kad'a,lokaci d'aya Wata irin zufa mai zafi ya fara karyowa ko wannensu,lokacin da y'an sandan suka lek'o su biyu ko wanne daga jikin windows d'in suna k'are musu kallo tare da nazartarsu. Daga cen d'aya b'angaren wani d'an sanda Ya ce. "Sir" Da sauri suka juya suna kallonshi don jin me zaice. "Sir ga wani mun kamashi da hudar iblis da daddaren yana Neman tsere da su" ya fad'i hakan yana numfashi don da alama ya sha wuya sannan ya kamasa,kuma da alama yaron d'an masu kud'i ne. To fa ganin Y'an sandannan sun tafi wajen wancen me laifin sai kuwa su Deen da Safiyya suka saki murmushi tare da juya motar zuwa wata hanyar. Sunyi tafiya me Nisan gaske a wannan Daren,ko tsoro ba sa ji kodon zuciyarsu ta k'ek'ashe ne oho? Wani tafkeken ruwa naga sun nufa da alama ruwan ruwan me matuk'ar girma ne,don haka Deen ya fito Shida Safiyya suka d'auko Jamila a hankali har suka k'ara sa wannan tafkeken kogin suka jefar da ita saida suka wuwulata har sau uku yadda zata shiga ruwan sosai sannan suka cillata. Da sauri suka shiga cikin motar suka bar wajen cikin sauri don kada wani ya kamasu. Mlm Bashir ne a gefen babban wani ruwa yana aikinsu irin na Malamai Amman fa ba na tsibbo ba,wata baiwar Allah zai had'awa maganin Haihuwa,kuma da wata itaciya za'ayi aikin acikin ruwan take. Koda yaga ba zai samu daga bakin ruwan ba kawai sai ya saka kayan ruwansa da ya ke sakawa aduk lokacin da zai yi irin wannan aikin. Dube_dube ya ke acikin ruwan har Allah yasa ya sameta,sai dai me?Mutum ya ji yana tab'awa dai dai jikin Y'ar bishiyar da ke cikin ruwan. Ya tsorata sosai Amman da yake a shirye yake,don Mlm Bashir baya wasa da addu'ah,don haka ya fara janyota har Allah yasa ya fito daga cikin ruwan. Masha Allah!abinda Mlm Bashir kenan ya fad'a ganin kyakyawan budurwa,sai da ya kalli k'afafunta ne yaga jini na zuba sosai kodon da tana cikin ruwa ne oho?. Da sauri ya saka ta acikin motarsa sannan yayi hanyar babban asibiti da ke jihar Bauchi,Suna shiga likitoci suka karb'eta hannu bibbiyu don sun San Mlm Bashir mutum ne Babba Wanda ajihar gaba kid'aya ake ji dashi don Mlm ne Wanda yasan takan magani kaka_kala. Sai da aka samu kamar 1hr sannan suka fito mode d'insu gaba kud'aya ya canza. Sun shaidawa Mlm MATAR tana da ciki,harma tayi b'ari sai dai har yanzu bata San inda kanta ya ke ba. Dai dai nan Jamila ta fashe da wani irin kuka tana kallon namesake d'inta sannan ta ce in tak'aice miki sai da nayi kwana d'ai_d'ai har bakwai sannan nasan inda kaina ya ke. Bayan na warke tsaf bisa kulawar likitoci da Matan Mlm don Mlm ya basu duka labarin abinda ya faru. To tun daga nan na koma Gidan Mlm da zama,in tak'aice miki Jamila sai da nayi wata 1 agidan Mlm sannan na fara sakin jikina,don suna bani kulawa Sosai,don Amaryar Mlm macece mai matuk'ar kirki da Jan mutane ajiki. "Kuma Jamila kin k'ara jin maganar gida kuwa?". "Hmm". "Tunda ganan ban k'ara jin labarin gidaba,sai dai har y'an gida ba,Amman ina matuk'ar jin tausayin halinda Masoyana zasu shiga musammam Mama,Baba,Fatima,da Ummanta". Kuka sosai Jamila ta fashe da shi,Namesake d'inta na rarrashinta. " Hmm Jamila kin gama naki labarin saura labarina domin idan kikaji nawa naki ba komai bane". To sai Ku biyoni don jin labarin Jamila 2 itama. *Miss green ce* *_JÂMÊÊLÊR_* Na💖 (Ummu Maher)Miss green💚 *MATAR BASH💡* Follow me on watt pad *Rabiatu333* 🟨10&11 Wannan ita ce rana mafi muni Dana fuskanta arayuwa ta,ranar da bazan tab'a mantawa da ita ba domin kuwa aranar ne Yaya Deen ya yimin fyed'e a gidansa kuma a d'akin Yaya ta Safiyya,kuka ne yaci k'arfin Jamila alokacin da take bawa K'awarta Jamila labarinta. "Kiyi hak'uri Namesake komai yayi farko yana da k'arshe tun kafin ki k'arasamin labarinki tausayinki ya k'ara ninkuwa a zuciyata,Amman Yaya Deen bai kyautawa rayuwarsa ba". " Hmm Jamila ki tsaya kiji k'arshen labarina domin kuwa haryanzu ban kai miki inda nakeson kaiwa ba,rayuwata cike ta da abin al'ajabi da ban mamaki,rashin tausayi,cin amana,tsantar yaudara. Fatima tayi kuka ranar kamar ranta zai fita,saboda yadda na bata labarin yadda Yaya Deen ya b'atamin rayuwa,Naso na sanar da iyaye na abinda ya faru Amman tuno abinda zai faru nayi hak'uri, na danne abinda yake cikin zuciyata,na yi jinya ta a d'aki har na warke,tun daga wannan ranar ne na shiga cikin k'unci na rame na lalace duk akan fyed'e da Yaya Deen ya yi min. Ana cikin haka ne fa na fara wani irin zazzab'in dare kullum sai na yi shi,ga tashin zuciya na shaidawa Fatima tace muje asibiti don ganin likita,har mukaje asibitin gabana yana fad'uwa don ban San me zai faru ba,ga wani irin fad'uwar gabar da na keji kiran sunan Allah na fara yi har sakamakon gwajin ya fito. Shingin kad'an in fad'i jin mummunan labarin da Likitan yake fad'amin wai inada k'ara min ciki,harda rubutamin scanning. Fatima ma kuka ta ke yi,don sai yanzu take Dana sanin b'oye maganar da sukayi ita da Aminiyarta Jamila,da k'er muka dawo gida dukkanin zuciyoyinmu kamar zasu fashe tsabar tunani da fargaba,muna shigowa Gidan da Yaya Deen muka fara cin karo alokacin da ya ke bud'ewa Aunty Safiyya mota,tana d'auke da d'an k'ara min cikinta daya fara fitowa,sai wani iyayi take koda ta hango mu nida Fatima muna tahowa saita k'ara shigewa jikin Yaya Deen tana wani shagwab'a. Kallonsu nayi cikin wata kwalla da ta fara fitowa daga idanuwa na tausayin kaina,don na lura Yaya Deen ko tunanin abinda ya yimin ba yayi,ya yi k'ibarsa ya sake wani irin fari kamar bature ko balarabe,Fatima CE ta fara wucewa ko agaishesu ba ta yi ba,ta yi wucewarta nima hakan ne a nawa b'angaren don ko kallo basu isheniba,inajin Aunty Safiyya tana tsaki tare da zagina,ni kuwa ko juyowa ban yiba nabi bayan Fatima,don jin kaina na ke yi yana juyawa tsabar damuwa,ina shiga d'akinmu na mak'ale jikin bango sai sannan wasu zafafan hawaye suka zubomin,sai asannan Fatima ta shigo tare da Mamanta. Gaba nane ya k'ara bugawa lokacin da na ji Maman Fatima tana yimin magana kamar haka. "Yanzu Jamila meye amfanin b'oye wannan maganar da ki ka yi,ni banga abin buyewa acikin wannan maganar ba,yanzu wa gari ya waya da kin fad'amin idanma ba zaki iya gayawa Mamanki ba ai da sai ki gayamin in gaya mata". Tunda ta fara yimin magana kuka kawai na ke yi don jin maganarta ta na ke yi kamar wata ta tsuniya don abinda ya faru ya Riga da ya faru don babu amfanin sake mai_mai ta ta. " yanzu lokaci ya k'ure na gayawa iyayenki,Amman babu Wanda zai fitar dake sai Allah,sai Shamsudden don koma menene shine ya janyo miki shi,don haka dole ne yanzu ya Sani ba sai an b'ata lokaci ba kamar yadda ku kayi daga farko. Haka kuwa a kayi Maman Fatima ta nemi alfarma wajen fad'awa Mamana CE wa zamu rakata unguwa, mama ta yi mana a dawo lfy. Fatima ce ta kirawo mana shi don ta tambaye shi ko yana gida ne,ya ce eh yana gida yanzu ya dawo daga kai Safiyya asibiti,Fatima ta ce mai to gasunan Amman da zai yiyu ya zauna a babban falonsa na bak'i ummanta CE ta ke son yi mai magana akan maganar abokinshi da ya ke son shi,nan da nan ya bada ammuna yana mai sake godewa Allah daba maganar da ya yi tunani ba ce don haka ya tashi ya kashewa Safiyya Ac ba ki d'aya sannan ya fita,yana Fita Safiyya ta fito cikin sand'a_sand'a ta bishi haka kawai taji bata yadda da wannan maganar ba don ta gane da Mmn fatima ya ke waya. Ummu Maher ce _*🍇JÀMÈÈLÈR*_🍇 *💖NA* _Ummu Maher(miss green💚🌱_ *MATAR BASH💡* Follow me on wattpad *Rabiatu333* 12🟨13 Sosai Umma ta yi nisa a maganar ta, tunkafin Ta k'arasa maganar da ta ke yi Yaya Deen Ya yi saurin ta shi tsaye yana muzurai k'asan zuciyarsa kuma tausayin Jamila ya ke ji Amman bazai iya zuba idanu yana ji yana gani ba mutuncinsa ya zube don haka cikin kakkausar Murya ya ce. "Gaskiya ni bansan da wannan maganar ba don ni rabona da ita tun kafin bikinmu da Safiyya,Amman na yi mamakin jin wannan zancen don Jamila ta zubarwa da su Abba mutunci...... K'arya ka ke Yaya Deen,suka jiyo muryar Jamila tana faman kuka kamar iyayenta sun mutu,Wallahi tallahi Kaine kayi min ciki domin ban tab'a aikata b'arna ba Kaine kayi min fyed'e a ranar da nazo Gidan nan Mama ta aikoni kawowa Matarka sak'o." Da k'er ta kai maganar tana numfarfashi,da sauri Umma ta rik'eta tana gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,Fatima ma tana taya ta da sauri Umma ta ruk'o hannun Jamila suka fito daga gidan. Da sauri Yaya Deen ya fito daga main farlonsa duk ya had'a gumi kana ganinsa kaga Mara gaskiya. Safiyya da ke lab'e ta ji komai don haka ta share hawayen da suka zubo mata tana sauri don ta koma d'akinta,Muryar Deen ta ji a bayan ta yana kiranta,Cak ta tsaya awajen harya k'araso ya juyo da ita yana fuskantar ta. "Yaya Deen da gaske ne Kaine ka yiwa Jamila ciki?". A bazata maganar tazo masa don haka ya fara had'a gumi yana kaicon halinsa nason zuciya da cutar k'anwarsa mafi soyuwa a rayuwarsa. Ni kuwa Ummu Maher Na ce so ko cuta.😏☹️ Da k'er ya had'e miyau d'in bakinsa wajen fara magana," Safiyya kinsan halina kinsan abinda zan Aikata wallahi ba nine na yi mata fyed'e ba,nima na yi mamakin irin sharrin da Umma ta yimin don dama matar bata kwanta min ba,tana da shishshigi sosai shiyyasa ban fiya shiga harkarta ba shiyyasa yanzu ta tsaneni tazomin da wannan zancen,Amman zanje har gida in San ta yadda zan Fara magana dasu Baba da Mama. "Amman kafin nan inason yin magana da Jamila....." "Wat wallahi baka isa kayi magana da Jamila ba su San yadda zasuyi wajen k'ara yi maka sharri to wallahi baza kaje ba,kuma tunda abin yazo da haka dole ne musan abinyi. Deen da aikin asiri ya ke Kansa har yanzu don duk abinda Madam Safiyya ta tsara agidan shi a ke yi don har mutane sun fara gane yadda Deen ya zama mijin tace. Dole yanzu Jamila tana shirya wani abin domin kuwa ni nasan ba zata zauna ta yi shiru haka ba,dole ta sanar da wannan maganar Amman nasan koda zatayi maganar to ba ayau ba sai zuwa gobe mu kuma a Daren nan zamu aikata duk wani shirinmu. Sulolo Deen ya yi kamar wani wawa yana kallon Safiyya Jan hannunsa ta yi suka shiga d'aki. Da k'er Umma ta shawo kan Jamila don ma Allah ya tai makesu da suka dawo Mama bata nan ta bada sak'o a gaya musu cewa taje dubiyar y'ar yayarta da ta haihu a kayi mata operation. Baccin wahala ne ya yi awan gaba da ita Umma da Fatima suna kallon ta suna tausayawa rayuwarta don sun San Halin Jamila ba zata tab'a k'arya ba,Fatima CE ta k'ara shaidawa Ummanta cewar tabbas Deen d'in ya aikata haka duba da irin abubuwan da ya ringa yi mata tun kafin yayi Aure da yadda Auren ya koma kan Safiyya. Sai dare sannan na tashi da wani irin mummunan mafarki wai wasu mutane suna bina. Da alama mutanen Gidan sun da d'e da bacci abin mamaki koda na duba a gogo k'arfe 9 na dare ba wani dare ne yayi sosai ba. Farlo na fito na zaunq har yanzu zuciyata babu dad'i Allah² na ke safiya ta yi don koma menene masu iya magana sunce ranar wanka ba'a b'oyen cibi. Ruwa na gani kan fridge mai sanyi da alama kuma wanine ya d'auko bai samu damar sha ba har ya yi bacci,don haka na d'auko na kafa kai a gorar ruwan sai da na shanye ruwan tas sannan na ji wani irin jiri yana d'iba ta ban Ankara ba sai da naji na fad'i saman kujerar da ke farlon. Deen da Safiyya suna d'auko Jamila suka fara tafiya akan titi suna sharara gudo,yadda Deen yasan gari shiyyasa kwata kwata baibi titi ba sai da sukayi nisa sosai,Y'an sanda kuwa masu patrol suka tsayar dasu don bin cike... *MISS GREEN ce✍🏼* _*🍇JÂMÊÊLÊR*_🍇 *💖NA* _Ummu Maher(Miss green💚🌱_ *MATAR BASH💡* Follow me on wattpad *Rabiatu333* 14🟨15 .......A matuk'ar tsorace Deen da Safiyya suka kalli junansu ganin y'an sanda sunyi cirko cirko agabansu hanjin cikinsu ya kad'a,lokaci d'aya Wata irin zufa mai zafi ya fara karyowa ko wannensu,lokacin da y'an sandan suka lek'o su biyu ko wanne daga jikin windows d'in suna k'are musu kallo tare da nazartarsu. Daga cen d'aya b'angaren wani d'an sanda Ya ce. "Sir" Da sauri suka juya suna kallonshi don jin me zaice. "Sir ga wani mun kamashi da hudar iblis da daddaren yana Neman tsere da su" ya fad'i hakan yana numfashi don da alama ya sha wuya sannan ya kamasa,kuma da alama yaron d'an masu kud'i ne. To fa ganin Y'an sandannan sun tafi wajen wancen me laifin sai kuwa su Deen da Safiyya suka saki murmushi tare da juya motar zuwa wata hanyar. Sunyi tafiya me Nisan gaske a wannan Daren,ko tsoro ba sa ji kodon zuciyarsu ta k'ek'ashe ne oho? Wani tafkeken ruwa naga sun nufa da alama ruwan ruwan me matuk'ar girma ne,don haka Deen ya fito Shida Safiyya suka d'auko Jamila a hankali har suka k'ara sa wannan tafkeken kogin suka jefar da ita saida suka wuwulata har sau uku yadda zata shiga ruwan sosai sannan suka cillata. Da sauri suka shiga cikin motar suka bar wajen cikin sauri don kada wani ya kamasu. Mlm Bashir ne a gefen babban wani ruwa yana aikinsu irin na Malamai Amman fa ba na tsibbo ba,wata baiwar Allah zai had'awa maganin Haihuwa,kuma da wata itaciya za'ayi aikin acikin ruwan take. Koda yaga ba zai samu daga bakin ruwan ba kawai sai ya saka kayan ruwansa da ya ke sakawa aduk lokacin da zai yi irin wannan aikin. Dube_dube ya ke acikin ruwan har Allah yasa ya sameta,sai dai me?Mutum ya ji yana tab'awa dai dai jikin Y'ar bishiyar da ke cikin ruwan. Ya tsorata sosai Amman da yake a shirye yake,don Mlm Bashir baya wasa da addu'ah,don haka ya fara janyota har Allah yasa ya fito daga cikin ruwan. Masha Allah!abinda Mlm Bashir kenan ya fad'a ganin kyakyawan budurwa,sai da ya kalli k'afafunta ne yaga jini na zuba sosai kodon da tana cikin ruwa ne oho?. Da sauri ya saka ta acikin motarsa sannan yayi hanyar babban asibiti da ke jihar Bauchi,Suna shiga likitoci suka karb'eta hannu bibbiyu don sun San Mlm Bashir mutum ne Babba Wanda ajihar gaba kid'aya ake ji dashi don Mlm ne Wanda yasan takan magani kaka_kala. Sai da aka samu kamar 1hr sannan suka fito mode d'insu gaba kud'aya ya canza. Sun shaidawa Mlm MATAR tana da ciki,harma tayi b'ari sai dai har yanzu bata San inda kanta ya ke ba. Dai dai nan Jamila ta fashe da wani irin kuka tana kallon namesake d'inta sannan ta ce in tak'aice miki sai da nayi kwana d'ai_d'ai har bakwai sannan nasan inda kaina ya ke. Bayan na warke tsaf bisa kulawar likitoci da Matan Mlm don Mlm ya basu duka labarin abinda ya faru. To tun daga nan na koma Gidan Mlm da zama,in tak'aice miki Jamila sai da nayi wata 1 agidan Mlm sannan na fara sakin jikina,don suna bani kulawa Sosai,don Amaryar Mlm macece mai matuk'ar kirki da Jan mutane ajiki. "Kuma Jamila kin k'ara jin maganar gida kuwa?". "Hmm". "Tunda ganan ban k'ara jin labarin gidaba,sai dai har y'an gida ba,Amman ina matuk'ar jin tausayin halinda Masoyana zasu shiga musammam Mama,Baba,Fatima,da Ummanta". Kuka sosai Jamila ta fashe da shi,Namesake d'inta na rarrashinta. " Hmm Jamila kin gama naki labarin saura labarina domin idan kikaji nawa naki ba komai bane". To sai Ku biyoni don jin labarin Jamila 2 itama. *Miss green ce* 🍀✨🍀 *_JÁMÉÉLÉR_* 🍀✨🍀 *BOOK2* Labarin Jamila2 ~ Na ~ _*Ummu Maher(Miss green💚🌱*_ 16<<>>17 *Jihar Bauchi* .....Ni Y'ar asalin jihar Bauchi ce mahaifina mai kud'i ne sosai don yana 1 daga cikin mutane masu arzik'i wad'anda ake ji dasu a K'asarmu Nigeria kuma na kasance y'a d'aya tilo awajensa ya kuma d'auki son duniya ya d'oramin,Mahaifiyata ta rasu tun ina shekara5 ta sanadiyyar Haihuwa. Sai ya zamanto duk wata k'auna da uwa zata bawa Y'ar ta ina samu gun Mahaifina,akwai watarana da bazan tab'a mantawa da ita ba. Tun ina shekara 8 aka d'auramin Aure da K'anin Matar Mahaifina don bayan rasuwar Mahaifiyata Mahaifina ya yi Aure,sunanta Sakina su y'an asalin kano ne Amman a wani k'auye suke Fulani ne na asali. Mahaifina yaje Neman Aurenta har garinsu Amman fir suka k'i,in har yana son Y'ar su sai sun gindaya mai wad'ansu sharud'a idan ya cinye sharad'an to zasu bawa Y'ar su Aurensa. Hakan ce kuwa ta faru bayan ya nemi jin sharud'anne yaji abinda ya rud'a sa,wai indai yana son Sakina sai dai su Aura wa y'arsa suma d'ansu,wai don masu kud'i idan suka Auri y'ay'ansu mantawa suke dasu Amman indai har haka ta faru to dole su waiwayesu. Allah ya Sani ba haka suka bar Mahaifin Jamila ba wato Alhaji Bashir,don su Wad'annan kalar fulanin akwai asirce mutum. Yana ji yana gani suka d'auki Jamila suka bawa Harisu aka d'aura Aure,ita dai Jamila koda alokacin bata da wayo taji ana cewa ita aka d'aurawa Aure. Shi kuwa Harisu da wayonsa don alokacin ya kai shekara 20 aikuwa awannan lokacin Alhaji ya biyawa Harisu Kud'in makaranta ya fara zuwa. Kuma anbar cewa sai Jamila ta mallaki hankalin kanta sannan zata tare,su kuwa y'an uwan Sakinat musamman Mahaifiyar Harisu, don ita Y'ar uwace ga Babar Sakina don ita Sakina bata da k'annai Maza sai mata. Mahaifina yana da sha'awar kaini waje inyi karatu,don haka bayan aurensu da Sakina sai ya fitar da ni waje don yin karatu,kuma har yanzu Y'anwansa Dana Mahaifiyata babu Wanda yasan ya aurar dani don yana tsoron sanar dasu shiyyasa ya bari har Jamila ta mallaki hankalinta. Matar Babana kuwa ba k'aramin bak'in ciki ta shiga ba don jin Mahaifina zai kaini k'asar waje,nan ta fara sababi wai da Aure na za a kaini wata k'asar karatu. Bak'aramin artabu aka shaba har dai aka samo kanta ta hak'ura,na tafi k'asar India karatu. <> After 5years Bayan shekara biyar Wata budurwa na hango wacce ba zata wuce shekara 16 ba kyakkyawar gaske don kyawunta ya yi matuk'ar bani tsoro kamar irin y'an matan Indian nan,sai da na k'arasa kusa da ita sannan na hango Ashe Jamila ce,tana zaune kan gras tana karatu don ayanzu Jarrabar fita daga Secondary suke. Tayi nisa akaratunta sosai kawai sai ta jiyo wani k'amshin da bata tab'a jin k'amshi mai dad'in irin wannan ba,maze wa ta yi ta cigaba da karatunta Amman ina ji ta yi k'amshin yana k'ara kusanto ta. Wata murya taji naji mai dad'in gaske tana yimin sallama da sauri na d'aga kaina don ganin mamallakin wannan zazzak'ar muryar gaba na ne ya yanke ya fad'i ban sanma na tashi ba tsabar daburce wa kallon2 muka shiga yi dashi irin kallon k'udannan. _Mu had'u agaba don jin waye wannan_ *_MISS GREEN CE✍🏻_* 🍀✨🍀 _*JÀMÈÈLÈR*_ 🍀✨🍀 ~ Na ~ *_Ummu Maher(Miss green)💚🌱_* Wattpad Name @Rabiatu222 18<<>>19 .......murmushi ya sakarmin sai da dimfil d'in shi ya lotsa,nima ban San lokacin da na sakarmai murmushi ba. "How are u" Cikin cool voice d'insa mai dad'in sauraro,amsa masa na yi da. "I'am fine" Sai da gabansa ya fad'i tsabar jin muryar da bai tab'a ji ba,muka zauna kan wasu kujeru na makarantar irin na simintin nan,Kallo ya ke yi sosai,sai na tsinci kaina a matsanancin jin kunyarsa don haka na sunkuyar da kaina,sai na tsinkayo muryarsa ya na cewa. "Sunana Khalid" "Ni haifaffan garin Kano ne a k'asar Nigeria mahaifiyata da Mahaifina suna k'asar England a yanzu inada k'annai uku duk mata ni ne d'an fari a gidanmu, ayanzu ina a matsayin lecture a awata makaranra mai suna Borney high college. Kinji ta k'aitaccen tarihina,saura na ki nan nima na fara bashi ta k'aitaccen tarihina,a nan muka cigaba da hira. To fa tunda ga wannan rana sai muka zama kamar wa da k'anwa, matuk'ar banga Khalid ba ko bacci bana iyayi, wata rana har fita bakin makarantar na ke yi bakin makarantarmu don inga tahowarsa,Ashe yana cikin makarantarmu harda gidansa guda a quarter's,tunda na gane b'angaren da ya ke kullum ta bakin tagar d'akinsa na kezuwa nida wata k'awata Khausar,muyi ta lek'ensa,harya gano hakan ya wata rana ya ke cemin indai na zuwa b'angaren malamai saboda gudun matsala,nan dai muka cigaba da hirarmu don yanzu munshak'u sosai yadda d'aya ba zai iya rayuwa babu d'aya ba. Alhmdh yanzu mun gama jarrabawa sai shirye_shiryen tafiya gida,Dady na da Kansa yazo d'aukata,har mun shiga mota na ce"Dady banyi wa Malaminmu sallama ba yana da kirki sosai wallahi shine ya ke koyamin karatu",na fad'i hakan ina kallon fuskar Dady na,dariya ya yi sannan ya ce to je ki kirawomin shi". Ina fitowa na nufi sashen Malamai sai dai ina tuno da maganar da ya fad'a ya ce indai na zuwa sashen Malamai,wani Malaminmu na gani mai suna Salim khan d'an asalin k'asar India ne,na tambayeshi Sir Khalid,ya ce min ai ya koma bakin aikinsa tun jiya da daddare ya tafi. Kasa motsawa na yi,na fara tafiya har na shiga motar. "Lafiya Jamila"? " ina Sir d'in"? Mahaifina ne ya ke yi min wannan tambayar,shiru na yi kamar ba zanyi magana ba sai na ce. "Baya nan". Na fad'i hakan kamar zanyi kuka," Jamila akwai wata matsalar ne?"naga kamar za kiyi kuka?k'ak'alo murmushi na yi sannan na CE"babu komai Dady,muna isa Airport jirginmu ya tashi sai Nigeria,muna isowa gaba na ya dinga fad'uwa don bansan wainar da ake toyawa ba don rabona da gida tun bayan da na gama primary na tafi India karatu,tuni na ji kewar k'asata ya kamani,duk da ina ganin Dady na duk wata yana zuwa min visiting, Amman na yi missing d'in y'an uwan mahaifiyata tare da childhood d'ina. Tun daga nesa na hango matar Mahaifina fuskarta babu yabo babu fallasa,tare da wani saurayi suna kama sosai sai dai shi ya fita gogewa. Da murna ya tareni ban Ankara ba naji ya rungumeni,sai da numfashina ya kusa d'aukewa,na juyo cikin fushi na b'anb'areshi kawai sai na ji ya CE"haba Jamila kefa matata ta CE". Please kuyi hak'uri na yi tyip k'ad'an🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Fans na Jamila INA gaisheku aduk Inda kuka na gode da k'aunarku za kuga na bar GRP to kuyi min uziri wani Abu ne daban 🙏🏻🙏🏻. ঊঊঊঊঊঊ Miss green ce✍️ ঞঞঞঞঞঞ 🍀✨🍀 _*JÀMÈÈLÈR*_ 🍀✨🍀 ~ Na ~ _*Ummu Maher(Miss green)💚🌱*_ Wattpad @Rabiatu222 20<<>>21 ....cikin fushi Na ce"ban gane Miji na ba? ta ina na zama matarka ni ban Sanka ban tab'a ganinka ba?sai kawai ka ce ni matarka ce?saboda ka rainamin wayo,na kalli Dadyna na ce"Dady wannan kuma waye Mara hankalin da ya samu damar rungumeni a gabanka kuma baka yi masa magana ba?sunkuyar da kai Abbana ya yi,baice komai ba ya bud'e murfin motar ya shiga,nima a zuciye na shiga gaba na zauna,sai da muka shiga motar sannan suma suka shigo,harararsa kawai na ke yi shi kuwa sai kallona ya ke yi kamar maye. "Yanzu Alhaji wulak'ancin da y'arka ta yiwa k'anina Sooraj ya dace kenan?ko kuma so kake inyi magana kace na takurawa y'arka,shiyyasa ka d'ebeta ka kaita k'asar turai tunda ga Primary har secondary saboda kada in cinye maka y'arka,ni na tabba ta idan da ace kabar Baby a k'asar ta yi karatu to da sun saba da Sooraj,da bata yi mishi wulak'ancin da ta yi mishi ba,kuma kada ka manta Sooraj har yanzu yana nan amatsayin mijin Baby?" Don haka kajawa y'arka kunne ba'a wulak'anta min K'ani,shiru Dady ya yi har Matarshi tabar d'akin,yayi tagumi yanzu ta ina zai fara wannan abubuwan,daya San haka zai faru da bai aurawa y'arsa Sooraj ba,domin kuwa ayanzu Sooraj ya canza a yadda ya sanshi,don Sooraj yanzu shine shaye_shaye,bin mata,yawace yawace marasa dalili. Da daddare muna lunch a dining, Abbana na ya kirawo sunana a hankali, na amsa ina kallon sa don bai fiya kiran sunana ba saboda sunan Mahaifiyarsa ne,Shiyyasa ya ke kirana da Baby,shiyyasa yanzu da ya kirawoni da Suna Jamila azahiri na ji gabana ya dad'i don bai tab'a kiran sunana haka ba sai yau. "Baby ki kalli wannan na kusa da ke sosai?ya nuna min na kusa dani,na kau da kaina don tun ranar da ya rungume ni a airport ban sake yi mai magana ba,don na lura bashida mutunci ko kad'an ballantana wani Abu waishi kunya. Na kalleshi na ya tsina fuskata na juya ba tare da na ce komai ba,hakan ba k'ara min bak'anta ran,matar mahaifina ya yi ba dama shi kansa Sooraj d'in. " wannan yayanki ne sunanshi Sooraj,so you have to respect,kinji Baby na ki d'aukeshi a matsayin Brother na ki don haka na gama magana ta, yana fad'in haka ya haura sama ya barmu a wajen,nima kuwa ina ganin ya tashi na bi bayanshi don kwata_kwata bama shiri da Momi wato matar Abbana. Hankali na a matuk'ar tashe na dube wayar tawa har yanzu number switch off,shin me yake faruwa da Sadiq ne,ya tafi babu Sallama sannan gashi haryanzu number bata shiga.kiran Hamida ne ya shigo wayata k'awata ce tun daga Jss1 har zuwa ss3 a India, na d'auka munsha hira sosai,kusan sai yanzu zuciyata ta yimin dad'i tun zuwa na,don Gidan namu gaba ki d'aya babu dad'i sam,Abbana ba zama ya ke yi agidaba daga ni sai Sooraj da Momi. "Dady ina son zuwa Kano wajen Goggo yabi kakata ta wajen mahaifiya,Dady bai hana niba sannan ya bani kud'ad'e isassu ya ce gone za,a kaini Shopping in siyayya ta zuwa kano,na yi murna sosai don inason ganin dangin Mahaifiyata. Tunda Dady ya fad'awa matarsa tafiyata ta kasa ta tsare tana ta faman masifa,ni kuwa ko kallo bata ishe niba,don nagama yarda Momi bata sona,tunda na je India bata tab'a nemana ba da zummar ziyarta na,sai yanzu don na ce zanje dangin Mamana za tayi fad'a. ** " yanzu Adda abinda Mutuminnan suke yi acikin gidannan ya dace?haryanzu bai fad'awa y'arsa cewa ni Mijin ta bane,wai ita Y'ar so,to wallahi Adda darajarki kawai ya ke ci idan badon haka ba da na gama dashi wallahi,da shi da y'arsa don wallahi naga take_takensa so ya ke yi ya hanani Aurenta,to wallahi bai isa ba,yadda na keson yarinyar nan ko ke bana so haka?amatsayinki na Yayata,don yarinyar ta had'a komai na Y'a mace,don haka ki jawa mijinki kunne Donni bazan d'auki wulak'anci ba,yana fad'in hakan ya yi ficewarsa yana zuk'ar tsabar sigarinsa,yana busa ta sama sosai irin na y'an duniya. Ranar litinin da sassafe na fito cikin shirina,na tafiya ina janye da troly na,babu kowa a farlon sai masu aiki suna sanye cikin uniforms d'insu suna aiki. Sashen Dady na tafi ina zuwa shima Dadyn yana fito wa yana saka link d'in rigarshi,Momi na bayan shi rik'e da hularshi tana ganina ta had'e rai nima ban ce da ita komai ba,na gaishe da Dady sannan itama na gaisheta ko kallona ba ta yi ba,ballan tana in saka ran zata amsa Nima ban damu ba,na kalli Dady na da yake yimin dariya wai na tashi da sassafe duk zumud'in tafiyarne,sai nima nayi dariyar cikin shagwab'a ina b'oye fuska. D'aga wa Dady na hannu na ke kamar zanyi kuka,driven ya ja muka tafi muna fito wa na hango motar Sooraj shima yana shigowa da Alama,kuma ba agidan ya kwana ba don tun jiya banji motsin sa ba,na turo bakina tare da yin tsaki na juyar da kaina don ya tsuramin idanu sosai kamar wani soko. Sai k'arfe 12 muka isa kano,sai k'ofar Gidan kakannina na wajen Mahaifiyata,ban gane Gidan ba sai da driven gidanmu yace min Alhaji yana aikoshi nan Gidan sannan na gane,don Gidan ba ki d'aya an canza mishi fasali ya yi wani irin kyau,rabona da Gidan kusan shekara 7 kenan,bayan rasuwar Mahaifiyata, ina shiga Gidan na hau raba idanu don Gidan sashe uku ne yanzu,wata Y'ar tsuhuwa ce na gani ta fito daga wani new building me kyau,tana ta faman mita wai an fiya ajje mata takalmi k'ofar d'aki,koda ba'a gaya min ba nasan Goggo ce kakata,ta vayanta na je na rungumeta ina dariya. "Na shiga uku ni Rabi wani gamon na yi kuma....maganarta CE ta sark'e ganin Jamila tana dariya, koda ba'a gaya maka tasan jikarta nan don har yau Jamila kama ta ke da dangin mamarta. " Sadiq yau fito ka ganemin wai Jamila ce ko kuwa?" Donni tunda ubanta ya kaita k'asar fararen fata ban sake ganinta ba Amman ai Jinin baya b'ata,ni kuwa har lokacin dariya kawai na keyi ina tsaye ajikin troly na,dariya ta ce ta sark'e ganin sahibina Sadiq sanye da jallabiya,hannunsa an nad'eshi da bendeji,shima numfashin shine ya kusa d'aukewa ganin Sahibarsa Jamila, da gudu na taho na tungumesa sosai,Inna kuwa ta hangame baki ta kasa rufewa. *Miss green CE* Don Allah idan kika karanta kiyi min share Vote Share Comments. *_🍀JÁMÈÈLÈR🍀_* Ummu Maher(miss green)🍀 _Wattpad@Rabiatu222_ _22/23_ Saurin juyowa na yi na ce"Inna rufe bakinki kada b'era ya shiga?"Shi kuwa Sadiq k'ank'ameni ya yi sosai ina mamakin ya ya akayi Sadiq yazo gidannan alhalin ban bansan shi acikin dangin mu duk da bana zuwa garin mahaifiyata amman muna chart da wasu daga cikinsu". "Wai ni a ina kuka san junane Jameela?" don naga tunda kika shigo kuka rungume juna ni kuma kuka barni a tsaye,?Sadiq ne ya bata labarin komai da yadda muka k'ulla soyayya duk sai da ya bata labari. Murna awajen Inna ba'acewa komai,don daman abinda ta dad'e tana jirane Allah ya kawo mata,na had'a jikokinta Aure,nan kuma Inna ta ke bani labarin dan ganta ka ta Da Sadiq,da Mahaifinsa da Mahaifiyata,uwa d'aya uba d'aya suke,Baban sadiq shine babba sai Mahaifiyata. "Jameela nasan za kiyi zaton yaudararki zanyi a,ah tafiya ce ta kamani Allah ya yi banyi miki sallama ba saboda tashin hankalin da na ke ciki,mahaifiyata ce Allah ya yi mata rasuwa!" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yaushe ta rasu?" "Wata 1 kenan yanzu sanadiyyar haihuwa, ta rasu da kwana7 ni kuma na yi hatsari to shine ya hana ki ji komai,don sanda na yi hatsarin bansan inda kai na ya ke ba,amman kiyi hak'uri da abinda na yi miki..... "Don Allah kayi hak'uri wallahi ban san ma anyi rasuwa ba,amman ka yi hak'uri". Daga nan Masoyan suka cigaba da hirarsu cikin so da k'aunar junansu. *** Hutun Jameela a kano ya yi mata matuk'ar dad'i sosai,don tana samun kulawa so da k'auna awajen masoyinta harma da y'an uwanta,kulawar da bata samu a da ba yanzu ne ta ke samu,ga wata shak'uwa mai k'arfin gaske da ta shiga tsakaninsu. Sai dai abinda bata sani ba shine mahaifinta har ya fad'awa Inna tasan komai,sai dai fa Inna ta buga tsalle tace babu wanda ya isa ya yi wa y'arta Auren dole,wannan munafukin Auren ma du kuncesa domin kuwa babu yadda za'ayi su yadda da wannan had'in,babu yadda mahaifin Jameela ya iya, don haka yaja bakinsa ya yi shiru bai ce komai ba. Abinda bai sai ni shine?Matarsa tasan komai a game da abinda ya faru don duk wayar da ya ke yi tana lab'ewa ta ji me yake cewa,don haka ta shirya yadda zasu b'ullowa lamarin ita da k'aninta Sooraj. " kin san Allah babu wanda ya isa ya hanani Auren Jameela matuk'ar kuwa aka hanani to komai ma zai faru,don ko kece kika hanani Auren Jameela to ki kuka da kanki"!ya juyo yana nuna yayar tashi da hannunsa. Tana matuk'ar mamakin yadda aka yi Sooraj ya ke mugun son Jameela don ta yi imani Sooraj zai iya ki sa akan hanashi Auren Jameela. "Ni shawarata kawai idan ta dawo ku gudu da Jameela don hakan shine zai kawo k'arshen komai,don na fuskanci Uban nata mata lallab'ata kawai ya ke yi bason Auren ya ke yi ba." "Babu inda zan gudu da ita?ko su so?ko kada su so?bai dameni ba ya zama dole Jameela ta zama mallakina,haba shekara nawa ina dakon yawo da soyayyarta acikin zuciyata kuma na iya hak'ura da Aurena da ke kanta,to yanzu ya zama dole Jameela ta zama mallakina na gaya miki. Sai da ya kusa buge Yayar tashi don tsabar b'acin ran da Sooraj ya ke ciki,don a rayuwarsa babu abinda ya keso Irin Jameela,ko uwar da ta haifeshi bai damu da ita ba kamar Jameela,donshi a ganinsa Jameela ita ce rayuwarsa,don ko yanzu Jameela ta mutu to shima ya zama gawa. 🤔Ni kuwa Ummu Maher na ce,Son ma so wani k'oshin wahala. *** Yaya Sadiq zan cen da nake gaya maka ba k'arya bane Mahaifina ya yi min Auren dole,a tunaninsa ban sani ba don na dad'e da sanin wannan labarin kawai sai bana nuna wa ne,kuma nasan kud'in mahaifina ne ya rud'esu,Amman mahaifina ya dad'e da Aurar dani........ " What Jameela kin san me ki ke cewa kuwa?" Please kuyi hak'uri nayi tyiping kad'an rasuwa aka yimin ne.🙏🏻 Ummu Maher ce🤞🏻💚✍️ *_🍀JÁMÈÈLÈR🍀_* By _Ummu Maher(Miss green)🍀_ _Wattpad@Rabiatu222_ _24/25_ Destiny _______ Hankalin Sadiq ya tashi sosai akan maganar da na gaya masa,sai da mukayi sati 1 ni da Sadiq muna wasan b'uya don tunda mukayi wannan maganar dashi hankalinsa ya yi mummunan tashi don arayuwarsa bayan Allah da manzon da kuma iyayensa babu wata halitta da ya keso kamar Jamila akullum burinsa bai wuce yaga ya mallaki Jamila a matsayin matarsa ba. ....sai yamma ya sauka a garin Bauchi da kwatancen da Inna ta bashi har yazo katafaren gidanmu kai tsaye ya shiga gidan ba tare da wanu tunani ba,me gadin Gidan ne ya taso da sauri yana cewa"Tsaya Mlm ina zakaje?wajen wa za ka je aciki ayi maka iso?had'e rai Sadiq ya yi sannan ya ce megidan na ke nema,ko baya nanne?"A'ah yana nan bari in tambayo jira ni ina zuwa. "Alhaji ka yi bak'o a waje yace ayi mishi iso". " kace waye"? "To Alhaji" Ba,afi minti na ba ya dawo ya ce" wai Sadiq ne daga kano d'an uwansu Jamila" Alhaji ya ce ya shigo dashi amman yana mamakin wannan waye haka da daga kano?kodai wani abu ne ya samu Jamilar sa?.. "Assalamu Alaikum" Da sauri Alhaji ya d'ago kansa yana kallon Sadiq yana hango wata fuska a fuskar Sadiq tabbas yasan me irin wannan fuskar. Bayan sun gaisa ne Sadiq ya yi mai cikakken bayaninsa nan Alhaji ya ke cewa tabbas yasan fuskar Sadiq don tun yana k'arami rabonshi dashi ya gane d'ana ga yayan Mahaifiyar Jamila. Sadiq bai b'ata lokaci ba ya fara gabatar da maganar da ta kawo sa don gani ya keyi Jamila ta yi hakanne don ba ta sonshi. Lokaci 1 idon Abba na ya dawo kan Sadiq ya shaida masa ya riga da ya yiwa Jamila miji don haka ya yi hak'uri,hankalin Sadiq ya tashi sosai da ya yi niyyar kwana A Bauchi Amman babu abinda zaisa ya cigaba da zama a garin Bauchi don jin garin ya ke yi kamar an zuba wuta mai zafi. Bayan sunyi Sallama da Abbana Sadiq ya bud'e murfin Duk maganar da Mahaifina sukayi da Sadiq Sooraj ya ji shida Yayar sa,don haka ayanzu sun shirya abinda za suyi wa Sadiq,don gani suke yi sunyi sakaci da har sukabar wani ya ce yana son Jamila har ya iya shigowa gidansu da sunan maganar Neman Aure. A kullum hankalinsu yana kan dukiyar da Mahaifina ya ke da ita don burinsu ace su kad'ai ne mallakinta. Don haka tun kafin Sadiq ya fito suka sace tayar motar yadda koda hatsari ya kama za,ayi mummunan hatsari. Ni kuwa Ummu Maher na CE Allah ka tsaremu da wannan mummunan zuciyar ka bamu Rayuwa mai kyau har k'arshen rayuwarmu. Innalillahi wa inna Ilaihi Raji'un lallai dukkan mai rai mamaci ne da sauri na yarda wayata a hannuna Inna tana ta magana Amman ban San me ta ke cewa ba sai tashi na yi a gadon asibiti na suma. Ina tashi na fara kiran sunan Allah,kwalla na fitowa a hankali daga cikin idanuwa,yanzu shikkenan ta tabbata Sadiq ya mutu ya bar wannan duniyar?. Inna ma kuka ta ke yi tana gogemun hawayen fuskata,Gefena kuma da k'annen Sadiq suma kukan su ke yi,alokacin ne na tabbatar da mutuwar Sadiq kuka na ke yi kamar raina zai fita.da k'er likitoci suka yimin allurar bacci. Sai da safe na tashi ina nayi wani mummunan mafarki wai ina gudu zan fad'a wani rami ina juyawa sai na hango Abbana ya fad'a gaba d'aya ina ihu ina kiran sunan Abbana dai dai nan na farka ina haki. Da Sauri Inna ta taso tana tambayata na kasa bata amsa,waya ta ce ta fara ringing Inna ta mik'omin na amsa da k'er na kai wayar tawa kunne. "Please ke ce Jamila"?. Da k'er na CE" eh ni CE"? "To daman Mahaifinki Allah ne Allah ya yiwa rasuwa jiya y'an fashi suka shigo Gidan......... Wani ihu na saka Inna na zubamin ruwan shayi a Kofi. 😢😭The destiny. Lallai wannan ita ce k'addara Allah yasa muci dukkanin kaddarorinmu n rayuwa Amin. *Ummu Maher CE* Vote Share And Comments👏🏼 *_📲📲Tyiping_* _ဎကကဎ ကခիer_ *_🏮JÂMÊÊLÊR_🏮* Ña _Ummu Maher(Miss green)💚☘️_ _Fans d'in Jamila kuyi hakuri abubuwane sukayi min yawa shiyyasa bana samun damar kawo muku shi amman yanzu zan cigaba_ _26//627_ "Jamila na yi kukan rashin mahaifina sosai don sai da na yi kusan wata 2 bana magana sai Hm sai A'a,amman saboda rashin imani irin na Mama Asiya ta saka aka b'atar dani b'at a duniya sai tsintar kaina na yi a wannan duniyar". " Lallai Namesake kin had'u da jarrabawa kala²sai dai ince Allah ya sa muci dukkanin k'addarorinmu baki 1,don labarinki ya k'ara koyar dani sanin waye d'an adam don rayuwar nan ba matabbata ba bace. ....... *Cigaban Labari* Masu karatu idan kuka ji na ce Jamcy ina nufin wacce ta fara bada labarinta,idan kuma kuka ji na ce Jamey to ina nufin ta k'arshen. To mu fantama don muga wata wainar ake toyawa gidan Mlm wanda ya taimaki Jamcy da Jamey. °•°•° • °•°•° Mama Amarya ita ce Amaryar Mlm mace me hankali da sanin yakamata,Inna kuma itace Uwargidan Mlm mata me son abin duniya da rashin mutunta mutane,Inna Mara kuma ita ce y'ar tsakiya kinfi Amarya kenan🙄🥴,macece me iya takunta da shegen wayo ammanfa idan ta samu waje za'a cuceka da ita don bata da imani ko kad'an. "Wallahi Mlm yarannan da ka kwaso zasu iya haifar mana da matsaloli don haka ka mayar dasu inda suka fito tun wuri,don kasan Allah duk yadda a kayi duk cikin shege suka yi suka shigo duniya"..... " Kar ki kuskura ki k'ara kiran wad'annan yaran da wannan kalmar koma me sukayi zan rik'esu tsakani na da Allah don bazan bati rayuwarsu ta lalace ba,yadda zan rik'e y'ay'a ns haka zan rik'e wad'annan yaran"... Yana kaiwa nan ya yi tafiyarsa yana Allah wadai da halin Uwargidan nasa wato Inna,don Inna irin mutanen nanne masu son zuciya da kuma wulak'anta d'an adam. Kai tsaye ya wuce sashen Hajiya Rabi wato Amaryarsa don yasan anan ne kawai zai iya samun farin ciki,don itama Inna Marak'isiyya ya gama gano ta yanzu don kanwa ce uwar had'e wato fuska 2. Yana shiga wani k'amshi me dad'i ya daki hancinsa har ya shiga babbsn farlonta yana jin wannan k'amshi me dad'i,Jamcy ya hango tana turare farlon da turaren wuta wanda aka kunna na Bunner,Sannu da zuwa Ta yi mishi ya amsa cikin fara'a sannan ya tambayeta y'ar uwarta. "Baba Jamey tana Sallah Hajiya kuma tana ciki". Ta fad'i hakan cikin jin kunya. Har ransa yaji son yaran don suna da Biyayya kwarai,yana fatan ya samu lokaci yaji labarin yaran don ya samu ya mayar dasu ga iyayensu. Sosai yaji dad'in ganawa da Hajiya Rabi ta ce" Malam wannan yaran da ka ke ganinsu Ajiyar Allah ce, kuma amana ce a hannunmu don haka don Allah Mlm inason muci gaba da yi musu addu'a kafin komai ya dai dai ta". *Bayan wasu watanni* Sosai Mlm ya tausayawa su Jamila da labarinsu da suka bashi kuma insha Allah zaiyi iya bakin k'ok'arinshi ganin ya dai daita komai cikin hikima. ...... Muna zaune muna shan hira da Hajiya Rabi wacce ayanzu muke ce mata Mami kawai sai mukaji Sallamar Inna Ladi wato y'ar tsakiya muka gaisheta cikin fara'a itama ta amsa cikin fara'a har tana tsokanarmu wai Y'ay'an Mami ta samu y'ay'a daga sama to tunda haka ne itama d'aya ta dawo wajenta,cikin hikima muka fara gano halin Inna ladi don mutunce me k'ananan magana don haka muma muka biye mata muna ta washe baki. Can kuma sai cewa ta yi"Hmm Wallahi Rabi na rasa hali irin na Inna wai ace tunda yarannan suka zo babu wata magana me dad'i da ta ke shiga tsakaninsu,jiya fa ina ji ita wannan y'ar lukutar ta nuna Jamcy jiya ana rabon abincin almajirai wasu basu samu ba Ta ce bari a k'ara dafa musu wani kawai sai cewa ta yi,wai tunda bana ubansu bane kada ta k'ara dafa wani ke zagi dai har da ce mats wai wa yasa ni ma ko karuwai ne su"..... Da sauri Hajiya Rabi ta ce"Kai Haba Hajiya Ladi wannnan fa ba magana bace koda ma ta ce hakan bai kamata ki fad'i haka ba don Allàh akiyaye". Sosai Hajiya Ladi ta ji haushi don a fuskarta ta nuna fushi sosai,amman bata ce komai ba ta yi shiru,sai cewa ta yi"Hava Hajiya Rabi be kyautu ki ce haka ba,saboda shi icce tun yana d'anye ake tankwarashi gwara ayiwa Hajiya Babba magana don ta daina"...... "Haba Hajiya Ladi kinfi kowa sanin wacece Hajiya Babba tunda itace babbarmu amman bai dace muyi mata magana ba,Allah dai ya kyauta". Tana fad'in haka ta tashi ta shiga d'akinta, kawai sai mukaji ta ce K'asa²" Hmm tana wani tafiya tana juya mazaunai d'uwawu kamar an hura balo🤨shiyyasa miji ya na ne mata".tana kaiwa nan itama ta tashi Fuu ta yi sashenta. Muka kalli juna muka saki dariya duk da ada hankalinmu a tashe ya ke don munji babu dad'i kirawo mu da karuwai da a kayi,amman sai gamu muna dariya daman Manya ma suna kishi😄😄. Ni kuwa Ummu Maher na ce ai kishi Halak ne amman fa na ilimi bana jahilci ba. *Ummu Maher ce* *Vote* *Share* And *Comments* *_📲Tyiping📲_* ပကကပ ကခիér *_🏮🌹JÂMÊÊLÊR🌹🏮_* Ña _Ummu Maher(Miss green)_☘️ _28to30_ ......"Jamcy!Jamcy!!kitashi muna cen muna ta aiki,Hajiya tana nemanki muk'arasa aikin." Da sauri na tashi ina mik'a harda Hamma,yau na yi mafarkin y'an gidanmu kuma wai suna wani hali na nema na suna bina suna kuka wai in dawo gida......"Haba Jamcy ina tashinki kinyi min shiru please ki tashi mana".Jamey ta fad'i hakan kamar zata yi kuka. Aiki muke sosai Ashe yau Twins d'in Mami zasu dawo don ta dad'e tana bamu labarinsu sunyi Aure su dukkansu suna Tunisia Bashir Wanda shine (Hussain) sai Ahmad (Hassan)shekararsu 2yanzu da Aure suna cen da matansu suna wani course ne da ya ke su dukkansu acan suka samu aiki Amman yanzu zasu dinga yi a Nigeria d'aya Likita ne d'aya kuma Sojane me zaman kansa, haka suka taso kowa da burinsa tun suna k'ananu shiyyasa Mlm wato mahaifinsu ya basu kwarin guiwar cika wad'annan burikan nasu. Har da decoration ranar sai da akayi ya k'atar sosai,Su Safiya da Anty Rabi'atu duk sunzo suma y'ay'an Mami ne daman y'ay'anta Hud'u 4, 2 maza mata 2. Haka Allah ya tsara mata Haihuwarta ita ba me yawan Haihuwa bace,yanzu Shekararta 48 da Aure sanda akayi mata Aure Shekararta 11 da yake su Fulani da Wuri suke Aure sai da tayi Shekara 5 sannan ta haihu Twins duk maza alokacin tana da shekara 21,Sai da ta yi shekara 5 again sannan ta haihu ta haifi Mace Safiya sannan tsakanin Safiya da Rabi shekara 4 tun daga nan bata k'ara Haihuwa ba. Ayanzu Bashir da Ahmad suna da shekara 33 zuwa da 4,Safiyya kuma 28 tana Aure a Sudan y'ay'anta 3,sai Rabi 24 tana da d'a 1 ita kuma gidanta babu nisa da gidansu. Hajiya Ladi ce kawai bata da d'a don bata tab'a Haihuwa ba,Inna Uwargida Y'ay'anta 6 uku maza uku mata duk sunyi Aure da y'ay'ansu har an Aurar da wasu. Less orange and Red Mami ta d'inka mana Wanda yasha adon stone work da ya ke Buba akayi mana sai mukayi kamar Twins har Lalle ja ranar sai da akayi mana harda Kitso. Mlm ne ya shiga kwala mana kira har ya k'arasa shigowa farlon yana cewa"Y'an biyuna kuna inane kufito zaku rakani Airport taro Mazaje".daman haka ya ke kiran Y'an biyun nashi. Da sauri muka d'auko hijabanmu Red me kyau irin Hijabin yayi da ake yi yanzu,sunsha guga Wow zokaga yadda sukayi kyau,Jamcy da kuma Jamey abin burgewa suka mak'ala glass d'insu irin me y'ar zaren nan abin ba'acewa komai. Wani Red d'in High Hill Wanda yasha adon Black and Red kasancewarsu duk masu matsakaicin tsayi ne,don haka sai suka fito gwanin sha'awa. Around 5:pm _______ Muka sauka a airport d'in me kyau da tsari iska me tare da wata ni'ima a hankali muka fito daga cikin motar cikin happy don muna tafiya muna shan hira a motar Malam. Kusan sandarewa mukayi a wajen tsabar kyau da haiba na Mazajen Mlm kowannensu hannunsa sak'ale da matarsa sai dai tun daga nesa zaka hango banbancin kamanni a tsakanin Bashir da Ahmad,Bashir yana da tsayi kuma yana da jiki,Ahmad kuwa ba shida jiki sannan d'aya yafi d'aya haske Amman duk da haka suna kama. Please kuyi hakuri ina tyiping kad'an jiki da jini😊👏👏👏. *Ummu Maher ce* *Vote* Share And Comments👏 Hope🤗🤗ina gaida maaoyana a ko ina👏. *_🍁☘️JAMILA☘️🍁_* _True life story📗📙_ Na _Ummu Maher(Miss green)☘️_ ~Dedicated to Aisha Fulani Girl,and Hajara L Sadiq💋💋 Inayin ku over²~ 🅿️34🟨35 "Wallahi matannan suna matuk'ar bamu haushi yadda kika San dabbobi haka suke kwata² basu San hakk'in d'an Adam ba,ni fa tunda Na ke basu tab'a yimin ko da kallon arzik'i ba." Kallon Aunty Hamida mukeyi da mamaki wai matan yayyinsu basu tab'a koda yi musu kallon arzik'i ba abin yayi matuk'ar d'aure mana kai,gaskiya abinda wasu matan suke basa kyautatawa Na raba y'an uwa musamman uwa 1. **** **** **** "Malam lfy naga kayi tagumi haka?" "Lfy klau Amman ba lauba ba?" Shiru Mami ta yi don tasan ba komai ne ya ke d'agawa Mlm rai ba matuk'ar kuwa kaga ya shiga irin wannan halin to abin yayi yawa ne,"Rabi inason had'a Auren Bashir da Jamey Ahmad da Jamcy". Da sauri Hjy ta tashi tsaye tare da dafe k'irjinta,tabbas tasan za'a Rina don yadda Twins d'in nata suka kafawa Y'ay'an nata idanu"Amman Mlm sune da bakinsu suka ce suna sonsu ko me?". "Kwarai kuwa jiya da magrib suka sameni da wannan batun yanzu inason ki kirawomin su inji ta bakinsu idan suna sonsu shikkenan"ba don ran Mami yaso ba ta k'arasa zuwa farlonta,da Jamcy t fara cin karo tana yiwa Anty Hamida kitso suna ta hirarsu kamar daman sun San juna. "Jamcy tashi daga kitsonnan ki kirawo y'ar uwarki Mlm yana kiranku"?. Gabana ne ya fad'i Amman sai Na tashi Na kirawo Jamey da ta duk'ufa tana tunani,hawaye na tarar yana fitowa daga idanunta tausayi sosai ta bani na dafa ta sannan na CE" Haba Jamey ki daina sakawa kanki damuwa kowa da kika gani akwai k'addararsa a duniyarnan don haka kiyi hak'uri ki taso Mlm yana nemanmu". "Jamcy a kullum ina tunowa ne da Mahaifina yana cen a kabarinsa ya kasa kwanciya saboda duk mutumin da yarasu abubuwa irin wad'annan suna faruwa zaki ga ya kasa kwanciya,ga shi momi wato matar Mahaifina ita da k'aninta sun gaje komai? Ga Sadiq d'ina sun kashe min shi " Sai na k'ara rushewa da kuka me cin rai. "Kiyi hak'uri Jamcy ni da kaina da kika ganni kullm sai na yi tunanin yaya y'an uwana suke?Mahaifina?mahaifiyata?aminiyata Fatima? A wani hali suke ciki?don nasan yaya Saif da Aunty safiya suna cen sun bud'e sabuwar rayuwa don daman basa son ganina a duniyarsu." Da k'er muka bawa kanmu hak'uri muka fita idanunmu jawur alamar munyi kuka harmun k'oshi,su Aunty Hamida suna farlo suka bimu da kallon tausayi har muka fita daga farlon. Aunty Hamida ta ce "Wallahi Rabiatu yarannan suna bani tausayi tunda suka bani labarinsu,gaskiya duniyarnan akwai Abubuwa sosai a cikin ta". Sai da Mlm ya fara mana da wa'azi sannan ya fad'a mana abinda yasa y kirawo mu,sannan ya k'ara da cewa kuma bazan d'aura muku Aure ba har sai kowaccenku ta had'a da iyayenta. Kanmu har lokacin a dunkufe ya ke a k'asa,hawaye yana silalo mana,muna tunanin had'uwarmu da familynmu may be zasu zargemu da munje Neman maza ne yanzu duniya ta juya mana baya mun dawo. Kuyi hak'uri bana jin dadi ne shiyyasa nake small² page. *Vote* Share And comments Ummu Maher (Miss green) *_🍁☘️JAMILA☘️🍁_* _True life tsory_📗📙 Na _Ummu Maher(Miss green)☘️_ *_please don Allah kuyi hak'uri rashin kawo muku JAMILA kwana biyu bana tyiping abubuwa ne sukayimin yawa,kuma zakuga spell din sunan Ya koma JAMILA,maimakon Jameeler complen d'in mutane ne mussaman fans d'in kuyi hak'uri insha Allah yanzu zamu cigaba_*. _31&32_ ``````•kallon² muka shiga yi don da sauri suka tsugunna suna gaishe da Mlm,bakinshi ya k'i rufuwa sai murna ya ke da ganin y'ay'an nashi,Ahamd ne ya fara kallonmu mussaman Jamcy da ya kasa d'auke idonsa a kanta,ita ma Jamey Bashir ne ya kafe ta da ido kamar wani maye,da sauri Amira matar Ahmad ta CE"Mlm wad'annan kuma su waye?". Da sauri Maryam ma ta CE"Wallahi nima tambayar da Na keso inyi kenan y'ar uwa kika Riga ni"?. Murmushi Mlm ya yi don sun bashi mamaki sosai baba wacce ta gaishesa a cikin su Amman daga ganin yara sun fata tambayar su waye? Juyowa yayi ya kalli Amira wacce kishinta ya fi fitowa a fili sannan ya CE"kada Ku damu da wad'annan suma y'ay'ana ne,y'ay'an d'an uwanane su da ya ke Cameron suka kawo min ziyara. Masha Allah Twins d'in Mlm suka had'a baki wajen fad'a,ran matansu kuwa ya yi matuk'ar b'aci daga dawowarsu sai kuma a tare su da bak'in ciki,wad'annan y'ammata kamar flower tsabar kyau. Ko da a kazo wajen shiga mota sai da a kayi d'an daru,don Mlm ne ya shiga gaba shi da Ahmad Sai Jamcy, ita kuwa Jamey da Bashir da kuma Amira da Maryam,dukkaninsu idan ka kallesu kamar an aiko musu da mutuwarsu tsabar bak'in ciki,don tun kafin mazajen nasu su d'aukesu zuwa Tunisia suka tsani Mlm mahaifin mazajensu don shi mutunne mai kamata gaskiya. Rungume Mahaifiyarsu suka yi sosai su duka biyun suna me godewa Allah da suka samu mahaifiyarsu cikin k'oshin lfy,don a duniya suna matuk'ar son Mahaifiyarsu don Mami uwace tagari,tun tasowarsu basu tab'a jin CeCe kuce a tsakanin iyayen nasu ba,shiyyasa ma suke matuk'ar son mahaifiyarsu don akwai ta da ladabi da biyayya. A wani yangance suka gaishe da surukar tasu suna wani k'arewa Gidan kallo,don babu k'arya Gidan ya yi kyau sosai,don tun Twins suna Tunisia suka aiko da kud'i aka k'ara gyare Gidan tsaf gwanin sha'awa. Itama Mami ta kula da kallon k'urillar da yaran suke mata Amman ta watsar da su don tasan tun kafin suyi tafiya haka suke mata suyi ta kallon k'asan zaninta tun bata kawo komai har yanzu ta fara ganewa. Wajen Inna Uwargida suka tafi suna gulmar surukar tasu don harga Allah har cikin ransu sun tsani surukar tasu,don babu abinda Mazajensu ba sa yiwa Mahaifiyarsu,wannan ne ya ke k'ara musu haushinta don sunyi su raba su Amman sun kasa,sai su kirawo inna Uwargida sau biyar ko Hajiya Ladi awaya ba su kirawo surukarsu sau 1 ba,don ma wani lokacin idan sunyi waya da mahaifiyarsu idan ta tambayi matan nasu su kirawo su su ba su wayar Shima ciki² suke amsawa don idan akwai wacce suka tsana to bai wuce Surukar tasu ba wato Mami, don haka sai suka k'ulla abota da su Inna Uwar gida,don daman duk wata gulma daga gurinsu ta ke fitowa shiyyasa suke zuwa wajensu. Sosai Twins suka zage dantse suka ci Dinner da aka baje musu,ita kuwa Mami sai kallonsu ta ke cikin so da k'aunar y'ay'an Na ta. Suna yi suna kallon y'an biyun Mlm Jamey da Jamcy Wanda har yanzu ba su saki jikinsu ba kasan cewar irin kallon da suke musu,don har yanzu les d'in nan lemon green d'inkin Riga da siket gashi ya d'an kama su,mussaman ma Jamcy ita CE me jiki. Suna cikin cin abincin Hamida ta CE"Wai Ammi inasu Anty Amira suka shiga ne gashi ana cin abinci babu su."? Rabiatu CE ta CE "Suna wajen Inna Uwargida kin San ita CE surukar ta su." Ammi CE ta katsesu da cewa"wai ina ruwanku da inda suka shiga ne?kun bi kunsa ka yara a gaba da mitarku cen inda suka je ai za suci don da cen da nan duk 1 ne." Tsit! sukayi ba su k'ara magana ba haushin matan yayyen nasu Na k'ona musu rai,don suna sane da yadda suke wulak'anta Mahaifiyarsu. To su ma dai Twins d'in Na Ammi sunji haushi matuk'a ta yadda suke wulak'anta Mahaifiyarsu suna sane kawai ido suka saka musu don masu iya magana sunce shiru ma magana CE. Muna gama cin abincin su Anty Maryam suka shigo suna jifanmu da mugun kallo,babu Wanda ya kulasu suka kalli Mazajen nasu sannan suka CE "Am: daman zamuje gidane muma mugana iyayenmu"?. Banza suka yi musu sai da Mami ta CE" Ku yi tafiyarku ai dama dole kuma kuje gida". Sun d'an ji dad'i kad'an don sun San indai ta mazajensu ne ko zasu kwana suna yi musu magana ba zasu amsa ba,Amman duk da haka Surukar tasu bata fita ba, suna fita suka fara gulmarta wai yanzu mazajensu sun zama remote control sai abinda uwarsu ta CE suyi shi su keyi. Ko kafin dare mun share ko ina mun gyara tsaf har falo mun gyara harda b'angaren Twins d'in Mami tare mukayi aikin da su Anty Hamida yaransu tuni sunyi bacci. "Jamcy kin kula da yadda wad'annan fitinannun Twins d'in suke bin mu da kallo Allah kamar Na yi fitsari a wando". Dariya Jamcy ta yi sannan ta CE Ayya Jamey ni wallahi Na fiki tsorata dasu gasu da kyau kamar aljan...... Dariya sosai Anty Hamida ta ke sannan ta yi bud'a ta CE" ai insha Allah sai sun Aureku,Ku sharewa Mahaifiyarmu hawaye. Kunya da nadamar maganar da mukayi suka hanamu d'ago idanu mu kalli Anty Hamidar da ke ta Smilling. *Ummu Maher CE* *_🍁☘️JAMILA☘️🍁_* _True life story📗📙_ Na _Rabi'atu B Abdullahi_ *Ummu Maher(Miss green)☘️* Not edited...... 🅿️36🟨37 Kallonmu kawai Mlm ya ke don yasan tunanin da muke yi bai wuce na had'uwa da danginmu ba sai ya CE"kuyi hak'uri Neman danginku a yanzu ya zama dole, saboda kuma ba zaku so Ku zauna haka ba tare da kunga y'an uwanku ba,don haka yana da kyau ayanzu kowaccenku ta shirya don yin wannan tafiyar". " Ku tashi Ku tafi Allah ya yi muku albarka",jikin a sanyaye muka tashi zuciyoyinmu kamar zasu buga tsoro da fargaba ne suka had'u suka yi mana yawa,y'ar nutsuwar da muka samu kwana 2 duk ta tafi,muna shiga d'aki kowaccenmu ta shiga tunanin da zullumi". "Jamcy bazan iya komawa gida a yanzu ba?ban shirya komawa rayuwar halaka ba don yadda suka Halaka Abbana babu makuwa nima sai sun halaka ni,don haka gaskiya ni dai bazan koma ba." Hayawaye ne ya kwaran yowa Jamcy ta saka hannunta ta goge tana Jan zuciya ita ma ta fara magana,"Ban San me zance ba?bakina ya rufe hankali na ya gushe Jamey,ke kina ma da damar furta komai Amman ni na kasa furtawa,bana son abinda zai rabamu ni da ke Jamey". Ga shi Mlm ya CE muyi shawara a game da Auran da zaiyi mana,na gwammace Mlm ya Auramin koma wanene?da in koma gida Yaya Safiyya da Yaya Deen su k'arasa min y'ar rayuwata wadda ta yi saura,a duniyata babu abinda n tsana irin mutum hud'u. "Na farko shine Yaya Deen,Yaya Safiyya, sai Mama Asiya,da k'aninta Kamal,Sune wad'anda suka lala ta mana rayuwarmu Jamey" sune...... Bubbuga baya na Jamey ta yi tana rarrashi na ita ma tana hawayen Fuskarta,ina jin k'aunar Jamcy har cikin raina wato abinda ya faru dani tana jin shi a jikinta itama har ta kasa rik'ewa ta fad'amin,Lallai ya zama dole nima in tsani duk Wanda ya CE baya son Jamcy don yadda na ke jikinta ba'a fad'a. Muna cikin wannan halin ne Mami ta shigo ta zauna tana me fuskartarmu ta CE "Yadda na kejin y'ay'an Dana Haifa acikina haka na ke jinku,zanfi kowa farin ciki idan aka CE kuma yau kun samu naku farin cikin, zan iya CE muku na fiku shiga wani hali a game da k'addarar Rayuwarku,Amman fa Ku Sani bazan tab'a goyon bayan abin da ba dai² ba". Familynku sune Abu na farko da zaku ringa kalla a doron k'asa kuna jin dad'in Rayuwarku,Amman bai kamata Ku yanke alak'a da dasu ba tunda ba sune suka yanke alak'a daku ba wasu mutanane acikin su suka b'ata muku,don haka ni zan jagoranci tafiyar nan taku don asamu daidai to don haka daga yau zamu fara shiri ba sai gobe ba, don masu iya magana sunce da zafi² akan d'auki dutse". Aranar mukaje kasuwa muka siyo kaya kamar zamu bud'e shago tsaraba da sauran abubuwa,Ammi ta yanke shawarar cewa Kano zamu fara zuwa gidansu Jamcy sannan Bauchi gidansu Jamey. Muna zaune da daddare muna had'a kayayyakinmu Aunty Rabiatu na taya mu,don Aunty Hamida ta koma Sudan tun tuni sai Aunty Rabiatu ita kuma mijinta ne baya nan shiyyasa bata koma gida ba,sai ya dawo zata koma. Wani almajiri ne ya shigo 1 daga cikin Almajiran Mlm ya CE wai Jamcy da Jamey Suzo?. Kallon kallo muka shiga yi a tsakanin muka had'a baki wajen fad'i "inji waye"?. " Mlm ne ya ce akirawo wai kuzo". to muka CE sannan muka sanya hijabanmu har k'asa muka fito,Aunty Rabiatu ta cigaba da had'a mana kayan. Muna shiga muka sunkuyar da kanmu,Ahmad da Bashir ne a zaune sunyi kyau cikin shadda ruwan dark Blue sai shek'i ta ke,ga Maryam da Amira sai cika suke suna batsewa haushin yaran na k'ara k'aruwa acikin ransu duk da basu San me za'a fad'a ba Amman sunji matuk'ar haushin ganin yaran a kusa dasu. *Ummu Maher CE* _*🍁JAMILA🍁_* True life Story✍️ *_A story by🖊️_* _Oum Maher(Miss green💚)_ _Dedicated to all my fans_ _*38to40*_ Guri muka Samu kusa da su Aunty Maryam da Amira da saurinsu suka matsa kamar dai sun ga wani abin k'i,a hankali Mlm ya kallesu sannan y kawar da kanshi yana mamakin matan y'ay'ansa yadda ko kad'an basa jin tsoron rashin kunya a gaban kowa. "Ba wani abu ne ya tara mu ba illa son k'ulla aure tsakanin Ahmad da Jamcy,Bashir d Jamey Insha Allah a wannan wa......" Wata irin ashar Amira t buga wato matar Ahmad don tsabar firgici ya yinda ita ma Maryam ta tashi tana sababi. "Wallahi tallahi anyi kad'an kuma anyi k'arya a ce wai mu za'a had'a da wadannan tsintattun magen wa ya Sani ma ko y'ay'an karuwai....... "Relax!abinda Ahmad da Bashir suka fad'a suma suna tashi tsaye suka nuna matan nasu cikin d'aga murya suka ce. "Kuka k'ara wata magana a wajennan wallahi n lahira sai ya fiku jin dad'in duniya don muna aurenku ba wai yana nufin daku zamu mutu bane tunda ba don ku kad'ai aka Yi mu ba,kuma kada ku k'ara yiwa iyayenmu rashin d'a'a idan ba haka ba wallahi sai kun kwammace kid'a da makad'i,kuma Aure Babu fashi anyi shi an gama, kuma kada ku k'ara xagin yarannan d mummunar kalmominku kamar kunci naman kare,idan kuma ba haka ba wallahi ranku sai ya Yi mummunan b'aci,kuma ku fita daga d'akinnan kafin mu gama tattaunawa don bama buk'atar Marasa tarbiyya anan. Suna fad'in haka suka zazzauna Mlm har lokacin bai ce musu komai ba,don ya Yi matukar mamakin rashin kunyar yaran basa tsoron,idon manya ko kad'an fatan shiriya ya Yi musu a cikin ranshi sannan ya cigaba da maganar da ya d'auko,da k'er Amira da Maryam suka zauna suna matsar kwalla tare da d'aukar alwashi akan wad'annan yaran Jamcy d Jamey,su kuwa bayin Allah wato Jamcy da Jamey sunyi tagumi kawai hawaye yana kwaranyowa daga idaniyarsu,na rashin mada fa da kukan rashin y'an uwansu a kusa dash,har yanzu Babu ko digon son Bashir da Ahmad a cikin zuk'atansu baron ba suyi musu ko wani abuba don Kyau,kud'i,ilimi,addini,duk sun had'a Amman zasu fi alak'anta hakan akan rayuwarda suka shiga a baya don har sun cire ran sake wata soyayya a gaba don su kan sun bar yin wata aba wai ita soyayya har abada. *Kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika* Kamar yadda Ammi ta bukata haka kuwa a kayi don Kano muka fara zuwa wato garinsu Jamcy,munyi tafiya Sosai don daga Adamawa zuwa kano akwai nisa,Jamcy kuwa kuka kawai ta ke a mota don har yanzu zuciyarta ba ta k'aunar ganin wadannan mutun biyun,Yaya Deen,da kuma Yaya Safiyya wato Yaya ta wadda suka had'u da mijinta suka jefar dani a dokar daji saboda mijinta ya yimin fyede har ciki ya shiga suna tsoron tonuwar asirinsu. Sai yamma muka shigo garin kano muna tafiya ina nunawa Yaya Ahmad hanya wanda tunda muka shigo motar ya ke ta kallona ta cikin glass ni kuwa sai kuka Na ke Mami na rarrashi na,daman ba mota d'aya muka shigo da su Jamey da Mlm da Yaya Bashir ba motarsu su uku daban ta mu daban. Unguwar anyi gine² sosai wanda da k'er na gane gidanmu,an k'ara gyara gidanmu ya Yi wani irin kyau kamar gidan shugaban k'asa ko gwamna. Sosai su Mlm suka yaba da kyawun gidanmu,har Mlm a fili ya ce "Allah sarki rayuwa ba kud'i ne jin dad'in rayuwar duniya ba,da kuwa Jamcy ta Samu farin ciki",ya goge kwallar da ta zubo Mishi n tausayin yaran guda biyu wad'anda ya ke jinsu kamar y'ay'ansa mafi soyuwa a arayuwarshi. An canza duk security d'in gidanmu an saka sababbi wadannan har da bindigunsu sab'anin na da da Babu bindigo,a hankali na saka k'afafuna acikin gidan na shak'i iskar gidanmu wacce na ji ta har ruhina sai dai abinda ke cikin gidan yafi gaban wasanka,na kalli compound d'in gidanmu motoci sunfi goma kamar company sai da motoci. Na kalli wajenda muke Shan iska ni da Yaya Deen d'ina, wasu hawaye ne suka wanke min fuska ta. "Hajiya wajen wa kuka zo"?. Tambayar da securities d'in suka Yi mana kenan,ba na kallesu da idanuwa da sukayi jawur Na ce "ni y'ar gidannan ce sunana Jamila na bar gidannan shekara uku baya",na fad'i hakan kamar zuciyata zata fito waje,wai yau ni ake tambaya wajen wa nazo?ni da gidanmu?wannan wacce irin rayuwa ce. Da sauri securities d'in suka ce"are u sure?ke ce jamila da muka dad'e muna nemanki ?ke ce wadda muke nema shekara uku baya,koda ba'a gaya mana ba mun san ke ce Hajiya Jamila don kamar ku 1 da Hajiya Safiya don...... "Wait!" Na fad'i hakan cikin k'araji don ko sunan Aunty Safiya bana son ji a halin yanzu,da sauri na shiga cikin gidanmu har ina had'awa da gudu don na matsu inga, Mama na,Fatima,da Abbana. Wani rantsatsan falo na iso mutane uku ne a farlon gidanmu umma na,da Abbana,sai K'anin Umma na Alhaji Adam. "Jamila ta ke ce ko kuwa"?abinda Abbana ya fad'a kenan yana murza idanuwansa don gani ya ke kamar mafarkin da ya saba Yi ne. More comments More tyiping🖌️. Ku tayani da addu'a n fara exam. Vote Share And Comments✍️. UMMU MAHER ce _*🍁 JAMILA🍁*_ By _*Oum Maher(Miss green💚*_ _41&42_ ....da gudu na rungume Mahaifina ina kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,sai a yanzu na k'ara tabbatarwa ba k'aramar cuta su Aunty Safiya suka Yi min ba,don da na rungume Mahaifina wata nutsuwa ce na ji tazomin wadda ada cen bani da ita. Mama ma rungume ni ta Yi tana kuka shi kuwa K'anin Mahaifina yana gefe yana murmushi tare da kallonmu cikin so da k'auna,mun dau lokaci sosai a haka sannan muka saki junanmu,Amman har yanzu ina lafe a jikin Abbana,su ma su Mlm suka shigo suka zazzauna suna kallonmu gwanin sha'awa,Mlm kuwa wani dad'i ya ke hi yau ya had'a y'an biyunsa da iyayensu ya sauke nauyin da Allah ya d'ora Masa. Jamey kuwa kallonmu kawai ta ke Yi cikin so da k'sunarmu,ta share hawayen da ya zame mata sana'a aduk sanda ta tuno da mahaifanta,yanzu shikkenan ita ba tada iyayen da zata fad'a musu damuwarta?ba ta da wanda za taji dumin jikinsa acikin iyayenta,wasu hawaye ne masu zafi suka zubomin na saka gefen mayafi na ina gogewa,na tuno Mahaifina da yana raye bazai tab'a bari inyi kuka ba,Bashir ya zubomin idanu yana yimin alama da in dai na kuka,idan ba haka ba shima zaiyi kuka,ya Yi alamar yara idan zasuyi kuka,sosai abin ya bani dariya na manta sam agaban mutane na ke sai da Ammi ta ce"lfy y'a ta Jamey"?da sauri na ce Babu komai. Bayani Mlm y Fara Yi musu sannan daga bisani ya fad'a musu abinda y kawo mu na son had'a Y'ay'ansa Aure dasu Jamcy,ba k'aramin murna iyaye na suka yi ba. Sai alokacin Iyaye na suka tambayeni wad'anda suka d'auke ni daga inda,shiru na yi naki Basu labarin sai kuka da hawaye kawai na Fara,don bana don tonuwar asirin y'an uwana. Ko da Mlm ya ga haka sai y Basu labarin abinda ya Sani sai dai bai bada k'ofar da zaisa a gane cewa y'an uwana sune suka yimin haka ba. Sosai Mahaifana da Baba Auwalu sukayi mamaki Amman ba abin mamaki bane a wannan rayuwar da muke ciki,har lokacin kuka na ke Yi ina tuno ko Yaya su Aunty Safiyya za suyi idan sukaji na dawo?. Sai alokacin na yiwa Iyayena bayanin Jamey da abinda ya faru da ita,sosai Mahaifana sukayi mamaki kuma sun dau aniyar sai sun kwatowa Jamey hakkinta a wajensu Mama Asiya da kaninta Suraj, sannan su maka su a kotu. Abinsha da abinci kala² akawowa Su Mlm,Mama da Ammi kuwa tuni sun d'inke da Ammi sai hira suke yi kamar sun san juna da ma. Rungume naji anyi da k'arfin gaske ana cewa"ga Aunty Jamila ga Aunty Jamila",ko da ba'a gaya min ba nasan Twins ne kanne na Raliya da Rayya,ni ma rungume su na yi ina kuka nima mai tsuma zuciya,mun dad'e kafin mu saki junanmu,na shiga kallonsu yadda na ga sun Zama y'an mata kyawawa,daman dukkansu dani suke kama,sai dai su Sirarane daman cen ni kuma yar duma² ce. Sosai na yi murna da ganin Twins ko da ya ke daman cen munfi sabo da su akan Aunty Safiya,don daman ita ba mutun ce me sakin fuska ba ce,wai kada mu raina ta. "Twins Ina Nasir da Fatima ta"don na ga Babu wanda ya Yi min maganarsu?". Shiru suka yi fuskokinsu suka canza,Rayya ce ta Yi k'arfin halin cewa"Aunty tun da kika tafi bai fi kwana 1 ba ita da ummanta muka meme su muka rasa har yau Babu wani labarinsu,Sai dai mun lura wad'anda suka sace ki suna da alaka da wad'anda suka sace ki,shi kuma Nasir yana Maxico karatu tun bayan tafiyarki". Shiru na yi ina wani tunani tsanar mutanen guda 2 tana k'ara ruruwa acikin zuciya ta,tabbas su Yaya Deen sune suka sacesu don sun san komai a game da fyed'en da Yaya Deen ya Yi min,cikin kuka na tashi na shiga wani d'aki da ke kusa da farlon,don gaba ki 1 an canza wa gidan fasali,Jamey ce ta biyo ni d'akin don matukar Jamey ta ganni acikin damuwa to ita ma yanzu zaka ga hankalinta ya tashi. "Jamcy bai kamata ace har yanzu kina kuka ba,don ga ki acikin gatanki Na uwa da uba,kada ki manta Jamcy ni bani da irin wannan gatan na ki Amman babu yadda zanyi haka na karb'i k'addara ta don haka dole ne a yanzu muyi hakuri ni da ke don munga rayuwa sosai,ya kamata ace yanzu muyi karatun ta nutsu." Share hawaye na nayi sannan na ce"Jamey dole na inyi hakuri,Amman ta taya Yaya Deen za suyi min haka? Why bayan sun b'atar dani bai Yi musu ba har sai sun b'atar da bayan Allah,me suka yi musu?". "Wallahi Jamey a yanzu na yi matukar tsanar wadannan mutanen masu azabtar da rayukan mutane,su d'in Basu da zuciyar imani"?. K'ara fashewa na yi da kukan tausayin k'auna,Jamey na rarrashi na. Har yamma ban tambayi su Aunty Safiyya ba yan uwa da abokan arziki an cika gidanmu ana tayamu murna. Safiyya & Deen Kuka sosai Safiyya ta ke tana da na sanin abin da ta aikatawa y'ar uwarta,don yanzu Mama ta kirawo ta ta ke shaida mata cewa Jamila ta dawo. Alokacin Deen ya fito daga band'aki yana goge jikinsa da ruwa,ya ce"ke kuma lfy kika sakani a gaba kina kuka kamar an aiko miki da mutuwar Abba ko Mama". "Ba gwara mutuwa da abinda ya faru damu a baya ba,ka ingizani na aikata babban kuskure na aikata mummunan abu akan k'anwata,ka cuci k'anwata ka Yi mata fyed'e har ta haihu". "Relax!" Kada ki k'ara cewa ni na sakaki aikatawa k'anwarki abu,nima duk abinda na aikata abin yana damuna,tabbas daman ance ba,a sarki mugu sai an Samu mugun bafade,kuma kin san daman cen ba ke na ke so ba Amman kika san yadda za kiyi sai da kika Aure ni,Amman duk ina kallonki na k'eleki,to wallahi kada ki sake ki kaini k'arshe don saboda su Abba na ke zaune da ke da tuni na dad'e da mantawa da ke". Sosai fad'a ya kaure a tsakanin Deen da Safiyya,don har sai da masu aikin gidan suka ji suka shigo,kowa yana Yi wa d'an uwansa tonon asiri. *Miss green ce* *_🍁 JAMILA🍁_* By *_Oum Maher(Miss gree💚)_* _*43&44*_ Sai da suka gama yiwa kansu Tonan asiri,sannan Suka hakura kowanne ya yi d'aki,Khalil d'ansu yana ta kuka acikin d'aki daman kullum idan sunayi sai dai ya Yi ta kuka,acikin d'aki babu me kulashi. Safiyya na hango ta ciko akwatinta taf da kayanta tana jansa da k'er har ta fito waje ta shige motarta sai gida,daman ba wani nisa ne da gidansu ba. Gabanta ne ya ke matukar fad'uwa har ta shigo cikin gidansu Hankalinta ba,a kwance ya ke ba,tunanin yadda zata had'u da k'anwarta ne fal acikin zuciyarta har ta gama shigowa farlon gidan nasu. Jamila kuwa tana ganin Yayar ta sai da gabanta ya fad'i ta tashi ta yi shigewarta d'aki ta Samu Jamey tana ta baccinta abinta,ita ma ta matsa kusa da Jamey tana kallon fuskarta tana Raya irin son da ta ke yiwa Jamey don ayanzu tafi son Jamey Akan Safiyya yayarta don ita ba zata tab'a cutar da ita ba,yanzu rayuwa ta lalace sai kaga d'an uwanka yana neman cutar da kai,Amman wanda ba d'an uwanka ba yafi janka a jikinsa. Ina cikin karanta Novels me suna A sanadin Abayar Sallah na UMMU MAHER,kawai sai naga Aunty Safiyya ta shigo d'akin da na ke,idanunta Fal da hawaye idanunta sunyi jawur abin tausayi,Amman fa ni banji ko da d'igon tausayinta ba don duk wanda ya sai rariya yasan zata zubar da ruwa. Har k'asa ta tsugunna guiwowinta ta ce"Jamila bani da bakin da zan baki hakuri don nasan na cuceki......" "Kin cuceni?ko kin cuci kanki?kada ki kuma cewa kin cuceni,na fad'i hakan cikin k'araji har sai da Jamey ta tashi ta k'ura mana Ido tana kallonmu,don duk ta ji abinda ya faru Tsakanin Jamcy da yayarta. "Am!don Allah ki tashi ki fita na yi miki tsana mafi muni arayuwata na manta da ke kamar yadda kema kika so ki birne tawa rayuwar,ko a cikin yan uwana bana buk'atar a sakomin ke,don ke annoba ce a cikinmu,ki Sani duk abinda kika yi sai anyi miki",na fad'i hakan cikin bud'ewar murya yadda ko da kana kusa da d'akin namu zaka iya juyo tashin muryata,don Allah ya Sani na tsani ganin Aunty Safiyya. Ina fadin hakan na tashi zan fita sai naji Jamey ta ruk'o hannuna sannan ta ce"Jamcy ashe mu bama yiwa Allah laifi ya yafe mana?,in dai kuwa muma baza mu yafewa wasu ba,to ba shakka muma Allah ya k'i yafe mana,kada ki manta a wata aya Allah shbhanahu wata'ala yana cewa _Innallaha Ma'assabirin_ wato Allah yana son bayinsa masu hakuri don haka kema ya kamata ki zamto me hakuri acikin bayinsa,hak'ik'a daga ni har ke an cuce mu an rugaza mana rayuwa,Amman haka gashi bai saka munk'i cigaba da rayuwarmu ba. Jamey ta d'an fasali sannan ta cigaba"Jamcy kina da uwa kina da Una kina da y'an uwa a zagaye da ke,to ki godewa Allah don ni bani da iyayenma ballanta na in gansu ko don inji dad'i,Masoyina Sadiq ma sun kasheshi........sai na fashe da kuka a dai dai nan wajen. Sosai jikin Jamcy ya yi sanyi da jin nasihar k'awarta ta rungume ta tsam a cikin jikinta tana jin wani abu acikin zuciyarta,tare da k'aunar Jamey har cikin zuciyarta. "Jamey ke ba marainiya bace?kuma kin kasance kina da y'an uwa don ni kad'ai na isar miki Jamey". kasak'e Safiyya ta Yi tana kallon su cike da so harda k'aunar yaran sun burgeta,lokaci 1 taji Jamey ta kwanta mata har a cikin zuciyarta taji ta kamar k'anwarta Jamcy. Har Aunty Safiyya ta tashi zata fita Jamcy ta janyo hannunta tare da cewa,ko da kashi ne Jamey ta nuna min a matsayin inso shi to fa tabbas saina so shi,ballan tana ke Yaya ta,na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki 1. Sai suka rungume junansu abin sha'awa,alokacin Ammi ta shigo ta samesu a haka ta ce su tashi su shirya za,a kaisu Gidan Kakannin Jamey. Da saurinsu suka shirya harda Aunty Safiyya,mina fitowa naji an janyo ni cikin wani dan corridor da ke jikin d'akinmu,da sauri na waro idanu Ganin Yaya Ahmad ya rungumeni tsam acikin jikinsa,ina shirin kwace kaina naji ya rad'amin a kunne na,"yau kin Zama mallakina an d'aura mana Aure". Da sauri na kalleshi kallon tuhuma,ya ce"yes". Kuka ne ke shirin sakkomin ba wai ina tsanar Alhamd bane a,ah kawai dai abinne yazo min Baga tatan. To ita ma Jamey acen Ido ya yi zuru² don ita ce ta Fara shiga cikin motar,bata san cewa Bashir yana ciki ba,kawai sai taji mutun ya rungume ta ya shiga aika mata da kiss ta ko ta ina....... See Hajara har an waro idanu😅👏👏... Ana zan tsaya saboda masu rashin comments idan kun Fara comments na k'ara yawan tyiping. Share and comments👏 *_🍁JAMILA🍁_* BY *_Oum Maher(Miss green)💚_* Not edited...... *45&46* ......da sauri Jamey ta ce"ikon Allah meye haka Yaya Bashir zaka wani rungumeni wannan ai iskan....."da sauri Bashir ya rufe mata bakinta Yana yi mata wani irin kallo me tab'a zuciya ce"ke ayanzu Mallaki na ce Jamila an Riga da an d'aura mana Aure,a yanzu duk abinda zanyi miki lada zamu Samu",kallonshi na ke kamar na Samu Tv na fashe da kuka alokacin su Jamcy ma suka fito ita ma daga ganin idanunta tasha kuka,ana cikin haka su Mlm suka shigo da Mahaifin Jamcy da goro harda ma Sweet,suna k'arasowa wajenmu Mlm ya umarcemu dukkanmu mu shigo cikin gidan akwai maganar da zamuyi idan an gama sai muyi tafiyar. Duk jikinmu a Sanya ye muka shigo muka Samu waje muka zauna a babban farlon gidan Mlm ya yi gyaran Murya sannan ya ce"dukkanmu mun taru anan ne don kowa ya shaida d'aurin Aura da aka d'aura yanzu a masallaci a yau Ranar Asabar 25, ga watan Afrelu shekara ta 2020 an d'aura Auren Jamey da Bashir,Jamcy da Ahmad,duk Akan sadaki Naira dubu 50²". Shiru farlon ya d'auka muka had'a baki wajen cewa to Allah ya bada zaman lfy,ni da Jamcy muka tashi muka shiga d'akinmu dukkanmu muka fad'a gadonmu sai kuka,ba wai bama son Auran bane a'ah?sai tunanin Auren da yadda zamu zauna da mazajen namu shine abinda ya sakamu kuka wanda aka san duk wata mace me kunya matukar za'ayi mata Aure sai ta Yi kuka. Har d'aki Ammi da Umman Jamcy suka samemu suna ta Yi mana Nasiha me ratsa jikin duk wani me imani kuma nasihar tayi mana tasiri acikin zuk'atanmu,daga baya sai gamu muna ta dariya har Aunty Safiyya tana tsokanarmu,kuma an saka ranar tarewar mu nan da 2 masu zuwa kuma a satinnan za'ayi mana lefe,a satin kuma muka je gidan Kakar Jamey da ke Kano itama ta Yi murna harda sujjada don ganin Jikarta Jamey kuma tayi murna da aka ce Jikarta ta Yi Aurenta tayi ta shiwa Bashir albarka sannan ta ce ya kula mata da Jikarta don marainiya ce, Inna ta Yi ta tsinewa su Mama Asiya da kaninta Suraj Akan cutar da suka yiwa Jamila,kwananmu 3 a gidan Inna Kakar Jamey muka tafi Bauchi don kwatowa Jamey hakkinta wajensu Mama Asiya da kaninta Suraj. Sosai hankalinmu ya tashi da muka je Bauchi aka ahaida mana cewa wai tun tafiyar Jamila su Mama Asiya suka yi tafiya har yau kuma ba'asan in da suke ba wannan abu ba k'aramin bata mana rai ya yi ba,daga k'arshe Mlm ya ce mu kyelesu duniya ce ta isa kowa Riga harda xanin d'aurawa. Gaba dayanmu muka dawo kano muna gidanmu duk da Inna taso Jamey ta zauna a wajenta kafin buki Amman Umman Jamcy ta rok'i Innah Akan Jamey ta zauna wajenta akwai abubuwan da ta keso ta yiwa yayan nata ne,Amman ta ce idan ya Zama na saura kwana biyu bikin Jamey zata dawo nan gidansu ayi yinin buki,Inna taji dad'in yadda Umman Jamcy ta ke kula da Jikarta ta Yi musu fatan alkhairi suka koma gida,Su Mlm kuma washe gari zasu koma a cigaba da shirye². Da daddare muna zaune a cikin d'akinmu bayan mun dawo daga yawon Shan ice cream da mazajenmu Umma ta shigo d'akin ta samemu mun zube Akan gado duk mun gaji,ta ce"oya ki tashi ki fito farlona yanzu zan hadaku da me gyaran jiki zaku tare a bangarena acen har lokacin buki". D'an turo baki Jamcy ta Yi wanda ya yi ja saboda tsotsar da yasha yau wajen Yaya Ahmad na ce"Allah Mama mun gaji yau fa a bari sai gobe yanzu bacci mukeji"..."da kuka fita yawo da mazajenku baku gaji ba sai da kuka dawo gida?,maza ku tashi yanzu² ina jiranku a farlon,da sauri Jamey ta tashi don gaskiya tana matukar son Mama don ta dauketa kamar matsayin yar ta Jamcy don haka itama ta ke matukar son ta da k'aunarta,Jamcy cikin turo baki ta tashi gefe na zuciyarta yana Yi mata suya na tunowa da ta Yi ita fa yanzu bata a matsayin Virgina sai taji zuciyarta ta k'ara tsanar Yaya Deen,don ma Ahmad yasan komai na game da rayuwarta bata da matsala dashi Amman duk da haka Yaya Deen ya yiwa rayuwarta babban gib'e. Sosai Mama ta yiwa me gyaran jikin bayani sosai na yadda za'a gyara mata yayanta,a Daren kuwa aka keb'e musu d'aki 1 har dame gyaran jiki. Muna fitowa da ga wanka Jamcy ta ce "Wow Jamey Kinga yadda jikinmu ya yi kyau kuwa?".harara Jamey ta aikawa Jamcy sannan ta ce"kuma a haka Mama ta ce mutun ya tashi don a gyaramu yak'i tashi ba"?.Dariya Jamcy kawai ta Yi suka kwanta kowa yana kallon jikinsa don kusan yanayin fatar suma iri daya ce sai babbancin kiba don Jamey siririya ita kuma Jamcy y'ar duma². *Washe gari* Da Wuri su Ammi suka Fara shirin komawa gida,Su Jamcy kuwa kowacce tana d'akin mijinta ana Shan minti kafin a tafi Amman Basu yi musu komai ba iya kacinsu Romance ne kawai suka yi,ko da suka zo tafiya ba da k'er suka rabu saboda ad'an kwanakinnan bak'aramin sabo ne ya shiga tsakanin su ba,har da kukan shagwab'a ya yin da su kuma mazan Nasu suka so sakankancewa sai da Mlm ya yi Jan Ido sannan suka fito suka shiga motar matayen nasu na d'aga musu hannu. Sai yamma su Mlm suka isa garin Adamawa(yola) kai tsaye Ahmad da Bashir gidajensu suka wuce bayan sun kai su Ammi da Mlm gida,inda Inna Uwargida ta ringa jefar da maganganu bayan Mlm ya fad'a musu D'aurin Auren Su Y'an biyu,nan da nan Inna ta shaidawa y'an uwa da kuma yayanta tana cewa wai yayan tsintuwa Mlm ya Aurawa y'ay'ansa. Hajiya Ladi kuwa Har makota sai da ta fad'awa wai Ammi ta iya had'a munafinci daman tasan Auren yayan ta tafi tak'i shaidawa kowa,Ita dai Ammi ta toshe kunnuwanta sosai saboda bata son jin kalaman kowa Akan Auren yayanta duk wanda ba zaisa alkhairi ba to ya yi shiru,falyak'ul khairan auli yasmut,Mlm ma da yaji zancen ya yi musu Jan Ido Akan maganar nan da nan kuwa kowacce su ta Yi shiru Amman ta ciki na ciki,don Mlm mutun ne tsayayye a gidansa. To fa can kuma gidansu Ahmad da Bashir ana cen ana kwasar rikici agidan Angwaye Wato Bashir da kuma Ahmad. *😅To fa su Hajara marubuciyar Najmat Abiy a fito a raba fad'a tunda ku kuka had'a wannan Aure*.😅😅😅ni na gudu💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻insha Allah kafin azumi zan gama littattafaina duka saboda ayi bautar Allah sosai,sai bayan Sallah mu d'ora inda muka tsaya. Miss 💚 green ce✍🏼 *Share and post*. ..... 51&52 nayi mistake Ɗin page daga 47&48. Amman a cigaba da karatu tunda pages ɗinne kawai. Wata uwar ashar maryam ta buga jin wai mijinta ya yi aure,ta ɗauki waya ta kirawo Ameera wato Hafsat,abu ɗaya ta faɗa mata shine wallahi ba za ayi mata kishiya a zauna lfy ba,ta jira ta gobe zata zo. Su kuwa mazajen nasu ko ajikinsu ƙarshe ma suka nuna musu ba ta su suke ba,,mlm mahaifinsu yasha zagi sosai wai duk shine munafukin da ya saka akai musu kishiya. Sassafe HAFSAT tazo ta samu MARYAM sai kuka ta ke ta kalleta sheƙeƙe sannan ta ce yanzu zan zamuje wani waje da za ayi mana maganin ƴan banza,sai kallonta maryam ta ke jikinta duk ya yi sanyi suka tafi a motar hafsat Ɗin. Wani daji suka shiga MARYAM sai ɗari-ɗari ta ke saboda tsoro,ita kuwa Hafsat sai kusa kai ta ke da alama ta saba zuwa wajen. Wani kango sukaje duk sai haƙi ne ya ke tashi acikin kangon Hafsat ta shiga tana kallon ogan nasa,ogan ya jefar da tabar wiwin da ya ke sha ya ce"shegiyar ƙwana biyu kin manta dani". dariya ta yi sannan ta ce buƙata nazo da ita jamble inaso a kashe min wasu mutane guda biyu. Da sauri Marym ta kalleta idanunta a warwaje,bata san sanda suka gama maganarsu ba har suka fito daga cikin dajin,tsoro fal a zuciyar maryam. Contact Ummu maher 07068606171 *JAMILA* Love&destiny story wattapad user name *Rabiatu333* 49&50 ,....Wani mugun tsoro ne ya kama Maryam don ita bata ɗauka iskancin hafsat ya kai haka ba,amman sai ta yi ta maza bata yi magana ba don Allah2 take ta samu su fito daga wannan baƙin wajen da suka je. Kuɗi Hafsat ta Basu sosai amman duk da haka sai suka biyota Bashin wani kuɗin don sunce kuɗin ba sunyi kaɗan sai ta daɗo,haka Hafsat ta yi musu alƙawarin cika musu kuɗin sannan suka fito daga cikin wajen,ai suna fitowa aka sai ta su da kan bindiga suka runtuma zasu gudu,dakarun sojin suka riƙe su cikin azama,suma mazan haka aka kamosu aka fito dasu,ƴan jarida sai ɗaukar hoto sukeyi. Lbaran ƙarfe 4 alhaji Abbas ya ke gani mahaifin Maryam yana cikin kurɓar sanyayyan lemonsa ya hango ƴarsa cikin guggun pan daban da aka daɗe ana nemansu Da hannu Alhaji Abbas ya ke nuna ƴarsa bakinsa yana ta kakkarwa,dai dai lokacin momin Maryam ta fito daga kitchen don kawowa Alhaji abinci,itama ta tararar da abin al'ajabin daya faru,a tsaye ta daskare itama tana nuna TV. Tun ƙarfe 4 Ahmad yaga wannan labaran da farko ya kiɗima sosai don ganin matarsa da ƴan daba,ya ɗaga wayarsa ya kirawo Bashir ya shaida masa,a lokacin jamey tana kwance a jikinsa yana aikin rarrashinta,sai taji ya yi saurin tashi ta tambayeshi lafiya ya ce lafiya amman bari yaje wajen Ahmad yaji abinda ake ciki,kuka ta saka mishi wai don Allah ya tafi da ita tsoro ta ke ji,don dole ta tafi da ita gidan. Suna zuwa suka rungume junansu amare wato Jamcy da Jamey suka fashe da kuka atare kamar an aiko musu da mutuwa,Twins ɗin Mlm suka kallesu sukayi murmushi tare da sha'awar matannasu. Da sauri suka fito suka miƙi hanyar babbar headqouter Ƴan sandan hankalinsu yana maruƙar a tashe,alokacin mahaifan Hafsat da Maryam suma sukazo hankalinsu duk a tashe. fashewa da kuka Jamey ta yi tana cewa"wallahi Jamcy dama banyi auren nan ba,wahala nasha sosai kamar zan mutu".saurin toshe mata bakinta Jamcy ta yi tana ƴan dube2 kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya ta ce"haba Namesake kamar wata ƙaramar yarinya aishi aure ni'ima ne,kada ki faɗar haka kinji. Ɗaga kai Jamey ta yi kamar ƙaramar yarinya ta ce"insha Allah bazan ƙara ba".nan suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'awa. Mlm yana Bauchi shi da matansa sunje hutu da ta ke daman can usul acen suke suka dawo Adamawa. Sosai hankalin mlm ya tashi,a tare suka taho da dukkanin matansa suma hankalinsu a tashe don duk da kishin da sukeyi da Ammi amman suna son ƴaƴanta don suna taimaka musu musamman ma Inna. *** *** *** Ba komai ne yasa su Maryam mamaki bai rin yadda su goje suka ce wai tare suke duk wani fashi da sukeyi,duk ƴan rantse2 su Maryam amman ƴan sanda basu yadda ba ƙarshe ma aka shiga gana musu azaba iri2. Ahmad ya yadda da zancen Maryam don Maryam bata ƙarya sam, sai dai tun acen ya rubuta mata takaddar sakinta don bazai iya cigaba da zama da ita a haka ba. To shima Basgir hakan ce ta faru don tun acen shi ya bawa Hafsat ta kaddarta don bazai iya zama da mugun iri a gidansa irin Hafsat ba don ya yadda shima da zancen matar ɗan uwansa Maryam da tace Hafsat bata gaya mata inda zasu ba kawai ta ja tane sai da sukaje taga inda Hafsat ta kaita. *To koma dai menene duk wanda baiji bari ba,ba zaiji wohoho ba💃🏼* don Allah kada a tura book ɗinnan jamila fans group don sun rage comments,, *🍂JAMILA🍂* by UMMU MAHER(MISS GREEN💚🍀) 49&50 . . . .Sosai Maryam da Amira suka zama abin tausayi don ko a cen gidan ma ba daɗi suke ji ba,don babu wacce iyayenta suka ɗaure mata kai,ƙarshe ma sune suka zama boyi-boyin gidansu don hatta wankan ƙannensu da komai duk sune suke a satin biyunnan ba ƙaramin damunsu abin yayi ba,a hakanma don ba a kaisu gidan yari ba iyayensu sunyi tsayuwar daka sun tsaya akan maganar case ɗin fitowarsu da ƴaƴan ya ku bayi ne da baza a fito dasu ba. Cen gidansu Ƴan biyun mlm kuwa soyayyace madararta ake sha don haka acikin sati biyunnan baƙaramin ƙiba suka ƙara ba gwanin sha'awa. Yau ma ta kasance ranar asabar yau ake yinin ɗan gidan hajiya Inna kishiyar Ammi,komai na bikin ƴan biyu ne sukayi shi,duk wani kuɗi da Inna ke kashewa to daga aljihun ƴan biyu ya ke,ayanzu Inna ta ɗan fara sakin jiki da ƴaƴan mlm wato Jamcy da Jamey,saboda suna yi mata alkhairi sosai ba ita kaɗai ba duk matan mlm ma saboda haka yanzu duk gidan ake ganin girmansu mlm kuwa kullum godewa Allah da ƴaƴansa suka sami mata na gari. Ƙwana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta mai kaya a yau Allah ya yi aka kama Mama Asiya ita da ƙaninta Suraj sakamakon danfarar wani shahararren ɗan kasuwa da sukayi wa damfara kuma ɗansa soja ne da akayi bincike aka gano su. A tv Jamey ta gansu ta dafe ƙirjinta tana kiran sunan Allah alokacin Bashir ya fito zai tafi unguwa sosai ya tausayawa Jamey kuma ya yi mata alƙawarin bari ya dawo daga aiki yanzu zai dawo sai suje inda aka tsaresu. Ko da suka daƙer aka barsu suka gansu ko da suka gansu kuka sosai Mama Asiya ta fashe da kuka tana neman yafiyar Jamey tare da gaya mata inda sauran dukiyar Mahaifinta suke. Bashir ne ya tona asirinsu Suraj na kashe mahaifin Jamey da sukayi dpn haka nan da nan case ɗinsu ya ƙaru aka canza musu wuri wanda matuƙar kaje wannan wajen to sunanka sorry,kuka da na dama babu irin wanda Suraj da Mama Hasiya ba suyi ba ƙarshe dai suka haƙura. A yanzu dukiyar Jamey ta koma hannunta gaba ki ɗaya dama dukiyar da su Mama Asiya basu taɓa ba duk an dawo mata dashi,yanzu komai ya zama tarihi sai dai fatan Allah ya bata haƙurin jure rashin mahaifinta don har yanzu matuƙar ta tuna mahaifinta da mahaifiyarta kuka tz ke sosai don ma Allah yasa Bashir yana matuƙar kula da ita sosai,baya son ɓacin ranta tattalinta ya ke tare da mayuƙar ƙaunarta,farin cikin da Jamey ta rasa acen baya a yanzu ta sameshi nin kin ba nin kin. Rayuwa kenan juyi-juyi ce duk abinda ka aikata wataran shi zaka girba walau mai ƙyau ko mara ƙyau,har gida yaya deen yazo ya nemi yafiyar Jamcy yana kuka kamar zai shiɗe Allah ya taimaka ranar ma Ahmad baya nan da sai anyi ɓatacciya,ban sanda na yafe mishi ba ko babu komai ɗan uwa na ne. A yanzu aurensa da Anty Safiya ya mutu,duk son Yaya Deen da ta ke yanzu sai dai ta kalleshi don ko kallon inda ta ke bayayi don gani ya ke duk matsalar da ya shiga ita ce sila,ɗan su ɗaya yana nan abin tausayi. Ita kuwa Anty Safiyya yanzu ta yi aure kusan sa an Abbanmu matansa uku ita ce ta huɗu,ranar da na je gidan na ganta kamar zan mata kuka don ta zama abin tausayi,sosai na taimaka mata don d alhmdh mijina ya wadatao ni sosai, kishiyoyinta sun saka ta agaba sosai wai juya ce don tunda tazo gidan bata taɓa ɓatan wata ba.ina ji ina gani haka nabar anty safiya cikin wannan halin don daman ita duniya ta isa kowa riga da wando. Tun safe Jamey ta ke ta kuka har da shagwaɓa wai sai taje gidan Jamcy babu yadda Bashir ya iya a haka ya ɗakko Jamey tana ja da ƙer don yanzu cikinta ya tsufa. Ita ma Jamcy yanzu cikinta ya tsufa sosai haihuwa ko yau ko gobe,ranar a gidan Jamey ta yini suna zaune suna kallo aka nuno wata matashiyar mata wacce ba za ta wuce shekarunsu Jamcy ba,mutane suna ta mata kirari da Uwar marayu matar gwamna. Da sauri Jamcy ta tashi duk da tsohon cikin da ya ke jikintanta ce"Daman zan ƙara ganin Fatima a rayuwata?". Nan Jamcy ta ƙara faɗawa Jamey wannan itace Fatiman da ta ke nema,suka yanke washe gari zasu je govn hause don neman iso wajen Fatima. Basu sha wahala ba wajen yardar mazajensu don da kansu suka kaisu wajen Fatima,Allah ya taimakesu da ranar Fatima tana gida bata fita ba,aka yi musu iso da ƙer suka ganta don ma Fatima macece mai son mutane ce. Da gudu Fatima ta rungume Jamcy tana kuka sosai,dukansu kukan suke murnar ganin junansu ta cikasu sosai. "Fatima yanzu muna gaei ɗaya ashe har kinyi Aure govn amman kika kasa nema na". "Jamcy ba zaki gane halin da na ke ciki bane don wallahi babu yadda banyi ba in nemo inda kike amman abu ya faskara,yanzu Umma na ahekararta ɗaya da mutuwa sakamakon ciwon zuciya,anan nema governor ya aureni don har gidan radio naje daga nan yaji tausayi na ya aure ni,jamcy na yi baƘin cikin rashin dangi don ko babu komai idan na ganki nasan ina da dangi amman na nemeki Jamcy amman abu ya gagara. Gaba ɗayansu suna cikin farin cikin ganin junansu kuma ko wannensu ya bada labarin bayan rabuwa,bayan sunsha kukan rashin Umma. Ɗan Fatima ɗaya abdul ƘyaƘƘyawa irin asalin fulanin yola. *After five years* a yanzu Jamcy tana sa ƴaƴa uku twins duk maza da kuma mace,Jamey kuwa tana da ƴaƴa biyu duk maza. Masha Allah yanzu ma auratan suna zaune cikin aminci da ƙaunar junansu. Tammat bi hamdillah Anan na kawo ƙarshen wannan book ɗin mai suna Jamila,dafatan zamu amfanu da abinda aka karanta. Aƙwai mistake na wattpad user na Rabiatu333 shine user na na wattpad. Domin sharhi ko gyara 07068606171