SARKIN SADAUKAI 1 Littafi na ɗaya 1 Sarkin marubuta yaƙi MANSUR USMAN SUFI Wthapp number & call 08137237071 Saurayi ne kyakkyawa na gaban kwatance mai kimanin shekaru ashirin da ɗoriya sanye da tufafi na fatu riga da wando tun daga sama har ƙasa, gashin kanshi ya zubo izuwa bisa kafaɗunshi har yana ɗauke da wani yaro mai shekaru goma a Kafaɗarshi, Yana faman tsala gudu babu sassauci a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin dogayen bishiyu, Duwatsu, Ƙoramu,da kwazazzabai, Saboda ƙarfin gudun da ya ke yi har tsallake ƙananan duwatsu ya ke yi. ko da ya shafe sa'a ɗaya yana gudun sai ƙarfin gudun nashi ya ragu ainun gajiya ta fara ka mashi. kwatsam bazato babu tsammani sai ya ga waɗansu irin masifaffun kibbau na sauka a dajin tamkar ruwan su ake daga sama. ko da ganin hakan sai ya shiga amfani da hikimar shi ya na zillewa kibbau ɗin cikin Matuƙar zafin nama naban al'ajabi tamkar ɗaukewar ruwan sama a ka daina harbo kibban. ko da ganin hakan sai saurayin ya nufi wata sarƙakiya mai cike da duhuwa a dajin ya sauke yaron daga Kafaɗarshi ya sayan shi cikin duhuwar ta yadda babu wanda zai iya ganinshi sannan ya juya ya yi kamar taku huɗu daga inda ya ke sannan ya ja ya tsaya yana mai jiran yaga abinda zai faru yana waige waige-waige da dube-dube. kwatsam sai ga waɗansu irin girda girɗa-girɗan dakaru masu kirar samudawa Masu tarin yawa suna fitowa daga duhuwar dajin. Dakarun suna da girma tamkar toron giwa suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro fuskokin su a sanye su ke cikin hulunan ƙarfe idanuwan su kadai a ke gani a hannayen su suna rike da miyagun makamai dangin su gatari, Takobi, Sungumi da Majaujawa. kafin saurayin yayi wani Yunƙuri dakarun sun rugo izuwa gare shi suna ihu da kururuwa mai firgitarwa ana haduwa a ka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini, a na cikin wannan yaƙi ne wani badakaren ya shammaci saurayin ya gabza mashi naushi a fuska ya bazar dashi a kasa Kawai sai shugaban dakarun ya uwarci wasu dakaru suka duba cikin duhuwar dajin sai gasu sun fito da yaron da saurayin ya ɓoye, kawai sai shugaban ya cillawa badakaren dake rike da yaron wata wuka ya riƙe shi kuma ya ɗora kaifinta wukar a kan wuyan yaron domin ya yi mashi yankan Rago wani barde dake kusa da shi ya a jiye wani farin kasko domin jinin yaron ya zuba a cikin shi. Kafin badakare ya yanka wuyan yaron da KAIFIN TAKOBIn shi kwatsam! bazato babu tsammani sai wani mahayi ya yi fitar burgu daga cikin duhuwar dajin a bisan wani ingarman Doki Fari Sol!. kafin badakaren ya yi wani yunƙuri mahayin ya zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayanshi ya sare ma shi wuya kan shi ya yi fitar burgu, Gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica. Sa'adda sarkin yaƙi lahmar yayi arba da gawar badakaren sai ya dakawa sauran dakarun tsawa yana mai yi musu nuni da su farma mahayin a lokaci guda dakarun sukayi ɗauki kan shi, A na haɗuwa da juna aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro daban al'ajabi. Nan take ƙarar karafniyar Ƙarafa ta cika dodan kunne, Ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin gaba ɗaya, Duk wajen da Mahayin ya sanya a gaba sai dai kaga mazaje na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga, Dakarun suna kai mashi miyagun hare-hare cikin matukar zafin nama, sa'adda wannan yaro yaji wajen ya kacame da artabu sai kawai ya Durƙusa ƙasa ya kama rarrafe ya ɓoye a bayan wani dutse. kafin shuɗewar Daƙiƙa saba'in mahayin ya hallaka fiye da kaso shida bisa goma na dakarun, Al'amarin da ya yi matuƙar firgita sauran dakarun kenan suka fara ƙoƙarin cika wandonsu da iska, Shi kuwa sarkin yaƙi ko da ya ga irin muguwar ɓarnar da mahayin ya yi mashi sai ya fusata ainun. Duk wannan fafatawa da a keyi saurayin da ke Ƙoƙarin ceto rayuwar yaron yana kwance magashiyan yana kallon abin da ke wakana tsakanin mahayin dasu sarkin yaki zuciyarshi cike da matuƙar mamaki yana mai cewa acikin ranshi. Ya a ka yi wannan mahayi yasan cewa ina cikin bukatar taimako?, Amsar tambayar da ya kasa bawa kan shi kenan, Lokacin da sarkin yaƙi yaga cewa mahayin ya kusa ƙarar da dakarunshi sai kawai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harbo shi daga cikin baka yana saman ya zare waɗansu zaratan takubba a gadon bayanshi ya dira a kusa da in da mahayin ya ke a lokacin da sauran dakarun su ka ja da baya a ka fara kallon-kallo tsakanin su. Abin tambaya a nan shi ne daga ina wannan saurayi da yaron suka fito?. Kuma mene ne dalilin da ya sanya waɗannan dakarun ke farautar rayukan su. Dalilin hakan kuwa shi ne :- ***** Fiye da shekaru dubu biyu da arba'in da huɗu a yammacin gaɓar tekun Bahar-maliya an yi wata ƙasaitacciyyar ƙasa da a ke yiwa laƙabi da zawatul-ifdal. Kasar madinatul-ifdal ta bunƙasa a arzikin noma da kiwo gami kasuwanci, Daɗin daɗawa kuma sun tara ZARATAN MAYAKA masu juriya a filin yaƙi. Sarkin da ke mulkin ƙasar yakasance gawurtaccen jarumin Matsafi, shekarun shi hamsin da ɗoriya, A na yi mashi laƙabi da Shazwan ibn zamaran, Sarki Shazwan yana da matar aure guda ɗaya jal wacce ta haifa mashi 'ya guda ɗaya mai suna sulairat. Gimbiya sulairat takasance kyakkyawar gaske da labarin kyawun ta ya yaɗu a nahiyar baki ɗayarsu. Ta gaji mahaifinta sarki Shazwan a fagen sadaukantaka da ilimin tsafi. Mutanen ƙasar madinatul-ifdal suna zaune lafiya babu tashe-tashen hankula sai dai kash! akwai wata matsala guɗa ɗaya da take ci musu tuwo a kwarya. Wannan matsala ita ce bayyanar wata GOBARAR DAJI duk bayan wata shida a shekara sau biyu take zuwa. Gobarar ta na samuwa ne daga wani daji da ke maƙwaɓtaka da kasar. Duk sa'adda da annobar ta bayyana tana haddasa hasarar rayukan jama'a dukiyoyin su haɗu da rushewar gine-gine. Bokayen nahiyar gami da masu bincike sun ce GOBARAR DAJIn na bayyana ne sakamakon waɗansu hatsabiban aljanu, Wasu kuma su ka ce wani shuumin boka ne ke haddasa GOBARAR DAJI ma'ana dai babu matsaya guda ɗaya ingantacciya game da annobar. Sa'adda Sarki Shazwan ya ga cewa wannan annoba taƙi ƙarewa kuma ya ziyarci manyan bokaye amma babu wata mafita. Sai kawai ya yanke shawarar ya tara gaba ɗaya bokayen shi, Kowannen su ya shiga gudanar da bincike na tsawon mako biyu domin nemo bakin zaren. A ranar da mako biyu ya cika ne bokayen suka hallara a wani daƙin sirri bisa jagorancin shugaban bokayen wani dattijo ma'abocin kwarjini mai suna Dargas ibn Aumal. Sa'adda Sarki Shazwan ya ga cewa daƙin taron yayi shuru, Sai kawai ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki ya yi gyaran murya yace "yaku waɗannan bokaye masana ilimin tsafi shin ina sakamakon da binciken ya baku?. Game da mafitar abin da ya taramu a nan ?. Ko da jin wannan batu sai bokayen su ka yi shiru wannan ya kalli waccan aka rasa wanda zai ce uffan a cikin su, Daga can sai sarkin bokaye Dargas ibn Aumal ya Miƙe tsaye ya fuskanci sarki sannan yayi gyaran murya gami da gyara riƙon kwagirin dake hannunshi cikin murya irin ta Hamshaƙan Matsafa ya ce "Ya shugabana zance mafi rinjaye da bincike ya tabbatar mana shine Babu wani matsafi ko wasu miyagun aljanu dake haddasa GOBARAR DAJI face wani hatsabibin jarumi ɗan baiwa mai tattare da abubuwan al'ajabi a halin yanzu babu wani GWARZON MAYAKI kamarshi a wannan nahiya ana yi mashi laƙabi da HUBAIRU IBN MURRASU ma'ana SARKIN SADAUKAI, HUBAIRU ya na rayuwa ne a cikin daji ba shi da abokin mu'amala da ya huce aljanu da dabbobi tun yana jariri mahaifiyarshi ta rasu bayan ta haifeshi a cikin dajin. Wannan dalili ne yasanya gaba ɗaya ɗabi'un shi irin na dabbobi ne yana da jarumtaka domin komai girman bishiya idan ya naushe ta take zata jijjigo har jijiyar ta ta faɗi ƙasa. Yana iya saɓa Zaki da Damisa a kafadarshi ya yi gudun rabin Sa'a batare da ya gaji ba. Komai tsananin yawan abokan gaba a cikin abinda bai gaza daƙika ɗari biyu ba yana iya ƙarar da su, Wani abin mamaki ga HUBAIRU shi ne shekarun shi basu haura sha bakwai ba da Haihuwa. GOBARAR DAJIn kuwa tana Bayyana ne a lokacin da Hubairu ke bawa wani tsuntsun tsafin shi horon yaki, Horan yaƙin da Hubairu ke bawa kan shi yana yi ne kawai domin kare martabar dabbobin dake dajin domin a Fahimtar shi sune zuri'ar shi, Domin bai taɓa ganin wani bil'adama a rayuwarshi ba. Sa'adda shugaban bokaye Dargas yazo nan ajawabin shi sai sarki Shazwan ya cika da matukar al'ajabi. Dargas yaci gaba da cewa bincike ya tabbatar da cewa SARKIN SADAUKAI zai fitowa sarari a wannan nahiya zai shigo cikin 'yan uwan shi bil'adama. Amma sai bayan ya kammala bawa tsuntsun tsafin na shi horon yaƙi, Tare da kammala karanta waɗansu dalasiman tsafi dake jikin wani zoben sihiri dake sanye a hannun shi na hagu, Adadin sirrikan tsafin dake jikin zoben shine iya adadin dabbobin dake dajin. Bincike bai bayyana a yaushe ne zai kammala karanta sirrikan tsafin ba Sai dai akwai hanya guda ɗaya da zamu bi wajen kawo karshen GOBARAR DAJI hanyar kuwa ita ce. Wajibi ne a yanka yaro makawo kuma Maraya, Za a yi amfani da jinin shi ne wajen zubawa a cikin rijiyar bauta da ke tsakiyar birnin mu. Wannan shi ne Abin da mafi yawan binciken sauran yan uwa na bokaye ya tabbatar. Sa'adda sarkin bokaye yazo dai dai nan a zancen shi sai sarki Shazwan ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa amma sai ya dubi boka Dargas a lokacin da ya koma bisa kujerar shi ya zauna yace buɗi baki ya ce dashi "Yakai masanin ilimin tsafi naji dukkan bayanin ka sai dai ina da tambaya guda biyu. Da farko ina so nasan a ina zamu samu yaro makaho kuma maraya?, Sannan ta Wace hanya zamu tsira daga sharrin SARKIN SADAUKAI a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan?. Ko da jin wannan tambaya sai sarkin bokaye yayi shiru yana mai zurfafa cikin kogin tunani, Daga can ya cigaba da cewa "Ya shugabana a halin yanzu yaron da za a yanka yana cikin dajin kasar ka tare da wani jarumi da ya ke kula da Rayuwar shu tun bayan rasuwar mahaifan shi, Game da amsar tambayarka ta biyu kuwa bayani ne mai tsawo da yake buƙatar bincike da dogon nazari, Yanzu dai abinda yafi muhimmanci da zamu gabatar shine farautar yaro makaho domin magance GOBABR DAJI dake tunkaro mu nan da mako shida, kasan masu iya magana na cewa idan duka yayi yawa na kai a ke karewa. Ya yin da boka Dargas yazo dai-dai nan a zancen shi, Sai sarki Shazwan ya cika da matukar farin ciki. Take bokayen suka yi bankwana su ka rabu a kan cewa zasu sake gudanar da bincike a karo na biyu a kan gano mafita game da SARKIN SADAUKAI, Sannan suka ɓace cikin alkalumman sihiri. Sai sarki Shazwan ya shafi wani kambun a damtsen shi da hannunshi na hagu ya ɓace bat tamkar bai taɓa wanzu wa ba, Bai bayyana a ko ina ba sai a cikin turakar shi. Koda bayyanar shi sai ya ƙwallawa wata kuyangar shi kira, Kuyangar ta bayyana a gareshi ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa. Sarki Shazwan ya dube ta ya ce. "ya Sunaila ina so ki tafi izuwa gidan Sarkin yaƙi ki sanar masa cewa ina son ganin shi yanzu cikin gaggawa. Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Shazwan sai kuyanga Sunaila ta sake risina wa ta ce "An gama ya shugaba na, Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta fice daga turakar da sauri, Kawai sai sarki Shazwan ya dunga kai komo a cikin turakar ya kasa zaune ya kasa tsaye. Yana cikin wannan hali ne Sarkin yaƙi ya bayyana a gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin ladabi, Sannan ya buɗi baki ya ce "Gani gare ka ya shugabana me ka ke da buƙata? Sarki Shazwan yayi gyaran murya sannan ya ce "Yakai Sarkin yaƙi lahmar kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi zuwa dajin dake ƙasa ta ka farauto mini wani yaro makaho ɗan shekara biyar. Farautar yaron shine zai tseratar da rayuwar gaba ɗaya al'ummar birnin mu daga GOBARAR DAJI, Zaɓi biyu gareka kodai ka kawo mini yaron a raye ko kuma ka yankashi ka kawo mini jinin shi. Ko da jin wannan umarni sai sarkin yaƙi lahmar ya ce "An gama ya shugabana cikin wannan zaɓi biyu da ka bani Dole ne ɗaya yakasance. Ko da gama faɗin sai sarkin yaƙi ya Miƙe tsaye ya nufi kofar fita daga turakar. Kallo ɗaya zaka yi wa sarkin yaƙi ka fahimci cewa ya cika mai karfi na Allah na isa, Duk da kasancewar shi saurayi amma yana da ƙirar samudawan farko, Ya tara Ƙwanji mai cike da curin tsoka tamkar duwatsu aka cusa ma shi a ciki ya na da doguwar fuska mai kyawu da kwarjini ƙasumba da gemu Baƙaƙe sidik. Idan ka ɗauke sarki da gimbiya a gaba ɗaya Birnin Madinatul-ifdal babu gwazon mayaƙi tamkar shi Kuma ya gaji sarautar ne a wajen mahaifin shi ma'ana sarautar ta su gado ce. Ko da ficewar Sarkin yaƙi lahmar sai ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu bisa dawakai suka fice daga cikin birnin madinatul-ifdal. Sa'adda su ka fice sai suka nausawa cikin daji suna lafiya cikin hanzari, Yar gajeriyar tafiya su ka yi su ka fara hango wata ƙaramar bukka a dajin guda ɗaya jal. Don haka sai suka kasu huɗu, waɗansu su ka yi bangaren Yamma,kudu,gabas wasu arewa, suna masu yiwa bukkar Ƙawanya. Cikin hanzari Sarkin yaƙi ya umarci waɗansu dakaru Mutum ɗari domin su shiga bukkar su buɗe su fito da a binda ke cikin ta. Ya yin da dakarun suka zo dai dai bukkkar sai suka kewaye ta waɗansu mutum ashirin daga cikin su suka kunna kai izuwa ciki. Kaico Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu domin inda waɗannan dakaru sun san abin da zai biyo baya da basuyi gangancin shiga bukkkar ba. Dakarun dake tsaitsaye suna jiran fitowar yan uwan su sai kawai suka ga ana wurgo gawarwakin dakarun daga cikin bukkkar. Al'amarin da ya fusata sauran dakarun kenan suka dunga kunna izuwa ciki, Amma sai yazamana gawarwakin su ake ta jefowa waje koda ihu basa yi an yi masu yankan rago Kafin wani lokaci fiye da rabin dakarun sun sheka barzahu. Ko da ganin hakan sai Sarkin yaƙi lahmar ya fusata ainun ya tako da kafafafunshi har izuwa bakin kofar bukkkar yana mai dakawa sau ran dakarun tsawa dakarun suka ja da baya, Sannan ya yunƙura da nufin ya kunna kai izuwa cikin bukkkar, Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai ya ji an gabza mashi wawan naushi a fuska saboda karfin naushin sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim!. Kafin ya yi wani yunƙuri kawai a kaga wani kyakkyawan saurayi ya yi fitar burgu daga cikin bukkkar kafadarshi rataye da wani ƙaramin yaro. Sa'adda dakarun suka yi arba da saurayin sai kuwa suka ce dawa Allah ya haɗa mu Kawai sai suka zare makaman su suka rufa mashi baya suna ihu da kururuwa mai firgitar wa, Ko da ganin hakan sai saurayin ya falfala da azababban gudu izuwa cikin dajin. Nan fa dakarun suka dunga kai mashi hare-hare ta ko ina amma sai yazamana saurayin ya na tsira, Duk yawan kibbau ɗin da su ke harba mashi sai yazamana yana zille masu cikin gwanintar yaƙi A na cikin wannan hali ne saurayin ya ɓace musu ya shige cikin duhuwa. Wannan shi ne dalilin daya sanya waɗannan dakaru ke biye da wannan saurayi mai ɗauke da ƙaramin yaro, domin su hallaka sa. ****** Lokacin da sarkin yaƙi ya yi arba da idanun mahayin sai yaji zuciyarshi ta buga da ƙarfi abinda ya faɗo mashi a zuciya shine ko da cewar bai ga fuskar mahayin ba amma yaji a jikinshi cewa tabbas ya taɓa ganin fuskar mahayin sai dai abin tambaya a nan shine a ina ya taɓa ganin mahahin kuma mace ce ko namiji amsar tambayoyin da sarkin yaƙi ya kasa bawa kanshi kenan kawai sai ya daga takubbanshi sama ya falfala da azababban gudu izuwa kan mahayin yana kwarara ihu. Ko da ganin hakan sai mahayin ya dako wawan tsalle daga inda yake ya kaiwa sarkin yaƙi lahmar wawan sara da takobinshi da nufin tsinke mashi wuya cikin zafin nama sarkin yaƙi yasanya takobinshi ya kare saran sannan suka ruguntsume da masifaffan yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance Wohoho! tabbas jarumtaka da sadaukantaka baiwa ce daga Allah komai hassadar mutum idan ya ga yadda gwanayen biyu ke tsallakewa miyagun hare-haren juna dola ne ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA. A zahiri ga wanda ya ke kallon yadda artabun ke wakana zai fahimci cewa sarkin yaƙi ya fi mahayin karfin damtse sai dai mahayin ya fi shi sanin salon yaƙi nanfa yazamana cewa jaruman biyu har daka tsalle su ke yi suna kaiwa juna hari. Wohoho! tashin hankali ba a sa mashi rana,GOBARAR ANNOBA kuwa idan ta taso babu mai ɗauke ta face Ubangiji, Nanfa yazamana cewa ba iya bishiyoyi da duwatsun da ke dajin ba hatta sauran dakarun suna cikin matukar tashin hankali domin bishiyun da ke karairayewa sakamakon artabun jaruman biyu suna yunƙurin murƙushe su ba shiri suka shiga guje-guje gami da ifice-ifice a na cikin wannan artabu ne wani tunani ya faɗowa mahayin,Tunanin kuwa shine matuƙar a ka cigaba da wannan artabu wannan jarumi dake kwance magashiyan. zai iya rasa rayuwarshi, koda gama tunanin hakan sai kawai ya shammaci sarkin yaƙi ya gabzamashi wawan naushi a kirji saboda karyfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau huɗu sannan ya kife a ƙasa. Kafin yayi yunkurin miƙewa tsaye mahayin ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya rikiɗa izuwa wata baƙar guguwa ya tashi izuwa sama ya keta gajimare ya bace bat!. Sarkin yaƙi ya miƙe tsaye zumbur kawai sai ya ga wajen wayam babu mahayin, Saurayin da wannan karamin yar, Cikin matuƙar takaici ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu a cikin wannan hali ne kwatsam! sai sarki shazwan, Sarkin bokaye Dargaz,waziri Rufyanda waɗansu zaratan dakaru suka rugo izuwa wajen a bisa dawakai suka yi turjiya, Sarki Shazwan ya kama linzamin dokin shi ya sauko ƙasa, Sarkin bokaye, Waziri, da sauran dakaru suka yi koyi dashi. Sa'adda Sarkin yaƙi lahmar ya yi arba dasu sarki shazwan sai hankulansu suka ɗugumzuma cikin matukar razani ya sunkiyar da kansa kasa na alamun jin kunya a matsayin sa na dirkar birnin madinatul-aɗfal wanda matukar ji da akansa a fagen jarumtaka, Amma ace bakon jarumi ya gagare sa tabbas wannan bakaramin abin kunya bane, Cikin alamun sanyin jiki ya tunkari inda su sarki shazwan suke tsaye, Tun kafin yace wani abu abu sarki shazwan ya dube sa cikin alamun tsananin fushi ya ce dashi, "Yakai dirkar birnin madinatul-aɗfal kayi sani cewa haƙika ka tafka babban kuskure da har ka bari wannan bakon jarumi ya tserar da rayuwar wannan yaro da saurayin da muke farauta, Yayin da sarki shazwan yazo nan azancen sa sai ya mayar da dubansa ga boka Dargas yace dashi "Ya abin alfaharin birnin madinatul-aɗfal ina so yanzu ka gudanar da bincike bisa halarar tsafinka Domin ka gano mini shin wane ne wannan mahayi da ya ceci rayuwar yaron da muke farauta sannan a halin yanzu suna in ne Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye ya zira hannun sa ɗaya cikin aljihun rigar sa ya ɗauke wani ɗan madaidaicin madubin tsafi da girman sa bai huce faɗin tafin hannu ba, Ya shafe sa da hannun sa na hagu yana mai karanto waɗansu dalasiman tsafi ya shiga gudanar da bincike, Sannan daga bisani ya ɗago da kansa cikin ladabi da girmamawa yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye cikin kakkausar murya yace"ya shugabana hakika mahayin da ya ceci rayuwar wannan yaro da muke farauta ya cika hatsabibi kodai wanda yasan sirrin mu ko kuma wani makusancin mu domin duk kokarin na gano sa abin ya faskara, Sai dai na gano cewa a halin yanzu suna gab da shiga gidan tsira wanda da zai sun shiga cimmusu abu ne mai matukar wahala. Sa'adda da boka dargas yazo yazo nan ajawabin sa sai takaici da bakin ciki suka mamaye zuciyar sarki shazwan ya dubi Sarkin bokaye yace "Ai sai kayi maza ka kai mu inda suke domin mu riske su cikin hanzari kafin su kai ga shiga gidan tsira, Kafin sarki yagama rufe bakin sa Sarkin bokaye ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna Sarki shazwan,waziri Rufyan da sauran dakarun da hannun sa na hagu take suka zama wani farin haske, Hasken ya dunƙule a waje guda, sannan ya tashi zuwa sararin samaniya ya ɓace cikin gajimare **** ***** **** Al'amarin wannan mahayi da ya ceci rayuwar wannan saurayi da makahon Yaron nan kuwa , Bayan ya karanto dalasiman tsafi sun ɓace ɓat basu bayyana a ko ina ba sai a cikin wani daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, Dajin yana ɗauke da gajerun bishiyoyi masu yawa da duwatsu,koramu haɗe da kwazazzabai, Kallo ɗaya mutum zai yiwa dajin ya fahimci cewa baza,a rasa wani abu mai cutarwa a cikin sa ba Koda bayyanar su sai mahayin ya zira hannun sa a aljihu ya ɗauko wata yar siririyar kwalba dake ɗauke da wani koren ruwa ya buɗe murfinta kawai sai ya miƙa wa saurayin yana mai umartar sa da ya shanye ruwan. Batare da fargabar komai ba ya karɓa ya kafa a baki ya kwankwaɗe ruwan, Faruwar hakan keda wuya sai ya ji gaba ɗaya ƙarfin jikin sa ya dawo tamkar babu wani rauni a jikin sa. Kawai sai ya miƙe tsaye zumbur ya na mai duban mahayin cike da matukar mamaki. Mahayin ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki yayi gyaran murya cikin tattausan murya yace" Yakai mafarauci Huzmal kayi sani cewa nasan cewa a halin yanzu zuciyar cike take da tambayoyi agareni Shin wane ne ni kuma me yasa na ceci rayuwar yaro Humair, Saboda haka ahalin yanzu ba lokacin da zan amsa maka tambayoyin ba ne saboda gagarumin aikin dake gaban mu na tseratar da Yaro Humair, Sa'adda saurayi Huzmal yaji wannan batu sai ya cika da matukar mamaki Abu na farko da ya faɗo masa arai shine Shin ya akayi mahayin ya san sunan sa , sannan ya kasa tantance Muryar mahayin mace ce ko namiji, Abin tambaya ma ana shine shin mene ne kudirin mahayin na ceton rayuwar mu? Amsar tambayoyin da saurayi Huzmal ya kasa bawa kansa kenan, Mahayin ya katse shirun da ya wanzu akaro na biyu ta hanyar buɗar baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna wata bishiya dake gaban sa akaro na biyu, Yana gama rufe bakin sa sai ga photon su sarki shazwan ya bayyana a jikin bishiyar suna tafiya a cikin gajimare cikin matukar sauri tamkar sun kasance aljanu ba bil'adama ba. Koda ganin Hoton sai mahayin ya sake karanta waɗansu dalasiman tsafi take su duka ukun suka ɓace ɓat basu bayyana a ko ina ba sai gaban wani kasaitaccen gida a cikin dajin, Gaba ɗaya ginin gidan an yi shi ne da zallar duwatsun wuta masu kwarin gaske, Yana ɗauke da tagogi barkatai ,da kofa guda ɗaya hal! Wanda aka sana'anta ta da zallar mulmulallan bakin karfen jauhari, Wacce inda za'a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ta ba, Cikin azama mahayin ya durfafi kofar gidan yana rike da makahon Yaro Humair a hannun sa, saurayi Huzmal na biye dashi, Yayin da aka isa daf da kofar gidan aka mahayin ya sanya hannun sa ɗaya ya shafi ginin gidan take wani rubutu da akayi shi da zallar zinare ya bayyana a wajen, Kawai sai mahayin ya karanta rubutun yana gama rufe bakin sa sai kofar gidan tayi wani irin ƙara da ya cika dajin baki ɗaya, Daga can sai kofar ta buɗe kanta,batare da wani jinkiri ba mahayin ya riƙe hannun yaro Humair ya kunna kai izuwa ciki, Saurayi Huzmal ya mara masa baya, su na shiga sai kofar ta mayar da kanta ta rufe ruf kamar bata taɓa wanzuwa ba. Lokacin da su saurayi Huzmal suka shiga cikin wannan kofa sai suka tsinci kansu a gaban wata kofar wacce ta nunka ta baya nauyi da fadi A gefe guda an ajiye wani teburin azurfa mai tsawon kamu huɗu, Teburin yana ɗauke da waɗansu manyan kubobi guda biyar da akayi su da zallar karfen jauhari suna sheki da ɗaukar idanu Komai kallon ƙurillar mutum bazai iya tantance kubobin ba Yayin da suka yi arba da su sai mahayin ya ɗaga kansa izuwa saman kofar take yayi arba da wani allon karfe da akayi rubutu a jikin sa da tawagar Za'afaran kamar haka, Yakai ma'abocin wannan gida kayi sani cewa wannan kubobi guda biyar dake ajiye a kan wannan teburi a cikin su ne zaka samu mabuɗin wannan kofa ta biyu, sai dai fa ina so kayi sani cewa matsawar ka ɗauki mabuɗin da bashi ne na kofar ba zaka faɗa izuwa cikin musiɓa maimakon shiga izuwa gidan tsira, Sa'adda mahayin yazo nan zancen sa sai hankalin sa ya dugunzuma ainun Abinda ya dugunzuma hankalin sa shine idan har yace zai tsaya bincika wacce ainihin Mabudin kofar su sarki shazwan zasu iya cimmusu, Haka kuma idan ya sanya kubar da ba itace mabuɗin kofar ba zasu halaka baki ɗaya, Wani abu daya kara dagula masa lissafi shine shirin tsafi baya taɓa tasiri a wajen Sa'adda mahayin yazo nan a tunanin sa sai hankalin ya dugunzuma ainun ya ƙurawa kubobin idanu yana nazarin su domin ya gane wacce ce mabuɗin kofar Sai da ya shafe tsawon dakika arba'in yana nazarin batare da ya gane wacce ce mabuɗin kofar daga cikin kubobin ba, Ana cikin wannan hali ne sai aka ji wani Irin ƙara ya cika wajen baki ɗaya, cikin hanzari suka waiga domin suga ko mene ne aikuwa sai suka ga ashe wannan kofa ta farko ce ke yin ƙaran alamar cewa zata buɗe wani ya shigo cikin gidan, Saboda matukar razani mahayin bai san sa'adda ya miƙa hannun sa bisa teburin azurfar ba ya ɗauki ɗaya daga cikin kubobin ya zira ta a cikin wani kwaroron rami dake tsakiyar kofar ya shiga murɗawa da dukkan karfin sa domin ya buɗe kofar, Shiru ka ke ji tsawon dakika hamsin babu alamun buɗewar kofar, Kawai sai aka ji kofar dake bayan su ta buɗe sai ga su Sarki shazwan sun bayyana Da yake daga inda su sarki shazwan ke tsaye zuwa inda su Huzmal suke akwai tazara mai yawa sai su sarki shazwan suka falfalo da azababban gudu izuwa kansu suna masu zare makaman yaƙin su. Sa'adda mahayin yayi arba da su sarki shazwan suka ya sake ɗimauce wa ya cigaba da murɗa kubar iyakar karfin damtsen sa har gumi ya fara keto masa, Shi kuwa saurayi Huzmal sai ya ɗauki Yaro Humair ya goya sa a gadon bayan sa domin ya ga abinda zai faru har kwallar takaici ta zubo masa, Har yazamana tazarar dake tsakanin su dasu sarki shazwan bai huce taku goma ba amma babu alamun kofar za ta buɗe, Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji kofar tayi kara ta buɗe, Cikin hanzari mahayin ya kunna kai izuwa ciki tare da saurayi Huzmal dake goye da yaro Humair a gadon bayan sa, Har Sarkin yaƙi lahmar ya dako tsalle ya saka kafar sa a kofar sai wata irin gagarumar iska ta cimimiyosa tayi wurgi dashi sai da yayi katantanwa a sama sau hudu sannan ta fyaɗashi da ƙasa, Sannan kofar ta mayar da kanta ta rufe ruf! Cikin matukar takaici Sarkin yaƙi lahmar ya mike tsaye, sarki shazwan, waziri Rufyan, Sarkin bokaye na cizon yatsa cike da takaici. Sa'adda su saurayi Huzmal suka samu nasarar shiga cikin wannan kofa sai suka tsinci kansu a cikin wani makeken falo mai ɗauke da kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, Daga can bangon yamma a falon akwai kofa guda ɗaya hal, A gefen kofar an ajiye wani kwarangwal ɗin murgunejen zaki amma an cire kasusuwan sa an ajiye su acikin kaskon tsafi A gefen kaskon an ajiye wata jimammiyar fatar damisa mai ɗauke da wani jan rubutu, Koda saurayin Yayi arba da abubuwan sai ya taka da kafafun sa ya durfafi inda suke yana mai yafito saurayi Huzmal da hannu yana mai nuna ya biyo bayan sa, Yayin da aka isa sai wannan mahayi ya ɗauki wannan jemammiyar fata mai ɗauke da jan rubutu ya shiga karantawa a fili Huzmal na saurare, Yakai ma'abocin wannan gida kayi sani cewa wannan ita ce kofa ta uku daga cikin kofofi biyar na wannan gida, Bazaka taɓa samun nasarar shiga cikin ta ba face ka ɗauki wannan kasusuwan ƙafafuwan zaki ka sanya a jikin kwarangwal ɗin inda mazaunin su yake,take zasu rikiɗa izuwa Mabudin kofar, Idan kuwa ka sanya ƙasusuwan ba a mazaunin su ba take ruhin zakin zai dawo jikin sa ya hallaka ka, Sa'adda mahayin yazo nan a karatun taswirar sai idanun saurayi Huzmal suka zazzaro ya dubi mahayin cikin alamun tsananin damuwa tamkar zai fashe da kuka yace "yakai wannan jarumi shin yanzu taya ya zamu iya sanin ina ne zamu sanya ƙasusuwan zakin har ya rikiɗa izuwa Mabudin kofar batare da mun halaka ba. Ka sani cewa ahalin yanzu abokan gabar mu suna biye damu kuma tabbas suna son su cimma na, Koda jin wannan batu sai mahayin ya sunkiyar da kansa ƙasa yana mai nazari Daga can sai ya ɗago da kansa yaja gworon numfashi yai ajiyar zuciya yayi gyaran murya yace"yakai Huzmal ina so ka kwantar da hankalinka domin ina da yaƙinin zamu iya buɗe wannan kofa, Koda yake cewar a halin yanzu abokan gabar mu zasu iya cimma na anan,kai dai kawai ka zuba idanun kaga abinda zai faru, 2 Koda ganin hakan sai mahayin ya sanya hannun sa ya ɗauko wannan kasusuwan zaki yana nazarin su har tsawon dakika arba'in Daga can sai ya sanya kashi ɗaya a jikin kafafun zakin take ƙashin ya fara motsawa wani irin haske naban al'ajabi ya gauraye sassan jikin sa, Koda ganin hakan sai mahayin da saurayi Huzmal suka ja da baya a tsorace Sannu a hankali kwarangwal ɗin ya dunga sauya launi har ya dawo izuwa cikakkiyar halittar sa ta zaki, Kawai sai ya takarkare ya kurma wawan ihu kai ko ganin girman zakin ya isa ya tsorata mutum, Kafin ɗaya daga cikin su yayi wani yunkuri zakin ya dako suma izuwa inda suke, Koda ganin hakan sai saurayi Huzmal ya yi koyi dashi suka tari zakin aka ruguntsume da azababban yaƙi mai ban tsoro, sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya, Hakan ne yasan ya tun da duku- dukun safiya mutane ficewa daga cikin gidaddajin su su ka tafi izuwa kasuwa domin tallata hajar su, Manoma suka fita gona domin yin noma, babban abinda ya kara sanya mutane farin ciki shine yadda garin yayi lullumi saboda Rashin fitowar rana, A wannan lokaci fadar kasar ta cika ta batse da al'umma babu masaka tsinke yara, da manya maza da mata Gaba ɗaya ginin fadar an yi shine da waɗansu irin duwatsu na zubar daju da yakutu, fadar ta ƙawatu da nau'ikan kayan kawa da alatun jin daɗin duniya har da ma abinda idanu basu taba gani ba, Shimfidar fadar anyi tane da wani koren kilishi mai taushi wanda idan mutum ya taka shi sai yaji tamkar kafar sa zata nutse a cikinsu saboda haushi. A ɓangaren yamma na fadar aka kirke wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da zallar mulmulallan jauhari aka yi mata feshi da farin ruwan zinare mai fatsi - fatsi, tana sheƙi da ɗaukar idanun duk mai kallon ta, Zaune a bisa karagar mulkin wani shirgegen mutum ne fari,mai tarin saje da ƙasumba kirar samudawan farko, yana da mitsitsin kai mai ɗauke da yan mitsi-mitsin idanu jajaye da faffafɗan hanci mai manyan kofofi tare da wani tafkeken baki tamkar kofar gari,. Cikin sa rundememe ne tamkar an kifa masa kwarya, A jikin sa yana sanye da wata doguwar koriyar alkyabba da aka yi mata cin baki da zaren Lu'u'lu'u Takalmin dake ƙafarsa yakasance mai ban sha'awa domin idan ka kalle sa sai kaga yana canza launi lokaci - zuwa - lokaci, sanye a kansa akwai lambu na sarauta, Tabbas wannan mutum ya cika mai kwarjini kuma mai ban tsoro, domin komai dakewar jarumi idan yayi arba dashi dole ne tsoro ya ɗarsu a zuciyar sa, Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga, Ba wani bane wannan mutum ba face sarki uslaim ibn kahmar, Sarki uslaim yakasance gawurtaccen mayaki kuma mashahurin attajiri ya hau karagar mulkin kasar Baharen tun da yana da shekaru sha biyar a duniya, A rayuwar sarki uslaim babu wani abu najin daɗin rayuwa daya rasa domin a kullum yana samun kuɗin shiga da adadin su yakai dinare miliyan ɗari, Batun dabbobin ni'ima kuma yana da sama da miliyan dubu, ballantana gonaki da kadarori, Duk wannan abubuwan More rayuwa daya tara bai hana sa jin kamar ya hallaka kansa ba saboda baƙin ciki, Bakomai ne ya haddasa masa hakan ba sai domin duk sa'adda ya tuna cewa 'yar sa daya fi so fiye da komai bata tare dashi, Dalilin rabuwar sarki uslaim da yarsa gimbiya zarifakuwa shine kamar haka , Wata rana gimbiya zarifa na zaune a cikin turakar ta, Turakar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin duniya, A wannan lokaci dare ya tsala yayi duhu dunɗum babu abinda kunne keji face kukan gyare da haushin karnuka, Tana cikin wannan haline sai kawai taji kukan jariri ya cika bangaren Turakar baki ɗaya, Al'marin da yayi matukar bata mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai domin a iya sanin ta a gaba ɗaya gidan sarautar babu wacce ke ɗauke tsohon ciki,ko mai shayarwa tsakanin kuyangi da barorin gidan, Abin tambaya anan shine daga ina wannan kukan jariri yake, Amsar tambayoyin da gimbiya ta kasa bawa kanta kenan Abu kamar wasa sai gimbiya zarifa tafi sautin kukan jaririn yana ƙaruwa,nan take taji zuciyar ta bazata iya jurewa ba sai taje ta ceci wannan jariri gama tunanin hakan keda wuya sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi kofar fita daga Turakar,ta tura kofar ta fita Ai kuwa sai taga dakarun dake tsaron wajen sun kamu da barci mai nauyi, Batare da fargabar komai ba ta cigaba da durfafar inda take jin kukan Amma abu kamar wasa sai gashi ta har ta fice daga lambun shaƙatawar ta batare da taga inda jaririn yake ba, Haka dai ta cigaba da tafiya zuciyar ta cike da matukar mamaki da al'ajabi, kawai sai ta ƙara azama domin ta isa inda wata farar kwalba take mai haske, Yayin da yazamana saura taku goma tsakanin ta da kwalbar ba sai taga cewa wannan kwalba na ɗauke da wani koren ruwa mai yauƙin gaske kuma kukan daga cikin ta yake fitowa, Al'amarin da ya yi matukar ɗaure mata kai kenan tace a cikin ran ta ya akayi kukan jariri ke fito daga cikin ta kuma wane ne ya ajiye kwalbar, Haƙiƙa al'amari ne na sihiri, yanzu zan buɗe kwalbar domin naga mene ne a ciki domin dai masu iya magana na cewa da a baka labari gwara ka bayar, Koda kamma ayyana hakan sai kawai ta ɗauki kwalbar ta buɗe murfinta, Kaico! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda ace zarifa tasan abinda zai faru da bata yi gangancin bude kwalbar ba , Domin koda buɗewar ta sai wannan koren ruwa ya rikiɗa izuwa wani narkeken baƙin aljani mai matukar muni ban tsoro daban al'ajabi, gaba ɗaya jikin sa cike yake da gashi, yana ɗauke da manyan fuka-fukai, Koda gimbiya zarifa tayi arba da aljanin sai ta ɗimauce ta buɗi baki da nufin ta kurma wawan ihu amma kafin takai ga aikata hakan aljanin ya busa mata wata iska daga bakin sa take barci mai nauyi ya ɗauke ta, Kawai sai ya suret ta ya luluƙa izuwa sararin samaniya ya ɓace ɓat a cikin gajimare, Tun kafin ƙetowar alfijir gaba ɗaya gidan sarautar ya hautsine da gujegujen jama'a bisa jin labarin ɓatan gimbiya zarifa, Abangaren sarki uslaim kuwa lokacin da labarin ya riske sa sai ya haukace ya kama kashe kuyangi da barorin sa, Al'amarin da ya sanya gidan sarautar ya hautsine kenan kowa ya shiga gudun ceton rayuwarsa, A cikin wannan haline bokan masarautar ya bayyana ga sarki uslaim a lokacin da yake kai komo a Turakar gimbiya zarifa hannunsa riƙe da takobin sa na digar da jini, fuskar sa a murtuke babu annuri tamkar an aiko masa da sakon Mutuwa, Koda sarki uslaim yayi arba da boka ƙarzum sai ya bude sa cikin matukar fushi da bai taɓa yin kamar sa ba yace "yakai ƙarzum shin wane shirmen banza kake yi har wani ya shigo gidan sarauta ta sace gimbiya, yi maza ka gano mini wane ne shi kuma ina ya kai ta, Na rantse da darajar iyaye na sai na yi masa kisa mafi muni da ba'a taɓa yiwa wata halitta ba, Koda jin wannan batu daga bakin sarki uslaim sai boka ƙarzum ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin ladabi cikin kakkausar murya yace"ya shugabana kayi sani cewa zuwa inda gimbiya zarifa take a halin yanzu dai -dai yake da mutum ya sayi ajalinsa da kuɗin sa bakowa bane ya ɗauke ta ba face Sarkin bokayen duniya wanda a halin yanzu babu mashahurin matsayi kamar sa walau mutum ko aljan, Ya shugabana kayi sani cewa duk faɗin duniya babu mahalukin da isa yaje inda gimbiya take har ya ceto ta face wani mutum guda ɗaya hal! Wannan mutum kuwa ba wani bane face. Jarumi Hibairu wanda ake yiwa laƙabi da SARKIN SADAUKAI na duniya Bincike ya tabbatar da cewa ahalin yanzu babu gwarzon mayaki kamar sa, Domin an ce yana iya gudun Sa'a goma ɗauke da zakanya a kafadar sa batare da ya gaji ba, Kuma duk girman zaki idan suka bangaji kirjin juna sai dai zakin ya faɗi ƙasa, Duk abin da bokaye zasu faɗa game da SARKIN SADAUKAI sai dai su faɗa kawai amma yace yadda ake tsammani, A wannan lokaci Hibairu na rayuwa ne a cikin daji da ake kira da suna Baitul-shamshan, Bai taɓa ganin bil'adama face dabbobi da aljan, Bazai taɓa fitowa daga cikin dajin Baitul-shamshan face a ranar da ya kammala bawa tsuntsun tsafin sa horan yaƙi,tare kammala karance sirrikan dake jikin ZOBEN SHIRIN sa Tabbas tunkarar Hibairu da buƙatar ceto rayuwar gimbiya zarifa a can fadar Sarkin bokaye dai dai yake neman jaki mai ƙawo, Ko kuma nace maka dai dai yake da mutum ya siyi ajalinsa da kuɗin sa, domin Hibairu yana magana ne da wani yare guda ɗaya dashi ne kaɗai ya iya shi a duniya domin mahaifiyar sa ta rasu bayan dakika goma da Haihuwarsa, Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan ajawabin sa sai idanun idanun sarki uslaim suka zazzaro kuma hankalin sa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, Ya dubi boka ƙarzum tamkar zai fashe da kuka yace "Ya samanin ilimin tsafi yanzu mene ne mafita, tabbas zan iya bayar da komai da na mallaka domin ceto gimbiya ? Da jin wannan batu sai boka ƙarzum yayi shiru yana mai dogon nazari gami da sunkiyar da kansa ƙasa, Daga bisani ya ɗago da kansa sama ya dubi sarki uslaim sannan yaja dogon numfashi yayi ajiyar zuciya yace "ya shugabana kayi sani cewa mafita ɗaya ce in cigaba da gudanar da bincike bisa halarar tsafi na domin gano yaushe ne jarumi Hibairu zai fito daga dajin Baitul-shamshan da kuma hanyar da zamu bi mu bayyana masa buƙatar mu, Lokacin da boka ƙarzum yazo dai dai nan zancen sa sai zuciyar sarki uslaim ta ɗan samu nutsuwa, Daga wannan furuci boka ƙarzum ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba , Wannan shi ne dalilin daya sanya sarki uslaim ke zubar da hawaye a kullum Tun da daga wannan rana sarki uslaim yakasance cikin shirin zuwa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI Haka dai sarki uslaim ya cigaba da tafiyar da sha'anin mulkin sa kamar yadda ya saba, Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin su saurayi Huzmal da zakin sihiri a cikin gidan tsira a bakin kofar shiga ta uku Yazamana cewa saurayi Huzmal da mahayin na kaiwa zakin hare hare cikin matukar zafin nama juriya da bajinta, Shi kuwa zakin ya wanzu yana mai kai musu hare tamkar wani ifritu, Nan fa su Huzmal suka fahimci cewa tabbas yau sun gamu da gamon su Ana cikin wannan fafatawa ne zakin ya shammaci mahayin ya yakushe sa da faratan sa a cinyar sa ta hagu Take inda ya yakushe san ya haddasa wani lafcecen rauni jini yayi feshi yayi tsartuwa Kafin shudewar wata rabin sa'a zakin ya samu nasarar yiwa Huzmal da mahayin miyagun raunuka sama da ashirin, Duk wannan artabu da ake yi wannan yaro makaho na goye a gadon bayan saurayi Huzmal yana jin duk abinda ke wakana , Ana cikin wannan gumurzu ne kwatsam bazato babu tsammani sai akaji kofa ta biyu ta buɗe dake bayan su, Sai suka yi arba da su sarki shazwan, kafin ɗaya daga cikin su yayi yunkuri boka Dargas ya cire wani dogo mashi a damtsen sa mai tsawo kaifi da jinin tsiya ya cillawa saurayi Huzmal da nufin yayi masa kisan farat ɗaya ya hallaka shi, Cikin wani irin bakin zafin nama Huzmal ya wurkila ya zamewa harin Bisa rashin Sa'a sai mashin ya soke ɗaya daga cikin idanun zakin Take zakin ya kama kururuwa,sannan ya rikiɗa izuwa wata bukatar haske take kubar ta tashi sama cikin iska ta shiga izuwa mazaunin da ke jikin kofar ta murɗa kanta. Har sau uku kawai sai ta buɗe Cikin matukar farin ciki saurayi Huzmal goye da yaro Humair makaho da mahayin suka kunna kai izuwa ciki Kafin sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin yaƙi,da Sarkin bokaye da sauran tawagar su suyi wani yunkuri, kofar ta sake rufe kanta ruf , wannan farar kuba ta sake rikiɗa izuwa wannan kwarangwal ɗin zaki kamar yadda yake a ɗazu.. Sa'adda su saurayi Huzmal suka shige izuwa cikin kofa ta huɗu, Sai suka tsinci kansu a cikin wani katon fili mai yalwa, A yammacin filin akwai waɗansu ɗaku na guda biyar, Ginin ɗakunan an yi sune da manyan duwatsun wuta masu kwarin gaske, kofofin su kuma an yi sune da mulmulallan jan karfe, inda za'a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ɗaya daga cikin kofofin ba, A kofar ɗaki na farko an ajiye wani ƙatuwar akwatu ta baƙin ƙarfe, Ɗaki na biyu kuwa an ajiye waɗansu akwushi guda huɗu, kowane akwushi na ɗauke da ruwa garai-garai kuma ya bambanta da ɗayan wato wani fari,baki,shuɗi da ja, Kofar ɗauki na uku kuwa yana ɗauke da waɗansu kwalabe da girman su bai huce na gwanda ba, Suna da ɗauke da wani koren ruwa a cikin su Kofar daƙi na huɗu da na biyar kuwa an ajiye waɗansu gumaka na waɗansu irin tsuntsaye masu ban tsoro, Idan mai kallo ya ɗaga kan sa sama izuwa saman kowace kofa ɗakin zai yi arba da waɗansu alluna masu ɗauke da rubutu da aka sassaƙa su da wani itace bishiya, Lokacin da saurayi Hizmal dake goye da yaro Humair makaho da mahayin sukayi arba da waɗannan ɗakuna biyar sai suka cika da matukar mamaki, Kuma ya dugunzuma ainun suka kama kalle-kalle da dube dube domin su gano wane ɗaki ne daga cikin ɗakunan biyar ɗin su shiga ga domin isa gidan tsira, Tsawon daƙiƙa Ɗari da Hamsin ɗayan su bai ce uffan ba, sai daga bisani saurayi Hizmal yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya buɗi baki ya dubi mahayin cikin alamun tsananin damuwa gami da tashin hankali yace yace"ya abokina shin yanzu wane ɗaki Yakamata shiga daga cikin ɗakunan biyar domin mu shiga izuwa gidan tsira tabbas hankali na a tashe yake tunda idan mu kayi rashin Sa'a a karon farko bamu shiga izuwa ɗakin da zamu tsira ba, To babu makawa abokan gabar mu zasu iya cimma mana har su samu nasara akan mu, Koda jin wannan batu daga bakin saurayi Hizmal sai mahayin yayi shiru yana mai sunkiyar da kansa ƙasa yana mai zurfafa cikin Kogin tunani, Sai da ya shafe tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali sannan ya ɗago da kansa sama ya dubi Hizmal sa idanunsa waɗanda su kaɗai Hizmal ɗin ke iya gani ya buɗi baki yace"yakai Hizmal kayi sani cewa a iya tsawon rayuwa ta babu abinda zan sanya a gaba face na cimma nasara akansa, Naji a jikana cewa wancan ɗauki na biyu shine ɗakin da zamu samu tsira, Koda jin wannan batu daga bakin mahayin sai Hizmal ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, kawai sai mahayin ya shige gaba, saurayi Hizmal na biye dashi a Baya goye da yaro Humair, Suka durfafi kofar wannan ɗaki na biyu, da isar su daf da kofar sai suka shiga nazarin waɗannan akwushi masu ɗauke da ruwa kala- kala a cikin su. Daga can sai mahayin ya dubi saurayi Hizmal yace"ya Hizmal ina ganin wannan koren ruwa dake cikin akwushi shine zamu ɗauka mu zuba a cikin wannan mazirari dake jikin kofar sannan ta buɗe, Koda gama faɗin hakan sai Mahayin ya tsugunna a ƙasa da nufin ya ɗauki wannan akwushi mai ɗauke da jan ruwa a cikin sa, Sai kawai a kaji yaro Humair yayi magana akaro na farko da fara wannan tafiya, Al'amarin da sanya mahayin ya fa sa ɗaukar akwushi kenan domin yaji me yaro Humair makaho zai ce. Yaro ya buɗi baki cikin murya mai daɗi Yace"yaku yan uwana kuyi sani cewa duk da kasancewar bana iya gani da idanuna na kasance makaho amma na fahimci cewa wannan ruwa ja dake cikin akwushi ba shi ne mabuɗin kofar ba domin kuwa duk inda ja yake tashin hankali ne da rashin zaman lafiya, Ina ganin akwushi mai ɗauke da farin ruwa shine mabuɗin kofar domin duk inda farin abu yake akwai zaman lafiya da kuma alkairi, Sa'adda mahayin da saurayi Hizmal suka ji wannan batu daga bakin yaro Humair sai suka cika da matukar mamaki da al'ajabi bisa wannan fasaha d hikima da yayi , Batare da wani ɓata lokaci ba Mahayin ya sake tsugunnawa aƙasa ya ɗauki akwushi mai ɗauke da farin ya zuba a cikin wannan mazirari dake jikin kofar, A Birnin Tehran anyi wata gawurtacciyar sarauniya,kuma Basadaukiya da ake yiwa laƙabi da Abidatul-auliya, Abidatul-auliya takasance kyakkyawa tagaban kwatance da bokaye da su hasashe suka tabbatar dacewa, A wannan KARSHEN ƘARNI babu wata mai kyan diri da sura tamkar ta,domin labarin kyawun ta ya bazu a ko ina a duniya, Daɗin daɗawa kuma ta shahara ainun a fagen sanin alƙalumman sihiri, Tun sarauniya Abidatul-auliya tana da shekara sha huɗu a duniya ta hau karagar mulkin birnin Tehran,kuma a halin yanzu tana da shekaru talatin cif, amma bata taɓa yin soyayya da wani ɗa namiji ba ballantana tayi maganar aure, Sautari manyan sarakuna, bokaye, attajirai kan bijiro da bukatar soyayyar su ga sarauniya Abidatul-auliya amma basa samun nasara, Al'amarin da yayi matukar ɗaure mane ma auren nata mamaki kenan, Su ka ce aransu anya kuwa sarauniya Abidatul-auliya tana da cikakkiyar lafiya, Ya za'ace mace takai waɗannan shekaru masu yawa batare da tana son wani ɗa namiji ballantana ta buƙaci namiji a kusa da ita, Bisa hakan yasanya boka suka shiga gudanar da bincike domin su gano dalilin faruwa hakan Amma haka suka gama binciken su babu wani cikekken bayani daga gare su, Abinda basu sani ba shine bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya bata soyayya ba ko batun aure ba sai domin wata matsananciyar lalura da ta addabeta tsawon shekaru masu yawa tun kafin ta hau karagar mulki, Wannan lalura dake addabar ta Ita ce tsagin jikin ta na hagu yana ɗauke ne da kuturta kowane dare Abidatul-auliya bata iya barci saboda raɗaɗin da kuturtar ke yi mata Ta samu wannan lalura ne tun tana da shekaru goma sha biyu a duniya wata rana ta shiga izuwa dajin dake makwabtaka da birnin Tehran domin yin farauta, Abidatul-auliya na tafe bisa kan ingarman doki ja sanye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,a gadon bayan ta tana rataye da waɗansu zaratan takubba masu kaifi da tsinin tsiya,. Ta wanzu tana tsala Azababban gudu a cikin dajin ma'abocin dogayen bishiyoyi duwatsu,da koramu, Sai da ta shafe tsawon Sa'a ɗaya tana tsala Azababban gudu batare da haɗu da wani abu mai cutarwa ba, hatta kukan yan kananan tsuntsaye bata ji, al'marin da yayi matukar ɗaure mata kai kenan kuma ya bata mamaki Domin tunda take fita farauta hakan bai taɓa faruwa ba, Tana cikin wannan hali ne sai wani tunani ya faɗo mata tunanin kuwa shine anya kuwa bawai gudun da take yi bane abisa dakin ta shine ya sanya namun dajin suka gudu, Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta cigaba da sassarfa , Abu kamar wasa sa gashi ta shafe wata sa'a ɗaya batare da taji motsin komai ba, A dai dai lokacin yaki bawali don haka sai taja linzamin domin ta ta tsaya cak! Sannan ta kama ta sakko kawi sai ta durfafi wata ƙorama mai ɗauke da ruwa garai-garai gwanin ban sha'awa don haka sai ya tsugunna a gefen tayi bawalin,. Sannan ta sanya hannun ta da nufin ta ɗebo ruwan ƙoramar amma sai ta lura cewa fitsarin da tayi ya shiga cikin ƙoramar ya canza launin ruwan, Sannu a hankali sai kalar ruwan ƙoramar ya canza launi izuwa ja, Kwatsam bazato babu tsammani sai Abidatul-auliya ta ji an dakamata tsawa mai ban tsoro Saboda matukar razana bata san sa'adda ta kife a ƙasa ba tana baƙi gami numfarfashi, kuma hantar cikin ta kaɗa tsoro Yakamata ainun, Daga bisani sai taga wani mutum tsoho tukuf ya bayyana a tsakiyar ƙaramar tamkar yana tsaye ne akan turba, Mutumin yakasance dogo tamkar bishiyar turare, gashin kansa da gemun sa farare ne solko ɗigon baƙi babu, idanuwan sa jajayene tamkar garwashin wuta, hancin a taɓe yake tamkar ba dashi yake shaƙar numfashi ba, yana da tafkeken baki tamkar kofar gari, yana da faffaɗan kirji tamkar faranti, A kwiɓin hannayen sa biyu yana maƙale da waɗansu fuka-fukai guda biyu daga kasan gadon bayan sa yana sanye da wata irin murtukekiyar jela irin ta kifi, Sanye a ƙugun sa yana sanye da bante na fatar damisa mai ɗauke da guraye da layu na tsafi, a tsakiyar kansa yana ɗauke da manyan ƙaho guda biyu irin na ɓauna, Tabbas wannan mutum ya cika abin tsoro domin babu wani mutum da zai yi arba dashi face ya ɗimauce, Sa'adda Abidatul-auliya tayi arba da mutum sai jikin ta yakama kyar ma tamkar mazari har tana sakin fitsari a wando saboda tsananin tsoro da razani, Yayin da mutumin yaga halin da Abidatul-auliya ta shiga sai ya takarkare ya bushe da dariya mugunta,mai kama da kukan baƙi sai daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da Sakon mutuwa sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace "yake wannan bil'adama kiyi sani cewa kin aikata mini laifi wanda ahalin yanzu babu wani mahaluki da ya taɓa yi mini shi kisani cewa wannan ƙorama da kika yi mini fitsari a ciki ba ruwa bane face JININ SARAKAI na baƙaƙen aljanun duniya na shafe tsawon shekaru dubu arba'in ina sihirce wannan jini domin in samu nasarar mallakar gaba ɗaya sarakunan ma'ana na zamo SARKIN SARAKAI na aljanu, A yau ne zan kammala wannan aiki nawa sai gashin kin wargatsa mini wannan buri na wa a cikin Abin da bai gaza daƙiƙa goma ba wanda na shafe tsawon shekaru dubu arba'in, Lokacin da mutumin yazo nan azancen sa sai hawayen baƙin ciki suka zubo masa, Sannan daga bisani ya cigaba da cewa "Na rantse da rayuwar mahaifina sai na yanke mini hukuncin da har abada bazaki taɓa mantawa da ni ba Koda gama faɗin hakan sai mutum ya a nuna Abidatul-auliya da ɗan yatsan sa na hagu take wani irin koren haske yayi fitar burgu daga gare sa ya shiga jikin Abidatul-auliya Nan take taji wani irin tsananin zafi a tsagin jikin ta na hagu tamkar ana ƙonata da wuta, Nan fa ta fara ihu da kururuwar neman taimako Sannan daga bisani mutumin ya ɗauke hannun sa na dubi Abidatul-auliya yace "yake wannan bil'adama kiyi sani cewa har abada baza'a taɓa samun magani lalurar ki ba domin nemo maganin dai dai yake da barkewar YAKIN DUNIYA na uku, Koda mutumin yazo nan a zancen sa take ya bace bat tamkar bai taɓa wanzu wa ba. Adai-dai wannan lokaci ne Abidatul-auliya tajiyo karar takun sawayen dawakai da haniniyar su, Ai kuwa koda ta duba sai tayi arba da dakarun masarauta su kimanin dubu biyu sun durfofi inda take, da zuwa su ka ɗauke ta batare da ɓata lokaci ba, suka juya suka nufi hanyar da zata kai su birnin Tehran, Tun daga wannan rana tsagin jikin Abidatul-auliya ya kamu da ciwon kuturta, Kuma sai dare yake yi mata raɗaɗi, sarki ya nemi bokaye da matsafa a sirrance akan su gano masa maganin cutar dake damun gimbiya amma abu yaci tura , domin duk bokan da yajewa da maganar sai yace masa shima bai san maganin lalurar ba, Har sarki ya mutu aka ɗora Abidatul-auliya akan karagar mulki amma ba'a gano maganin cutar ba, Kuma yazamana cewa gaba ɗaya birnin Tehran babu wanda yasan cewa Abidatul-auliya na ɗauke da wannan cuta ta kuturta, hatta dakarun da suka ɗauko ta daga cikin wannan daji a lokacin da al'amarin yafaru, Tun daga ranar da wannan abu yafaru bata ƙara bari wani mahaluki yaga jikin ta koda kuwa hannayen ta da kafafunta face fuskar ta kaɗai, ko wanka da kwalliya zata yi da kanta take yi bata bari kuyangi su yi mata, Wata rana Abidatul-auliya na zaune acikin Turakar ta bisa ƙasaitacciyar kujera ta tafka uban tagumi, a wannan lokaci dare ya tsala kuma yayi duhu dunɗum babu abinda kunne keji face haushin karnuka da kukan gyare tsilli-tsilli. Abidatul-auliya na cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai wani kyakkyawan tsuntsu ya bayyana agare ta a cikin iska yana mai ƙura mata idanu, Koda tayi arba da tsuntsun take ta dawo cikin hayyacin ta daga duniyar tunanin da ta shiga zuciyar ta cike da matukar mamaki da al'ajabi Bisa mamaki sai Abidatul-auliya taji tsuntsun ya bushe da dariya tamkar yakasance bil'adama sannan daga bisani ya fara magana cikin murya mai ɗan karan daɗi tamkar ana busa sarewa Yana mai cewa"Barka da warhaka ya sarauniyar kyawawan duniya Abidatul-auliya bintu shafwaz, Ya ke wannan sarauniya mai daraja nasan cewa a halin yanzu zuciyar ki cike take da matukar mamakin yadda akayi nake magana alhalin nakasance tsuntsun ba bil'adama ba, Tabbas ni bil'adama ne kamar ki sai dai na boye miki siffa ta ne saboda waɗansu muhimman dalilai, Ya ke wannan sarauniya kiyi sani cewa bakomai ne yakawo ni gareki ba sai domin na taimaka miki wajen samun maganin lalurar da ta addabeki atsagin jikin ki na hagu tsawon shekaru masu yawa, Koda jin wannan batu sai Abidatul-auliya ta dubi tsuntsun cike da mamaki tace"Kace mini kai bil'adama ne to shin wane ne kai? Kuma mene ne ribarka idan ka taimake ni na samu maganin lalura ta? Koda jin waɗannan tambayoyi sai tsuntsun yayi ajiyar zuciya sannan yayi gyaran murya yace"Haba ranki ya daɗe me kike ci ne na baka na zuba ai cikin bayanin dazan yi miki za kiji duka amsar tambayoyin ki amma tun da kina buƙatar su bari na fara sanar dake. Da farko ni suna na shubairu ibn mauzur mahaifina mashahurin boka ne da yayi shura a yankin nahiyar larabawa, Duk cikin ya'yan mahaifin mu ni ne kaɗai na gaje shi tun banfi shekara goma sha biyar ba da rasuwar sa, Game da amsar tambayar ki ta biyu kuwa zakiji amsar acikin bayanin da zan yi miki, Binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na ya tabbatar mini dacewa tun mahaifin ki yana raye ya ziyarci bokaye da dama domin samo maganin lalurar ki amma abu ya ci tura, Yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa har abada bazaki taɓa warkewa daga wannan lalura taki ba face kin sha wani tsumin tsafi dake ajiye a cikin wata salka a fadar Sarkin bokayen duniya, Bincike ya kara tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki da ya isa yaje fadar Sarkin bokaye ya ɗauko tsumin tsafi face wani hatsabibi kuma taƙadirin jarumi da ake yiwa laƙabi da SARKIN SADAUKAI, Hibairu wani irin mutum ne da yake rayuwa ta daban domin ya taso ne a cikin dabbobi da aljanu tun yana jariri, bai taɓa ganin wani bil'adama ba ballantana ya iya Yaren su, An kira sa ne da SARKIN SADAUKAI saboda tsanin jarumtakar sa ya huce hankali, Bazai taɓa fitowa daga dajin Baitul-shamshan ba face ya kammala karanta waɗansu dalasiman tsafi dake jikin wani ZOBEN SHIRI dake hannun sa wanda adadin sirrikan tsafin shine adadin dabbobin dake cikin dajin, Game da amsar tambayar ki ta uku kuwa akan mene ne riba ta idan na taimaka miki wajen samun maganin lalurar ki shine Sai domin na gano cewa kece kaɗai wacce zata taimaka mini wajen biyan tawa Bukatar, Kamar yadda kike ɗauke da lalurar tsagin jiki Ni ma ina da irin ta sak amma a tsagin dama kuma na samu tawa lalurar ne alokacin da nake fafata artabu da yan uwana a ƙoƙarin su na rabani da muhimman sirrikan tsafin mahaifin mu, Bisa wannan dalili ne yasan ya nake so mu haɗa karfi da karfe domin mu sadu da sadauki Hibairu a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan domin mu bayyana masa buƙatar mu ta zuwan sa fadar Sarkin bokaye, Koda tsuntsun ya zo nan azancen sa sai kawai ya rikiɗa izuwa wani zabgegen kyakkyawan saurayi ba ya sanye da riga ko wando face bantai na fatar damisa da ya rufe al'aurar sa zuwa kwaurin sa, Sa'adda sarauniya Abidatul-auliya tayi arba da saurayin nan take taji zuciyar ta buga da karfi kuma tsikar jikin ta ta tashi, Bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya taji zuciyar ta ta buga da karfi ba sai domin tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin wani ɗa namiji mai kwarjini da kyan diri tamkar saurayin ba, Abinda yasanya tsikar jikin ta ta tashi kuwa shine Yayin da ta kalli saurayin sai taga barin jikin sa na dama na zubar da wani ruwan mugunya na kuturta, Daga can sai saurayin ya sake rikiɗa izuwa wannan kyakkyawan tsuntsu ya buɗe baki a karo na uku yace "Na barki lafiya ya sarauniyar kyawawa sai mun sake saduwa a ranar da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a dajin Baitul-shamshan, Koda gama faɗin hakan sai ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Nan take sarauniya Abidatul-auliya ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa yazamana cewa a kullum idan dare ya tsala sai ta zauna a wannan baraba ta Turakar ta koda wannan tsuntsun zai sake bayyana gareta wato shubairu ɗan boka mauzur Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Abidatul-auliya ya birnin Tehran dake yammacin duniya. 3 Kwatsam bazato babu tsammani sai saurayi Hizmal da mahayin suka ji ƙarar alamun zare sakatun wannan ƙofa daga ciki, Daga bisani sai ƙofar ta bude sai ga wani irin haske da kamshi mai nan sha'awa ya ratso daga ciki Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa mahayin ya kunna kai izuwa ciki saurayi Hizmal yayi koyi dashi goye da yaro Humair a gadon bayan sa, Su na kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!. Adai dai wannan lokaci ne sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar su suka bayyana a wajen bayan buɗewar ƙofa ta huɗu, Sa'adda suka bayyana sai sarkin bokaye ya dubi sarki shazwan cikin matukar takaici yace"ya shugaba na haƙiƙa munyi babban rashi da har mu kayi kuskure su saurayi Hizmal suka ƙetare kofa ta biyar suka shiga izuwa gidan tsira Bisa tsarin wannan gida babu wanda ke da ikon shiga cikin gidan tsira matukar akwai wanda ya ƙetare kofa ta biyar har sai nan da kwanaki uku, Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kowa ya cika da matukar takaici, shi kuwa Sarki shazwan saboda matukar takaici bai san sa'adda ya takarkare ya kurma wawan ihu ba wanda ya firgita duk wata halitta dake wajen har da boka Dargas, Sai Daga bisani ne ya turɓune fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarkin bokaye a lokacin da idanuwan sa suka kaɗa su kayi jawur tamkar garwashin wuta cikin kakkausar murya yace"ya Sarkin bokaye ina so kayi ma za ka gudanar da bincike gano mini shin mene ne abin da ke faruwa a birni na, Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai idanun Sarkin bokaye suka zazzaro su dube sa cikin ladabi yace"ya shugaba na shin ka manta ne cewa abisa ƙa'ida da dokar wannan gida sihiri baya tasiri, Idan kuwa har ka naso na gudanar da binciken dole sai dai mu koma da baya, Sai dai ina da wata shawara,shawarar kuwa ita ce mu kasu guda biyu kaso na farko su jira anan har zuwa nan da kwanaki uku domin su samu damar shiga izuwa kofa ta biyar su cimma su saurayi Hizmal, Ni kuma da wasu zamu koma izuwa birnin mu domin mu kai ɗauki jikina ya bani cewa tabbas bayan tafiyar mu wani mummunan al'amari ya faru sai dai bazan iya sanin ko mene ne ba tunda bani da halin gudanar da bincike, Yayin da sarki shazwan yaji wannan shawara daga Sarkin bokaye sai yayi shiru yana nazari Daga bisani kuma ya dubesa yace"Ka kawo shawara mai kyau saboda ka tafi kai da sauran Yan uwan ka bokaye mutum biyar,tare da waziri Rufyan Ni kuma da Sarkin yaƙi zamu zauna nan mu jira cikar kwanaki uku domin mu cimma su saurayi Hizmal. Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye ya juya da baya ya shige izuwa cikin wannan kofa ta huɗu da suka fito waziri tare da bokaye biyar suka mara masa baya, Suka bar su sarki shazwan a tsaitsaye cirko cirko fuskokin su cike da matukar damuwa, Wannan shi ne abinda ya faru da su sarki shazwan da su saurayi Hizmal a cikin gidan tsira, ****. *****. ***** Daji ne ma'abocin kwarjini,da ban tsoro, ya tara bishiyoyi, duwatsu,koramu haɗe da kwazazzabai,gami da manyan tsaunuka, Komai rashin tsoron Mutum idan ya yaga yadda dajin yakasance dole ya razana, Domin da gani dole ne a samu miyagun dabbobi ko aljanu a cikin sa, Tsananin shirun da ya wanzu a wajen ya ishi ya firgita Mutum Sai dai abinda zai bawa mai kallo mamaki shine duk yadda dajin ya tara wadannan abubuwan ban tsoro amma sai gashi wani bil'adama ya wanzu a cikin sa amma babu alamun tsoro ko razani a tare dashi Kyakkyawan saurayi ne ɗan kimanin shekaru sha biyar yana sanye da bante iya gwiwar sa, babu riga a jikin sa, https://youtu.be/tsdKzDyEuVk Hakan ne abinda ya bayyana surar jikin sa ta jarumtaka , jikin sa a murɗe yake tamkar na ƙarfe,yana da faffaɗan kirji tamkar duwatsu aka cuccusa masa a ciki,gashin kansa baƙi ne siɗik mai kyalli ya zuba akan fuskar sa da kirjin sa, Kafar sa ko takalmi babu, a hannun sa yana riƙe da wani dogon mashi mai baki tamkar zarto mai kaifi tamkar takobi, Kallo ɗaya za ka yiwa saurayin ka fahimci cewa yana da karfi na Allah ya isa, Tafiya yake a dajin cikin ƙasaita yana mai ratsa duwatsu koramu da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi tamkar yana cikin turakar sa, Yana cikin wannan tafiya ne ya jiyo alamun motsi a bayan,. Koda ya waiga bayan sa sai yayi arba da wata zakanya da mijin ta suna tsere cikin nishaɗi, Idan namijin ya ba wa macen tazara sai macen ta zage damtse ta tsere masa, ta mai yimasa gurnani dake nuna cewa ta samu nasara , Sa'adda saurayin yaga abinda zakanyar da mijin ta ke yi sai ya kalle su yayi murmushi har suka zo suka gifta ta gaban sa suna matsanancin gudu suka yi nisa sosai har yazama dakyar yake iya hangosu. Sai kawai shima ya takarkare ya falfala da azababban gudun mai ban al'ajabi daban mamaki, Domin ƙorama, duwatsu da bishiyoyi basa tsaida sa, Duk faɗin ƙarama tsallake ta yake yi. A wasu lokutan sai kaga ya daga tsalle sama yana yana mai rike rassan bishiyoyi tamkar wani ɗan biri, A wasu lokutan ma idan yaga bishiya zatayi masa waigi sai kaga ya sanya hannun sa ɗaya ya naushe ta ta faɗi ƙasa ya bi ta kanta ya huce, Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa goma sha biyar ba sai gashi ya dira a can gaba ɗaya inda zakunan suke, Ya yin da su kayi arbda da saurayin sai suka ja suka suka tsaya cak, A kayi kallon kallo sai bisani sai zakanyar da mijin ta suka dako sufa izuwa kan saurayin yayin da suka hada kirji da juna sai su duka biyun suka faɗi ƙasa tim,. Amma saurayin ko da ƙafarsa bata motsa ba ballantana yayi gezau, Sai da akayi haka har sau goma, koda zakunan suka ga cewa sun kasa samun nasara sai kawai suka risina da kawunan su ƙasa suka durƙusa alamun dake nuna cewa sunyi MUBAYA'A ga saurayin, Ba wani bane wannan saurayi ba face jarumi Hibairu wato SARKIN SADAUKAI. Yayin da Hibairu yaga zakunan sun risina agareshi sai kawai ya juya ya cigaba da tafiya a dajin hannun sa riƙe da wannan mashi mai baki biyu, Wannan shi ne abinda ya faru da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI a cikin dajin Baitul-shamshan. Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sa'adda suka samu nasarar shiga izuwa gidan tsira sai suka tsinci kan su a cikin wani kasaitaccen gida da aka kawata sa da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin duniya, gaba ɗaya ginin gidan anyi sane da zallar duwatsun zubar daju yana sheƙi da walwali, ko ina an kawatashi da furanni da furanni da shuke-shuke gwanin ban sha'awa. Gidan yana ɗauke da manyan falo guda arba'in kowanne na ɗauke da kayan alatun jin daɗin duniya daya bambanta da ɗayan, Haƙiƙa babu wani Basarake ko attajiri da zai tsinci kansa a cikin gidan face ya raina kansa ya tabbatar dacewa ya shiga cikin maƙurar aljannar duniya, Bayan su saurayi Hizmal sun sauka a cikin wata ƙasaitacciyar turaka sai kowa ya shiga kimtsa cikin sa bayan an kammala an samu nutsuwa ne sai Hizmal yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye ya dubi mahayin nan yace"ya kai wannan jarumi ma'abocin karfin damtse lokaci yayi da ya kamata ka bani amsar tambayoyin da nayi maka a baya, Koda jin wannan batu sai Mahayin ya ɗora hannun sa a kansa ya cire rawanin sa fuskar sa ta bayyana a fili ƙarara, Sa'adda saurayi Hizmal yayi arba da fuskar mahayin sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki, Bakomai ne ya basa mamaki ba sai bisa ganin cewa mahayin yakasance tsaleliyar kyakkyawar budurwa, A iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin mace mai kyan diri tamkar mahayin ba, A karon farko Hizmal yaji soyayyar ya mace ta shiga zuciyar sa, Kyakkyawar budurwar ta jefi Hizmal da wani irin kayataccen murmushi mai ɗauke da alamar tambaya, Sannan ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai daɗi tamkar sarewa tace"yakai Hizmal a yanzu na bayyana maka wace ce ni Yanzu kuma zan sanar dakai dalilin da ya sanya taimaka maka wajen ceton rayuwar yaro Humair, Da farko dai suna na Husnaila bintu ishwar, mahaifina ƙasurgumin matsafi ne kuma ƙasaitaccen sarki da yayi shura a yankin ƙasashen yamma ta tsakiya, Dalilin rabuwa da mahaifina da ƙasar mu kuwa shine , ****. *****. ***** Kimanin shekaru arba'in bayan shuɗewar KARSHEN ƘARNI na shida da yin YAKIN DUNIYA na biyu, An yi wata ƙasaitacciyar ƙasa da ake yiwa laƙabi da Baitul-Mausul, Ƙasar Baitul-Mausul ta bunƙasa a harkar kasuwanci,noma da kiwo daɗin daɗawa sun tara zaratan Jarumai masu juriya a filin daga, Sarautar ƙasar na karkashin mahaifina sarki ishwar, Sarki ishwar yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga, ya na da tarin dukiya,gami da sanin ilimin tsafi, Mutum adali mai tausayin talakawan sa, bisa wannan dalili ne yasan ya jama'a ke matukar kaunar sa da yi masa biyayya, Kuma sarakunan dake nahiyar suke shakkar sa basa yunkurin kawo masa farmaki, Mahaifina yana da matan aure guda huɗu kuma dukkanninsu sun haifa masa ya'ya Yarima ubaiyu shine babba, sannan Hushriba,yarima Zaiyum sai ni yar autar su Husnaila, A kaf cikin ya'yan mahaifin mu ni kaɗai ce na gajeshi a fagen halaye na kwarai, saɓanin yan uwa na su yarima ubaiyu, Yayin da yan uwana suka ga cewa sarki da ma sauran juma'ar gari sun ɗora soyayyar agareni kuma suna nuna cewa nice zan gaji karagar mulki sai yan uwa na suka fara bayyana mini ƙiyayya, Sau babu adadi sun kawo mini hari domin su cutar dani amma sai na tsalleke, Haka ma a bangaren mahaifiyata tana fuskantar tsangwama daga kishiyoyin ta A wasu lokutan haka zamu zauna ni da ita suna kukan baƙin cikin abinda ake yi mana A kwana a tashi wata rana sai mahaifin mu ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da aka kasa gane kanta,komai na jikin sa ya daina motsi sai dai idanunsa da bakin sa da yake iya magana, Nan fa manyan bokayen ƙasar suka dukufa gudanar da bincike domin su gano musabbin abinda ya haddasa cutar da kuma maganin dazai warkar da cutar, Amma mahifina bai taɓa sani ɗaya daga cikin matayen su sun sa abin da binciken ya bayar ba, Wata rana tunda dukun safiya ni da sauran Yan uwa na muka shiga turakar mahaifin mu domin mu duba sa, Da shigar mu mu ka tarar dashi kwance abisa kan gadon sarauta, Kai idan ka gansa sai kayi tsammanin cewa gunki ne domin komai na jikin sa ya daina motsi idan ka cire idanuwan sa dake kiftawa, Sa'adda mu kayi arba da halin da mahaifin mu ke ciki muka shiga zubar da hawaye Tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali sannan Daga bisani muka miƙe tsaye domin ficewa daga Turakar, Yarima Ubaiyu ne a gaba sannan Gimbiya Hushriba yarima Zaiyum sai ni a ƙarshe, Har na sanya ƙafa ta ɗaya a waje sai naji bisa mamaki mahaifina ya yi gyaran murya yace"ya yata dawo izuwa gareni domin in sanar dake wani sirri, Koda jin wannan batu daga bakin mahaifina sai na dawo da baya nazo na tsugunna a gaban mahaifina, Kawai sai abbana ya buɗi baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi take wani haske ya bayyana yaje ya shiga jikin kofofi da tagogin turakar take suka rufe kansu, Kana haske ya dawo ya cure waje guda ya rikiɗa izuwa wata fitilar haske, Nan fa Turakar ta gauraye da wani irin haske na ban mamaki wanda koda allura ce ta faɗi mutum yana dubawa zai ganta. Kana daga bisani mahaifina ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai tattare daban tausayi yana mai cewa "ya yata abar alfahari na kiyi sani cewa bakomai ne ya sanya na keɓe da ke ba sai domin na sanar dakai wani boyayyen sirri guda ɗaya game da wannan cuta da ta same ni, Ya yata kiyi sani cewa binciken da bokayen wannan ƙasa su kayi ya tabbatar dacewa wannan cuta tawa Yan uwan ki su yarima ubaiyu ne suka yi mini Shirin tsafi domin su hallaka ni su gaji karagar mulki na, Saboda da mugun shirin da su kayi mini ne yasan ya na umarci waziri daya tura ku izuwa sassan duniya domin ku nemo mini maganin cutar, Duk wanda ya samu nasarar nemo maganin shine zai gaji karagar mulki na, Ya yata kiyi sani cewa kece kaɗai na fi kauna a cikin yan uwan ki da mahaifiyar ki, Saboda haka ne nake so na sanar dake maganin dazai warkar dani daga wannan cuta, Domin ina son ki gajeni bayan raina na ta tabbata cewa jama'a zasu samun farin ciki da zaman lafiya har abada, saɓanin yan uwan ki, Maganin dazai warkar dani daga wannan cuta shine sihirtaccen DAMARAR SIHIRI ta Sarkin bokayen duniya dake sanye a ƙugun sa DAMARAR SIHIRIn na dauke da waɗansu sirrika na sunayen Ubangijin wadansu ma'abota wani addini da ake kira da suna Musulunci, Ina da ace JARUMAN DUNIYA zasu taru waje guda baza su iya raba Sarkin bokaye da wannan DAMARAR SIHIRI ba matsawar yana tare da ita Ya yata kiyi sani cewa bazaki taɓa samun nasarar mallakar ɗamarar ba face kin nemi taimakon wani hatsabibi jarumi da ahalin yanzu yake zaune a dajin Baitul-shamshan, Ana kiran jarumin Hibairu bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu Hibairu shine SARKIN SADAUKAI na duniya domin babu jarumi mai karfin damtse kamar sa, Hibairu bai taɓa ganin bil'adama a rayuwarsa ba domin ya na rayuwa ne a cikin dabbobi da aljanu, don haka ya taso da wani yare da wanda ya iya yinsa a duniya face yaro Humair makaho, A halin yanzu makahon Yaron yana ajiye a hannun saurayi Hizmal yana kula da https://youtu.be/bq_-9I3FtnA sa tun bayan mutuwar mahaifan sa, Lokacin da mahaifina yazo nan a zancen sa sai yace ya yata na umarci da kika kara matsowa kusa da ni Koda jin hakan sai na daɗa matsa kusa dashi Kawai sai abbana ya buɗe bakin sa take wani dunkulallan farin haske ya fito daga bakin sa da girman sa bai huce na kwan jimina ba Take hasken ya dunga shiga jikina lokacin da hasken ya kammala shiga, Take naji wani irin gagarumin karfi ya shige ni naji tamkar zan iya yaƙar duniya baki ɗaya, Mahaifina yayi guntun murmushin ƙarfin hali sannan yace ya yata Kiyi sani cewa ahalin yanzu kina ɗauke da sirrikan tsafina guda miliyan biyu, Haƙiƙa babu wani al'mari da za ki sanya a gaba face kin samu nasara, Saboda haka sai ki jira nan da kwanaki domin kiji bayanin da waziri zai bayyana. Sa'adda mahaifina yazo nan azancen sa sai hawaye suka shatato daga idanuwan sa Al'amarin daya sanya na rungume mahaifina kenan na fashe da kuka saboda da mutukar tausayi, Sa'adda jaruma Husnaila bintu ishwar tazo dai dai nan a labarin ta sai hawaye suka zubo daga idanuwan ta, Al'amarin da ya sanya saurayi Hizmal yaji ya kamu da matukar tausayin ta kenan har kwalla ta zubo masa, Shi kansa yaro Humair daya kasance makaho baya gani sai da yaji ya kamu da tausayin Husnaila, Tsawon daƙiƙa hamsin Husnaila tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta sanya hannayen ta biyu ta share hawayen ta sannan ta cigaba dacewa Kamar yadda mahaifina ya faɗa haka al'amarin yakasance ranar da kwana uku suka cika waziri yayi umarni akayi shela a cikin birni da kauye akan cewa sarki zai tura ya'yan sa izuwa nemo maganin lalurar sa duk wanda ya samu nasarar nemo maganin da ya warkar da shi da jinyar sa Shine zai gaji karagar mulki, yayin da jama'a suka ji wannan shela sai sukayi cincirindo a fadar babu masaka tsinke kowa ya hallara, Mu kaɗai ake jira, ana cikin wannan hali ne kwatsam sai yan uwa na su yarima ubaiyu suka shigo fadar shirye shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro, Yayin da jama'a suka yi arba da su sai suka miƙe tsaye domin girmama wa a gare su, Har sai da suka je suka zauna a wajen da aka tanadar mu su sannan fadar tayi tsit Bayan shuɗewar Kamar daƙiƙa hamsin ne sai na shigo fadar tare da dakarun rakiya masu tsaron lafiya Sa'adda jama'a suka yi arba dani nan take fadar ta rude da shewa da tafi inda wasu ke cewa ni ce zan gaji karagar mulki, wasu nace ni ce zan zamo shugabar su,. https://youtu.be/bq_-9I3FtnA Al'amarin da ya harzuƙa zukatan yan uwana kenan suka kama tafarfasa tamkar zasu kone, Duk wanda ya kalla ne daga cikin su sai naga ya kada mini uwar harara Sai da kowa ya zauna abisa kujerar da aka tanadar ma sa Sannan waziri ya miƙe tsaye ya ɗaga hannun sa fadar tayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta, Sannan ya fuskanci jama'a yayi gyaran murya yace "Da farko mu na yiwa jama'a Barka da zuwa wannan fada mai albarka barka da zuwa, Bayan haka koda cewar mutane sun san abinda ya tara mu anan, Amma akwai bukatar nayi ƙarin haske akai, Sanin kanku ne cewa mai girma sarki ishwar ya kwanta jinyar rashin lafiya tsawon lokaci Bisa wannan dalili ne yasan ya sarki yayi umarni da a tura su yarima ubaiyu su shiga izuwa duniya domin su nemo maganin da zai warkar da cutar mai martaba, Dukkan wanda ya samu nasarar nemo maganin da ya warkar da cutar mai martaba to fa shine zai gaji karagar mulkin wannan birni mai albarka, Saboda haka yanzu za muyi wa su yarima rakiya har izuwa kofar gari tun da dama tuni an tanadar musu dawakai da abin guzuri, Koda waziri ya zo daidai nan azancen sa sai muka miƙe tsaye daga wajen zaman mu muka nufi kofar fita daga fada, waziri,yan majalissa da sauran jama'ar gari suka mara mana baya, Yayin da aka fita sai muka kama dawakan mu muka sakar musu linzami, Sai da aka yi mana rakiya har izuwa kofar gari sannan kowanne mu ya debi dakarun rakiyar sa guda Ɗari biyu da ɗoriya ya nausa cikin daji, Ma'ana yarima ubaiyu ya nausa izuwa bangaren yamma, Hushriba gudu,yarima zafiyar arewa, ni kuma nayi gabas, Kowa ya rabu da ɗan uwan sa, sai na shafe tsawon Sa'a uku i na gudu tare da dakaru na sannan na yada zango, Bisa mamaki sai naga dakaru na na rakiya sun zare makaman yaƙi sun afka mini domin su hallaka ni dakyar da siɗin gishi na tsira da raina bayan na samu manyan raunuka. Wannan shi ne taƙaitaccen labari na da kuma abinda ya sanya na fito farautar yaro Humair kuma na taimaka maka wajen ceton rayuwar sa domin ya taimaka mini na sadu da Humairu SARKIN SADAUKAI. Sa'adda jaruma Husnaila tazo dai dai nan a labarin ta sai saurayi Hizmal ya kamu da matukar tausayin ta ya dube ta a nutse yace"yake Husnaila haƙiƙa labarin ki cike yake da ban tausayi, Ina mai tabbatar miki dacewa matsawar ina numfashi zan taimaka miki wajen cika burin mahaifin ki, Sa'adda Husnaila taji wannan batu daga bakin Hizmal sai ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa, Daga wannan ne kuma sai fira ta ɓarke a tsakanin su, Wannan shi ne abinda ya faru ga baƙon jarumi wato jaruma Husnaila,da saurayi Hizmal a cikin gidan tsira bayan sun samu nasarar tseratar da Yaro Humair makaho daga sharrin sarki shazwan wanda yake son ya hallakashi domin ya bayar da jinin sa ga abin Bautar su don tseratar da jama'ar birnin sa daga saharrin GOBARAR DAJI. *****. *****. ***** Duk wanda ka gani a birnin tsakanin maza, mata, yara da manya kowa gudu yake domin ya tsira da rayuwar sa, Kaico! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sama sa rana kuma ita GUGUWAR ANNOBA idan ta taso babu mai ɗauke ta face Ubangiji, Babu abinda zai karya zuciyar mutum kuma ya sanya shi zubar da hawaye Face idan yaga yadda wata irin guguwar Wuta ke kama jikin yara ƙanana da mata suna ci da wuta suna ihu da kururuwar neman taimako amma babu mai ceto, Wani abin takaici shine hatta kwalbati da hanyoyin ruwa wuta ke ciki babu wani waje da mutum zai sami fakewa, Kafin shuɗewar rabin sa'a gaba ɗaya birnin ya cika da gawarwakin yara da tsofaffi, Gidaje duk sun rushe sun ƙone kurmus,ihu da koke-koken ƙananan yara da mata ya cika dodon kunne, mutane suka dunga guje-guje gami da ifice-ifice, Komai rashin imanin mutum idan yaga wannan ƙazamar musiba dole ne ya zubar da hawayen tausayi. Ana cikin wannan musiba ne su Sarkin bokaye suka bayyana a dai dai kofar fada, Sa'adda suka ga yadda wannan GOBARAR DAJI ke hallaka jama'ar birnin su sai suka cika da matukar tausayi da baƙin ciki, Waziri Rufyan ya dubi Sarkin bokaye Dargas cikin tashin hankali yace "Ya shugaban bokaye Yakamata kayi wani abu game da wannan musiba, Domin fa idan musibar nan tayi tsamari karshe zamu iya rasa dukkan iyalan mu Bama jama'a birnin mu kaɗai, Koda jin wannan batu daga bakin waziri Rufyan dai sarkin bokaye ya dake murtuke fuska ya dubi waziri Cikin alamun karayar zuci yace Ya shugaba na shin ka manta ne cewa yau tsawon shekaru wannan musiba tana bayyana amma duk lokacin da zata taso ilimin tsafi baya taɓa tasiri akan ta, Duk lokacin da nayi yunkurin aiwatar da wani al'amari akan hakan zan iya rasa dukkan sirrikan tsafi na, koda boka Dargas yazo dai dai a zancen sa sai idanun sa suka kaɗa kuma kwallar takaici ta zubo masa, Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga wani mahayi ya bayyana bisa kan ingarman doki sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ya tunkaro inda su Sarkin bokaye suke tsaye yana mai ratsawa ta cikin gagarumar wutar dake ci Amma bisa mamaki shi dokin da yake kai wutar bata kama jikin su ba. Al'amarin da yayi matukar ɗaurewa su Sarkin bokaye kai kenan kuma ya basu mamaki, Kawai suka saki baki suka kura mahayin idanu, Lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku hamsin ba, A sannan ne su Sarkin bokaye suka fahimci cewa mahayin ya mace ce kyakkywa ta gaban kwatance, Lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin bata huce taku goma sai budurwar ta ja linzamin dokin ta ta tsaya cak, Kawai sai buɗe bakin ta ta karanto waɗansu dalasimai Tana mai nuna sararin samaniya da hannayen ta biyu Tana gama rufe bakin ta sai wata walkiya da tsawa suka bayyana a sararin samaniya haɗe da ci da Sannan ruwan sama ya kece tamakar da bakin kwarya, Amma wani abun mamaki ruwan bai jiƙa budurwar ba, Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa hamsin ba gaba ɗaya GOBARAR DAJI dake birnin ta mutu ƙurmus, A sannan ne jama'a suka fara dawowa cikin hayyacin sa kowa ya shiga duba irin muguwar asarar da yayi, A lokaci guda ruwan saman ɗauke ɗif tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Cikin alamun tsananin farin ciki maral misaltuwa Sarkin bokaye, waziri Rufyan Sarkin yaƙi suka taka da kafafun su izuwa inda budurwar take tsaye, Lokacin da suka isa daf da ita sai suka ƙara cika da mamaki ainun Ita dai budurwar takasance kyakkyawa tagaban kwatance, tana da kyan diri da sura tamkar ita ce ta ƙera kanta yadda take buƙata, fatar jikin ta wankar tarwaɗa ce ma'ana ba baƙa ba ce ba fara ba, A gadon bayan ta tana rataye da wata zabgegiyar takobi mai tsawo da kaifin tsiya, shekarun budurwar ba zasu haura ashirin ba Lokacin da aka isa sai boka Dargas ya buɗi baki cikin tattausar murya fuskar sa cike da annuri ya dubi kyakkyawar budurwar yace "Yake wannan jaruma ma'abociyar abubuwan ban al'ajabi mun zo ne gareki domin muyi miki godiya bisa wannan gagarumin taimako da kika yi mana na ceton miliyoyin jama'ar birnin mu daga musibar GOBARAR DAJI, Sannan idan babu damuwa muna san ki sanar damu wace ce ke a cikin jerin bokayen duniya,? Shin akwai wani abu da kike da bukata daga garemu har ya shigo dake cikin wannan ƙasa ta mu mai albarka? Koda jin waɗannan tambayoyi daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kyakkyawar budurwar ta bushe da yar karamar dariya Sannan daga bisani ta tsuke baki tayi gyaran murya cikin tattausar lafazi mai daɗin sauraro tace "Yaƙi waɗannan SARAKAI kuyi sani cewa ceton rayuwar al'ummar ku a waje na tamkar taimakon kai na ne, Nasan za kuyi mamakin jin na faɗi haka, amma zan sanar ɗaku abinda zai shafe mamakin a cikin amsoshin da zan baku anan gaba, Da farko dai ni suna Hushriba bintu ishwar mahaifina ƙasurgumin matsafi ne da yayi shura A halin yanzu na fito ne bisa umarnin mahaifina na ne mo masa maganin cutar da ke damunsa Bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa maganin dana fito nema tabbas yana da alaƙa da musibar da ta addabe ku ta ANNOBAR GOBARAR DAJI. Don haka nake so mu haɗa karfi da karfe domin kowanne mu ya amfana Ina nufin bani ƙishiri na baka manda, domin duka mu samu tsira, Sa'adda Hushriba tazo dai dai nan azancen ta, sai sarkin bokaye Dargas ya dube ta cikin farin cikin matukar farin ciki maral misaltuwa yace "Ya jaruma ma'abociyar abubuwan ban al'ajabi tabbas munyi matuƙar farin ciki da bayyanar ki a cikin wannan birni, Akwai bukatar akai ki masauki ki samu hutu kiyi kalaci sannan daga bisani sai mu tattaunawa, Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye sai Hushriba ta gyaɗa kai alamar gamsuwa, Gama faɗin hakan keda wuya sai sarkin bokaye yayi wa wani badakare inkiya ta da hannu take badakare ya zaburi dokin sa ya shige gaba yana mai yiwa jaruma Hushriba nuni da ta biyo bayan sa, Batare da wani jinkiri ba Hushriba ta sakarwa dokin ta linzami ta mara masa baya, A sannanne Sarkin bokaye ya dawo da uban sa ga waziri ya dubesa cikin ladabi yace "ya shugaba na shin me ka fahimta game da wannan bakuwar jaruma Hushriba? Koda jin wannan tambaya sai waziri ya nisa Sannan yayi ajiyar zuciya yace"Ya Sarkin bokaye kayi sani cewa duk da irin taimakon da Hushriba tayi mana baza mu saki jiki da ita ba Lallai akwai bukatar ka gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka domin ka tabbatar AAA, kuma wajibi ne mai martaba sarkin yasan da wannan al'amari Dajin wannan batu sai sarkin bokaye yace "Maganar ka haƙƙun yakai waziri zan zartar da duk abinda ka umarta, 08137237071 Daga wannan batu ne kowa ya kama gaban sa waziri ya huce izuwa cikin gidan sarauta, Sarkin bokaye da sauran Yan uwan sa bokayen suka durfafi ɗakin sirri domin gudanar da bincike game da jaruma Hushriba, **** SARKIN SADAUKAI Book 2 page 2 Littafin Yaki Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 BIRNIN TEHRAN Acan birnin Tehran kuwa, tun sa'adda sarauniya Abidatul-auliya ta gana da boka shubairu wanda ya bayyana gare ta acikin surar kyakkywan tsuntsu Sai ta kasance a koda yaushe cikin zaƙuwa take domin ta ga cewa ranar tafiya izuwa dajin Baitul-shamshan tazo domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI, Bangare guda kuma zuciyar ta cike take da tsananin begen saurayi shubairu, A kowa ne dare sai ta zauna a harabar turakar ta tana tana kallon inda saurayi Hibairu ya bayyana a gare ta tana mai karanta waƙoƙin so da bege, Kaico ! Haƙiƙa so shine shammatar zuciya, tabbas Abidatul-auliya ta kamu da tsananin kaunar shubairu wacce baza ta misaltuwa ba, Kuma wani abin mamaki shine raɗaɗin da ciwon ta ke yi mata sai yazamana ta samu sassauci, Haƙiƙa SO yana tasiri matuka wajen ba wa jikin ɗan adam wata garkuwa ta musamman. Wannan shi ne abinda ya faru ga sarauniya Abidatul-auliya dake birnin Tehran Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sai da suka shafe tsawon kwanaki uku a cikin gidan tsira tare da yaro Humair makaho, Tsawon wannan lokaci da suka shafe a cikin gidan duk wani abu da suke buƙata na sha'anin rayuwa da sun bukace shi sai suga ya bayyana gaban su, Kuma a iya tsawon wannan lokaci shaƙuwar soyayya ta ƙara kullu wa ainun tsakanin jaruma Husnaila da saurayi Hizmal A ranar kwana na ukun ne da la'asar sakaliya su Hizmal suka kammala shiri domin cigaba da gudun tsira, domin tseratar da rayuwar yaro Humair, Bayan sun kammala shirin ne Sai saurayi Hizmal ya giya yaro Humair a gadon bayan sa, Sannan suka durfafi wata kofa ta musamman a cikin gidan domin su fita, Lokacin da suka isa bakin kofar sai suka tarar da kofar a garƙame babu alamun wajen da za'a bude ta, Al'amarin da ya dugunzuma hankalin su kenan ainun suka shiga dogon nazari, Suna cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka ga wani aljani ya bayyana gare su ya faɗi yayi sujjada, Aljanin yakasance gabjejen kato mai tsawo da kwarjini, yana da fuka fukai guda huɗu, da jela guda ɗaya, yana da kwalakwalan idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancin sa kuwa ashafe yake tamkar bada shi yake shaƙar numfashi ba, a haɓar sa yana maƙale da dogon gemu fari sol mai tsawon kamu huɗu Hakika wannan aljani ya cika mai ban tsoro gami da muni Su kansu su saurayi Hizmal a matsayin su na zaratan Jarumai sai da suka firgita da sukayi arba da aljanin, Aljanin ya ɗago da kansa sama ya dubi Hizmal da sunaila ya buɗe tafkeken baƙin sa mai kama da kofar gari, sannan yace cikin kakkausar murya, "Da farko dai suna na Marhutul-Azab kuma nine hadimin dake kula da wannan gidan tsira yau fice da shekaru dubu bakwai, Ya ku waɗannan bil'adama ma'abota gudun tsira kuyi sani cewa na bayyana gareku ne domin na fitar daku daga cikin wannan gida na kai mu duk inda kuke bukata a fadin duniya, Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai Hizmal da sunaila suka cika da mamaki , Sunaila tace "Yakai wannan aljani haƙiƙa munyi farin ciki maral misaltuwa bisa wannan taimako da zaka yi mana, Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina so kayi sani cewa tafiya damu abu ne mai matukar wahalar gaske da zai iya jefa rayuwar ka a cikin tsaka tsaka mai wuya, Ina ganin abinda zai fi kawai shine ka nuna mana hanyar da zamu fita kai kuma ka cigaba da gadin wannan gida kamar yadda ka saba , Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Aljani Marhutul-Azab ya bushe da yar karamar dariya mai kama da haniniyar doki sannan yace "Yaku waɗannan bil'adama kuyi sani cewa fiye da shekaru dubu biyu nasan da labarin bayyanar ku a cikin wannan gida dama abinda zai kawo ku nan ɗin Da kuma abinda zaku tafi nema, Bisa al'adar wannan gida kowa ne mai gadi zai shafe tsawon shekaru dubu huɗu ne cif, Kuma a yau ne shekarun kammala aiki na suka cika na samu yanci zan iya shiga ko ina a duniya Babban muradi na shine na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI wanda shine kuka fito ne ma Tsawon shekaru na shafe ina jiran zuwan ranar da zan sadu daku domin na cika burina na ceto rayukan al'ummar kabilar mu, Wanda a halin yanzu ruhikan su ke ajiye a can fadar Sarkin bokayen duniya DURUSUL-FANNAR A bisa cikin wata akwatu ta baƙin ƙarfe, Kowa ce rana Sarkin bokayen duniya sai na tsafe ruhikan kabilar mu da wani sinadaran sihiri, Da zarar ya kammala sihirin waɗannan ruhikan zasu koma nasa, Ma'ana kenan zai zamo cewa yana ɗauke da rayuka guda dubu arba'in, Kowa ne ruhi guda ɗaya zai shafe shekaru dubu huɗu kafin ya mutu, Baban burin Sarkin bokayen duniya shine ya cigaba da rayuwa da waɗannan ruhikan bazai mutu ba har abada, zai cigaba da kasancewa SARKIN SARAKAI, Bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa babu wani mahaluki da zai iya zuwa fadar Sarkin bokaye ya ceto ruhikan kabilar mu face SARKIN SADAUKAI Hibairu, Sannan babu wani abu dazai iya buɗe wannan akwatin baƙin ƙarfe face ZOBEN SHIRIn dake hannun jarumi Hibairu kuma zoben ne zai karya sihirin dake jikin ruhikan kabilar ta mu har ya dawo zuwa gangar jikin su su cigaba da rayuwa kamar kowa, Sa'adda aljani Marhutul-Azab yazo nan azancen sa sai hawaye suka zubo daga idanuwan sa, Al'amarin da yayi matukar bawa su saurayi Hizmal tausayin sa kenan, Hizmal ya dube sa cikin matukar damuwa yace "'yakai Marhutul-Azab kayi sani cewa haƙiƙa labarin ka akwai ban tausayi duk da ka bamu shi a takaice, Ina mai tabbatar maka dacewa ni da abokiyar tafiya ta zamu taimaka ka har mu sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI tun da dukkan bukatar mu kusan ɗaya ce Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe zuciyar Marhutul-Azab ya buɗi baki karo na uku yace Yaku abokanan tafiya ta kuyi sani cewa ina farin cikin sanar da ku cewa Ina ɗauke da dukkan taswirar fadar Sarkin bokaye, Wacce babu wani mahaluki dazai shiga wannan fada face yana tare da taswirar, A halin yanzu nasan cewa kowa ya ɗora idanun sa akan taswirar, Wacce ko shi kansa Sarkin bokaye basan cewa ina ɗauke da wannan taswira ba , Tsawon shekarun da na shafe ina gadin gidan tsira domin na mallaki wannan taswira ne, Na ji ajikana cewa wannan tafiya tamu cike take da nasara, Tun da gashi muna tare da taswirar fadar Sarkin bokaye da kuma yaro Humair makaho wanda shine kaɗai a faɗin duniya ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI, Sa'adda aljani Marhutul-Azab yazo nan azancen sa sai kowa ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa, Gama faɗin hakan ke da wuya sai Marhutul-Azab ya shimfide gadon bayan sa Hizmal goye da yaro Humair da sunaila suka hau suka zauna, Sannan Marhutul-Azab ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya ya na mai keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba, Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Husnaila da saurayi Hizmal a cikin gidan tsira domin tseratar da rayuwar yaro Humair makaho, **** Lokacin da boka Dargas da sauran tawagar matsafa biyar suka bayyana a ɗakin sirri domin gudanar bincike bisa bayyanar bakuwar jarumar da ta ceci rayuwar al'ummar kasar daga GOBARAR DAJI wato gimbiya Hushriba bintu ishwar, Bayan binciken da bokayen suka yi suka gabatar da jawabin binciken su Sai sarkin bokaye Dargas ya dube su yayi gyaran murya yace "Bisa ga dogon nazari da kuma abinda bincike ya tabbatar shine jaruma Hushriba ba tazo domin ya cutar da mu ba kawai dai taso ne mu haɗa karfi da karfe domin kowanne mu ya kai ga biyan buƙatar sa, Amma sai dai ba zamu saki jiki da ita ba domin kunsan cewa ba'a bawa mata yarda a cikin al'amura Matukar baku mallake su ba shin ina cewa kun taɓa karanta Littafin KUNDIN MATSUBBATA Hikayar jarumi Hilairu da Baiwa luzra Kun ji irin cin amana da yaudarar da tayi masa daga karshe m Bayan ya siyar da rayuwar sa ya ceto ta da ma mahaifan ta, Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai sauran maysafan su kayi na.am Boka Dargas ya ɗora dacewa "wani abun takaici da na gani a cikin halarar tsafi ma shine tuni su saurayi Hizmal sun samu nasarar fice daga cikin gidan tsira sun bazama izuwa duniya bisa taimakon wani hatsabibin aljani mai Marhutul-Azab da halin yanzu babu saurayin aljani mai tashen balaga kamar sa a fagen karfin damtse da jarumtaka, Yanzu batare da bata lokaci ba zan umarci hadimin aljani na domin ya dawo dasu mai girma sarki Shazwan domin a halin yanzu jiran gawa babu rai suke yi a can gidan tsira, Sa'adda Sarkin bokaye Dargas yazo nan a jawabin sa shafi wani gurun tsafi a damtsen hannun sa Take wani aljani mai kama da tsuntsun batoyi ya Bayyana gare sa, ya kwashi gaisuwa Boka Dargas ya dubesa ya kai Haulatul- infal kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa gidan tsira ka ɗauko mai martaba sarki Shazwan da tawagar sa acan inda ka dauko mu a ɗazu ni da jama'a ta, Koda jin wannan umarni sai Aljani Haulatul-infal ya risina sannan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Daga wannan jawabi ne kowa ya kama gaban sa ɗakin taron ya watse, Wannan shi ne abinda ya wakana acan birnin zawatul-ifdal. Lokacin da aljani Marhutul-Azab ya tsala da matsanancin gudu a sararin samaniya ɗauke da Jaruma Husnaila,saurayi Hizmal da yaro Humair makaho, Sai ya wanzu yana mai keta gajimare tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya, Nan fa Saurayi Hizmal ya kama kalle-kalle yana mamakin yadda sararin samaniya yakasance domin wannan ne karon sa na farko a rayuwarsa da ya taɓa tashi sararin samaniya bisa kan aljani, Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan tafiya babu wanda yace ƙala, Sai daga bisani ne jaruma Husnaila ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki tayi gyaran murya sannan dubi saurayi Hizmal tace"Yakai Hizmal shin kana ganin cewa yanzu kai tsaye zamu huce ne izuwa hanyar da zata sada mu da dajin Baitul-shamshan?, ko kuwa zamu jira ne har izuwa lokacin da SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI? Koda jin waɗannan tambayoyi Daga bakin Husnaila sai Hizmal yayi gyaran murya yace "Ya sunaila haƙiƙa kin kawo maganganu masu muhimmanci daya kamata muyi dogon nazari akan su, Amma dai bisa shawara ta ina ganin zai fi kyau ace mun tunkari dajin Baitul-shamshan domin a halin yanzu, Dalili na na faɗin hakan kuwa shi ne a Kowa ne hali bokaye,sarakai cikin farautar yaro Humair suke Idan muka ce zamu tsaya sai ranar da jarumi Hibairu zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI zai kasance waɗansu sun riga mu isa dajin Baitul-shamshan, Haƙiƙa dai masu iya magana na cewa a bari ya huce shine ke kawo rabon Wani, Koda jin amsar tambayoyin da ga bakin Hizmal sai sunaila tayi shiru tamkar tana nazari Daga bisani ta dubi aljani Marhutul-Azab tace"yakai Marhutul-Azab mene ne ra'ayinka akan wannan magana, Marhutul-Azab yace cikin kakkausar murya"Tabbas maganar da Hizmal ya faɗa shawara ce mai kyau, Domin abinda baku sani ba shine, Daga nan izuwa dajin Baitul-shamshan tafiya ce ta tsawon shekaru ɗaya bisa saurayin aljani mai tashen balaga, Amma ni zan iya gajarce mana tafiyar cikin kwanaki sittin da huɗu, Domin ahalin yanzu a kaf jinsin aljanu babu aljani mai tashen balaga da karfin gudu tamka ta, A yau saura kwanaki sittin da huɗu cif jarumi Hibairu ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI. Kun ga kenan ranar da zamu isa dajin ranar ne SARKIN SADAUKAI zai bayyana a sararin duniya, Bani da tabbacin akwai wanda zai riga mu isa dajin Baitul-shamshan ɗin, Koda jin wannan wajabi daga bakin aljani Marhutul-Azab sai Hizmal da sunaila suka cika da matukar farin maral misaltuwa, Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru aka cigaba da tafiya, Wannan shi ne abinda ya faru da Jaruma Husnaila da saurayi Hizmal da yaro Humair makaho, Bayan aljani Marhutul-Azab ya dauko su daga cikin gidan tsira, ***** BAHREN A Can ƙasar bahren kuwa, al'amarin sarki uslaim kuwa tun ranar da boka ƙarzum ya bayyana gare sa, Domin ya yi masa bayani game da batar yar sa gimbiya zarifa, Bai sake bayyana a gare sa ba sai wata rana da hantsi sarki uslaim na zaune a bisa karagar sa ta mulki a fadar sa, A wannan lokaci fadar ta cika Maƙil da al'umma babu masaka tsinke kowa na zaune bisa kujera, Kwatsam sai aka ga wani bakin duhu ya bayyana a tsakiyar fadar Sannu a hankali sai duhun ya riƙiɗa izuwa wani dattijo fari kakkaura ma'abocin kwarjini, Fuskar sa cike da ƙasumba da gemu farare sol Sanye da jajayen tufafi, hannun sa riƙe da kwagirin tsafi dake canza launi izuwa siffa daban daban-daban, Ba wani ba ne wannan dattijo ba face boka ƙarzum Da bayyana sa sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa Ga sarki ƙarzum, Bayan sarki ya amshi gaisuwar sai boka ƙarzum ya miƙe tsaye tsam ya nufi wata ƙasaitacciyar kujera dake kusa daf da inda karagar mulki take yana mai dogare da kwagirin sa, Ya na isa ya zauna abisa kujerar, sai ya juya ya fuskanci sarki uslaim fuskarsa babu yabo babu fallasa cikin wata irin kakkausar murya yace"ya shugaba na kayi sani cewa bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa lokacin gudanar da tafiyar mu yayi domin saduwa da SARKIN SADAUKAI domin ka bayyana masa buƙatar ka na son ya ceto maka yarka gimbiya zarifa daga fadar Sarkin bokaye, Ya shugaba na kayi sani cewa a halin yanzu ilimin tsafi ya tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki dazai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI face wani yaro da ya kasance makaho ana kiransa da suna Humair, A halin yanzu wani hadimin aljani da ake wa laƙabi da Marhutul-Azab ya dauki yaro Humair tare da waɗansu jarumai biyu domin su isa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI Domin su ma su bayyana ma sa nasa bukatun, Saboda a halin yanzu ba mu da wani abin farauta da huce yaro Humair makaho, Domin dole shine zai iya magana baki da baki da Sarkin sadauki, Ya zama wajibi agare mu mubi sahun aljani Marhutul-Azab domin mu riski yaro Humair, Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan a jawabin sa sai sarki uslaim ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa bai san sa'adda murmushi haɗe da yar karamar dariyar farin ciki suka suɓuce masa ba Cikin hanzari sarki uslaim ya mike tsaye zumbur ya shiga izuwa gidan sarauta domin ya kimtsa, Jim kadan sai gashi ya bayyana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi tare da dakarun rakiya gudu dubu ashirin, haɗe abin guzuri da kuyangi masu hidima, Batare da wani ɓata lokaci sarki uslaim ya miƙa rikon sarautar sa ga wazirinsa, Sannan aka dunga aka fita izuwa wajen faɗa, bayan an fita ne sai boka ƙarzum ya kwalawa hadimin aljanin kira har sau huɗu, Aljani ya bayyana gare sa ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa Aljanin yakasance gabjejen kato mai tsawo da kwarjini sosai, Komai jarumtakar Mutum idan yayi arba dashi sai ya ɗimauce saboda tsanin munin sa Boka ƙarzum ya dubesa yace "Yakai Darmanu ibn kauƙas kayi sani cewa bakomai ne yasanya na kirawo ka izuwa nan ba Sai domin ina so ka ɗauke mu ni da wannan tawagar Kabi sahun aljani Marhutul-Azab da halin yanzu ya durfafi dajin Baitul-shamshan, Ina so ka cimmu su a Kowa ne, ya Darmanu ibn kauƙas kayi sani cewa matsawar ka gudanar da wannan aiki yadda na buƙata, To zan yan taka da bauta da ka shafe tsawon shekaru kana yi agareni, Koda jin wannan umarni daga bakin boka ƙarzum sai Aljani Darmanu ya sake risina agareshi yace "An gama ya shugaba na yana Gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa take sarki uslaim da boka ƙarzum suka hau bisa kan sa suka zauna, Dakarun rakiya, guzuri gami da kuyangi suka koyi koyi dasu suka hau bisa gadon bayan Aljani Darmanu, Cikin kuzari da karfin damtse Darmanu ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya tare da kaɗa manyan fuka fukan sa, Jama'a na ɗaga musu hannu tare yi musu fatan samun nasara har suka ɓace ɓat a cikin gajimare tamkar basu taɓa wanzuwa ba, Wannan shi ne abinda ya faru da sarki Uslaim na Birnin bahren wanda sarkin bokayen duniya ya sace masa yar sa gimbiya zarifa Kuma a halin yanzu ya fito farautar yaro Humair makaho domin ya samu nasarar saduwa Hibairu SARKIN SADAUKAI. Lokacin da aljani Haulatul-infal ya ɓace ɓat daga ɗakin sirri domin zartar da umarnin sarkin bokaye Dargas, Kamar yadda boka Dargas ya umarce sa haka al'amarin ya kasance domin cikin abinda bai huce daƙiƙa hamsin ya bayyana a kofar gidan sarauta ɗauke da sarki shazwan da tawagar sa, Bayan Haulatul-infal ya sauke su sarki shazwan sai ya yunkura ya sake tashi izuwa sararin samaniya ya ɓace ɓat Sarki shazwan bai samu ganawa da Hushriba ba sai da gari ya waye bayan ya kammala kalaci sannan Hushriba da waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar matsafa suka iske sa a cikin turakar sa ta ganawa da baƙi, A wannan lokaci sarki shazwan na zaune bisa wata ƙasaitacciyar kujera ya caɓa ado irin na hamshakan sarakai, Kyawun surar sa ya bayyana a fili, jikin sa na fitar da wani irin kamshin turare mai daɗin gaske, Lokacin da gimbiya Hushriba tayi arba da fuskar sarki shazwan sai taji zuciyar ta ta buga da karfi a karo na farko ta kasa gane shin mene ne abinda ya sanya zuciyar ta zata buga da karfin, Shin ta faɗa farkon soyayya ne ko kuwa tsananin kwarjinin sarki shazwan ne Amsar tambayoyin da Hushriba ta kasa bawa kanta kenan Ta samu waje ta zauna bisa kujerar da aka tanadar mata dake fuskantar sarki shazwan, Bayan kowa ya zauna ne bisa wajen zamansa Sai sarki shazwan ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu, Duk wanda sarki shazwan ya kurawa idanu sai kaga ya sunkiyar da kan sa ƙasa, Amma bisa mamaki koda ya haɗa idanau da Hushriba sai ya ga ita ma ta ƙura masa idanun ko kiftawa bata yi, Al'amarin da yayi matukar ba sa mamaki kenan yace a ransa shin wannan jarumi bata san Mene ne matsayi na ba ne ta ƙura mini idanu batare da ladabi ba Wani ɓangare a zuciyar sa kuma na cewa shin baka lura da nau'in kallon da Hushriba ke yi maka ba ne, Tabbas kallo mai ɗauke da alamun shauƙin so To kai ma meyasa ka cigaba da ƙura mata idanun fiye da ƙima Sa'adda sarki shazwan yazo Nan a tunanin sa sai yaji kunya ta kama sa, Kawai sai ya dawo da duban sa ga Sarkin bokaye yayi gyaran murya sannan ya fara magana akaro na farko cikin nutsuwa "Da farko ina yiwa dukkan waɗanda suka hallara a wannan waje Barka da zuwa tare da yiwa bakuwar jaruma maraba, Bayan haka dalilin daya tara ku wannan waje shine domin na saurari dukkan bayani game da wannan musiba da ta afka mana ta GOBARAR DAJI da kuma karin bayani akan hanyar magance wannan al'amari, Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye Dargas ya yi gyaran murya yace"Ya shugaba na dukkan wani bayani da Ya kamata nayi maka nayi maka shi game da bayyanar wannan jaruma wato Hushriba, Abinda ya rage dai yanzu kawai shine mu saurari bayani daga bakin Hushriba akan hanyar da zamu kawar da wannan annoba, Sa'adda sarkin bokaye Dargas ya zo nan azancen sai jaruma Hushriba tayi gyaran murya tace "Yakai sarki shazwan kayi sani cewa babban muhimmin abinda ya kawo ni wannan ƙasa taka kuma har na ceci rayuwar al'ummar kasar ka daga ANNOBAR GOBARAR DAJI Shine yaro Humair da kuke nema domin ku yanka da ku bayar da jinin sa ga abin Bautar ku domin kare kanku daga GOBARAR DAJI A halin yanzu ni ma shi na fito farauta domin na cika burina na mallakar tsumin tsafi dake fadar Sarkin bokaye, Hakan kuma ba zai tabbata ba face na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI na bayyana masa buƙata ta ta zuwa fadar Sarkin bokaye domin ya samo mini tsumin tsafi Yaro Humair shine kaɗai yasan Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI Kun ga kenan a halin yanzu ina matukar kaunar ganin Yaro Humair makaho a raye saɓanin ku da kuke yunkurin hallaka sa, Hanyar da zaku kawar da wannan guguwar annoba kuwa shine, A halin yanzu saura kwanaki ɗari uku da sittin da uku SARKIN SADAUKAI HUBAIRU ya kammala bawa tsuntsun tsafin sa horan yaƙi domin ya samu nasarar fito wa daga dajin Baitul-shamshan ya bayyana a wannan duniya tamu Ya kai wannan sarki kayi sani cewa kasar ka ce ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara bajewa daga doran ƙasa, Kuma yaro Humair ne kaɗai ne zai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI har ya fahimci hanyar da zai roƙar muku alfarma a wajen sa, Kaga kenan a halin yanzu idan ma kun mallaki yaro Humair kun yanka sa kun bayar da jinin sa ga abin Bautar ku Dai -dai da kun dabawa kanku wuƙa domin dazarar SARKIN SADAUKAI ya fito daga dajin Baitul-shamshan zai baje Birnin ka baki ɗaya babu wata halitta mai rai da zai bari ta cigaba da numfashi, Sa'adda jaruma Hushriba tazo dai- dai nan a jawabin ta sai hankalin gaba ɗaya jama'ar dake cikin turakar ya dugunzuma ainun Kuma ɗakin yayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta, Sai daga bisani Hushriba ta cigaba da cewa "A halin yanzu zama bai same mu ba, Dole mu sake bazama farautar yaro Humair makaho domin ya zamo cewa mun mallake sa, Domin hakan ne kawai zai sanya dukkan mu mu kai ga cika burikan mu, 08137237071 Wani abu da baku sani ba shine wannan mahayi da ceci rayuwar yaro Humair da saurayi Hizmal ba wani ba ne face yar uwa ta gimbiya Sunaila, Nasan cewa ko wace yar uwa ta kuma nasan hanyar da zan rabata da yaro Humair Lokacin da gimbiya Hushriba ta sake zuwa nan azancen ta sai kowa ya cika da matukar farin ciki gami da mamaki, Hushriba tayi ajiyar zuciya ta ɗora da cewa "A daren yau nake so kayi umarni ga dukkan al'ummar wannan birni da su hallara a fada a lokacin da zamu tafi izuwa farautar yaro Humair domin masu iya magana na cewa da zafi-zafi akan daki ƙarfe, Tabbas a lokacin da jama'a suka hallara zai basu wani sinadaran tsafi da zasu nasu kariya daga GOBARAR DAJI har zuwa lokacin da zamu dawo daga abin da muka fita farauta, Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai sarki shazwan ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa, Nan take batare da wani ɓata lokaci ya umarci shamaki ya sanar da zagi cewa sarki yana son ganin kowa a fada kuma ba'a ɗauke wa kowa ba koda jariri ne sabuwar haihuwa, Bayan sarki shazwan yayi wannan umarni nan take ya sallami su waziri Rufyan domin kowa yaje ya kammala shiri kuma yayi bankwana da iyalan sa, Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Hushriba da su sarki shazwan. Lokacin da aljani Darmanu ya tsala da azababban gudu a sararin samaniya ɗauke da sarki Uslaim,boka ƙarzum,da dakarun rakiya domin rabi sahun aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da yaro Humair,saurayi Hizmal da sunaila domin ya cimmu su, Sai Darmanu ibn kauƙas ya wanzu yana tsala Azababban gudu babu sassauci yana keta gajimare, Ana cikin wannan tafiya ne sai yazamana cewa rana ta kwalle tayi tsananin zafi, Don haka sai boka ƙarzum ya umarci Aljani Darmanu da ya yada zango, Koda jin wannan umarni sai Darmanu ya saki fuka- fukan ya sauka ƙasa luuuh! Ya sauƙa a bisa turba, inda ya saukan ya kasance daji ne mai yalwar duwatsu, koramu haɗe kwazazzabai, Har wasu daga cikin tawagar rakiya sun yunkura zasu sakko daga kan Aljani Darmanu sai boka ƙarzum ya daka musu tsawa yana mai nuna cewa su dakata, Kawai sai ya dubi gabas,yamma,kudu da arewa, Sannan ya juya ya dubi Sarki uslaim cikin ladabi yace "Ya shugaba na wannan daji jikina bai kwanta da shi ba, da alamu akwai wani tarko mai cutar wa, ina ganin zai fi kyau mu sake cigaba da tafiya har sai mun samu waje mai cikekken tsaro sannan sai mu haɗa zangon, Kafin boka ƙarzum ya gama rufe bakin sa sai kawai akaga waɗansu waɗansu ayarin gwaggwan birrai na fito wa daga kowace kusurwa a dajin waɗansu na dirowa daga saman bishiyoyin dajin waɗansu daga cikin ƙarƙashin ƙasa, Kafin kace me yarin birran sun yi musu ƙawanya Su dai birran suna da girma tamkar toran Giwa munin fuskokin su kuwa ya huce misali,gaba ɗaya jikin su cike yake da gashi buzu-buzu babu kyan gani gaba ɗayan su na shanye cikin sulken yaƙi nau'i daban -daban tamkar sun kasance bil'adama, A hannayen su kuwa suna dauke da miyagun makamai masu barazana da dukkan wata halitta mai numfashi. Lokacin da aka fara kallon- kallo tsakanin ayarin gwaggwan birrai da su sarki uslaim, Sai aka shafe tsawon daƙiƙa goma a cikin wannan hali, Sai daga bisani ne su sarki uslaim suka yi wuf suka zare makaman yaƙin su, A lokacin da ayarin gwaggwan birran su kayi kukan kura suka yi ɗauki kansu, Lokacin da aka haɗu da juna nan take waje ya kare da azababban yaƙi, Bangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta Ana fara wannan artabu ne fa su sarki uslaim suka fara gane kuren su Domin duk inda ɗaya daga cikin gwaggwan birran ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun rakiya na zube wa ƙasa matattu, Wani abu da ya ɗaurewa su sarki uslaim kai kuma ya basu mamaki shine yadda akayi makaman su suka kasa yin nasara akan gwaggwan birran Abangaren boka ƙarzum kuwa ya wanzu a tsakiyar birran tamkar wani ifritu, Sai dai aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa ɗaya daga cikin su sarki uslaim bai samu nasarar koda hallaka gwaggwan birran ba, Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin su kenan suka shiga damuwa ainun bisa ganin cewa Tabbas wankin hula zai kaisu dare, Sa'adda boka ƙarzum yaga cewa idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka zasu rasa rayukan su baki ɗaya sai kawai ya shiga amfani da karfin sihirin tsafi domin ya ga ya ragargaji birran, Amma sai abu ya ci tira,ya zama na cewa yayi amfani da sirrikan tsafi fiye da dubu biyu amma basa tasiri akan birran, Abangaren sarki uslaim kuwa lokacin da ya zurfafa izuwa cikin Kogin tunani domin samun mafita, Koda samun mafitar sai sarki uslaim yayi wuf ya mayar da takobin sa izuwa cikin kube, Cikin wani irin baƙin zafin zafi ya suri wani reshen bishiya dake wajen ya shammaci wani gwaggwan biri ya maka masa akai, Bisa mamaki sarki uslaim yaga gwaggwan birin ya kurma ihu ya faɗi a ƙasa magashiyan, Koda ganin hakan sai sarki uslaim ya zage karfin sa ya shiga yaƙar gwaggwan birran da wannan reshen bishiya, Duk inda ya sanya a gaba sai kaga birran na zubewa kasa magashiyan, wasu sun sheƙa barzahu, Koda ganin yadda sarki uslaim ke samun nasara akan birran sai suka yanyame sa tamkar yadda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro, Domin a tarihin su babu wata halitta da taɓa yi musu barnar da sarki uslaim yake yi musu, Sa'adda su boka ƙarzum suka hango Yadda sarki uslaim ke samun nasara akan gwaggwan birran, Sai kawai su kayi koyi dasu suka shiga ɗaukar rassan bishiyoyin dajin suka shiga dukan birran, Wohoho! Kaico haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da su ka ce inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, kuma idan rawa ta kiɗa ya canza dole ne rawa ta canza, Nan fa yazamana cewa filin yaƙin ya hautsine da ƙarar karafniyar ƙarafa da ihu haɗe da kururuwar birran, Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, bishiyoyi suka dunga rangaji suna faɗuwa ƙasa, Duwatsu kuwa suna karo da juna suna bindiga suna farfashewa, Abangaren aljani Darmanu ibn kauƙas kuwa ya wanzu a tsakiyar birran tamkar GOBARAR DAJI domin duk inda ya kai damƙa da hannun sa sai kaga ya cafko birrai guda biyu ya ɗaga su sama ya maka kansu a jikin duwatsu sun faɗi ƙasa matattu, Lokacin da gwaggwan birran suka ga cewa bala'i yakai ba'a'i sai suka fara kokarin tserewa, Amma sai da su sarki uslaim suka dunga binsu a baya suka ƙure musu gudu suna rafkewa, Kafin shuɗwar Sa'a ɗaya su sarki uslaim sun samu nasarar hallaka ayarin gwaggwan birran, A sannanne ƙura ta lafa kuma kowa ya dawo cikin hayyacin sa, A sannanne sarki uslaim ya lura da irin muguwar barnar da ayarin gwaggwan birran sukayi musu, A kalla sun kashe dakarun rakiya mutum ɗari biyar Batare da bata lokaci ba a kasa shiga kwashe gawarwakin tare da duba lafiyar waɗanda suka samu raunuka, Aka kafa tantuna domin a yada zango, kuma kuyangi suka shiga hidimar dafa abin kalaci, Wannan shi ne abin da ya faru da sarki uslaim da tawagar sa akan hanyar sa ta farautar yaro Humair, ***** Zaratan ƴan mata ne su biyar, kyawawa na gaban kwatance, waɗanda kallo ɗaya zasu iya ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji, Ke ta faman falfala azababban gudu bisa duga-dugan su tamakar zasu fice daga duniyar, Suna gudun abisa cikin kasaitaccen daji mai ɗauke da manyan bishiyoyi, duwatsu, koramu haɗe kwazazzabai, Kallo ɗaya zaka yi wa yan matan ka fahimci cewa sun kasance ma'abota bota rayuwa a cikin daji Saboda tufafin da ke sanye a cikin su yakasance an sana'anta sa ne da fatar damisa,kafafun su ko takalmi babu, Duk sa'adda da yan matan suka ɗaya ɗaga kawunan su izuwa sama sai kaga sun sake zage damtse sun ƙara karfin gudun su fiye da ɗazu suna cikin wannan gudu ne sai kawai suka ji an suri ɗaya daga cikin su an yi sama da ita, Nan fa suka tsaya cak suna haƙi da numfarfashi, tamkar ran su zai fita, Hawaye na zubo wa daga idanun su, su ka shiga dube- dube da kalle-kalle suna masu kwalawa yar uwar tasu kira tare da kiran su nan ta, Daga can kwatsam sai suka an jefo da gangan jikin ta babu kai, Nan fa sauran Yan matan suka sake ɗimauce wa suka sake falfawa izuwa cikin daji domin tsira da rayukan su, Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda yan matan ke gudun tsira dole ne ya zubar da hawaye. Su dai waɗannan yan mata bakomai ne ke biye dasu ba face waɗansu miyagun halittu masu ɗauke da siffa irin ta ƙurar Kuma yan matan sun fito ne daga wani birni da ake yiwa laƙabi da Garul- mausul , Birnin Garul-mausul ya kasance kasaitaccen birni da ya shahara ainun a fagen kasuwanci,noma da kiwo Daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan Jarumai masu juriya a filin daga, Sarauniya Nuwairat bintu Darhaz ita ce ke rike da Sarautar birnin Nuwairat takasance kyakkyawa tagaban kwatance wanda labarin tsananin kyawun ta ya watsu a ko ina a sassan duniya, Mace ce mai matsakaicin kaurin jiki, ba doguwa ba ce ba gajere ba,fatar jikin ta wankar tarwaɗa mai sheƙi da taushi tamkar ta jariri sabuwar haihuwa, Tana da dara-daran idanuwa farare ƙal, masu haske tamakar tatacciyar madarar shanu, kwayar cikin su takasance baƙa sidiƙ,tamkar an ɗiga tawada, Hancinta dogo mai lankwasa da kyau, a ƙasan sa an tsaga wani ɗan madaidaicin baki da laɓɓansa suka kasance jajur, haƙoran sa cikin su masu haske da sheƙi, Wuyan ta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa a cike yake kuma a tsaye ƙyam bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, Cikin ta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, Ƙugun ta a tsuƙe yake daga gaba, Daga baya kuma yayi tudu sosai, tamakar idan aka ɗora tuffa zata zauna akan kai saboda tudu su, Tana da sharɓa sharɓan Cinyoyi masu ɗaukar hankali, yatsun kafafun ta da hannaye sun kasance zarara masu ban sha'awa, Gashin kan ta baƙi siɗiƙ mai kyalli da sheƙi tamkar gilashi ya zuba izuwa kan kwankwason ta. Wohoho! Haƙiƙa duk in da kyawu yake idan aka zo kan sarauniya Nuwairat to batu ya ƙare. Gawurtacciyar Basadaukiya ce mace mai kamar maza, daɗin daɗawa kuma takasance azzaluma tagaban kwatance, Tsananin zalunci Nuwairat ya huce tunanin bil'adama Domin kowa bata kyale ba babba da yaro, Wani abu da yake tayar da hankalin jama'a shi ne yadda aka yi sihirin tsafi kowane iri baya tasiri akan ta, Kuma babu wani al'marin da zata sanya a gaba face ta cimma nasara akan sa, Duk wata ƙasa da Nuwairat ta sanya a gaba sai taga bayan ta, Ta cinye mutanen kasar da yaƙi sun zamo ganima gare ta, Bisa wannan dalili yasanya ta zamo gagarabadau kuma kadangaren bakin tulu a tsakanin sarakuna bokaye da matsafa, Duk saurayin da ya bayyana soyayyar sa ga sarauniya Nuwairat baya taɓa samun nasara, Da yawa daga cikin su ma sun rasa rayukansu bisa bakin cikin rasa Nuwairat a matsayin abokiyar rayuwar su. Bisa al'adar sarauniya Nuwairat duk shekara tana yin hawa na musamman da kan ta, Ta kai mamayar bazato da rundunar mayakan ta, Kwatsam a kashe garin ranar da Nuwairat zata yi wannan fita yaki ne, Ta yi wani mafarki da ya firgita ta ya hana ta sukuni, Ba wani abu ta gani har ya hana ta barci ba face surar wani kyakkyawan saurayi, Wanda tun da take a rayuwar ta bata taɓa ganin bil'adama mai kyawu tamkar sa ba, Tun a daren sarauniya Nuwairat ta ƙasa rintsawa bisa yadda zuciyar ta kamu da matukar kaunar saurayin da ta gani a Cikin barcin ta, A lokacin tashi Manzo ta aika aka kirawo mata bokan masarauta mai suna jadwar ibn zairum, Lokacin da boka Jadwar ya bayyana a gaban sarauniya Nuwairat a Turakar ta barci sai ya zaɓe ƙasa ya kwashi gaisuwa a gare ta, Sannan daga bisani ya ɗago da kan sa sama, Saadda yayi arba da halin da sarauniya Nuwairat ke ciki sai ya ɗimauce dakyar ya samu sake sunkiyar da kan sa ƙasa a karo na biyu amma sai jikin ya kama kyarma, Ba a Kowa ne hali boka Jadwar yaga Nuwairat ba har ya ɗimauce face bisa arba da yayi zahirin kyakkyawar surar ta bayyana a fili Domin a wannan lokaci ne tana sanye ne da rigar barci shara-shara wacce bata kai ƙwaurin ta, kuma bata rufe rabin kirjin ba, hasken fitilun dake turakar ya kara bayyana kyakkyawar surar ta ya mace dake cikin rigar barcin shara-shara. Cikin alamun matukar damuwa sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar cikin sanyayyar murya mai ɗauke da damuwa tace"ya abin dogaro na shin ina dalilin wannan kyarma taka da kuma sunkiyar da kanka ƙasa batare da ka dube ni ba?, Koda jin wannan tambaya sai boka Jadwar ya buɗi baki Muryar na rawa yace "Ya shugaba ta na rantse da kyawun surar ki, Bazan iya kallon ki a cikin wannan yanayi ba koda kuwa na daƙiƙa goma ne domin, Domin kallon kyakkyawar surar ki zai iya sanya wa na manta da kai na da ma dukkanin sirrikan tsafi na, Koda jin amsar waɗannan tambayoyi daga bakin boka Jadwar, Sai a sannanne ta lura cewa ashe rigar barci a jikin ta kawai sai tayi wuf ta janyo wani mayafi na alhariri ta rufe jikin ta, Sannan ta sake duban boka Jadwar ta buɗi baki a karo na biyu ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu amma sai boka Jadwar ya ɗaga ma ta hannu yana mai nuna cewa ta dakata, Sannan yayi gyaran murya a karo na biyu cikin kakkausar murya yace"ya shugaba ta ba sai kin wahalar da kanki wajen sanar da ni abin da kika gani a cikin mafarkin ki ba, hakika duk na gani a cikin madubin tsafi na kuma nayi bincike, Ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa haƙiƙa kin faɗa tarko mai wahalar fita, Domin saurayin da kika gani a cikin mafarkin har kika kamu da soyayyar sa ba wani ba ne face Wani hatsabibin jarumi da ake kira da suna Hibairu wato SARKIN SADAUKAI na duniya, Hibairu wani irin mutum ne daya rayu a cikin daji da dabbobi da aljanu bai iya kowane irin yare ba, A halin yanzu ba zai fito daga daga cikin dajin Baitul-shamshan da yake zaune a cikin sa ba face ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a ranar da zai bayyana a wannan duniya ta mu zai yaƙi biladama ne domin ya kare martabar dabbobi, Babu wani mahaluki da zai iya magana da Hibairu har ya fahimci Yaren sa face wani yaro makaho mai suna Humair, Wani abin baƙin ciki da na gani a cikin madubin tsafi na shine akwai wata budurwa guda ɗaya wacce ita ce mace ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara yin arba da ita a cikin dukkan biladama, Don haka ita ce wacce HUBAIRU zai kamu da ƙaunar ta fiye da komai a rayuwar sa, Saboda tasirin cewa ita ce jinsin mace ta farko daya fara gani a rayuwar sa, Sa'adda boka Jadwar yazo nan azancen sa sai sarauniya Nuwairat ta cika da matukar al'ajabi, Amma sai ta dube da cikin alamun matukar damuwa tace "shin wace ce wannan budurwa da zata fara saduwa da SARKIN SADAUKAI, Hakika duk inda take sai na farauto ta na hallaka ta domin ya zamo cewa nice mace ta farko da sarkin sadaukai zai fara arba da ita, Har ya kamu da tsananin kaunata,. Boka Jadwar ya yi ajiyar zuciya a dai dai lokacin da zufa ta keto masa. Ya dubi Nuwairat cikin alamun tsananin damuwa yace"ya shugabata kiyi sani cewa haƙiƙa farautar wannan budurwa abu ne mai matukar wahalar gaske, Domin lokacin da matasa Cikin halarar tsafi domin na gano birnin da budurwar take sai na sha bakar wahala har da na su ma sau arba'in Sannan na gano birnin , ana kiran sa da suna Darul-arzik, Yana ne sa kaɗan da birnin ki. Abinda na fahimta kawai shine tabbas mutanen birnin Darul-arzik sun kasance hatsabiban mutane masu ƙarfin sihirin tsafi tunda dai gashi tsawon shekaru kina kai farmaki izuwa kasashe da bira ne amma ba ki iya gano wannan birni na Darul-arzik ba. Sa'adda boka Jadwar ya zo nan a jawabin sa sai sarauniya Nuwairat ta cika matukar farin ciki maral misaltuwa ta dui Jadwar tace "Babu ruwa na da hatsabibancin su tabbas na gano wannan budurwa na hallaka ta Shin ka manta ne cewa babu wani al'amari dazan sanya a gaba face na samu nasara akan sa Tabbas ina so ne alfijir ɗin gobe ya keto Ina tsaye a bakin kofar Darul-arzik, Daga wannan batu boka Jadwar yayi bankwana da sarauniya Nuwairat ya fice daga turakar. Kamar yadda sarauniya Nuwairat ta faɗa haka al'amarin yaksance wato tun sulesainin dare ta kammala haɗa rundunar mayakan ta, Su ka ɗauki hanyar zuwa birnin Darul-arzik, tun kafin hudowar rana suka isa kofar birnin, Lokacin da isa sai boka Jadwar ya dubi sarauniya Nuwairat cikin ladabi yace"ya shugabata ina ganin zai yi kyau mu jira anan har izuwa lokacin da za'a buɗe kofar birnin, Koda jin wannan batu sai sarauniya Nuwairat ta fusata ainun ta dube sa tace "wannan wata irin maganar banza ce kake yi Tabbas yanzu batare da ɓata lokaci zamu karya kofar birnin mu afka musu da yaƙi, Dajin hakan sai boka Jadwar yace"ya shugabata tuba nakeyi Amma kiyi sani cewa bakomai bakomai ne yasanya na faɗi hakan ba sai domin cewa idan har mu ka afka birnin zai zamo cewa tamkar harin bazato mu ka kawo musu, Tabbas dole ne a samu waɗanda zasu yi gudun tsira daga cikin al'ummar birnin wata ƙila a samu rashin Sa'a a cikin masu gudun tsirar har da budurwar da muke nema, Koda jin wannan ƙarin bayani daga bakin boka Jadwar sai sarauniya Nuwairat tayi ajiyar zuciya sannan ta dube sa tace"tabbas zancen ka dutse ne ya abin dogaro na tabbas na yi maka mummunar fahimta, Kamar yadda boka Jadwar ya bada shawara haka al'amarin ya kasance sai aka jira dakarun birnin Darul-arzik suka fito, Sannan aka shiga fafata yaƙi, kasancewar masu iya magana na cewa karfin yawa yafi Sarkin Karfi dai yazamana cewa dakarun Nuwairat sun samu nasara akan dakarun birnin Darul-arzik, Kamai rashin imanin mutum idan yaga yadda gawarwakin ƙananan yara da tsofaffi mata suka cika Birnin dole ne ya zubar da hawayen tausayi, Batare da bata lokaci ba aka ribace waɗansu yan mata guda biyar dasu kaɗai suka rayu daga cikin Jama'ar birnin, Bayan an kwashe dukiyoyin birnin a matsayin ganimar yaƙi Sai aka ɗauki hanya domin komawa izuwa birnin Garul-mausul, Tare da waɗannan kyawawan yan mata guda biyar da suka tsira daga cikin jama'ar birnin Darul-arzik, Inda a lokacin da aka isa birnin ne aka tafi dasu izuwa wani gida na musamman, A daren ranar da aka kawo su ne su kayi yunkurin tserewa daga hannun dakarun masu tsaron su bayan sun hallaka dakarun ta hanyar yi musu kisan gilla, Bisa wannan dalili ya sanya boka Jadwar da sarauniya Nuwairat suka shiga farautar su a cikin daji har suka turo musu waɗannan miyagun halittu domin su hallaka su, Wannan shi ne dalilin da ya baro da waɗannan yan mata guda biyar daga birnin Garul-mausul kuma suke gudun tsira domin kada waɗannan halittu su hallaka su, Lokacin da zaratan yan matan huɗu suka ci-gaba da falfala azababban gudu domin tsira da rayukan su daga miyagun halittun da suka turo su, Sai suka shafe tsawon daƙiƙa Ɗari biyu suna wannan tsere a dai dai wannan lokaci ne halittun suka karfin gudun su ya fara raguwa saboda tsananin zafin rana da kishi ruwa da suka addabe su, Wannan shi ne abinda ya bawa halittun samun nasarar hallaka yan matan uku Ta hanyar farke cikin su suka cinye kayan cikin, Ya zamana cewa sauran budurwa guda ɗaya wacce har yanzu take falfala gudun babu ƙaƙƙautawa Sa'adda budurwar taga cewa miyagun halittun sun kusa cimma ta kuma an kashe gaba sauran Yan uwan ta matan, Kawai sai taja ta tsaya daga gudun da take yi ta fuskanci halittun batare da ta riƙe wani makami a hannun ta ba, Hawaye na zuba daga idanun ta, koda halittun suka ga cewa tayi yi gaba da gaba Sai kawai suka diro daga sararin samaniya suna masu yi mata ƙawanya suna dalalar da wani irin yawu daga bakunan su, Daga can sai halittun su kayi kukan kura suka afkawa Kyakkyawar budurwar da azababban yaƙi mai matukar muni da ban tsoro suna kai ma ta miyagun hare hare da fuka -fukan,bakunan su da faratan hannayen su masu kaifi tamkar takobi, da nufin yi masa kisan gilla, Budurwar ta wanzu tana kai cewa da zillewa hare- haren miyagun halittun cikin gwanin ta da kwarewar yaƙi, Duk Sa'adda ɗaya daga cikin halittun ya kai ma ta hari idan budurwar ta goce sai kaga duk abin da harin ya taɓa ya tarwatse koda kuwa dutse ne Koda hassadar Mutum idan yaga yadda budurwar take zillewa hare haren miyagun halittun dole ne ya jinjina mata ya tabbatar dacewa ta cika Basadaukiya mace mai kamar maza, Su kansu halittun sai da suka cika da matukar mamaki da al'ajabi, Domin a wannan karon ne suka taɓa fafata yaƙi da wata bil'adama da suka shafe tsawon Sa'a batare da sun samu nasarar hallaka ta ba, Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin halittun ya kai wa budurwar wani wawan hari da fuka -fukan sa,bisa Sa'a sai ya make ta faɗi ƙasa jini na zuba daga hancin ta da baki, Kuma numfashin ta na fita sama sama, koda samun wannan nasara, Sai halittun suka yunkura izuwa kan ta suna wani irin gurnani da dalalar da yawu daga bakunan su domin su yi fata fata da sassan jikin ta, Kwatsam bazato babu tsammani sai kyakkyawar budurwar taga halittun sun kurma ihu sannan su faɗi ƙasa suna shure shuren mutuwa, Al'amarin da yayi matukar bawa budurwar mamaki kenan, tace a cikin ranta shin kowane ya hallaka waɗannan halittu, Amsar tambayar data kasa bawa kanta kenan Kawai sai ta yunkura ta miƙe zaune da ƙyar, Ai kuwa sai tayi arba wani narkeken baƙin aljani dauke da waɗansu jarumai guda uku mace ɗaya namiji ɗaya sai karamin yaro Tsaye daf da inda take zaune, Budurwar ta ƙura musu idanu ko kiftawa bata yi Ba wa su bane Waɗannan mutane ba face su jaruma Husnaila, Koda su sunaila suka lura da halin da budurwar ke ciki sai ta durfafi inda take domin ta bata taimakon gaggawa, Yayin da ta isa sai sunaila ta firo wata jakar fata a gadon bayan ta ɗauko wani ƙyalle ta shiga goge mata jinin dake zuba a bakinta da hancin ta, Bayan ta kammala ne ta ɗauki wani garin magani daga cikin jakar ta haɗa a cikin wani kofi na azurfa bayan ta zuba ruwa ta cakuɗa sai ta kafa budurwar a baki ta shanye, Koda kammala shanye ruwan maganin nan take budurwar taji ƙarfi a jikin ta har ta iya muƙewa tsaye Batare da wani ɓata lokaci ba sunaila da saurayi Hizmal suka yi wa budurwar jagora har bisa kan Aljani Marhutul-Azab suka ɗora bisa gadon bayan sa Bayan kowa ya hau sai Marhutul-Azab ya sake yunkurawa ya tashi izuwa sararin samaniya ya shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya, Bayan tafiyar su saurayi Hizmal tare da wannan budurwa da suka ceci rayuwar ta. Sai sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka bayyana a wajen, Sa'adda Nuwairat da Jadwar suka yi arba da gawarwakin halittun sai suka cika da matukar baƙin ciki maral misaltuwa su shiga kallon alamun takun sawayen inda aljani Marhutul-Azab ya sauka, Cikin hanzari boka Jadwar ya buɗe bakin sa sannan ya runtse idanun sa ya karanto dalasiman tsafi yana Gama rufe bakin sa sai yayi nuna da hannun sa ga wata bishaya dake fuskantar inda suke tsaye sai ga hoton dukkanin abinda yafaru tsakanin budurwar da su saurayi Hizmal ya bayyana a jikin bishiyar tun daga farko har ƙarshe, Cikin alamun tsananin takaici sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar tace "ya dodon bokaye shin yanzu Mene ne mafita Haƙiƙa idanuwa basu taɓa rintsawa ba matsawar budurwa NIHLA tana numfashi a doran ƙasa Kuma bazan taɓa koma izuwa ƙasa ta har sai yaga na hallaka ta na mallaki SARKIN SADAUKAI Hibairu amatsayin abokin rayuwa ta, Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai boka Jadwar yayi shiru Sannan daga bisani ya buɗi baki yace"Ya shugaba ta tabbas nayi matuƙar baƙin ciki da bamu riski waɗannan jarumai ba da su ka samu nasarar ceton rayuwar budurwa Nihla ba, Domin kuwa sune suke ɗauke da yaro Humair makaho wanda shine kaɗai ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI a kaf fadin duniya, Sannan aljanin dake ɗauke da su kuwa shine ke dauke da taswirar fadar Sarkin bokaye, Haƙiƙa bakamar asarar mukayi ba da mun riske su shi kenan burin mu ya cika na duniya baki ɗaya, Yanzu abinda kawai za su muyi shine mu bazama farautar su domin mu cimma su, Sai dai kuma ya shugabata wani hanzari ba gudu ba Yanzu gashi zamu yi wannan tafiya kuma bakiyi sallama da jama'ar ki ba, Koda jin wannan tambaya sai Nuwairat tace "nasan da hakan abinda nake buƙata kawai shine ka tashi Manzo na sihiri ya tafi izuwa Birni na domin ya sanar da jama'a ta labarin tafiya ta, Koda jin wannan umarni sai boka Jadwar ya sake buɗurwar baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi sai ga wani saurayi ya bayyana a wajen, Bayan Jadwar ya sanar da saurayin duk abinda ke wakana sai Saurayin na sihiri ya ɓace ɓat, Sannan boka Jadwar ya karanta wadansu dalasiman a karo na uku take wata dardumar sihiri ta bayyana a wajen, Ba tare da wani jinkiri ba sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka hau bisa kan Dardumar Take Dardumar sihirin ta tashi sama a cikin iska ta shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya, Hakika boka Jadwar yayi shura a fagen ilimin tsafi Wannan shi ne abinda ya faru da budurwa Nihla da sarauniya Nuwairat ke son ta hallaka bayan ta kashe baki daya mutanen birnin su, Da kuma abinda ya wakana tsakanin ta dasu saurayi Hizmal akan hanyar su ta sada yaro Humair makaho da SARKIN SADAUKAI Hibairu, Mu haɗu a GOGA SHA FAMA littafi na 1 Domin jin cigaban wannan kayataccen labari, Daga mai ɗebe miki kewa a kullum da ko yaushe Mansur Usman Sufi Sarkin marubutan yaƙi