SARA SA SASSAƘA... AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOUNG TALENTED WRITE'S ASSOCIATION (YOTA 002) BRIGHT PENS. ƘI BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM P1 15 ga watan Ogusta, hadari ya yi ganganko a sararin samaniya, babu abin da ake iya gani face hasken walƙiyyar da hadarin yake ta yi babu ƙaƙƙautawa. Haka zalika babu abin da kunnuwa ke iya ji, banda sautin rugugin cidar hadarin nan. Riƙe yake da hannun matashin yaron da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma riƙe da kaya, su na ta sauri, suna ratsa tsakanin zangarniyar hatsi, da ta yi tsawo, kasancewar tsakiyar damuna ne, amfanin gona ya fito ya yi kyau. Da kyar yaron yake cira ƙafafuwansa, duk da saurin da mutumin da ya riƙa masa hannu yake yi. Zuciyarsa ɗauke da wani nauyi da yake barazana ga numfashinsa, haka yake bin mutumin, yana jin kansa tamkar ba shi ba. Sannu a hankali yayyafi ya fara sauka kaɗan-kaɗan, a daidai lokacin da walƙiyya ta haska wata ragargajajjiyar hanya mai tarin kwazazzabai da da ramuka suka fito. Mutumin ya kalli yaron, zuciyarsa na wani irin raɗaɗi, tamkar mai ci da wuta, raɗaɗin da yake tasowa daga zuciyarsa har maƙogwaronsa yake ji, tamkar zai tsage,ya ja ya tsaya. A raunane ya dubi yaron ya ce "Ka yi haƙuri, tun da na fito da kai hanya, maza ka yi sauri ka bar garin nan, kar ka bari gari ya waye su cim maka, ka dai ji abin da suka faɗa da kunnenka. Idan Allah ya ƙaddara saduwarmu a gaba, sai mu sake haɗuwa. Ya damƙawa yaron ƙullin kayansa, sannan ya zura hannunsa a cikin aljihunsa, ya ciro kuɗi ya damƙa masa. "Ga wannan, maza ka ci gaba da tafiya, idan ka samu guri ka laɓe kar ruwa ya dake ka" Tun da ya fara maganar, yaron yake bin idanunsa da kallo ta cikin hasken walƙiyar da ake yi. Jikinsa a sanyaye ya ce "Ka tafi sumale, kar su same ka" Ba tare da ya furta uffan ba, yaron ya juya ya fara takawa, bai fi taku biyar ya yi ba, ya tsaya ya waiwaya, ya ga mutumin ya kama hanyar komawa cikin ƙauyen. Ya tsaya ya zuba masa ido, a dai-dai lokacin da ruwa mai ƙarfin gaske ya ɓalle, ya fara zuba a jikinsa. "Zan dawo, tabbas zan dawo, gobe, jibi, ko kuma gata? Ban sani ba, amma dai na san zan dawo" Ya furta yana haɗiye wani raɗaɗi da yake yi masa ɗaci a maƙogwaronsa. ***** Gari ya yi tsit, babu abin da ke tashi, sai sautin kai komon ababen hawan jami'an tsaro, tituna babu kowa sakamakon dokar ta ɓaci da aka sanya, saboda gudun tashin tarzoma a daidai lokacin da ake shirin sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasa. Galibi mutane na cikin gida, da radio wasu da waya wasu talabijin, wasu da na'urar buga lissafa, su na lissafin yawan ƙuri'un da wanda suke so suka samu, su na dakon faɗin sakamakon, daga hukumar zaɓe mai zaman kanta. **** Dattijo ne ɗan shekaru sittin da takwas, wanda hutu da jin daɗi ya ɓoye tsufan nasa, ya koma tamkar ɗan shekaru hamsin. Yana tsaye ya zubawa hotuna uku da suke jikin katafaren ɗakin ido. Hoton shugaban ƙasa, da gwamna sai kuma sarkin garin. Bayansa kuma wasu manyan dattijan ne sa'aninsa, a zazzaune sun yi shiru, su na dakon abin da zai ce. Ya juyo a hankali, ya ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya, ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce "Haƙiƙa ya ƙetare iyakokin da muka gindaya masa, ba tare da duba mu muka ɗora shi a kan mulki ba. Motar kawai muka ba shi, amma sitiyari yana hannunmu. Dan haka zamu murza sitiyarin da fasinjojin zuwa inda muke so. Idan ya so a mutu har liman in dai lissafin siyasarmu ya fita shikenan" "Wannan gaskiya ne" suka amsa cikin girmamawa. "Za mu ƙirƙiri abin da zai hana shi mulkin nan cikin kwanciyar hankali, zamu ɗora daga inda muka tsaya a wancan karon, zamu haɗe koko giya, zamu saka masa pressure da hankalinsa zai koma kan kawo daidaito, a dai-dai lokacin da zamu saka a matsa masa lamba" Ɗaya daga cikin mutanen ya ce "Amma ta yaya kenan ranka ya daɗe?" Mutumin ya ƙara murtuke fuska ya ce "Amfani da tsaro mu sanya tsoro!!!" ***** MAFARI... Masu iya magana na cewa tushiya masomar dawa, kuma duk wanda ya bar gida gida ya bar shi. Kowace halitta na alfahari da tushiyar da ta samar da ita, sai da tamu tushiyar, ta ginu a kan wata mummunar aƙida da muka buɗi ido, muka ga iyaye da kakaninmu a kanta, ba tare da sanin yadda aka yi ta fara ba, sai jin wai wai a cikin labarai da su kan bamu. Har gaban abada majigin abin da ya faru, ba zai taɓa barin allon zuciyata ba, hakazalika zuciya ba zata gushe ba, tana raɗaɗi da sanya idanu zubar hawaye, a sanadiyar gadon bashin gabar da iyaye da kakaninmu zuwa kanmu, babu abin da muke yi bayan lissafa asararta. Ƙauyenmu na can wani yanki a can cikin ƙauyukan wata jiha a arewacin ƙasarmu. Inda ƙabilu uku zuwa huɗu ne muke rayuwa a guri ɗaya. Kowane ƙabila a cikinmu, akwai nau'in sana'ar da suka ƙware a kai. Sai dai wannan zama da muke guri ɗaya, bai zame mana Alkhairi ba, domin ƙabila ɗaya daga cikin ƙabilu uku, sun fi mu yawa, da ƙarfi dan haka sun mayar da mu tamkar bayinsu. Sauran ƙabilun nan ta ƙarfin tsiya suka bar tsakiyar garin Yelwa, su ka bar garin baki ɗaya, zuwa nesa kaɗan su ka kafa nasu garuruwan, aka bar ƙabilu biyu a cikin garin. Bari na gajarce muku dogon labari zuwa gajere, domin hana shi gundurarku, labarin da nake son baku, ya fara ne daga wani lokaci. Damuna uwar albarka, in ji masu iya magana, kasancewar ta lokaci da al'umma ke amfana da tarin alkhairan da take tattare da ita. Yanayin garin ya canza da sassanyar iska mai samar da nutsuwa. Korayen bishiyu masu kyawun kallo ga idaniya, kuma abinci ga dabbobin tudu da na Daji. Tumbatsar tekuna, da samun wadataccen ruwa, ga mutane da dabbobi, ga uwa uba na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar, wato noma da ake a wannan yanayi, domin samar da abinci. Zukatan makiyaya tare da manoma, yana cika da farin ciki, a dai-dai lokacin da damuna ta kankama. Cak na tsaya na ɗaga kaina, ina kallon yadda garin ya yi duhu, hadari yake ta rugugi, wanda idan har ya zubar da ruwa, zai zama ruwan farko da ya zuba a wannan damunar. Duk da son yanayin na damuna da nake yi, ƙasan zuciyata a cike yake da zullumi da tashin hankali. Domin daga lokacin da damunar ta kankama ya kan zama tamkar zagoyawar jijjiga tsohuwar gaba, da mummunan tashin hankalin da yake tsakanin ragowar ƙabilu biyun da ke rayuwa a ƙauyen Yelwa. Adadin yadda garin yake ƙara duhu, haka tashin hankali da mummunar fargaba, ke ƙara mamaye lungu da saƙo na zuciyata. Ina kallon yadda mahaifina ke kaiwa yana komowa a tskar gida, yana magana da Innarmu, sai dai a muryarsa nake iya karanto damuwa da rashin nutsuwa. "Kai abin nan da mamaki fa, ina Iro ya shiga a wannan tsohon daren, ga gari na damina fisabilillahi, ai ko yawon zai je, ya bar wa gobe. Kwata-kwata yaushe ya dawo ma, da zai yi nisa haka? Ke Mairo, ba ni tagiyata na zagaya ko Allah zai sanya na gan shi" Ya yi maganar cikin damuwa. Innarmu ta amsa masa da to, ta ba shi hularsa ya karɓa  ya fita. Ban san dalili ba, na ji jikina ya yi sanyi, na ji tamkar ƙafafuwana ba za su iya ɗauka na ba. Haka nan zuciyata ta din ga bugawa, da wata irin matsananciyar fargaba da ban san ta mece ce ba. Daki-daki nake tuna abin da ya faru. Kwanaki biyu kenan, da dawowar Iro daga kiwo da ya tafi, ya shafe watanni huɗu, ba ya garin da dabbobinmu. Na dawo daga rafi, ina tafe ina ta karanta wasiƙar Jaki a zuciyata, da tunanin ta inda zan samu nasarar abin da nake kwana nake tashi da shi a cikin zuciyata. A dai-dai lokacin  na hangi kyakyawan murmushi a kan kyakyawar fuskarsa. Ban yi ƙasa a gwiwa ba, na mayar masa da martanin murmushin na ce " Wannan kwalliyar da ka sha haka? Ina aka nufa?" Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kin aike ni ne?" Na girgiza na ce "Ai gani na yi bamu gama ganin ka ba, amma har za ka fita. Ko zance za ka je?"  Na ƙarasa maganar ina yin ƙasa da muryata. Daƙuwa ya yi mini ya ce "Wuce ki shiga gida, idan na dawo akwai tarin labaran da zan baki. Kuma ki kula da karsanar nan dan Allah, alamu sun nuna, ta kusa haihuwa" Na jinjina kai na ce "Sai ka dawo. Ina jiran ka zo ka bani labarin, dan ka san duk inda labari yake ina gurin, kuma bana raina saurarensa, komai ƙanƙantarsa. Dan akwai darasi a cikin kowane labari. Tun daga wannan fitar, har wannan lokacin, kusan ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare, bai dawo ba. Sallamar Baffa ta katse mini tunanin da nake yi, sai dai gabana ya yanke ya faɗi, ganin Baffa shikaɗai ba tare da Iro ba. Tun kafin Baffa ya furta komai, bugun zuciyata ya ƙaru, abin da ya furta kuwa ya kusa katse mini numfashi. "Na je duk inda nake tunanin zan gan shi, ban same shi ba" Inna ta ɗora hannu a ka ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ina yaron nan ya shiga haka? Iro bai taɓa irin wannan ba" Ni dai tamkar an shuka ni, domin gani nake su da suka haife shi ma, ba su kai ni tashin hankali da fargaba ba. A hankali kunnuwana su ka fara jiyo mini hayaniya sama-sama, na kalli su Baffa ko sun ji, amma na ga babu alamar suna jin hayaniyar. Sai daga Baya Baffa ya ɗan yi shiru ya ce "Kamar hayaniya nake ji fa" Da sauri na ce "Nima haka" Jin hayaniyar na ƙara kusantowa, ya sanya Baffa yin waje da sauri, ba mu jira komai ba daga ni har Inna, mu ka rufa masa baya, hannunmu ɗauke da cocilan. Dandazon mutane mu ka gani, ɗauke da cocilan a hannayensu, da sanduna su na ta hayaniya. Kafin mu ƙarasa tuni Baffa, ya ƙarasa ya kutsa cikin dandazon mutanen. Tsananin azalzalar son sanin abin da yake faruwa ya ingiza ni, na taka da gudu, ba tare da tunanin komai ba, nima na kutsa  domin ganin abin da yake faruwa. Sai dai kafin idanuna su gane mini komai, sautin salatin Baffa ya karaɗe kunnuwana, fiye da hayaniyar mutanen, wanda ya yi daidai da ganin Ironmu a kwance, cikin jini jikinsa futu-futu da taɓo, sai zubar da jini yake yi. Durƙusawa na yi jikina na karkarwa, tamkar ana kaɗa mini mazari. Baffaa ya rirriƙe Iro, ya fashe da kuka yana tambayar "Me ya yi muku? Me Iro ya yi muku daga dawowarsa Sale?" Ba tare da Sale, ya duba adadin furfurar kan Baffa ba, ya haske shi da fitila ya ce "Au tambaya ma ka ke yi? Hukunci ne da muka zartar a kan wanda yake tunanin karansa ya kai tsaikon da zai iya taɓa ahalinmu. Kai ku ja shi a ƙasa, ku ɗaure shi a jikin bishiyar nan, ya zama izina, ga duk wani wanda ya gaza ɓoye ƙwalamarsa a kan 'yan matan manoma" Ras gabana ya yi mummunar faɗuwa, me Saleh yake nufi? Me yake Irona ya aikata da har ya cancanci wannan tozarcin? Na yi kukan kura, na damƙe jikin Iro, da ba ni da tabbacin akwai rai a gangar jikinsa, ina kuka, na gaza furta komai. Saleh ya haska ni da fitilar hannunsa nima,  ya saka hannunsa ya fizge ni daga jikin Iro, ya yi jifa da ni gefe ɗaya, ya hankaɗe Baffa, ya ja Iro a ƙasa, sauran matasan suka rufa masa baya, wasu na dukan Iro da ƙafa, wasu na kwaɗa masa sandunan hannunsu. Maƙwabtanmu suka fito, su na yi wa Saleh magiya, a kan ya yi haƙuri, a yi magana a sansanta, a ji me Iron ya yi musu, amma ya ce duk wanda ya kuma yi masa magana, sai ya haɗa da shi. Na tashi na kuma nufar su, ina gursheƙen kuka, amma babu wanda ya saurari kuwwa da magiyarmu a cikin matasan nan. Aka rirriƙe ni, saboda kada Saleh ya cutar da ni. Mu na kallo su ka ɗaure Iro a jikin bishiyar darjebiya. Cikin isa da bayar da umarni Saleh ya ce "Ku je gidan su, ku kwanto mini dabbobin da suke garken gidansu, zai zamana tamkar diyyar abin da ya aikata mana. Kuma wallahi duk wanda ya kwance shi daga jikin bishiyar nan, sai na yi masa abin da ya yi mana. Ba wannan ba ma, ina mai sanar da ku da jaddada muku, wannan hukuncin shi ne zai biyo bayan duk wanda ya aikata irin laifin da Iro ya aikata. Mun kama shi da yinƙurin haikewa ɗaya daga cikin yaranmu a bayan gari, dan haka wannan sai ya zama izina ga duk mai yinƙurin aikata laifi makamancin wannan. Suman zaune na yi, da jin maganganun da suka fito daga bakin Saleh. Ko rantsuwa na yi ba na tunanin kaffara za ta hau kaina, ƙarya yake yi wa Ironmu. Innarmu tuni ta sume dama, mu na ji mu na gani aka kaɗo dabbobinmu, aka shiga cikin gidanmu aka burkice komai, suka tafi suka bar Iro ɗaure a jikin bishiyar nan. Na yi kuka, na yi gunji, na yi yinƙurin zuwa inda ɗan uwana yake, amma aka tare ni aka hana ni, saboda gudun abin da ka iya biyo bayan zuwa gurin nasa. aka kece da ruwan sama, ma ƙarfin gaske, haka mu ka yi kwanan baƙin ciki da takaici, zukatanmu da na kusa da mu cike da baƙin ciki da ɓacin ran, da baki ba zai iya bayyana nauyin da zukata ke ɗauke da shi ba. Da Asubar fari, muka fito, babu alamar rai a jikin Iro. Har rana ta fito ta take, babu wanda ya iya zuwa inda Iro yake, saboda tsoron abin da ka iya faruwa. Kamar yadda tun tasowarmu, haka muka tarar da iyayenmu na rayuwa a cikin wannan tsoron, da ya yi wa rayuwar su dabaibayi, ake yi musu cin kashi yadda aka ga dama, mu ma kuma su ka haife mu, muka tashi a haka. Sai da rana ta take, sannan Saleh ya taho da tawagar sa, ɗauke da wasu miyagun sanduna. Su ka kwance Iro, yadda ya faɗo timm, ya ƙara tabbatar mana da babu rai a jikin Iro. "Ka biyo mu bayan gari, ka binne wannan najastaciyyar gawar ɗan naka, dan ba za a sallaci mazainaci a cikin garinmu ba, ka je ka haƙa rami ka binne shi, a can bayan gari shikaɗai, dan wannan ƙazamar gawa ce, ba ta cancanci sutura ba". Duk da ƙulli gami da ƙudurin da yake cikin zuciyata tun bayan da na tasa, na fara mallakar hankalina kaina, a yau na ajiye alwashina a gefe, na fito gaban mutane na sanya gwiwoyina a ƙasa, cikin magiya da hawaye a gaban Saleh, muryata na rawa na ce "Ka duba girman zatin Allah, ka yi haƙuri a yi masa sutura a binne shi kamar yadda addini ya tanada, ko wani laifin ya aikata, musulmi ne shi, dan Allah" Ya zura mini ido na wani lokaci, daga bisani ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya, mai cike da rashin ɗigon imani ya ce "Jikar makiyaya, har kin karaya? Har kin manta alwashin da ki ka yi a kaina? Yau ke ce a gabana ki ke neman alfarma? Na so a ce zan iya yi miki wannan alfarmar, ko dan duƙa mini da ki ka yi, sai dai kash ɗan uwanki fasiƙi ne, kuma da ya tashi bai gwada halin nasa a kan kowa ba, sai a kan ahalinmu, dan haka wannan shi ne abin da ahalinku ya cancanta" Ina kuka su ka tasa Baffa shikaɗai ƙwal, suka ja gawar Iro a ƙasa suka nausa cikin daji. Duk dandazon mutanen da suke gurin, babu mutum ɗaya da zai iya faɗa a ji, balle ya tsawatarwa Saleh. 'Yan uwan mahaifina, su ka haɗa kai su ka tafi gidan su Saleh, wanda mahaifinsa ne, jagoran garin namu baki ɗaya, amma suka dawo gwiwa a saɓule, saboda yadda ya goyi bayan abin da ɗan sa ya yi. Tare da Jaddada cewar, an kama Iro da yinƙurin aikata wannan mummunan laifi, ba ƙazafi aka yi masa ba. Duk da ba yau aka saba danne mu, da yi mana mulkin kama karya a ƙauyenmu ba, amma wannan karon an bar mana wani mummunan miki da zai dauwwama a cikin zukata har gaban abada. A iya sanina da ɗan uwana, mutum ne mai taka tsantsan da gudun duniya, kullum hankalinsa yana kan, yadda zai kiyaye mu, ya kiyaye mutuncinmu mussaman ni da Akuyata ta yi kuka a garin, kuma nake takun saƙa da Saleh. Kullum cikin nasiha yake yi mini, da ja mini kunne, a kan na yi haƙuri da abin da Allah ya hukunta mana, na rayu cikin salama da aminci. Baba ya yi niyyar haɗa Iro, shi da 'yar Baffanmu Mariya aure, amma ya nuna shi ba ya buƙatar aure a wannan lokacin, kasancewar Babanmu mutum ne mai son 'ya'yansa, sai ya ƙyale Iro bai sake yi masa maganar ba. Sai dai na damu matuƙa da son sanin, wace yarinyar ce wannan, da har ake cewa ya yi yinƙurin ketawa haddi? Mutumin da ya shafe watanni huɗu ba ya gari, yaushe ya dawo da har ya yi yinƙurin haikewa wata? "Wace yarinyar ce a garin nan? Dole na nemo wace ce, sai ta ɗanɗana abin da Iro ya ɗanɗana, kuma ko a mutu ko a yi rai, jinin ɗan uwana Iro ba zai tafi a banza ba. Amma wace ce wannan yarinyar?" Na sake tambayar kaina. Ghost writer 12/7/.... A hankali ta ja guntun tsaki, ganin a inda labarin ya tsaya, ta kai ta komo a cikin group ɗin, amma babu ci gaba. **** Dandazon 'yan makarantar islamiyya ne suke ta fitowa daga cikin makarantar, wasu sun tsatstsaya su na ƙoƙarin tsallaka titi da ababen hawa ke ta kaiwa su na komowa. Matashiyar yarinya ce, aƙalla za ta yi shekaru sha huɗu zuwa sha biyar, hannunta riƙe da jakar islamiyyarta, tare da wasu yaran, su na ta surutu, suka tsallaka titi, suka gota wani matashi a tsaye su ka wuce. Sosai suke dariya cike da nishaɗi, suna hirarrakinsu. Ta waiwaya ta hango shi a bayansu yana tafiya. Ba ta damu ba, suka ci-gaba da hira da ƙawayenta. Suna tafe duk wadda aka zo kan kwanar gidansu, sai su yi sallama ta tafi, har ya rage saura su biyu. Suka ƙarasa wata mararraba, ta dubi ɗayar Ta ce "To sai kuma Allah ya kaimu gobe, ki riƙe dai-dai inda ki ka tsaya mini, za ki ƙarasa bani labarin, ni idan Yaya ya kama ni da karatun littafi ina ga kashe ni zai yi, amma duk yadda za a yi ki karanto ki zo ki bani labari" Ɗayar ta yi dariya ta ce "Nima a ɓoye nake yi, sai kowa ya yi bacci, nake haska fitila ƙasa-ƙasa, ki gaida gida da matar Yaya" "Za ta ji in sha Allah, ki gaida su baby" Tana ƙoƙarin shiga wani layi, ta waiwaya baya suka sake yin ido huɗu da matashin nan. Dogo ne launin fatarsa ba za ka kira shi baƙi ba, kuma kai tsaye ba za ka ce fari bane. Fuskarsa na ɗauke da yanayi na samartaka, yana da ɗan jiki, sai dai fuskarsa a cike da ƙasumba, ya sanya wata uwar babbar riga duk ta yamutse babu guga, yana da manyan idanuwa sai dai ba farare bane, sun sirka sun yi ja, haka kurum ta ji tsoro na neman ya shige ta. Da sauri ta shiga layin nasu, amma da ta yi nisa ta waiwaya sai ta sake ganinsa. Ba shiri ta fara sauri tamkar za ta tashi sama. Ta sake waiwayawa cikin tsoro, sai ta ga ba taga gan shi ba. Ta yi ajiyar zuciya, ganin layin babu kowa, ya sanya ta kyalla da gudu ta ƙarasa gida. "Assalamu alaikum" Ta yi sallama daidai lokacin da ta faɗo tsakar gidan. Matashiyar mata ce a tsaye, tana kwashe shanya ta ce "Yaya? Ke da wa?" Ta ɗan waro ido "Wani mutum na gani, tun daga ƙofar islamiyyarmu yana bina"Ta yi maganar fuskarta na bayyanar da tsoro. Matar ta yi turus tana nazarin maganganunta. "Yake binki saboda me?" Ta ce "Ina na sani, daga baya dai da na shigo layin nan, ya daina bina, dan da na waiwaya ban gan shi ba" Ta yi murmushi ta ce "Alina kenan, ƙila ma hanya ce kawai ta biyo da shi, ki ka sani ma, ko saurayi ki ka yi, gani yayi yana so ya biyo ki? Amma ki ke ta guje-guje kamar ba budurwa ba" Ta waro ido tana ƙiftawa ta ce "Kai rufa mini asiri, kar Yayanmu ya ji wannan maganar ma, wai a ce na zo da saurayi ai sai ya kusa kashe ni, rufa mini asiri. Amma an rage abinci?" Matar ta  tsuke fuska ta ce "To acici, ai kya fara zuwa ki cire kayan ki nutsu tukuna" Alina ta nufi ɗakin tana murmushi ta ce "Kin san ina da tsutsar ciki ne, da na ci take cinyewa" "Ke ce tsutsar ai" Ta yi dariya tana shiga ɗaki. **** Tana tsugunne a cikin turken awakin da ke tsakiyar ƙaton tsakar gidan. Ta share turken tsaf, ta din ga kama dabbobin tana ɗaurewa ɗaya bayan ɗaya. Ta gama ta zuzzuba musu abinci da abin sha. "Sannu da aiki Ramatu" ta ɗago ta kalli farin dattijon, da yake zaune a kan tabarmar kaba, gefensa da radio yana saurare. "Baffa dan Allah ka din ga gaya mini sunan zamani, tun da ka je mini visiting, ka faɗi Ramatun nan, ake tsokanata" Ya yi dariya ya ce "To Ramata" "Kash ana jika dai kunamar bebe Baffa, ka ce Rahma" "Na ƙi" ya yi maganar yana dariya. Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi a kan tabarmar. "Idan kin huta, zan baki magani ki kai wa Talatu, an ce yaronta yana masassara" Ramata ta rausayar da kai "To Baffa" ta yi maganar tana ɗan sunkuyar da kai. "Ramata, na san abin da ki ke tunani, babu ruwanki da su, da kin kai ki dawo, kar ma ki tsaya ki ji me za su faɗa" Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Baffa, amma dama... "Dama me?" Ta ɗan daidaita nutsuwarta ta ce "Baffa zan samu ci gaba da karatun kuwa?" Ya ɗan yi shiru, sannan ya dube ta "Ramata, zan yi alfahari na ga kin yi karatu mai zurfi, wataƙila albarkacinki, mu samu ci gaba da mafita a garin nan, amma kina kallo a haka ma, su na nema su kafirta mu, saboda makarantar da ki ka yi. Ki yi haƙuri a manemanki, ki samu wani ku daidaita ko ba yanzu ba, idan da rabo sai ki ga kin ci gaba a gaba. Amma ba na so baki ya yi mini yawa a kanki. Duk da na san ko a yanzu mun ciri tuta kaf rigar garin nan, babu wadda ta samu ilimin da ki ka samu, na shiga kundin tarihi ginis rikol suke cewa a radio ko me?" Ramata ta tuntsire da dariya ta ce "Baffa guinnes world record ake cewa. Kar ka damu ko kai ba ka shiga ba, ni zan shiga, zan rubuta littafi mafi tsawo a duniya, ko kuma wani abu mai ban mamaki dai, da sai duniya ta tafawa Ramatanka" Baffa ya yi dariya ya ce "Ko a yanzu dole na tafa miki ai. Ai ni tun da aka nuno mini ke a salalula, kin ci gasar lissafi, sannan na ji sunanki da nawa a radiyo, na ce haihuwa mai rana, dalilin ramatuna ga sunana a radiyo" Wata mata ce ta fito, daga ɗaya daga cikin jerin bukkokin da suke harabar gidan, tana jan guntun tsaki, da surutai ƙasa-ƙasa. Ta harari inda su Ramata ke zaune suna hira. Ramata kuwa hankali kwance suka ci gaba da hira da Baffanta. "Yanzu ka ga Baffa, da karatun boko ka yi, tsaf za ka zama farfesa, kana da saurin gane abubuwa da riƙe su" Suka yi dariya baki ɗaya. ***** Su na zaune da daddare su na cin abincin dare. "Alina" ya kira sunanta "Na'am Yaya" "Tunanin me ki ke yi ne?" Ta ce "Ba komai, abinci nake ci" Yaya ya ce "Faɗi gaskiya dai" Matar Yaya ta yi murmushi ta ce "Alina na faɗa" Ta ɗago ta ce "Me?" "Abin da ki ke tunani mana" Alina ta yi dariya ta ce "Ai babu abin da nake tunani" "A'a fa, Yaya saurayi ta yi shi ne... Da sauri Alina ta ce "Innalillahi, wallahi yaya ba haka aka yi ba, haba Anty idan ya zane ni fa?"ta ƙarasa maganar a shagwaɓe, kamar za ta yi kuka. Ta kwashe da dariya ta ce "Yaya ka san ba zan yi mata ƙarya ba ko? Siriki ta samo maka" Cikin tsoro ta ce "Wallahi ni ba saurayina ba ne ba, kin gan shi kuwa, ƙazami da shi fuskarsa duk gashi" Ta yi maganar duk a ruɗe, da ƙoƙarin kare kanta, kar yayan ya ɗauka da gaske ne. Ganin ta ruɗe shi ma ya ce "A'a mutuniyar gaya mini gaskiya, idan aure ki ke so ai ba wani abu, ki turo shi mu gaisa mana" Kawai ta hau kuka "Ni wallahi ba saurayina ba ne, ba aure nake so ba" Gaba ɗaya suka hau yi mata dariya, ya ce "Ni dai kin san bana son kwana-kwana, abin da ki ke so shi nake so. Masoyiyya ina ga zan ba ki kuɗi a fara sayayya" "A'a da wasa nake yi, haba Alina daga wasa sai kuka, ba mai yi miki aure yanzu, sai mun gama jin ɗumin juna ko ƙanwar yaya?" Ta yi maganar tana janyo Alina jikinta. Ya yi dariya ya ce "Wai kukan take da gaske?" "Wallahi kuka take yi" Ya miƙe yana faɗin "Babu ruwana, ai kun fi kusa, Kano da jigawa in ji kanawa, ke ki ka haɗa zancen" Da kyar ta rarrashe ta ta daina kukan. **** Uniform ɗin makarantarta sun sha karin guga, tana tafe tana ta ƙara karkaɗe ƙura daga jikin uniform ɗin, idan ta karkaɗe uniform, sai ga koma karkaɗe jaka, ta koma kan goge takalmi. Ta ɗaga kai zata shiga lungun da zai ƙarasa sadar da ita da titi, kawai ta gan shi a tsaye cak yana kallonta, da manyan idanunsa tamkar za su faɗo, yau ma da wannan Koriyar babbar rigar a jikinsa, wadda take duk a yamutse. Gabanta ya yi wata irin faɗuwa ta tsaya cak. 1k ne littafin nan a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Sai shaidar biya ta 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA SA SASSAƘA... AISHA ADAM (AYSHERCOOL) YOTA 002 Wannan littafin 1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Shaidar biya ta 08081012143 Page 2 Ganin yadda ta tsaya tana kallonsa, ya sanya shi yin gaba ya bata hanya dan ta wuce. Haka kurum ta ji jikinta ya yi sanyi, kawai ta canza hanya zuwa wata hanyar daban. Tana tafe tana waige-waige cike da matsanancin tsoro, dan gaba ɗaya ba ta yarda da mutumin ba. Ana tsaka da assembly sannan ta shiga cikin makarantarsu, sai da ta ga ta shiga tukuna, sannan hankalinta ya kwanta ta samu nutsuwa. **** Tana zaune ta yi shiru, ta lula a duniyar tunani, hankalinta da tunaninta ya yi nisa sosai da duniyar da muke ciki. Daga can sama-sama ta jiyo muryarsa "'Jikar makiyaya hattara, idan shanunki suka yi mini ɓarna, da ke zan tafi a maimakon ɓarnar da suka yi mini" A firgice ta waiwayo dube shi, ta yi ajiyar zuciya. Ya zauna a kusa da ita yana murmushi. Cikin damuwa da sassanyar muryarta ta ce "Wallahi ka tsorata ni, na ɗauka da gaske ne, har na fara tunanin ɓarakar da zata iya faruwa, a dalilin hakan" Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, Ubangiji Allah ya kawo mana ƙarshen wannan tashin hankalin in sha Allah duk zai zama tairhi wataran. Ni ki ke jira ne ko ya ya?" Ramata ta dube shi, dogon matashi baƙi. Ta rausayar da kai ta ce "Bayan kwana biyu ko ka neme ni" Ya lumshe idanunsa yana kallon kyakykyawar fuskar Ramata, mai ɗauke da siririn bille "Kin san ba na son a gano mu ne, kar a samu matsala, amma ki na nan ɗi na" Ya yi maganar yana nuna mata saitin zuciyarsa. Ta kwaɓe fuska ta ce "Ni na yi fushi" Ta yi maganar tana tura baki, tare da kawar da kanta gefe, dan ba ta iya haɗa ido da shi. Ya haɗa hanneyensa biyu ya ce "Tuba nake yi, ki yi haƙuri dan Allah hasken rayuwata" Ya yi maganar yana murmushi. Ta yi murmushi ta ce "Ka san ba zan iya fushi da kai ba ai" Ta yi maganar cikin ƙoƙarin faranta masa rai, duk da matsananciyar kunyar da take ji. Ta saka hannu ta ɗaukko wayarta da take ajiye a gefenta, ta duba. Ta dube shi ta ce "An saki sakamakon jarrabawarmu, ka ji yadda ƙirjina ya buga da sauri kuwa?" Ya leƙa fuskar wayar, kamar zai iya gano wani abu a ciki ya ce "A'a ki kwantar da hankalinki, khairan in sha Allah, ina da yaƙinin za ki cinye duka jarrabawar" Jikinta a sanyaye ta ce "Allah ya sa, ka san jarrabawa ikon Allah ce kawa. Aikuwa dole gobe in Allah ya kaimu in tafi cikin gari na duba." Bukar ya dube ta ya ce "Babu wanda zai dubo miki sai kin je har cikin gari da kanki?" Ramata ta ce "Gara na je da kaina, ba lallai wanda zai je ya iya duba mini yadda nake buƙata ba" Bukar ya ce "To ko na jira ki a bayan gari mu tafi tare?" Ta girgiza kai da sauri ta ce "A'a Baffa zai raka ni. Idan kuma Allah bai sanya na duba yanzu ba, sai kuma idan na koma makaranta tun da su can kafe ta ake yi gaba ɗaya, wannan kuma a computer ko waya ake dubawa. Bari na je gida na gaya masa ma, Ubangiji Allah ya sanya sakamakon nan ya yi kyau, na sanya shi farinciki" Ta yi maganar tana tashi tsaye. Shi ma ya tashi tsayen ya ce "Amin ya rabb, Allah ya sa sauran mutanen ƙauyen nan, su yi koyi da baffanki a kan jajircewa, a yi ta samun yawan wanda za su nemi ilimi." Jikin Ramata ya yi sanyi ta jingina da jikin bishiya ta ce "Yaya Bukar" "Na'am Ramata" ya amsa cikin nutsuwa yana kallonta "Duk da yadda muka shaƙu,na san babu lallai aure ya yiwu tsakaninmu, ka ga a garin nan su na ce mini karuwa, saboda Baffa ya kai ni birni makarantar kwana, kuma na kai wannan shekarun Baffa bai yi mini aure ba. Ga kuma abin da yake tsakaninmu da zuriyarku na rashin jituwa, ba za su taɓa bari mu yi aure ba ko?" Bukar ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ramata, ki ƙarfafa zuciyarki ki yi koyi da Baffanki a kan jajircewa. Kar mu bar wata gaba da rashin jituwar da ba mu san lokacin da aka fara ba, su hana mana cikar burinmu. Sai dai ban sani ba, ko ba za ki iya aurena ba, saboda ni ba ɗan boko ba ne kamar ke" Ta durƙusa ta ɗauki sandar kiwonta, ta kalli Bukar ta ce "Karatun boko baya cikin sharuɗan aure, kuma boko ba ta sanya na sauya da komai ba, sai abin da na san ba daidai ba ne" Bukar ya ce "Gaskiya ne. Muje na taka miki zuwa kan iyaka" suka tafi su na ci gaba da hira. Ko da ta koma gida, ta shigar da shanun turke, tana tsaka da yi musu hayaƙi, Baffa ya fara ƙwala mata kira. "Na'am Baffa" "Wai ke kina 'yar boko amma ba za ki fasa fita kiwo da shanu ba, ba kya gudun a samu matsala ma" "Baffa ba za a samu matsalar komai ba da yardar Allah, na kula da komai yadda yakamata" Ta yi maganar tana fitowa daga cikin turken. "Kina dai bawa 'yan boko kunya, ina ɗan boko ina yawo da nagge" Ramata ta yi murmushi, ta ci gaba da karkaɗe hannunta. "Idan kin gama, ki zo mu je ki raka ni zan duba marasa lafiya" "To Baffa" ***** Matsakaicin gida ne, mai ɗauke da 'yan madaidaitan ɗakuna. Wata mace ce take ta kai wa tana komowa a tsakar gidan, tare da wasu 'yan mata su uku, biyu na ta aikace-aikace ɗaya kuma na zaune tana kallon waya tana tsifa. Ta dubi ta zaunen ta ce "Mariya, tashi ki je gidan su Bilal, ki ce idan ta haɗa ƙanzon ta baki ki kawo mini. Sai ki biya ta shagon iliyasu ki karɓo man wanke baki, ki sayo sugar sonake zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa jibi an gama haɗa mata kayan komawa makarantar nan" Mariya ta tsuke fuska ta ce "Mama wannan makarantar, in dai za ta koma duk sai kin ɗaga mana hankali, kamar ita kaɗai ce 'ya" Ta yi maganar tana harar Nana da take wanke-wanke. Naja ta yi murmushi ta ce "Kwantar da hankalinki, idan ba za ki je ba, ni idan na gama wanke-wanke na je na karɓo" "Dama hakan aka yi, da ke da Yaya duk lokacin da ku ka zo hutu, idan za ku koma duk sai ta tashi hankalin kowa, idan kun tafi ma ba ta da aiki sai zancenku" Ɗaya yarinyar da tun da aka fara ba ta yi magana ba, ta dubu Mariya ta ce "malama ki tashi ki je aiken da aka yi miki" Mariya ta tura baki tana tashi tsaye. Mama ta ce "Ai Hafsan ita ce daidai ke, tun da ni kin raina ni. Taho mini da wayata idan ina da ɗan canji na kira yaron kirki na ji ya yake" Mariya ta fito riƙe da hijjabinta, da wayar Mama ta miƙa wa mama wayar. Ta karɓi wayar ta daddana, ta saka a kunnenta ta ɗan yi shiru ta ce "Alhamdillah ta shiga" A nutse ya yi sallama, fuskar Mama ta faɗaɗa da murmushi ta ce "Soja mazan fama" Tamkar yana gabanta, haka ya risuna ya ce "Mama ina wuni?" "Lafiya kalau Harisu, ka tashi lafiya?" "Alhamdillah Mama, ya su Naja ya shirye-shiryen komawarta makaranta kuma?" "Kana lissafe kenan, Alhamdillah ga shi mu na ta yi" Harisu ya ce "Ma sha Allah, Mama ku yi haƙuri dai, haryanzu ba a biya albashi ba, na so a biya mu kan ta koma, a ƙarasa mata sayayya, amma Allah bai nufa ba. Ki ba ta haƙuri, idan na samu yadda nake so bayan salary abin da ba a saya ba zan je da kaina na kai mata har school" Mama ta ce "A'a, ka kwantar da hankalinka ma, na haɗa mata abin da ya samu, kai ma ka kula da kanka, ku na barikin ne?" "A'a mu na daji fa a yi mana addu'a, ban gaya miki bane kar damu kanki" Kan Mama ta yi magana Mariya ta ce "Yaya dan Allah idan an yi muku albashin ka sayo mini nama" Hafsa ta ce "Ka ji mahaukaciya" Harisu ya ce "In sha Allah ko ban samu zuwa ba, zan aiko da shi a saya miki. Mama bani Naja zan yi mata magana" Mama ta miƙa wa Naja wayar, ta karɓa tare da yin sallama "Hello Yaya" "Sallama dai ko" "Yi haƙuri. Assalamu alaikum" "Wa'alaikum salam, ya shirin koma wa makaranta?" "Alhamdillah Yaya ya aiki" Harisu ya ce "Lafiya ƙalau Alhamdillah, ki na ji na Naja, ki yi haƙuri da abin da ya sauwwaƙa, in sha Allah abin da bab zan zo har makarantar na kawo miki. Ku yi haƙuri in sha Allah wataran sai labari zai wuce, za mu zame wa Mama ababen alfahari. Duk wannan wahalar za ta wuce" Naja ta yi murmushi cikin nutsuwa ta ce "Yaya dan Allah kar ka damu, wallahi ko ban tafi da komai ba, zan ci abincin makaranta na rayu, karatu kuma da yardar Allah ba zan baku kunya ba" "Alhamdillah barakallah, Allah ya yi mana albarka, ba wa ƙanwata wayar" Ta miƙa wa Hafsa ita ma su ka gaisa, Mariya ma ta karɓa tana ta rashin hankali, wayar ta katse katin ya ƙare. Soyayya da tausayin da suke nuna wa junansu ba ƙaramin sanya Mama farin ciki yake yi ba, ba ta jin tana damuwa da halin da suke ciki na babu, idan ta ga yadda Allah ya ba ta su shiryayyu. Harisu kuwa bayan ya ajiye wayar, Suleiman ya dube shi ya ce "Wannan duk ƙannenka ne Haris" "Eh Oga, ƙannena ne su uku ne Abbanmu ya rasu ya bar mini, su haɗu ma zan ce har da Mamanmu" "Wow, kai kaɗai ne namiji kenan?" "Eh nikaɗai ne" "Allah sarki, Allah ya baka wuyan ɗauka Haris, zan zo Mama ta bani ɗaya na aura" Haris ya yi dariya ya ce "Girmanka ne oga an riga ma an baka" Ya ƙarasa maganar yana murmushi. ***** Tun da Alina suka rabu da su Hafsa ta nufo hanyar gidansu, kawai gabanta ya hau faɗuwa, da tuna mutumin nan da take gani, da ta fara tunanin ko mahaukaci ne, yake bin ta. Ta fara addu'a a zuciyarta, da fatar Ubangiji Allah ya tsare ta daga sharrinsa koma wane iri ne shi ɗin. Sai dai ganin har ta shiga layinsu, ba ta gan shi ba, hankalinta ya ɗan kwanta. Sai dai tana sake waiwayawa ta hango shi a ƙofar wani ɗan ɗakin langa-langa, da ke ƙofar wani gida, yana ɗinke takalmi. Ta na tsayawa, su na haɗa ido, ta ji wani irin abu a jikinta. Ya yi mata dabaibayi da manya-manyan idanunsa, da suka surka da kalar ja. A take ta hau tsuma, ta kwasa da gudu ta ƙarasa gida. Daga cikin ɗakin Ismail ya ji Alina ta faɗo gidan ya ce "Yaya mene ne haka za ki faɗo gida haka da gudu kamar an sako shanuwa?" Cikin fargaba ta ce "Ni wallahi Yaya wannan mutumin kullum sai na gan shi, tsoro yake bani" Ba shiri ya fito daga ɗakin fuska a murtuke yana faɗin "Waye shi, me ya yi miki?" Tana ɗan rarraba ido ta ce "Bai yi mini komai ba, tsoronsa kawai nake ji, kuma kusan kullum sai na gan shi" "Mu je na ji dalilin da ya sanya yake tsorata ki" Ya yi maganar yana zura takalmansa a fusace. Anty Nadiya ta ce "Haba masoyi, kamar ba ka san shirirtar Alina ba, ban da shirirta ya za a yi haka kurum kawai ta din ga jin tsoron mutum, ka san ta saba irin wannan rashin kan gadon, kar ka je ta saka ka ji kunya." Sai kuma ya ɗan sassauta tsuke fuskar da ya yi, ya dubi Alina ya ce "Babu ruwanki da shi, muddin ya yi miki wani abu na rashin kyautawa, kawai ki gaya mini" ta jinjina kai, sannan ta nufi ɗakinta. Kwanaki biyu a jere, Alina duk lokacin da za ta fita, za ta ga mutumin nan, a ƙofar shagon nan, yana gyaran takalmi. Ta din ga ƙoƙarin koyawa kanta rashin jin tsoronsa, amma ta kasa mussaman idan ta tuna idanunsa, muddin suka haɗu suka haɗa ido, sai gabanta ya yi mummunar faɗuwa gaba ɗaya sai ta rikice. In dai za ta fita har addu'a take yi, Allah ya sa kar ta haɗu da shi. Cikin sa'a yau har ta je makarantar boko, ta je islamiyya ta dawo ba ta gan shi ba, sai da aka taso daga makarantar dare sannan ta gan shi a ƙofar makarantar su. Sosai abin ya fara damunta, ga shi tana tsoron jarabar Yaya, da sai ta sake gaya masa. Ta lura gaba ɗaya yanzu mutumin a layinsu ya tare, da safe zuwa azahar ya yi gyaran takalmi zuwa yamma ta ga ya kasa wani abin daban. A daren ranar ma dai da gudun ta shiga gida, ta laɓe a bayan ƙofa ta daidaita nutsuwarta, sannan ta shiga cikin gidan, dan haka babu wanda ya gane halin da take ciki. Da safe kuwa tamkar ta ce "Ba za ta je makarantar bokon ba, ko ta ce Yaya ya rakata. Yau ma sai da ta makara sannan ta fita, amma kamar yadda ta yi tsammani, yana jikin gidan da yake kallon nasu, ya zubo wa ƙofar gidan su ido kamar mai jiran tsammanni. Babu shiri ta koma cikin gidan, tana ɓata fuska da rarraba ido. Yaya ya ce "Wai me yake damunki ne? Kin makara fa mene ne haka ne?" Kawai ta fara hawaye "Wallahi Yaya mutumin nan kullum sai na gan shi, tsoro nake ji, na fara tunanin ko gamo na yi ma nikaɗai nake ganinsa, ni tsoro nake ji" Cikin rashin fahimta ya ce "Gamo kuma? Wai wane ne? Wane mutumin ne?" Nan Alina ta sake yi masa bayani, tun ranar da ta fara ganinsa. Tamkar zai dake ta ya ce "Kuma shi ne baki gaya mini ba, uban waye mu je ki nuna mini shi" Anty Nadiya ta ce "A'a Masoyi, ka tsaya a bi a hankali" "Ba ruwanki" ya yi maganar yana kallon Nadiya a hasale. Ya tasa Alina a gaba suka fita. Ko da suka fita, suka tarar da shi a zaune, yana ta kokowa da wani takalmi zai yi masa round ya gyara shi. Yaya Ismail bai jira komai ba, ya yi fatali da kayan gayarn takalimin matashin, ya damƙi kafaɗarsa ya tashe shi tsaye. "Malam waye kai? Meye haɗinka da yarinyar nan ka ke bibiyarta?" Ya yi maganar yana nuna masa Alina. Ya kalli Yaya ya kalli hannunsa da ya riƙe shi, ya juya yana kallon Alina da ta yi tsuru-tsuru, tana rarraba ido kamar a ce kyat ta gudu. "Waye kai malam?" Yaya ya ƙara maganar cikin ɗaga murya, yana ƙara riƙe kwalar mutunin. "Wallahi ni ba kowa ba ne, kuma ba bin ta nake yi ba" Ya amsa da wata dakakkiyar murya, mai cike da nutsuwa da kamala, tamkar ba daga gangar jikinsa mai ɗauke da wannan yamutsatsun kayan maganar ta fito ba. "Ƙarya ka ke yi, kusan sati biyu kenan, tana maganar wani yana bin ta, mene ne alaƙarka da ita, idan ma wani abin ne a ranka, ko mugun nufi ne da kai a kan yarinyar nan, wallahi wani abin ya same ta, sai ka zubar da hawaye a kan matakin da zan ɗauka a kanka na gaya maka" Jiki a sanyaye ya ce "Ka yi haƙuri dan Allah, wallahi ni babu abin da zan yi mata" Ya yi maganar yana ɗaga hannunsa alamar saranda. Tuni mutane suka fara taruwa, suna tambayar ba'asin abin da ya faru. Maigidan da mutumin yake zaune a ɗakin langa-langar da ke ƙofar gidansa, ya fito yana tambayar hayaniyar me ake yi, aka taru a ƙofar gidansa haka? Yaya Ismail ya ce "Rana tsaka mun ga mutum yana kwana a ƙofar gidanka, ba tare da mun san waye ba, yana bin Alina, bamu san daga ina yake ba, wallahi aka yi mata wani abin daga kai har shi ba za ku ji daɗi ba. Dan mummunan mataki zan ɗauka a kanku baki ɗaya" A rikice mutumin ya kalli matashin mai gyaran takalmi ya ce "Me ka yi mata, meyasa ka ke bin ta?" A rikice ya ce "Wallahi ba bin ta nake yi ba, hanya ce kawai take biyo da ni, sai ta yi zaton bin ta nake yi, amma ba bin ta nake yi ba, ni wucewa kawai nake yi" Mutumin ya sassauta muryarsa ta ce "Kana ji malam Isma'il, dan Allah ka yi haƙuri,  wannan da ka ke gani, almajiri ne kawai ya ɗan zo ci rani ne, aka roƙi na ba shi dakin nan na masu gadina tun da babu kowa, ya zauna tun da yanzu ba ni da masu gadi, kan ya samu gurin zama, amma ina da yaƙinin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba. Ɗalibin Alqur'ani ne" Yaya Ismail ya sakar masa wuya, yana zazzare ido, tare da yi masa wani irin mugun kallo. Yana sakinsa matashin ya durƙusa yana tattaro kayan gyaran takalminsa, da Isma'il ya yi fatali da su. Gaba ɗaya sai jikin Alina ya yi sanyi, ta yi dana sanin gaya wa Yaya Ismail, ba ta ji daɗin yadda ya ɗauki abun da zafi har haka ba. Sai ta ga kamar mutumin ya muzanta da yawa. Ya ce "Gara dai da na yi magana, tun da mu bamu san wane iri bane kawai ka kawo shi ka ajiye, babu bayani. Wallahi duk abin da ya faru ba zan lamunta ba" Alhaji Sadi ya ce "Da yardar Allah babu ma wani abu da zai faru sai alkhairi, in sha Allah" Ismail yadube ta ya ce "Wuce muje" ya riƙe hannunta suka yi gaba, ta waiwaya ta ga maƙwabcin nasu na yi wa mai gyaran takalmin magana, yayin da shi kuma yake ƙarasa harhaɗa kayan sa da Yaya Ismail ya watsar, Ya ɗago suka haɗa ido ita , ta yi saurin kawar da kanta suka shiga gida. MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN. Ayshercool 08081012143 AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA AYSHERCOOL BRIGHT PENS YOTA 002 Arewapen ayshercool Page 3 Da sauri ya sunkuyar da kansa, sai dai saƙon da ya aika mata ta idanunsa, sun yi tasiri jikinta ya yi sanyi, har ta ɗan rasa nutsuwarta. Da sauri ya tashi ya kwashi kayan aikinsa da ya tattare, ya shige ɗakin da yake kwana ya rufo ƙofar. Gaba ɗaya sai Alina ta ji babu daɗi, a ce babba kamar wannan, Yaya Ismail ya yi masa tijara a gaban mutane, har sai da fuskarsa ta nuna yanayi na damuwa, sai ta ji sam ba ta ji daɗi ba, har ta ji dama ba ta gaya wa yayan ba. ***** Ramata na tsugunne, tana ta aikin wanki, yayin da Juma ke ƙoƙarin tuƙa tuwo, Baffa ya yi sallama. Suka amsa masa gaba ɗaya. Ramata ta yinƙura ta tashi ta je ta karɓi kayan hannunsa. Juma ta kalle shi ta ce "Sannu da zuwa" "Yauwwa sannu da gida" Bayan Ramata ta ajiye kayan ta ce "Baffa sannu da zuwa" Baffa ya ce "Yauwwa Ramatuna autar Baffa, Ubangiji Allah ya raya mini ke, ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare" "Amin Baffana" Ta yi maganar cikin murmushi. Juma ta ce "Nima Allah ba mantawa ya yi da ni ba, da bai bani haihuwa ba, da kullum sai ka saka Ramata a gaba ka na ce mata 'yar auta, domin ka goranta mini" Baffa ya kalle ta ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba Juma ya za a yi na yi miki gori ma, ke ce dai ki ke tunanin haka, amma ni ban yi miki gori ba" Juma ta tsuke fuska tare da yi masa banza. Bayan ya zauna a kan tabarma ya buɗe ɗaya daga cikin ledojin da ya zo da su ya ce "Ramatu, ga man shafawa da man wanke baki, da sauran abubuwa na shirye-shiryen komawarki makaranta na fara sayo miki, sati mai kamawa za ki koma ko?" Cikin farinciki ta ce "Eh Baffana. Baffa kana yi mini addu'a ko? An kafe jarrabawarmu fa" Baffa ya ce "Ba nima na gaya miki na ji a radiyo, an sako jarrabawar ba? Ai Allah ba zai kunyata mu ba Ramata, in sha Allah sai kin zama abar alfahari da kwatance a garin nan" Ramata ta ce "Allah ya amince Baffa. Amma Baffa zan ci gaba da karatun kuwa?" Baffa ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ramata zan so hakan, domin shi ne cikon burina. Amma kina kallon tambarin da aka yi mana a garin nan, saboda karatun da ki ke yi. Ni na san ko iya haka ki ka tsaya Alhamdillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Amma idan Allah ya kawo damar ki yi karatun, ko bayan raina ne, zan bar wasiyya a abin da na bari, a ware wanda za a biya miki, ki ci gaba da karatu, ko ma ni ma ware da kaina. Juma ta juyo ta zuba masa ido, daga bisani ta taɓe baki ta ce "Taɓɗi abin na yi ne ashe" Ba su kula ta ba, Baffa ya sake cewa "Ramata ga wannan saiwoyin, ki dafa su da kyau, gobe in Allah ya kaimu zan je duba mara lafiya" Ramata ta yinƙura ta tashi tana faɗin "To Baffa" ***** Alina ce ta shigo da sallama, ta ɗora da cewa "Anty na dawo" "To sannu da zuwa, ya makarantar?" Alina ta amsa da "Lafiya ƙalau, Yaya bai dawo ba?" "Ban da abin ki Alina, dama yana da ƙa'idar lokacin dawowa ne? Amma dai ɗazu ogansa ya kira shi, zai je ya dubo masa wasu kaya, ya ce idan bai dawo ba, mu rufe ƙofa wataƙila sai Allah ya kaimu gobe" Alina ta ɓata fuska ta ce "Ni wannan ogan nasa ya fiye matsala, ni ba na son wannan aiken da yake yi masa" Nadiya ta yi murmushi ta ce "Kin fiye rigima ke kuma ba. Alina shi ne babban yaronsa, duk sauran cin amanarsa suke yi. Kuma idan bai je aiken ba da me zamu rayu, tun da a ƙarƙashinsa yake nema" Jiki a sanyaye Alina ta ce "Antynmu tafiye-tafiyen nan ne da yake yi fa ba na so" Cikin mamaki Nadiya ta ce "Saboda me?" "Ba na son bin manyan hanyoyin nan, ba na son ya yi hatsari" Da sauri Nadiya ta ce "A'uzubillah, wace irin magana ce haka Alina?" Tuni idanun Alina suka cika da hawaye ta ce "Kullum ya yi tafiya hankalina ba ya kwanciya sai ya dawo, ina jin tsoron ya yi hatsari wataran a hanya. Duk ranar da aka ce babu ke ko Yayana a duniya ya zan yi?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska. "Na san dole hakan za ta faru watarana, amma b a na fatan ku riga ni barin duniyar nan, Allah ya sanya zamu daɗe tare" Nadiya ta ce "Alina, shi ajali ba sai na kan titi ko na cikin ɗaki ba, yana iya faruwa a kan kowa, sai dai mu yi addu'ar Allah ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare da juna, kamar yadda ki ke fara. Bari a yi sallar magariba, sai na kira miki shi ki ji muryarsa" Alina ta jinjina kai tana share hawayen fuskarta. Ta nufi ɗakinta Nadiya ta bi ta da kallo, har ta shige,  sannan ta yi ajiyar zuciya ta ci gaba da abin da take yi. Washegari da yamma, Yaya Ismail ya dawo gida, Alina ta rirriƙe shi tana murna har da hawaye. Nadiya ta ba shi labarin abin da Alina ta yi jiya, da ta dawo ta tarar baya nan. Ya kalli Alina, cike da matsananciyar ƙaunarta ya ce "Ƙanwata, da gaske ki na tsoron na mutu na bar ki?" Ta jinjina masa kai cikin damuwa. "Aikin gama ya gama, mutuwa dole ce Auta" Cikin kuka Alina ta ce "Dan Allah ka daina faɗa ba na so, dan Allah ka gaya wa oganka ya daina yawan aikenka guri mai nisa ƙanwarka tsoro take ji" Rungume Alina ya yi yana murmushi tare da rarrashinta. "Babu abin da zai faru sai alkhairi, idan na zauna da ya ya zan kula da ku? Ki yi haƙuri ki din ga yi mini addu'a kin ji ko?" Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta ta ce "Bari na je na shirya, na gaya wa Anty zan je sayo cardboard paper, zan yi assignment" Ya ce "To a dawo lafiya, ta baki kuɗi ko na ƙara miki?" "Ƙara mini" Ta yi maganar tana miƙa masa hannu. Ya yi dariya ya zura hannunsa a aljihu, ya ciro ɗari biyar ya bata. Bayan fitar Alina, ya dubi Nadiya ya ce "Masoyiyya ya dai?" "Alina fa yanzu ba yarinya ba ce ba, lokaci kaɗan ya rage ta shiga shekara goma sha biyar" Ta yi maganar tana tsuke fuska. Cikin rashin fahimta ya ce "To meyafaru?" Nadiya ta ce "Ina maganar rungume ta da ka ke yi, wannan ba dai-dai ba ne ba, ba abu ne da ya dace ba" Ya ƙare mata kallo ya ce "To abin ya motsa kenan, shaiɗan zai yi miki kururuwa" Ta girgiza kai ta ce "Shaiɗan bai yi mini kururuwa ba, ina dai gudun kai ya yi maka ne" Ya shafa sumar kansa ya dube ta ya ce "Nadiya, ƙa'idar ba za ta canza ba, a kan Alina, zan iya lalata komai ciki har da ƙa'idar, shi kansa shaiɗai ɗin ya san na fi ƙarfin ya yi mini kururwa a kan Alina. Alina ƙaddarata ce, kuma jarrabawata. Kin san bawa ba ya gujewa ƙaddararsa, a ƙoƙarin gujewa ƙaddarar mutum ka iya halaka ba ki ɗaya. Dan haka dole ki yi haƙuri ko domin gudun halaka. Nadiya ta dube shi cikin ƙunar rai, amma ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba. Kasancewar ba a daɗe da idar da sallar la'asar ba, rana ba ta gama yin sanyi ba, balle masu zaman majalissa su fara bin dakali da tebura su na zama. Alina na fitowa hanya, ta tarar da shi a tsaye a bakin titi, hannunsa rungume da bagco yana ƙoƙarin tsallakawa, su na yin ido huɗu, cikin azama ya yinƙura zai tsallaka titi, dan yanzu kamar tsoron ganinta ma yake yi tun da Isma'il ya tijara shi a gaban mutane. Yana ƙoƙarin tsallakawa wani matashi ya taho a kan babur da gudu, ya buge shi. Take ya faɗi, bagco hannunsa ma ta faɗi, yalo ne fal a cikin bagcon, aikuwa ya watse a ƙasa, a kan ƙaramin titin cikin unguwar. Matashin da ya buge shi kuma, ya ja baburinsa ya zura da gudu, ba tare da ya tsaya ba Da sauri Alina ta bi yalon da gudu, ta fara tsintowa, tana sakawa a hijjabinta, saboda yadda suke ƙoƙarin shiga kwata. Sai da ta tsince su tsaf, sannan ta  nufo inda yake, a ɗan tsorace ta ce "Sannu" sau ɗaya ya kalle ta, ya sunkuyar da kansa ƙasa. Ta ɗauki buhun, ta tattare ta zuba masa a ciki. Ta sake cewa "Sun ɓaci da ƙasa sai dai ka wanke. Still ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ta fara tunanin ko kurma ne. Sai kuma ta tuna ranar da Yayanta ya je yana yi masa faɗa a kanta ya yi magana. Ta sake cewa "Ko ba zaka iya tashi ba?" Bai ɗago ba ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye. Sai dai ya ji rauni a babban yatsansa na ƙafa farcen ya ɗago, sai zubar da jini yake yi. Da sauri ta yamutsa fuska saboda ba ta ƙaunar ganin jini, yanzu hankalinta zai tashi. Ya miƙa hannu zai karɓi bagconsa, ta girgiza kai ta ce "Muje na kai maka" Bai sake magana ba, ya ɗaga ƙafarsa ya fara takawa a hankali. Da kyar yake taka ƙafar, saboda ya bugu, ga jini na zuba. Gaba ɗaya sai tausayinsa ya mamaye ta, da ta kalli ƙafar sai ta yamutsa fuska ta kawar da kanta gefe. Tana tafe yana biye da ita, ta ja ta tsaya ta ce "Laa ka ga chemist ɗin Albarka ya fito, muje ya duba maka, ko jinin zai daina zuba kar jininka ya ƙare ko tetanus ta shiga ciwon, duk da kwalta ce ba ƙarfe ba. " Ta yi maganar tana nuna ƙofar shagon. Ya ɗan kalle ta, yadda take magana Allah ya hore mata iyayi. Daki-daki take maganar tana demonstration, dai 'yar siririyar muryarta mai kauɗi tamkar tsuntsuwa. Kansa a ƙasa ya basar ya ce "Ba ni da kuɗi" Ta ce "Mu je da kuɗi a gurina" Bai sake cewa komai ba ya bi bayanta. Da sallama ta shiga, mai chemist ɗin na ganinta ya hau murmushi. "Alinan Yaya, ina Yaya?" Ta yi murmushi ta ce "Yaya yana gida. Dan Allah ka duba masa ƙafarasa babur ne ya buge shi, kuma ya gudu"  Mai Chemist ya tashi yana faɗin Subhanallah. Ya dudduba ciwon sannan ya wanke masa ciwon, ya yi masa allurai, da magunguna. Alina ta ce "Nawa?" "Dubu uku da ɗari biyu" ya bata amsa. Ta waro ido ta ce "Danƙari, to ka sakawa Yaya a cikin lissafinsa" Mai chemist ya ce "To amma ki yi masa bayani" Ta ce "Zan yi masa in sha Allah" Daga haka suka fito suka tafi, sai da suka je ƙofar ɗakin da yake zama, ya tsaya yana kallon kayansa da ke hannunta, bai ce ta ba shi sai kallonta da yake yi. Ta miƙa masa ya karɓa, ta ce "Ko na kawo maka baho da ruwa ka wanke?" Ya jinjina mata kai. "To bari na je gida" Ta ajiye kayan, ta nufi gidansu. Ƙasan zuciyarsa cike da fargaba, kuma sai gargaɗinsa zuciyarsa take yi, da tuna irin abin da yayanta ya yi masa, da kuma kashedin da ya yi masa a kanta. Ba a yi mintuna biyar ba, sai ga ta ɗauke da baho ta shaƙe shi da ruwa a ciki. Yana tsaye yana kallonta, ta ɗauki yalon nan ta juye a bahon duk ta ɗauraye su, ta zuba masa a cikin bagcon sannan ta zubar da ruwan. Ta yarfe bahon ta dube shi ta ce "Allah ya tsare gaba" "Amin" Har za ta tafi ta ji ya ce "Na gode" ta tsaya ta waiwaya ta kalle shi, amma jikinta ya yi sanyi, saboda yadda ya tsare ta da manyan idanunsa. Jinjina kai kawai ta iya yi, ta nufi gida. ***** Ramata na zaune da wayarta a hannunta, ta tattara hankalinta tana sauraren radio a cikin wayar. Tana zaune hannunta riƙe da biro da takarda, ga kuma fitila a ci balbal tana haska mata littafin gabanta. Cak ta tsaya da rubutun, ta ƙara tattara hankalinta a kan sauraren bayanan da mutumin cikin radion yake yi, yadda turawa suka mamayi Afrika. Yadda suka fara zuwa African ta jirgin ruwa, su kan zo gaɓar teku domin yin cinikayya a ƙarni na sha biyar. Su na kasuwancin zinare, hauren giwa da makamatansu. Daga baya aka fara cinikayyar bayi, mussaman tsakaninsu da sarakuna, yadda suke dibar mutane daga Afrika su tafi da su ƙasashen su, su yi musu bauta. Daga bisani a ƙarni na 16 suka fara kafa sansanoninsu, da kawo coci-cocinsu, da Asibitoci da makarantu a Afrika. Suka daina tsayawa a gaɓar teku suka fara watsuwa a cikin ƙasashen Afrika. Cinikayyar bayi da yarjejeniyar bogi, tsakaninsu da sarakunan Afirka, shi ya fara kawo rarrabuwar kawuna a Afrikan tare da kawo koma baya. A ƙarni na 19 alif dubu ɗaya da tamanin da takwas, manyan ƙasashen nahiyar Turai suka yi taro, suka rarrabawa kansu ƙasashen Afirka ba tare da sanin ƙasashen Afrikan ba. Ramata ta riƙe haɓa, jin an tafi talla. Ta dubi Baffa da yake gefenta yana sauraren radion shi ma. "Taɓ Baffa" "Na'am Ramata" "Tabbas ba a taɓa cin gari har abada ba tare da ɗan gari ba. Ƙulafuci da son zuciyan sarakunan Afrika na ƙarnukan baya, na daga cikin dalilan da ya sanya muke cikin wahala haryanzu, kuma muke ƙarƙashin mulkin turawa ta wasu fuskokin" Baffa ya yi murmushi ya ce "Ba an ce mun samu 'yanci ba? Kuma duk da haka mutanen wancan ƙarnukan ai sun fi na yanzu wadatar zuci ma da amana. Duk da ni ba wani gane kan wannan abubuwan nake yi ba" Jiki a sanyaye ta ce "Baffa, duk da ba na nan abubuwan nan suka faru, na san Alƙawarurrukan da turawa suka yi musu, baya rasa nasaba da basu tarin dukiya, ko kuma wani abu da za su amfana ba tare da kallon makomar al'ummarsu ba. Ban da haka ya za ku din ga ɗaukar junanku ku na sayarwa mutanen da ba ma launin fatarku ɗaya ba, daga wani guri suka zo, ba ma yankinku ɗaya ba, alhalin su ba sa sayar muku da na su mutanen, tun a lokacin sun nu na ba su san ciwon kansu ba fa kenan? Baffa ya kwashe da dariya, ya ce "Ramatu kenan. Ga shi nan sun dawo daga tallan ai, bari mu ci gaba da jin meyafaru" "Assalamu alaikum " su ka ji an kwaɗa sallama. Baffa ya amsa sannan ya kalli Ramata ya ce "Maza shiga ɗaki" Ta tashi tsam ta shige ɗaki, Baffa ya sake cewa "Bismillah" Tamkar korarre haka ya faɗo gidan, Baffa ya miƙe yana yi masa sannu da zuwa, ya nuna masa gefen tabarmar da yake kai domin ya zauna. Yana zama Juma ta fito kanta da lulluɓi, ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa, sannan ya mayar da idonsa kan Baffa. "Wato kai dai ba zaka taɓa hankali ba ko Jibo?" Cikin rashin fahimta ya ce "Yaya lafiya kuwa?" "Ka tambaye ni ko lafiya mana, to ba lau ba. Saboda tsabar ɗan kanka ne kai, mun haƙura mun zuba maka ido kana yadda ka ke so. Ban da rashin mafaɗi har dukiyarka zaka tattare idan ka mutu Ramata ta ci gaba da yahudanci ko? To baka isa ba wallahi. Babu wannan maganar na soke ta. 'ya ce dai tun da ba zaka aurar ta ba, mun zuba maka ido, a garin nan dai ka san babu mai auren ta. Ka ɗauke ta ka kai ta can wata uwa duniya ta yi kwana da kwanaki babu wanda ya san inda take da abin da take yi, babu wanda zai aure ta dan haka sai ka jiƙa ta ka sha" Baffa ya kalli Juma, ta tsuke fuska tana kawar da kai. Ya girgiza kai ya ce "Yaya haryanzu ba ku fahimci manufata ba, ana ta samun ci gaba a duniya, mu mu na guri ɗaya duk a dalilin rashin ilimi. Ko mulkin kama karya da ikon da ake yi mana a garin Yelwa rashin ilimi ne ya haddasa mana shi." "Ni rufe mini baki, 'yan bokon ba su ne suke kashe-kashe ba, suke mulkin ƙasar gaba ɗaya ba, wane zalunci ne su ba sa yi. Sau nawa ana kai ƙorafin abin da yake faruwa a garin nan, amma su ke goya musu baya. Wallahi idan baka yi wasa ba, yadda ka fifita yahudanci a kan aurar da Ramata, sai ka zubar da hawaye a dalilin bokon nan, sai ta zame muku masifa daga kai har ita" Ras gaban Ramata ya faɗi, jin yadda ɗan uwan mahaifinta ke janyo musu jafa'i ga shi dattijo. Ta jingina da jikin katangar ƙasar da ke ɗakin, zuciyarta na bugawa da sauri. Baffa ya ce "Ba za a yi haka ba in sha Allah, Alkhairi za ta zame mana baki ɗaya" "Wannan kuma matsalarku ce" Ya tashi ya kaɗe rigarsa ya fice. Baffa ya dubi Juma ya ce "Kin kyauta, na gode sosai da sosai" Ta tashi sumi-sumi ta wuce ɗaki tana ƙunƙuni. **** Ko da Alina ta taso daga makarantar dare, ba ta ga mutuminta ba, ta yi ta tunanin ko ya ƙafarsa, ko ya warke? Haka ta yi ta saƙe-saƙe, har ta koma gida. Daga nan sai da aka kwana biyu, sannan ta sake ganinsa. Sai dai kan ta ƙarasa inda yake ta yi magana, ya shige ɗakinsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi. ***** Danƙareriyar mota ce ƙirar higlander take ta zuba gudu, sai dai jikin motar babu lamba. Yana zaune a bayan motar, fuskarsa a rufe da rawani, sai idanunsa kawai ake iya gani. Sai rarraba idanu yake lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma sai ya sunkuyar da kansa ƙasa yana duba agogon hannunsa. Check point suka tarar a hanya, wanda tilas direban motar ya yi slow, ya ja ya tsaya. Sojoji ne su uku a a check point ɗin, ya yin da wasu ke zaune a cikin mota, babban cikinsu ya ƙaraso, ya kalli direban ya ce "Daga ina?" Direban ya amsa da "Maigida ne ya aike mu" "Waye mai gida?" "Lamba ɗaya" A ɗan hasalae sojan ya ce "Malam ka yi mini bayani, daga ina kuma ina za ku je? Sannan suwa ka ɗaukko, ga motar ta ku babu lamba, kai ba ku da gaskiya." A hankali ya sauke gilashin motar, ya yi wa sojan alama da ya ƙarasa. Ya ƙarasa daidai tagar yana son ganin fuskar mutumin. "Kacalla Sumale, shugaban manyan ƙungiyoyin ta'addanci na yankin nan, da ku ke nema babu dare babu rana, shi ya aike ni. Manyanku sun saka a ɗaukko ni domin wata yarjejeniya" Ya yi maganar yana ƙare wa sojan kallo, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakykywar fuskarsa fari sol ta bayyana. Ya sake duban sojan ya ce "Ka buɗe mini hanya zan wuce" Sojan ya ɗana bindigarsa yana ƙarewa fuskar matashin kallo. Shi ma matashin ya tsare shi da nasa idanunsa da suka da kalar ja. Ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kan sojan ba, ya ciro wayarsa ya daddana, ya saka ta a hansfree. Daga cikin wayar wata murya ta ce "Ya aka yi ne?" "Ka janye mutanenku sun tsare mini hanya, ko kuma su riga rana faɗuwa" Waro ido sojan ya yi, jin muryar mai maganar, saboda duk wanda yake cikin battalion ɗin su, babu wanda bai san wannan muryar ba. "Argungu are you with me?" Cikin rawar murya ya ce "Yes Sir" "Clear the road" "But Sir" "I said clear the road" "Ok sir" Tamkar soko haka ya ja da baya a hankali, yana kallon motar. Ya yi wa sauran alama da hannunsa, suka buɗe hanya motar ta wuce. ***** "Alina, wai bacci ki ke yi da la'asar ɗin nan?" Alina ta amsa da "A'a idona biyu" ta fito tsakar gida ta ce "Saƙa nake yi, safa da hula zan saƙa idan ki ka haihu mu saka wa jaririyar" Nadiya ta yi murmushi ta ce "Alina kenan. Kin ga gobe in Allah ya kaimu litinin ki zo ki kai wankin takaliminki, ga nawa ki haɗa da shi a yi mini round, na yi wa Yaya maganar ya manta" Alina ta ce "To bari na saka hijjabina" Ta yi maganar tana ɗan yin hamma, sai kuma ta katse hammar da ta tuna mutumin nan da ko sunansa ba ta sani ba yana gyaran takalmi. Da sauri ta janyo hijjabin ta zura, ta ɗauki takalman ta fita. Sai dai baya gurin da yake zama, dan haka ta je ƙofar ɗakin da yake kwana cikin tsoro, ta fara bugawa. Har ta sare ta fara tunanin baya nan, kawai ta ga ya buɗe ƙofar, sai da ta razana ta ɗan ja da baya tana kallonsa. Ya ƙura mata ido, a ɗan rikice ta ce "Ahh da..da..dama gyaran takalmi na kawo maka" Ta yi maganar tana nuna masa takalman hannunta. Ganin ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta sha jinin jikinta, tsoro ya ƙara bayyana a fuskarta. Kawai ta ga ya koma, ta tsaya sororo tana kallon ƙofar, har za ta juya ta tafi, ta ga ya sake buɗewa ya fito da kayan gyaran takalmin. Ta yi ajiyar zuciya ya samu guri ya zauna, ta gaya masa abin da zai yi wa takalman, sannan ta koma gefensa kan dakali ta zauna. Ya duƙufa yana wanke takalmin, ya din ga jujjuya takalmin Alina, tomes na 'yan makaranta baƙi, mai tsadar gaske. Ta ɗan zuba masa ido, haka kurum ta ji tana son ta ga fuskarsa, amma ya tara uwar ƙasumba dogon hancinsa kawai ake iya ganewa sai manyan idanunsa da suka fi komai razana ta. Bayan haka ga wata uwar hula da yake sakawa a kansa ya rufe, ga uban kwalli da yake rambaɗawa a idonsa. Kayan jikinsa sun sha jiki, dark bluen yadi ne a jikinsa, amma ya koma sky blue saboda tsufa. "Ciwonka ya warke?" Ta yi maganar ba tare da ta shirya ba. "Ya warke" Ya faɗa a taƙaice. "Allah ya ƙara sauƙi, ya kiyaye gaba" "Amin" Yayi maganar yana ci gaba da abin da yake yi ba tare da ya ɗago ba. Ya gama gyaran takalmin, ya wanke mata nata, sannan ya miƙo mata. Ta karɓa ta ɗan yi murmushi ta ce "Kai ya naga takalmina ya koma sabo? Wannan ƙyallin ai sai na gano fuskata a ciki saboda kyau da sheƙin da yake yi" Ta yi maganar tana ɗaga takalmin tana kallonsa. Ga mamakinta sai ta ga ya ɗan kalle ta ya yi murmushi. Ita ma murmushin ta sake yi sannan ta ce "Nawa ne?" "A'a ki bar shi" Alina ta ce "A'a ai sana'a ka ke yi, Yayana ya ce a duniya kar ka zalunci mai sana'ar hannu". Ya ce "Idan kin kuma kawowa sai ki biya" "To Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata, idan su na raye Allah ya ja kwanansu" Ya amsa da "Amin na gode" Ba ta kai ga tashi ba, sai ga Isma'il ya shigo layin a kan babur, idonsa na sauka a kansu, ya tsuke fuska kamar ya ga bala'i... 1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic. Shaidar biya ta 08081012143 Ayshercool 08081012143. AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA... AYSHERCOOL YOTA/002 BRIGHT PENS P4 Bai kula su ba kawai ya wuce, Alina ta tashi ta ce "Sai anjima na gode" Cikin fargaba ta shiga gida, ta tarar da Yaya Ismail a tsaye yana jiran isowarta. Aikuwa ya tare ta da "Meye haɗinki da mutumin nan? kin kawo mini ƙara na je na tsawatar masa, yanzu kuma na ganki a gurinsa me ya kai ki gurinsa kuma?" Alina ta nuna masa takalman hannunta A ɗan tsorace ta ce "Gyaran takalmi na kai masa, ni fa dama babu abin da yake yi mini Yaya, tsoronsa kawai nake ji da, kuma daga baya na gane mutum ne, shi ne na kai masa gyaran takalmanmu, nawa da na Anty" Ya ce "To dai ki din ga kula da kyau, kuma ki din ga addu'a" Alina ta jinjina kai, ta ajiye takalman. ***** Yau Juma'a, da yamma liƙis Ramata ce sanye da ɗinkin riga da skirt na yadi, ta yi wa fuskarta ado da jam baki da kwalli, ta yi kyau. Ta tsaya dai-dai jikin wata bishiyar tsamiya, tana ɗan leƙe-leƙe. Wanda ta gani yana tahowa ne, ya sanya ta tsuke fuska, gabanta ya tsananta faɗuwa, idanunta suka fara kaɗawa, ta ji tamkar ta juya ta zura da gudu. Tun daga nesa yake wage baki yana dariya cike da ƙeta, ya ƙaraso inda take tsaye, jikinsa sanye da kayan farauta, da karnuka su na bin sa, sai abokansa su biyu. Ya ƙare mata kallo ya ce "Jikar makiyaya wannan kwalliyar fa?" Ta ƙara tsuke fuska tana jin yadda zuciyarta ta fara tafasa, ta haɗiye wani abu mai ɗaci a maƙogwaronta, tana kallonsa. Hannu ya miƙo zai kai jikinta, cikin zafin nama, ta buge hannun ta ja da baya tana huci. Ya sake kwashewa da dariya sannan ya ce "Kafiya da taurin kai tamkar mahaifinki Ramata. Daga nan shiyyarku na so shiga domin na ganki a bar ƙaunata, sai dai na taki sa'a na yi gamo da ke a nan. Ko akwai wanda ki ke jira ne?" Ta tsare shi da idanunta da suka kaɗa suka yi jawur. "Idan shiyyarmu ki ke son shiga, ki shiga babu wanda zai yi miki komai saboda ki na da ni. Gaya mini wa ki ke jira? Hanne ko kuma Bukar?" Ras gabanta ya yi mummunan faɗuwa. Ta ɗaga ta sake kallonsa. Ya kwashe da dariya, ya ce "Kin ɗauka babu wanda ya sani ko? Yaro man kaza" Ya sassauta murya ya matso daf da ita  ya ce "Idan ki ka bari abin ɓoye ya fito fili, kin san ke da zuriyarku ne za ku karɓi hukuncin, babu wanda zai hukunta Bukar. Kamar yadda Iro ya karɓi hukuncinsa da shi da Hanne" Sake ware ido ta yi, ta ja da baya, tana ƙoƙarin magana amma maganar ta gagara fitowa. "Ya ki ke ja da baya, kullum ƙoƙarin nuna ke ta Allah ce ki ke yi, bayan kowa ya san yadda son abin Duniya ya sanya Babanki kai ki birni nema masa kuɗi, ta hanyar karuwanci.. cikin ƙwarin gwiwar da ba ta san tana da shi ba, ta ɗauke shi da wawan mari, sakamakon yinƙurin taɓa ƙirjinta da ya yi lokacin da yake maganar. A zafafe ta fara magana, duk da siririyar murya ce da ita ta ce "Kai kuma za ka karɓi hukuncin kaf laifukan zuriyarku muddin ina raye, shashasha kawai" karnukansa ne suka fara yi wa Ramata haushi, abokansa kuma suka yinƙuro, amma ya dakatar da su. "Marin soyayya ne, tukuicinsa kuma Bukar ne zai biya" Ya yi maganar yana ci gaba da dariya. Ramata ta ce "Wannan kuma matsalarku ce, dama idan mutum yana mugunta, idan bai yi wa kansa ba, bai iya ba, kuma da sannu wannan zaluncin da ka ke yi, zai waiwayo ku, matsa ka bani hanya kan na ƙara maka wani marin" Yana murmushi ya yi taku biyu, ya bata hanya ta wuce fuuu tana zubar da hawaye. "Gaskiya ka bada maza, mari fa, mace ta mare ka kana kallonta?" "Shhh, kar na sake jin bakin wani daga cikinku" Gaba ɗaya suka yi shiru, ba su sake cewa komai ba, suka bar gurin. Ramata ta yi tafiya mai nisa, ta ji muryar Bukar na ƙwala mata kira, kamar ta share shi ta wuce, amma ta fasa ta ja ta tsaya, ta share hawayen fuskarta. Ya ƙaraso yana sauke numfashi ya ce "Ramata, na fi awa biyu a rafi ina jiran zuwanki, ga shi yau juma'a ban ganki ba" Ta numfasa ta ce "Hanyar tsamiya na je na jira ka yau mu tafi tare, kuma ban ganka ba" Jiki a sanyaye ya ce "Ramata meyafaru ne, na ga fuskarki wani iri" Ganin ya rikice ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Babu komai fa, ka san duk lokacin da zan koma makaranta sai na ji kewar gida" Ya yi murmushi ya ce "Yakamata a ce kin saba zuwa yanzu fa. Na so mu haɗu yau mu sha hira sosai da sosai, na san sai kin yi watanni uku zuwa huɗu ban sake ganinki ba, kuma kin hana ni zuwa makarantar taku" "To ai da nisa sosai ba kaɗan ba, kuma ba na son a gida a gane kana zuwa. Bari na ƙarasa gida" Bukar ya ɗan tsare ta da ido sannan ya ce "Da alama dai wani na damunki, ban so mu rabu a haka ba, amma shikenan Ubangiji Allah ya tsare ya bada nasara. Ga sayayyarki nan ba yawa ki ƙara, zan yi kewarki abar ƙaunata" Ya yi maganar yana miƙa mata ledar hannunsa. Ta tsaya tana kallon ledar. Ya sake miƙa mata ya ce "Karɓi mana" Sai da ta risuna sannan ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai. Wai ni kuwa ina Hanne? Tsawon lokacin nan ka ce mini ta yi tafiya, haryanzu ba ta dawo ba?. Ya ɗan girgiza kai ya ce "Ba ta da lafiya ne, jinya take yi sosai" "Allah sarki, idan ka je gida ka gaya mata  ina gaishe ta, kwana biyu na daina ganinta, kuma ka gaya mata abin ɓoye na shirin fitowa fili. Na so zuwa da kaina na duba ta, amma ina jin tsoro saboda yadda alaƙa a tsakaninmu ta ƙara yin tsami" Ta ƙarasa maganar tana murmushi mai ciwo. Ya ce "Kamar yaya kenan?" "Idan ka gaya mata zata gane" Daga haka ta wuce ta bar shi a tsaye, yana kallonta. Ramata ta gama haɗa komai na tafiyarta, dan washegari Baffa zai mayar da ita makaranta. Ta ɗaukko wayarta Tab,, da ta samu kyautarta a lokacin da ta ci gasar lissafi. Da fari Baffa cewa ya yi bai yadda ta yi amfani da ita ba, saboda an ce tana lalata tarbiyya, sai dai ya saya mata irin tasa mai madannai. Sai da malamansu suka gaya masa, za ta taimaka mata a gurin karatu, sai kuma ya amince ta riƙe. Dan wasu lokutan har koya masa yadda ake amfani da ita take yi. Ta daɗe tana ɗan rubuce-rubuce sannan ta ajiye ta yi shiru tana tunanin maganganun da Sale ya gaya mata ɗazu. Kamar yadda Iro ya karɓi hukuncin Hanne? "Kai ba zai yiwu ba" ta furta a fili tana kashe Tab ɗin gaba ɗaya. Ta tattare komai ta gyare ɗakin nata, ta nemi guri ta kwanta tana ta tufka da warwara ba dan makaranta da za a mayar da ita ba, tabbas tana buƙatar ƙarin bayani a kan wasu abubuwa da suka saka ta a duhu. Duk da zuciyarta a cunkushe ta kwanta, hakan bai hana ta ganinsa a mafarkinta ba yau. Tana tsugune tana wanki a rafi, ta ɗaga kai ta gan shi a tsaye a cikin rafin. Yana sanye da tufafi na birni kamar yadda ta taɓa ganinsa. Fuskarsa babu yabo babu fallasa. Babu shiri ta miƙe tsaye tana faɗaɗa murmushinta, cike da farin ciki. Sai dai bai ce mata komai ya juya ya tafi ya ɓacewa ganinta. Ta buɗe idonta a hankali, duhu ya mamaye ko ina na cikin ɗakin nata. A zahiri tana son Bukar. Amma wannan kyakykywan matashin ya addaba wa rayuwarta. Har wani farin ciki take shiga, a duk lokacin da ta kwanta bacci ta yi mafarkinsa. Sai dai ta san har gaban abada ya fi ƙarfinta, ba za ta taɓa samunsa a matsayin miji ba. Tun a ganin farko da ta yi masa, yake yawan zuwa mafarkinta a kai a kai. Washegari. Ramata na cikin motar haya, Baffanta na daga gefenta, hannunsa riƙe da carbi yana ta tasbihi. Ya nisa ya ce "Ramatu bacci ki ke yi ne?" "A'a Baffa idona biyu, kewar gida nake yi ne, duk lokacin da zan koma makaranta sai na ji na damu" Ya yi murmushi ya ce "Ranar da aure kuma ya zo ya za a yi Ramatun Baffa? Ƙila ma Allah ya kawo wanda zai fito da ke daga Yelwa zuwa birni. Abin da nake so da ke dai, abu ne da nake nanata miki kullum. Ke ba 'yar kowa ba ce face makiyayin daji, ki riƙe mutuncinki, sannan ki ji tsoron Allah. Ba wai ina zarginki ba ne a'a ita dai tunatarwa tana da kyau ga mumini. Ramata ko bangon duniya za ki je ke kaɗai, ba dan hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da ya ce bai halatta ga wata musulma ta yi tafiyar sama da kwana uku ba tare da muharraminta ba, da Ramata zan bar ki saboda yardar da na yi da ke. Amma a matsayina na uba, ina sake nanata miki ki ji tsoron Allah, kuma ki yi addu'a." Baffa kenan bai samu wani ilimin addini ko na zamani mai zurfi ba, tsabar alaƙa da radio ce, ta sanya shi sanin rayuwa, har yake iya wa'azi. Sai dai duk da rashin ilimin nasa nutsatsen dattijo ne mai dattakun gaske. Haka suka ci gaba da tafiya yana ta yi wa Ramata nasiha. Ƙarfe ɗaya na rana suka isa makarantar 'yan mata ta kimiyya da fasaha, da Ramata take yi, ana ta mayar da ɗalibai ranar. Baffa suka gaisa da malaman su Ramata, cikin girmamawa Ramata ma ta gaida su. Vice ya dubi Ramata ya ce "B Yalwa, kin duba jarrabwarki kuwa?" Cikin tsoro Rahama ta girgiza kai. Ya yi murmushi ya ce "Kin ci jarrabawa, kuma mun yi ƙoƙari, an bar mana ke a nan reshenmu, dan ba zamu gama rainonku ba, a yi posting ɗinku wasu makarantun ba, su fi mu amfanarku ba, muna alfahari da ke Rahama Bashir Yelwa" Cikin matsanancin farin ciki ta ce "Alhamdillah, Allah na gode maka" Baffa ma cikin farin ciki ya wahse baki ya ce "Ma sha Allah, malam ta yi nasara kenan, za ta ci gaba da bokonta babu wata matsala?" "Ƙwarai kuwa, ai ko ba ta yi nasara ba, za ta ci gaba da boko, sai dai nasararta a wannan jarrabawar yana nufin za ta ci gaba da karatu ƙarƙashin makarantu na mussaman na koyar da ilimin kimiyya da fasaha" Baffa ya ce "To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya albarka" Ƙawayen Ramata suka zo gaida Baffa, babban dalilin da ya sanya suke son zuwa gaida Baffa, duk yanayinsa na ƙauyanci wasu lokutan, ya din ga kwarara musu addu'a kenan. Addu'ar uba da 'ya'ya, addu'a da nasiha mai shiga jiki. Farkon zuwan Rahama makaranta ta fuskanci ƙalubale, saboda ƙauyancinta, hakazalika babanta ya zama abin bayar da labari, kasancewarsa makiyayin ƙauye typical, dan takalmin nan nasu na roba da makiyaya da ake cewa fillo tomes shi yake sakawa. Abin yana sosa mata zuciya sai dai ba ta bari hakan ya zama rauninta ba. Da alfahari take nuna mahaifinta ga kowa bata ɓoye asalinta. Tamkar kar su rabu, haka ta ɗan raka Baffa zuciyarta cike da karaya ta juyo. Ta ɗauki kayanta, tare da ƙawayenta, suka nufi hostel cikin farinciki, kasancewar galibi sun ci jarrabawarsu, kuma ba a yi musu transfer zuwa wasu makarantun ba. ***** Sannu a hankali ya sanya ƙafarsa a cikin katafaren falon, ya tsaya cak yana ƙarewa falon kallo. Set ɗin kujeru kawai uku ne a ciki, ga wani irin sanyi da yake ratsa ko ina. Ya saki wani irin murmushi, ya sake gyara zaman takunkuminsa ƙafarsa sanye da takalminsa ya shiga falon. Wanda yake yi masa jagorancin, ya yi gaba suka wuce wannan falon, suka ɗan yi tafiya sannan suka shiga wani. Shi ma wani falon ne a can ƙuriyar gidan, an yi masa da ado da dukiya mai yawan gaske. Ya sauke idanunsa a kan agogon ɗakin, ƙarfe biyu saura mintuna goma na daren juma'a. Babban mutum ne dattijo a zaune, ya miƙe tsaye yana murmushi ya ce "Barka da zuwa kacalla Sumale" Ya tsaya ya ɗan ƙarewa mutumin kallo da falon, sannan ya yi taku biyar ya tsaya, ya ce "Ba mai gida bane, yaron mai gida ne, Sadauki nake, amanar kacalla Sumale mai Allah" Ya yi maganar yana sauke rawanin fuskarsa. Mutumin ya yi turus. "Amma meyasa Sumale zai yi mana haka? Ya zan yi magana da shi, kuma ya turo mini wani daban?" "Ka shirya harƙallar, ko na juya na tafi?" Ya yi maganar yana tsuke fuska. Ya jinjina kai ya ce "Bismillah zauna" Ya samu guri ya zauna a ƙasan carfet ya miƙa ƙafafuwansa. Ya ɗago idanunsa da suka sha uban farin kwalli ya dubi mutumin ya ce "Shi madugu, hawainiya ne, idan ya juyo nan a wannan kalar, idan ya juya can a wata kalar za a gan shi. Haka zalika kullum a tafe muke mu, bama zama guri ɗaya. Yau zaka iya ganina gobe ka ga wani daban. Amma ka kwantar da hankalinka, ni karɓar aikin ne nawa, aiwatarwa kuma tasa ce. Ina jinka. Mutumin ya ce "Ko kana buƙatar wani abu na ci?" Sadauki ya ce "A'a faɗi harƙallar kawai" Ya yi maganar yana kunna karan taba sigarinsa. Dattijon ya gyara zamansa cikin nazarin matashin ya ce "Amma na san ka san waye ni a ƙasar nan ko?" "A'a" ya ba shi amsa kai tsaye yana jingina da kujerar da take bayansa. Dattijon ya yi saroro yana kallonsa, yana ganin amsar tasa kamar rainin wayo. Mutumin ya dake ya ce "Amm to ni ne... Sadauki ya tari numfashinsa ya ce "Ba gabatar da junanmu ne ya kawo ni ba, yarjejeniyar aiki ce ta kawo ni, Kacalla ya san yadda zai ji da komai" Dattijon ya yi murmushin ƙarfin hali sannan ya ce "Gaskiya ne. Haƙiƙa muke riƙe da sitiyarin ƙasar nan, mune muke juya lamura yadda muke so. A duk lokacin da aka kawo abin da yake saɓanin tsarinmu, muna iya karkata motar mu kifar da kowa. Nan da na gayyace ka, ina magana ne da yawun wasu mutane da ba lallai sai ka san suwaye ba. Mu na son a ɓata ruwa ne ba dan a sha ba. A mayar da tsaro tsoro, a gwamutsa gari da ƙasa." Ya yi murmushi ya dubi dattijon ya ce "Aikinmu ne wannan, gwari-gwari ku na so a yi kururuwa a gabas sai kuma a koma yamma a tayar da ƙura a gabas?" Dattijon ya yi murmushi ganin ya ɗau haske ya ce "Gaskiya ne" "Mene ne sadakin aikin?" Za a yi raba dai-dai a ganimar, mu ne sitiyari ku ne injin mota, sai an bi mu sannan komai zai tafi yadda ake so. Sadauki ya miƙe ya ce "Za ku yi magana da Madugu, yallaɓai ku na sararawa fa, irin wannan duniya haka, mu muna dawa muna riƙe muku ƙasa" Ya yi maganar yana ƙyaƙyata dariya. Dattijon ya miƙe ya ce "Za a baka saƙonka a hanyar komawarka gida" "Yayi" Ya furta yana nufar hanyar fita. Ya bi bayan Sadauki da kallo, muddin wannan ba shi ne Kacalla Sumale ba, to shi ma ba ƙaramin tsagera ba ne ba.... ***** Yau kasancewar Asabar ce, kuma an yi hutun islamiyya, Alina ta nemi izinin Yaya, ta tafi gidansu Hafsa. Wuni suka yi wasanninsu, da shiriritarsu ta yara. Yayar Hafsa da suke satarwa littafi su karanta, ta saka Alina a gaba, sai da ta yi mata kitso, saboda kullum kanta a tsfefe yake babu kitso. Bayan sun keɓe a ɗaki su na hirarrakinsu, Hafsa ta ce "Alina kin san wani abu?" "A'a" "Babanmu ne ya ce mu na gama makaranta aure zai yi mini, wannan ɗan abokin nasa ne wai sona yake yi, ni tsoro nake ji" Alina ta ce "Meyasa ki ke jin tsoro, ba kya son sa ne?" Hafsa ta ce "Nima ban sani ba, ba na son na yi aure ya din ga zagina kamar yadda babanmu... Da sauri Alina ta rufe wa Hafsa baki tana girgiza mata kai. Tuni hawaye ya cika wa Hafsa ido, ya fara gangarowa. Jiki a sanyaye ta sauke hannun Alina, ta ce "Dan Allah Alina Yaya yana zagin Antynku? Ai kamar ma su ba sa faɗa ko?" Alina ta ce "Wallahi ban sani ba ko su na yi, amma bai taɓa zaginta ba, dan Allah kar ki gaya wa kowa Baba na zagin Ummanku" "Wallahi Alina ji nake ba na son shi, idan na ga ya zage ta tana kuka, jiya har miyar kuka mai zafi ya watsa mata. Idan kuma abin ya wuce, sai na ji na fara son sa, idan ya kuma yi mata sai raina ya ɓaci. Ba na son na yi aure mijina ya din ga zagina ko dukana, wallahi zan iya mutuwa, Alina ba na son na yi aure tsoro nake ji" Cikin kulawa Alina ta saka hannu tana share mata hawaye ta ce "Ba zai din ga dukan ki ba ko zaginki in sha Allah, ki yi addu'a. In sha Allah rayuwa za mu yi irin ta littafin da muke karantawa" Hafsa ta waro ido ta ce "Novel fa ba gaske bane" Alina ta ɗan yi shiru ta ce "Haka ne, amma dai ai idan muka roƙi Allah zai bamu" da haka suka koma hirar littafi, suka bar waccan maganar. Sai bayan magariba Alinan ta taho gida, sai dai ta san sai Yaya ya yi mata faɗa, ƙila ma ya haɗa mata da ranƙwashi ko murɗe kunne. Tana ta sauri, ta zo daf da inda za ta karya ta shiga layinsu, aka ɗauke wuta. Ta ja ta tsaya, tana ɗan waige-waige. Kamar mai tsoron shiga duhun, ta ɗan yi jimm sannan ta shiga. Daga bayan ta ta ga an kunna fitilar waya ana haska hanyar. Ta yi ajiyar zuciya, tana bin gefen hanya tana tafiya a hankali, da son bawa mai fitilar damar wucewa, amma ta ga idan ta rage sauri sai ya rage, idan ta ƙara sai ya ƙara kamar dai ita ake haskawa fitilar. Ta nemi guri ɗaya ta tsaya, tare da waiwayawa, dan ta fara tsorata da tunanin ko bin ta ake yi. A hankali ya ƙaraso yana haske mata fuska. Ta saka hannu ta kare tana ɗan motsa baki za ta yi tsiwa. "Wai waye?" Ta yi maganar tana tura baki. Bai amsa ba, sai da aka yi wasu sakanni, sannan ya haska mata fuskar sa da fitilar wayar. Ajiyar zuciya ta yi tare da faɗin "Wai dama kai ne, ka bani tsoro fa" Bai ce komai ba, ya ci gaba da haska mata hanya. "To na gode" Ta faɗa tana bin bayansa ganin zai wuce ta. "Amm ƙafarka ta gama warkewa?" "Eh" ya furta a taƙaice. Ta ce "To ina ka tafi kwana biyu na daina ganinka?" Ya amsa da "Gida" "Ina ne gidan naku?" "Wani guri" Ta sake cewa "Ina ne gurin, nan unguwar ne, ko wani gurin?" "A'a" "To ya ka baro 'yan gidan naku?" Ya yi shiru bai amsa ba, dai-dai lokacin da suka shiga layinsu. Ta dube shi ta ce "Na gode sosai da sosai" Ya ce "Mu je na ƙarasa haska miki" Alina ta ce  "Idan ka hasko mini ma daga nan zan hango har cikin soronmu" Gaba ya sake yi ya bar ta, a dole ta sake bin sa tana cewa "Ai da kar na wahalar da kai ne, amma shikenan" Daga tsallaken ƙofar gidan ya tsaya yana haska mata har cikin soron su. Ta tsaya ta waiwayo ta ɗaga masa hannu "Na gode sosai da sosai, sai da safe" Shi ma ya ɗaga mata hannu, ya tsaya har ta shige. Ya juya zai tafi, ya yi karo da Isma'il a tsaye a bayansa yana kallonsa. More pages available at Arewapen 1k ne a telegram via 0069675881 Aisha Adam stanbic shaidar biya ta 08081012143. AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA YOTA 002 P5 A tsorace Ya yi turus yana kallonsa, jikinsa a sanyaye yana jiran cin mutuncin da Isma'il zai yi masa a wannan karon. Sai dai ga mamakinsa bai yi masa magana ba, ya raɓa shi ya wuce. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya juya ya tafi. "Alina" ya shiga gida yana ƙwala mata kira. "Na'am" Ta yi maganar tana fitowa daga ɗaki. "Me ya haɗa ki da mutumin nan?" A shagwaɓe ta ce "Yaya har ka bani tsoro, na dawo daga gidan su Hafsa, aka ɗauke wuta a hanya, shi ne ya haska mini fitila" "Gidan su Hafsan ne ki ka je ki ka yi zamanki har isha'i ko Alina? Wallahi da na san ba ki dawo ba, har gidan su Hafsan zan je na same ki, na zane ki tun daga can mara ji kawai" Ta risunar da kai ta ce "Ka yi haƙuri dan Allah" "Ni ƙyale ni, sai kin yi laifi ki wani kwantar da kai kina a yi haƙuri kamar kyanwa" Ta yi shiru tana sunkuyar da kai. A gida ya yi sallar isha'i, sannan Nadiya ta zuba masa Abinci. Ganin yana jin haushinta, ya sanya Alina ba ta yi masa surutu ba kamar yadda ta saba, ta ja bakinta ta yi shiru. Can Alina ta ce "Antynmu ni ko na tambaye ki mana" "To tambai, me za ki tambaya?" Alina ta karkace ta ce "Anty wai dan Allah ku na faɗa da ke da Yaya?" Nadiya ta ce "Ai ga yayan naki a nan tambaye shi mana" Alina ta noƙe kafaɗa. Nadiya ta yi dariya ta ce "Meyasa ki ka tambaye ni?" "Hafsa ce take cewa babansu na zagin mamansu. Ya ce aure zai yi wa Hafsa da ta yi candy, shi ne ta ce ba ta son ta yi aure, mijinta ita ma ya din ga zaginta" Nadiya ta numfasa ta ce "Duk yadda muke sonki ba kya laifi mu yi miki faɗa?" alina ta jinjina kai. "To babu zamantakewar da babu saɓani, amma fahimtar juna ke kawo zaman lafiya.  Ni da yayanki... Yaya ya katse su a fusace "Shiyasa ba na son yawace-yawacen nan, a can ake gurɓata miki tunani. Babu wani mijin kirki da yake zagin matarsa. Ni kin taɓa ganin na zagi Masoyiyya?" Alina ta girgiza kai. "Amma idan ta yi laifi, ina yi mata faɗa, shi ma ba kullum nake yi nata a gabanki ba, haka mijin arziki yake. Dan haka baban ƙawarki mahaukaci ne" Nadiya ta ce "Subhanallah baban ƙawarta ne fa" "To babanta ne? Mahaukaci ne mana, banda mahaukaci ya za a yi yaranka su san kana zagin babarsu a gabansu dan hauka. Ke tashi ki tafi ki je ki kwanta. Kema tashi mu tafi" Alina ta tashi sumi-sumi ta tafi ɗakinta. Ko da suka shiga ɗaki Nadiya ta ce "Yaya Masoyi, ka din ga gaya wa Alina gaskiya fa. Idan mu soyayya muka saka a gaba lallai ne ta samu miji irirnka". Ya haye kan gado yana faɗin "Na raini yarinyar na aura maka, ka zagar mini ita, da kuwa na fasa wa mutum baki wallahi. Balle a ce duka sai na kusa binne mutum da ransa ba" Ta tuntsire da dariya ta ce "Allah mai 'ya" Ya ce "Sa wasa, ai yau ko da wani aka kama Alina, gara ya sako mini ita salin alin, a kan ya taɓa lafiyarta ko ya zage ta. A yadda Alina take babu yadda za a yi ta yi wa mutum laifin da zai dake ta ko ya ci mutuncin ta. Babu abin da ya yi mini zafi da laifin da ta yi, na aura wa mutum ita ya wulakanta mini sai ya gwammace mutuwarsa wallahi. Idan ta yi ba daidai ba, gara mutum ya dawo mini da kaya ta ta fasa auren" Nadiya ta ce "Ohh anya zaka iya aurar da ita kuwa?" "Eh mana, shiyasa ke ma nake ƙara lallaɓa ki masoyiyya, saboda kar na zaluce ki, wani ya auri ƙanwata ya cutar da ita Allah ya ba wa Alinana wanda so ta ya kula mini da ita kamar yadda nake sonta. Shiyasa sai na dirje na tantance yadda yakamata zan ba wa mutum" Ya yi maganar yana kwanciya a jikinta. Ta so ta furta abin da ke ranta, amma ta san tana maganar za su yi faɗa, a dole ta haɗiye ta yi shiru ta rungume shi. **** Yana daga kwance ya dafe kansa, da sallama ta shigo bakinta ɗauke da sallama, ya amsa ba tare da ya ɗago ba. "Ashe kana nan, ina ƙasa ina ta bulayin neman ka ai" Ya sauke hannun a hankali ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ina nan" Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ni wai dan Allah ya maganarmu ne?" "Wacce kenan?" "A'ah maganar motocina mana, waɗanan fa tsofaffi ne wanda waccan first ladyn ta yi amfani da su ne, a cikin allowances ɗina ka bayar da umarnin a sayo mini sababbi, wannan na rarrabawa mutanen da suka yi mana wahala" "Dan Allah ni dai a yanzu ki ƙyale ni, mene ne aibun motocin nan, daga zuwanmu sai mu saka wa dukiyar al'umma wawa" "Haba dan Allah, ba batun saka wawa bane ba, abu ne da yake a rubuce fa, ni dai gaskiya ka yi wani abu a kai, ni wannan motocin sun yi mini tsufa gaskiya" "Shikenan na ji, zan yi magana da Halilu su duba" Ta sauke numfashi tana murmushi ta ce "Ko kai fa" Ta tashi ta fice, ya bi ta da kallo, sam ba ta damu da jin damuwarsa ko ƙoƙarin taimaka masa ya sauke hakkin al'umma ba, kawai hanyoyin azurta kanta take nema. Ya janyo wardrobe ɗin gefen gado, ya ɗaukko waya ɗaya ya gyara kwanciyarsa ya hau internet. Twitter ya fara shiga ya dudduba gidajen jaridu, da al'amurn siyasar duniya. Ya gama da twitter ya shiga wani shafin. Shafinta suka fara hasko masa, fuskarta ɗauke da murmushin da baya gushewa daga fuskarta, a duk lokacin da zai ganta a kan screen ɗin wayarsa. "Amincin Allah da yardarsa su tabatta a gare ku, ma'abota shafina. Kamar kullum ina miƙa saƙon gaisuwa ta musamman ga Babana na kaina, kuma his excellency mr. President. Eh mana so so ne amma son kai ya fi. Babana ne, ɗan yankina kuma ɗan garinmu. Yau ba labari zan ba ku ba. Har kullum nice taku Baby Laila Umar Faruk. Ku zo mu yi wa mr. President ɗan waken gujjiya. Ya yi abincin dare da shi" Sai ya shagala a shafin nata, yana kallon yadda take gudanar da aikin ɗan waken komai daidai na talaka, sai dai tana yi tana bayyana ayyukan gwamnatinsa, tare da koɗa shi a cikin videon. Bai san lokacin da ya shagala da kallon matashiyar yarinyar ba, har ya manta da wasu daga cikin damuwoyinsa ba. A hankali ya furta "Lallai har abada ba a iya biyan masoyi. Wasu ayyukan nasa yadda take zayyano su, ka san ba ƙaramin bincike ta yi ba, kafin ta gano su. Dan wasu ma tun kan ya ci zaɓe. Ya tsinci kansa da shiga shafinta, ya din ga duba videos ɗin ta na baya. Ya kan ganta lokaci zuwa lokaci, amma yau ne ya tsaya sosai yake kallon abubuwan da take yi. Sai dai tana fuskantar ƙalubalen cin mutunci daga masu bibiyar shafin nata, mussaman waɗanda suke adawa da gwamnatinsa. Sai dai kaf babu wanda take yi wa martani da cin mutunci. Alarm ɗin wayarsa ya fara ƙara, ƙarfe ɗaya da rabi na dare, ya tashi tsam ya ajiye wayar, ya tafi banɗaki ya yi wanka ya fito ya fice daga ɗakin. **** Awanni biyu kenan Baffa su na tafiya a mota, a hanyarsa ta dawowa gida daga kai Rahama makaranta. Tun daga ranar farko da ya kai ta makarantar kwana da ƙanan shekaru, duk lokacin da ya kai ta, yana jin babu daɗi a ransa. Amma a wannan karon ba iya kewa ce ke damunsa ba, fargaba ce da ya rasa ta mece ce. Kawai ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ɓangaren Rahama ma, haka ta din ga jin wannan fargabar da ta kasa tantance dalilin jin hakan, duk da tana cikin farincikin cin jarrabawa da ta yi. ***** Gaba ɗaya hankalinsa ya tattara a kan matashin, da fuskarsa ke ɗauke da matsananciyar damuwa. "Majeed, ka nutsu ka yi mini bayani, are you serious wai?" "Ta yaya zan yi jokes da serious issue like this. Wallahi Alpha da idanuna da kumma kunnuwana. Su Okoro ba su san me aka yi ba. Oga  shi ya ce na ba su hanya su wuce, ka ji zuciyata ka ji zafin da zuciyata take yi... "Shhh ka san me zai faru? Wannan maganar daga ni sai kai, kar ka kuskura ta fita, idan ka bari aka ji maganar nan wallahi kashinka ya bushe" Majid ya shafi fuskarsa ya ce "Anyway ban gaya wa kowa ba, kai kawai na gayawa in sha Allah ba wanda zan sake gaya wa" Alpha ya daki kafaɗarsa ya ce "Good boy, ka koma office" Majid ya jinjina kai, ya juya ya fita. Bayan fitarsa Alpha ya ɗaukko wayarsa, ya daddana, ya kara a kunnensa. Sai dai har wayar ta gama ringing bai ɗaga ba. Ya sake buga wayar ta sake ringing ta gama ba a ɗaga ba. Ya ja guntun tsaki tare da faɗin "Ɗan rainin hankali, babu wanda nake yi wa kira sama da ɗaya idan ba kai ba" Ya yi maganar yana ajiye wayar. **** Tun da ta fito daga gida yake kallonta, tana tafe tana ta karkaɗe uniform ɗin ta, duk da gugar da su ka sha, da hankicinta a hannu, ta durƙusa ta goge takalmi ta karkaɗe uniform, ta karkaɗe jakarta. Har ta zo tsakiyar layin abin da take ta yi kenan. Sai da ta ɗago suka haɗa ido, sai ta yi murmushi, shi kuma ya sunkuyar da kai, ya ci gaba da kallon Alqur'anin hannunsa. Sai da ta zo inda yake sannan ta risuna ta ce "Ina kwana" "Lafiya kalau" Ya amsa yana ɗan ɗagowa cikin tsoro, saboda fargabar kar yayanta ya gansu. Ta sake cewa "An tashi lafiya?" Sai ya jinjina kai kawai. "To na gode da haska fitilar jiya da daddare" Sai ya ɗan yi murmushi kawai. Ita ma murmushin ta yi, ta ce "Da aka ɗauke wutar nan fa tsoro ne ya kama ni, ba na son duhu, ina tsoron duhu kwanan ne na daina kwana da fitila ma" Ya ɗan kalle ta ya yi murmushi, ƙamshin turaren da take yi, duk ya cika gurin da ƙamshi. "Na tafi makaranta, idan ka idar ka saka ni a addu'a" "In sha Allah" Ya furta a hankali yana jinjina kai. Ta ce "To na gode" Har za ta tafi ya sake cewa "Ba ki kawo takalmi an wanke ba" Ta kalli ƙafarta ta kalle shi ta ce "Goge shi kawai na yi da duster, ai bai yi datti ba ko?" "Kawo a saka masa mai" Ya yi maganar yana kallonta. Duk da kwarjinin da yake yi mata sai da ta yi murmushi ta ce "Ai ba ni da kuɗi yau". "Eh kawo" Ya yi maganar yana fito da kayan gyaran takalminsa. Ta zauna a dakalin gefensa, ta ciro masa takalman. Ya zauna ya ɗauki takalmin nata tomes, ya fara gogewa. A zuciyarta take faɗin dama ya cire wannan gashin na fuskarsa sai ya fi kyau. Ya shammace ta ya ɗago idanunsa, ta yi saurin sunkuyar da kanta, tana goge jakarta. Ya kammala goge mata ya ajiye mata a gabanta. Cikin murmushi ta saka hannu ɗago takalman ta ce "Wow wannan ai sai na gano fuskata a jikin takalmin nan,  ya yi kyau sosai ya gogu,  na gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Ka na bi na bashin wankin takalmin nan" Ta ƙarasa maganar tana ajiye takalmin a ƙasa. Tana kallon yadda yake  ta ƙyalli. Ya jinjina mata kai, ta saka takalman ta tashi ta tafi. **** Hanne ce take kallon Bukar, ya gyara zamansa ya ce "Hanne, Ramata ce ta ce mini na gaya miki, saƙon nan, cewar abin ɓoye ya kusa fitowa fili, me hakan yake nufi?" Hanne ta sunkuyar da kanta, hawaye ya fara gangarowa daga idanunta. "Ki yi mini bayani, me Ramata take nufi da abin da ta faɗa?" Hanne ta girgiza kai tana sunkuyar da kai. "Hanne ki yi mini bayani kin san me take nufi" Ta ɗago fararen idanunta. Hanne baƙa ce mai fashin goshi irin nasa. Ta ce "Yaya mene ne alaƙarka da Rahama ne, har ta yi wannan sakewar da kai, ta baka saƙo ka gaya mini?" Ya tsuke fuska ya ce "Ina tambayarki kina tambayata?" Ta ja numfashi ta ce "Ina kyautata zaton alaƙar da ke tsakaninka da Ramata, ita ce ta shiga tsakanina da yayanta. Kaf Yalwa Rahama ba ta da ƙawar da wuce ni, na san halinta ciki da bai, bana raba ɗaya biyu soyayya ku ke yi" Ba shiri ya gyara zamansa yana waiwaye da fatan babu wanda ya ji abin da ta faɗa, ya yi ƙasa da muryarsa ya dube ta da kyau ya ce "Hanne, kar dai abin da nake tunani ne, dama saboda ke ne aka kashe Iro?" Ta fashe da wani irin matsanancin kuka tana kallonsa. "Hanne dama saboda haka ne, aka saka miki takunkumi aka hana ki shiga, aka hana ki fita? Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin masifa ce wannan?" Hanne ta haɗa kai da gwiwa tana wani irin kuka, mai tsuma zuciya. Saleh da ke laɓe a jikin taga ya ja da baya yana ƙwafa, ya fice daga gidan. ***** Dandazon 'yan mata ne, suke ta ɓarkowa daga area classes zuwa hostel ɗinsu, kasancewar an tashi daga ɗaukar darasi. Sannu a hankali cike da nustuwa take takawa, fuskarta ɗauke da yanayi na gajiya, ko da ta shiga Hostel ɗin su, kai tsaye kwanarsu ta wuce. Cak ta tsaya tana murmushi, wadda take yi wa murmushin, ita ma ta hau murmushi ta ce "B Yalwa, ina ta addu'a Allah ya sanya kar a yi miki transfer" Ramata ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita tana faɗin "Anty Ruƙayyata, dama za ki dawo, na ga sati guda kenan da dawowa amma shiru ba ki dawo ba, har na fid da ran za ki dawo" Anty Ruƙayya ta ce "Ina can ina ganin Likita ne, ba ni da cikakkiyar lafiya, sai da na gama sannan aka dawo da ni. Wai ƙodata ce ke cikin hatsarin kamuwa da ciwo" Cikin tausayawa Rahama"Allah sarki, ya jikin naki?" "Alhamdillah. Na samu sauƙi sosai da sosai" "Allah ya ƙara afuwa" Ruƙayya ta ce "Amin, su Rahama an shiga Ss1 ina fatan komai normal?" Rahama ta jinjina kai tana murmushi. "To Alhamdillah, duk da ba na jinki, ƙwaruwa ce ke, amma duk abin da ba ki gane ba, ki yi mini magana Rahama, iya wuya sonake muƙamin headgirl ko health prefect kar ya bar kwanar nan tamu mai albarka, dan haka za mu ƙara zage damtse a kan karatu" "To iyayen son zuciya, wallahi kuwa sai ya bari, ko ba kwa so" Cewar ta gefen gadon Ruƙayya, da take class mate ɗin Ruƙayya. Ruƙayya ta ce "Ƙwalli ki kiyaye ni, so so ne amma son Kai ya fi ehe, an san yan kwanarmu dai akwai kai" Rahama dai murmushi kawai take yi, ba za ta taɓa mantawa da Ruƙayya ba, lokacin da aka kawo ta, ga ƙuruciya, ga ƙauyanci, kusan ma ƙyamarta ake yi. Ruƙayya ce take yi mata komai, dan haka akwai shaƙuwa sosai a tsakanin su, yanzu Ruƙayya na ss3 Rahama kuma ss1 wanda suka yi candy head girl da health prefect 'yan kwanarsu ne, Ruƙayya aka bawa riƙon ƙwaryar head girl. Ta kuma bawa Rahama gudunmawa sosai a wajen karatu. Kamar kullum bayan dawowa daga pref, sai da Ruƙayya ta tara 'yan kwanarta su Rahama, suka yi karatu, sannan suka hau gado domin su kwanta A kan gadon ma, Rahama addu'oin kwanciya bacci ta yi, ta ɗan sake buɗe litattafanta tana karantawa, bacci ya yi awon gaba da ita. Misalin ƙarfe uku saura, Ruƙayya na gadon ƙasa tana karatu ita ma, kawai ta ga Rahama ta diro daga saman gado, a gigice za ta yi waje. Da sauri ta fito daga net, ta riƙo Rahama. "Rahama lafiya kuwa?" Gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta, kamar wadda hankalinta zai gushe. Ruƙayya ta sake cewa "Rahama lafiya kuwa?... "Hayaniya na ji ne" "Wace irin hayaniya kuma? Mafarki ki ke yi, amma ba wata hayaniya" Da kyar ta lallaɓa Rahama ta koma kan gadonta ta kwanta, amma zuciyarta na ci gaba da bugawa, saboda ita dai kamar a zahiri ta ji hayaniyar mutane. Sai dai kwanciyar tata babu wuya, ta tafi mafarkin abin ƙaunarta da bai san tana yi ba. Mutumin da ba ya shafe sati bai zo a mafarkinta ba. Wasu lokutan yanayin mafarkin har kunya yake saka ta. ***** Tun da Alina taje makaranta, take kaffa-kaffa da takalmin nan, take goge shi, gani take idan ta bari ya yi ƙura bata kyauta ba, saboda yadda ya dage ya goge mata shi ya saka mata mai, ba tare da ta bayar da ko sisi ba ***** Cikin girmamawa yake kallon ubangidansa, ya risunar da kansa yana ɗaga masa babban yatsansa alamar jinjina ya ce "Kacalla mai Allah, ka tsare gida ka tsare daji, uban gidana na kaina, gugan ƙarfe sha kwaramniya" "Sadauki" "Na'am Kacalla" "Ka san mutanen nan, miyagu ne, ba kuma abin yarda ba ne, dan haka za mu yi musu aiki, bisa ga tsatstsauran sharaɗi, da ko an shiga hanyar da ba za ta ɓulle ba, mutuwar kasko za mu yi da su. Sannan dole Jagora ya san da sun bayar da wannan aikin" Sadauki ya ce "Wannan gaskiya ne" "Ya ce maka su ne sitiyari mu ne inji, su dirje mu yadda suke so kenan yadda suke so ko? Tabbas sai mun je tsakiyar hanyar za mu ɗau zafi mu tsayar da aikin motar. Za mu yi musu aiki, amma mu ma mu na da bamu sharuɗan. Idan suka cika sharaɗinmu. Za mu ba su abin da suke so koma fiye, idan suka saɓa yarjejeniyar injin mota zai buga a tsakiyar hanya" Sadauki ya yi dariya yana gyaɗa kai, Allah ya taimaki uban gidana" Ya gyaɗa kai yana murmushi tare da faɗin "Ka huta na wajena" ***** Hafsa har mamakin Alina take yi, ta saba idan suka taso daga makaranta, har sake tsayawa suke yi a bakin hanya, su sha hira, har lokaci ya nemi ya ƙure musu, sannan su rabu, amma a kwanakin nan, sai ta lura Alinan har Alla-Alla take yi su rabu ta tafi. Ta daina tsayawa su yi wannan hirar da suka saba. Yau ma ana tashi daga makarantar, Alina ba ta ko tsaya Hafsa ba, ta fice ta nufi hanyar gida. Sai dai duk saurin da take yi, tana shigowa layinsu, ta tarar da inda yake kwana, a rufe da kwaɗo. Take jikinta ya yi sanyi, ta so sake yi masa godiya amma ba ta tarar da shi ba. Ta shiga gida da sallama, ta tarar da Yaya da Anty, su na ta aikin kayan ciki. Ya ɗago kai ya kalle ta ya ce "Alinan Yaya, an dawo?" Ta gyaɗa masa kai. Nadiya ta ce "Yau mai kurmanataka ce kenan?" Ba ta ce komai ba, ta nufi ɗakinta. Yaya nata nuna mata kayan ciki, yana tsammanin ta yi murna, dan masoyiyyar nama ce, amma ya ga ba ta yi murna ba. Gaba ɗaya ta ji babu daɗi, rashin ganin mai gyaran takalmi da ba ta yi ba, mutumin da ko sunansa ba ta sani ba. Da azahar ma ta shirya ta fita Islamiyya,  ta dawo, ta tafi makarantar dare ta dawo, amma babu shi babu alamar sa, ɗakin nan a rufe. Haka kurum ta din ga jin babu daɗi, tare da tunanin ina ya tafi haka?. Da daddare, kamar an mintsini Alina ta ce "Antynmu kin san wani abu?" "A'a Alinanmu" "Ɗazu mutumin nan, na ƙofar gidan Malam Sadi, ya ce ban kawo masa wankin takalmi ba, na ce masa ai ba ni da kuɗi ne, ya ce na kawo ya wanke mini, ya wanke mini kyauta. Kuma tas ya fita takalmin. Ni fa ko, ban taɓa ganin an wanke mini takalmi ya fita kamar yadda yake yi ba shi" Kasa haɗiye abincin ya yi, ya tsura wa Alina ido. Nadiya ta ce "Aikuwa ya kyauta, kin ga yanzu kun ji kunya da ke da yayanki, kun je kun tara masa jama'a, kun yi masa tijara, kuma ya zo yana miki mutunci. Shiyasa wulaƙanci babu kyau. Alina ta yi murmushi ta ce "Wallahi da tsoro yake bani ne, mussaman idanunsa ƙwal-ƙwala, ashe yana da kirki, idonsa ne abin tsoro, ƙatun-ƙatun kuma jajaye, idan ya kalle ni sai na ji gabana ya faɗi. Har ruɗewa nake yi wallahi, na ji ni kamar dai ba ni da gaskiya ko dai makamancin haka. To yanzu ba na bari ya kalle ni, na daina haɗa ido da shi kwata-kwata dama bana iya haɗa idon ma da shi. Ga shi ya wanke mini takalmina. Da na dawo daga gidansu Hafsa ma aka ɗauke wuta na yi dare, shi ya haska mini hanya." Kasancewar inda yake zaune, babu haske zuba wa Alina ido ya yi, amma ba ta san yana yi ba daga ita har Nadiyan, Alina kuwa da farinciki take hirar, tana ba yi mata hirar mai gyaran takalmi. Ismail ya din ga jujjuya cokalin hannunsa yana kallonta tare da sauraren yadda take bayani a kan mutumin. A wannan karon ma, kwanaki uku a jere, ba ta sake ganinsa ba, ƙofar ɗakinsa a kulle da ƙaton mukulli. Sosai Alina ta din ga jin babu daɗi, tare da tunanin ina ya tafi. Babu tsammani, an taso su daga islamiyya, ta hango shi a bakin titi, a gefen mai shayi, yana kankare rake.  Babu tunanin komai ta nufe inda yake da fara'arta. Tsayawa ya yi yana kallonta, har ta ƙaraso. Tana zuwa inda yake ta hau surutu "Ina ka tafi kwana uku baka nan?" "Na je gida ne" Alina ta jinjina kai ta ce "Ina ne gidan naku ne wai?" "Ƙauye" ya bata amsa. "Ohh Allah sarki, to sayar da rake ka dawo yi, gyaran takalmin fa?" Ya ce "Ina yi haryanzu" "Ma sha Allah, to ba ni na ɗari" Ta yi maganar tana duba jakarta ta ciro ɗarin. Ya ɗaukko sandar raken ya fara kankarewa. Ta ƙare masa kallo yana kankare raken ta ce "Laa tsawonka ɗaya da raken, kanka ma ya wuce raken tsawo" bai ɗago ba ya yi murmushi, ya ci gaba da kankarewa. "Dan Allah kar ka bani tsolo, ƙasan nan zaka bani" Ya jinjina mata kai. Ta ga yana ta sara sandar raken. Har ta yi shiru, ta ɗan gyara tsayuwarta ta ce "Na ɗari fa zaka bani" Bai amsa mata ba, sai da ya gyara sandar raken duka, ya saka a cikin leda, ya miƙa mata. Ta kalli ledar ta ce "To ai na ɗari na ce fa" Ya ce "Eh na sani" "To ai kuɗina bai kai ba" Idanun da suke bata tsoro, ya ƙura mata, da sauri ta saka hannu biyu ta risuna ta karɓa ta ce "To na gode" Ta yi maganar tana miƙa masa ɗarin. Bai ko kalli ɗarin ba, ya koma ya zauna. Haka Alina ta yi dakon rake, ta tafi gida. Da Yaya ta fara karo, ya yi alwala dan magariba ta kusa. Ismail ya ce "Wannan raken fa?" Ta yi shiru tana kallonsa. "Tambayarki fa nake yi" "Bani aka yi" Ta yi maganar numfashinta na kaiwa da kyar. "Waye ya baki?" "Amm.. ban san sunansa ba" "Waye shi, a ina yake?" "Mai gyaran takalmi ne ya bani" Ya tsare Alina da ido, yana nazarinta, tare da tsuke fuskarsa, fuuuu ya raɓe ta ya wuce. Ta waiwaya tana kallonsa tare da fatan Allah ya sanya ba zuwa zai yi ya yi masa wata maganar ba. 1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Shaidar biya ta 08081012143 *MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN* AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g *MAI BUƘATA DAGA FARKO, YA BI LINK YA DUBA CHANNEL ƊIN NAN. AND MORE PAGES ARE AVAILABLE AT AREWAPEN* SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 Page 6 Nadiya na jin su ba ta yi magana ba, ta basar Alina ta ajiye ledar raken, tana ta addu'a a zuciyarta dan ta san halin Isma'il sarai, tsaf zai saka ta a gaba da faɗa. Ga shi ita ba wani abu ne tsakaninsu ba, tana ƙoƙarin kula shi ne, dan wanke abin da yayan ya yi masa har ya tara masa jama'a ya yi masa tijara a cikin jama'a. Kiri-ƙiri 'yan makarantar su maza, ba sa shiga harkarta, tun da wani yaro ya ce yana sonta tun a Jss 2, yaron yana Ss2, daga ta ba wa Nadiya labari, ta gaya masa yaje har makarantar, ya zane yaron, case har da iyaye da zuwa gurin 'yan sanda. Samari na cikin unguwa kuwa, babu wanda yake shiga harkarta, ko kula ta, da ka nuna alamar sonta ka ke yi ko da gaisuwa ce ta fiye haɗa ku, sai Ismail ya yi wa mutum tijara ya ce za a lalata masa ƙanwa, ba zai lamunci hakan ba. Ita kuma Allah ya hore mata farin jinin mutane, saboda yawan fara'arta da kuma surutunta, da wuya ka yi zaman minti goma da ita ba ku saba ba. Ko da Isma'il ya je masallaci, sahu ɗaya Ismail ya yi salla da mai gyaran takalmin nan, kallo ɗaya ya yi wa Isma'il, ya sunkuyar da kansa, ya ƙarasa azkar ɗin sa ya tashi sumi-sumi ya fitaya bar masallacin. Yana cikin tafiya ya ji an dafa kafaɗarsa. Babu shiri ya waiwayo a tsorace. Ismail ya tsare shi da ido ya ce "A tunaninka haɗa sahu da kai da na yi kawai faruwa ya yi ne haka kurum? Gurinka na zo ne ai. Ba kuma tsawaita magana zan yi ba. Hawainiyarka ta kiyayi ramata. Shi ne kawai abin da zan iya gaya maka" Ya sakar masa kafaɗa ya kewaye shi ya wuce. Yaje gida ya tarar da Nadiya da Alina sun kewaye rake, su na sha su na hira. Sai da Alina ta gan shi, sannan ta tuna ma a yadda ya fita. Sai dai bai kula su ba, ya shiga ɗaki. ***** "Barwa" Ya kira sunansa. "Na'am sir" "Ka ce yaronsa ya aiko maka ba shi ne ya zo da kansa ba?" Barwa "Eh ranka ya daɗe" "Dole mu yi taka tsantsan da mutanen nan, amma abin da muke so ba zai yiwu ba, sai da su dole. Ka gaya musu mun amince da dukkanin buƙatunsu, za kuma mu yi, su fara aiki kawai" "Amma ranka ya daɗe, yarjejeniyar ta yi tsauri da yawa fa, kuma za a kashe kuɗaɗe ne ba kaɗan ba" Dattijon ya yi murmushi ya ce "Ai yaro bai san wuta ba sai ya taka, bamu za mu biya kuɗin aikin ba, gwamnatin da kanta za ta biya kuɗin aikin da za a yaƙe ta, ka zuba idanu ka gani, sannan kuma na nemi haɗin kan ƙusoshin tsaro, komai zai tafi dai-dai babu gargada. A hanzarta shirya yarjejeniyar kamar yadda suka buƙata" Barwa ya ce "Shikenan ranka ya daɗe, an gama da yardar Allah" "A hanzarta domin Allah, dan bamu da lokacin ɓatawa, a gaggauce yakamata mu yi komai. Ba na son ya rufa shekara guda, lissafi bai ƙwace masa ba. Anjima zamu zauna da su Ade, da zarar yaran nan sun fara aikinsu, akwai buƙatar dala ta yi ƙaranci a kasuwa" Barwa ya kwashe da dariya ya ce "In dai lissafi ne a bar maka Yallaɓai" "Kash, kai dai ka zuba ido, ka ga yadda za mu mayar da komai baibai ai Jagora ya tsaya mana, sai mu ga da mu da shi, wa zai haƙura ya bi wani. Taƙamarsa ko da mu ko babu mu, yana da soyayyar jama'a yana da yaƙinin zai sake komawa gadon mulki, tun da mun tura motar zai bule mu da hayaƙi, amma mu zuba mu gani... ***** Baffa na zaune bayan sallar asuba yana lazumi, ya kashingiɗa da jikin gado, yana jan carbi. Yana jin Juma ta shigo, ta kawo masa madara ta ajiye ta fita, amma bai motsa ba. Ya rasa wace irin fargaba ce take ratsa shi har haka, komai baya yi masa daɗi. Tun da ya mayar da Rahama makaranta, ya rasa mene ne yake ba shi tsoron ko saka shi fargabar ji yake yi tamkar ya koma ya ɗaukko ta kawai. Rahama kuwa na zaune a ɗakin karatunsu na makaranta, tana duba wani littafi, ta ci karo da taƙaitaccen tarihin sir isaac newton, da ake yi wa laƙabi da father of modern physics. Masanin kimiyya ne sosai da sosai. Yana cikin wanda suka bayar da gudummawa a harkar lissafi. Duk da bincike ya nuna kai tsaye ba za a ce shi ne kaɗai father of physics ba, tun da ga Albert Einstein, ga Galileo Galilei. Shi ya samar da law of motion, bincike ya nuna Isaac newton introvert ne, ana kyautata zaton yawan ta'amalli da chemical ne ya yi sanadiyar mutuwarsa. Babban abin da ya fi ɗaukar hankalin Rahama shi ne, da aka ce bai taɓa aure ba, babu kuma ƙwaƙaƙwarar hujjar da take nuna, ya yi soyayya a rayuwarsa. Kawai ta yi murmushi tana tunanin, ƙila da ya yi soyayya, ko da yana da aure, da wannan nasarorin bai cin musu ba, dan Sai ya fi mayar da hankali a kan gina iyalinsa, haka zalika da yana da yawan surutu babu lallai ya cimma abubuwan da ya cimma. Saboda mata na son attention, da kulawa, babu lallai ya din ga samun isasshen lokacin tunani, da bawa ƙwaƙwalwarsa damar samar da abubuwa. Ta yi ajiyar zuciya tana tuna Bukar, tabbas mata na son kulawa da attention,  sai dai ta su soyayyar na fuskantar barazana, du da ƙoƙarin da Bukar yake yi a kan hakan. Sai dai gudun faruwar matsala ya sanya a ɓoye suke haɗuwa. Sai dai sam ba ta jin irin wannan zunzurutun soyayyar tasa a cikin ranta. Babban abin da ya sanya take tare da Bukar tausayinsa ne da take ji. Sai kuma ta mayar da tunaninta kan Hanne, tare da son tabattar da abin da Saleh ya faɗa gaske ne? "Kenan idan ina buƙatar yin nasara a rayuwata, dole na fara ajiye batun wannan gurguwar soyayyar tawa da ban ga ta inda zata haifar da ɗa mai ido ba." Ta yi maganar a zuciyarta. "To wani hali Bukar zai shiga? Idan na jingine batun soyayyarmu" Wata zuciyar ta tambaye ta. Gaba ɗaya sai ta ji ta gaji, ta daina fahimtar abin da take karantawa, kawai ta rufe littafin ta kwanta. "Bacci a Library Rahama" Ta buɗe idonta, sannan ta tashi zaune a hankali ta kalle shi ta ce "Ba bacci nake yi ba sir" "Ƙarya na yi kenan?" Ta girgiza masa kai, tana sunkuyar da kai. Ya ce "Me ku ka shirya presenting ne, next week in Allah ya kaimu?" Ta ɗaga kai tana kallonsa. "Press club i mean" "Introvert" Ta faɗa a taƙaice. Ya yi dariya ya ce "Rahama B Yelwa, Introvert kawai? Meye alaƙar introvert da presentation na press club? Ko da yake akwai alaƙa ai. Amma you went deep, ko personality ɗinki ki ke son yi wa mutane bayani a kai?" Ta girgiza kai ta ce "No sir, ai am not introvert, za mu rubuta mu kawo maka ka duba" Ta yi maganar tana murmushi. "To shikenan ina jiranki" Ta tashi ta tattare litattafanta, ta fice daga Libraryn. ***** Yau a makarantar dare, Alina bacci ne ya dame ta, dan haka ana tashi babu wanda ta tsaya jira, ta rungumo jakarta ta fito hanya. Tana ta uwar hamma, katse hammarta ta yi ganinsa a tsaye a ƙofar makarantar, ya saka ƙofar makarantar a gaba. A hankali ta ƙarasa inda yake tsaye, tana ɗan layi saboda baccin da yake kanta. "Wani ka ke jira ne?" Ta yi maganar tana kallon ɗalibai da suke fitowa daga cikin makarantarsu. Ya kunna fitilar hannunsa ya ce "Wucewa zan yi, sai na ga an ɗauke wuta" Dariya ta yi ta ce "Saboda ina tsoron duhu ko? To na gode sosai da ka tuna da ni, ka taimake ni mu tafi" Ya jinjina kai su ka jera yana haska musu hanya. Alina ta ɗan dube shi ta ce "Ka ce mini ka je garinku, ina ne garin naku? Kullum na tambaye ka baka gaya mini" "Can wani guri" "Ina?" Ya ce "Wani waje ne, can ƙauye" "To meyasa ka baro garinku ka dawo nan?" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Almajiri ne ni" Alina ta ce "Almajiri kuma? Babba da kai haka, ba 'yan yara ne suke almajiranci ba? To ina ce makarantar ku?" Ya ɗan yi jimm, jin yadda take ta jero masa tambayoyi kashi-kashi kamar shari'a. Ya numfasa yana tunanin amsar da zai bata daidai da hankalinta. Ya ce "Eh, na yi sauka ne, tuntuni, neman kuɗi nake yi, shi ya zaunar da ni, amma ina zuwa makarantar haryanzu ai ba a girma da neman ilimi ko?." "Laa nima na kusa sauka fa, mu na kammala haddar izifi ashirin za a haɗa mu yi bikin sauka, Yaya ya ce zai saya mini ƙaton rago idan na yi sauka" Ta faɗa cikin farincikinki. Ya ɗan yi dariya da gefen bakinsa ya ce "Hakan na da kyau, Allah ya sanya albarka" "Amin. To yaya sunanka?" Ta yi tambayar daidai lokacin da suka ƙaraso layin. "Bawan Allah" Ta ɗan ɓata fuska ta ce "To ai kowa bawan Allah ne, sunanka fa da ake kiran ka da shi, sunanka na gaskiya" "Mamman" Ya faɗa a taƙaice. Ta yi murmushi ta ce Muhammad dai ko? Tun da a birni ka ke. Ni kuma sunana... "Alina" ya ƙarasa mata. Ta yi turus ta ce "A ina ka san sunana?" Bai bata amsar ba ya ce "Sai da safe" Ta yi murmushi ta ce "To ai ba shi ne sunana na gaskiya ba, sunana na gaskiya Fatima". Ya ɗan yi turus yana kallonta, fuskarsa ɗauke da murmushi. "Ya na ga kana murmushi?" "Sunan Innata ne da nake matuƙar so, duk da ba ita ta haife ni ba" Alina ta yi dariya ta ce "Ashe kai ɗana ne, to ɗan albarka zan din ga ce maka" Jinjina kai kawai ya yi, yana murmushi, ita kuma ta shiga gida. Murmushi ta ɗan din ga yi, da ta tuna saboda ita ya je makarantar su, saboda ya haska mata hanya. Da ta tuna abin da Yayanta ya yi masa sai ta ji babu daɗi, kasancewar yanzu ta fahimci yana da kirki, kawai dai ɗabi'unsa ne wasu lokutan kamar mara gaskiya. Mamman kuwa bayan ya shiga ɗakinsa, ya zare rigar jikinsa, ya gyara shimfiɗarsa, ya fito da indomie a leda, ya zazzage a wani kwano, ya cinye ya sha ruwa. Ya ɗaga ƙasan 'yar katifar da ke ɗakin, ya din ga kallon ƙasan katifar sannan ya mayar da katifar ya gyara ya kwanta yana ɗan yin miƙa. Ya ciro wayarsa daga gefen katifarsa, ya tura wasu code zuwa ga wata lamba. Ya juya ya kwanta. ***** YELWA Baffa ne ya yi zuguum yana sauraren radion da ke gabansa, yanayin fuskarsa ya nuna ruɗewa da tsoro. Ya numfasa ya ce "Juma" "Na'am" Ta amsa tana tattara hankalinta a kansa. "Ki na jin wata masifa ko?" "A ina?" "A radion nan da nake ji" Ta girgiza kai ta ce "Me aka ce?" "Faɗan manoma da Makiyaya a can wani yanki, an yanka manoma yankan rago su kusan goma sha biyu da sunan ɗaukar fansa" Juma ta waro ido ta ce "Yankawa kuma?" "Wallahi yankawa, ga shi ina ji a radio" "Innalillahi, yanzu Jauro sai a yanka mutum, kuma da wuƙa aka yanka su ko da me?" Baffa ya ce "Ina zan sani, abin da dai suka ce kenan. Wallahi abin nan yana bani tsoro. Mu ma kusan irin wannan rikicin muke fuskanta tsawon shekaru, ina tsoron ya rikiɗe ya zama wani abu daban." Juma ta ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi da yardar Allah" Baffa ya jinjina kai ya ce "Haka nake fata, amma haryanzu ina haƙurƙurtar da samarinmu, a kan lallai sai sun ɗauki fansar abin da aka yi mana. Ke dai Allah ya kyauta kawai". ***** Rahama ce ke zaune a bakin kwanarsu, tana kallon 'yan hostel ɗinsu, sun sha kwalliya su na ta raye-raye kasancewar weekends ce. Sun saka bokitai da jarakuna su na ta kaɗe-kaɗe. Littafi ne a hannunta amma tana kallon littafin tana kallonsu, saboda abin da suke yi ɗin yana saka ta nishaɗi. "Yelwa, kin noƙe kina wani murmushi, taso ki taka" Cewar wata senior ɗin ta. Rahama ta hau dariya tana girgiza kai. Ruƙayya  ta ce "Idan Rahama ta yi rawa, na yi alƙawarin bayar da kyautar sadine gwangwani goma wallahi" Shewa suka hau yi, Rahama kuwa rufe fuska ta hau yi tana dariya. "Ai wallahi Ruƙayya kin san sadine ɗin nan ba zai ciwu ba, in dai sai Rahama ta yi rawa za a ci shi. Ita a makiyayan ma ma irin na 1980s ɗin nan ne." Suka din ga tsokanar Rahama, ƙarshe ta bar musu Hostel ɗin. Naja ce ta biyo bayanta tana faɗin "Yaya Rahama" Rahama ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am Nana". "Dan Assignment ne da ni, na kasa ko za ki koya mini" Rahama ta ce "Me zai hana na koya miki, wanne subject ne?" Naja ta ce "Your favourite Maths" Rahama ta ce "Mu je Library, sai mu yi a can" Naja ta jinjina kai, ta karɓi litattafan hannun Rahama suka tafi. Boarding kenan, gidan ka zo na zo, amma duk ƙin ka da mutane haka zaka haɗu da wanda za ku rayu tare tamkar yan gida ɗaya. Duk da akwai ƙalubale, amma ana koyon darussan rayuwa. ***** "Assalamu alaikum. Salamu alaikum" Cikin bacci yake jin 'yar muryar na yi masa sallama. Da kyar ya iya motsawa, ya tashi ya saka rigarsa, ya buɗe ƙofar. Da idanunsa ta fara tozali, ta ɗan ja da baya a tsorace. "Ahh, ka yi haƙuri, ban san bacci ka ke yi ba, da dam..dama takalimina na kawo, yi haƙuri." Ya miƙa mata hannunsa yana tsare ta da ido. Jikinta na ɗan rawa ta miƙa masa takalaman nata. Ya fito tare da kayan aikinsa, sai dai yau ta ga fuskarsa a tsuke sosai da sosai. Ta lura da yadda yake aikin yau a hankali sosai da sosai. So take ta tambaye shi ko lafiya, amma ta kasa sai satar kallonsa da take yi. Gani ta yi ya tsaya cak da wanke takalmin, yana ɗan rintse idanunsa. "Meyafaru?" Ta faɗa a ɗan rikice tana kallonsa. Da hannunsa ya nuna mata cikinsa, ya tashi, ya ajiye komai a gurin, ya koma ɗakinsa. Jikinta na rawa ta tashi ta tafi gida. A kitchen ta samu Nadiya tana aikin girki. Cikin damuwa ta ce "Antynmu idan ki na da maganin ciwon ciki ki bani zan ba wa Mamman cikinsa ne yake ciwo" Nadiya ta tsaya ta ce "Waye hakan?" "Mai gyaran takalmi" "To  ba shi da lafiya, to Allah ya ba shi lafiya, duba jakar magungunan ki gani idan akwai" jikin Alina na rawa ta shiga ɗakin Anty, tana duba jakar da suke ajiye magunguna, ta dubo maganin ciwon ciki. Ta fito tana faɗin "Anty na samu, amma akwai sauran kunu? Kin ga ba zai sha magani bai ci komai ba" Nadiya ta ce "Eh gaskiya ne, amma dai da yayanki na ajiyewa kunun, kin san zai iya nema da rana ya ce zai sha" Cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Antynmu ki kawo a ba shi, sai ki cewa Yayan kununan ya ƙare. Nadiya ta ce "To Alina, a ba shi Allah ya sauwwaƙe, ya sanya kaffara" Ta tsiyaye kunun gyaɗar a kofi mai murfi, ta yi waje da sauri. Nadiya ba ta kawo komai a ranta ba, saboda sanin halin Alina. Wasu lokutan a hanya za ta tsinto almajiri, ta kawo shi gida ta ce sai a ba shi Abinci ko ta ce sai Isma'il ya ba shi kuɗi. Duk da rashin mu'amala da ita da samarin unguwar ba sa yi, amma tana shiri da alamajirai sosai da sosai. Saboda tana son bayar da abu. Cike da wauta da ƙuruciya, Alina ta faɗa ɗakin Mamma, ba tare da sallama ko neman izini ba. Da wani irin mugun zafin nama, ya saka filo akan wani abu ya rufe. Idanunta ba su kai ga tantance mata abin da ta gani ba, ya rufe da fulon. Ta ɗan sororo amma ta basar ta miƙa masa kofin kunun ta ce "Ga kunu sai ka sha, sai ka sha maganin. Tsigar jikinsa duk ta tashi, saboda azabar ciwo har wani gumi ne yake tsatsafo masa ta kan karan hancinsa. Ya saka hannu ya karɓi kofin. Kunun  da zafinsa ya kafa kai ya din ga zuƙarsa. Bai shanye ba, ya miƙa mata hannunsa, ta saka masa maganin ya ɓalle ya haɗiye ba tare da ko ya haɗa da ruwa ba. Ta tsaya cike da rashin sanin abin yi tana jera masa sannu. Bai amsa mata ba, sai yatsun ƙafarsa da ta ga yana ta lanƙwasawa, alamar yana cikin matsanancin ciwo. Ya juyo da fuskarsa a hankali, duk gumi ya tsatstsafo masa, wasu irin jijiyoyi sun shata a goshinsa raɗa-raɗa, sai idanunsa da suka yi jawur. "Je ki" Ya furta da kyar. Maimakon ta fita sai ta tsaya tana kallonsa, ganin kamar zai fita hayyacinsa. "Ki fita!" Ya yi magana cikin tsawa, yana nuna mata hanyar fita. saboda rikicewa ba ta san yadda aka yi ta ganta a waje ba. Ta kwashe takalmanta ta nufi gida a tsorace. Nadiya ta ce "Alina yanzu nake shirin fita na ga ko lafiya, ki ka daɗe, kin san fa fita zan yi, zan je Asibiti" Alina ta ce "Lafiya ƙalau, sai kin dawo" Ta shige ɗaki. Nadiya ta bi Alina da kallo tana mamakin meya tsorata ta haka, ba ta sake magana ba ta fita. Cike da tausayawa Alina take tuno yanayin da ta bar shi a ciki, amma da tuna tsawar da ya yi mata, sai ranta ya ɓaci gaba ɗaya, ta ji haushi ba kaɗan ba" Sai dai ba ta daina tantama da zuciyarta ba a kan abin da ta gani a ɗakin nasa ba. Idan ba gizo idonta ya yi mata a kamar dai bindiga ta gani a ɗakin ya saka pillow ya rufe. Sai dai ta ƙi yarda da hakan ta gani, ta basar ta ci gaba da kokwanton ba bindiga ta gani ba. Sai dai hakan bai hana ta lokaci-lokaci ta din ga leƙa ƙofar gida ba, ta ga ko za ta hango ya fito ba. ***** Kacalla ne tsaye a cikin dokar daji, tare da Sadauki, gabansu wani buhu ne a ajiye. Ya dafa kafaɗar Sadauki yana kallon idonsa. "Sadauki amanar kacalla" ya yi murmushi ya ce "Allah ya taimaki Uban ɗakina" "Ka ga dai yadda lamari ya kaya, na yarda da kai na san ba za a samu kowace irin matsala ba da yardar Allah. Ka je ka ƙarasa shirya komai da mutanenka, duk abin da ake ciki, mu yi waya." Sadauki ya ce "An gama shugabana, ka yi layar zana, ka bi ta gabasa zan Kudu da kayan, ka saka a gyara mana hanya" "Shikenan babu damuwa, Allah ya tsare" "Amin" ya saɓa buhun nan a kafaɗarsa ya yi gaba. ***** ALINA wunin ranar ba ta sake ganin gilmawarsa ba, abin ya din ga damunta, ta din ga tunanin ko yaya yake. Monday da ta fito makaranta, ta tarar da ɗakinsa a rufe, amma bai saka mukulli ba. Har guri ta samu ta ɗan tsaya, ta gani ko zai fito, amma shiru ta gaji ta tafi, dan sai da ta makara ma. ***** YELWA Baffa ne yake tafe sannu a hankali, yaje ya bawa wani yaro maganin maciji, saboda maciji ya sare shi a ƙafa, ya duba ya ga wani mara lafiya da ya yi wa ɗorin karaya, daga nan ya biya kasuwa, ya ɗan yi sayayya ya nufo gida. Yana ta sauri, ya ji ana yi masa sannu da zuwa, ya tsaya ya waiwaya ya ga wane ne, kawai ya ga Saleh. Baffa ya yi shiru bai ce komai ba, ya sa kai zai ci gaba da tafiya. "Ba za ka amsa sannu da zuwan nawa ba? Babu faɗa mai ya kawo gaba?" Baffa ya tsaya, ya kalle shi ya ce "Ɗan samari, ina gama ka da Allah, idan ka san shi. Kana kuma tsoron sa, ka fita daga harkata" Ya yi maganar idanunsa suna yi ja, muryarsa na rawa. "Baba tun da Allah ya haɗa mu zaman guri ɗaya, ai haraka ta zame mana dole. Abin da zai iya cutar da kai na gano, na ce bari na sauke hakkin maƙwabtaka" Baffa ya tsaya cikin rashin fahimta yana kallon Saleh. "Duk da lokaci ya so ya ƙure, amma ina tausayawa yadda ƙaddara ke bin ahalinku, mussaman ma kai. Duk da Ramata ba ta gari, amma kana iya ɗaukar mataki." Baffa ya ce "Ramatan kuma me ta yi muku, yarinyar da tana makaranta ma?" "Tana soyayya da ɗan uwana Bukar, wanda ka sani na sani, babu ga maciji a tsakaninmu da ku, duk abin da ya faru ka kuka da 'yarka, na gaya maka ne ka yi wa tufkar hanci, kar ita ma ka rasa ta" Cikin mamaki Baffa yake kallon Saleh, sai dai ya gaza cewa komai, sai bin sa da yake yi da ido baki buɗe cikin mamaki. Sam bai ji maganganun Saleh sun shige shi ba. Yarinyar da ba ta garin ma, ga ta da gudun magana yaushe za ta je ta yi wannan katoɓarar. Kawai ya sanya wa zuciyarsa ƙarya Saleh yake yi. ***** Bayan kwana biyu. An taso 'yan makarantar su Alina, Hafsa ta ce "Ke na sato mana littafi, yau zan karance shi cikin dare in sha Allah" Alina ta ce "Haba dai ya sunansa?" Hafsa ta ɗan yi shiru ta ce "Na manta, amma dai zan karanta mana" "To shikenan, sauran gobe in Allah ya kaimu, ki ƙi ba ni labarin. Allah dai ya sa an zuba soyayya a ciki" Hafsa ta yi dariya ta ce "Ai da ganin bangon littafin ma, ke dai ki jira, zan karance mana shi, shi kuma mu ji me aka yi a cikin sa" Alina ta ce "Kin san littafi idan da soyayya a ciki, subhanallah har wani nishaɗi yake sakawa." Hafsa ta gyaɗa kai ta ce "Ina ta ƙoƙarin ganin na sake da yaya Hafiz ɗin nan, nima mu din ga soyayyar nan na kasa, kunya ma nake ji wallahi" Alina ta kwaɓe baki ta ce "Ke kenan, da aka bawa damar ki yi soyayyar ma, ni duk wanda ya ce yana sona zagi yake sha a gurin Yaya ya kore shi, wai ni yarinya ce. Idan aka ganni zata ake babba ce ni" Hafsa ta ce "Kuma ga maza na sonki, amma wataƙila sai kin yi candy zai bari" "Mhmm ai ni na zubawa sarautar Allah ido ne ma, na bar Yaya da halinsa" Tun da Alina suka fito daga makaranta, take ankare da yana bin su a baya, amma ta basar, suke ta hira da Hafsa. Amma a ƙasan zuciyarta, ta ji daɗin ganinsa da alamar ya warke. Suka yi sallama da Hafsa ta bi hanyar gidansu, Alina ma ta bi tata hanyar. "'yar ƙwalisa" Ya yi maganar yana ɗan ƙara sauri. Sauri ta ƙara ita ma, ta ƙi ko waiwayowa, ta basar da shi. "Alina" ya kira sunanta. Ta tsaya tana zumɓura baki, ta  waiwaya kai tana kallonsa. "An taso?" Ya yi maganar yana kallonta. Ta yi shiru tana kawar da kanta gefe. Ya sake cewa "Amm dama zan ce miki na gode ne" "Da aka yi me?" Ta yi maganar tana tattaro jarumtar kallon idonsa amma abu ya gagara. Ya ɗan ja numfashi ya ce "Maganin ciwon ciki, da kuma Abinci da ki ka bani" Ɗan murguɗa baki ta yi ta ce "Daka yi mini tsawar" Ta yi maganar tana tura baki. Ya ɗan rungume hannayensa ya ce "Ohh zafin ciwo ne fa, kuma ina jin tsoron kar a zargi wani abu, mussaman yayanki, na san ya ganki a ɗakina zai iya yi mini duka ma" Idanunta ta ɗaga tana ƙare masa kallo, sai dai ba ta kalli idonsa ba, ta tura baki ta ce "Tun da abin alkhairi na yi maka, sai ka gaya mini a hankali ai. Amma ka yi mini tsawa. Kuma ni ba na son a yi mini tsawa, sai da na tsorata" Ya yi shiru yana kallonta. Ba tare da ta kalle shi ba a shagwaɓe ta ce "ka bani haƙuri to" Ya yi turus yana kallon 'yar abar da da kaɗan ta fi ƙugunsa, tana iƙirarin ya bata haƙuri, kuma yanayin fuskarta ya nuna da gaske take abin da take faɗa har zuciyarta... Ayshercool 1k ne via 0069685771 Aisha Adam stanbic Sai shaidar biya ta 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA... YOTA /002 P7 Ganin ya ƙi magana yana ƙare mata kallo, ya sanya ta yi gaba ta bar shi a gurin, Tana ƙunƙuni, da mita ƙasa-ƙasa. Bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, ganin tsagwaron ƙarfin hali irin nata. ***** PRESIDENTIAL RESIDENCE. Garin ya yi shiru, ba a iya jin motsin komai, tamkar babu halitta mai numfashi a gurin. Sannu a hankali yake kaiwa yana komowa a cikin katafaren ofishin. Ya koma ya dafa kan kujera yana juya ta a hankali da hannunsa. Ya kalli agogon office ɗin, ƙarfe uku saura mintuna goma. Yana sauke idanunsa, aka buɗe ƙofar ofishin aka shigo. "Halilu ka ƙaraso?" Ya yi maganar yana ajiyar zuciya. Cikin girmamawa kamar ya dungura ya ce "Yes sir na ƙaraso, a yi mini afuwa, ina fatan ban ɓata maka lokaci ba?" Ya girgiza kai ya ce "A'a. Bismillah zauna" Halilu ya ja kujera ya zauna, yana daga tsaye ya tura wa Halilu jarida ya ce "Ina fatan ka ga wannan, na san ma wataƙila ka riga ni gani?" Halilu ya ja jaridar ya fara dubawa. Ya shafi goshinsa, da yake jin kansa na yi masa wani irin ciwo. "Da na san abin da zan tarar kenan a ƙasar, da ko a mafarki ban nemi mulki ba. Tun bayan rantsar da ni, babu abin da na cimmawa mai muhimmanci sai ma koma baya da na fara fuskanta a ƙasar. Wannan case ɗin shi ne na uku da ya faru a tsukin kwanakin nan, dole mu yi wa tufkar hanci, kafin lamuran su fi haka ƙazanta. Wancan yankin na yamma satar mai ya ta'azzara, gabas kuma rikicin manoma da Makiyaya, da rikicin ƙabilanci. Gobe in Allah ya kaimu ka tara manema labarai, ka sanar musu na ƙoƙarin ɗaukar matakan inganta tsaro, ka dai san abin da yakamata ka yi a kai. Sannan a shirya mini zama da shugabannin rundinonin tsaro, gobe da misalin ƙarfe tara na dare. Za kuma mu naɗa wakilai su je ta'aziyya gurin da abin ya shafa" Halilu ya numfasa ya ce "Shikenan sir, za a gabatar da duk abin da ka ce, na bar ka lafiya" Jinjina kai kawai ya yi cikin ƙarfin hali. ***** Tana zaune a kan kujera, ta ɗora wayarta a kan ƙaramin table ɗin gabanta, tana kallon paper gabanta, da ta yi rubuce-rubuce a jiki, tana rehearsal. Ta bayanta ya ƙaraso yaka leƙa paper, ya ja guntun tsaki ya ce 'Yar wahala, ke dai kin ga ta kanki Laila" Ya yi maganar yana dungure mata kai. Ta ɗago tana murguɗa baki ta ce "Ba ruwanka da ni, na gaya maka ka fita daga sabga ta" "Da ruwana da ke, ke ba ki san yanzu haushinki nake ji ba, kamar na shaƙe ki na huta" "To sai ka kashe ni ka huta ai" Mama ce a gefe, a kwance a kan fulo hannunta riƙe da counter, ta ɗago tana faɗin "Sadam ba ruwanka da ita dan Allah, ka ƙyale ta" "Mama ke ki ke goya mata baya dama, kiri-ƙiri yarinyar nan, ɗan aikin nan da ta samu, ɗan abin da ake ba ta yana taimakawa, amma saboda baƙin hali, ta ja an kore ta, ta dawo wahala wai content creation. Ko uban wa ya gaya mata ɗan jarida yana ɗaukan side ya shiga siyasa oho mata" Laila ta ce "Ni fa ba siyasa na shiga ba, tun da an kore ni, i decided to take another decision. Dama can ina content ɗina. Beside yanzu na samu cikakkiyar dama na yi abin da nake so, a hankali zan yi building pages ɗina na fara samun kuɗi" Sadam ya yi tsaki ya ce "Aikin banza ƙiba a kunne, comment section ɗin ki ban da zaginki ma babu abin da suke yi" "Duk da haka ba zan gaji ba, masu yaba mini sun fi masu zagin yawa. Sannan masu zagin ma taimakona su ke yi gurin pushing ayyukana. Ni fa na gama gane ka. Kuma ina yawan gaya maka, da arziki a garin wasu gara a gidanku." "Gidanku ke a wa? Da ya ci president ɗin uban me ya tsinana miki, kullum cikin ƙona datarki ki ke a banza, da hauragiya ba a san da ke ba ma" Laila ta yi murmushi ta ce "Mu siyasar aƙida muke yi. Ko bamu samu komai ba, muddin al'umma na amfana shikenan. Ko kowa ya watse ya bar tafiyarsa, nikaɗai zan tsaya a bayansa ƙuri'ata tasa ce" Wani uban tsaki ya ja ya ce "Su na can su na satar kuɗin talakawa su na ci, yaran talakawa ku na nan kuna wahalar banza" "Idan Allah ya tsayar da kai ranar shaida, zaka nuna abin da ya sata?" A hasale Mama ta ce "Ko dai ku daina wannan musun banzan da na wofi, ko ku fita ku bar mini ɗaki. Sadam ba ka da girma sai na jikinka. Kawai ku zauna ku cika mini kunne ku hana ni sakat ni da gidana. Ko a yi mini shiru ko ku fita ku bar mini ɗaki na huta, iskancin banza kai" Laila ta yi masa gwalo, ya galla mata harara, ya fita. Ta saita wayarta ta kunna video ta fara recording. Mama ta ce "Malama ki yi ƙasa-ƙasa kin cika mini kunne, ko kema ki fita yanzun nan ki bani guri" Laila ta ce "Na fuskanci videon nan ne dai ba kya son na yi, bari na tafi tsakar gida" "Eh sauka lafiya. Haba wannan abu har ina, kai da gidanka ba zaka huta ba" Laila ta kwashi kayan videonta, ta fito waje. **** "Amanar kacalla" "Allah ya bar mini kai Madugu" "Ya ake ciki?" "Kaya sun zo hannu, an samu shanu ɗari biyu da goma sha biyu. Ga kuma tumaki da raguna guda ɗari" Kacalla ya numfasa ya ce "Ku kaɗa su boda, akwai tireloli su na nan su na jiranku, za su karɓa su bar ƙasar da su" Sadauki ya ce "To ina fatan sun gyara mana hanya, saboda aka samu kuskure zubar ruwa za mu yi kan mai uwa da wabi" Kacalla ya ce "A huce haka Sadauki, na kula da komai, an share hanya ku saka kai kawai" "Allah ya bar mini kai ubangidana, ina sanya ran zuwanmu nan da kwana biyu" "To shikenan, duk yadda a ke ciki mu yi magana kawai. Ka kiyaye da lokutan kirana" Sadauki ya ce "Na kiyaye" ***** Ɓangaren Alina ta daina gaida Mamman, ta kuma daina kai masa wankin takalmi, idan ta zo wucewa ma sai ta kawar da kanta gefe tana haɗe rai, da zumɓura baki. Yana zaune a bakin hanya, ta zo ta wuce shi za ta tafi makaranta, ta yi nisa sosai wani almajiri ya biyo ta yana ƙwala mata kira. Ta tsaya tana kallon yaron. "Ga shi in ji wani mutum ya ce a baki" Ta kalli takardar da ya miƙo mata, ta karɓa ta buɗe. Shiru ta yi tana kallon rubutun ajamin da yake jiki. "Na yi ba daidai ba, ba zan sake ba" Ta waiwaya ta ga yaron ya tafi,  ta ɗan yi murmushi ta ninke takardar ta saka a jakarta. Bayan an tashi daga makarantar boko sun fito tare da Hafsa, da shi ta fara cin karo a waje, a ƙofar makarantar yana jiran ta. ba ta ce masa komai ba, suka wuce shi da ita da Hafsa. Sai da suka yi sallama da Hafsa suka rabu a hanya sannan ta tsaya. Ya ƙaraso yana tsare ta da ido. Tsiwa ta so ta ɗan yi masa amma kuma sai ta kasa, idanunsa suka ɗaure ta, ta gaza cewa komai. A hankali ya ce "Kin ga saƙona?" "Na gani" Ta amsa tana juya masa ƙeya. "To ya wuce?" Alina ta jinjina kai. Ya ɗan yi murmushi ya ce "To ki juyo mana" Ta ɗan ɗago, amma ba ta bari sun haɗa ido ba. Ta rufe fuska tana murmushi. Ya sake kwantar da murya ya ce "Ina fatan za a ci gaba da kawo mini wankin takalmin, kuma za a daina fushi da ni?" Tana ƙoƙarin yin murmushi tana mazewa ta ce "Zan kawo maka ma idan na taso daga islamiyya" Ya ce "To ya yi, yaushe ne saukar ne?" "Mun kusa in sha Allah" "Allah ya sanya albarka" "Amin na gode sosai" "Idan da taimakon da ki ke buƙata, ko inda ba ki iya ba, ki gaya mini na koya miki" "Kai amma na ji daɗi sosai, na gode." Ya jinjina kai ta wuce gida. Ya tsaya shiru yana bin ƙofar gidansu da kallo. Yana sake nazarinta. Kamar yadda suka yi da ita, bayan ta dawo daga islamiyya ta kai masa wankin takalmi, ta kai masa har da abinci. Ya kalli flask ɗin Abincin ya kalle ta, ta yi shiru tana jiran ta ji me zai ce. Sai kuma ta ji ya ce "Yayanki ba zai yi miki faɗa ba?" Ta jinjina masa kai, jiki a sanyaye ya karɓa, dan ya ga alamar idan bai karɓa ba akwai daru. "Yaya Mamman" Ta kira sunan shi, hannunta riƙe da ƙulu tana saƙa. "Ba ka gaya mini sunan garinku ba." Ya numfasa ya ce "Ai ko na gaya miki ba ki san ina ne ba" "To da ka yi ciwon cikin nan ka je Asibiti ne?" Ya amsa da "A'a" "Meyasa?" "Ba ni da kuɗi" "Ka je a duba me yake damunka, idan aka rubuta maka magani sai na bawa yaya ya saya maka" Mamman ya kalle ta ya ce "Idan zan mutu yayanki ba zai saya mini magani ba" Ta ce "Wallahi zai saya maka in dai na kai masa. Yana da kirki fa, kawai dai saɓanin fahimta ne ku ke samu da kai da shi" Tun yana biyewa surutun Alina, har ya yi shiru, dan da alama ita ba gajiya take yi ba. Ya gama wanke mata takalminta, ya bata abin ta. Sai dai a wannan karon ma bai karɓi kuɗin ba. Godiya ta yi masa cikin harshen turanci tana murmushi, sai dai yadda ta lanƙwasa harshenta ta yi magana, tamkar baturiya" Sai da ya kalle ta da mamaki, duk da makarantar da take zuwa ta boko, mai tsadar gaske ce. Amma abu ne mai wuya a ce a nan iya wannan turancin. Ya numfasa ya ce "Ina fatan dai ba zagina ki ka yi ba, tun da kin san ban iya yaren nasara ba" Ta yi dariya ta girgiza kai ta ce "Godiya kawai na yi maka fa, yaya za a yi na zage ka ma?" "To ai na ji turancin ma, ba irin na 'yan nan ba, kamar na turawa ki ka yi, ya aka yi ki ka iya irin wannan?" "British Academy na yi Nusery da primary, daga baya na ce bana son makarantar, Yaya ya dawo da ni nan" Ta yi maganar tana karkaɗe gefen rigarta. Ya yi murmushi ya ce "Lallai yaya attajiri ne, British Academy ki ka je?" "Wai kai ma ka yi Makarantar boko ne?" Ya yi murmushi ya ce "A'a, na san dai makarantar turawa ce, kuma tun da makarantar turawa ce, za ta yi tsada sosai" "Aikuwa da tsada sosai, har breakfast da lunch ake bamu fa, malamanmu har da turawa, sai da muka tashi daga waccan unguwar ga nisa, ga wataran Yaya baya gari, nima dai na ce ba na son makarantar, aka dawo da ni wannan" Ya jinjina kai ya ce "Lallai yaya ya yi ƙoƙari sosai, yana son ki yi karatu" Ta ce "Eh mana, kuma ina yi sosai da sosai ba" Sannu a hankali, wata irin shaƙuwa ta din ga shiga tsakanin Alina da Mamman mai wankin takalmi. Wanda har ta kai Alina ta saka masa kwanon abinci, a gidansu safe rana dare, duk abin da aka dafa sai ta zuba ta kai masa. Tun tana ɗan jin ɗar-ɗari, saboda jarabar Yaya Ismail, har ta rage jin tsoron. Hatta alaƙarta da Hafsa sai da ta ja baya, saboda Mamman. Ba ta taɓa zaman mintuna ashirin ba ta yi zancensa ba. Idan ta taso daga Islamiyya, sai ta tsaya a gurinsa, su yi hira ya jiye mata hadda. Wataran kuwa a ƙofar makarantar take tarar da shi su tafi tare. Nadiya nata bacci, ta yi juyi kawai ta ga Ismail a zaune a kan gado. Ta kai hannu ta shafa bayansa ta ce "Masoyi ya dai na ganka a zaune, kai ba salla ba meyafaru ne?" "Alina" ya ba ta amsa a taƙaice. "Me ta yi kuma?" Ya ja numfashi ya jingina da allon gadon ya ce "Alaƙarta da mutumin nan ce ba na so ko kaɗan, alamu sun nuna na yi sake shaƙuwa ta shiga tsakaninsu, na kuma fuskanci idan na matsa, za ta iya jin haushina. Na fuskanci yadda magana ɗaya biyu a gidan nan sai ta ce Mamman, hatta yadda take rawar jikin kai masa abinci duk ina ankare da ita, kallonta kawai nake yi" Nadiya ta tashi zaune ta ce "Masoyi, ko muna so fa ko ba ma so, dole Alina a ce ana sonta, kuma dole a aurar da ita, yawan hana ta kula samari da ka ke yi, kar ya zame mata matsala fa a gaba. Sai dai kuma idan abin da nake so tsoro ne zai faru" A kausashe ya ce "Za ki fara ko? Sau nawa zan gaya miki ki daina ɗarsa wannan shirirtar da a ranki? Alina yarinya ce ƙarama fa, soyayya kuma barazana ce ga mutum mai ƙallafa abu a rai kamar ta. Idan Alina ta kamu da soyayya za ta sha wahala, kuma ban shirya bawa ƙasƙantaccen mutum kamar wannan auren Alina ba, dan ni gaba ɗaya ban yarda da shi ba, yanayinsa gaba ɗaya na marasa gaskiya ne, ina nan ina bibiyar lamuransa, ta ƙarƙashin ƙasa zan yi maganinsa sai ya bar unguwar nan. Sannan dole ni zan nemawa Alina wanda ya dace da ita, saboda gudan abin da ka iya zuwa ya dawo" Nadiya ta numfasa ta ce "Maganganun ka gaskiya ne, amma Alina ba soyayya take yi ba, kawai dai jininsu ya haɗu ne. Ina saka ido sosai da sosai nima a kanta" Kawai ya yi dariya ya kwanta, ya ce " za kuwa ta baki mamaki, za ki ce na gaya miki. Na saka masa ido ta kowace fuska yanayinsa da ƙirarsa ta marasa gaskiya ce, amma ina nan ina bin diddiginsa" Alina ce tare da Mamman, tsaye a ɗan madaidaicin shagon provision ɗin da Alhaji Sadi ya buɗe masa a cikin layin, ya ce ya din ga zamar masa a ciki. Cikin washe baki Alina ta ce "Allah ya sanya maka albarka, ya sanya daga wannan ka buɗe plaza ƙatotuwa, kamar rabin unguwar nan" "Amin 'yar ƙwalisa" Ya yi maganar yana dariya. Ta ce "Ɗan albarka" "Na'am" "To yanzu shikenan ka daina wanke mini takalmina, wa zai din ga wanke mini kenan"'?" Ya din ga kallon idanunta, har sai da ta sunkuyar da kai ta daina kallonsa. Can ya ce "Na daina gyaran takalmi, ko wankin takalmi,sai naki kawai" ya yi maganar yana kallonta. Ta yi dariya tana rufe fuska. Can kuma ta ɗago ta ce "To ka gaya wa mamanka ta yi maka addu'a, an buɗe maka shago?" Ya jinjina kai ya ce "Tun jiya, na kuma ba ta labarinki, ta ce na gaishe ki. Ta kuma gode da ciyar da ni da ki ke yi" Ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Ka ƙi bani ita mu gaisa, ina son ta yi mini addu'a, na ji ya ake ji" Cikin rashin fahimta ya tattara hankalinsa a kanta, ya ce "Kamar yaya kenan?" Ta yi shiru jikinta a sanyaye ta ce "Ban san mamanmu da babanmu ba, Yaya ya ce mini dai ni kama ta ɗaya sak da mamanmu, shi kuma da babanmu yake kama" Mamman ya ce "Ban fahimce ki ba, sun rasu ne?" Ta gyaɗa kai. "Oh Allah, ki yi haƙuri ki din ga yi musu addu'a, Allah ya gafarta musu" Maimakon ta amsa sai ya ga ta fashe da kuka. Sai ya rikice ya yi ƙasa da murya ya ce "Ki daina kuka dan Allah, ki rufa mana asiri kar a ce ko wani abin na yi miki ma, ki yi haƙuri mu yi musu addu'a" Ta jinjina masa kai tana share hawayenta. "Yauwwa kar ki saka yaya ya zo ya zane mu" Ta saki murmushi ta ce "Haba dai, ba zai zane mu ba, sai dai ni ya zane ni, kuma nima ɗin baya dukana ai" "Hmm ke ba zai zane ki ba, amma ni fa" "Kai ma ba abin da zai yi maka" Suka ci gaba da hira cike da shaƙuwa. ***** 'yan boarding su na cikin walwala da farinciki, kasancewar yau ranar visiting ce, makaranta ta cika ta batse da iyayen da 'yan uwan yara. Tun da Rahama ta ga azahar ta wuce ba ta ga Baffa ba, ta fitar da ran za a zo mata. 'yar kwanarta Anty Ruƙayya ce, ta janyo ta cikin 'yan uwanta, suke ta hira kamar tare aka zo musu. Dan tun Rahama na jss 1 Ruƙayya ke bayar da labarinta a gidansu, idan an zo visiting ko hutu ma su na haɗuwa da 'yan uwan Ruƙayya. Maman Rukayya na son Rahama, mussaman da ta ji labarin, daga ƙungurmin ƙauyen da babanta ya ya sadaukarwar kawo ta makaranta, kasancewarta 'yar boko. Maman Ruƙayya ta ce "Rahama ni wannan kunyar taki ta yi yawa, ko dai a cikin yayyen Ruƙayya wani ki ke so ne?" Rahama ta sunkuyar da kai tana murmushi. "To matso nan mu ci abinci tare, ke dole ma a yaran nan zan yi miki miji. In dai Baffanki zai ba mu ke. A ba wa Abdallah ko Ammar" Kamar ta nuste, haka ta ɗan cakali Abincin nan, saboda Rahama akwai gudun Duniya da abin hannun mutane. Ga su Rukayya kuma masu kuɗi ne sosai da sosai. Idan za a zo mata visiting sai an yi nata na package ɗin. Har Baffan Rahama 'yan gidansu Ruƙayya sun sani. Mami ta miƙa wa Rahama wayarta da take ringing. Ruƙayya ta ce "Waye" "Karɓi ki duba mana" Ruƙayya na ganin sunansa, ta yi murmushi ta koma gefe ta ɗaga. "Yaya Mubarak" "Na'am shalelen, ashe su Mami sun ƙaraso, na so zuwa ayyuka ne suka yi mini yawa sosai, kin san yayyen nan namu, sai su cinye mutum idan bai yi abin da suke so ba" Ta yi murmushi ta ce "Take your time ka yi aikinka a hankali, kawai idan ka samu time ka zo na ganka" Mubarak ya ce "Wanne dole ne, dan ba zan iya shafe wata uku ban ganki ba, zan zo in sha Allah." Sun yi hira sosai kafin su yi sallama. Yana zaune a cikin mota, ya kwantar da kujera, ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya, ya ɗora a saman sitiyari yana ɗan kaɗa ta, hannunsa ɗaya riƙe da waya yana magana. "Wallahi Ummi ce ta sako ni a gaba, wai sai an zo wa yarinyar nan visiting, daga zuwana gidan na ɗan huta, dan dai ba yadda zan yi ne" Daga cikin wayar mai amsa wayar yake magana, cike da kamala, da har kamalar tasa take nuna isa isa. Yayinda nauyin muryarsa ya sanya in da da wani mutum a cikin motar bayan shi zai iya jin abin da yake faɗa, duk da wayar ba a hansfree take ba. "To mene ne a ciki dan ka je wa Ruƙayya visiting, I wish ina da little sister da za ta ga gata" Na cikin motar ya kwashe da dariya ya ce "Ta ga gata, ko ta ga gwale-gwale, kai da gidanku gidan maza ne, Ummi ce kaɗai mace, da kuna da ƙanwa azaba za ta sha ne kawai" "Alfa zan zage ka wallahi" Alfa ya ce "Ware, gidan nan naku imaninku da sauƙi wallahi, ku kanku ganawa kanku azaba ku ke yi" Ya yi maganar yana ƙyaƙyata dariya. Tsaki wancan ya ja ya ce "Stupid" "Kai tsaya, ga su can ina ga sun gama tafiya za mu yi, zamu yi waya anjima take care" "Take care like? Mace ne ni da za ka wani ce mini take care?" "Zan zage ka fa, ma yi waya dai. Don't care, stay wrecked tun da baka da mutunci" "Am wrecked already ai" ya katse wayar yana ɗan tsuke fuska. Ummi ce ta fara ƙarasawa gaban motar ta ce "Ammar ba dai baƙin hali ba, for more than 5 months bana tunanin kun haɗu da yarinyar nan, ka fito ka gana da 'yar uwakka amma ka ɗauki motar ka tafi gantali ta zo baka nan" Ya kalli Rukayya, ta risuna ta ce "Yaya Ammar Ina wuni, ya aiki?" "Lafiya kalau, ya karatu?" "Lafiya kalau Alhamdillah." "To a mayar da kai a yi karatu da kyau idan ana son a ga daidai." Ta yi murmushi ta ce "In sha Allah thanks" "Ina wuni" Rahama ta faɗa daga bayan Ummi a tsorace. "Lafiya sannu" Ya yi maganar yana sake mayar da hankali kan wayarsa. Ummi ta ce "Wannan wace irin amsa ce? Haka ka amsawa 'yar uwakka? Ka daina irin haka. Ita ma ƙanwarka ce ai" Ya jinjina kai ya ce "To hajjaju, tuba nake." Ya ciro kuɗi ya miƙa wa Ruƙayya kuɗi ya ce "Ga shi nan ki ƙara, a kula da karatu sosai" "Ita ɗayar me ta yi maka?" Ya ce "Wa?" "Ban sani ba" Rahama kuwa tuni ta juya za ta tafi, amma Ummi ta kira ta, ta saka Ammar ya ba ta kuɗi ita ma. Sai dai da fari ƙin karɓa ta yi, sai da Ummi ta haɗe rai. Su na tafe a hanya Ummi na yi wa Ammar faɗa."Ammar ba ka kyautawa abun da ka ke yi, yaran nan ƙannenka ne, su na sonka su na ƙaunarka, su yi ta murna idan za ka zo, amma ka yi ta wulakanta mini yara dan baka da kirki?" Ammar ya na kallon hanya ya ce "Ummi kin san raini ne ba na so, amma nima ina murnar ganinsu ai" "Ƙarya ka ke yi, kuma dan wulaƙanci har da baƙuwa, yadda ka amsawa Rahama gaisuwar da ta yi maka ya bani haushi" Ammar ya waiwaya ya ce "Wace Rahama?" "Yarinyar da suka zo da Ruƙayya mana, Junior ɗin ta ce, wulaƙanci ba shi da daɗi ai" "To Ummi, ban san yarinya ba sai na din ga washe mata baki kamar wani shashasha" "Kai ubanka, ina yi maka magana kana kawo mini useless excuses ɗin ka" "Allah ya baki haƙuri" "Amin. Baƙin hali ba abin yi ba ne Ammar, ba a san inda rana za ta faɗi ba" Ƙasa-ƙasa ya ce "A yamma mana Ummi" jin ta yi shiru ya ɗan waiwaya ya ga tana hararsa ya kawar da kansa ya ci gaba da tuƙinsa. Rahama a ƙasan zuciyarta ta ji babu daɗi rashin zuwan Baffa, tare da rashin sanin dalilin da ya hana shi zuwa. Da daddare da suka koma Hostel, kowa yana ta murna, Rukayya na ta ƙoƙarin ganin Rahama na walwala amma da ta hau kan gado sai da ta yi kuka. ***** Dattijo ne a ƙalla mai shekaru hamsin da takwas, yana zaune a kan buzu, hannunsa riƙe da Alqur'ani bugun warsh, yana karantawa. Opposite ɗin sa wata irin ƙatuwar rumfa, shimfiɗe da tabarmi da alluna a jijjingine, almajirai sun tafi bara. Sallama ya yi wa dattijon, ya nemi guri ya zauna a gefensa. Dattijon ya kai aya, sannan ya amsa sallamar suka gaisa. Ya dubi dattijon ya ce "Malam Ɗayyabu ko?" "Eh nine" "Dan Allah tambaya na zo na yi maka, kai malamin Alqur'ani ne. Ma'abocin Alkur'ani kuwa za a same shi da gaskiya da tsoron Allah. Kuma yanayin dattakunka, ya sanya mini yarda da komai zai fito daga bakinka, gaskiya ce" Malam Ɗayyabu ya jinjina kai ya ce "Wannan gaskiya ne, in sha Allah yadda ka kyautata mini zato, ina sanya ran gaya maka gaskiya da yardar Allah" "Akwai wani matashi da ya tare a unguwarmu, ya ce shi ɗalibinka ne, ya yi sauka a hannunka, daga baya kuma ya sake dawowa garin nan, neman kuɗi. To ina son tabattar da hakan daga gare ka ne, saboda yana ɗan bibiyar 'yar uwata ne, ina tsoron wani abin da ba a so ko fata ya faru, na ga yakamata lallai na bibiya" Malam Ɗayyabu ya ce "Wannan gaskiya ne, ka yi kyawun kai, mussaman zamanin nan da ya lalace. Amma ka ga tun ban fi shekara ashirin da biyar ba, nake harkar ɗalibai, dan haka wanne daga cikin ɗaliban nawa?" Ya ce "Sunansa Mamman, ban san sunan garinsu ba, amma ga hotonsa". Ya yi maganar yana ciro wayarsa ya ɗan daddana, ya miƙa wa malam Ɗayyabu. Hoton Mamman ne a zaune yana wankin takalmi, Alina na gefensa a kan dakali tana magana. Malam Ɗayyabu ya karɓi wayar ya yi shiru yana kallon wayar, ya numfasa ya ce "Wannan ce yar uwar taka?" "Ba a kanta mu ke magana ba malam, wannan mutumin da ya ce shi ɗalibinka ne, nake magana a kai" Malam Ɗayyabu ya yi shiru ya zuba wa hoton ido. "Malam ka yi magana mana" Ismail ya yi maganar yana kallonsa. Malam Ɗayyabu ya ɗago kai yana kallon Isma'il. Ismail ya ce "Ina ƙara tuna maka, ka dubi girman mai littafin da yake gabanka, ka gaya mini gaskiya" "Ɗalibina ne" Ya yi maganar yana gwama numfashi. Ismail ya yi shiru yana nazartar fuskar malamin. "Ka tabattar ɗalibinka ne?" Ya jinjina masa kai yana ɗan zazzare ido. "Idan akasin gaskiya ka gaya mini, mai Alqur'anin nan ba zai bar ka ba" "Me zai sanya dattijo kamar ni, ya yi maka ƙarya, alhalin baka sanni ba ban kuma sanka ba? Mamman ɗalibina ne, sai dai ya sauke ya haddace, dan haka ya kai munzalin da zai zaɓi abin da yake so, kuma ina da yaƙinin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba" Ismail ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne,na gode sosai da sosai Malam" Suka yi musabiha, ya tashi ya tafi. Yana tafiya jikin Malam Ɗayyabu ya yi sanyi, wani irin gumi ya fara tsatstsafo masa, ya kalli Alqur'anin da yake gabansa ya furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, da wani bakin zan nemi gafarar Allah" 'yar ƙaramar wayarsa da ke cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya ciro ta, yana kallon yadda kira yake shigowa babu suna kuma babu lamba. Hannunsa na rawa ya kara wayar a kunnensa. "Aikinka ya yi kyau, idan aikin naka ya ci gaba da kyau, shikenan ka tsira, idan kuma aka samu matsala salin alin zamu ɓatar da kai".... Ayshercool 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g *MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN* *Masu nema daga farko, su duba cikin channel link ɗin nan* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** SARA DA SASSAƘA... AYSHERCOOL YOTA/002 Page 8 Sannu a hankali ya ajiye wayar, jikinsa na ci gaba da tsuma, ya tashi tsaye a hankali yana waige-waige, ya ga ko zai hango wani a gurin, da ko shi ne ya bayar da rahoton zuwan matashin, amma bai ga kowa ba. Zuciyarsa ta raya masa haɗin baki ne, ana sane aka turo shi, dan a gani ko zai faɗi wani abu ko ba zai faɗa ba. Ya sanya hannu ya ɗauki Alqur'aninsa ya tafi yana ta istigfari. ***** Tana tsaye daga nesa da shagonsa kaɗan, ya buɗe ƙofar ya tsaya yana kallonta. Doguwar riga ta saka, da wani ɗan ƙaramin mayafi, hannunta riƙe da flask ɗin Abinci. Tun kan ta ƙarado, ƙamshin turaren da take yi, ya karaɗe ilahirin gurin. Ta saka jam baki a bakinta, idanunta kuma ta saka kwalli. "Ɗan Albarka" "Mmm 'yar ƙwalisa" Ta yi murmushi ta ce "Bacci ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a. "Me ki ka dafa mana ne yau?" "Buɗe ka gani" Ta yi maganar tana miƙa masa flask ɗin Abincin, ya karɓa ya buɗe, ya ga tuwon shinkafa da miyar wake. Ta miƙa masa ledar hannunta ta ce "Ga zoɓo mai muslmin sanyi kuma" "Na gode sosai 'yar ƙwalisa" Cikin jin nauyinsa ta ce "Nima na gode, sai anjima" Ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Ina kuma za ki je?" "Zan je titi ne sayo wa Antynmu abu" "'Yan mata mayafin nan ya yi ƙarami fa, ana ganin jikinki. Kuma ga shi kin yi kyau sosai da sosai" Ta rufe fuska ta ce "Dan Allah ka daina bani kunya mana" "Hmm ba kunya nake baki ba, gaskiya na faɗa, kuma mayafin nan ya yi kaɗan, ba ki san kin fara girma bane?" Ji ta yi tamkar ta nutse saboda kunya da ta mamaye ta. Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Yanzu zan dawo fa" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓe. "A dawo lafiya, na gode sosai da abinci" Ta juya ta tafi, ba tare da ta sake cewa komai ba. Yana zaune bayan ya gama cin abincin, ya jiyo hayaniya a waje, sarai ya ɗauki muryar Isma'il sai bala'i yake yi, har ya basar saboda ya riga ya fuskanci Ismail masifaffe ne lamba ɗaya. Sai dai tuna cewa ba a jin kansa, idan ba Alina aka taɓa ba, ya sanya ya tashi da sauri ya leƙa. Aikuwa kamar yadda ya yi tsammani, wani matashi yake yi wa hargowa, tun daga titi ya gano shi, ya bi Alina yana yi mata ɗan kira, ya biyo su a babur sai da suka shigo cikin layi, ya rutsa su yana zazzaga wa matashin bala'i. Tuni mutane suka taru su na ba wa Isma'il haƙuri. Alina kuwa yanayin fuskarta ya nuna rashin jin dadin tijarar da yake yi wa matashin, ga jama'a ya tara musu, sai ɗaga murya yake yi. Takaici ya sanya ta wuce gida ta bar su a gurin. Da kyar aka ba shi haƙuri, matashin ya tafi. Mamman ya girgiza kai kawai yana murmushin gefen baki. Kamar guguwar baƙin hadarin kaka, haka Ismail ya shigo gidan yana ci gaba da bala'i. "Wallahi Alina idan ba ki kiyaye ni a kan gayyar mazan nan da suke bibiyarki ba, a gabansu zan naɗa miki duka wallahi. Ke ba ki san halin da ƙasar nan ke ciki ba na rashin tsaro, kowa ba abin yarda ba ne, amma da yake kin fi kowa mutunci kowa sai ya biyo ki yana yi miki surutun banza kina washe baki, mara hankali kawai da ba ta san ciwon kanta ba" "Yaya wallahi ban san shi ba, biyo ni kawai fa ya yi" "Rufe mini baki ina magana kina magana" Yadda ya yi maganar cikin ƙaraji, ya sanya babu shiri, ta shige bayan Nadiya tana ɓuya. "Ki ci gaba kar ki fasa. Wataran sai kin janyo mana abin da ya fi ƙarfinmu, ko tilasta mana komawa inda muka fito yadda mu ma za a kashemu kamar yadda aka kashe iyayenmu. Shi kansa wannan ɗan iskan da ki ka saki jiki da shi kamar ubanki, ki ka liƙe masa kallonki kawai nake yi. Gaba ɗaya mutumin nan da ganinsa ka san munafuki ne ba shi da gaskiya. Ƙirarsa da idonsa duk na miyagun mutane ne, babu ta inda ya siffantu da wani almajiri, amma kin liƙe masa, na rasa uwar da yake gaya miki. Amma za ki ga matakin da zan ɗauka a kanku" Alina ta fashe da kuka, Nadiya ta rungume ta ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Ki daina kuka rabu da shi, ya yi faɗansa ya gama, kar ma ki sake kare kanki, ƙyale shi" Bayan fitar Ismail Alina ta ce "Antynmu ni shikenan haka zan zauna, yaya ya korar mini ƙawaye, ya hana ni hulɗa da kowa? Kuma wallahi Mamman mutumin kirki ne, ai kema kin san ba zan je inda zan lalace ba, ai ina bin nasiharku ba zan baku kunya ba. Kuma ni ba saurayina bane" "Na sani Alina, amma duk wanda zai so mu, ba zai kai yadda Yaya yake sonmu ba. Duk abin da yake yi, yana yi ne, domin ya bamu kariya kar wani abu ya cutar da mu, ki yi haƙuri wataran sai labari" Alina ta jinjina kai. "Alina" Nadiya ta kira sunanta tana nazartarta. "Na'am" "Son Mamman ki ke yi ko?" Alina ta ɗago da sauri ta ce "So kuma? Haba Antynmu, ni wallahi ba son shi nake yi ba, kina ganin mutuncin da yake yi mini, ni kawai dai mun saba ne. Yana da kirki kuma yana koya mini karatu" Nadiya ta jinjina kai tare da yin murmushi ta ce "Shikenan tashi ki je" Ismail kuwa yana dawowa daga sallar isha'i, ya manta da faɗan da ya yi wa Alina, sai da bai ganta a tsakar gida ba, ya tambayi Nadiya ta tuna masa ai ta yi bacci tun faɗan da ya yi mata. Bayan kiran sallar asuba na farko, Mamman ya buɗe ƙofar ɗakinsa domin kama ruwa ya yi alwala, kawai ya yi tozali da Isma'il a tsaye kamar bayyanar aljan. A tsorace ya ce "Lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Isma'il. "Ba lafiya ba, gurinka na zo" Ya ajiye butar hannunsa, ya ce "Allah ya sanya ba laifi na yi ba" Ismail ya ce "Na je gurin mutumin da aka ce ka yi karatu a hannunsa,  ya tabattar mini da kai ɗalibinsa ne, sai dai Haryanzu ni ban ji na yarda da kai ba. Amma na san komai girman gona akwai kunyar ƙarshe. Na fuskanci amfani da ƙarfi gurin raba ka da kanwata, zai iya zama cutarwa a gare ta, ka yi amfani da yaudara ka sanya kusanci tsakaninka da ita. Kuskure mafi girma da za ka yi shi ne fara soyayya da Alina, na kuma fuskanci idan ban yi da gaske ba abin da zai faru kenan. Ka sani akwai layin da idan ka ƙetara a kan Alina zan iya sadaukar da rayuwata na yi zaman prison na har abada saboda ita" Mamman ya kalli Ismail ya yi murmushi ya ce "Ban san dalilin da ya sanya ka tsane ni har haka ba. Ni da Alina zaren ba kalar yadin bane ba, kawai mutumtaka ce a tsakaninmu. A ɓangarena na yi maka alƙawarin, kare martabar Alina, ba zan faɗa soyayya da ita ba, sai dai ban yi maka alƙawarin hana ta sona ba" Wani mugun kallo Ismail ya yi masa ta hasken fitilar solar gurin, ya yi ƙwafa ya juya ya bar gurin. Gari ya fara haske, Ismail ya yi sallama a ƙofar ɗakin Alina, ta amsa masa murya ƙasa-ƙasa. Ya ɗaga labule ya shiga. Ta tashi zaune daga kwancen da take, ya zauna a gefen katifarta yana kallonta. "Alina fushi ki ke da ni, ko gaisuwa ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a zan gaishe ka, tsoro nake ji, kar na je wani laifin na sake yi ne" Ya ɗan jinjina kai, tare da kaɗa ƙafafuwansa da ya miƙe, ya ce "Ƙanwata, na san maybe kin yi fushi da Yaya, amma duk abin da Yaya yake yi, ƙoƙari yake bawa halittu mafi soyuwa a gare shi kariya, wato Fatima da Nadiya, a duniya yanzu ba ni da kamar ku, gurin baku kariya daga duk abin cutarwa, sai inda ƙarfina ya ƙare. Ke yarinya ce Alina, haryanzu ba kya banbance mene ne daidai da akasin haka, kuma kina kan shekaru mafiya hatsari na ruɗin ƙuruciya, zuciyarki a buɗe take, duk abin da ya yi mata daɗi, ko ya burge ta, karɓa za ta yi. Shiyasa nake taka tsantsan gurin tantance miki aya da tsakuwa. Ni gaba ɗaya mutumin nan bai yi mini ba, yana da sifofin munafukai marasa gaskiya. Amma ba na son ɓata miki rai shiyasa nake ta saka muku ido. Ki yi haƙuri faɗan da na yi miki, amma ki yi a hankali kar ki kawo mana abin da zai kawo mana barazana ga kwanciyar hankalinmu." Har ya yi magana ya gama, Alina ba ta ce uffan ba, ya tashi ya fita. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ba ta son abin da za ta ɓata wa yayanta rai, amma gefe guda sun shaƙu da Mamman, rana tsaka ta daina kula shi ba ta kyauta ba. Ga shi gaba ɗaya cikin abin da bai fi wata ɗaya da satuttuka ba, suka yi wannan shaƙuwar. ***** Ruƙayya ce ta ƙura wa Rahama ido, yadda take ta juya abu a kofi ta kasa sha. "Rahama ya ne? Me yake damunki ne?" Ta ɗago ido ta kalli Rukayya, ta sunkuyar da kanta. "Ke kalle ni, mene ne?" Ta girgiza kai alamar, babu komai. "A'a da komai, mene ne?" "Baffa bai zo ba, bai kuma kira kowa ba a gaya mini dalilin rashin zuwan nasa, a tsorace nake" Ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido. Ruƙayya ta ce "Haba Rahama, wataƙila wani abin ne ya hana shi zuwa, amma da yardar Allah zai zo" Rahama ta ɗan rausayar da kai ta ce "Duk da ƙaunar makaranta da nake yi, a duk lokacin da na taho, hankalina a tashe yake. Saboda rashin sanin abin da yake faruwa a garinmu. Garinmu babu cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali". Rukayya ta dafa kafaɗarta ta ce "Babu abin da yake faruwa sai alkhairi. Share hawayenki ki gama ci, ki zo mu je Clinic akwai marasa lafiya" Ta jinjina kai ta kammala abin da take yi suka bar Hostel ɗin. A clinic ɗin suka tarar da wata ɗaliba da ƙofa ta ji wa rauni, zai yi mata ɗinki. Yana ganin Rahama ya hau murmushi ya ce "Ai yanzu nake saka ran na aika a nemo mini ke, na ga yau ban ganki ba" Ruƙayya ta ce "Yaushe za ka ganta, tana can tana shagwaɓa, wai Baffa bai zo mata visiting ba, tun da yan gidanmu da suka zo mata dodanni ne" Ya ɗan yi dariya ya ce "Ai ba a shiga tsakaninku, ina ga idan ki ka yi Candy sai kin jira Rahama" "Wannan dole ne" Ta yi maganar tana dariya ta wuce ɗakunan da ake ajiye ɗalibai idan ba su da lafiya" Rahama kuma a gefen Likitan ta zauna, tana ci gaba da yi masa tambayoyi kamar yadda ta saba. ***** Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, yana tsaye a jikin tagar ɗakinsa, yana shan sigari, ya sha ta kai uku. Sannan ya dawo ya canza kayan jikinsa, zuwa shirt da dogon wando, ya samu wani mayafi, ya rufe fuskarsa, ya ɗaga ƙasan fulonsa, ya ɗauki abun da zai ɗauka, ya ɗau ƙaramar wayarsa, da wata wallet, ya rufe ɗakin ya fita. Da safe Ismail na kallon Alina nata rawar jikin kai wa Mamman Abincin safe, wanda da wani abin ne ya nuna baya so, da tuni ta bar abin, amma nasihar da ya yi mata ba ta shige ta, dan bai ga alamar za ta ja baya da hulɗa da mutumin nan ba. Shi dai fargabarsa ɗaya kar Alina ta faɗa soyayya a shekarun ƙuruciya, mussaman da mutum irin wannan da haryanzu ya kasa nutsuwa da shi. Ba ta fi mintuna uku da fita ba ta dawo, tana faɗin "Antynmu ga Abincin Mamman, baya nan ko ina ya tafi da sassafen nan, idan ya dawo ya ƙwanƙwasa miki ya karɓa, ko ki aika masa idan ɗan malam ya zo karɓar nasa" Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar jakarta. "Yayanmu na tafi" Ya ɗaga kai ya kalle ta, ya yi shiru bai amsa ba. Ta ɗan tsaya cak tana kallonsa, ta sake cewa "Yaya na tafi" "Sai kin dawo" Ya furta a taƙaice, jiki a sanyaye, Alina ta fita. Sai ta ji gaba ɗaya duniyar ta yi mata babu daɗi, ganin fushi da damuwa ƙarara a fuskar Yayanta. ***** Rahama na zaune a class ɗin su, kasancewar lokacin prep ne, tana zaune tana karanta wani littafi, da yake ƙunshe da yadda turawan mulkin mallaka suka mamayi Afrika, da sace musu wasu daga kayan tarihinsu, da kuma mallke musu kadarorinsu. Kawai ta din ga jin zafin abubuwan da suka gudanaz saboda yadda ta yi zurfi a karatun gani take kamar a gabanta abin ya faru. "A Yelwa" da sauri ta ɗaga kai. Prefect ɗin da ta kira sunanta ta ce "Ki je ofishin pc ana neman ki" "Tom" Ta amsa tana tattare litattafanta tana zuba wa a cikin jakarta, ta yinƙura ta tashi ta fita. Hannunta na cikin hijjabinta tana tafiya a hankali. Muryar Baffa ta jiyo, su na magana da principal ɗin su. Da sauri ta ƙarasa cikin ofishin. Murmushinta ya gaza ɓoyuwa. Ta gaisa da Principal sannan Baffa ya fito suka keɓe. "Baffa na zata ba za ka zo ba, hankalina a tashe na fara tunanin ko wani abin ne ya faru a gida" Jikin Baffa a sanyaye ya girgiza kai ya ce "Babu abin da ya faru, sai dai tsoron faruwar tasa ne ya sanya na kasa zuwa ko ina." Rahama cikin kaɗuwa ta ce "Baffa mene ne?" "Ramata dama akwai wata alaƙa a tsakanin ki da yaran manoma ban sani ba?" Ras gaban Ramata ya faɗi, ta hau tambayar kanta, ya aka yi Baffa ya sani, duk ɓoye-ɓoyen da take yi. "Kin yi shiru Ramata, ke yanzu ba kya duba mana halin da muke ciki ko? Sai kin janyo ke kaɗai ɗin da ki ka rage mini, kema na rasa ki ko wata fitinar ta tashi ko?" Ramata ta yi ajiyar zuciya, ta gyara zamanta ta ɗan kalli Baffa ta sunkuyar da kai ta ce "Baffa abin da ka faɗa ba ƙarya ba ne, Bukar ya daɗe yana bibiyata tun ƙawancen da nake yi da Hanne. Sai dai na saki jiki na ba shi dama ne, ba domin komai ba, sai dan na san wacece wadda ake zargin Ironmu a kanta, na tattara hujjar da zan bi hakkinsa" Ta ƙarasa maganar tana kallon Baffa. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ramata yaushe ki ka koyi baƙin taurin kai haka? Ni da nake ubansa na haƙura na fauwwala wa Allah, ke da ba ke ki ka haifar mini shi ba, ki dage sai kin ɗauki mataki, a gurin wa za ki ɗauki matakin? Ramata kar ki ɓata mini rai , ki yi abin da za ki janyo mana tashin hankali, ba zan iya kirga iya tashin hankali da barazanar da na gani a rayuwata a zamana a garin nan ba, yakamata na huta haka" Rahama ta yi shiru tana goge hawaye, saboda yadda komai yake dawo mata tun daga cikin kwanyarta har zuwa cikin idanunta. Baffa ya koma yi mata nasiha, ya bata abin da ya riƙo mata ya tashi ya tafi. Gudun kar hankalin malamansu ya dawo kanta, a zo ana tambayarta lafiya, ko su zata kukan tafiyar Baffa take yi, su yi mata faɗa, dan haka ta goge hawayenta ta tashi ta tafi. Sai dai da aka tashi daga prep, ta kai kayan kwanarsu ta ajiye, ta tafi keɓanttacen guri ta zauna tana tunani. Tabbas tana son bin jinin ɗan uwanta, amma ta fuskanci yanayin shari'a a ƙasar nan ka na buƙatar ilimi, kuɗi da kuma hanya, idan ba haka ba wahalar banza za ka yi ta sha, idan ba Allah ya tarfawa garinka nono ba. Mussaman ita da ga ƙarancin shekaru kuma ba ta da tabbacin samun cikakken haɗin kan mutanen garin, kowa cewa zai yi babu ruwansa saboda tsoron manoma da ake ji a garin. ***** Yana riƙe da leda a hannunsa, yana ƙoƙarin shiga layin, ya ga daidaita sahu na ƙoƙarin fitowa, da Alina a ciki a kwance a jikin Nadiya. Da sauri ya tare a daidaita sahun ya riƙe ƙarfen yana kallon Nadiya ya ce "Lafiya kuwa?" Nadiya ta ce "Alina ce babu lafiya za mu je Asibiti" A ɗan rikice ya ce "Subhanallah, Asibiti kuma meya same ta" Cikin basarwa Nadiya ta ce "Tana da ciwon kai mai tsanani ne, mai Napep mu je, kar ta ci gaba da galabaita" Mai baburin ya ja suka tafi. Mamman ya tsaya yana bin adaidaita sahun da kallo, da tunanin ina yayanta za su tafi Asibiti sukaɗai? Kuma kwanaki uku kan ya yi balaguron da ya yi, lafiyarta ƙalau. Wayarsa ya ɗaukko mai madannai, ya daddana, sannan ya ƙarasa shagonsa ya shiga. Ya gama abin da zai yi ya fito ya zauna a bakin hanya, ko zai ga dawowarsu, amma bai gani ba, dan ya yi mamaki a yadda yake da Alina, babu yadda za a yi ya yi magana ba ta ɗago ba. Wata maƙwabciyarsu, da take jikin gidansu Alina, ya gani ta fito daga layin, ta riƙo kwando da kwanukan Abinci. Ya tashi ya ƙarasa, suka gaisa. Ya ce "Dan Allah Asibiti za ki jegurin su Alina?" Ta ce "Eh zan kai musu Abinci ne" Cikin damuwa ya ce "Subhanallah, wane Asibitin ne?" "Bright ne, a can suke kwanciya idan ba su da lafiya" "Dan Allah kar ki ce na dame ki, dama tana yawan rashin lafiya ne?" Maman Hanan ta ce "Gaskiya dai dan kwana biyu ma Alina ta yi lafiya, amma tana da yawan rashin lafiya" Ya jinjina kai ya ce "Shikenan na gode sosai" Alina na kwance a kan gadon Asibiti, Idanunta a lumshe, ɗakin an kashe fitila, saboda ba ta son haske, idan ciwon kan ya tayar mata. "'Yar ƙwalisa"  Ya kira ta a hankali. A hankali ta motsa ta buɗe idanunta a saboda hasken fitilarsa da ya haske mata fuska. Sai dai idonta ya yi ja sosai. "Sannu" Ya furta yana ƙasa da muryarsa. Ta mayar da idanunta ta lumshe, ta ce "Ina ka tafi babu sallama, nake ta neman ka?" Ta yi maganar cike da kasala da rashin ƙwarin jiki. "Na je gida ne, kin san Innata ba ta da cikakkiyar lafiya ita ma." Ta jinjina masa kai kawai. Cikin tausasawa ya ce "Me yake yi miki ciwo ne?" Ta ɗaga hannunta a hankali, ta nuna masa kanta. Kawai ta ga ya saka hannu yana share mata gumin da yake tsatstsafowa a goshinta. Ta buɗe idanunta tana kallon fuskarsa ta hasken fitilar wayarsa. Ji ta yi zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri, har numfashinta ya fara fita da sauri. Idanunsa da suke ba ta tsoro ya tsare ta da su. Ga kusancin da yake tsakaninsu, wani irin ƙamshi jikinsa yake fitarwa mai kwantar da hankali. Hakan ya ƙara sanya mata kasala da wasi-wasi. "Yaya Mamman" Bai amsa ba sai kallonta da yake yi. "Ƙamshin turare ka ke da ƙaurin wani abu, kamar... Sai kuma ta yi shiru." Ya ɗan ja dogon hancinsa, ya basar, ya ce "Tashi zaune ki ci abin da na kawo miki" Kafin ta yinƙura ya riga ta ya ɗaga ta zaune. "Wayyo Allah kaina, ka yi mini a hankali mana, zai rabe biyu" Ta yi maganar muryarta na rawa. Ya jinginar da ita, sai dai gaba ɗaya a tsorace take, idan ban da Yaya babu wani namiji da ya taɓa gangancin kai hannunsa jikinta, ko da kuwa samun kusanci da ita ne. Bayan rashin ƙwarin jiki da take fama, wani irin yanayi take ji a jikinta da ya ƙara kashe mata jiki fiye da da. Ya janyo ledar da ya zo da ita, ya fito da yoghurt, ya fito da fruit, ya ce "Wanne za ki ci?" Tsura masa ido ta yi, tana tsoron kar wani ya shigo ya gan su a haka, saboda yadda yake zaune daf da ita, gaba ɗaya a tsorace take. Ta zuba wa wuyansa ido, idan ba gizo idanunta suke yi mata ba, sarƙa ce a wuyansa, sai dai ba ta fitowa sosai, tana cikin rigarsa, tana son ta yi magana amma ta kasa. Ya ci gaba da bin ta da kallo, da mamakin abun da yake gani a tare da ita. Ya buɗe robar yoghurt ɗin ya ce "Na baki a baki ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. Laɓɓansa take kallo a hankali, kamar yau an canzo shi gaba ɗaya. Idan su na magana bai fiye son su din ga haɗa ido ba, kuma yana ƙoƙarin kiyaye duk wani abu da zai sanya ko hannunta ya taɓa, ko zama ta yi yana nesa da ita, amma yau kamar zai rungume ta. Ba haka ba hatta muryarsa tamkar an canza ta. Muryar ta ƙara buɗewa, kuma babu alamun wasa a cikin muryar tasa. Babu tsammanni su ka ji an buɗe ƙofar ɗakin gaba ɗaya. AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. Ayshercool 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA... Ayshercool YOTA/002 P9 Aka kunna fitilar ɗakin, da sauri Alina ta rufe idanunta, saboda ba ta son haske idan tana wannan ciwon kan. Nurse ce ta ƙaraso tana turo trolley. Ta ce "Yi haƙuri Alina, zan ba ki magani ne" Ta gaida Mamman ya amsa, ya sake duban Alina ya ce "Kar ɓi ki sha kafin ta baki maganin" Ta girgiza kai ba tare da ta ɗago kanta ba, ta ce "Ina Anty ta tafi?" Nurse ɗin ta ce "Ta je sayo miki magani, ba a samunsa a nan haka" Ya sake tausasa muryarsa ya ce "'yar ƙwalisa daure ki sha ko kaɗan ne" Ya yi maganar yana ajiye mata a kan cinyarta. Idanunta a rufe ta fara laluben cokalin dan ta sha. Ya ɗebo ya kai bakinta. A hankali take karɓa, amma idonta a rufe. Kaɗan ta sha ta ce ta ƙoshi amai take ji, ba za ta iya ci gaba da sha ba. Nurse ta kama hannunta, ta buɗe cannula ta fara yi mata allura. Alina ta kawar da kanta gefe ta rintse idonta, saboda yadda ba ta son allura. Ya fakaici idonta, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro sirinji, ya kalli Nurse ɗin da idonsa, ta koma gefe ya kama hannun Alina, cire sirinjin da ta saka mata, ya saka wanda ya ciro a aljihunsa ya fara yi mata. A gigice ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai dai ba ta yi magana ba, jikinta ya saki ta fara bacci, a hankali ya gama zuba ruwan allurar a jikinta, sannan ya gyara mata kwanciyarta, ya kalli Nurse ɗin ya ɗaga mata babban yatsansa alamar jinjina. Sannan ya yi mata alama da ta tafi. Ta juya da trolley ɗin ta fice. Ya ciro babbar waya a aljihunsa, ya ɗauki hotunan Alina. Ya kwashe sauran kayan ya fice ya bar ɗakin da sauri. Ba a yi mintuna goma da fitarsa ba, Nadiya ta shigo ɗakin, ta ƙarasa gaban gadon Alina tana faɗin. "Fatima, haryanzu ba ki tashi ba?" Ta yi maganar tana dafa goshin Alina. Ta ajiye magungunan da ta sayo, sannan ta ciro wayarta da ke ta ringing. "Hello masoyi" "Na'am ya jikin nata?" "Jiki Alhamdillah, tana ta bacci, ka san ƙa'ida sai ta yi kwana biyu tana fama" "Na kusa shigowa garin ai nan da awa biyu in sha Allah" "Wai dawowa zaka yi da gaske? Aikin fa" Ismail ya ce "Kin san hankalina ba zai kwanta ba, ba na son ciwon kan nan da take yi, na kusa shigowa in sha Allah. Kin samu magungunan kuwa?" "Eh na samo su, amma da kyar aka bani su, wai ba a sayar da su barkatai" "To Alhamdillah, da ta tashi a bata ta sha, kuma su yi mata duk abin da yakamata, su tattara mini bills ina dawowa zan bayar, dan bana tunanin akwai isassun kuɗi a file ɗinmu" Nadiya ta jinjina kai tana faɗin "Ai ka san ko babu ko sisi, za su yi mana duk abin da yakamata, sai ka ƙaraso" Ya amsa da "To shikenan" Ya katse wayar. ***** Tun da Baffa ya zo, Rahama ta rasa nutsuwarta gaba ɗaya, kanta har wani ciwo yake yi mata. Tabbas babban dalilin da ya sanya ta karɓi soyayyar Bukar, amfani da shi ne ta gano haƙiƙanin wace ce wadda aka tozarta mata ɗan uwa saboda ita. Amma daga baya ta fahimci kamar shi ma bai san wace ce ba, sai dai kyawawan ɗabi'unsa ya sanya ta saki jiki da shi, har take jin ta fara sonsa. Ta sake tuna maganganun da Saleh ya gaya mata. Ji ta yi tana son ta haɗu da Hanne ko ta halin ƙaƙa. Litattafan da suke gabanta ma, sai ta ture su a gefe, ta nemi guri ta kwanta saboda ba ta jin dadin komai. Sai dai tana ɗarsa batun son Bukar a zuciyarta, sai mutumin nan ya bujiro mata, ya mamaye ko ina. ***** Mariya na zaune tana goge uniform ɗin ta na Islamiyya. Mama ta dube ta ta ce "Mariya, dan Allah idan kin je, ki ba wa malam haƙuri, in sha Allah a satin nan za ki kai kuɗin makarantar ya ƙara haƙuri" "Tom zan gaya masa in sha Allah" Hafsa ta shigo ɗakin da sallama tana cire hijjabinta. Mama ta amsa ta dube ta ta ce "Yaya?" "Na fita kenan Yaya ya kira ni, ya sako mini dubu uku, ya ce mu yi haƙuri mu lallaɓa, ya je wa Naja visiting shekaranjiya ba kuɗi a hannunsa" Mama ta ce "Hafsa ba dai gaya masa ki ka yi cewa bamu da komai a gidan ba?" "Haba Mama kema kin san ba zan gaya masa ba. Dama ba son zuwa gurin Kawu Babballen nan nake yi ba, da an taɓa shi shi ma cewa zai yi ba shi da shi, mu je yaya ya bamu" Mariya ta ce "Ya ma haɗa ka da masifa ma" Mama ta ce "Allah sarki yaron kirki, Ubangiji Allah ya tsare mana shi, ya yi masa jagora. Allah dai ya saka masa da alkhairi. Mariya kan ki tafi makarantar nan karɓo mana gari kowa ya sha, mu cancana kuɗin" "To Mama" Haka ta ci gaba da yi musu addu'a da fatan, Allah ya haɗa mata kan su. Miƙa ya ɗan yi, idanunsa jawur saboda gajiya, ya cire bindigarsa ya ajiye yana duba wayarsa. "Haris yane? Ka zo mu je cin abinci, rana ta yi fa" "Oga Suleiman ka je kawai, bacci nake ji ne" "Kai Haris, bacci a yanzu, shikenan bari na je" Haris yana jin yadda cikinsa yake ƙugi, saboda yunwar da yake ji, amma ya rage kayan jikinsa ya nemi guri ya kwanta. ***** Alina ce ta yi shiru tana tunanin da gaske Mamman ya zo, ko kuwa mafarki ta yi? Cikin kulawa Yaya yake ta jera mata sannu cike da kulawa. Ta jinjina masa kai, tana ƙara riƙe hannunsa a cikin nata. "Sannu Alinan Yaya, Ubangiji Allah ya yaye miki wannan ciwon kai, ya yi miki maganinsa" Suka amsa da Amin. "To yanzu ya ki ke ji?" Ta ɗan yi shiru ta ce "Kan ya daina ciwo, ni yanzu mu tafi gida kawai" Ta yi maganar da sigar magiya. Ismail ya ce "A'a ki yi haƙuri ya ƙara sakinki tukuna" Ta kwaɓe fuska ta ce "Yaya gobe in Allah ya kaimu Asabar, idan ba a ji karatuna ba, makina zai iya yin ƙasa a cire ni daga cikin yan sauka" Nadiya ta ce "Alina ai larura tana gaban komai, ki bari dai mu gani" Ta shagwaɓe tana yi musu magiya. Ismail ya ce "Ina ganin hakan za a yi, tun da haka take so. Bari na je na ji nawa ku ka ci" Nadiya ta ce "To shikenan" Ya fito reception, suka gaggaisa da ma'aikatan, kasancewar sun san shi sosai, patient ɗin su ne, mussaman saboda yawan rashin lafiyar Alina. Ya ce "Hajiya duba mini file ɗinmu, nawa ku ke bi na, nawa Alina ta ci?" Aka ciro file, ya sake cewa "Ina ga wancan karon bai fi dubu uku ce ta yi saura a file ɗin ba" Matar ta ɗaukko file ta duba, ta kalli Ismail ta ce "Ai ba a binku ko sisi, kun biya" Ismail ya ce "Hajiya ya idon ne? Duba dubu uku ce a cikin file ɗin, sun kawo Alina kwanansu biyu yau. Ki ga nawa suka ci na saka muku yanzu" Ya yi maganar yana daddana wayar hannunsa. "Da gaske fa nake, an biya har da canjin dubu talatin a file ɗin." Ya kalle ta, ya ja file ɗin gabansa ya fara dubawa. Shekaranjiya ranar da aka kai Alina Asibiti aka saka kuɗi dubu saba'in a file ɗin, kuma da sunansa a saka. Ya yi shiru. Ya kira Nadiya a waya, ya ce ta zo reception. Ba a jima ba sai ga ta ta iso. "Masoyiyya, waye ya biya kuɗin Asibitin Alina?" Nadiya ta ce "A'a ba a biya ba" Ya ce "To zo ki ga" Ta ƙarasa ta kalli file ɗin, ta ce "Gaskiya ba su biya ba" Aka kira wayar wanda ya yi duty ranar, ya ce ta POS kawai ya ga transfer, ya ga sunan Isma'il a jiki, da narration, dan haka ya yi setting bills ɗin. Ismail ya yi shiru yana tunani, bai sake cewa komai ba, ya ce Nadiya ta haɗa kayanta su tafi. ***** Babbar mace ce, za ta shekara Arba'in da uku, ta sha kwalliya, ta fito katafaren falonta, ta yi turus ta ɗan tsaya tana kallonsa. "Baba Mai Kano saukar yaushe?" "Ko na koma ne?" Ya yi maganar yana ɗan kallonta. Ta gyara zaman gilashin fuskarta, ta ce "Wane mutum inji mutuwa, barka da sauka" Bai amsa ba ya nufi fridge, ya buɗe ya ɗauko coc mai sanyi, ya ɗauki glass cup, a saman fridge ɗin, ya zuba ya sha. Ya dawo falo ya zauna. Ya dube ta ya ce "To kina lafiya?" "Mmm ba gani kana gani ba, Alhamdillah na godewa Allah" "Ya jikinki fa?" Ta yi murmushi ta ce "Alhamdillah" "Allah abin godiya. Amm na ce duk takardunki masu muhimmanci su na nan a ajiye inda na sansu ko?" "Eh me za a yi?" Ya miƙe tsaye ya ce "Abu nake nema" Ta dube shi ta ce "Me za ka yi ne?" ya yi gaba cikin hanzari ba tare da ya ce komai ba. "Mai Kano me za ka yi ne wai? Kai ba ka zo gurin mutum ba, a yi ta maka magana ka mayar da mutum iska, ba za ka amsa ba" Ya shige bedroom ɗin ta, wardrobe ya buɗe, ya din ga duddubawa ya ciro wata takarda, ya din ga kallon takardar a tsanake, daga bisani ya tashi ya mayar da wardrobe ɗin, ya fito falon ya tarar da ita a zaune, da remote a hannunta, tana canza tasha. "Sai anjima" Ya furta yana nufar hanyar fita. "Ina fatan baka hargitse mini ɗaki ba?" "Ki saka a gyara miki" Ya yi waje da sauri. BAYAN KWANA HUƊU. Tun daga nesa ya zuba mata ido, har ta shigo cikin kantin nasa. Guri ta samu ta tsaya tana hararsa. "'Yar ƙwalisa, ya aka yi ne, ya jikin?" Ta murguɗa baki ta yi shiru. Ya fito daga cikin kantin, ya zauna a gefenta a kan bencin da yake ciki. "Me na yi miki ne?" "Sau ɗaya ka zo duba ni, baka sake nema na ba?" Ta yi maganar tana tura baki. Ya yi murmushi ya ce "Ki yi haƙuri, tsoron yayanki nake ji, kin san ba ya son alaƙata da ke, amma kina raina na damu sosai da sosai, kamar na cire miki ciwon". "Ba wani nan" Ta yi maganar tana zumɓura baki. "Da gaske nake 'yan matan Yaya" Ta ɗan ɗago ta saci kallonsa, ya kashe mata ido, kawai ta hau dariya. Shi ma ya yi dariyar. Ya ce "Kin rame sosai, me yake saka miki ciwon kai haka?" Ta gyaɗa kai ta ce "Nima ban sani ba, tun ina ƙarama, wani Likita dai ya ce Magrine headache sunan shi. Ka san ranar da ka zo duba ni ɗin nan, bayan ka tafi... Ya katse ta da cewa "Waye ya zo duba kin?" "Kai mana, lokacin da ina Asibiti fa" Ya girgiza kai ya ce "A'a ban zo ba" Ta yi saroro ta ce "Ka zo mana, na manta kalar kayan da ka saka, amma ka manta ka zo. Har ka kawo mini yoghurt" "Ta yaya zan zo bayan yayanki yana yi mini kashedi a kanki" Cikin mamaki Alina ta kalle shi, ta ɗan dafa kanta ta ce "To mafarki na yi kenan? Har ka ɗaga ni zaune fa, lokacin Antynmu ta je sayo mini magani" Ya ce "Anya kin gama warkewa kuwa, ko dai a koma Asibitin nan? Gaskiya mafarki ne, yanzu me zan ɗaukko miki da za ki ci?" Ta girgiza kai ta kasa cewa komai, saboda mamakin da ya cika ta. Ta tashi tsaye ta ce "Ni ba na son cin komai, ga wannan" Ta yi maganar tana ba shi leda. Ya saka hannu ya karɓa yana faɗin "Me na samu?" Ya buɗe ledar ya fito da abin da yake ciki. Hankici ta saƙa mai kyan gaske, ta saƙa shi fari da ja, ta rubuta Ɗan albarka, sai kuma hular sanyi ita ma ta rubuta ɗan albarka a jiki. Sai uban ƙamshi suke yi. Sosai yake murmushi, ya ɗago ya kalle ta, ya tsare ta da idnaunsa, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "'Yar ƙwalisa, wannan duk nawa ne?" Ta ce "Eh, ka din ga canza hula, tun da na ga kullum da hula ka ke zama, ko ka na da sanƙo ne?" Ta yi maganar tana dariya. Kawai ya yi wata 'yar gajeriyar dariya, jin abin da ta faɗa. Ya cire hular kansa, kansa cike da suma ya ce "Ba ni da sanƙo, ina dai saka hular ne ina rufe kaina" "Eh na gani ka bani gyaɗa zan koma gida na yi bacci, magungunan nan bacci suke saka ni, duk su kashe mini jiki" Ya miƙe ya ɗaukko bokitin gyaɗar ya ce "Ɗauki iya wadda za ta ishe ki" Ta ɗauki ƙulli biyu ta ce "Wannan ta isa" Ya kalli kantin, ya dube ta ya ce "Sai kuma me zan baki?" Ta girgiza kai ta ce "Wannan ta ishe ni" "Kai 'yan matan, na rasa me zan ce miki ne ma gaba ɗaya, amma na gode sosai da sosai Lina, Thank you in ji turawa. Nima yakamata ki din ga koya mini turancin nan" Ta ce "To shikenan, zan din ga koya maka, amma ka daina wannan godiyar ta yi yawa. Ai ba zan biya ka ɗawainiyar da ka ke yi da ni ba" Ya saki murmushi ga ta yarinya sai manyance, da iya tsara magana. Ya ɗan lumshe idanunsa, yana nazartar fuskarta. "Ke ki ke ɗawainiya da ni ai, ki bani abinci, ki taya ni hira, ga kyauta kin bani, kuma... Sai kuma ya yi shiru. Ta ɗaga kai suka haɗa ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. "Sai ka ce na baka wata duniya, ai ba yawa,na gode nima" Ta fice daga kantin, tana tafiya a hankali. Ya zura mata ido, har ta ɓacewa ganinsa. ***** "Sadauki" "Allah ya taimaki Madugu" "An gama saita komai?" "Na gama Madugu, umarninka kawai muke jira" "To ku jira ni daga yanzu zuwa kowane lokaci, ku saurare ni, ina jiran a gama gyara mana hanya ne, saboda ba a son kuskure a aikin, sama ta ka zamu kai mamayar" Sadauki ya ce "Allah ya bar Kacalla Sumale, kai mu ke saurare" "Good" ***** Sosai ya zuba wa kayan da Alina ta ba shi ido, yana murmushi. Ya din ga jujjuya hular, ta saƙu sosai da sosai, sai ƙamshin turare take yi, ga handkachief ɗin ma ya yi kyau sosai, har beza ta yi masa da wani abu mai ƙyalƙali. Ya kai hancinsa ya shaƙi ƙamshin turaren da suke yi, irin wanda take yi ne. Ya yi murmushin gefen baki, ya haɗe su a guri ɗaya, ya ɗaga ƙasan kayansa ya saka su. ***** YELWA Tarin makiyaya ne maza, dattawa da matasa, su na zazzaune, a kan wata ƙatuwar tabarma, su na tattaunawa. Moddibo da ya kasance shi ne jagora a ɓangren makiyayan garin, ya yi gyaran murya yana magana "To tunatarwa ce dai da muka saba yi duk shekara, yanzu ma ga mu mun zo da ita. Mun san wasu za su dawo da dabbobi gida, wasu kuma za su fita da su. To ga kuma labarai marasa daɗi da muke samu, ga kuma rigimgimun cikin garin nan. Saboda haka nake roƙonku, duk inda za ku je, ku kasance mutanen kirki, duk inda ku ke ku wakilan makiyaya ne, makiyayi kuma ba a san shi da tashin hankali da neman rigima ba. Domin girman Allah ku kula da dabbobi, kar su shiga su yi wa kowa ɓarna. Sannan wanda za a bari a gari, kuma ina roƙon waɗanda za a bari a gida, kowa ya kula da dabbobinsa, kar ya bari su shiga gonar wani su yi ɓarna. Hausawa sun ce; kowa ya kwana lafiya shi ya so. Kun san mutanen nan sun fi ƙarfinmu ta kowacce fuska, tsokanarsu ko neman rigima da su, ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba. Mu na sane da tabon da yake zukatanmu, na cutarwa da suke yi mana, da har abada ba zamu warke ba, dan haka kowa ya kula dan Allah" Duk suka amsa masa da In sha Allah. "Ko akwai mai magana" Baffa ya ɗaga hannu, Modibbo ya ce "Mu na saurarenka Jibo" Baffa ya miƙe ya ce "To 'yan uwana Assalamu alaikum, ni ɗorawa zan yi abin da ka faɗa. Mu na jin yadda al'amuran rikicin manoma da makiyaya ke komawa wani abu daban. Duk ma'abocin jin radio, ko wanda yake shiga birni, na san yana da labarin hakan. Saboda haka nake sake roƙonmu mu ƙara kulawa sosai, dan kamar jira suke yi wani abin ya haɗo mu ma su far mana. Sannan duk wani abu da muka gani baƙo da bamu yarda da shi ba, mu sanar da junanmu... Ɗan uwan Baffa  ya ce "Dan Allah Modibbo, idan an gama taron nan mu tafi, ya tashi sai iyayi yake yi mana. Koma mene ne ba ɗanka ne yaje ya tsokane su ba, ya ƙara tayar mana da tsohuwar gabar nan ba, da bai je inda 'yarsu take ba, ai da abin bai ƙara tsauri ba." Wani a gefe ya ce "Gaskiya ne, yo mutumin da bai iya kula da gidansa ba, ya ɗauki yarsa ya kai wata uwa duniya ne, zai wani tashi yana mana surutu da sunan shawara?" Sai jikin Baffa ya yi sanyi. Maddibo ya tsuke fuska ya ce "Jatau, Iro meye haka? Iro da aka kashe mana, ai ba Jibo kawai aka yi wa ba, mu aka yi wa. Kisan gillar da aka yi masa zuriyar makiyaya aka yi wa. Kuma ba domin mu na son zaman lafiya ba sai mun bi kadin jinin iro. Batun kai Ramata birni wannan abu ne da shi ya shafa. Mu na jinka Jibo ci gaba da magana" Baffa ya girgiza kai, fuskarsa ɗauke da murmushin ƙarfin hali, ya ce "Ahh dama shikenan maganar tawa, na gode" Ya nemi guri ya zauna yana yaƙe. **** "Vice" "Ranka ya daɗe" Ya yi taku biyu da sanda a hannunsa, ya nemi guri ya zauna, ya ɗaga idanunsa, ya saka a cikin na kan Kangiwa. "Na san ka san faɗin tashin da muka yi, muka kawo ku kan mulki ko?" "Na sani Allah ya baka yawan rai" "Masu iya magana sun ce, ɗan halal baya manta alkhairi, sai dai farawa da bismillah, Kankiya yana ƙoƙarin nuna mana, an tura motar zai bule mu da hayaƙi, ba tare da sanin direban da yake tuƙin motar namu ne ba. Tun da ya nuna zai mana butulci, ba zai yi mana biyayya ba, zamu yi masa yaren da zai gane. Idan ka amince ka bamu haɗin kai ɗari bisa ɗari, zamu mayar da shi fanko, ka jagoranci ƙasar, zuwa lokacin zaɓe mu hankaɗe shi, kai mu ɗora ka." Cikin mamaki yake kallon Makama, murya na ɗan rawa ya ce "Ta yaya hakan zai faru ranka ya daɗe?" "Wannan aikinmu ne, kai dai ka zama mai biyayya kawai, idan ba haka ba daga kai har shi, zaku rasa zamu nemo wanda za mu tsayar, dan ba za ku yi tazarce ba, dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan ka shirya ka amince, zamu hargitse ƙasar kai kuma ka ji da sauran... Ayshercool 08081012143 AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 P10 AYSHERCOOL Kangiwa ya yi shiru yana lissafa maganganun a cikin zuciyarsa. Ya jinjina kai a hankali ya ce "Shikenan, zan je na yi shawara" "Ina saurarenka" Kangiwa ya tashi sumi-sumi ya fice. Ya zuba lemo a kofin gabansa, ya ɗago kofin ya kai bakinsa yana zuƙa a hankali, yana jujjuya lemon a kofin yana kallon katafariyar talabijin din da ke cikin ɗakin. Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗauke ta a gefensa, ya kalli lambar bai santa ba, ya dai ɗaga ya kai kunnensa ya yi shiru bai yi magana ba. Jin an yi shiru ya sanya shi cewa "Waye a kan layi?" "Kacalla Sumale" Da sauri ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Yaya ake ciki ne? Mu na ta nemanka a waya ba mu samu ba, kai fa muke jira" "Ba na gaggawa a aikina, yaƙin sunƙuru ka ce a yi, dan haka kar ka shigar mini aiki." Cikin mamaki mutumin ya buɗe baki, jin yadda baƙauyen ɗan ta'adda yake yi masa magana gatse-gatse. "Ba zan ci gaba da ƙaddamar da hari ko ta ina ba, nima aikina lissafi nake yi. Na kira ka ne na jaddada maka na kuma ja maka kunne, kar ka kuskura ka saɓa yarjejeniyar mu. Kuma ka ce za ka kula da ɓangaren kwaɗin nan, idan aka kashe mini mutane, ko aka kama wani zan yi fyaɗar 'ya'yan kaɗanya ne, har iyakar da bai kamata ba sai na ci. Kuma wannan kwantiragin, ko a mutu ko a yi rai ne, ka tabattar ka kula da ɓangarenka. Idan da wani abu, ko kana nema na, ka tuntuɓi Sadauki... Ƙit ya kashe wayarsa. ***** "Masoyiyya" Ismail ya kira Nadiya. "Masoyi" "Jikina yana bani wani abu" Cikin rashin fahimta ta ce "Wani abu me kenan?" "Haryanzu ina mamakin wanda ya biya kuɗin Asibitin Alina kuma da sunana, wannan ya tabattar mini da akwai wani abu a ƙasa" Nadiya ta ajiye ninkin kayan da take yi, ta dube shi ta ce "Nima dai abin ya ɗaure mini kai, sai dai bana tunanin akwai wanda zai din ga bibiyarmu, saboda me ma to za a bibiye mu, ni nafi tunanin ko mistake aka samu" Ya yi dariya ya ce "Mistake? Ba kuskure ba ne, wani abu ake ƙoƙarin gaya mini da hakan. Ina tunanin Alina na yin sauka, zamu bar garin nan, shi ma dan na ga yadda ta ƙallaffa ranta a kan saukar Alqur'anin ne. Kawai ina jin akwai matsala zamanmu a nan" Nadiya ta ce "Amma duk shekarun da muka yi, ba a samu matsala ba, sai a wannan karon? Ina zamu koma?" Ya ce "Alina, Saboda Alina dole mu bar garin nan, da daga ni sai ke ne, babu inda za mu je, tun da bamu takawa kowa ba, ba kuma mu zubarwa kowa ba a garin nan. Amma ba na son duk wani abu da zai kawowa ƙwaƙwalwarta cikas, kin san me nake nufi ai" Nadiya ta numfasa tare da sauke numfashi. Ya sake numfasawa ya ce "Wai me mutuniyar ta saƙa ne, da ulun da ta addaba mini sai na sayo mata?" "Ina na san mata, ka san idan ta ga dama ta yi saƙar ta sayar, ko ta kyautar. Dan kai ta gado a ungo" Ya yi guntuwar dariya ya ce  "Ta saƙa wa Mamman hula ta ba shi, ya saka ta yaje masallaci da ita. Abin da nake gudu ya faru, amma zan ɗau mataki na ƙarshe a kai" Da sauri Nadiya ta ce "A'a masoyi, kar ka... "Shhhh" Ya katse ta yana zare mata ido, tare da tsuke fuska tamkar bai san yadda ake dariya ba. ***** Daga nesa kaɗan yake tsaye, yana hango ƙofar gidan Malam Ɗayyabu, da rumfar almajiransa aka shimfiɗa tabarmi ake zaman makokin rasuwarsa. Duk wanda yakamata ya tambaya, da binciken da yakmata ya yi, amma babu wani gamsashen dalilin rasuwar malamin, kowa yana faɗin ya kwanta bacci lafiya kalau, aka wayi gari da gawarsa.! Alina ce a tsaye, hannunta riƙe da takalmanta na makaranta, tana tsaye a bakin shagon yana ta sallamar mutane. Ya yi ƙoƙarin sallamarta, amma ta ce masa ya gama tukuna. Kasancewar yamma ce, ana ta zuwa sayayya. "Nifa na gaji da tsayuwa" Ta yi maganar tana tsuke fuska. "To ai ke ki ka ce na sallame su, bari na ƙarasa ranki ya daɗe" Ya sallami kowa, ya fito yana gyara zaman hularsa da ta saƙa masa. Ya saka hannu zai karɓi takalman, ta janye abin ta, ta ɓoye a bayanta. "Meyafaru kuma?" Ya yi maganar yana kallon ta. Ta harare shi, ta kawar da kanta gefe. "Subhanallah me na yi?" "Ka sallami kowa ka ƙi kula ni, kuma kana sallamar su, kana yin murmushi" Ta ƙarasa maganar tana kawar da kanta gefe fuskarta ɗauke da damuwa. Ya yi dariya ya ce "Ni ne nake murmushin? Rigima dai ki ke ji, amma ban da ke kin ga ina yi wa wani murmushi? Ai ba na dariya murmushin ma ke kawai nake yi wa" Ta ɗago kanta suka yi ido huɗu, kawai ta hau dariya, wanda hakan ya sanya shi ma ya yi guntuwar dariyar. "Ɗan albarka" "Na'am 'yar ƙwalisa" "Yaushe za ka cire gashin nan na fuskarka ne? Ina son na ga fuskarka sosai da sosai" Mamman ya shafa fuskarsa ya ce "Yanzu ba kya ganin fuskartawa?" "Eh mana, gashi ya fi yawa, idan ka aske sai ka fi kyau" Ya jinjina kai ya ce "Ai abin da Mumsy take so shi nake so, zan aske ki ganni sosai" Ta kalle shi ta ce "Mumsy, amma dai Mamman ka yi karatun boko?" Ya girgiza kai ya ce "Ai ba sai mutum yaje boko ba zai san wani abin ba, amma bari na din ga ce miki Inna" "Ni wallahi ba Inna ba ce" Ta yi maganar tana dariya. Ya karɓi takalmanta, tana zaune ya goge su ya yi musu mai. Wayarsa ce ta fara ringing, ya ciro wayar ya kalla, ya kalle ta sannan ya ɗaga ya yi sallama. Ba ta san me ake ce masa a wayar ba, ta ɗaga takalminta tana kallo, ta ga ya sauke wayar a hankali, fuskarsa babu walwala. "Ya dai meyafaru? Ko jikin Innar ne?" Ya girgiza kai ya ce "Maƙwabtan ƙauyenmu ne, aka yi rikici da manoma, da maharba, an karkashe mutane" Cikin razana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ubangiji Allah ya taƙaita. Ko za ka je gidan to ka gani?" Jiki a sanyaye ya ce "Sai abin da Allah ya yi" "A'a gara ka je, irin wannan kuskuren Yaya ya yi. Ya ce mu garinmu rikicin manoma da makiyaya ake yi, ba su ɗau abin serious ba, sai da ya yi yawan da muka rasa iyayenmu, kuma aka kori wanda suka rage daga garin. Shi ne su suka taho nan, ya ce mukaɗai muka rage a gidanmu. Kafin mu zo nan a gidan su Antynmu muka zauna, har ya aure ta, ita ma aka yi ta rikici a garinsu, aka kashe musu yan uwa muka taho nan. Duk an ƙarar da danginmu, daga Allah sai yaya muke da shi." Ta yi maganar tana sanya tafukan hannayenta, ta rufe fuskarta tana fashewa da matsanancin kuka. Ya yi shiru yana nazarinta, ya jinjina kai, sannan ya yi ƙasa da muryarsa. "Ki yi haƙuri 'yan mata, bayan yaya, gani kuma, in sha Allah zan kula da ke, idan yaya ya bani cikakkiyar dama, zan ba ki kulawa fiye da yadda ya baki. Amma ban san meyasa ba ya so na ba" Ta share hawayenta ta ce "Ba sonka ne ba ya yi ba, baya son kowa ya raɓe ni ne, saboda baya son ya rasa ni nima. Allah ya taƙaita muku yaya Mamman rashin ahali ba shi da daɗi" "Ki daina kuka, ko ki na son ki saka ni kuka nima? Ki daina" Ta jinjina masa kai. "Ba ki ga hulata ba ne?" Ta yi murmushi ta ce "Na gani, ta yi maka kyau sosai da sosai" Ya tashi tsaye ya ɗaukko biro da takarda, ya yi rubutu a jiki, ya miƙa mata. "Wai a ina ka iya rubutu?" "Koya na yi" Ya ƙarasa maganar yana damƙa mata takardar. Ta buɗe takardar tana kallo, ta ɗaga idonta ta kalle shi, ta ga ya tsare ta da ido. Kawai ta tashi tsaye tana murmushi, ta kwashi takalmanta ta yi waje. Ya bi bayanta da kallo yana murmushi. Sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya tashi ya shiga cikin kantin, ya ɗaukko wata wayar daban, ya danna wasu lambobi, ya saka a kunnensa. A ƙofar gida ta tarar da Yaya a ƙofar gida a tsaye. "Wankin takalmin ne sai yanzu?" Alina ta yi shiru tana sunkuyar da kai. Bai ce mata komai ba, ya yi gaba ya bar ta. ***** Ana ta jarrabawa, saura guda ɗaya a kammala, Rahama na ta shirin gida. Bayan sun dawo daga night pref. Ta je ta yi wanka, ta shafa alamun ɗin ta, ta yi shirin kwanciya bacci. Tana jin Ruƙayya na ce mata, ta taso su ci abincin dare, amma ta ce ta ƙoshi, saboda wani irin bacci da take ji yau. Dogon wandon skin tied ta saka, sai vest doguwa har gwiwa, sai da ta hau kan gadonta, sannan ta cire hijjabinta ta kwanta, kasancewar lokacin yanayin na zafi ne, garin da zafi sosai. Duk da tana jin bacci, ta janyo littafinta a jakarta, ta kunna fitilarta tana haskawa. Tarihin gwagwarmayar karɓar 'yancin take karantawa. Gudunmawar da su Sir Ahmadu bello Dr. Nnamdi Azikiwe Chief obafemi owolowo Sir Abubakar tafawa ɓalewa suka bayar gurin karɓar wa ƙasa 'yancin kai. Yanayin yadda mulki ya fara gudana, a wancan shekarun. Yanayin yadda sir Abubakar tafawa ɓalewa, ya zama priministre  na farko, yadda ya fara gudanar da mulkinsa. Gaba ɗaya ba dukiyar ƙasar ce a gabansu ba, ƙasar suka yi ƙoƙarin ginawa da dukkanin karfinsu. Sai dai kash an yi juyin mulki a alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da shida 1996 a sha biyar ga watan January. Juyin mulkin da wasu tawagar sojoji suka yi, ƙarƙashin jagorancin wani soja Major Chukuma Kaduna Nzeogwu, da wasu sojoji irin su Major Emanuel Ifeajuna. Inda aka je har gida aka tafi da shi. Daga bisani kuma aka tsinci gawarsa an kashe shi. Kisan Sir Abubakar tafawa ɓalewa ya kawo rikici a ƙasar a wancan lokacin. Daga nan General Aguyi-Ironsi ya karɓi mulkin ƙasar. "Kash mtseww" Ruƙayya na daga gadonta na ƙasan Rahama ta ce "Rahma lafiya kuwa?" "History nake karantawa" Rukayya ta yi dariya ta ce "Na zata kin daɗe da yin bacci ai. Ina mamakin abin da ya haɗa ɗalibar kimiyya da karance-karancen tarihi" Rahama ta ce "Anty Ruƙayya zama guri ɗaya tsautsayi in ji kifi, kuma shi karance-karancen na karawa mutum ilimi. Tarihin mazan jiya nake karantawa yadda aka faro kafa ƙasar nan da samar mata 'yanci, da yadda aka fara mulki. Da an bi tafarkin da suka ɗora ƙasar tun da farko, da tuni mun fi haka ci gaba. But so sad an zubar da jini da yawa, an yi wa Sir Abubakar tafawa ɓalewa coup an kashe shi, despite all his efforts. Ba ki ji zuciyata ba" Ta ƙarasa maganar a ɗan shagwaɓe. Rukayya ta saka dariya ta ce "Lallai ma Rahama, ita kanta Duniyar, da ƙasashen da suka kai inda suke yanzu da zubar da jini suka kafa ta. Ki ci gaba da karanta tarihin akwai abin da ya fi wanda aka yi masa ma" Rahama ta yi guntun tsaki ta ce "Ni na karaya ma. To ina sojojin da suke tare da shi, suka bari har aka shiga aka ɗauke shi, aka tafi da shi aka kashe dan Allah?" "Rahama kenan, ba a cin gari ai sai da ɗan gari. Galibin juyin mulki da ake yi, da sanin masu tsaronsu. Da Yaya na nan da kin sha bayani. Babu yadda a aikinsu ko kaɗan. Wataran zan haɗa ki da Yaya Ammar, ki sha labari" Rahama ta ce "Daina bani labarin nan, zuciyata za ta karye da yawa. Sai da safe bari na yi azkar na kwanta" Ta yi maganar tana sauke ajiyar zuciya. Ta lumshe idanunta ta ɗaga hannayenta tana karanto addu'a kwanciya bacci. ***** "Kangiwa, kana ganin yadda al'amura suke neman fin ƙarfinmu a ƙasar nan ko? Dama haka mulkin yake? Wallahi da na san haka yake ba zan yadda na karɓi ƙasar nan ba" Kangiwa ya ce "Haba mr. President kar ka saka mu karaya mana, ka daure mu ga abin da za mu iya yi" "An dabaibaye komai fa, yanzu kalli uban bashin da ake bin ƙasar nan. Trillion ɗari da hamsin da biyu da ɗigo huɗu fa" "Mr. President, ƙasashen da suka ci gaba a duniya, ai duk da basussuka suka gina ƙasashensu" "Amma Kangiwa su ƙasashensu suka gina, mu kuma wasu ne suke gina kansu. Ana maganar billion sau billions ne fa. Me da me aka yi a ƙasar na wannan uban kuɗin haka? Ga uban kuɗin ruwan da ake lafta mana. Yanzu babu ta inda za mu yi kasafin kuɗin shekara mai zuwa fa, babu komai a ƙasar nan, kai shaida ne da muka zo mulkin nan account ɗin ƙasar babu komai sai abin da ba a rasa ba" Kangiwa ya jinjina kai cikin damuwa ya ce "Your excellency, bamu da wata mafita da ta wuce mu ranto kuɗin da zamu yi kasafin kuɗin baɗi" "Kangiwa bashi again?" "Mr. President bamu da wata mafita idan ba wannan ba, harajin da muke samu, ba zai samar mana da wannan kuɗin ba. Ga ɗanyen mai ya faɗi a kasuwar duniya, ga satar mai da ake yi da yake ƙara kassara mu. Ciyo bashin nan ne kawai mafitarmu" Kankiya ya kashingiɗa yana cije lips ɗin sa, ya buɗe idanunsa da kyar ya kalli Kangiwa ya ce "Ina tausayin al'ummata. Amma kafin mu kai ga wannan gaɓar, zan zauna da shugabanin hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa. Dole a matsa tsofaffin wanda suka riƙe madafun iko, a matsa duk wanda aka kama da ha'inci, su dawo mana da dukiyar da suka sata." Kangiwa ya yi murmushi ya ce "Wannan ma dabara ce, bari na je meeting ɗin da ka sanya ni, na ga lokaci ya yi" Kankiya ya ce "To shikenan babu laifi" Kangiwa na baro office ɗin, ya ja ya tsaya, ganin kiran Makama na shigo wayarsa. Ya ɗaga yana faɗin "Ranka ya daɗe" "Ka yi ganawar sirri da Kankiya, me ku ka tattauna?" Kangiwa ya waiwaya bayansa, sannan ya ce "Na naɗi komai zan tura maka yanzu in sha Allah" "Ina saurarenka" ***** Alina zaune a ajinsu ta ajiye Alqur'aninta a gabanta ta zuba masa ido, sai murmushi take yi. Hafsa ta taɓa ta ta ce "Lafiya, murmushin me ki ka yi haka ne? Karatun kuwa ki ke yi?" Alina ta girgiza kai ta ce "Wani abu na tuna" "Yaya Mamman ɗin ne? Alina wai Mamman ɗin nan saurayinki ne? Soyayya ku ke yi? Ke kuwa me za ki yi da mai wankin takalmi, provision store ɗin ma fa ba nasa bane ba" Alina ta ɓata fuska ta ce "Ce miki na yi mu na soyayya ne? Mutunci kawai muke yi" "Kuma shi ne kullum sai kin yi zancensa, ko ya biyo ki Islamiyya ku tafi tare?" "Wai ke Hafsa haka aka ce miki? Babba ne fa ya kusa Yayanmu" Hafsa ta ce "Ke wallahi soyayya ku ke yi, kuma Yaya Ismail ya sani?" Alina ta kwaɓe baki ta ce "Yaya ba ya son alaƙata da shi, amma yana yi mini kirki ne kawai" Hafsa ta addabi Alina a kan lallai sai ta yarda soyayya suke yi da Mamman, amma Alina ta share ta. Ko da aka tashi daga Islamiyya, su na fitowa daga gate ɗin makarantar, suka hango shi a tsaye hannunsa riƙe da wayarsa mai madannai. Hafsa ta taɓo Alina da ke sayen Agwalima, ta ce "Ga saurayinki can ya zo yana jiranki" Alina ta ɗaga kai, ta gano Mamman yana nufo su. Hafsa ta ɗan ja baya, saboda tsoro yake ba ta. "Nawa za a sayar mana da agwalumar nan gaba ɗaya" Ya yi maganar yana kashewa Alina ido. Sai da ta ɗan rikice, tare da kallon Hafsa ko ta ga abin da ya faru. Wani irin sassanyan ƙamshi ne yake tashi daga jikinsa, gaba ɗaya suturar jikinsa ba ta dace da ƙamshin turaren da yake yi ba. Idan ba ta manta ba, lokacin da yaje Asibiti irin wannan ƙamshin yake yi, amma ya ce mata shi ba shi ba ne ba. "Inna mu saya duka ne?" Ya yi maganar yana karɓar ta hannunta da ta riƙe. "Inna ko?" Ta yi maganar tana hararsa. Ya yi murmushi ya ciro ɗari biyar a aljihunsa, ya miƙa wa mai agwaluma ya ce ya zuba mata ta 500. "Ta ɗari biyar ai ta yi mini yawa, ta ɗari zai bani, kuma guda biyu manya" Mamman ya ce "A ɗari za a baki biyu manya, ga wannan ƙara mata" Ya ƙara ciro ɗari biyar ya ba shi. Ta ɗaga kai za ta yi masa magana, amma ya harare ta, aka cika mata baƙar leda da Agwaluma suka tafi. Hafsa kamar ta bi Alina da gudu ta shaƙe ta, ta tsaya jiranta, ita kuma ta yi tafiyarta ta bar ta. Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro leda ya ce "Ungo" Ta saka hannu ta karɓa ta ce "Na waye?" "Nawa ne" Ya yi maganar yana basarwa. Alina ta ce "Yi haƙuri, nawa ne?" "Mmm babu yawa" "Na gode sosai da sosai Ɗan albarka, amma dan Allah ka daina kashe kuɗinka haka, ka ga... "Kin raina kyautar almajiri ko?" Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ba haka ba ne, na gode sosai da sosai" Har ƙofar gida ya raka ta, sannan ya juya ya tafi shago. Ko da ta shiga gida, ta tarar da Nadiya kamar ita take jira ta ce "Kin dawo? Dama ke nake jira" Alina ta ajiye kayan hannunta, ta ce "Meyafaru?" "Leda za ki karɓo mini, da zan ƙulla tuwo. Sai da na gama tuƙawa na duba na ga bani da ita. Meye wannan a hannunki?" Alina ta miƙa mata ledar tana faɗi. "Mamman ne ya saya mini agwaluma, sai kuma wannan ledar, da nake son ganin mene ne a ciki". Ta ƙarasa maganar tana zaro turare a cikin kwalinsa. Ta ce "Wow kin ji ƙamshinsa" Nadiya ta karɓi turaren, tana jujjuya shi tana kallon Alina. Ta ce "Amma kuwa ya yi ƙamshi sosai, je ki ki karɓo mini ledar" Alina ta karɓi kuɗin ta sake fita. Ismail ya fito daga ɗaki ya ce "Yanzu kin yadda da abin da nake gaya miki ko?" Nadiya ta jinjina kai, jikinta a sanyaye. "Jibi in Allah ya kaimu, huɗun Asuba za mu bar garin nan,kar ki gaya mata ma, ba zan jira ta yi saukar ba ma" Nadiya ta jinjina masa kai. Tana jujjuya turare. Wani matashi Alina ta hango a cikin shagon a tsaye, zai yi Mamman a tsaye, har ƙirar jikinsu iri ɗaya, sai dai ba ta taɓa ganinsa ba sai yau. Ba ta damu da shi ba, ta shiga ta tsaya, sai dai ta ji ta a takure saboda mutumin. Mamman ya ce "Na zo ne?" Ta girgiza kai ta ce "A'a leda baƙa ƙanana ta saka tuwo zaka bani" Ya ce "Waye ya yi tuwon, ke ko Antynmu?" "Anty ce, Yayanmu ya ce nata ya fi daɗi, ni jagwalgwalo nake yi" "Ni kuma naki ya fi daɗi a bakina. Ya ki ka ga kyautar tawa, ta burge ki?" Alina ta jinjina kai tana murmushi, ta karɓi ledar, ta miƙa masa kuɗi, ya ƙi karɓar kuɗin. Na cikin kantin na ta son ya kalle ta, amma ta juya masa baya ta fita. Tana fita ya tuntsure da dariya ya ce "Allah wadaran naka ya yi expire" Mamman ya tsuke fuska ya ce "Fita ka bar gurin nan ka tafi dan Allah" "Ba zan tafi ba, ji wata riga a wuyanka kamar korarre, saboda tsabar mutuwa har ta fara gari za ta koma audugarta" Ya yi maganar yana ƙyaƙyata dariya" Mamman ya ce "Dalla malam ware, dan Allah ka tafi" "Kai wallahi ba zan tafi yanzu ba. Kai tsaya wai kai ne ka ke kashewa yarinya murya haka kana mata wani kallon iskanci anya kuwa kai ne?" Mamman ya ja guntun tsaki ya ce "Bari kawai, sai shashashanci nake da yarinyar da na haife ta ko? Ni kaina kamar na yi wa kaina shegen duka" "Ka haife ta a ina? Gyambo sarkin girma?" Mamman ya yi tsaki ya ce "Za ka wuce ka je ka shirya abin da ya dace, ko kuma zaka ci gaba da rashin mutuncin ne?" Da kyar yake ƙoƙarin controlling ɗin dariyar da yake yi, ya ce "Na ji. Amma sace yarinyar za a yi kenan?" "Ina tunanin haka, sai dai yadda plan ya kasance. Ka ga a zahiri babu alamun kuɗin nan a tattare da su. Amma dai na tabattar da duk abin da yakamata na tabattar. Matashin ya jinjina kai ya ce "Daren yau ko na gobe za mu ƙaddamar da aikin?" Mamman ya fito ya ce "Mu je hanya mu ƙarasa" "Amma yarinyar nan fa, kamar sonka take yi fa. Kai amma tun da aka haife ni ban taɓa ganin abin da ya bani dariya kamar yau ba. Madakin maza a cikin tsummokara yana kashewa yarinya murya Allah ya isan maza" Ashariya Mamman ya ɗura masa yana hankaɗa shi waje, amma ya maƙale yana ƙyaƙyata dariya. ***** Duk da nisan da baccinta ya yi, amma haka kurum ta kasa jin daɗin baccin. Banda miyagun mafarkai marasa daɗi babu abin da take yi. Wata irin hayaniya mai razanarwa ta din ga ji a saman kanta, ta kasa tantance wace irin hayaniya ce haka, kuma ta kasa farkawa daga mummunan mafarkin da take yi. Sautin murya kawai take ji ana ƙwala mata kira "Rahama!Rahama!" Kamar daga sama ta ji an danƙota an yo ƙasa da ita daga kan gadon. Sai a lokacin ta buɗe idanunta, ta din ga jin guje-guje da iface-iface a zahiri. Hostel ɗinsu ya hargitse, sai kururuwar 'yan mata kawai ake iya ji. Tozali ta yi da wani gabjejen ƙato, sanye da kaya ya rufe fuskarsa da rawani, ga uwar bindiga a hannunsa. Ta ɗaga kai ta ga ba shikaɗai ba ne ba a cikin hostel ɗin nasu akwai wasu ma. Su na ta tarkata kan ɗaliban tamkar dabbobi. Daga ita sai shigar jikinta, ƙafafuwanta babu ko takalmi haka ya fige ta kamar abin banza kasancewar ba ta da jiki, ya yi waje da ita. Ƙarar sautin harbe-harben da ya fara tashi, ya ƙara rikita Ramata, ta gigice gaba ɗaya, sai dai ta kasa yarda da cewar ido biyu ne wannan abin yake faruwa, ta saka a ranta mafarki ne da haryanzu ba ta farka ba. ***** Fafur Hafsa ta ƙi kula Alina, cikin damuwa Alina ta ce "Dan Allah Hafsa ki yi haƙuri, wallahi na zata kin tafi ne" "Eh mana tun da an saya miki agwaluma, ana kallonki ana kashe miki ido kin makance" "A'a ban makance ba" Hafsa ta ce "Wallahi kin makance da ƙauna" Shugaban makarantar ne ya shigo ajin nasu a ɗan rikice yana faɗin "Subhankallauma wa bi hamdik, ashhadu alla ila ha illa Allah, Astagfiruka wa a tubu ilaik. Maza kowa ya tashi ya tafi gida, kar wanda ya tsaya wasa ko ya tsaya a wani gurin" Cikin rashin fahimta ɗaliban suka mimmiƙe, su na mamakin mene ne dalilin tashinsu a daidai wannan lokacin, da bai kamata a tashe su ɗin ba. Su na fitowa harabar makarantar, suka tarar da 'yan sauran azuzuwa su na fitowa, su na fita dan haka su ma suka fita. Yanayin yadda mutane ke ta kaiwa su na komowa, ya nuna akwai matsala. Kowane dalibi ya kama hanyar gida, ga babu wuta, Hafsa suka yi sallama da Alina ta tafi gida. Nadiya ce take kallon Yaya ta ce "Masoyi fita za ka yi?" "Alina zan je na ɗaukko daga makaranta, hankalina ba zai kwanta ba" "Amma da ka kira waya makarantar, ina tsoro" Bai ma tsaya sake tanka mata ba, ya yi waje yana sassarfa. Tun da Alina ta doso layinsu, ta ga wasu irin zabga-zabgan ƙarta na kaiwa su na komowa. Jikinta ya yi sanyi ƙalau, ta bi ta wani lungu ta zagaya ta baya ta shiga layin nasu. Security light ɗin da ke ƙofar gidan Malam Sadi, ta haske sashi mafi yawa na layin. Ga wata mota sienna a tsaye a cikin layin nasu, an yi parking ɗin ta. Daga inda take tsaye take kallon ikon Allah, Yaya ne ya fito daga cikin gida, ya yi turus bayan ganin ƙarti a tsatstsaye a layin, wasu na facing ƙofar gidan sa. A aljihunsa ya zura hannu, amma cikin zafin nama wani ya haska masa wani abu mai kama da bindiga, take ya durƙusa a kan ƙafafuwansa yana karkarwa. Mamman ta gani ya zare tsummar rigar jikinsa, daga shi sai wata baƙar shirt da dogon wando. Ashe wannan tsummokaran ne suke ƙara ɓoye girmansa. Ƙara ƙura ido take yi, domin tabattar da shi ɗin ne ko wani daban? Ya ƙarasa gaban Ismail ya sunkuya daidai fuskarsa, yana yi masa magana, daga inda take tsaye ba ta iya jin me yake ce masa. "Ka ga inda wasan ya kawo mu ko?" Ismail ya yi murmushi ya ce "Gaskiya ne, sai dai ba zai ƙare a nan ba, yanzu za a fara, kai kuma ka zuba ido ka ga inda zamu ƙarƙare. Ka saka a ranka yanzu ne aka buɗe shafin farko. Jikin Alina wata irin rawa yake yi, ƙafafuwanta suka yi sanyi, jikinta ya jiƙe sharkaf da gumi. Abdallah ya miƙa wa Ammar hannu, ya miƙo masa igiya, ya banƙare Ismail ya yi masa wata allura a dokin wuyansa, a take jikinsa ya saki. Ya yi masa wani irin ɗauri tamkar zai karya shi. Ya saɓa shi ya jefa a bayan mota ya zagaya ya shiga motar aka ja motar suka bar layin. 1K NE A TELEGRAM VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC. MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN. Ayshercool 08081012143 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN. SARA DA SASSAƘA... YOTA/002 AYSHERCOOL Page 11 Aƙalla ta kai mintuna goma sha biyar a tsaye, ta kasa gaba ta kasa baya, fatanta da addurata Allah ya sanya bacci take yi, kuma duk abin nan da yake gudana mafarki ne ba gaskiya ba. Da kyar ta iya jan ƙafafuwanta ta shiga gida, tana jin yadda gumi yake ratsa ta ta ko ta ina. A tsakar gida ta tarar da Anty Nadiya, cikin yanayi na damuwa. Ta ce "Alina, ina Yayan?" Alina ta girgiza kai ba tare da iya yin magana ba. "To ai ke ya tafi ɗaukkowa daga makarantar fa, an ce gari babu lafiya, ba ki haɗu da shi a hanya ba?" Girgiza kai ta yi alamar a'a. Nadiya ta ce "wataƙila saɓani ku ka yi, maybe yanzu zai dawo. Ga abincinki can, shi kuma wancan mutumin na aika masa abinci baya nan, idan ya dawo daga yawon ya zo ya aiko ya karɓa". Har Nadiya ta gama surutanta Alina bata tofa komai ba. Ta shiga ɗakinta jikinta a matuƙar sanyaye. Ta ajiye jakarta tana kallon tagar ɗakinta, ta din ga tuhumar kanta a kan dalilin da ya hana ta yi ihu, ko ta fito ta nuna wa Mamman ta gan shi. Ta sake yin shiru tana tunani tsawon wannan lokacin dama Mamman basaja yake yi? To mene ne dalilinsa na yin haka? Me Yayanta ya yi masa? Garkuwa ya yi da shi kenan, ko kuwa me hakan yake nufi? Ta zauna ta yi shiru tana ta tufka da warwara tana tunanin me za ta gaya wa Nadiya, duk abin da ya faru ita ce sila, kasnatuwar babu irin gargaɗai da jan kunnen da Yaya bai yi mata ba. Ba ta san ta yi zurfi kuma ta daɗe tana tunani ba sai da ta ji Nadiya ta ce "Alina, kin ga har sha ɗaya da rabi yayanki shiru. Ko tunaninsa ba ki dawo ba ne?" Alina ta ɗaga kai ta kalle ta. Amma ta yi shiru ba ta ce uffan ba. Nadiya ta koma ɗakinta, ta ɗauki wayarta, ta hau kiran wayar Yaya, sai dai shiru bai ɗaga wayar ba, ta yi missed call ya fi biyar shiru, amma shiru babu amsa. Ta sauke wayar a hankali ta yi shiru, tana nazari. Tana sauke wayar Alina ta shigo ɗakin, ta ajiye wayar. Ta kalli yadda jikin Alina ya yi sanyi ta ce "Ba za ki ci abincin ba?" Ta jinjina mata kai. "To zo ki kwanta dare ya fara yi" Alina ta nemi guri ta kwanta ta takure jikinta. Nadiya ta kashe musu fitila. "Anty "Na'am" "To kwana za mu yi Yayan bai dawo ba?" "Zai dawo yana nan lafiya in sha Allah, wataƙila ogansa ne ya neme shi da gaggawa" Alina ba ta sake magana ba, kawai ta tuna lokacin da ta shigar wa Mamman ɗaki, cikin zafin nama ya ɗora pillow a kan wani abu da idan ba gizo Idanunta suka yi mata ba, tamkar bindiga ta gani, amma ta yi iya ƙoƙarinta gurin kawar da wannan tunanin a wannan lokacin. Ta sake tuna lokacin da ya je Asibiti, ita dai ta san tabbas ba gizo ba ne ba, zahiri ne abin ya faru, amma ya ce shi bai je ba. Kasancewar bacci ɓarawo ne, ba ta san lokacin da ya zo ya yi awon gaba da ita ba. ***** Dare ya tsala, yayin da al'umma ke kwance su na hutawa, su Ramata na dokar daji su na tafiya, babu suturar kirki, wasu ƙafafuwansu babu takalma. Zaratan maza ɗauke da muggan makamai sun saka su a tsakiya. Wasu na gaba a kan babura, wasu na a bayansu, wasu kuma na biye da su a ƙafa, ɗauke da makamai masu ban tsoro. Rahama ba za ta iya ƙididdige adadin yawansu ba, tafiya suke ƙarƙshin hasken farin wata kawai. Ko ƙwaƙwƙwaran tari babu wadda take iya yi, saboda barazanar da mutanen suke yi musu. Rahama za ta iya cewa, bayan mutuwar Iro, wannan shi ne tashin hankali na biyu da ta gani a rayuwarta. Ta kalli jikinta ta kalli suturar da take jikinta, da za ta iya cewa banbancinta kaɗan da tsirara. Sai dai gara ta ta shigar da ta wasu. Tana jin yadda ƙayoyi ke huda mata ƙafa da abin da ma ba ta san mene ne ba, amma ta kasa cewa uffan. Ba za ta iya tantance adadin nisan tafiyar da suka yi ba, domin tuni ta ji ƙafafuwanta na neman bijirewa ɗaukarta saboda wahala da gajiya. Har gari ya waye ya yi tarwai tafiya suke yi tamkar fatake, maƙogwaronta ya bushe kamar zai tsatstsage. Gazawa jikinta ya nemi yi, a dole ta ja ta tsaya, ta yi ruku'u tana mayar da numfashi. "Ke! Uban waye ya ce ki tsaya, tashi ki wuce" Wani daga cikin su ya daka mata tsawa. "Ruwa" Ta furta cikin sassanyar muryarta. "A gidan uban wa ki ka ga ruwa a nan? Za ki tashi ko sai na saka bindiga na harbe ki?" Ko gezau ba ta yi ba, sai a lokacin suka haska fitila, suka lura da yadda ƙafafuwanta suke ta zubar da jini. "Kai ku tsaya a nan. Bari mu kira Sadauki, idan babu matsala a yada zango su huta, duk sun fara galabaita" Ya daddana wayarsa ya saka a kunnensa. "Amanar Kacalla" "Bani labari" "Yaran nan sun galabaita, amma mun wuce mararraba, mu na iya yada zango su huta?" "Eh awa guda kawai, daga haka kar ku sake tsayawa sai kun dangana da inda na ce" "An gama" Yana gama wayar, saƙo ya shigo wayar, kasancewar a lokacin ya kunna wayar. Miƙewa ya yi da sauri bayan karanta saƙon. ***** Ba tare da sanin dalili ba ta farka daga bacci a sukwane, ta tashi zuciyarta sai bugun tara-tara take yi. Ta duba wayarta ta ga ƙarfe uku na dare. Sannu a hankali ta sauka ƙasan bene, ta buɗe ɗakin yaranta mata, ta gan su a kwance kowacce a kan gadonta tana bacci. Ta zagaya ta fita falo, ta buɗe ƙofa ta nufi boys quarter's. Ta tarar da Amir shi ma yana bacci. Sai dai ta ji jikinta ya ci gaba da rawa, ta ɗaukko wayarta ta nemo lambar Ammar, ta hau kiransa. "Hello Ummi" "Me ka ke yi haryanzu ba ka yi bacci ba?" Ya yi dariya ya ce "Hajjaju ni da nake gurin aiki, ai ke zan tambaya meyasa ba ki yi bacci ba" "Dan ubanka ina tambayarka kana tamabayata?" "Ummi aiki nake yi" "To kana ina?" "Mun je wani aiki ne, lafiya dai?" Cikin dakiya take ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce "Kana gida ne, ko kuma sun tura ku dawa?" "Ummi wai lafiya kuwa? Ina lafiya fa wani aiki dai muke yi, ina tare da Mega, mun je aiki ne" "Shikenan Allah ya tsare" Ta katse wayar ta nufi cikin gidan. Sai dai ba ta bari ta koma bacci ba, ta yi alwala ta tayar da salla. ***** "Alina" Nadiya ta kira sunanta. Alina ta ɗago manyan idanunta, ta dubi Nadiya. "Ki daure ki sayo mana buredi a gurin Mamman, ki karya" Ta jinjina kai ta karɓi kuɗin, ta fita. Sai dai kantin a kulle, haka ma shagonsa. Alina ta nemi guri ta zauna ta yi shiru, har sai da ta gaji da zama, sannan ta tashi ta koma gida, ta ce wa Nadiya baya nan. Duk yadda Nadiya ta so mazewa ta kasa, ta fita ta ƙwanƙwasawa maƙwabcinsu, ta sanar masa da halin da ake ciki. Alhaji Sadi ya ce "Amma da mamaki, ni jiya sai bayan na dawo ake ce mini, wai yanayin unguwar kamar babu lafiya, an ga wasu mutane na ta kaiwa su na komowa, ba a san suwaye ba. An kuma sanar da 'yan sanda ba su ce komai ba. Amma bari na tuntuɓi Alhaji Sadi. Ba a jima ba, maƙwabtan da suka rage ba su fita ba duk su ka tattaru. Har su ka fara yi wa Nadiya faɗan, dan meyasa ba ta sanar tun a daren jiya ba. Nan aka fara bin diddigin abin da ya faru. Duk wani bincike da mutanen layin suka yi, babu wani gamsashen bayani, a kan haƙiƙanin abin da ya faru daren jiyan, sai cewar kawai dai an fuskanci yiwuwar samun tashin hankali a lokacin. Suka dangana har ga gurin Jami'an tsaro, sai dai 'yan sanda suka ce, babu wani abu mai kama da tashin hankali da ya faru a unguwar, kawai dai mutanen unguwar sun tayar da hankalinsu ne, amma batun ɓatan Yayan Alina za su duƙufa bincike a kai. Alina kuwa gaba ɗaya a kwana ɗayan nan, ta yi zuru-zuru, tashin hankali ya addabe ta, ta kasa cin abinci kukan ma kuma ta kasa, ga shi ta kasa gaya wa kowa, balle ta samu sassauci. Babbar damuwarta duk ta san laifin nata ne, ita ta ƙanƙame Mamman ta janyo shi kusa da su. Daga ita har Nadiya wunin damuwa suka yi da tashin hankali. Maƙwabta suka din ga shigowa yi musu jaje, tare da fatan Allah ya bayyana Ismail. ***** Ji ya yi an watsa masa ruwa mai zafi a jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi, ya buɗe idanunsa a hankali. Dishi-dishi yake gani. Amma ya tattara nutsuwarsa har sai da ganinsa ya zama clear, sannan ya ɗago kansa a hankali yana ƙarewa gurin kallo. Ya motsa ya ji shi a ɗaure tamau, tamkar huhun goro. Ya sauke idanunsa a cikin na su. "Ka farko kenan?" Ya yi shiru yana ƙare masa kallo ba tare da ya yi magana ba. "Ina fatan zaka sauƙaƙa mana, kuma sauƙaƙa wa kanka, gurin amsa dukkanin abin da zamu tambaye ka, ko mu nema daga gare ka" Ya yi murmushi sannan ya ɗago kansa ya ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya, ya tsayar da kallonsa a kan Mamman,ya ci gaba da kallonsa ba tare da ya yi magana ba. Kawai ya sunkuyar da kai yana murmushi. ***** Su na kitchen su na aikace-aikacen su, suka jiyo saukkowar Ummi daga kan bene, tamkar za ta ruso benen, cikin rige-rige, suka fito daga kitchen ɗin su na jiran jin ba'asin saukkowarta daga bene da gudu haka. "Ummi lafiya kuwa?" "Safiyya, Ruƙayya" "Ruƙayya meyafaru da Rukayyan?" "Wai 'yan bindiga sun shiga har makarantar sun tafi da yaranmu. Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ku taso mini Amir ya ɗaukko mota mu tafi" Na'ima ce ta ƙarasa ta riƙe Ummi, ganin yadda duk ta rikice, ta ce 'Ummi ya za a yi a je makaranta a sace ɗalibai, a ina ki ka taɓa jin an yi haka?" "Ga shi a radiyo ina ji, an sace ɗalibai hamsin a makarantar su Ruƙayya" Safiyya ta ce "Ummi dan zatin Allah ki kwantar da hankalinki, kin san halin da ki ke ciki, ai babu wanda ya tabattar da an sace har da Rukayya ɗalibai sun kusa dubu a makarantar su. Kuma ki bari mu tabattar" "Wane tabattarwa kuma? Radio za su yi ƙarya ne?" "To zauna, bari a taso Amir ɗin" Safiyya ta yi gaba tana kiran wayar Ammar. ***** PRESIDENTIAL RESIDENT Faruk Kankiya ne yake kaiwa yana komowa. Jikinsa har tsuma yake yi. "Your excellency, dan Allah ka kwantar da hankalinka, komai zai zo da sauƙi" Cikin ɗaga murya ya ce "Halilu when? Abubuwa na taɓarɓarewa za a ce komai zai zo ƙarshe ta yaya? A mulkina a shiga har cikin makaranta, a shiga makwancin ɗalibai, a kwashe yara mata 'yan makaranta. Kuma ka ce na kwantar da hankalina how? How Halilu? Gaya mini kaf tarihin duniya a inda aka taɓa haka. Sai a zamanin mulkina. Ko yaƙi ake yi ba a taɓa mata da ƙanan yara. Amma ni matan aka kaiwa farmaki. A mulkina wannan wane irin baƙin tarihi ne?" Halilu ya yi shiru yana sunkuyar da kai, cike da tsoro da razani. "Nan da mintuna talatin, a tattara masu riƙe da muƙaman tsaro a ƙasar nan, idan ba za su iya ba, su ajiye mini aikina" Halilu ya jinjina kai ya fita yana jin tamkar ya ƙwato daga bakin kura da kyar. **** Taimama suka din ga yi su na kallon duk inda ta kama su yi salla. Tsananin baƙin ciki da damuwa ya sanya Rahama kasa zub da hawaye. Wanda suke da shigar kirki a cikin su kaɗan ne, ga su a zube a dokar daji a gaban mutanen da ba muharramansu ba. "Anya ba daga rayuwata ba ne babu sa'a?" Ramata ta kalli kanta, tana ƙanƙame jikinta, zuciyarta na wani irin zafi. 'yan yaran cikinsu da basu wuce Jss 1 ba su na ta 'yan koke-koke ƙasa-ƙasa. "Yaya Baffa zai ji, idan ya samu labarin an sace ni?" Ta sunkuyar da kanta tana jin wata irin fargaba na ratsa ta. **** Shiru ta yi tana kallon wayar hannunta, ta rasa abin da ma yake yi mata daɗi. Cikin sauri ta janyo ɗaya wayartata, ta shiga shafinta na sada zumunta ta wallafa dogon rubutu. Duk da iya ƙoƙarin da gwamanti take yi gurin kawo ci gaban ilimi, mussaman a yankinmu da ilimin yake da yake fuskantar koma baya, mussaman ga 'ya'ya mata, hare-haren ta'addanci ya fara yawa, wanda hakan yana nuna gagarumin koma baya ga yankin. #Bring back our girls". Daga haka ta yi posting ta ajiye wayar. Sadam ne ya fito daga ɗakinsa yana faɗin "Ke Laila, kina ina? Yau kin yarda gwamantin taku ta gaza ko? Saboda abin kunya da Allah wadai, an je har cikin makaranta an sace ɗalibai, mummunan abu na farko a tarihin ƙasar nan, da ya faru a gwamantinku" "Kai kuma murna ka ke yi da hakan kenan? Gwamnati fa ba ta mutum ɗaya ba ce, ta al'umma ce kuma kowane ɓangare yana da wakili... Saddam ya ce "Ba wani gwamanatinku ta gaza kawai malama, yanzu zan hau na wallafa rubutu a facebook na yi tagging ɗinki kuma an yi abin kunya" Mama ce ta ja tsaki, bayan ta idar da sallar walha da kyar, saboda surutunsu, da musun da suke ta , sai rafkanuwa take yi. Kofin silva ta jefawa Sadam ta hau shi da faɗa. "Wallahi Mama na fuskanci kema yar adawa ce, duk lokacin da muke maganar siyasa da yarinyar nan sai ki goya mata baya, ki din ga kora ta. Da alama ke ma tana shaƙa miki tsari ne, aishikenan na bar muku gidan ma amma dai gwamantinku ta gaza Yasin" Mama ta kalle ta ta ce "Kar ki kula shi, ƙyale shi tun da bai san ƙaddara ba" ***** Sanye suke da uniform su huɗu a office ɗin, sai kuma ƙarami da babban ministan tsaro, sai kuma President Faruk Kankiya. "Wannan tattaunawar da muka yi, ta zamo ta sirri, bana buƙatar manema labarai su ma san me muka tattauna. Kwanaki bakwai kawai na baku, ku nemo inda ɗaliban nan suke a dawo da su, kuma bana buƙatar ko ƙwarzane ya samu ɗaliba ɗaya. A yi ƙoƙari a tabattar da lafiyar wanda ba a ɗauka ba, a damƙa su a hannun iyayensu. Kwanaki bakwai kawai na baku. Akasin haka za ku ajiye mini muƙamai na na bawa wasu". General Jalal ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Mr. President tabbas wannan kuskurenmu ne, zan iya cewa sakacinmu ne ma da har wannan al'amari ya faru. Amma mu na mai baka tabbacin da yardar Allah, yaran nan za su kuɓuta. Amma muna neman alfarmarka mako guda ya yi kaɗan... A fusace ya ce "7days Lieutenant General Jalal, 7days kawai ku ke da shi, akasin haka ku ajiye mini muƙamaina" "Ok sir" Haka suka tashi sumi-sumi suka fice daga ofishin. Su na fita Barwa ya ciro wayarsa ya daddana. Ya kara a kunnensa. "Jagora barka da wannan lokaci" "Barkanmu dai Barwa, bamu labari" "Shugaba fa ya ɗauki zafi ba kaɗan ba, kwana bakwai kawai ya bayar a nemo yaran nan, ko su ajiye masa muƙamansa ciki har da ni" Ya kwashe da dariya ya ce "Ƙaryar banza ce ƙiba a kunne, shi ya isa ma? Zan yi magana da Boss Ɓagwai, tun da shi ne God father ɗinsa, dole ya janye wannan maganar. Kana ganin yadda muka fara raba kan ƙasar ko? To ba a yi komai ba ma. Sai ya tattara hankalinsa a kan yaran can, za mu sake ɓallo masa ruwa, kai dai ku ci gaba da bin abin da aka tsara. Ka kwantar da hankalinka yara dai ba za su fito yanzu ba, ka zuba ido... ***** Tuni labarin sace ɗaliban makaranta mata, kimanin hamsin ya cika gidajen rediyo da kafafen watsa labarai da na sada zumunta na ciki da wajen ƙasa. Duk inda ka buɗe babu abin da ake yi sai maganar, saboda abu ne da bai taɓa faruwa ba a tarihi. Sai da su Rahama suka kwana guda curr, babu ko ruwa a cikin su, a kwana na biyu, aka bi su da ruwa ɗaya mutum biyu, sai buredi mai yanka-yanka kowa guda biyu. Ƙafafuwan Rahama suka kumbura sosai saboda azabar tafiyar ƙafa da suka yi. Inda suke daji ne sosai da sosai, sai dai saboda tsabar surƙuƙinsa ko rana ta take, bata wadatar dajin da wadattacen haske saboda tarin dogwayen bishiyu. **** Alina ta yi wata irin mummunar rama, ta yi zuru-zuru saboda azabar tsoro da kuma tashin hankali. Tun safe Nadiya ta fita ta koma gurin jami'an tsaro, domin jin ko akwai wani labari. Alina na zaune ta yi zuru a tsakar gida, ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar gidan su. Jiki a sanyaye ta sanya hula a kanta, ba tare da ta tambayi waye ba, ta buɗe ƙofar gidan. Turus ta yi bayan tozali da fuskar Mamman, kawai ta hau bin fuskarsa da kallo. Fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "'yan mata, abin da ya faru kenan? Na je gida duba jikin Innata, na dawo Alhaji yake gaya mini an nemi Yaya Ismail an rasa" Tsuruu ta yi da ido tana kallonsa, ta ma rasa me za ta ce masa gaba ɗaya. "Ya na ga kina kallona a haka?" Ta sunkuyar da kanta, sai a lokacin hawayen da ta gaza zubarwa ta samu damar zubar da su, zuciyarta na wani irin ƙuna da tafasa. Cikin tausasa murya ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah za a gan shi, an je gurin 'yan sanda an sanar musu?" Ta jinjina masa kai kawai. "Ki yi haƙuri dan Allah, ki daina kukan nan haka" Ta ɗaga fuskarta a hankali tana kallon idanunsa masu bata tsoro, a yau ta samu kallonsu da cikakken ƙwarin gwiwa, amma ta gaza furta komai. Sai dai da ta ƙara matsawa kanta ta fuskanci akwai wata ɓoyayyiyar fuska a bayan wannan fuskar da yake mu'amalantarta da ita... Ayshercool 08081012143 1k ne a telegram 0069685771 Aisha Adam stanbic https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 AYSHERCOOL Page 12 Turus ya ja ya tsaya cikin tashin hankali, bayan da ya kunna wayarsa ya ci karo da batun sace ɗalibai da aka yi. Cikin sauri ya kira wayar Ummi. Sai dai wayar ba ta shiga. Cikin tashin hankali ya lalubi wayar Amir, sai dai ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Cikin hargowa Ammar ya fara yi masa faɗa "Wani irin iskanci ne zan din ga kiran wayarka ka ƙi ɗagawa?" Amir ya ce "Ba ƙin ɗagawa na yi ba wayar na mota... "Dalla ina Ummi take? Me yake faruwa ne?" "Abin da ka ke son tabattarwa ya faru, an shiga makarantar su Ruƙayya an yi garkuwa da ɗalibai hamsin, amma Alhamdillah luckily she's not among, mun je ɗaukko ta ni da Baba Sani, sai dai tana cikin tashin hankali sosai da sosai" Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya nemi guri ya zauna yana faɗin "Amir, ka tabatta tana lafiya babu abin da ya same ta?" "Eh lafiyarta ƙalau, sai dai a tsorace take ne kawai" "Shikenan take care, zan sake kira in sha Allah " ya kashe wayar yana hamdala. Wayar ce ta fara vibrating, kira yana shigowa. Ammar ya ɗaga wayar ya saka a kunnensa. "Yaya ake ciki?" Ammar ya numfasa ya ce "She's safe, ba ta cikin wanda aka sace" Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Alhamdillah" "Wai komawar ka sake yi da gaske?" "Eh, ai ban gama ba, alamu sun nuna akwai sauran rina a kaba" Ammar ya ja guntun tsaki ya ce "Ka na da matsala Mega, wannan ɗin ma da aka yi, ba wani appreciation na kirki, ana ma doubting idan mai laifin ka kama. Ka kuma koma, ban san me ya mayar da kai ba kuma" "Ba aikinsu kawai na koma yi ba, wannan aikina ne, ina son gyara ɓarnar da na yi" Ammar ya ce "Kuma sun san da hakan? Sun san ka koma?" "A'a. Akwai abin da nake bibiya ne, and ban bayar da wayarsa ba, tana hannuna ina son za mu yi aiki a kanta" Ammar ya ce "Good, keep it safe kar ka kuskura ka damƙa musu ita tukuna, ka fara tsayawa mu ga iya gudun ruwansu" Mega ya ce "Kai na san abin da nake yi fa, idan na kammala abin da nake yi, idan na tabattar babu sauran wani abu, zan dawo soon in sha Allah" "Anyway yadda ake ciki, ka yi mini magana. Take care" "Shikenan" Ya katse wayar. ***** Yana zaune a ƙarƙashin bishiya, yana shan sigari, gefensa wasu manyan matasa ne su huɗu. Riƙe da manyan bindigogi su na kaiwa su na komowa. Ya ciro ƙaramar wayarsa ya duba saƙon da ya shigo. "Da alama dara ta ci gida, 'yan maza sun shiga hannu" A sukwane ya miƙe tsaye yana sake karanta saƙon. Da sauri ya fita ya sake danna lambar amma shiru. Cikin sauri ya buɗe bayan wayar, ya zaro layukan da ke cikin wayar, ya kakkarya su, ya watsar ya cillawa ɗaya daga cikin matasan da ke tsaye a kansa wayar ya ce "Ka jajjage ta yanzun nan, mu bar gurin nan dawa ta ɓaci" Nan da nan suka je inda suka ajiye baburansu ƙirar boxers, suka hau suka bar gurin. ***** Dattijo ne da shekaru sun ja, duk da hutu da jin daɗin da ake ciki, amma yanayin tsufa ya bayyana a tattare da shi, yake zaune a kan kujera 3 seater. President Faruk Kankiya na kan kujerar da ke facing ɗin dattijon cikin girmamawa. Dattijon ya ce "Mu na mai jajanta maka, gami da takaicin abin da ya faru a mulkinka, na sace ɗalibai 'yan makaranta. Amma ina mai tausarka da baka shawara ka bi komai a nutse sannu a hankali, kar ka yi garaje ko gaggawa ko kaɗan, idan ba haka ba lissafi zai ƙwace maka. Batun bawa rundunar tsaro kwanaki bakwai su dawo da yara ba abu ne da zai yiwu ba. Kai ba jami'in tsaro bane ba Faruku, ka ba su dama su yi aikinsu domin ceto yaran nan cikin sauƙi ba tare da an yi asarar rai ba. Duk da a rahotannin da muke samu an kashe masu tsaron yaran, da yarinya guda ɗaya, amma ba ma fatan a sake rasa rai. Batun za ka sauke shugabanin tsaro ba shi ne mafita ba. Kamar yadda ka ke faɗa aiwatarwa ne naka, yiyuwar lamari na Allah ne. To su ma hakan ne, ka ba su dama, ka toshe kunnuwanka da surutu da tashin hankalin mutane za su ruɗuka ne kawai. Sai kuma ka je ƙafa da ƙafa makarantar, ka ga halin da makarantar ke ciki ka kuma jajantawa iyayen yaran da ba su ƙwarin gwiwa, ka nuna yaran nan da aka sace naka ne" Jiki a sanyaye Kankiya ya ce "Na fahimce ka ranka ya daɗe, na kuma gode sosai da sosai da wannan shawarwarin da ake bani, atleast na samu releif na kuma fahimci kuskuren da na so tafkawa. Na gode sosai da sosai " "Good, a yi ta haƙuri da yardar Allah komai zai daidaita" Ya jinjina kai ya tashi suka yi musabaha da dattijon ya fice. ***** Jikin Mama ne yake karakarwa, tamkar mai shirin hawa bori. Hafsa da Mariya sun yi mata ƙuri da ido, su na jiran su ji me za ta ce, bayan ta sauke wayar daga kunnenta. Hafsa ta ce "Mama mene ne? Me aka ce miki?" Da kyar ta iya ƙwato "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta miƙe tsaye ta fizgo mayafinta a kan gado" Mariya ta ce "Mama kin ƙi yi mana magana, kuma jikinki sai rawa yake yi me aka gaya miki ne?" "Mariya Naja, Naja'atu an ce ba a ganta a cikin sauran ɗaliban ba, shiyasa dama na ce da ku bari na je a duba" Hafsa ta ce "A'a Mama, ko kin je babu abun da zai canza, yanzu ina za ki je?" "Gurin su Babballe zan je na sanar musu" Mariya ta ce "Mama babu abin da za su tsinana mana, dama ki rabu da su" "A'a ku jira ni ni dai na je na gaya musu" Ta nufi hanyar fita, sai dai ta ji jikinta ya yi mata nauyi, da kyar take ɗaga ƙafafuwanta. YELWA Can garin su Ramata, tuni labari ya cika garin an sace ɗaliban makarantar su Rahama. Cikin matsanancin tashin hankali Baffa ya tafi makarantar ,domin duba waɗanda ba a sace ba, ko da Rahama a ciki, sai dai cikin ɗaliban kaf babu Ramata. Jikinsa na tsuma ya fito ya samu wata baranda ya nemi guri ya zauna yana nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Shugaban makarantar ne, ya nufo Baffa jikinsa a sanyaye ya ƙaraso gefensa ya zauna. Ya dafa kafaɗarsa cikin ƙoƙarin kwantar masa da hankali, ya ce "Ka yi haƙuri, Malam Bashir mu ɗauki wannan al'amarin a matsayin ƙaddara. Mu kuma yi addu'a. Gwamnati ta bamu tabbacin yaran nan za su dawo cikin aminci. Da yardar Allah za su dawo gare mu" Baffa ya numfasa ya ce "Na yi imani da ƙaddara, na sani ko a gida hakan za ta iya faruwa. Ni tunanina ɗaya Ubangiji Allah ya tsare mana su, ka sani ni ita kaɗai ce da ni yanzu" Ya ƙarasa maganar cikin rawar murya. "Ka yi haƙuri, mu ci gaba da yi musu addu'a, in sha Allah za su kuɓuta cikin aminci" Har da jami'an tsaro aka haɗu a ka din ga tausar Baban Ramata, duk da akwai sauran iyaye da aka sace wa yara. Amma duk wanda ya ga yanayin mahaifin Rahama dole ya tausaya masa. Idanunsa da farar fatarsa ta yi jawur, jijiyoyi duk su ka fito raɗa-raɗa a goshinsa saboda tashin hankali. Har tasha wani jami'in tsaro ya kai shi aka saka shi a mota, ya nufi Yelwa. ***** Tun da Isma'il ya yi ɓatan dabo, kwana na biyar kenan, mutane na ta shigowa yi wa su Alina jaje, tare da fatan Allah ya bayyana shi. Sai dai haryanzu abin da yake ɗaure mata kai, bai wuce yadda Mamman ya nuna damuwarsa a kan ɓatan Yayanta ba. Ga shi tamkar ya yi mata asiri, ta kasa gaya wa kowa abin da ya faru. Yau ma da ya aika yaro ta zo, Nadiya ba ta ce komai ba, dan a ganinta, zuwansa na ɗan ragewa Alina damuwar da take ciki. Tun da ta fito ya tsare ta da ido, amma ta sunkuyar da kanta ƙasa. "Ya nuna mata gefensa kan barandar gidan, ta nemi guri ta zauna. "'yar ƙwalisa, kin ga ramar da ki ka yi kuwa?" Ya yi maganar daki-daki. Ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba. "Alina, wannan yanayin da ki ka shiga, ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ki yi haƙuri ki kwnatar da hankalinki. In sha Allah duk inda yake zai bayyana, amma wannan damuwar ba ta kamace ki ba. Tsananta addu'a yakamata mu yi a wannan gaɓar" Ta yi shiru ta kawar da kanta gefe guda. "Alina" Ya kira sunanta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalli cikin idanunsa. A take abin da ya faru ya fara dawo mata, kuma tana da yaƙinin shi ta gani ba wani ba. Tun da Isma'il ya ɓace sai a lokacin hawaye ya samu zubowa daga idanunta. Cikin sanyin jiki ya ce "Alina kar ki yi kuka dan Allah. Ki yi haƙuri" Tamkar ya ziga ta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta tashi da sauri ta shige gida ta bar shi a gurin a zaune. ***** YELWA Duk da yadda 'yan uwan Baffa ke jin haushinsa, na ƙin aurar da Ramata ya kai ta makarantar boko, sun shiga tashin hankali da labari ya fara bazuwa cewar an shiga makarantar su Ramata an saci ɗalibai. Ko da ya tafi dubawa ko har da Ramata a ka ɗauka, bai gaya wa kowa ba sai Juma. Ita kuwa yana tafiya ta je ta gaya wa su Maddibo. Aikuwa hankalin kowa ya tashi. Mussaman 'yan uwan mahaifiyar Ramata da babu yadda ba su yi ba, ya yi mata aure amma ya ƙi. Sai bayan la'asar sosai sannan ya dawo gida. Aikuwa ya tarar da gidan a cike da mutane. Su na ganinsa suka yi kansa da tambayoyi a kan ina Ramata. Jiki a sanyaye ya samawa kansa gurin zama. "Kai Jibo, ina yarinya take ka dawo kai kaɗai?" Modibbo ya yi maganar cikin zaƙuwa. "Ramata na cikin yaran da aka yi garkuwa da su" Ya ba su amsa kai tsaye, dan bai ga amfanin ɓoye-ɓoyen ba. Salati suka saka gaba ɗaya. Cike da takaici Sambo ya ce "Ka gani ko? Babu irin abin da bamu gaya maka ba, game da kai yarinyar nan can wata uwa duniya da sunan boko, ga shi yanzu ka salwantar da rayuwarta a banza. Ita kaɗai dama ta rage maka, yanzu ga abin da ka janyo" Maddibo ya ce "Ya isa haka, Ramata dai 'yarmu ce, yanzu tayar da jijiyoyin wuya da hayaniya ba namu bane ba, iyaka kawai mu riƙe addu'a Ubangiji Allah ya bayyana ta".. Baffa ya kwashi takaici da miyagun maganganu a gurin 'yan uwansa, duk da halin da yake ciki. Yana ji yana gani, abinci ya gagare shi, salla sai ya sallame sau biyu, saboda rafkanuwa. Ya zauna ya ja uban tagumi, ya ji sallamar ɗan gidan Iro Yayansa Amiru, wanda aka so haɗa shi aure da Ramata, Baffa ya dage makaranta za ta yi. Baffa ya amsa masa, ya yi masa iznin shiga. Ya shiga yana sake sallama, Baffa ya yi masa iso, tare da nuna masa kusa da shi ya zauna. Jiki a sanyaye Amiru ya ce "Baffa ashe tsautsayin da ya faru da Ramata kenan?" Baffa ya sauke numfashi ya ce "Wallahi kuwa Amiru, an sace su Ramata. Duk ana ɗora mini laifin faruwar hakan, amma ni uba ne, ba zan taɓa aikata abin da zai cutar da 'yar da na haifa kuma ta kasance itakaɗai ta rage mini ba" Amiru ya ce "Na sani Baffa, kuma na fahimce ka, sai dai mu haɗu mu yi haƙuri, mu yi ta addu'a Allah ya bayyana ta" Amiru ya din ga rarrashin Baffa, sun daɗe tare sannan Amiru ya yi masa sallama ya tafi. Sai dai Baffa bai karaya da lamarin ba, sai da dare ya tsala, ya tuna Ramatansa bai san a inda take ba, bai kuma san a yaya za ta kwana ba. Tsakar gida ya fito, ya tsaya a tsakiyar farin wata, ya sakawa ƙofar ɗakinta ido. Lokacin da ya kai ta makaranta, tare da shugaban makarantar primary ɗin su Rahaman, sai da aka kai shi har ɗakin da aka bata, da gadon da aka bata ya tabattar da tana kauwwame a guri ɗaya, sannan ya amince wanda tsawon shekarun nan, ko ya kaita makarantar wasu lokutan sai ya yi ta damuwa da rashinta a kusa da shi. Balle yau da ba a san ma a inda take ba. Ya ja da baya a hankali ya jingina da jikin danga, sai kuma abubuwa daban-daban suka fara dawowa kansa game da garin, baya tunanin kaf garin YELWA akwai wanda ya haɗu da masifu kala-kala kamarsa. Haka ya wanzu yana tuna abubuwa daban-daban marasa daɗi da suka faru da shi a garin. ***** Tamkar baƙin hadarin damuna, mai ɗauke da iska haka ya murtuke fuska hanunsa riƙe da waya, ya kara ta a kunnensa yana jiran a ɗaga. Yana kwance a kan doguwar kujera yana kallon talabijin, kiran wayar ya cika masa kunne. Kuma wayar da ba kowa kiransa a ita ba, sai mutane na musamman. Ya duba ya ga lamba ce babu suna, ya ɗaga kai kunnensa. Sai dai shiru ba a yi magana ba. "Wa ke magana?" "Sadauki ne" "Waye hakan?" "Idan ma ka gane waye, idan ba ka gane ba, ɗaya daga cikin manyan yaranmu, ya yi ɓatan dabo, bamu san inda yake ba, kuma Kacalla Sumale na matuƙar ji da shi, dan haka ina fatan babu hannunku a cikin kama mana yaro" "To kai ɗan samari, ta yaya ka ke tunanin zan saɓa yarjejeniyarmu ne? Bamu saka an kama kowa ba, hasali ma mu na ta ƙoƙarin ƙara gyara muku hanya ma" Sadauki ya ja ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, ya yi ɓatan dabo ne bamu gan shi ba, mu na kyautata zaton ko kama shi aka yi, amma za mu ci gaba da duddubawa. Yaran nan su na nan a tare da mu, ku sako kuɗin Abincinsu. Sannan duk abin da gwamanati ke ciki a sanar da mu, dan idan rana ta ƙwace tare za ta ƙwace mana" "Ka kwantar da hankalinka, ina da tabbaci a kan shirin da muka yi" "Shikenan" "Yauwwa ɗan samari, za a kawo muku saƙon, zan turo da lambar motar, da inda za ku je ku karɓa" "Yayi" Sadauki ya faɗa a taƙaice ya katse wayar. Dattijon ya yi dariya ya ce "Idan rana ta ƙwace, zata ƙwace mana mu da ku a ina? Yaro bai san wuta ba sai ya taka. ***** Wani irin azababben sanyi ake yi a gurin, Ramata ji take yi tamkar ta fi kowa jin sanyi. Jikinta sai wata irin karkarwa yake yi. Yunwar da take ji, har ta ci ta cinye ta, abin da ake ba su sam baya isar su. Gaba ɗaya hancinta a toshe yake,  da baki take numfashi saboda matsananciyar murar da ta kama ta, bayan tunanin Baffa da ya addabe ta, babu abin da ya dame ta, irin rashin suturar kirki da ke jikinsu, ga ƙarti a kewaye da su. Kumburin da ƙafafuwanta suka yi kuwa, ba su riga sun sace ba, saboda dafin ƙayoyin da ta din ga takawa. Tana zaune ko kwanciya ta kasa yi, ta duƙunƙune jikinta, tana kallonsu a zube a daji kamar dealer gwanjo. Ɗaya daga cikin maharan nasu, da suke tsaronsu, ta lura da yadda yake takura mata da yawan kallo, hakan ya ƙara takura ta, mussaman rashin cikakkiyar sutura da take jikinta. **** Tana zaune a kan gado, tana shan tea, ta kammala ta sauka daga kan gadon ta fita falo, kawai ta tarar da shi a zaune a ƙaton falon, ya miƙe ƙafafuwansa ya jingna da jikin kujera. Kai tsaye ta nufe shi tana faɗin "Mr. President a gida zaka kwana kenan, ai ban san ka shigo ba" Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta zagaya ta zauna a kan kujera ta ce "Bikin 'yar gidan ministan al'adu da za a yi, ina son sabuwar mota gaskiya latest mai kyau. Kalli lace ɗin da zan yi order shi nake son sakawa, 5.5million wannan sarƙar ma direct daga Dubai na sayo ta" Cike da takaici ya ce "Dan girman Allah Fatiyya ki rabu da ni na ji da abin da yake damuna. An sace yaran mutane a makaranta, na rasa ta ina zan fito na taushe su, yaran mutane na inda ba a ma sani ba, kuma duk da matsayinkii a ƙasar nan, ko sau ɗaya ba ki nuna dmauwarki ko kin yi wata magana ta kwantar da hankali ba. A lokacin da ƙasar nan ke fama da rashin kuɗi  durƙushewar tattalin arziki, ga ɗalibai an sace a mulkin mijinki a gaɓar ne ki ke shirin saka kayan miliyan biyar. Ke ko gudun magana ba kya yi?" Fatiyya ta ɓata fuska ta ce "To wai dan Allah mu muka sace su ne? Abin da zai faru ya riga ya faru, Allah ya kuɓutar da su, amma dan an sace yara kuma shikenan ba za mu yi walwala ba?" Ya ƙare mata kallo tsaf ya ce "Anya kuwa ke uwa ce Fatiyya? Kin ga je ki ki bani guri ne, kar ki sake dagula mini lissafi" Kwaɓe baki ta yi ta fice ta bar shi a gurin a zaune. Duk da yadda yake samun masu rarrashinsa a kan abin da ya faru, amma ya takura ƙwarai da matsin lambar da yake fuskanta daga jam'iyyun adawa, ƙasashen ƙetare da uwa uba al'ummar ƙasa da su ka fara Allah wadai da mulkinsa. ***** Laila na zaune ta idar da sallar la'asar, ta yi shiru. Sadam ya shigo da sallama ɗakin ya ɗora da kiran sunanta. "Ke Laila, amma dai da wuri yau za ki ɗora mana girkin dare ko? Dan ni wallahi ba na ganewa taliyar nan ko minti sha biyar ba ta yi a cikina, nake jin wayam ba komai" Sai dai ya ga ta yi shiru bata amsa ba. Ƙarasawa ya yi inda take, ya taɓa kanta, kawai ya ga tana sharɓar kuka wiwi. Cikin mamaki yake kallonta ya ce "Lafiya?" Jin sheshsheƙar kukan nata, ya sanya Mama shigowa da sauri tana tambayar kukan me take yi. Laila ta goge hawayenta cikin ƙunar rai ta ce "Wallahi tunanin 'yan uwana da aka sace nake yi?" Sadam ya ce "Wane 'yan uwan naki aka sace?" "Ɗaliban makarantar nan mana" Ta ba shi amsa tana share hawaye. "Ko a tarihi ban taɓa jin wannan masifar ba, yaya za a yi a ce an sace ɗalibai mata har cikin makaranta kamar wasu kayan sakawa" Saddam ya yi tsaki ya ce "Ji banza, shi ne ki ke wa mutane kuka har haka? A gidan uban wa suka zama 'yan uwan naki? Kawai kin saka gabana ya faɗi a banza" Mama ta ce "Ni wallahi kin bani tsoro" Ta girgiza kai ta dube su ta ce "Sai ranar da ya zamana an sace da ni, za ku ji babu daɗi? Idan ɗalibai a makarantu ba su tsira ba, ni wane tabbaci nake da shi zan tsira?" "Ke dalla yi wa mutane shiru da wannan falsafar banzar taki. Ba nan ki ke zama kina video kina goyon bayan gwamnatin ba. Dalla tashi ki ɗora mana tuwo" Mama ta ce "Kai dakata mini, Laila na da gaskiya. Duk inda iyaye da yan uwan yaran nan suke, hankalinsu a tashe yake. Ubangiji Allah ya tseratar da su cikin Aminci. Ni kaina abin ya tsaye mini. Har da yarinyar wata class mate ɗinmu aka sace wallahi abin gwanin ban tausayi. Tare muka yi islamiyya da ita" Sadam ya ɓata fuska ya ce "Ahh lallai aiki ya ganku, gara na fita tun wuri na nemi abin da zan ci, tun da naga alamar zaman makoki zaku yi yau, ba za ku dafa abinci ku bani ba" ***** Tamkar marasa amfani, haka suke hantarar ɗaliban. Su na jere a zazzaune, ana raba musu buredi a wulaƙance, mai rabon buredin ya miƙa wa Ramata. Ta miƙa hannu za ta karɓi buredin, ya haɗa da hannunta ya riƙe yana ƙare mata kallo. Jikinta ya yi sanyi ya hau rawa, ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta. Amma cike da rashin ɗa'a ya fara shafa hannun nata da ɗaya hannun nasa, har zuwa damtsenta. Jikinta ya hau rawa cike da tsoro tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ya tsare ta da ido da baƙar fuskarsa yana sauke numfashi. "Kai kar fa ka kuskura ka yi abin da ba shikenan ba, kar ka ja mana tashin hankali" cewar na kusa da shi, da suke raba buredin tare. Ya yi murmushi tare da sakar mata hannunta, yana yi mata murmushi. A hankali Rahama ta yi ajiyar zuciya, dan tsoro ne ya shige ta, ta zata wani abin zai yi mata. Ƙarar sautin kusantowar babura ce ta cika gurin, gaba ɗaya suka zuba wa inda suke jiyo sautin ido. Su goma sha biyu ne suka zo a kan babura kowannensu riƙe da miyagun makamai. Idan da sabo, ya ci a ce Rahama ta saba da ganin tashin hankali, amma a wannan karon ma sai da tsoro ya shige ta, ganin uban bindigun da suke hannun maharan kamar za su yaƙin duniya. Cikin girmamawa suke gaishe shi, ya din ga jinjina musu kai, ya din ga ƙarewa 'yan matan kallo, ya tsayar da idanunsa a kan Rahama. Ya yi shiru yana ƙara ƙura mata ido, tamkar mai son hango wani a kan fuskarta. Sai dai ita ma ta ɗan tsura masa ido, ba ta kai ga janye idanunta ba, ya tako a hankali nufo ta, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa ta daina kallonsa. Ya ƙarasa ya tsuguna a gabanta yana kuma ƙare mata kallo, tun zuwansu ya lura da yadda take ta kare jikinta da hannunta. "Kalle ni" Ya faɗa cikin kakkausar murya. Tamkar zuciyarta za ta faso ƙirjinta ta fito, saboda luguden da take yi, haka ta ɗago idanunta da kyar ta kalle shi. Ta mayar da kanta ta sunkuyar. "Kin sanni ne?" Ta girgiza kai a hankali. Ya saka hannu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Da gaske? Kalle ni dai, na ga kina kallona kamar kin sanni ko?" Ya yi maganar yana murmushi. Ta sake girgiza masa kai tana sunkuyar da kanta ƙasa, ba tare da ta kalle shi ba. "A jam fullo?" (Ke Bafulatana ce?" Ta jinjina kai alamar eh. ""ko honɗun wuro njahaa?" (Daga wani gari ki ke?" "Yelwa" Ta faɗa a tsorace. Ya waro ido tare da yin murmushi ya ce "Daga Yelwa aka kai ki makarantar kwana? gaskiya ne, lallai makiyayan Yelwa sun waye, an samu gagarumin ci gaba Sannu ko, ku kwantar da hankalinku babu abin da za mu yi muku, za ku koma gida lafiya in sha Allah, za mu ajiye ku ne nan da wani ɗan lokaci, domin cikar muaradanmu da na iyayen gidanmu. Da mun kammala za mu sake ku. Kun kafa tarihi a duniya, ɗalibai na farko da aka yi garkuwa da su. Ya yi maganar yana murmushi. Ba tare da ta san ita yake kallo ba, ta sake ɗagowa ta kalle shi, fari ne sai dai ba tas ba, idanunsa sun sha farin kwalli rabajau, yanayin fuskarsa da yadda yake magana, ba ka ce ko kwari da baka zai iya ɗauka ba, balle bindiga. "Za ki ce wani abu ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. Ta girgiza kai da sauri tana sake sunkuyar da kanta. "Ya sunanki?" "Rahma" Ta furta kamar mai raɗa cikin tsoro. "Ramata" Ya furta yana guntun murmushi, ya miƙe tsaye ta kalle shi da mamakin jin yadda ya faɗi sunan da ake gaya mata a gida, Alhalin ita ba ta san shi ba, ba kuma ta taɓa ganinsa ba... Ayshercool 08081012143 1k ne a telegram 0069685771 Aisha Adam stanbic https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g More pages available at Arewapen. SARA DA SASSAƘA... AYSHERCOOL YOTA/002 BRIGHT PENS 13 Murmushi ya yi ganin yadda alamun mamaki suka bayyana a fuskarta baki ɗaya, a lokaci ɗaya. ***** Fuskar Ummi ɗauke da matsananciyar damuwa take kallon Ruƙayya, tana kwance a gadon Asibiti sai dai ba ta magana. Sai dai Likitoci sun tabattar wa su Ummi cewar, tsoro ne kawai da razani suke damunta. Haka suka karɓo ta suka tafi da ita, da niyyar su canza mata Asibiti, zuwa na kusa da su can cikin gari. Babu yadda Ammar bai yi ba, ya samu release ya je gida, ya ji halin da ake ciki game da Ruƙayya amma aka hana shi, sai dai su yi waya ya ji ya jikinta, saboda su na daji ma a lokacin. ***** Nadiya ta takura wa Alina a kan lallai sai ta koma makaranta, dan idan Yaya ya dawo, ya tarara ta jingine zuwa makaranta, sai ya yi mata faɗa. Ko da ta shirya ta je makarantar ma, jikinta duk a sanyaye yake, malamai da ɗalibai su na ta yi mata jajen ɓatan yayanta. Hafsa ta yi ta rarrashinta tana bata haƙuri, ji ta yi kamar ta gaya mata haƙiƙanin abin da ya faru, amma tamkar wadda aka asirce ta kasa furta mata komai. Haka ta je Islamiyya ma, tana tafe tana jan ƙafarta jikinta a sanyaye. Ta jiyo muryarsa "'yan mata" Kamar ta yi banza ta tafi sai kuma ta tsaya cak. Ya ƙaraso yana faɗin "Alhamdillah, kin koma makaranta kenan? Ai hakan ne ya dace zama a gidan damuwa zai ci gaba da saka ki" Ta ɗago idanunta ta zuba masa, tare da haɗiye wani abu mai ɗaci, idanunta ya cika da hawaye. "Lafiya mene ne kuma?" Ta yi shiru tana bawa hawayen idanunta damar zubowa. Jiki a sanyaye ya ce "Ki na ji 'yan mata, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ki ci gaba da addu'a in sha Allah zai dawo cikin ƙoshin lafiya da aminci" "Yaushe? Zuwa yaushe zaka dawo mini da shi?" Ya yi saroro yana kallonta. "Ka gaya mini yaushe za ka dawo da shi? Na ganka fa, na ga komai, amma na kasa gayawa kowa, ina ta kallonka in ga ko za ka dawo da shi, amma ka ƙi. Na san kai da Yaya ba kwa jituwa amma abin da ka yi ya yi tsauri" "Me ki ke nufi?" "Na ganka, na gani, a kan idona ka ɗaure shi kai da wasu ku ka tafi da shi Da daddare ranar na dawo daga makarantar dare. Ta can baya na zagayo ina tsaye a bakin lungun can, na ganka. Dan Allah Mamman dan darajar iyayenka ka dawo mini da yayana dan Allah" Ya waiwaya layin ya ga babu kowa, ya sassauta murya ya ce "Ni fa ban gane me ki ke nufi ba" "Ka sani wallahi ka sani, kai ka ɗaure Yaya da igiya ku ka tafi da shi" Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba ni ba ne ba, dan ranar da ki ke magana bana garin nan, na je gurin Inna" "Kai fa ma'abocin karanta Alqur'ani ne, bai kamata ka yi ƙarya ba, dan Allah dan Annabi ka dawo mini da shi" "Amm ina ga ki je gida kawai, wataƙila damuwa ce ta yi miki yawa ki kr irin wannan tunanin, amma gaskiya ba ni ki ka gani ba." Ya wuce ta ya bar ta a tsaye a gurin. Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ƙarasa gida, ko da ta je gidan ta tarar Nadiya ta fita, dan haka ta samu cikakkiyar damar yin kuka. ***** "Haƙiƙa mu na yabawa yadda mr. President yake ta ƙoƙarin ganin yaran nan sun kuɓuta, mun san ayyuka sun yi maka yawa, kuma duk wani abu da ka ke yi, domin al'immarka ka ke yin su. Amma Allah wadai da fadarka ta yi da sace ɗalibai, ta bakin mai magana da yawunka ta yi kaɗan. Ko ba ka je da kanka ba, ka rarrashi al'ummarka mussaman iyayen waɗanda aka sace ɗin nan, za su ji daɗi, komai ƙanƙantar abin da zaka gaya musu kuwa za su ji daɗi domin kai uba ne ga kowa. Please ka ce wani abu ko babu yawa, za mu ji daɗi" A hankali ya ja ajiyar zuciya, bayan kammala kallon videon da ta wallafa, gaba ɗaya ƙasar ta ruɗe, ko ta ina bring back our girls ake posting. Ji ya yi ya samu ƙwarin gwiwa da kalamanta, ko da maganarsa ba za ta yi tasiri ba, akwai buƙatar ya yi magana da bakinsa, ba a ji iya ta bakin mai magana da yawunsa ba. Halilu ne ya shigo ofishin, hannunsa riƙe da takardu. Cikin matuƙar girmamawa, suka gaisa. Bayan an yi masa iznin zama, ya dubi Kankiya ya ce "Mr. President, tafiyarka taron kasashe masu arzikin man fetur fa jibi ne, ina yi maka tuni duk da na ga ka yi busy da yawa." "Na soke tafiyar" Da sauri Halilu ya dube shi ya ce "Mr. President ka soke kuma?" "Eh, hankalina na kan batun yaran nan, ba zan iya komai ba" "Haka ne, amma akwai buƙatar ko wakilci a naɗa ka tura" "Babu buƙata, mutanen nan hawan ƙawara suke yi mana kawai, wannan shekarar ba zamu halarci taron ba, hanyoyi da yarjejeniyoyin da za su durƙusar da mu, su azurta kansu kawai suke yi" "Amma Your excellency, ƙin halartar zaman, ya saɓa da yarjejeniyar da tsohuwar gwamnati ta saka hannu, kafin karɓar bashin biliyoyin da aka yi a shekarun baya, za su iya hukunta mu, ta hanyar janye mana wani tallafin, ko kuma sanya mana takunkumin da zai durƙusar da tattalin arzikinmu ma baki ɗaya" Ya ɗan yi shiru yana matsa yatunsa, ya dubi Halilu ya ce "Ina buƙatar zama da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa. Ina buƙatar bincikar yadda aka gudanar da wannan maƙudan kuɗaɗen, da ainihin kwafin yarjejeniyar basussukan da aka karɓa. Dan yanzu haka ma, ƙasar ba za ta tafi ba sai an ciyo wani bashin, kuɗaɗen da suke asusun ƙasar nan, ko jihohi goma ba zai riƙe ba" Halilu ya risuna ya ce "In sha Allah, za a yi yadda ka ce, amma mr. President ka sake nazari a kan batun taron nan" Kai kawai ya jinjina. Bayan fitar Halilu ya sake ɗaukko wayarsa yana dubawa. Comments ne na rashin kyautawa, da cin zarafi aka cika Laila da shi. Cin mutumci har da iyayenta, cin mutunci mai matuƙar muni ga ita da iyayenta, ban da ƙazafi da kushe mata halitta a ƙoƙarinta na bawa gwamnatinsa kariya. A hankali ya dafe goshinsa yana ɗan murzawa a hankali. Yana tunanin meya kamata ya yi. ***** YELWA Duk da dakiya da juriya irin ta Baffan Rahama, sai da ya yi wata irin muguwar rama, dan ko lokacin da aka kashe masa ɗa, bai shiga mummunan tashin hankali kamar yanzu ba. Ko Abinci baya iya ci, baya iya bacci, 'yar kasuwar da yake ɗan zuwa ma ya daina saboda matsananciyar damuwa da kuma tashin hankali. Tashin hankali da damuwa da yake ciki, bai hana jama'ar garin zunɗensa ba, har da masu yi masa dariya da Allah ya ƙara. Hanne na zaune a ɗakinta, tana saƙar mafici, Bukar ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. Ta ɗaga kai ta bi shi da kallo tana mamakin me ya faru. "Hanne, kin san me yake faruwa kuwa?" Ta girgiza kai tana tsare shi da ido, tana jiran ƙarin bayani. "Su Ramata aka sace s makarantar boko" "Kamar ya ya aka sace su? Ta ya za a sace mutum? Ko dai ba ka ji dai-dai ba ne?" Bukar ya tsuke fuska ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Da gaske nake an sace su Ramata a makaranta, ba a ma san inda suke ba" Hanne ta dafe ƙirji tana nanata "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin abu ne? Allah sarki Baban Ramata, anya akwai wanda Allah ya taɓa jarabta a garin nan kamar sa? Amma ni ta yaya za a ce an sace mutum" Cikin damuwa Bukar ya ce "To nima dai haka na ji" "Gaskiya zan je gidan nasu, zan sake tambayar Baffan" "A'a babu ruwana, kin san a ƙarƙashin takunkumi ki ke, kuma a gan ki a gidansu Ramata?" Hanne da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Wallahi ko za su kashe ni sai na je, har Duniya ta naɗe Ramata da ahalinsu su na bin mu gagarumin bashi, ba zan iya jurewa ba sai na je" ***** Sosai ɗaya daga cikin masu tsaron su Rahama, yake ƙoƙarin kai musu farmaki. Da ƙoƙarin fito da zalamarsa a fili a kansu. Duk dare haka ake ɗaure musu ƙafafuwa, domin kar ma a samu mai yinƙurin guduwa. Idanun Rahama biyu, tana rarraba su a cikin duhu, ta ji wani abu mai sanyi, yana bin ƙafarta. Ta ɗan motsa ƙafarta a hankali, ta ji abin ya daina bin ta. Wata irin ƙara ta saki, bayan jin wani irin raɗaɗi ya ratsa ƙwaurinta zuwa cikin ƙwaƙwalwarta ta gigice. Cikin hanzari masu tsaronsu, suka yo kanta su na haskata da fitila, su na yi mata tsawa. Tuni gumi ya wanke ta, sai dai kafin su yi magana suka hangi wani irin ƙaton baƙin maciji ya bar gurin. Su ka haska ƙafar Rahama, ga shaidar gurin da ya cije ta, jikinta sai wata irin tsuma yake yi. Da yawa daga cikin ɗaliban, har da wanda suka fara bacci, duk su ka zubo mata ido, su na yi mata sannu. Ya yin da tsoro ya shige su, kar ya kuma cizon wani. "Dare ne yanzu babu abin da za mu iya yi, zuwa da safe a sanar da sadauki" cewar ɗaya daga cikinsu. Babu wanda ya damu ya ba ta wani taimakon gaggawa, kawai suka koma mazauninsu, suka bar ta. Rahama kuwa ji take yi tamkar ranta ne zai bar gangar jikinta, saboda azaba da raɗaɗin da yake ratsa ta. Duk yadda ta so gwada jarumta sai ta kasa, ta fara kuka mai sauti, mai nuna tsantsar azaba da galabaita. "Ke ki rufe mana baki, ko mu ƙarasa ki" Ya yi mata tsawa. Sai dai ba ma ta fahimtar abin da yake faɗa, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, jikinta ya din ga karkarwa. Gaba ɗaya hankalin ɗaliban ya tashi wasu suka fara kuka. Dukansu suka fara yi, da kan bindigogi su na taka su da ƙafa, tare da yi musu barazanar harbi, hakan ya tilasta musu jan bakinsu su yi shiru. Jin Rahama ba ta da niyyar yin shiru, ya sanya ɗayan sanya bakin bindiga ya buga mata a kanta, hakan ya sanya ta sulalewa a gurin. ***** Ta na daga kwance a kan gadon Asibiti, duk ta rame ta yi zuru-zuru, cikin damuwa Ummi ta riƙo hannunta ta numfasa ta ce "Ruƙayya, haryanzu jikin naki? Yakamata a sallame mu zuwa gida" "Tsoro nake ji ne" Ta yi maganar cikin rauni, tana fashewa da kuka. "You are safe dear, gida zamu koma babu wanda zai biyo ki gida ya cutar da ke, in sha Allah. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki yi ta addu'a. "Ummi an tafi da Rahama fa. Kuma harbi suka harbe securitynmu" Ta yi maganar tsoro na bayyana a muryarta. Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah za ta dawo cikin aminci." Ta yi maganar tana shafa kanta da sigar rarrashi. ***** Safiyar Lahadi yana zaune a cikin ɗakinsa, yana daddana wayarsa, ya ji alamar motsi a bakin ƙofa, ya ɗan yi shiru yaga alamar motsi a gurin. "Waye a nan?" Ya yi maganar yana kallon ƙofar, tare da zura hannunsa ƙarƙashin pillownsa. Ɗaga labulen ta yi ta shiga, ya yi saroro yana kallonta. "Lafiya kuwa? Me ki ka zo yi ɗakina da sassafiyar nan Alina, sai kin saka a zarge mu?" Ya yi maganar yana ƙarewa kumburarriyar fuskarta ido. Allah ya wadata Alina da manyan idanuwa, sai dai sun rine sun yi jawur kamar an zuba mata kala. Gani ya yi ta durƙusa a kan ƙafafuwanta, ta haɗa hannayenta biyu, hawaye na rige-rigen zubowa daga idanunta ta ja numfashi da kyar ta ce "Dan girman Allah, dan son da ka ke yi wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ka taimaka ka gaya mini ina ka kai mini Yaya? Ka san ba mu da kowa sai Allah sai shi, ban san yadda zan rayu babu shi ba, shi ne komai nawa. Dan Allah ka gaya mini inda yake, na kasa gaya wa kowa abin da ya faru, dan Allah dan Annabi ka dawo mana da shi, ka yi haƙuri dan ma wani laifin ya yi maka ka yafe masa dan Allah" "Alina" Ya kira sunanta yana tsare ta da ido. Ta ɗaga kanta tana kallonsa. "Sau nawa zan gaya miki cewar ni ba ni bane ba ki yarda? In ɗauki yayanki na kai shi ina?" "Wallahi kai ne, na ganka da idanuna, kai ne ba wani ba. Dan Allah Mamman ka taimake ni ka dawo da shi. Ba wanda zan gaya wa na ga abin da ya faru, dan Allah ka taimaka. A duniya bayan Allah da ma'aiki ba ni da kowa sai Yayana ka duba rayuwata da maraicina dan Allah" Wani irin motsi ya din ga ji a ƙasan zuciyarsa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga kai komo, lissafi na neman ƙwace masa, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita ya ce "Zo ki tafi, zan fita" Jiki a sanyaye ta taso, ta sake nufarsa, amma ya murtuke fuska ya ce "Ki fita ki bani guri" Ta girgiza masa kai tana haɗa hannayenta tana kuka, ya kawar da kansa daga kallonta yana nuna mata hanyar fita. Wani irin tsoro ya mamaye ta, ta fita tana jan ƙafarta a hankali tana kuka mai sauti. ***** Yanayin fuskar Laila ne ɗauke da damuwa, da alama ta sha kuka ne sosai da sosai. Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara da sallama, kamar yadda ta saba a dukkanin videos ɗin ta. "Na ga alamar posting ɗina na ƙarshe a kan mr. President, bai yi wa da yawan mutane daɗi ba. Na ci zagi da ni da iyayena, da masu ce mini karuwa, da masu cewa kuɗi ake ba ni, nake kare gwamanti. Ni babu wanda ya bani kuɗi na kare gwamanati, hasali ma ba a san da zamana ba. Son da nake yi wa shugaban ƙasa ya faro ne, silar sunansa ɗaya mahaifina marigayi DSP Faruk Kankiya. Wanda ya rasa rayuwarsa shekarun baya, bayan artabunsa da 'yan fashi, wanda wani case ne daban. Tun Mr. President yana riƙe muƙami a matakin jiha nake son sa, Saboda son da nake yi wa mahaifina aka kashe shi, kuma 'yan fashin da ya kama aka sake su. Har Mr. President ya zama shugaban ƙasa, ina bibiyar lamarin siyasar sa, ina son shi, yana burge ni, kuma halayensa sun yi kama da mahaifina a wasu ɓangarorin. Ba zan iya daina son sa da ba shi goyon baya ba, son zuciya ɗabi'ar zuciya ce, ba zan iya kushe shi dan na faranta muku ba. A ƙarshe ina baku haƙurin, duk wanda baya son abin da nake yi ya yi haƙuri, ya daina following ɗina, roƙona ɗaya ku daina zagin Abbana dan baya raye. Mr. President kuma har abada bana fatan ko shi ko muƙarabbansa, wani ya maganta mini sisinsa ba na buƙata. Shugaba ne da nake wa kallon Uba, zan yi masa addu'a Allah ya yi riƙo da hannayensa kuma zan ci gaba da goyon bayansa ɗari bisa ɗari". Mama na wanke-wanke a tsakar gida, ta ji ana ta ƙwala sallama a ƙofar gida. "Waye?" Ta yi maganar tana kallon hanyar soro. "Bala ne" "Shigo" Ta amsa tana ɗauraye plate ɗin hannunta. Ya shigo yana sake sallama ta amsa masa tana faɗin "Dama kai ne ka maƙale a waje ka na kwaɗa sallama?" "Wallahi kuwa, mutuniyar fa?" "Ta je karɓo caji" Ya zauna a kan tabarmar da ke shimfiɗe, ya ce "Bari na jira ta" Su na cikin hira, Laila ta dawo, tana ganinsa ta yi murmushi ta ce "Balansy" Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Dalla zauna, mai abin haushi" Ta tsuke fuska ta ce "Me na yi?" "Videon da ki ka wallafa ɗazu mana, uban wa ya aike ki? Ina ruwanki da wasu masu Comment da zagi, ko dai ki rama zagin ko ki ƙyale su" Ta sake ɓata fuska ta ce "Ni ba zan zama 'yar balaja'u na din ga zage-zage ba" Bala ya ce "Ina ruwanki da wani balaja'au in dai za ki samu kuɗaɗenki? Next week akwai yiwuwar dollar ta ƙara tashi, sai ki cire kuɗinki" Ta yi murmushi ta ce "Kai ka ce ina cikin alkhairi, nawa zan samu?" "Kusan dubu ɗari da hamsin a ƙiyasi, sai dai yadda ta kaya. Ke ba wannan ba, na ji wai-wai, shugaban ƙasa zai zo garin nan, jajen abin da ya faru na ɓatan matan nan, idan hakan ta tabatta dole ki halarci gurin nan, duk yadda za mu yi, ko hoto ki yi da shi" Ta waro ido ta ce "Dan Allah? Ni ba sai na yi hoto da shi ba, ko ganinsa kawai na yi" Mama da ke kitchen ta ce "Bala me ka ke ƙulla mata, ba dai wata tsiyar za ka saka ta kuma aikatawa ba ko? Kun yi ƙulle-ƙullen da sai da ta rasa aikinta, yanzu kana kitsa mata wani abin, ni dai kar ku janyo abin da za a zo har gida a same mu, mu shiga uku ina lallaɓa rayuwata" Bala ya ce "Hajiya Mama ba za ki gane ba, idan Allah ya ɗaga likkafar Laila, sai kin manta duk wata wahala fa, za ki sarara" Sadam ya fito daga ɗakinsa, fuskarsa duk alamun bacci ya ce "Maƙaryaci, wace likkafa kullum cikin wahala ku ke, ba kwa samun ko sisi, sai ma kuka da baƙin ciki da take kwasa" Bala ya ce "To ina ruwanka? Duk ranar da Allah ya sanya ta fashe mana, muka sha kwana zaka sha mamaki. Mu na nan  zamu fara wallafa ayyukanmu a jaridarmu mai zaman kanta ta online". Saddam ya yi tsaki ya ce "Jaridar bugaggu ba" Bala ya ce "Laila, kar gwiwar ki ta yi sanyi, za mu ba su mamaki da yardar Allah" Ta yi murmushi ta ce "Ba zan gajiya ba, ba kuma zan sare ba in sha Allah" ***** Can a daji kuwa, Rahama tana yashe a ƙasa, su maharan ba su bari an taɓa ta ba, kuma ba su taɓa ta ba. Ɗaya ne daga cikinsu ya saka ƙafarsa yana taka tata. A hankali ta motsa, ta buɗe idanunta da suka yi mat nauyi, sai dai ta ji kanta kamar ba nata ba. Ga shi ba ta gani sosai sai dishi-dishi. Ya yin da ƙafar da maciji ya sare ta, take jin ta tamkar ba a jikinta take yi ba. Ga jikinta sanyi ƙalau. Ganin ta motsa ya sanya ya durƙusa a kanta yana kallonta. Ta kalle shi da kyar, amma ta kasa motsi. Ya yi wani irin murmushi yana lashe laɓɓansa, ya miƙa hannunsa jikinta yana faɗin "Ashe dai da sauranki ba ki yi mushe ba?" Ya yi maganar yana neman ɗage mata riga a gaban mutane. Tafasar da zuciyarta ke yi, ya bata wani irin ƙwarin gwiwa da niyyar ta hankaɗe shi, amma tana ɗaga hannunta ya koma ya faɗi. "A'a Halliru, kar ka yi wa yarinyar nan wani abu, kar Sadauki ya zo ya yi mana hauka" "Shhh" Ya yi maganar yana kallon Salisu, da fuskarsa ke bayyanar da tsoro. "Ba zai yiwu a bawa kura ajiyar nama a hana ta ɗanɗanawa ba" Ya yi maganar yana ɗago Rahama, yana kallonta cikin murmushi. "Kai ba fa zai yiwu ba, idan na gama sai mu ƙarasa ta, mu ce saran macijin ne ya kashe ta kawai"  Ya yi maganar idanunsa na yin ja, jikinsa na rawa, saboda sosai yake ƙarewa jikinta kallo, mussaman da kullum cikin takurewa take. Ayshercool 08081012143 Mun kusa Kammala free pages. 1k ne a telegram via 0069685771 Aisha Adam stanbic Sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira sai an kammala 1500 za su biya. AMANA KAYAN MATAN Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto. Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su.. Gumbar madara Gumbar mata Gumbar aya Gumbar chaku Gumbar dake saukar da ni'ima Gumabar taƙadari Gumbar riɗi Gumbar dabino Gumbar uku alkhairi Kazar amare Jijjiɓen saniya Tabaje Tsimi Rikita mai gida Jigidar tada sha'awa Ruwan boom ruwan daɗi kenan Ɗan matse Karya gado Maganin sanyi Zumar ƙarin ni'ima Zumar rage ƙiba Zumar ƙarin ƙiba Zumar riɗi Mai zamani Emergency powder Tarhama Kafi budurwa Sabon budurci Alfijir Gamzaki Garin dahuwar nama Sabaya Miskin ɗahara Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina. *ALBISHIR ALBISHIR ALBISHIR* *Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar* *Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;* 1. Graphic design 2. Magungunan mata 3. Sabaya 4. Turaren wuta 5. Fara 6. Candies 7. Skin care products 8. Importation 9. Snacks 10. Yoghurt 11. Oil perfumes 12. Bead work 13. Hair cream/oil 14. Dabarun kiwon kaji 15. Huluna 16. Spice's 17. Dabarun sana'ar kayan kitchen 18. Noma a zamanance 19. Dabarun kasuwanci Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin. 08081012143 07037977211 08069611181 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA YOTA 002 AYSHERCOOL Page 14 Cikin sauri Sabi'u ya saki Rahama ya tashi, saboda jin ƙarar babur a bayansu, ba tare da jin sautin tahowarsa ba. Ya sauka daga kan babur ɗin, sauran 'yan bindigar suka nufo shi, su na yi masa barka da zuwa, ya miƙa musu bindigarsa suka karɓa. Ya ƙarasa inda Ramata ke yashe kamar abin banza, ya saka hannunsa ya ɗago ta zaune. Ya kalli leɓenta ya bushe, jikinta sanyi ƙalau. Sai motsa hannunta take yi, tana ƙoƙarin kare jikinta. Ya dubi ɗaya daga wanda suka zo tare, ya ce "Ba ni abin nan" Ya ƙaraso ya miƙa masa wata 'yar ƙaramar kwalba. Ya kwance ta ya ɗaga bakin Rahama ya zuba mata abin da yake cikin kwalbar. Mintuna kaɗan ya ɗaga ta zaune, aikuwa ta fara sheƙo amai babu ƙaƙƙautawa, ta galabaita sosai, sai da ya fuskanci ta gama sannan ya ja ta ya jinginar da ita a jikin bishiya. Sai haki take yi tana sauke numfashi. "Kina jikar makiyaya, ya aka yi ba ki sha maganin dafin maciji ba?" Ta yi shiru tana bin sa da kallo a galabaice. Ya kalli inda ƙafar da macijin ya sare ta, ya fara kumbura. Ya ciro wata aska ya tsaga gurin, ya tsare ta da idanunsa, da idan ta kalli idon nan nasa da ya sha farin kwalli sai tsoro ya kama ta. Ya durƙusa ya kafa bakinsa a dai-dai gurin. Ji ta yi tamkar yana fizgar wani abu a cikin jikinta. Wani irin wahalallen kuka ta din ga yi jikinta na karkarwa, tamkar za ta shiɗe. Ya ɗago ya buɗe kwalbar da ya bata magani a ciki, ya zuba abin da yake cikin bakinsa. Abun baƙi ƙirin babu kyawun gani. Ya dube ta ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah macijin zai kawo kansa, za ki ga hukuncin da zan yanke masa. Ya yi maganar yana goge mata gumin da ya tsatstsafo a goshinta. Ya ciro hiramin da yake rufe fuskarsa da shi, ya yagi wani sashi a jiki, ya kama ƙafar saman gurin da ya cije ta ya ɗaure. Ya sa aka kawo masa ruwa, ya ba ta ta sha, ta rage tana daga zaune ta yi alwala, ta yi sallar asuba a haka a yadda take zaune. Yana tsugune a gefenta, ta idar aka ba ta waina a cikin leda fal da ƙuli-ƙuli, ta riƙe wainar a hannunta, ta ɗaga kai tana kallon sauran 'yan uwanta da suke tsare tare, sannan ta kalli Sadauki. "Nasu abincin yana hanya, idan ba ki ci naki ba, maganin da ki ka sha zai iya halaka ki" Hannunta na rawa, ta gutsiri wainar, sai dai ta riƙe a hannunta, tana sinne kai ta kasa ci. Ya yi murmushi ya matsa gefe ya kawar da kansa daga kallonta, sannu a hankali ta fara kai wa bakinta tana ci, tamkar tana cin magani. Sadauki ya ɗan waiwaya ya ce "Sabi'u zo ka karɓi kwalbar nan, ka ajiye mini zan yi aikinta na kama macijin nan" Ya yi maganar yana miƙa masa kwalbar da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma ya zura a cikin Aljihunsa. Sabi'u ya ƙaraso ya kawo hannu zai karɓi kwalbar. Sadauki ya janye kwalbar, Sabi'u ya sake ƙarasawa zai karɓa, amma Sadauki ya fito da ɗaya hannun nasa riƙe da bindiga ƙirar pistol ya harbe shi har lahira. A take da yawa daga cikin ɗaliban suka saka ihu cike da tsoro. Jikin Rahama kuma ya hau rawa ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi saboda jinin sai dai ya ɓata mata fuska. Idanunta da suka yo waje suka ƙara bayyanar da tashin hankalin da ta shiga. Sadauki ya ɗan tsura mata ido, ganin yadda numfashinta ke kai komo a ƙirjinta. Ya sake ciro hiraminsa ya kamo fuskarta, ya fara goge mata jinin yana faɗin "Yi haƙuri na tsorata ki ko? Ya aka yi jinin makiyaya ta kasance cikin matsorata ne? Mu fa ba matsarota bane ba a sammunda tsoro ba" Ya yi maganar yana ci gaba da goge mata fuskarta. Ya sakar mata murmushi ya ce "Kar ki yi mini mummunar fahimta fa, ni mutumin kirki ne" Ita kuwa ba ma ta gama iya tantance a wani yanayin take ciki ba, balle ta fahimci me yake faɗa. Sai da ya gama goge mata jinin sannan ya miƙe tsaye, ya murtuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba ya ce "Wannan shi ne abin da zai biyo bayan duk wani wanda ya yi yinƙurin aikata halin ɗan taure a tsakanin yaran nan. Kai Gulafa, ku je ku binne shi, kai kuma je ku ƙarasa aikin da na saka ku ku yi mini, saboda zan din ga zagayowa ba tare da na sanar muku ba. Ya kalli sauran 'yan matan ya ce "Ku kuma ku kwantar da hankalinku, na gaya muku babu wanda za mu cutar" Ya saka hannunsa ya cire babbar rigar yadin da take jikinsa, ya durƙusa ya saka wa Rahama da har a lokacin jikinta bai daina rawa ba. Ba ta iya motsawa ba har ya gama saka mata, shi ma kuma bai sake ce mata komai ba. Ya nufi baburinsa ya hau, suka miƙa masa bindigarsa ya karɓa ya tafi. ***** Laila ce a zaune, ta duƙufa a kan wayarta, hannunta ɗaya riƙe da biro da takarda tana rubuce-rubuce. Mama ta shigo ɗakin ta tsaya a kanta ta dube ta cike da takaici ta ce "Wai Laila uban me ki ke yi ne a kan wayar nan?" Laila ta yi miƙa ta ce "Mama aiki nake yi" "Aikin banza ba, awa ashirin da huɗu, kullum idonki a kan waya, ina jin wani likita na magana a radio, ya ce ba da jimawa ba idanun matasan yanzu duk zai mutu, saboda azabar kallon waya." Laila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Bincike nake yi ne, neman kuɗi nake yi da wayar nan Mama, dan Allah ki bani dubu ɗaya zan je wata unguwa ne" Mama ta dube ta sheƙeƙe ta ce "Shegiyar wayar taki da ki ke wuni a kanta, ki ke neman kuɗin da ita, ba ta kawo miki dubu ɗayar da zaki yi yawon ba" Laila ta yi murmushi ta ce "Hajiya Mama kenan, bari na yi wanka na je Cafe ɗin su Saddam, na san ko ya gama yi mini gori zai bani" "Tsaya tukuna ma ina za ki je?" Laila ta hau murmushi ta ce "Ba daɗewa zan yi ba, zuwa zan yi na dawo" "Tambayarki na yi, ina za ki je?" Laila ta ci gaba da murmushi ta ce "Mamansy, kin san ba zan je inda zan ɗaukko miki magana ba" "To wallahi idan ba ki gaya mini ba, ba za ki fita ba" Ta ɗan sunkuyar da kanta, jiki a sanyaye ta ce "Mama zan koma batun filinmu ne, ina ci gaba da bibiya, idan ba za su yi mana adalci ba, akwai yiwuwar na wallafa rubutu a kan lamarin" Mama ta nemi guri ta zauna ta  dube ta ta ce "Laila, na san an cutar da ku. Wannan filin shi ne abin da muka tsira da shi da wannan gidan, tun da an yi ƙarfa-ƙarfa a kan filin nan ki yi haƙuri kawai. Tun da mun tsira da gidan nan shikenan. Kin ga ɗan uwanki da na ba shi baki ya haƙura, to kema ki bar wa Allah kawai" Laila ta sunkuyar da kanta, sannan ta ɗago kanta idonta duk hawaye ta ce "Mama shikaɗai fa muka tsira da shi, kina gani hakkin babanmu abokansa suka ci abin da suka ga dama, suka bamu wanda suka ga dama. Kuma filin da aka saya mana tsawon lokaci, mu na saka ran mu na da kadara mai tsada a ajiye, rana tsaka gwamnati ta ƙwace an bamu diyyar da bata kai rabin kuɗin kadararmu ba. Kuma an saya mana wani filin shi ma wasu su mallake su ce nasu ne, mu zuba ido" "Laila ya za mu yi tun da sun fi ƙarfinmu? Da aka ƙwace filayen mun daina rayuwa ne? Muka rasa mahaifinku ma balle wani fili, mu bar wa Allah kawai. Albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da Alqur'ani filaye idan mu na raye sai dai ku bawa wani kyautar su ma, mu bar wa Allah kawai" Ba haka Laila ta so ba, amma gudun ɗaga wa Mama hankali, ya sanya ta jinjina kai ta nuna mata cewar komai ya wuce. ***** Ɓangaren Alina, abubuwa sun ƙara rikice mata, yadda ta kai ba ta iya sarrafa kanta sosai. Hankalin Nadiya ya tashi sosai, dan Alina ta kwanta rashin lafiya, saboda damuwa wannan ciwon kan ya tayar mata. Ga shi a duk lokacin da ta yi yinƙurin gaya wa Nadiya abin da ya faru, sai ta ji ba za ta iya ba, gani take yi kowa sai ya zarge ta da laifin faruwar komai dalilinta, dan babu irin kashedi da jan kunnen da Yaya bai yi mata ba a kan Mamman. Tun safe Alina ke kallon Nadiya daga kwance, tana harhaɗa musu kayansu a bagco. Ta dubi Alina cikin kulawa ta ce "Sannu ƙanwar Yaya" Alina ta jinjina kai ta ce "Anty ina zamu ne, na ga kina haɗa kaya?" "Tafiya zamu yi" Ta bata amsa. "Ina za mu je?" "Garin nan zamu bari" Cikin rashin fahimta Alina ta ce "Mu je ina? Idan yayan ya dawo kuma fa?" Nadiya ta ce "Alina kin fiye tambaya, ki zuba ido za ki gani, ci gaba da zamanmu a nan ba shi da wani amfani, Yaya kuma duk inda muka shiga, in dai ya dawo zai neme mu" Alina ta sake cewa "Ta yaya zai san ina muka tafi, ko kin san inda yake ne?" "Alina, ki kwanta ki yi shiru ki samu bacci, wannan ciwon kan ya sake ki, idan abin ya ci tura kin san sai mun je Asibiti abin da ba kya so" Alina ta jinjina mata kai kawai ta lumshe idanunta, sai dai ƙasan zuciyarta tana ci gaba da mamakin ina za su bar garin nan su tafi, su da ba su da kowa. ***** Tun da sadauki ya tafi, Rahama a cikin fargaba take, idan ta kalli babbar rigar da ya saka mata, ga shi ya suturta nata jikinta da take ta ɓoyewa, amma a mugun tsorace take. Ga rigar sai ƙamshin turare take yi. Da ta tuna yadda ya harbe Sabi'u sai ta razana kamar hankalinta zai gushe. Sai dai ɓangaren ƙafarta da maciji ya sare ta, a hankali ta saki ta daina yi mata wannan mugun zugin da take yi mata. Daga nesa kaɗan suka din ga jin ƙwale-ƙwale, sai dai ba su san me ake yi ba. Ko a tsakaninsu ɗaliban, ba a bari su yi hira a tsakaninsu saboda gudun kar su ƙulla wani abu a tsakaninsu. A hankali Rahama ta takure jikinta, saboda wani irin azababben sanyi da yake ratsa ta, bacci ɓarawo ya fara ɗibarta. Sannu a hankali take ratsawa cikin ƙauyen Yelwa, kai tsaye ta tunkari rigarsu, ta shiga cikin gidansu, ta tarar da Baffa a zaune yana addu'a. Ta ƙarasa da gudu ta je gabansa ta zauna tana yi masa magana, sai dai ta ga alamun baya ganinta. Sadauki ta ga ya shigo gidan nasu, tare da su Saleh a bayansa, da wasu daga matasan garin nasu, riƙe da miyagun makamai. Kafin ta farga kawai Sadauki ya harbe Baffa, jininsa ya watso a fuskarta kamar yadda ya yi wa Sabi'u. Wani irin ihu Rahama ta yi tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"', Wayyo Allahna Baffa" Sadauki ne ya riƙe ta da hannayensa biyu, ya mayar da ita ya zaunar da ita. Ƙara rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza masa kai "Dan Allah kar ka kashe shi, kar ka kashe Baffana dan Allah bai yi maka komai ba" "Shhh. Ai kin baro mafarkin, kalli ba gaskiya ba ne" Ya yi maganar cikin sigar rarrashi, yana haske fuskarta da fitila. Ya sake girgiza mata kai, yana yi mata nuni da ta kwantar da hankalinta. Ta kalli gurin duhu ya yi sosai, alamar dare ya tsala, ga wuta an kunna a tsakanin su. Sai da ya tabattar da ta ɗan nustu, sannan ya saki hannunta, ya janyo wata ledar Viva, ya buɗe ya haska mata cikin ledar da fitila. Maciji ne a ciki baƙi ƙirin da shi, yana buɗe shi ya fasa kai, aikuwa ta zabura ta ja da baya. Ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Shi ne ya sare ki, na yi amfani da dafinsa na nemo miki shi, ya ki ke son a kashe shi?" Ta girgiza masa kai. "Sai fa an kashe shi, ya ki ke so a yi masa?" Ta takure jikinta tana kallon ledar cikin tsoro. Kawai ya saka hannu ya damƙo kan macijin, ya jefa shi cikin wutar da take ci a gurin. Za ta yi ihu ya saka mata kan bindiga a ƙafarta, da sauri ta saka hannu ta toshe bakinta, ta ƙarfin tsiya ta haɗiye ihun. Zuciyarta ta karye ganin yadda macijin yake ta wutsul-wutsul a cikin wuta yana miƙewa yana neman hanyar guduwa, yana fitar da wani sauti mai ban tausayi. Ya waiwaya ya kalli wutar, sannan ya kalli yadda take kallon wutar hawaye na zuba daga idanunta, ya ciro kwalbar da ya zuƙe dafin macijin daga jikinta ya jefa a cikin wutar. Su na haɗa ido, ta sunkuyar da kai, tana jinjina girman rashin imani, da Allah ya dasa a cikin zuciyar Sadauki. Ya miƙe ya tattaka ya je ya ɗaukko wani abu, ya zo kanta ya tsaya ya buɗe shi,ƙaton bargo ne mai kaurin gaske ya lulluɓa mata a jikinta. Ya miƙe ya yi gaba abin sa. ***** YELWA Baffa ya yi iya yin sa, gurin yin tawakalli, da miƙa lamuransa ga Allah, da ƙoƙarin danne zuciyarsa a kan abin da ya faru. Sai dai a ƙarƙashin zuciyar tasa wuta ke ci, da take ƙona shi shikaɗai ba tare da kowa ya sani ba. Cikin ƙarfin hali, yana zaune a ƙofar gida da radionsa da saurarenta ya zame masa jiki. Can ya hango Bukar na nufo inda yake tare da Hanne, hakan ya sanya shi tsayawa cike da tsoro da fatan ba wani laifin ya aikata ba. Cikin girmamawa Hanne da Bukar suka gaishe shi, ya amsa yana kallonsu da jiran jin abin da yake tafe da su. "Baba shin da gaske ne labarin da muka samu, na cewa an sace su Ramata a makaranta?" Baffa ya numfasa cikin ƙarfin hali ya ce "Haka ne Hannatu, sai dai ku taya mu da addu'a" Bukar ya ce "Amma Baffa, Babu wani labari a kan inda aka kai su, ko labarin ƙoƙarin nemo su?" Duk da Baba idan ya kalli su Bukar, yana fama masa mikin da ke zuciyarsa, na abin da ahalinsu, suka yi wa zuriyarsa, sai dai ya danne, duba da yadda suka zo yi masa jajen abin da ya faru da 'ya ɗaya da ta rage masa. Ya ce "To, ko ma ana ƙoƙarin nemo sun, ka ga ni ina nan a cikin ƙauye, babu lallai na san halin da ake ciki. Amma na bayar da lambata ina tuntuɓar malamansu". Jiki a sanyaye Bukar ya ce "Baffa ka yi haƙuri, in sha Allah Ramata za ta kuɓuta cikin aminci da yardar Allah" Baffa ya ce "To, Allah ya sa" Hanne ma cikin sanyin jiki ta ce "Za mu ci gaba da addu'a, da yardar Allah Rahama za ta kuɓuta cikin aminci" Baffa ya ce "Ina fatan hakan, kuma yakamata ku koma haka kar a zargi wani abu, ko mu yi laifi daga ni har ku" Suka yi wa Baffa sallama suka tashi suka tafi. **** Kwana biyu Mama tana saka wa Laila ido, tare da sake rarrashinta, a kan batun filayensu da aka ƙwace, dan tana yawan mita a kan lamarin. Ranar Talata da yamma, Mama ta fito daga ɗakinta, tana yi wa Saddam mitar, Laila tun safe ta fita amma haryanzu ba ta dawo ba. Ya ce "To ki kira lambar wayarta mana" "Na kira bata shiga, Ubangiji Allah ya shirya mini wannan yarinya, ni duk godiyata ga Allah da ya zamana ba wani abin ashshan take aikatawa ba, amma 'ya mace dole sai da saka ido ai" Saddam ya ce "Mhmm, In dai Laila ce, tana can neman abin wallafawa a shafukanta ne, za ta dawo na san, iyaka idan ta dawo ki zane ta wallahi" "Ba zan dake ta ɗin ba, ziga zigi"  Mama ta yi maganar tana hararsa. Ya ce "Daga bayar da shawara? Allah ya baki haƙuri ai kun fi kusa" Sai dai abu kamar wasa, har magariba babu Laila babu dalilinta, wanda hakan ne ya ƙara ɗaga wa Mama hankali, ba ita ba har da Saddam, babu shiri ya fita yawon neman ta. Ga shi ita ba ƙawaye ne da ita ba, babbar ƙawarta Murja su na gama makarantar Sakandire aka yi mata aure, maƙwabciyarsu ce, da aka yi mata aure sai ta ci gaba da abotar da Bala, wanda yake Yayan Murja, wanda shi ne ya sanya mata sha'awar harkar sarrafa waya da kuma aikin jarida. Laila ce rufe a cikin cell, sai rarraba ido take yi, ta kalli yadda duhun magariba ya fara yi. Ta jijjiga ƙarfe cell ɗin ta ce "Yallaɓai ka yi wa Allah da ma'aikinsa ku sake ni na tafi, babata dattijuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, hankalinta yana nan a tashe na sani. Wannan kamun da ku ka yi mini kun take mini hakkina fa" Babu wanda ya kula ta, daga cikin office wani ɗan sanda ne a zaune, sanye da uniform ya ɗaga wayarsa ya daddana ya saka a kunnensa. "Allah ya taimaki honourable" "Yauwwa ya aikin?" "Alhamdillah, game da yarinyar nan ne, haryanzu ba ka ce komai ba" Honourable ya ce "Eh ina sane, ku ajiye mini ita sai na waiwaye ta. Ba dai ba ta da kunya da mutunci ba, za ta gane ba ta da wayo ku ajiye ta sai na waiwaye ta." Ɗan sandan ya ce "Na fahimce ka sir, amma ka san yarinyar nan mutane sun fara gane ta a shafukan sada zumunta, idan abu ya bayyana ka saka an tsare ta, kar abu ya zama surtu" "Ba na san aikinka ba ne?" "Sorry sir" "Ka ajiye ta sai na waiwaye ta, zan saka maka kuɗin mai" Gidan su Laila kuwa kwanan tsaye Mama ta yi, saboda rashin Laila a gida. Tuni Saddam da Bala suka kai ɓatan Laila gurin jami'an tsaro. Da sassafe Bala ya zo musu da labarin tana gurin 'yan sanda, dan haka Saddam ya zo su je. Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yanzu Laila ce ta kwana a hannun 'yan sanda me ta aikata har haka?. Ba zan iya zama a gida ba, mu je tare kawai" Saddam ya dubi Mama ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri ki zauna a gida, wallahi ko mun je babu abin da za ki yi, ki bari mu je mu gano tukuna" "In kwana yarinyar ba ta gida, ta kwana a hannun 'yan sanda ka ce mini ba zan bi ku ba" Bala ya ce "Saddam ina ga ka bari kawai mu je tare, hankalinta sai ya fi kwanciya" Ba dan Saddam ya so ba, ya ƙyale Mama ta yafo mayafinta suka tafi. ***** Alina na ta son sake tambayar Nadiya, inda za su tafi idan sun bar garin, amma ta fasa ganin yadda Nadiya ta nuna mata ba ta son tambayoyin. Sai da Nadiya ta dangana da kai Alina Asibiti, aka bata magunguna da allurai, suka taho gida. Da kyar Alina ta yi sallar isha'i ta kwanta, saboda baccin da take ji, a sakamakon magungunan da ta sha. Baccinta ya yi nisa, ta din ga jin motsi da ɓuruntu a cikin gidan, a hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idonta. Gani ta yi an haske ta da wata irin fitila mai matuƙar haske, sai ta kasa tantance mafarki ne ko gaskiya. Muryar Nadiya ta ji tana faɗin "Kar ku taɓa yarinyar nan, wallahi ba za ku iya ganin bayan Ismail ba. Babu ruwanku da ita. Ba dai shi ka ke son ka kama ba, ka kama shi, amma kamun da ka yi masa shi ne kuskure mafi girma da za ka aikata a rayuwarka". "Shut up, da harbina za ki yi kenan?" "Dole na kare kaina, abin da baka sani ba, tuntuni Isma'il ya san wane ne kai. Kar ka yi abu da ka, baka san abubuwa da yawa ba, zaka aikata mummunan kuskure" A hankali Alina ta buɗe idanunta, ta yinƙura, ta miƙe tsaye a razane da ƙarfinta, tana son ganin suwaye suke wannan jayayyar da Nadiya, ammaba ta kai ga hakan ba, ta ji an shaƙa mata wani hankici ta baya, take ta ji ɗiff ta daina gane komai. Duhu ya ƙara mamaye ganinta. 1k ne a telegram. Ayshercool 08081012143 *Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar* *Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;* 1. Graphic design 2. Magungunan mata 3. Sabaya 4. Turaren wuta 5. Fara 6. Candies 7. Skin care products 8. Importation 9. Snacks 10. Yoghurt 11. Oil perfumes 12. Bead work 13. Hair cream/oil 14. Dabarun kiwon kaji 15. Huluna 16. Spice's 17. Dabarun sana'ar kayan kitchen 18. Noma a zamanance 19. Dabarun kasuwanci Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin. 08081012143 08069611181 07037977211 https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g SARA DA SASSAƘA... YOTA 002 AYSHERCOOL Page 15 Hankalin Maman Laila ya yi mummunan tashi, ganin a inda Laila take. A babbar headquarter yan sanda ta jiha aka kai ta. Shi ma sashen da aka kaita, aka gaya musu wanda case ɗin yake hannunsa baya nan sai dai su jira. "Yanzu Saddam a gurin nan duk maza yarinyar nan ta kwana? Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Wai laifin me ma ta yi ne?" Saddam da ransa yake a ɓace shi ma ya ce "Mama tare da ke fa muka zo gurin nan, nima ban san abin da ta yi ba, sai dai mu jira mu ji me za su ce" Bala ya ce "Ki yi haƙuri Mama, da yardar Allah yau zamu tafi da ita." Duk magiyar da Mama ta yi, aka hana su ganinta. Har azahar su na gurin a zaune, sai bayan azahar wanda case ɗin yake a hannunsa ya zo, shi ma da ya zo ya ce musu su na da meeting da IG dan haka su ci gaba da jira. "Wallahi ban da mahaifina ma ɗan sanda ne a cikin aikin ya mutu, da sai na tarkata su na tsine musu wallahi yan wahala" Bala ya ce "A'a Saddam kar ka yi abin da za su ƙara shanya mu, kuma kowane aiki akwai ɓata gari, wani abin kuma yanayin aiki ne a haka, ba za a karya dokar aiki domin a burge ka ba" Saddam ya ja uban tsaki kawai yana sake turɓune fuska. Sai bayan la'asar aka saurare su, aka fito da Laila, fuskarta duk cizon sauro. Cikin nutsuwa ɗan sandan yake kallon Mama, ya ce "Hajiya yarinyarki ba ta ji gaskiya. Ta je ta taɓa manyan mutane, ta ce da saka hannunsu ake ƙwacen" Cike da takaici Mama ta ce "Laila, idan ba ki kiyayi rayuwa ba, wataran sai kin janyo an kashe mu. Allah wadaran wannan harkar jaridar taki. Wallahi ranka ya daɗe, babu irin jan kunnen da ban yi mata ba, a kan ta yi haƙuri ta bar wa Allah ba, amma ta ƙi. Ku dubi girman Allah ku yi haƙuri. Marainiya ce kuma 'yarku ce, mahaifinta tsohon ɗan sanda ne yarku ce" Ya kalli Laila ya ce "Yarinya, kina da ƙanan shekaru, ki mori rayuwarki ta hanya zuba ido ga duk abin da ba ki da ikon gyara shi, idan ba haka ba, wahala za ki sha a banza." Laila ta sunkuyar da kai ta ƙi magana. Ya daddana waya ya kira wata lamba ya kara a kunnensa. Bayan sun gaisa ya ce "Honourable batun yarinyar nan ne, dan Allah a yi haƙuri, ga mahaifiyarta tana ta kuka tana bayar da haƙuri, dan Allah su na neman belinta" "Kar ka kuskura, ba zai yiwu ba, ai sai na banbance mata aya da tsakuwa, ko da wasa aka sake cewa ta fito ta yi soki burutsu irin wannan ba za ta yi ba" "Amma ga mahaifiyarta a gurin ba dan ita ba... "Babu ruwana na gaya maka, sai na wulaƙanta yarinyar nan, za ta ga ƙarshen rashin hankali" Ɗan sandan ya kashe wayar. Mama ta riƙe haɓa, ta ce "Yanzu a kan wannan yar da ya haifa yake iƙirarin zai wulaƙanta? 'yar da ya haife ta? To Allah ya kyauta idan Allah bai wulaƙanta ta ba, babu wani wanda zai wulaƙantata" "Shiyasa ake cewa, ku din ga ja wa yaranku kunne, ku din ga ba su tarbiyya su din ga iya bakinsu" "Ku yi mata duk abin da za ku yi mata, kai ka ga alamar rashin tarbiyya a tattare da ita? Tsawon shekaru mahaifinmu na yi wa ƙasa hidima aikin ɗan sanda, ɗan abin da ya mutu ya bar mana, wasu sun yi kashe mu raba a tsakanin su, kuma a ce kar mu yi magana ƙasa za mu ci mu rayu? Idan hidimar wani ta tashi a cikinmu wani zai yi mana ne". Saddam ya ƙarasa maganar jikinsa yana rawa saboda baƙin ciki. "Kai, ka zo har gurin aikin nawa ka nemi ka gaya mana magana, yaran talakawa tarbiyyar ce da ku? Zan saka a rufe ka wallahi" "Ba rufe ni za a yi ba kashe ni za a yi" Bala ne ya danƙi hannun Saddam suka yi waje, yana rarrashinsa. "Saddam mutanen nan, wasu ba mutunci ne da su ba, babu Allah a ransu. Ka rabu da su, na san abin da zan yi, ko ba yau ba zuwa gobe in Allah ya kaimu, Laila za ta fito" Haka ya rarrashi Mama ma, suka sai Abinci aka ba wa Laila suka koma gida, ya din ga basu ƙwarin gwiwa a kan yana da hanyar da zai fitar da ita. Tun da suka koma gida, daga Saddam har Mama babu wanda yake walwala. Duk da Mama na ta faɗan halin Laila na azabar kafiya. Shi kuwa Saddam daga baya bai ga laifin Laila ba, dan yarinya ce mai sauƙin kai mara hayaniya, amma akwai kafiya, kuma duk abin da ta wallafa ya san tana da cikakkiyar shaida da hujja a kan abin da ta yi. Bala kuwa shi ma rubutun ya wallafa a shafinsa, da bayanin cewar an kama Laila, saboda maganar da ta yi da sunayen yan siyasar da kama, da cewar an haɗa kai da su ana ƙwacewa mutane filaye. Duk da wasu na jin haushinta, amma kasancewar ayyukan da take yi a shafinta ba siyasa bane kawai, ta kan faɗakar, koyarwar addini, girke-girke motivational speaking, idan baka ƙaru da ita ta wani fannin ba, za ka ƙaru ta wani, dan haka nan da nan mutane suka din ga reposting abin da ya faru. ****" A hankali ta motsa, ta yinƙura domin tashi zaune, amma ta koma yuuu saboda wani irin azababben jiri da ciwon kai da ya ɗebe ta. Ta buɗe idonta a hankali ta din ga gani dishi-dishi, ga kanta da yake yi mata wani irin azababben ciwo. Ta koma ta kwanata ta yi lamo, a hankali komai ya fara washewa. Ta kalli gurin ɗaki ne na Asibiti, da gadaje kusan biyar a ciki, sai dai itakaɗai ce a ɗakin. Ga hannunta ɗaya sanye da ruwa. Hayaniya ta din ga jiyowa sama-sama, ana wani irin yare ana haɗawa da broken English. Sai kuma ta ji ɗif an daina sai alamar takun takalma. Ƙofar ɗakin aka buɗe, maza ne suka shigo zabga-zabga, sanye da kaakin soja a jikinsu. Sai dai a wanda suka shigo ɗin duk ya kere su a tsayi. Wandon sojoji ne a jikinsa, sai riga armless shirt army green. Gefen wandonsa a soke da wata 'yar ƙaramar bindiga. Ya ɗan tara suma a kansa, sai dai yanayin askin gaban kan tafi cika, zagayen kuma kwantacciyar suma ce, gwari-gwari dai yanayin askin da ake kira da balatoli. An yi wani abu mai kama da arrow a gefen kan. Babban abin da ya sake jan hankalinta bai wuce sarƙar da take wuyansa ba, da ya zura ta a cikin rigarsa, amma saman chain ɗin ba za ta manta da shi ba, lokacin da ya zo tana Asibiti amma ya musa mata, ya ce ba shi ba ne. Gefensa wani matashin ne da za su iya yin tsawo ɗaya da shi, hatta askin kansu iri ɗaya ne, sai dai kowanne kamarsa daban. Sai dai ta tuna ranar da ta je sayen leda shagon Mamman da yamma ta gansu tare. Kenan duk tsawon wannan lokacin da take ganinsa, wani abin ne shi daban ba abin da take tunani ba? Ashe Yaya Ismail ya fita gaskiya. Tana nan kwance suka ƙarasa har gaban gadon take, sai dai tana kwance kamar an dasa ta, ta kasa komai. Suka ƙarasa suka kewaye gaban gadon take. Gani ta yi tamkar an canza shi, gaba ɗaya ya juye daga Mamman ɗin da ta sani, suka shaƙu, da suffarsa da kamaninsa sun koma wani abu na daban. Fuskarsa a tsuke tamkar bai san hanyar inda ake bi a yi dariya ba, babu alamar annuri, sai ɗan rarraba manyan idanunsa yake yi da suka ɗan kaɗa suka yi jawur, duk da idanunsa sun saba ba ta tsoro, amma sai ta ga gara lokacin da ta san shi a Mamman, babu alamar afuwa ko sassauci a cikin waɗannan idanuwan. Wannan gashin na fuskarsa ma babu shi, fuskarsa tas take sai ɗan yarfin gashin baki kaɗan. A hankali take buɗe idonta tana lumshewa. Ya riƙe ƙugunsa yana kallon drip ɗin da yake shiga jikinta ɗis-ɗis. "Kai Mega kamar haryanzu she's unconscious" "Yeah" Ya faɗa a taƙaice, ya janyo side drower, ya ɗaukko file ya buɗe ya yi dube-dube, ya duba ya ɗauki ya biro, ya yi rubuce-rubuce a cikin file ɗin, ya mayar ya ajiye. Ya duba cikin kayan maganin da ke gurin, ya ɗauki wata allura, ya zuƙe ya fara zubawa a cikin drip ɗin. Miƙa ta yi tana yamutsa fuska, jin yadda shigar ruwan, tare da allurar ya burkita mata jiki gaba ɗaya, ta ji wani irin raɗaɗi, ƙoƙarin tashi ta yi saboda yadda allurar ta gigita ta. Ya saka hannayensa ya danne ta. A hankali jikinta ya saki, bacci ya ɗauke ta. Alfa ya ce "Mega, me ka ke yi mata haka kuma? Kar fa ta ƙarasa" Mega ya ce "Shut up" Ya yi maganar yana ɗan zaro masa ido. "An ƙi ɗin, ka san zuwa gobe in Allah ya kaimu Oga Musa za su zo, su ganta" Ya kalli sauran sojojin da suka zo tare, ya yi musu alama da su fita. Bayan sun fita ya dubi inda Alina ke bacci ya ce "Ta na da magrine headache, tana cikin damuwa da kuma tsoro. Akwai buƙatar ta huta sosai ƙwaƙwalwarta ta samu nutsuwa. Sai ta zama stable ne za a iya samun bayanan da ake buƙata daga gare ta" Ammar ya jinjina kai cike da gamsuwa. "To yanzu what next?" "Eh, zamu je gurin matar nan, ina son grabbing wasu abubuwan daga gare ta, ina buƙatar tattaunawa da ita" Ammar ya yi shiru yana kallon Alina, ya kalli Mega ya ce "Omega, ka san tsabar soyayya kun fara kama da yarinyar nan?" Tsaki Mega ya ja, ya saka ƙafarsa ɗaya, ya daki ta Ammar da ƙarfi tare da furta "You are not serious" Ammar ya biyo shi yana murmushi ya ce "Wallahi sai na rama" ***** Laila na zaune a cikin cell, wani ɗan sanda ya buɗe ta ya ce ta fito. Ta tashi jiki a sanyaye ta fito. Ɗan sandan jiya ne ya saka aka kawo mata kayanta ya dube ta ya ce "Kin ci sa'a, an bayar da umarnin gaggawa a sake ki, idan kin ga dama ki je ki ci gaba da iskanci. Ku ba 'ya'yan kowa ba amma kun fi kowa rashin mutunci. Kuma a nan da awa arba'in da takwas, ki koma ki yi video ki ba wa Honourable da sauran mutanen da ki ka kama sunansu, haƙuri ko kuma abin da zai biyo baya ba zai yi miki daɗi ba" Ba ta ce komai ba, ta karɓi jakarta za wayoyinta, ta fito reception, ta waiwaya ta kalli ɗan sandan ta ce "Na gode sosai Sir, abin da ya faru da ni ya ƙara mini ƙwarin gwiwar gwagwarmaya, ka gaya wa Honourable zan yi video na ba shi haƙuri. Ba zan sake ba 'ya'yan talakawa mun bar wa masu duniya su ci gaba da cin jahannama a cikinsu" "Laaa" Ɗan sandan ya faɗa bakinsa a sake. "Sir yarinyar nan fa ba ta daku ba" "A'a ki je ga ki ga su nan ai, a banza za su illata rayuwarki, babu abin da aka isa a yi kuma, sauka lafiya" Ɗaya ɗan sandan ya ce "Ikon Allah, gaba ɗaya fuskarta ta salihai ce" ISP Sagir ya ce "Ta munafukai dai, ni na yi mamaki, daga sama fa aka bayar da umarnin sakinta" Suka ci gaba da tattaunawa, Laila kuma ta tsare abin hawa ta tafi gida. ***** Ɓangaren su Rahama kuwa, dawowar Sadauki inda ake tsare da su, ya ɗan sama musu sassauci, ana ba su Abinci an daina dukansu. Tun da macijin nan ya sari Rahama, ba ta sake taka ƙafarta ba. Sai dai yau da ya dawo daga yawonsa, daga nesa da su kaɗan ya tsaya a kan babur, ya yi mata nuni da ta zo. Ta kalle shi ta kalli ƙafarta, ya sake yi mata alamar ta zo. A hankali ta yinƙura ta daddafa bishiya, ta miƙe ta tsaya ta ji ƙafafunta tamkar an ɗaura mata duwatsu. "Ta ko da Bismillah, da sunan Allah" Ya yi maganar yana zuba mata ido, ta fara takawa a hankali cikin tsoro, yana zaune a kan babur ɗin yana kallonta. Ji take yi tamkar ta faɗi, amma ta daure ta ci gaba da takawa har ta je inda yake ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta. "Yayi kyau,koma ki je ki zauna" Ta sake juyawa ta koma, har za ta zauna cikin ɗaga murya ya kira sunanta "Rahama" Ta waiwayo. "Waa ɗoo" (Zo nan) Ta sake dawowa, sai cukuikuye jikinta take yi a cikin babbar rigarsa da ya bata. "Ya jikin naki?" "Da sauƙi" "Alhamdillah, ba wata matsalar?" Ta jinjina kai. Ya ce "Ba ki da baki ne?" "Babu matsala" Ta yi maganar tana sunkuyar da kai. "Allahumma yashfiki, je ki zauna Allah ya sauwaƙe. Je ki ki zauna" Ta amsa da Amin, ta juya za ta tafi. "Ke zo nan" Ta waiwaya ta sake tsayawa. "Duk abubuwan alkhairin da na yi miki, babu ɗaya da za ki iya cewa kin gode?" "Na gode" "Wuce ba na so" Ya yi maganar yana kafe babur ɗin sa ya sauka daga kai. Ita dai ba ta sake cewa komai ba, ta koma gurin zamanta ta zauna. ***** Arewapen Zaune suke su biyar a cikin office ɗin, kowannensu sanye da kaakinsa na aiki. Sun baje wani map a kan table su na dubawa. Ɗaya ya numfasa ya ce "Haryanzu mr. President, da al'ummar ƙasa, su na jiran ji daga gare mu, duk da pressure da aka saka mana, dole ne mu yi amfani da hikimomi da dabaru, dan kar rayuwar yaran ta salwanta" Suka amsa da gaskiya ne. "Commadore Edward, za mu jira, ku duba mana exact gurin da yaran suke, mu kuma za mu shirya duk abin da yakamata. Duk wani abu da zamu yi, za mu yi shi ne within 8days, mu fitar da kyakyawan result" Commadore Edward ya ce "Babu case, komai zai tafi yadda aka tsara, akwai yiwuwar su canza guri, muddin suka farga mu na neman inda suke. Amma gano inda suke ɗin shi ne babban target, ba wani abu" Suka kammala tattaunawa, suka yi musabaha da juna, sannan suka naɗe map ɗin suka bar office ɗin. ***** Laila ce ta yi sallama a gidansu, Da sauri Mama ta fito daga kitchen, cike da son tabattar da Lailan ce. Tana tozali da Laila kuma sai ta tsuke fuska. "Sun ga dama sun sako kin kenan?" Laila ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba. "Yanzu kin ga sakamakon mai bijire wa maganar iyaye ko? Babu yadda ban yi da ke ki bar maganar nan ba, amma ki ka ƙi. Ke ba kowan kowa ba, ba ki da wani gata sai na Ubangiji, amma fitina ta yi miki yawa Laila. Ni dai lafiya na rabu da iyayena da mijina, balle na ce ko hakkinsu ne yake bibiyata ya sanya ba kya jin magana ko kaɗan. Saddam da shigowarsa kenan, ya ce "Haba Mama dan Allah, daga dawowarta ki yi haƙuri ta huta ta ci abinci mana" Mama ta juya kansa da faɗan "Ba zan bari ta huta ɗin ba, ni kwana biyu a jere hutawar na yi? Yanzu abin arziki ne a ce mace ta kwana a hannun 'yan sanda har kwana biyu, gurin 'yan sandan ma, sashen kula da manyan laifuk, ita ba kisan kai ba, ba fashi ba?" Saddam ya yi wa Mama shiru, ya dubi Laila da take kuka, ya ce "Shigo ki zauna rabu da ita" "Eh a rabu da ni mana, tun da ga mahaukaciya tana faɗa ko? Ku je ku yi abun da ku ka ga dama, babu mai kashe ni lokacina bai yi ba" Saddam kuwa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri, ɓacin ran kin kwana biyu a gurin 'yan sanda ne ya sanya take yi miki faɗa, amma ki yi haƙuri. Ina fatan ba su yi miki komai ba dai ko?" "Sun mare ni" Ta furta tana sake fashewa da kuka. Saddam ya yi shiru yana kallonta, wani abu ya tokare masa a ƙirji, idanunsa suka yi ja. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar ki gaya mata an dake ki, ki yi haƙuri ni na fahimce ki, hakkinmu ne aka danne, shi ki ke fafutuka a kai, zan taya ki da yardar Allah ko ba za mu yi nasara ba, duk abin da ki ke nema, ki yi mini magana zan taimaka miki, amma ki daina kuka ki yi haƙuri" Ta jinjina kai tana share hawayen da yake gangarowa a kan fuskarta. Ya miƙe tsaye ya ce "Bari na je gurin Umman su Bala, na karɓo miki ruwan zafi ki yi wanka, ki ƙyale Mama ta gama faɗanta ta huce" Jinjina masa kai kawai ta yi ya fice. ***** Sannu a hankali suke ratsa tsakanin ofisoshin, har suka ɓulla can wani ɓangare da babu wadatattun ma'aikata a gurin. "Alfa, tun da muka kawo mutumin nan fa, ba a sake bari mun gan shi ba" Alfa ya ɗan sosa girarsa ya ce "I wonder, ina ta so na yi maganar amma dai na yi shiru, amma kamar na ji Oga Musa kan ya tafi yana cewa, za a canza masa guri, maybe ma a bar garin nan da shi gaba ɗaya" Mega ya ja ya tsaya, ya ce "A bar nan garin da shu a kai shi ina?" Alfa ya ɗage kafaɗa tare da faɗin"I don't know" "Amma kana ganin ya dace a yi hakan, ba tare da mun ji komai ba, mussaman ni da na yi duk ƙoƙarin?" "And someone is taking the credit of your work ba, so sad. Na tausaya maka Mega" Abdallah ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "We shall see" Ya ƙarasa maganar ana buɗe musu wata ƙofa, da gurin yake ɗauke da duhu. Mai tsaron gurin ya sara musu, sannan ya sake buɗe musu wata ƙofa, mai kama da ta fursinoni. Suka ajiye wayoyinsu a waje, da bindigoginsu, aka caje su. Mai cajesun ya damƙo wani abu a aljihun Alfa. Alfa ya zura hannu ya ɗaukko ƙaramin biro a jikinsa, aka karɓi biron aka ajiye, sannan suka shiga. Tana zaune ta takure guri ɗaya, tamkar mai taɓin ƙwaƙwalwa, ta ɗago ta yi musu kallo ɗaya, ta mayar da kanta ƙasa ta sunkuyar. Abdallah ya gyara zaman hular sojojin da ke kansa, ya ƙarasa gabanta ya durƙusa yana kallonta. Sai dai ta sunkuyar da kanta, ta ƙi ɗagowa su haɗa ido. "Nadiya ko?" Ya furta yana tsare ta da idanunsa. Ta ɗago a hankali ta dube shi ta ce "Au ba ka ma tabattar da sunan nawa ba?" Mega ya girgiza kaiya ce "A'a, ina son sake samun tabbaci daga bakinki ne. Ina son zan yi miki wasu tambayoyi ne, da nake buƙatar ki bani haɗin kai, ki yi mini cikakken bayani" Ta yi murmushi tare da maimaita faɗin "Tambayoyi? Ni za ka yi wa tambayoyi na baka amsa? Shikenan ina jinka faɗi" "Suwaye iyayen Alina na haƙiƙa?" Ta yi shiru tana ɗan kaɗa kanta, sannan ta ɗago fuskarta ɗauke da murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa ta ce "Kai da uban gayyar yake hannunku, yaya za ku zo ku na tambayata?, ai shi ya fi kyautuwa ku je tambaya? Shi ne yake da amsar tambayar ba ni ba" Mega ya tsuke fuska, saboda yadda ya fara ƙuluwa da murmushin da take yi, ya ce "Ke nake tambaya yanzu" "Ba ka da ikon tambayarsa, saboda an killace shi an hana ka ganinsa ko? Haryanzu fa ba ma a yarda da kai ba, na cewar ka kama Kacalla Sumale ba. Sannan ba ka da tabbacin yana ina a halin yanzu. Na san ka fara jin kanka kai wani jarumi ne, saboda ka kama shi, tabbas ka cancanci jinjina na ɗan lokaci, dan babu wanda ya taɓa gano gaskiya da ka gano a cikin duhu, sai dai gaskiyar ta suɓuce a hannunka, kuma ita ma ta yi duhu ta sake ɓacewa ganinka a cikin duhun. Wannan kuskuren da ka yi zai iya zama ajalinka, dan duk wanda ya gano shi, sai ya kawar da shi daga doron duniya, idan ba wanda ya yarjewa ya gano shi ba. Abu na gaba kuma muddin Kacalla na rayuwa a doron duniya, zai iya zubar da kowane irin jini, zai kashe kowane ne, domin Alina! Ka tafka babban kuskure mai muni da hatsari gare ka da rayuwarka" Gaba ɗaya suka yi shiru su na kallonta. Ta jinjina kai ta ce "Ƙwarai, zai ci gaba da bibiyarka, zai yi farautarka babu dare babu rana, saboda ita. Kacalla Sumale ya shallake duk yadda ka ke tunani, yana da abin da baka tunani. Ni kaina a tsawon lokacin da na riƙe Alina da ina da hali, sai na ba ta guba na kashe ta, saboda tsananin kishin yadda yake ƙaunarta fiye da ransa. Sai dai ina kyautata zaton baƙin alhaki ne yake bibiyarsa, saboda iyayen Alina ne jini na farko da Isma'il ya fara zubarwa a Duniya da hannayensa!" Tsit suka yi gaba ɗaya su na jin ta, tare da yin jarumtar ɓoye mamakinsu, mussaman ma Mega. Alfa ya ce "Ke ban gane ba, iyayenta ne mutane na farko da ya fara kashewa, to ta yaya aka yi ya ɗauke ta ya riƙe ta? Suwaye iyayen nata? Sannan kema kuma wace ce? A ina sauran ahalinta suke?" "Wannan tambayoyin duk shi ne zai ba ku amsar su. Abin da ba ka sani ba shi ne, Ismail ya san waye kai. Shi ne ya kashe Malam Ɗayyabu bayan da ya yi masa ƙarya. Bai yi maka komai bane ba, saboda gudun halin da Alina za ta iya shiga. Sannan ai ina aikinka a kansa ne kawai, tun da ka gama aiki a kansa babu buƙatar ka zurfafa a kan Alina babu ruwanka da ita. Ka sani ya gama tsara komai, a kan matakin da zai iya ɗauka a kanka, bai kai ga aiwatarwa ba, ka riga shi motsawa. Ina mai baka tabbacin zai fita, dan Kacalla Sumale ba mutum ɗaya ba ne ba, mutane da dama masu burin cimma muradai daban-daban a cikin mutum guda, kuma muddin ka na yawo a doron ƙasa ko shi ko na cikinsa za su hallaka ka, saboda ka gano abin da duk wanda ya gano mutuwa yake yi. Har ya buɗe baki zai yi magana, ya jiyo muryar mai tsaron Nadiya ya ce "Oga Mega time fa ya yi, kar a zo a kama mu, daga ni har ku mu shiga matsala" Mega bai iya cewa uffan ba, ya miƙe tsaye,, Alfa kansa bakinsa tambayoyi ne a ciki, gaba ɗaya maganganun Nadiya sun ɗaure musu kai, amma haka suka yi waje suka bar gurin. Mega ya dafa kafaɗar Mai tsaron ya ce "Thank you Nelson" "Welcome sir" Ya yi maganar cikin girmamawa yana yi wa Mega murmushi. Yadda yake tafiya yana dukan ƙasa da ƙafafuwansa, tamkar ƙasar ce ta yi masa laifi. Ba tare da ya sani ba, haka yake ta wani irin huci, tamkar zai shiɗe saboda tashin hankali. Sai da suka ƙarasa office ɗin su Mega, Ammar ya rufe ƙofa ya dubi Abdallah ya ce "Mega wata sabuwa in ji 'yan caca, ka yarda da maganganun matar nan kuwa?" Ya jinjina kai ya ce "Biri ya yi kama da mutum, but was fooled Alfa, meyasa tun da muka kawo shi, bamu sake ganinsa ba ko jin inda yake ba, aka hana mu ganinsa mussaman ma ni da muka yi aikin tare da sauran jami'an?" Alfa ya ce "Yes tambaya ce mai ma'ana, amma ni ban ji na yarda da ita ba, amma ni abin da ya bani mamaki, meyasa ya kashe iyayen yarinyar? Me kuma ya sanya ya ɗauke ta ya riƙe, yake yi mata irin wannan mugun so? Kai Mega akwai maganganu da dama a bakin matar nan da suke buƙatar fashin baƙi. Suwaye mutanen da suke cikin Kacalla Sumalen, suwa yake yi wa aiki?... Ayshercool 08081012143