Ouummey 01 (7/27/2022 3:36 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey✍️ Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* PAGE 1️⃣ BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM!!. Dukka yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki, Ubangijin sammai da ƙassai, Ubangijin talikai, Ubangijin Al~arshi me girma. Dubun salati su tabbata ga shugaba kuma fiyayyen halitta, Annabinmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan littafin mallakar Ouummey (khairert) ne, ba yarda wata ko wani su juya min littafi ba ta kowace siga bata reda yardata ba, duk wanda yai gangancin yin hakan kuwa zai haɗu da fushin hukuma. Wannan labari ƙirkirarren labari ne dana ƙirƙireshi bisa fasaha da baiwar da Allah yai min, kamanceceniyar suna ko halayya akasi ne kuma arashi ne, fatan za'ayi haƙuri da hakan. Gareku masoyana masu bibiyar rubutuna da nuna min ƙauna da soyayya, to gani na kuma dawowa gareku cikin salon rubutuna da ya bambanta dana kowa. Salon yasha bambam da wadanda suka gabata, tafiyar me ƙarƙo ce, tsarin me matuƙar tsayawa a rai ne haka kuma soyayyar me garɗi ce, ina fatan zaku biyo ni sannu a hankali don tabbatar da duk abinda na faɗa. __________ Dogon ginin me matuƙar girma da faɗi da za'a iya kiransa da gari guda, gidan da ko ba’ace ba Kai tsaye zaka kirasa da gidan sarauta sabida yanda aka tsara ginin ga kyau ga girma had’ida tsawon gini.... Tsugunne a gaban babban mutumin da ya sha naɗin rawanin da ya rufe fuskar sa ruf da ba'a ganin komai sai hancinsa da idanunsa yake, daga ganinsa ko ba'a faɗa maka ba kasan shine Sarkin dayake mulkar wanna babbar masarauta me daɗaɗɗen tarihi gami da ababen mamaki da al'ajabi haɗu da tarin izza da tsantsar mulki me tafiya da tsofaffin al'adu, SARKI MUHAMMED HASHIM II kenan, wanda ya kasance na bakwai a jerin sarakunan da suka jagoranci kuma suka mulki wannan babbar masarauta. Masarautar DAULATUL NOOR kenan dake garin Giwa a nan kudancin ƙasar Hawarya, masarautar da take cikin manyan masarautu huɗu da suke a faɗin ƙasar Kamar yadda na fara faɗa a baya, masarautar DAULATUL NOOR masarauta ce me cike da shahararren mulki da iko haɗi da ilimin addini da na zamani, sarakuna bakwai ne suka mulki wannan babbar masarauta kawo yanzu da mai martaba sarki Muhammad Hasheem ke jan ragamar ta. Sarki Muhammad Hasheem kamili kuma adalin sarki ne da yai suna wajen zartar da hukuncin adalci batareda duba ga girma, kusanci ko muƙamin wanda ya aikata laifi ba, ya kasance sarki jajirtacce kuma mara tsoro wanda hakan yasa bayi da dukkan talakawansa suke alfahari dashi da jin daɗin zama a ƙarƙashin sa. ___ Idanunsa masu matuƙar kaifi da tasirin da yake amfani dasu wajen yiwa mai laifi hukuncin farko ya zuba akan babban ɗansa dake ɗuke gabansa yana mai tsattsare shi da su. Kaifin idanun mahaifin nasa akan sa baisa yaji wani ɗar ba ko kaɗan dan har yanzu yana akan bakansa na bazai karɓi laifin da aduniya ya tsani mai aikata shi ba, laifin da yake jin da yana da iko se ya hana wanzuwar masu aikata shi a ban ƙasa, sai gashi an wayi gari yau shi ake tuhuma da aikata wannan laifin har ake ƙoƙarin tursasashi wajen ya amsa da bakinsa saidai yana jin ko wuƙa za'a ɗora a maƙoshinsa a raba shi da numfashinsa bazai taɓa yin abinda suke so ba. Janye idanunsa sarki Muhammad Hasheem yayi daga kallon yaron nasa kana ya maida dubansa ga dubban jama'ar da suka cika fadar tashi dan ji da kuma ganin hukuncin da za'a yankewa YARIMA SARAKI da aka kama da ɗaya daga cikin manyan haramtattun laifin da masarauta ta hana tai kuma Allah wadai da aika tasu. Gyaran murya mai martaba yayi kana cikin tsantsar izza da ƙasaita ya fara magana a hankali cikin muryarsa mai cike da dattako wadda banda waziri dake kusanshi hatta ɗan sa dake duƙe gabanshi baze ce yaji me mahaifin nasa ya faɗa ba. Miƙewa tsaye waziri yayi bayan ya gama sauraren jawabin da mai girma sarki yai masa ya dubi al'ummar dake cike a fadar ya fara magana. "Sanin kowa ne da ke cikin wannan gari me Albarka ZINA na ɗaya daga cikin manyan laifukan da masarauta tai Allah wadai tare da hani da aika tawa Wanda aka tanadar da hukunci me matuƙar tsauri da girma ga duk wanda ya kasance victim ɗin wannan aiki, sai dai kwatsam aka sami YARIMA SARAKI da aikata mafi munin laifin da girmansa ya shafe laifin zina wato FYAƊE". Sauke numfashi waziri yayi sannan ya ɗora "Bisa hujjoji masu yawa da ƙarfi da aka gabatarwa wannan fada me Albarka, an sami yarima saraki da aikata laifin fyaɗe ga ƴan matan bayi guda biyu haɗi da yi musu barazana in har suka sake suka sanar da koda iyayensu ne, wanda ɗaya daga cikinsu ta rasu yayin haifar cikin yariman yayinda ɗaya ke raye ɗauke da cikin shi na wata biyu a jikinta, haka kuma a shekaranjiya ne aka kuma kama yarima saraki da laifin aikata fyaɗe wa ƙanwar gimbiya Saudat da ta kawowa yayarta ziyara wato gimbiya Husna ta masarautar kangiwa, yariman yayi amfani da ƙarfin sa yayin ɗaukar gimbiya Husna zuwa turakarsa inda ya wulaƙanta rayuwarta, dan haka adalin sarkin mu ya zartar masa da hukunci bayan sauraren dukkan ɓangarorin dake ƙara tareda gudanar da ƙwaƙwaran bincike inda aka sami yarima dumu dumu da aikata wannan Laifuka dan haka a yanzu maga takarda zai karanto mana hukuncin da shugaban mu ya yanke wa mai laifi". Sauke ajiyar zuciyan dogon surutun da yayi waziri yayi kana ya koma ya zauna haɗi da miƙa wa magatakarda paper ɗin da maimartaba ya bashi. Fadar tayi tsitt ba abinda kake ji illa sautin Muryar magatakarda data karaɗe ilahirin fadar saboda tsananin zaƙin murya da Allah ya bashi. "Bayan gabatar da hujjojin da suka bayyana yarima saraki a matsayin mai laifi, wannan fada mai adalci ta yanke masa hukuncin haramtawa yarima saraki zama a cikinta na har abada, ma'ana yarima saraki zai bar cikin wannan masarauta a yau batareda ya fita da ko tsinke da ya zama mallakin masarauta bane, Wannan hukuncin fada ne, A ɓangaren hukuncin uba da ɗan sa kuwa maimartaba ya zare yarima saraki daga cikin ƴaƴan da ya haifa haka kuma yana umartarsa da ya ajiye dukkan abubuwan da yasan ya samu ne daga gareshi ciki har da kwalayen takardun karatun da yayi zuwa katin ATM na gidan sarauta har kan kayan sawa, haka ya haramta masa kusantar garin nan haɗi da iyalansa in kuwa yayi hakan to ya tabbatar yana cikin fushin Ubangiji". Tuni fadar ta hautsine da hayaniya jin hukuncin da maimartaba ya yiwa yarima saraki, da yawa basu ji daɗin shi domin dai basu yarda ze aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba yayinda wani ɓangare na cikin gidan sarautar suke murna da farin ciki da abinda ya faru a lokacin. Fadawa ne suka tsawatar nan da nan kowa yaja bakinsa ya tsuke dan dukan bafade ba wasa bane. Tun fara jawabin waziri zuwa ga karanto hukuncin da magatakarda yayi kansa na duƙe batareda ya ɗago ba har saida aka gama hayaniyar. Miƙewa yayi a nutse kamar yadda ya kasance ɗabi'arsa yasa hannu ya fara zare alkyabbar da ke jikinsa bata reda ya dubi kowa ba ciki kuwa harda mahaifinsa har lokacin kuwa kansa na kallon ƙasa. Ajiye alkyabbar yayi gaban waziri kana ya duƙa ya cire takalmin da yake ƙafarsa wanda ya kasance mai matuƙar taushi na sarauta shima ya ajiye, hannu yakai bisa kansa ya warware naɗin rawanin dake kansa duk ya zube, hatta da zobunan hannunsa da wata ƴar sarƙa mai ɗauke da tambarin masarautar saida ya cire ya zube, duk wani abu da yasan ya danganci sarauta dake jikinsa haka ya ajiye su a wajen kana ya duƙa yayi godiya ya juya ya fita daga fadar zuwa ainahin part ɗin sa dake gidan sarautar yayinda duk inda ya wuce bayi da barori ke nuna shi suna ƙusƙus ɗin abinda ya faru. Ko da yashiga part ɗin nasa dukkan katinsa na banki ya ɗebo ya ware na masarauta da nashi na kanshi, bawansa ya bawa ya kaiwa waziri duk katin banda guda ɗaya da yasan wahalar sa da guminsa suka samar da kuɗaɗen dake ciki. _______ Kanta sade a ƙasa take zubar da hawaye Masu matuƙar ƙuna da raɗaɗi yayinda zuciyarta ke mata azababben zafi, ta rasa me tayi wa maƙiyanta da suka sako mata ɗan ta a gaba , ɗan da ta fiso da ƙauna a cikin ƴaƴan ta, ɗan da bata son taga ko ɗigon damuwa akan fuskarsa sai gashi yau maƙiya sunyi nasara akanta dashi har sun kai ga rabasu tana ji tana kallo ba yadda zata yi. Sanarwar isowar yarima yasa ta maza ta saka hannunta ta goge fuskarta ta daidaita kanta kafin ta bada izinin shigowar tasa. Gaban Mahaifiyarsa gimbiya halimatus~sadiya ya durƙusa ya miƙa gaisuwa sannan ya ɗaga hannunta na dama ya ɗora akanshi yana jiran ta saka masa albarka kamar yadda ta saba. Danne kukan da ke taso mata tayi tareda furta masa albarka kamar yadda ya zame musu jiki kana ta zaunar dashi a gefenta. Kauda kansa yake yi yaƙi bari su haɗa ido dan yana jin idanunta akansa tana ƙare masa kallo. "Saraki nah, yau mamin ce ba'a son kalla? Juyowa yayi ya fuskanceta ya kuma sunkuyar da kansa ba tareda yace komai ba. "Naji dukkan abinda ya faru a fada, kar kaji komai a ranka mahaifiyar ka ta yarda da kai ta yarda da tarbiyyar da ta bawa ɗan ta dan haka ko kaɗan zantukansu basu sa zuciyata tayi rauni akan yarda dakai ba kaji ɗana". Wannan karon sosai ya zubawa Mamin tasa idanu kafin kuma ya faɗa jikinta ya rungumeta har lokacin bece ko uffan ba kuma hakan bai dame ta ba kasancewar tasan in yana cikin fushi da ɓacin rai baya magana gudun furta kalaman da basu dace ba. Shiru sukayi yana kwance akan ƙafarta ita kuma tana shafa kansa har zuwa wani lokaci kafin ya buɗi baki "Mami ki samin Albarka zan tafi, zan yi biyayya ga umarni da hukuncin me martaba duk da ban kasance mai laifi ba". "Albarka ta na tare da kai a ko yaushe a kowane hali, ina mai maka nasiha da ka kasance mai gaskiya a duk inda ka kasance, ka gujewa haram duk daɗinta duk babunka, ka nemi halal ɗin ka ko da a wuta ake nema, ka gujewa zaluntar wani dan daka zalunta gwara a zalunceka, ina mai maka nasiha da kaji tsoron Allah ka kiyaye al'aurar ka daga datti da dauɗar zina, kar ka fara ko da hangar gonar da bata kasance mallakinka ba, ka kasance mai tausayin na ƙasa da kai kuma mai taimako da duk ƙanƙantar abinda kake dashi, ka guji zargi domin Annabinmu ya hane mu dashi a ƙarshe ina kuma tunasar da kai ka zama me gaskiya da riƙon Amana, ka kuma kasance mai yafiya, kuma ina so ka lura a duk inda zaka zauna dole zaka samu masoya da maƙiya, to kaso masoyanka ka kuma yi taka tsantsan da maƙiyanka domin ko anan su suka fitar da kai daga gadon ka kuma abin tunƙahon ka, ka girmama kanka kar ka yadda a wulaƙanta domin kai ɗin mai daraja ne, kasa a ranka ina matuƙar so da ƙaunar ka sosai saraki nah". Goge mata hawayen da ke fuskarta yayi kana ya sake rungumarta kafin a hankali ya zare jikinsa ya sumbaci goshinta sannan ya miƙe ya fice. Fashewa tayi da kuka dan tasan shikenan sallamar tasu sai kuma watarana in Allah ya ƙaddara saduwarsu in gaskiya tayi halinta......✍️ ©️ Khairert ☑️ote Comments Share fisabilillah Ouummey 02 (7/28/2022 3:05 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* Page 2️⃣ _________________📖 Tafiya yake a nutse cikin kwanciyar hankali kai baka ce yana cikin damuwa ba alhalin a lokacin inda za'a bincika zuciyar sa to fa sai an tadda ta tafi gawayi baƙi saboda baƙin cikin sharrin da akai masa. Duk yadda ya tsani kallo yau dole ya haƙura ya kau da kai domin kuwa ya san sai an kalle shin dan yau yasan sharrin da akayi masa ke trending a garin nasu. Tuno da facemarks ɗin da ke cikin aljihun wandan sa yasa ya saki ajiyar zuciya kafin ya laluba ya ciro shi kana ya maƙala a fuskar sa. Ta ƙofar baya ya fice daga gidan sarautar dan yasan ƴan jarida nacan cike a main ƙofar shikuma a halin da ake ciki bazai so yin magana dasu ba, bawai dan ba shida abun faɗar ba, a'a sai dan yin biyayya ga umarnin mahaifin sa. Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa Save more Bank dake kusa da unguwar sarki wato unguwar su, ATM ɗin sa ya zaro wanda yake ɗan ajiye kuɗi aciki sa'i da lokaci dan lalura in ta taso, bai san nawa ne ainahin yawan kuɗin ciki ba shi dai kawai yana zubawa ne ashe zai masa amfani a rana irin ta yau. Dubu Ashirin yai withdrawing kana ya tare ɗan acaɓa ya kai shi tasha sai dai in da matsalar take ba wasu garuruwa ya sani ba a ƙasar ta Hawarya dan kaso mafi yawa na rayuwar sa ba anan yayi ta ba. Jin wani karen mota na ta maimaita sunan Garin Manya yasa kawai ya nufi motar dan haka kawai yaji sunan yayi masa kuma ya na san zuwa garin. Kuɗin mota ya biya 10k dan Garin Manya yana arewacin ƙasar Hawarya ne yayin da Garin Giwa ke kudanci dan haka akwai tazara sosai tsakani. Tafiyar kwana da wasu awanni ce ta kai su garin na Manya, garin da akewa kirari da "BABBA DA YARO KOWA DATTIJO NE, MANYA MASU HALIN MANYAN MUTANE DA MUTUNTAKA, HAWARYA IN BA MANYA KANGO CE! Sosai Yarima Saraki ke yawatawa da idanunsa kusufi kusufi ganin yadda Garin yake a cike, kowa se sana'ar sa yake ba ruwan kowa da kowa in ba neman arziƙi ne ya haɗa ba, masu dako, masu abinci , masu ruwa har ma da masu shayi duk acikin tashar. Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin ina zai nufa dan ba inda ya sani a wannan garin, hasalima bai taɓa jin ko sunan ba sai ko yau balle ayi batun zuwa. Driver ɗin motar da ya sauke su ne ya ganshi har lokacin ya na tsaye yayin da duk ragowar fasinjoji sunyi nasu wuri, bai masa magana ba sai da ya gama ƙare masa kallo tare da nazartar sa kana ya matsa kusa dashi. Sallama yai masa suka gaisa bayan ya amsa, nan yake tambayar sa ina zashi yayinda take Saraki ya amsa masa da baisan inda zashi ba bashi da kowa a garin arziƙi ya zo nema. Ƙare masa kallo driver ɗin yayi tun daga sama har ƙasa sai dai shi sam baiga alamar talauci ko wahala a jikin sa ba dan duk wahalar zaman motar da yasha bai hana sheƙi da ƙyallin da fatar sa keyi bayyana ba, sai dai banda haka ba wani kayane mai tsada a jikin sa ba, simple shirt and trousers ne wanda suka ɗan cukurkuɗe saboda zaman mota. Gyaɗa kansa yayi bayan ya tabbatar wa da kansa insha Allah mutumin kirki ne dan sosai nutsuwa da hankali ke bayyana kansu a tattare dashi, wayar sa ya fito da ita daga aljihu tare da dialing number ƙanin sa ya Kira shi kan yazo yana neman sa. Kallon Saraki yayi yana masa bayanin ga ƙanin sa nan zai zo ya rakashi inda zai sami wajen zama na haya in Yana so tare da ɗan aikin da baze gagara ba dan dillali ne shi amma na kasuwa. Cikin yabawa da karamcin mutumin Yarima Saraki yai masa godiya. Cikin mintuna ƙalilan ƙanin driver ɗin ya ƙaraso, yaro ne matashi dan bai wuce sa'an Sarakin ba, gaisawa sukai kana ya'yansa yai masa bayani, cikin fara'a ya jagoranci Saraki zuwa jerin wasu shaguna dake bakin kasuwar durumi wadda itace babbar kasuwar garin, ya kawo shi nan ne dan yaji sauƙin fita neman kuɗin sa tun da yace arziƙi yazo nema. Dubu Ashirin da biyar ya biya kuɗin hayar shekara na ɗakin kana idriss ƙanin driver ya rakashi cikin kasuwa dan ya siyo kayayyakin da ze buƙata na rayuwar yau da kullum. Kayan shayi ya siyo masu ɗan auki, se kayan sawa jeans da t shirt set huɗu, jallabiya guda biyu, silifas guda biyu sai takalmin kwalliya mai ɗan kyau suma biyu, bucket madaidaita biyu sabulun wanka da klin kowanne biyar biyar, sabulu wanka ne ya ɗan so ya basu matsala dan shi da mai tsada ya saba amfani sai dai a wannan gaɓar dole ya karɓi sauyin rayuwar da ya zo masa kwatsahan batare da ya shirya ba, dudu osun idriss yai masa recommending dan haka ya siya kusan guda goma sha biyar, dan shi ɗin kamar kifi yake wajen son wanka, se kuma katifa da suka siya irin wadda ake ɗin kawa rigar nan bayan mutum ya siya, suka siyo net da ɗan ƙaramin carpet da zai wa ɗakin daidai, labulaye suka ɗin ko guda biyu na ƙofa da window se kuma akwati mai sauƙin kuɗi da turarurruka masu ɗan sauƙi suma, kayan abinci ya siya kaɗan kaɗan,macroni rabin carton, sphagetti ma haka, se mudun shinkafa uku se ko wake mudu ɗaya, Maggi Leda biyu, gishiri da kuma kayan spices, Mai kuwa nacikin jarka ya siya dan yace bai yarda da ingancin wannan ɗan ɗurin ba. Kafin kace me kuɗin hannun sa sun ƙare wadda a banki ya tsaya ya ciri 100k sedai yanzu yan canjin da suka rage a ciki ƙalilan ne, dole ya ciro wasu idriss ya na nuna masa hanya suka siyo 4 plates da bowls guda biyu se spoon uku dan shi ɗin yana da tsantseni baze iya cin abinci da abubuwan siyar wa ba, mayukan gashi ya siya suma set hakan yasa kuɗin hannun sa suka sake yin ƙasa, padlock kawai ya siya suka koma shagon. A jimillance da Idriss yai lissafi sun kashe kusan 200k da hawa, Idriss akwai kirki, shi ya taya Saraki gyara ɗakin yana masa fira duk da shi Sarakin ba wani amsa masa yake ba se eh, a'a ko yai amfani da body language i.e jijjiga Kai ko gigizawa. In a blinking of an eye har sun gama, sosai kuma ɗakin yayi kyau kamar bashi bane kangon ɗakin da baya ɗauke da komai sai tiles dake ƙasan ɗakin. Daɗin ɗakin ɗaya Saraki yaji ganin cewa akwai toilet a ciki, dashi yayi amfani yai wanka bayan Idriss ya ɗebo masa ruwa cikin bucket a wani gidan wanka dake bayan su. Se kusan ƙarfe 11pm Idriss yai masa sallama ya wuce bayan ɗumbin godiyar da ya sha wajen Saraki, basshi dai da miskilancin sa amma yasan Alkhairi, yana matuƙar daraja dukkan wanda yai masa Alkhairi komi ƙanƙantar sa haka kuma bai da girman kai wajen yin godiya in an kyautata masa. Kwanciya yayi bayan ya canja kayan sa zuwa na bacci cikin kayan da ya siya, suratul mulk yake biyawa ƙasa ƙasa wadda bakin sa ke motsawa cikin alamun nuna karatun yake, cikin wannan yanayin bacci yai gaba dashi dan ba ƙaramin gajiya ke nuƙurƙusar sa ba duk kuwa da wankan da yayi. ******" *MILLIONAIRE'S QUARTERS, MANYA STATE, HAWARYA* Unguwa ce ta riƙaƙƙun masu kuɗin da suka tara ya taru, cikakkun ƴan boko da kuma manya manyan jiga jigan siyasa. Da wani irin ihu budurwar ke magana cikin tsakiyar parlon da ya haɗa ƙofofi uku se ko stairs ɗin da zata kai mutum zuwa wani ginin dake sama. "Na rantse da Ubangiji wannan karon Bazan yarda ba, nakai maƙura da haƙuri da wulaƙaci da rashin mutunci wannan shegiyar yarinyar, Mommy...Mommy ki fito kizo kiji dan kar ma kice ban faɗa miki ba". Ɗaya daga cikin ƙofofin dake falon ce ta buɗe yayin da wata farar mace mai matsakaicin tsayi ta bayyana, ba laifi za'a iya sata cikin jerin mata masu kyau dan ba laifi akwai wadatar idanu se ko hancin ta da bai fiya tsayi sosai ba. Ƙarasa fitowa tayi ta nemi ɗaya daga cikin kujerun dake falon ta zauna kafin cikin yamutsa fuska ta fara magana "Haba Megado, me yasa kin fiya wutar ciki ne? Ko kin san ihunki ne ya tashe Ni daga bacci? Dan Allah ki dinga sassauta wa haba". Wani kallo budurwar da aka kira maigado takewa mahaifiyar tata "Ai dai kin san bazan zauna ina wage baki alhalin ba ayi min komai ba ko? To kiyi ewa waccan mara mutuncin yarinyar magana dan wallahi ta kaini maƙura dan haka zan fara ɗaukar mataki". "Ke wai me yasa kin fiya wauta ne, kin san sarai yarinyar nan ba mutunci ne ya cika ta ba yanzun nan zata saka mahaifin ku yazo ya ci mutuncin mu tunda kin san tsoron ta yake ji, nace mu bi a hankali kema kin san bazan taɓa ƙyale ta ba dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzu faɗa min me tayi miki? "Abinci fa nasa Rayya ta dafa min saboda ina da lectures Kuma ni wanda suka dafa be min ba Shine ƴar iskar nan ta karɓe ta cinye, yanzu gashi in nace Zan jira makara zanyi". "Ki barta dani, ba tana taƙama dukiyar ta bace muke cin arziƙi, na miki alƙawarin sena wulaƙanta rayuwar ta kuma kin tabbatar da zanyi ko? Gyaɗa kai maigado tayi kana ta karɓi dubu biyun da mahaifiyar tata ke bata ta saka a jaka, buɗe baki tayi zatai magana sai dai ƙamshin da ya gauraye falon tareda takun takalmi ne ya katse ta. "Ƙwas ƙwas ƙwas" haka sautin takalmin ke bayarwa wanda ya shaida na mace ne, a hankali suka ɗaga kansu zuwa staircase ɗin dake parlon duk kuwa da sun tabbatar ita ɗin ce ke saukowa. Matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekaru 18-19 ba, fara ce sosai domin skin ɗin ta har wani yellow yellow yake yi saboda tsabar hutu da jin daɗi, sanye take da wata guntuwar red gown da bata gama ƙarasa sauka a gwiwar ta ba, sosai rigar ta kamata ta kuma haskata, ƙafar ta na sanye da red high hill takalmi se gashin kanta da ya sha gyara ya lafe a gadon bayan ta se ko red hat da ta ɗora masa, hannunta ɗaya riƙe da car key da take karkaɗawa se ɗayan riƙe da mini red purse da ta sha adon stones se walwali da ɗaukar ido take yi. Ƙarasawa tsakiyar falon tayi cikin takunta na cat walk, hannu ta saka ta ture hat ɗin baya hakan yasa fuskar ta bayyana kana ta ɗago ta dubi Mommy dake zaune ta sakar mata wani makirin murmushi. Se yanzu na tabbatar da kyanta domin iya fuskar ta abar kallo ce, wasu irin idanuwa gare ta masu matuƙar maiƙo da ɗaukar hankali wato oily eyes, Haka Kuma ƙwayar idanunta ba baƙa bace golden brown ce wadda kalar take sake dulmiyar da duk me kallon ta, idanunta matsakaita ne masu ɗauke da zara zaran thick black eyelashes Wanda suke kwanciya sosai in ta rufe idanun, haka girarta cikakkiya ce dan har tana neman haɗewa sai dai ba ta ƙarasa haɗewar ba, siririn hanci gare ta mai matsakaicin tsayi se ƙaramin bakin ta mai ɗauke da kyawawan luscious pink lips Wanda kallo ɗaya za'a yi musu asan zasuyi matuƙar daɗi da laushi a baki, a taƙaice dai ita ɗin na tsananin kama da jarumar nan sridevi ta ƙasar India. Karkaɗa mukullin hannunta tayi daidai fuskar Mommy kafin ta ce mata "Hi". Takaici da baƙin ciki ne suka cika zuciyar Mommy da ɗiyar ta mai gado sedai ita gogar ko a jikinta, juyawa tayi ta nufi entrance ɗin falon ta fita, sai da ta buɗe ƙofar sannan ta juyo ta kalli Mommy cikin yamutsa fuska tace "oops, kinga na manta, ki faɗa wa mijinki account balance ɗina yayi low, Ina buƙatar transfer ɗin 2 millions urgently in ya fito". Tana gama faɗar haka ta fice daga falon zuwa farfajiyar gidan. Girman farfajiyar gidan kawai ya isa sanar da ainahin girman gidan, domin kuwa kuwa manya manyan flats uku ne a cikin gidan wanda duk flat ɗaya ya yi girman gidan masu rufi asiri uku ko huɗu. Ba tareda ta tsaya amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke ma ta ba ta ɗaɗɗaga musu hannu dan sauri take yi, wata jar mota ta buɗe wadda ke cikin motoci sama da goma dake harabar gidan, motar se ƙyalli da ɗaukar ido take yi, shiga ciki tayi tai mata key kana ta fice daga gidan cikin matuƙar gudu kamar yadda ta saba. Gudu take yi sosai yayin da ta ƙure volume ɗin motar cikin waƙar Dil to pagal hai dan ita ɗin die hard fan ɗin Indian films and music ce, yanzu haka cinema zata je kallon sabon Film ɗin jaruma Rani me suna Black, gashi ta kusa makara duk datasan bata da matsalar ticket nata a ajiye yake. Wayar ta ce ta fara ringing hakan yasa ta rage volume ɗin waƙar tai picking tareda sa wayar a speaker ta ajiye ta. "Hey Kisnah beauty, kina Ina ne, gamu har mun shiga cinema baki ƙaraso ba? "On my way babe" "Okay, se kin ƙaraso". Kashe wayar tayi ta ƙure volume ɗin waƙar ta, tana tuƙi tana bin waƙar tareda girgiza kanta cikin zallar nishaɗi. Gudun da take yi sam ba na hankali bane amma ba yadda mutane suka iya da ita dan har sun fara sabawa, shiyasa da yawa masu ababen hawa ke kaucewa suna bata hanya, wasu na zagi wasu na tsine mata yayin da ita bata masan sunayi ba. Haka salan tuƙin ta yake shiyasa Bata driving da kanta se dai ta ɗau driver, to driver ɗin nata ne babansa ba lafiya dole ya ajiye aikin dan kula dashi, yanzu hakan tana kan neman wani ne shine fa kwana biyu take tuƙa kanta dan bazata iya zama gida ba dole se ta fita. A gurguje tayi parking motar ta dan lokacin har an fara Film ɗin, hakan yasa tayi wrong parking tayi blocking wasu manyan motoci uku. Zama tayi a gurin zamanta na musamman inda ta sami ƙawayenta huɗu duk sun iso, ba tareda ta kula kowacce ba ta zauna tareda fito da park ɗin creamy crackers ɗin ta ta fara jefawa a baki tana maida hankalin ta kan Film ɗin.................📝 Ouummey ✍️ ☑️ote Comment Share. Ouummey 03 ( 7/29/2022 7:56 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣ __________________📖 jefa crackers ɗin take bakin ta yayinda hankalin ta gaba ɗaya ke kan moves ɗin jaruman. Kwaɓe fuska tayi lokacin da aka haska scene ɗin da jarumi Amitabh bachan yake saka jaruma Rani Mukherjee a cikin ruwan sama, kan kace me se ga hawaye na zuba a fuskar ta, meenah da ta san haka ze faru ce ta riƙo ta jikin ta tana lallashin ta, juyowa ragowar sukayi, Hameedah, Surayya, da Maleeka sukayi suna sake comforting ɗin ta har tayi shiru, tagumi ta saka tana cigaba da kallon, ita ɗin me tausayi ce most especially ga masu nakasa da kuma talakawa, most of the times in tazo cinema se tayi kuka saboda tausayi, either na yadda wasu ke fama da talauci, yadda ake ciki zalin wasu ko rabuwar masoya kuma ba hakan ne ze Hana ta dawowa gobe ba. "Yeeeeeeehhhhhh". Ta buga tsalle tana ihu lokacin da jarumar ta kammala degree ɗin ta tana speech ranar convocation , gaba ɗaya ta ruɗa wajen da ihun ta da tsalle wai murna take, majority na occupants ɗin ji suke kamar su shaƙe ta dan takaici yayinda minority basu ko kalle ta ba dan sun saba da ihunta tun bare in tana kallon wrestling, yanzu zaka ji tana ihun "yauwa, dake shi, ɗaga shi ka buga shi, karka bari ya yarda kai, wayyo, tashi, yauwa kauce, ehen kai masa duka........" and many more of this. Ɗaukar ledar crackers ɗin ta tayi ta nufi hanyar fita tana waƙe waƙen ta da suka zauna a bakin ta kai kace ita ce ta raira su, bin bayanta su Hameedah suka yi yayinda meenah ta ƙara sa suka jera suna tafiya har suka fita daga cikin ainahin cinema ɗin zuwa parking lot ɗin da ta ajiye motar ta. Maza huɗu suka tarar tsaye jikin motoci ukun da tayi blocking saboda saurin da take yi, nufar motar ta tayi zata buɗe ɗayan ya sha gaban ta yana jifanta da wani ɗan iskan kallo, ɗagowa tayi itama tana masa kallon mamaki dan bata ma lura da cewa tai blocking ɗin su ba. "Wace iriyar kidahum ce ke da Zaki blocking ɗin mu da wata gwanganin motar ki, ko baki da idanu ne da baki ga motocin mu ba lokacin da zaki yi parking? Sakin baki tayi tana kallon shi jin wai ita yau wani useless being ya Sami bakin zagi, bata gama dawowa daga duniyar mamakin ba ta ga wani ya zo ya tsaya gefen wancan yana hararar ta kafin ya fara magana "Kayi mamaki ne Haroon, kalle ta fa, da ganin su kaga ƴaƴan talakawa masu shegen buri da fafa, anje an aro kaya da mota an shigo cinema dan a sami wani me ɗan maiƙo a liƙe masa, bana tantama ta ga shigar mu shine bari tayi blocking ɗin mu dan tayi driving attention ɗin mu towards her, sedai bata san tayi a banza ba, mara hankali kawai". Wani irin tafarfasa zuciyar ta ta fara a ƙirjin ta, inda sun mata magana cikin mutuntaka ita me basu haƙuri ce dan bata da wannan girman kan, sedai yanzu da suka biyo mata ta wannan hanyar zata gwada musu ainahin wacece Kisnah. Sam be lura da intention ɗin ta ba se ƙarar marin da ya karaɗe gurin se ko raɗaɗin da ya ratsa kwanyar sa, kafin a ankara ta saukewa ɗayan ma nasa a kuncin sa, zaro idanu Hameedah tayi yayinda Meenah tayi hanzarin riƙe ta ganin tana aniyar ƙara marin wanda aka kira da Haroon, fincikewa tayi ta ƙarasa gaban ɗayan tana nuna shi da yatsa tace "inga uban da ya tsaya maka yau a garin nan in Kai ɗan halak ne". Juyawa tayi da nufin wucewa ragowar biyun suka sha gabanta fuska a haɗe duk da cikin ransu fargaba ce cike dan basu san wane ɗiban albarkar zata yi musu ba su kuma. Kamar wanda ya fita daga shock haka yayi firgigit yana kallon ta cikin tsantsar takaici da baƙin ciki "Lallai yau se na yi maganin ki, se n ga uban da ya tsaya miki a garin nan". Ya faɗa yana zaro dalleliyar wayar sa yayi danne danne na ƴan sakanni kana ya sa a kunnen sa. "Ina buƙatar motar ƴan sanda biyu yanzun nan ciki har da mata, ina parking lot ɗin clear screen cinema". Gyara tsayuwa Kisnah tayi tana sakin murmushi yayinda ragowar matasan biyu suke kwarzanta wanda yayi kiran "Gaskiya Abeed ka nuna wa yarinyar nan ko waye kai in ba Haka ba ai ƙimar mu ta zube, ace har mace ta samu guts ɗin ɗaga hannu ta mareka, gaskiya this is so disgusting". Hura hanci kawai Abeed yake Yana aiyana abinda ze sa ayi mata a police station ɗin dan se ya sa an wulaƙan ta ta, jinginewa tayi jikin wata mota dake bayan tata ta maƙala airpeace a kunnen ta tana maming waƙar guzarish tana gyaɗa kai, su Surayya da suka san ba abinda aka isa ai mata su ma hankali kwance suka jijjingina da motocin su suna pressing phones ɗin su. Jiniyar motar ƴan sanda ce ta cika wajen yayinda suka ƙaraso har inda Abeed ya faɗa musu, kashe motar suka yi sannan ragowar suka fiffito. Da hannu Abeed ya nuna inda take tsaya yana haɗe fuska irin ba wasa ɗin nan "Arrest her know". Ya faɗa cikin sigar bada umarni. Da hanzari ƴan sanda biyu mata suka ƙara sa inda take har lokacin idanun ta a lumshe, buɗe idon ta tayi jin an riƙe mata hannu ana ƙoƙarin ɗaura mata abu, cikin zafin rai ta janye hannun tareda wanke ta da zazzafan marin da seda tayi baya kamar zata faɗi, gani take tunda tazo duniya ba'a taɓa yi mata tozarci irin na yau ba. Da sauri ɗayar ta tare ƴar uwar ta tana wurgawa Kisnah wani mugun kallo, bata ko kalle ta ba ta janyo wayar ta daga purse a fusace ta Fara dannawa, cikin tsiwa da rashin kunya ta ke magana tana wawwatsa hannaye "Har ni jami'an ku zasu zo suce zasu kama, waye su, eye nace waye su, waya tsaya musu, to wallahi se sun san sun taɓa ni, kuma ina buƙatar ganin ka yazun nan in ba Haka ba kasan sauran". Kashe wayar tayi tana huci yayinda jami'an suka sha jinin jikin su, kallon kallo suka tsaya yi a tsakanin su da alama communicating suke ta hakan, tsayuwa suka gyara dan babban su yace su tsaya su gani, maybe ma duk kurari ne kawai. "Shigowar motar ASP ne ya sa gaba ɗaya ƴan sandan zaro ido, basu kaɗai ba har su Abeed sun sha jinin jikin su da ita dan su kansu sun zata irin pretending ɗin nan ne se ga ASP a gaban su. Tura hular kanta tayi baya shedar zata yi rashin mutunci, kallon uku saura kwata tayiwa ASP kana ta nuna matan nan biyu "A basu suspension ɗin wata ɗaya, su kuma waɗannan a tafi da su har se na neme su, mind you wallahi aka sake a ka bada belin su without my consent se rai ya ɓaci". Ta ƙarashe tana nuna su Abeed, ba tare da ɓata lokaci ba ASP yasa ragowar ƴan sandan suka riƙo su Abeed aka danna su a mota su ma matan ƴan sandan suka shiga da kansu. Dogon tsaki taja ta buɗe motar ta ta shiga ta tayar, batare da ta kula ko ɗaya daga cikin ƙawayen nata ba tayi wa motar key ta fice a 360, girgiza kai kawai Meenah tayi tana fatan Allah ya kai ta gida lafiya dan a yadda ranta ya ɓacin nan ta san yau gudun da zata sheƙa ba na hankali bane, sallama sukayi kowacce ta shiga motar ta ta ɗau hanyar gidan su, dama tafiyar ta suke jira dan ba wadda ta isa ta tafi ta barta sedai ita ta tafi ta barsu. Zagi ne tashi shi har ba adadi dan da yana fitowa a jiki to fa yau da ba zata sake ganuwa ba, wani shegen parking ɗin ganganci tayi ta fice daga motar ko samun arziƙin rufewa batayi ba, daidai ƙofar da zata shiga parlor taji an bangaje ta, ɗagowar da zata yi sukai ido huɗu da Maigado, bata jira komai ba ta sauke mata nata marin a kuncin ta kafin ta ja tsaki ta wuce tana tsartar da yawu, sakarere Maigado tayi da hannu a kunci kafin ta bi ta ciki a fusace, fizgota tayi tana daidai zata fara hawa matattakala, riƙe hannun Maigado tayi wanda ta ɗaga da sunan marin ta ta murɗe shi har se da ta fara ihu kuma taƙi saki, ihun Maigado ɗin ne ya fito da Mommy dake nata parlon da baƙi, kallon kallo suka yi kafin Mommyn ta ƙaraso ta ƙwace hannun Maigado wanda ta saki ne kawai ba dan Mommyn ta ƙwata ta ƙarfi ba. Nuna Mommy take da yatsa cikin nuna gargɗi tana faɗin "Ki jawa ƴar ki kunne kiyi mata gargaɗi, hawainiyar ta ta kiyayi rama ta wallahi, in ba haka ba wataran se na karya ta a gidan nan, in ta ƙaryata kuma kar ta fasa in har ta haifu cikin uwar ta wato ke". Tana gama faɗa abin da ke ranta ta hayewar ta sama cikin tafiyar gudu gudu sauri sauri, key ta sa ta buɗe ƙofar ta shiga parlon tare da maida ƙofa ta rufe. Haɗaɗden falo ne da yaji kayan ado na zamani masu matuƙar tsada da kyau wanda samun irin su se gidan wane da wane, tun a nan ta fara cire kayan jikin ta tana watsar wa, kafin ta shiga bedroom saura pant da bra kawa a jikin ta, toilet ta wuce ta shige cikin jacuzzi tana kunna tap ɗin ruwan sanyi. Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ruwan ya fara sauka a jikin ta, haka ta kasance cikin cold water for at least 30 minutes kafin taji ga dawo daidai ta buɗe rariya ya fita, fita tayi daga jacuzzin kana tai diluting hot water with cold one daidai yadda take so ta shiga ta fara wankan ta. Towel ta ɗaura ɗan guntu da beko gama sauka ƙasan kwankwason ta ba ta fita daga toilet ɗin, wardrobe ɗin ta ta buɗe dan duba kayan da zata saka, cike damƙan wardrobe ɗin take da kaya kamar za'a buɗe shago, sutturu ne gasu nan kamar zasuyi magana kama da ga kan atamfa, lace, shadda, abayas se ƙananan kaya wanda sune sukai dominating. Tsaki taja dan ta rasa wane ma kayan zata saka, kan gado ta faɗa ta ja bargo rabin jikin ta ta rufe ido, bacci take ji kamar me, sauƙin ta ma yau bata da lectures shiyasa zata yi abin ta ta more. Kamar wadda akayi wa magana ta tashi da sauri zuwa jikin wasu drowers dake jikin bango, ɗaya dag ciki ta jawo slowly, hannu ta ɗora kan photo album ɗin dake ciki kafin ta jawo shi a hankali cike da takatsantsan dan bata buƙatar abinda ze taɓa mata shi balle har ya yage. Zama tayi bakin gadon ta buɗe shi a hankali tana yi tana shafawa, photo ne ya bayyana a shafin Farko na album ɗin, hoton wasu kyawawan couple da kallo ɗaya za'a yi musu a tabbatar da tsananin ƙauna da soyayyar dake tsakanin su, ƙurawa hoton ido tayi tana kallo cikin wani irin maɗaukakin shauƙi da ya kasa ɓoyuwa kan fuskar ta, hannu ta ɗora daidai saitin fuskar macen ta shafa haɗi da lumshe kyawawan idanun ta, tsawon mintuna kafin ta buɗe idanun ta janye hannun ta ta maida fuskar namijin yayinda idanun ta suka cika da hawaye, shafa fuskar take cikin kewa da son kusan ci sedai hakan ba me samuwa bane. Next page ta buɗe wanda ke ɗauke da hoton same couple sedai wannan karon hannun su riƙe yake da jaririya nannaɗe cikin showel me tsananin kyau da ɗaukar hankali dan an masa ado ne irin na yara a jiki, ko daga idanu kasan ze yi tsananin taushi, fuskokin ma'auratan ɗauke da kyakkyawan murmushi da ya ƙara musu kyau duk da duk cikin su ba baya wajen kyan. Hawayen da ya zubo daga idon ta yasa ta maza ta rufe album ɗin tareda janye shi dan bata so ya ɗiga akai balle ya ɓata shi, maida shi tayi wajen ajiyar sa kana ta dawo kan gadon ta kwanta, ɗaga pillown ta tayi ta janyo wani photo guda ɗaya wanda shima dai photon wannan couple ɗin ne ta rungume a ƙirjin ta kana ta kashe wutar ɗakin haɗi da lumshe idanun ta..........................✍️ ©️ Ouummey 📚✍️ ☑️ote,Comment andShare fisabilillah. Ouummey 04 (7/30/2022 6:00 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 4️⃣ __________________📖 ƙarfe huɗu da rabi sannan ta tashi daga baccin, miƙa tayi ta ɗan zauna for some minutes har ta ji tayi daidai sannan ta miƙe ta shiga toilet. Wanka tayi sannan ta ɗauro alwala ta fito, zama tayi kan madubi ta lailaye jikin ta da mayukan shafawan ta masu matuƙar tsada da suke tashin ƙamshi kamar wani turare, busar da gashinta tayi tayi oiling ɗin sa ta parking ɗin shi in a crazy style. Kwalliya ta zauna ta tsara a fuskar ta kamar me shirin zuwa zaɓen sarauniyar kyau na duniya, though nude make up ne amma ba ƙaramin haɗuwa tayi ba, gajeran wando ta saka wanda ya tsaya iya cinyar ta se ƴar shimi me siraran hannuwa biyu a each kafaɗa, band kalar wandon ta saka a kanta tareda sake yiwa jikin ta ɓarin turarurruka masu ƙamshi sosai. Jikin wardrobe ɗin ta koma ta buɗe wani side ta Ciro dogon hijab Wanda take sallah da shi ta zura kana ta koma inda praymat ɗin ta yake ta tada sallah. Shaf shaf tayi sallar ta idar da Azahar, without any azkar ta Kuma miƙewa ta tada sallan la'asar shima nan da nan ta idar, gaba ɗaya raka'a takwas ɗin a mintunan da basu fi huɗu ba tayi ta idar. Cire hijab ɗin tayi ta saka wani flat shoe me matuƙar taushi ta buɗe ɗakin ta fita, ta ƙofar bayan dake jikin stairs ɗin nata ta fice zuwa garden, Zama tayi cikin ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata kyakkyawan gurin da yake da matuƙar kyau da ɗaukar hankali duba da yadda korayen flowers da ciyayi suka lulluɓe shi, gefe ɗaya kuma swimming pool ne me ɗan girma ruwan cikin sa tsaftatacce dan ana iya hango ƙasan pool ɗin. Gefen hagu kuma bishiyu ne da sukai girma na ban sha'awa, bishiyar guava, bishiyar ayaba, bishiyar mango and some other kinds of fruits. Airpeace ta saka a kunnen ta ta lumshe idanunta tayi tana sauraren waƙar ta cike da jin daɗi da nishaɗi, a duk lokacin da take buƙatar kaɗaici nan ne wajen zaman ta, ta ji waƙar ta in ta Kai Mata ta taka rawar ta. Se kusan ƙarfe bakwai ta bar wajen dan har an ɗan jima da idar da sallar magrib, wannan karon ta cikin main parlor ta ratso ta wuce su Mommy zaune suna hira ita da ƴaƴan ta, wani banzan kallo Maigado tabi ta dashi haka ma Mommy banda Awwaf da ya bita da kallon ƙurilla kamar ya cinye ta ɗaya. Bata dubi ko ɗaya daga cikin su ba ta haye stairs ɗin ta tana yi tana moving jikinta towards each sound na waƙar. Sauke ajiyar zuciya Awwaf yayi ya dubi mahaifiyarsa, haɗa ido suka yi tana jefa masa kallon gargaɗi, shafa kansa yayi ya ɗan zame zuwa kishingiɗa, hannun Mommyn ya riƙo yana marairaice murya "Mommy I can't take my eyes off this beautiful creature, pls ki bar ni na aure ta mana". Wani irin fisge hannun ta Mommy tayi tana watsa masa wulaƙantaccen kallo sedai kafin ma ta buɗe baki tuni Maigado ta riga ta "Over my dead body, yanzu kai yaya da bakin ka kake faɗar zaka auri wannan karuwar? Are You in your right sense or yau ɗin ma kaje kasha kayi tatul ne, duk wulaƙanci da rashin mutuncin da take mana baka gani ba kake batun aurar ta? what came over you ne? Ko da yake ba abin mamaki bane zaka iya fiye da haka ma zakayi tunda ba uban mu ɗaya ba ai dole se ka nuna mana wannan bambancin". Zaburowa yayi ze dake ta Mommy ta riƙe shi tana hararar shi kamar idanun ta zasu faɗo "You stupid boy, har ni zaka kalli fuskata kace zaka auri maƙiyar da bani da sama da ita? Eye, ko da yake gaba ɗaya zantukan Maigado akan daidai suke , zaka iya fiye da haka tunda ka zama son of that worthless bitch, lemme tell you something, wallahi ko da wasa na kuma Jin that bitter sentence from your mouth se na saɓa maka ta yadda baka taɓa tunanin zan iya ba, stupid being kawai". Komawa yayi ya zauna yana me dafe kansa kafin kuma ya buɗe su yana kallon ta "Naji na bar maganar auren ta, but sincerely speaking I can't take my eyes off her, dan haka I'll follow ko ma wace irin hanya ce in same ta dan I have passion in her". Washe baki Mommy da Maigado sukayi, Mommy ta dafa shoulder ɗin sa "That's my son, se yanzu naji daɗi, nima ban ce ka ƙyale ta ba, ka bi kowace hanya ka biya buƙatar ka akan ta zan tsaya maka, in fact ma Sena fi kowa farin ciki da murna saboda rayuwar ta ta lalace". Murmushi ya sake jin yadda Mommy ke goyon bayansa tareda ƙara masa ƙarin gwiwa, sosai yaji yana zumuɗin samun damar aiwatar da ƙudurin sa dan yasan ko ta wace hanya Mommy bazata taɓa bari a gano shine ba, haka suka cigaba da tsare tsaren su na abubuwan da zasu yi wa Kisnah su huce takaici da baƙin cikin da take ƙunsa musu. Baiwar Allah ita tana can ɗakin ta kwance a gado bayan ta idar da sallar magrib, chatting suke yi da su Hameedah suna bata haƙuri kan abinda ya faru ɗazu ta bada umarnin a sake su Abeed ita kuwa ta kafe tace bata san zance ba, dole a wulaƙanta mata su dan bazata yarda su tafi Scot free ba. Kashe datan tayi ganin tara yayi, a ƙa'ida tara take bacci in har bata da party ko club ɗin zuwa, wanda tuni ta ware ranakun juma'a, asabar da Lahadi as clubbing days ɗin ta. Miƙewa tayi cikin shigar kayan baccin da tai wadda ƴar guntuwar riga ce da ta tsaya can saman cinyoyinta, ƙaramin hannu gare rigar masu kama da na brazier, flat bedroom slippers ɗin ta masu taushi ta zura ta fita daga falon gaba ɗaya zuwa ɗakin kawun ta mijin Mommy a Haka batareda ta nemi abin suturce jikin ta ba. Gaba gaɗi ta murɗa ƙofar ɗakin fa shiga parlon nasa without any permission or sallama, Mommy kaɗai ta tarar zaune kan one of the cushions na ɗakij tana danne danne a waya, zagaye falon tayi da idanun ta amma bata ganshi ba which means Yana bedroom, hanyar bedroom ɗin ta nufa ta buɗe ta shige bata kula kiran da Mommyn take mata ba kan ta jira ya fito. Sanye da jallabiya yana tsane ruwan kansa ta same shi, zama tayi gefen gadon sa shikuma yana gaban mirror sedai tun shigowar ta ya ajiye towel ɗin ya dawo gefen ta shima ya zauna. Wani irin kallo yake ƙare mata ta gefen ido yayinda ita sam bata san yanayi ba dan abinda ya kawo ta ta shiga faɗa batareda ta gaishe shi ba dan tuni ta yaye gaisar da mutanen gidan. "Nace matar can ta faɗa maka ina buƙatar 2 million urgently Amma sedai har yanzu ban ji alert ba, me hakan yake nufi? Washe baki Kawu yayi duk kuwa da cewa zancen ta ba ƙaramin ɗaci yayi masa ba a zuciya "Kuɗin Company ne yayi ƙasa ƴar Kawu shiyasa kika ga ban turo ba akan ta faɗa min, dama ina jiran gobe tayi ne se in turo Miki ko 1 million ne tunda ba 2 million a ƙasa". Wani banzan kallo take bin Kawu dashi tun lokacin da ya fara magana har ya gama kafin cikin tsiwa da rainin hankali ta fara nata faɗan "Bangane kuɗin Company yayi ƙasa ba, wai Kawu me kake da kuɗin nan ne da duk sanda zan yi maganar kuɗi seka kawo min wani banzan uzuri, wait, wane Company ɗin ne kuɗin sa yayi ƙasa, specify Ina jinka tunda dai kasan ai companies ɗin da yawa". Haɗiye wani yawu Kawu yayi yana ɗan inda inda "Ehm dama, dama , ehm dama Company ɗin flour ne amma ba ma wani ƙasa yayi sosai ba kawai dai na faɗa ne dan naga karɓar kuɗin da kike yayi yawa". Wata muguwar harara ta watsa masa kana ta miƙe tana riƙe ƙugu "Excuse me dattijo, the last I checked dai kuɗin bana wani ƙaton banza bane nawa ne ko? Ko kuwa kun haɗa ƙarfi da Abbu lokacin neman su da tara su ne ban sani ba?, bana son wani banzan excuse, dukiya dai ta wace , wakilci na baka to meye zaka ringa wani son nuna min gadara da iko, okay nagane duk laifi nane amma xan gyara, a tattara min bayanan shiga da ficen kuɗin kowane Company da nake dasu, ɗaiɗai har biyar , dole in canja wakilai dan nagaji da wannan baƙin halin naka, and mind you, kafin in ahiga ɗaki kayi min transferring ɗin 2 million ɗin da nace". Ficewa tayi tana banging Masa ƙofar, dafe kai Kawu yayi cikin tsantsar takaici da ɓacin rai ganin yadda ƴar cikinsa take kallon idanun sa tana faɗa masa maganganu, har shi take kira da ƙaton banza batareda tayi la'akari da alaƙa da matsayin da yake dashi a wajen mahaifin ta ba, ƙwafa yayi yana miƙewa tsaye dan ƙarasa shirin bacci daidai shigowar Mommy, wata banzan kallo Kawu yayi wa Mommy Yana nuna mata ƙofa da hannun sa alamar ta fice masa daga ɗaki, turus Mommy tayi kafin ta buɗe baki zatai magana sedai rikitacciyar tsawar da Kawu ya daka mata yasa ta juya ta fice da sauri a ranta tana tsinewa Kisnah dan duk ta ji abinda take faɗa kafin ta fice. Dogon tsaki Kawu yaja yana hararar ƙofar kamar Mommyn na gurin har lokacin. Ita kuwa Kisnah tana shiga ɗakin ta wayar ta ta fara jawowa ta kunna, pop up ɗin message dake yawo kan screen ɗin ta ta danna, kyakkyawan murmushi ta saki akan fuskar ta da ya kuma ƙara mata kyau ganin 2 million ɗin da tace har ya shigo, ƙwafa tayi tana jijjiga kai dan fa dole ta canja Kawu a kan dukiyar ta tunda har yan da guts ɗin cewa karɓar kuɗin ta yayi yawa kamar wani gadon sa. Ajiye wayar tayi ta koma tayi locking ɗakin sannan ta dawo ta kwanta, a maimakon addu'ar bacci se airpeace ɗin ta tajawo ta maƙala a kunnen ta bayan ta saita wani indian remix me awa huɗu, hoton ta ta jawo daga ƙarƙashin pillow ta rungume a ƙirjin ta ta rufe idanun ta, within seconds bacci yayi gaba da ita. ************* Tsaye yayi gaban madaidaicin mirror ɗin da ya siyo dan gyaran fuskar sa, dubu da ɗari biyar ya siye shi dan yana da ɗan girma, towel ne ɗaure a ƙugunsa yayinda yake taje sumar kansa cikin nutsuwa bakin sa na motsi alamar yana karanta wani abu ne. Oiling gashin yayi bayan ya tsaneshi tas da towel, tunanin yadda ze siyi hand dryer yake yi sedai kuɗin hannun sa gaba ɗaya dubu ɗaya da ɗari biyu suka rage, ajiye comb ɗin hannun sa yayi bayan ya taje shi to his satisfaction ya fara shafa mai a jikin sa, ɗaya daga cikin set ɗin ƙananan kayan da ya siyo ya ciro ya saka bayan ya saka undies, sosai kayan suka karɓe shi kamar dan shi aka yi su, perfumes ɗin sa ya ɗauka ya feffesa a jikin sa kana ya ajiye, gyara ɗakin yayi dan tun kafin yai wanka ya wanke toilet ɗin, seda ya gyara komai sannan ya share, plate, spoon and bowl ɗin da yaci abinci jiya da dare. Tsane hannun sa yayi bayan ya gama ya ajiye su mazaunin da yai musu a ɗakin ya fita tareda rufe ɗakin. Wajen me communication ɗin gaba da su kaɗan yaje ya karɓi waya ya kira Idriss kan gashi fa ya gama shiryawa har ya fito, amsa masa Idriss yayi da gashi nan ƙarasowa, kashe wayar yayi ya bawa me communication ɗin tareda kuɗin kiran da yayi Naira hamsin. Nan wajen ya tsaya jiran Idriss ɗin har ya ƙara so, musabaha sukayi tareda tambayar lafiyar juna kana ya hau machine ɗin Idriss ɗin suka shiga cikin kasuwa inda za'a nema masa aikin da ze dinga yi maimakon zaman banza tunda yace arziƙi yazo nema.................✍️ ©️ Ouummey 📚✍️ ☑️ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 05 (7/31/2022 4:13 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 5️⃣ __________________📖 Sosai suka zagaya cikin kasuwar suka shisshiga shaguna da yawa inda Idris yake zantawa dasu har Azahar tayi, tsayawa Idris yayi wajen wata me abinci ya siya yayinda Saraki yace a ƙoshe yake. Sallah suka yi bayan Idris ya gama, juyowa yayi ya dubi Saraki bayan sun idar da Sallah "Me kake gani game da ayyukan da muka tuntuɓa? Munje shaguna da dama dakai, shagon kayan masarufi, kayan sawa, kanti nan sai da takalma da kuma aikin shara a Company, wanne kake ganin ka fi so yanzu muje in kaika dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, kar mu zauna a cike gurbin da wasu". Shiru Saraki yayi yana tunani yayinda zuciyar sa ta fi kwantawa da kasuwar takalma, buɗe bakin sa yayi cikin yanayin maganar sa a hankali kamar baya so "I prefer shagon takalman". Though Idris be fahimci abinda yace da turanci ba saboda be yi karatu ba amma ya jin takalmi a ƙarshe ya gane ya zaɓi shagon takalmin. "To tashi muje in kaika su san da kai". Miƙewa suka yi suka fita daga masallacin tareda hawa machine ɗin suka shiga cikin sabon gari ƴan takalma, wani ƙaton shago suka tsaya, shiga suka yi yayinda Idris ya ƙarasa wajen ainahin me shagon suka tattauna na tsawon lokaci kafin suka yi musabaha ya dawo wajen Saraki, jan shi yayi suka fito waje "Da a nan shagon nake, me shagon tsohon megida na ne, nasan shi mutumin kirki ne kuma adali, a iya sanin da nayi masa bashi da wata matsala, zaka ji daɗin zama dashi gwargwado, duk da ban daɗe tare da kai ba zan bada shaidar kai mutumin kirki ne, ina fatan tafiya tayi nisa tsakanin ku da me gida insha Allah zakuji daɗin juna, zaka fara aiki dasu yau, Allah ya bada Sa'a". Motsa bakin sa yayi alamar Ameen, hannu yasa ya bubbuga kafaɗar Idris tare da yi masa murmushi alamar godiya kafin ya juya ya koma cikin shagon, juya wa Idris yayi ya hau machine ɗin sa yana girgiza kai, daga shekaranjiya zuwa yau ya gama fahimtar magana tana bawa Saraki wahala, sedai ya fahimci shi ɗin mutum ne me kirki da sanin ya kamata in an fahimce shi, tashin machine ɗin yayi ya wuce. Zama Saraki yayi kan wani bench dake baki bakin shagon har zuwa la'asar da Alh Musa me shagon ya fito ya ganshi zaune, mamaki ne ya kamashi dan a tunanin sa ya shiga cikin ragowar yaran shagon suna hidimar su. Sunkuyar da kai yayi ya gaishe da Alhajin ya amsa masa tareda cewa ya tashi su wuce masallaci. Alwala yayi suka tafi masallacin, tambayoyi yake masa suna tafiya inda yake bashi amsa iya abinda ya tambaya har suka ƙarasa, sallah suka gabatar suka dawo shago, tara yaran shagon Alh Musa yayi ya gabatar musu da Saraki matsayin ɗaya daga cikin su tareda neman haɗin kansu. Amsawa sukai yayinda suka dinga bawa Saraki hannu suna gaisawa ɗaya bayan ɗaya tareda sanar dashi sunan su, murmushi kawai yake musu har lokacin tashi yayi, Naira ɗari uku Alh Musa ya bashi as sallamar shi, karɓa yayi yana godiya cikin yanayin maganar sa can ƙasa. Napep ya tare ya koma shagon sa, wanka yayi canja kaya ya ɗaura alwala sannan ya kulle shagon ya taka da ƙafa zuwa masallacin da ke gaba da su kaɗan. Azkhar ya zauna ya cigaba da yi har lokacin sallah ya cika aka kira sallah ya bi jam'i, ko da aka idar be tafi ba nan ya zauna ya cigaba da karatun Alqur'ani har aka kira isha itama yayi cikin jam'i kafin ya fito. Cikin tafiyar sa ta nutsuwa haɗi da ƙasaita ya koma ɗakin sa, indomie ya dafa saboda tafi sauri dan yunwa yake ji, wunin yau be ci komai ba tun tea ɗin da ya karya dashi. Ko da ya gama ci tashi yayi ya fita ya rufe ɗakin ya fita strolling dan ya riga ya Saba duk dare se ya fita yayi exercise haka ma da safe, a hankali yake bin gefe gefen titi yayinda ababen hawa ke ta tsuga gudun sa akan titi, be yi nisa sosai ba ya dawo dan ba sanin garin yayi sosai ba kar yaje ya shiga inda baze fito ba. Addu'ar bacci yayi bayan ya rage kayan jikin sa dan baya bacci da kaya ko wane iri ne, boxers kawai ya bari ya ja blanket ya rufe rabin jikin sa bayan ya ƙure gudun fanka kasancewar sa me matuƙar san sanyi. **************** Sanye da dogon jeans ya bi fatar jikin ta ya kwanta ta sauko, rigar jikin ta buɗaɗɗiya ce da ta sauko har kan cinyar ta sedai ta ɗaure ta daga ƙasan ƙirjin ta da zaren da aka tanada, ƙafarta sanye da hill shoe kamar kullum hannunta ɗauke da wayoyinta biyu se makullin motar ta. Abinci Maigado ke ci a dining tareda Awwaf, tana tawowa Maigado ta ja wani dogon tsaki tana hararar bayan ta wanda tana jinta amma tai mata banza, har takai ƙofar fita falon ta dawo zuwa kan dining taja kujerar gefen me gado ta zauna. Ruwan Lipton dake cikin flask ta tsiyaya a cup ɗin gaban ta, ɗauka tayi kamar zata sha ta kai kusa da bakin ta kawai ta sake shi daidai ƙafar Maigadon, wani irin ihu Maigado ta tsala na tsananin azaba yayinda itama Kisnah ta taya ta, ihu take tun ƙarfin ta tana tsalle kai kace ita ruwan ya zubar wa. Da gudu Mommy ta baro kujerar ta ta jawo Maigado jikin ta, har lokacin Kisnah bata bar ihu da tsalle ba daidai lokacin Kawu ya fito, ƙara ɓare baki tayi tana kallon Kawu tana yarfe hannu "Wayyoooo Abbu na Nana ta, wayyo ƙafa ta zata cire, wayyoooo Allah Sena Rama". Haka take ta ihu tana faɗa kamar gaske. Da sauri Kawu ya ƙaraso ya tsugunna gaban ta, "Menene ya sameki daughter, faɗa min me ya faru? "Ba Maigado bace, daga kawai na zo zan fita shine tace min wai karuwa nikuma nace mata ai a wajen uwar ta na koya shine fa kawai ta ɗauko hot tea ta watsa min a ƙafa, da suka ga zaka fito se kawai ta zubawa ƙafar ta kaɗan wai dan kar ka yarda dani" Wani irin zabura Kawu yayi ya juyo wajen su Maigado da suka saki baki suna kallon Kisnah dake matsar ido tana girba ƙarya. Wani irin zazzafan mari kawu ya sauke wa Maigado, ai tuni ta manta da ciwon ƙafarta ta shige bayan Mommy tana ihu, binta kawu yake zai dake ta tana ƙara laɓewa bayan Mommy, garin Haka Mommy ta samu rabon mari, anje Marin Maigado ta tare aikuwa ya sauka a fuskar ta. Wata irin dariya ce ke cin Kisnah amma ta daure ta haɗiye, seda ta tabbatar ƙafar Maigado tayi tsami saboda takata da take yi haka ma shikansa kawun ya gaji sannan ta kwaɓe fuska tace "Kawu ka ƙyale ta kaje wajen aikin ka na haƙura amma gaskiya in ta ƙara sedai ta bar min gidana ita da uwar ta dan ita take zugata, rannan naji tana cewa wai a zuba min maganin ɓera a abinci". Zaro ido Kawu yayi cikin tashin hankali zuciyar sa na bugawa, amma wallahi Haleema ba ƙaramar mara mutuncin mata ba ce, yanzu so take a kashe yarinyar tun kafin burin sa ya cika aikuwa zata ga iskanci "Ai dama nasan duk abinda ke faruwa ita take shirya shi, saboda tsabar baki da mutunci kike cewa a kashe ƴar ɗan uwa na da bani da kamar sa ko, to kije gidanku se na neme ki". Zaro ido Mommy tayi "Yanzu alaji ni zaka cewa in tafi gidan mu, saboda kawai wannan shegiyar yarinyar ta ƙulla min sharri se ka yarda, ai shikenan da ƙafar ka zaka zo nema na". "Kaji ko Kawu dama rannan take faɗawa ƙawar ta wai ai ko ka koreta bata yin sati biyu kake biyo ta saboda baza ka iya rayuwa ba se da ita". Cewar Kisnah tana kyaɓe baki irin wai mamakin nan Aikuwa Kawu ya shaƙa, watau har ƙawayen ta take barbaɗawa baze iya rayuwa ba ita ba, to kuwa ze bata mamaki "Kar ki bari in dawo in same ki, in ba Haka ba wallahi se na baki mamaki kuma zaki ga abinda ze biyo baya ne". Yana faɗar haka ya fice fuuuu cikin fushi, yana fita Kisnah ta tashi daga zaunen da take tareda karkaɓe kayan ta, p-cap ɗin kanta ta gyarawa zama, hannu ta saka a aljihun ta ta ciro cingum ta ɓare ta jefa a bakin ta. Cikin taku ɗai ɗai ta ƙarasa gaban Mommy da ta daskare tsabar takaici da baƙin cikin korar ta da Kawu yayi, ƙas ƙas haka Kisnah ta tauna cingum ɗin bakin ta tareda yin ƙwai ta hurawa Mommy. "To ya Kika gani Halima? Ai dama se da na faɗa miki in har baki takawa ƴarki birki ba wataran zata janyo miki abin da yafi ƙarfin ki, to kaɗan kuka gani". Juyawa tayi ta nufi ƙofa cikin takunta na cikakkun ƴan mata masu aji da ji da kan su ta fice. Yau ma kamar kullum cikin salon tuƙin ta ta figi motar a tsiya ce ta hau kan titi, wani irin gudu take kamar bakowa a titin se ita kaɗai, jikake fit fit ta wuce. Zagi da tsinuwa kam ta ɗibe su kamar yadda ta saba saidai bata ma san suna yi ba dan earpiece ne a kunnen ta. Wani irin horn take zubawa a kan titin tun kafin ta ƙaraso gate ɗin makarantar, da hanzari security biyu dake zaune suka tashi suka buɗe gate ɗin dan tuni sun gane ta, in har suka ji wannan horn ɗin to ita take tuƙa kanta kuma bata jira dan ta taɓa yin gaba da gate ɗin akai pressing charges a kanta ta biya dan ba za'a iya korar ta ba saboda kuɗin da take dashi. Da gigitaccen gudun ta ta shige makarantar, ɗaliban da ke kan hanya kowa matsawa yake yana bata hanya dan gudun afkuwar matsala, parking tayi a parking space ɗin malamai dake gefen department ɗin su ta kashe motar sannan ta zare earpiece ɗin. Fitowa tayi daga motar tana gyara zaman Black shade ɗin da ta maƙalawa fuskar ta, Hameedah ce ta ƙaraso wajen ta, rungumar juna sukayi sannan Kisnah ta miƙa mata mukullin motar hannun ta, sororo Hameedah tayi cikin takaicin yadda Kisnah take mai da su kamar wasu ƴan aiki ita da su Surry saboda su ta raina dan bata yiwa Meenah haka. Haka badan ranta ya so ba se dan ba yadda ta iya ta buɗe motar ta kwaso mata litattafan ta kana ta rufe mata ƙofar sannan ta bi ta cikin hall. Tsayawa Kisnah tayi tana bin hall ɗin da kallo ganin yadda ya cika har bata hango wajen zama, rarraba idanu ta cigaba da yi har ta hango wani space na mutum biyu sedai ba kowa a kai, cikin tafiyar ta na cat walk ta ke takawa tana ratsa jama'a har ta ƙarasa seat ɗin ta zauna, da sauri wani namiji da ke kan kujerar ya hayayyaƙo yana faɗa mata the seat is reserved. Ko kallo be ishe ta ba se ma Instagram da ta shiga tana posting hoton da tayi yau da safe tana zaune kan gado sanye da ɗaya daga cikin kayan training ɗinta kafin ta fita jogging. Ran saurayin ne ya ɓaci ganin ta ƙi ma kallon sa bare ta nuna ta san yana magana, kun san samarin jami'a da ɗaukar kai ga zuciya tuni yasa hannu yai watsi da litattafan da Hameedah ta ajiye mata kafin ta koma wajen zamanta. Da wani irin kallo Kisnah ta bi litattafan da suka watse a ƙasa kafin ta kalli Hameedah da bata ƙarasa seat ɗin ta ba, wani ɗan fito tayi nan da nan Hameedah ta juyo dan hakan inkiyar su ne wa junan su, takowa Hameedah tayi ta dawo wajen Kisnah. Miƙewa tsaye Kisnahn tayi daga seat ɗin kamar zata fita sedai kafin saurayin ya ankare yaji saukar mari mafi zafin azaba daya taɓa ji a rayuwar sa dan Kisnah akwai bala'in zafin hannu. Cikin gigicewa saurayin ya fidda hannu da sunan ze rama sedai ko kafin hakan tuni Hameedah ta tare hannun tana watsa masa wani matsiyacin kallo kafin ta tsartar da miyau a gefe alamun dai an raina ka ɗin nan. Sosai hall ɗin ya ɗau shiru kamar ba kowa, da yawa matan ajin so suke yau ayi musu maganin Kisnah dan majority sun tsane ta saboda yadda take da masoya kama daga malamai zuwa ɗalibai. Cikin zafin rai saurayin ya miƙe ya fara zagin Kisnah "Shegiya karuwa asararriya mara tarbiyya, an ji kunya dai wallahi wai nan sunan Musulma ce amma kusufa kusu far karuwanci ta haddace shi, nasan badan komai kika zauna kusa dani ba se dan kinga sabon jini bari ki je ko a sosa miki inda ke miki ƙaiƙayi sedai ki sani ƙwalelenki ƴar karuwai kawai dan da alama gado kikayi wajen gyatumi ko gyatuma". Take hall ɗin ya ɗau sowar ihu dan an daɗe ba'a sami me guts ɗin da ya zagi Kisnah kamar haka ba, tun lokacin suna level 1, korar da aka yiwa ɗalibin bayan ƴan sanda sun hukunta shi yasa ba wanda ya sake attempting sedai a bayan idonta. Murmushi me ƙayatar wa ta saki kafin cikin daddaɗar Muryar ta ta fara magana "Silent everyone, Kamar dai yadda wancan jaririn ya faɗa Yes ni karuwa ce sedai na fi ƙarfin jariran da kaciyar su bata warke ba, wannan gurin se manya kamar gyatumin sa though yayi min ƙazanta da yawa, by the way a Samo projector se in haska muku yadda muke karuwanci da gyatumin sa". Ihu gurin ya sake ɗauka har ma fiye da da kafin ta sake ɗaga hannu akai shiru "We have 37 minutes free, I think that would be enough for you to have fun". Kafin kace me tantiran mate ɗin su sun tafi samo projector, yayinda ragowar ke ihun zasu ga eya ne..........................✍️. 🤣😂😂 Shagali 💃, amma gaskiya Kisnah duniya ce, cikin sauƙi tayi maganin Mommy da Maigado 🤣 su Mommy za'a tafi hutu😜 team Mommy sry for u guys🤣😉. To fa😱yau zamu sha kallo, Bari in gyara zama, kai mhiz jidderh akwai son gulma har dasu leƙe, gaskiya ku tafi department ɗin ku😂, ke meenat Ni fa na tsani sa ido meye na lekowa ta window 🙄, kai bari dai in gyara wayata in Yi wa masu karatu vedio musamman shamsiyya aradu nasan in ban ajiye mata ba seta min dundu biyu 😜😜😝. ©️ Ouummey 📚✍️ *Vote, comment and share fisabilillah* Ouummey 06 (8/1/2022 3:22 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 6️⃣ ___________________📖 Cikin ƙanƙanin lokaci se ga projector an kawo, socket suka kunna tareda jona shi, kujera Surayya da ƙarasowar ta kenan ta sami labari ta miƙowa Kisnah, zama tayi tareda harɗe ƙafafun ta ɗaya kan ɗaya kana ta tura p-cap ɗin ta baya, hakan yasa gaban goshin ta dake cike da baƙin sassalkan gashi kwantacce ya bayyana. Daga zaunen da take a tsakiyar class tayi connecting wayar ta da projector ɗin, watsapp ɗin ta ta shiga da sunan mutane da komai na ciki ke bayyana kan projector, sannu a hankali har ta ƙarasa kan wani suna da tayi saving da *TRASH* ta shiga cikin messages ɗin sa. Can farkon chat ɗin ta koma sannan ta fara scrolling a hankali yadda kowa ze iya karantawa bayan ta ƙara wa text ɗin girma, kan kace me hall ɗin ya kacame da ihun irin kalaman batsan da baban yaron me suna Ishaq yake turowa, tsaff suka gama karance text ɗin kafin ta juya zuwa inda Ishaq ke tsaye, miƙewa tayi hakan yasa kowa yayi shiru "Kana da tantama akan ba mahaifin ka bane a nuna maka shaida?". Ta tambaya cikin sigar rainin wayon nan, sunkuyar da kai Ishaq yayi yana zubar da hawayen kunya da nadamar abinda yayi gashi yana zaman zaman sa cikin mutuntaka ya zubar wa da kansa mutunci. Ƙasaitaccen murmushi Kisnah ta sake kafin ta juya ga ƴan class "Oops yaron ya bani tausayi, kun san mu karuwai akwai imani i can't display his father's nude, se dai ya kamata kafin ka san yadda zaka zagi wani ka san su waye iyaye da relatives ɗin ka, har ila yau You all have to know and believe *KISNAH IS THE REAL QUEEN, AM BORN TO RULE* ". Tana faɗar hakan ta juya wajen zaman da tun farko ya janyo case ɗin, hayaniya ce ta cigaba da tashi a hall ɗin, da yawa sun sha jinin jikin su da Kisnah ɗin dan yau kam sun ƙara tabbatar da ba ƙaramar hatsabibiya bace, ranar dai Ishaq se guduwa yayi dan be dawo seat ɗin da yake faɗa akai ba. Shigowar lecturern su ya saka ta zare earpiece ɗin da ta maƙala tun bayan zaman da tayi wanda Meenah dake gefen ta ce ta taɓo ta, duk iskancin Kisnah tana da matuƙar san karatu, babban burin ta a wannan duniyar ta zama *LAWYER* dan har rehearsal ɗin yadda sunan ta ze koma *BARRISTER KISNAH* take yi shiyasa bata wasa da karatu haka bata taɓa missing school in har ba Rashin lafiya ba. Sosai ta maida hankalin ta kan malamin da ke ta bayani tana jotting wasu tana understanding wasu, wata irin ƙwaƙwalwa Allah ya bata me saurin fahimta da ɗaukar abu, wuyar ta ta saka kanta tofa duk wahalar karatu a wajen Kisnah se ya koma bakomai ba shi yasa dole su Surayya ke haƙurin zama da ita dan suna amfana sosai ta ɓangaren karatu haka kuma ba dan ita ba da yawanci karatun ma ba yi zasuyi ba dan baya gaban su. Ko da malamin ya fita tattare littattafan tayi waje ɗaya Meenah dake gefen ta ta ɗauka haɗe da nata, fita sukayi a hall ɗin dan basu da wata lecture ɗin se after 2 hours, library ta wuce suka bi bayan ta, haushi sosai ya kama Surry da Hameedah dan su in akwai abinda suka tsana be wuce wannan shiga Library ɗin ba se dai kuma ba yadda zasu yi dan indai zata shiga dolen su su bita. Haushin Kisnah Hameedah ke ji ganin yadda ta zama boss ɗin su, komai se abinda tace zasu yi, in partying ɗin ne, in clubbing ɗin ne, karatun ne ko zaman gida du se abinda tace. Haka ba yadda suka iya suka shiga, circulation suka samu suka zauna kowacce ta ciro book ɗin da zata karanta suka mai da hankali kai. _____________ *MASARAUTA* A can masarautar DAULATUL NOOR kuwa al'amura na tafiya yadda ya kamata a ɓangaren sha'anin sarauta, sedai a ɓangaren Haleematus~Sadiya kawai dai tana rayuwa ne blankly, Sam babu ɗigon farin ciki a rayuwar ta se ɗumbin baƙin ciki da damuwa da take ɓoyewa a ranta saboda wasu rayuka da ba zata so dakushe rayuwar su ba. Kamar yau da take zaune cikin hamshaƙin falon ta da yaji kayan alatun sarauta, duk inda ake neman haɗuwa da tsari na ƙyale ƙyalen gidan sarauta to fa tabbas akwai shi a wannan falo. Kishingiɗe take akan kilisar ta idanun ta lumshe tayi nisan kiwo cikin duniyar tunani da ta zame mata abokiyar rayuwa tun bayan barin hasken ranta kuma gudan jinin ta YARIMA SARAKI ƙasar, a kullum ba ta da wani aiki se wannan tunanin dan ma tana ƙoƙarin ganin ta danne wani abin a ranta ko dan ragowar ƴaƴan ta su samu farin ciki sedai wani abun yana gagara dannuwa har ya fito ya bayyana kansa a zahiri. Duk kirarin da ake yi na isowar Yarima Jamal bata ji ba ba kuma ta san anayi ba har se da jakadiyar ta ta ɗan bubbuga gefen kilisar ta kafin ta yi firgigit ta dawo duniyar mu. "Allah ya ƙara wa gimbiyar Giwa lafiya, yarima Jamal ke neman iso". Gyaɗa kanta kawai tayi batare da ta iya magana ba dan a lokacin da zata sami dama to tabbas kuka zata yi. Cikin takun ƙasaita haɗi da izzar da ta zagaye jinin jikin sa yake takowa cikin falon yayinda bayi da kuyangi ke ta zubewa suna gaida shi, da fara'a yake amsa musu dan Yarima Jamal mutum ne me fara'a da barkwanci haka ko ga talakawan ƙasan sa be kasance me girman kai da ɗagawa be se ko ɗan abinda ba'a rasa ba na jinin sarauta dake yawo jikin sa. Gaban mahaifiyar sa ya zauna yana tanƙwashe ƙafafun sa kana ya sunkuyar da kansa "Barka da rana Mamin saraki, gimbiyar Giwa kuma sarauniyar mai martaba, fatan na same ki lafiya". Murmushi ne ya wanzu kan fuskar sarauniya Haleematu, duk da soyayyar saraki a ranta daban ce amma tana matuƙar so da ƙaunar ragowar ƴaƴan ta suma. Hannu takai kanshi dake sunkuye ta shafa sumar kansa da ta kasance baƙa ƙirin kuma me tsayi da kuma taushi kamar me kasancewar su jinin larabawa da kuma Fulani. Hannu yakai ya riƙo na mahaifiyar sa kana ya ɗago yana sakin kyakkyawan murmushi, fatabarakallahu Ahsanul khaleeqeen, tabbas yarima Jamal kyakkyawa ne da ze amsa sunan kyakkyawa a ko ina, haka fara'ar fuskar sa na daɗa ƙara masa kyau da haiba. "Ina fatan gimbiyar Giwa ta kasance cikin walwala da farin ciki, ya zamo bata da wata damuwa". "Ina cikin farin cikin sanin ina daku a tare dani yarima sedai zuciya ta baza ta iya daina tunani da damuwa da halin da saraki na ya ke ciki ba". "Shin ban alƙawaran tawa sarauniya sama mata farin ciki a duk inda yake ba?". "Bana fatan yarima na yayi abinda mahaifin sa ze yi fushi da shi, kai kaɗai gare ni yanzu dan haka ba zan so rasaka a kusa dani ba in ba Haka ba zuciya ta zata buga ne dan bazan iya jurewa ba". "Karki damu Mamin Saraki, maimartaba baze taɓa sanin na fita neman Yaya ba sedai in ke zaki faɗa masa, a yanzu haka na shigar da uzurin son barin ƙasar nan zuwa ƙasar Sarbila dan yin wani course a ɓangaren karatu na na tsawon shekara biyu, ki taya ni da addu'a Allah ya sa maimartaba ya yarda domin amincewar sa ita ce komai". "Addu'a ta na tare daku a koda yaushe, kai da Saraki na har ma da ƙanwar ku da ke gidan aure, Allah ya tsare min ku a duk inda zaku sami kanku ya baku Sa'a da Nasara a rayuwar ku, Allah ya haskaka min rayuwar ku ya kare ku daga sharrin duk wani abin ƙi tare da ku da al'ummar Musulmi baki ɗaya". Da Ameen yake ta amsa addu'ar mahaifiyar sa zuciyar sa cike da tsantsan tausayin ta, batun yau ba ya daɗe da sanin irin so da ƙaunar da mahaifiyar tasu ke yi musu sedai Saraki daban ne a ranta, ko da yasan hakan be damu ba domin ta na nuna musu so ne equally haka kuma dole taso Sarakin tunda shine ɗa na fari da ta fara haifa haka kuma ɗan da ke tsananin so da ƙaunar ta tare da yi mata biyayya matuƙa. Sallama yayi mata ya fita daga kilisar ta ya wuce zuwa ɓangaren sa, alkyabbar jikin sa ya zare kana ya rage kayan jikin sa ya kwanta kan gadon sa ya shiga wassafa yadda ze fara neman ɗan uwan sa, ba wai ze dawo dashi gidan sarautar bane, a'a su san inda yake kawai suke so da kuma lafiyar shi ko hankalin su da na mahaifiyar su ya kwanta. Ƙarar wayar sa ce ta katse masa lissafe lissafen sa, janyo wayar yayi yai picking, lumshe ido yayi lokacin da sassanyar Muryar ta ya daki kunnen sa. "Barka kadai lovely, hope kina lafiya". "Lafiya na ƙalau Alhamdulillah dear, ya su Mamin yaya Saraki". "Tana lafiya lau Alhamdulillah, ya nan wajen su Mama". "Itama suna lafiya, yau ban ji kiranka ba shine na kira inji ko lafiya". "Lafiya lau lovely nayi busy ne kawai, dama ina so in shigo muyi magana". "Okay to in jiraka kenan yau". "Se gobe dai, yau zamu zauna da maimartaba". "A fito lafiya, Allah ya ƙarawa Sarkin Giwa lafiya". "Ameen, Ameen". Kashe wayar yayi yana komawa kwance yana saƙe saƙe, hasashen yadda zasu ƙare da maimartaba yake bisa saƙon kiran da aka isar masa daga Sarkin, yana haka har bacci ya ɗauke shi. _______________ Tsaye yake bakin shago yana miƙa wa Faruq ɗaya daga cikin abokan aikin sa a shagon takalman mata yana miƙa wa wasu ƴan mata suna gwada wa dan zaɓar wanda yayi musu, a sati da kwana biyar da zuwan Saraki shagon sun ƙara samun customers sosai Musamman ƴanmata wanda yawanci in suka zo haka za suyi ta ƙoƙarin jan Sarakin da hira sedai kallo basu ishe shi ba balle ya tanka musu, haka za suyi ta zuba sedai ragowar yaran shagon su amsa musu amma ba hakan ke hana su dawowa gobe ba. Yanzu ma haka yarinyar se wani iyayi take yi amma Saraki ko kallo bata ishe shi ba dan wallahi shi ko kalar ta baze iya cewa gata ba, ita da Faruq take ta zubar ta wanda yawanci tambaya ce take masa game da Sarakin yana bata amsa iya wadda ya sani wata kuma yayi dariya har ta gama ta wuce. "Kar ka kuma sanar da kowa komai a kaina Faruq, bana so". Dariya Faruq yayi yana sara masa tare da faɗin Yes sir, murmushi kawai Saraki yayi da ba kowa ze San yayi ba, tuni su Faruq suka gane halin sa na rashin son magana da hayaniya shiyasa ba sa wani damuwa dan sun yi masa magana yayi murmushi ko body language. Yau da wuri suka tashi kasancewar juma'a, wanka yayi yana komawa dan Allah yasani yana ƙoƙari da haƙuri da rashin wanka da yawa da yake yi yanzu a rana, singlet ya bari da dogon wandon jeans ɗin jikin sa ya ɗau Alqur'ani ya ɗora da bitar da yake yi dan baya son haddar sa ta Sami matsala. Haka yake rayuwar sa kullum tsawon sati biyu kenan da zuwan sa garin manya, da safe yayi wanka ya dafa tea ya karya, ƙarfe tara ya wuce kasuwa, da rana baya cin komai dan baze iya cin abincin kasuwa ba, ƙarfe shida zuwa da rabi ya dawo gida, wanka yake fara yi se yai kwanciyar sa ya huta ko ya yi karatun sa kamar dai yau daga nan baya fita se masallaci magrib ya jira ayi isha sannan ya dawo daga nan kuma se gobe ze fito da asuba yayi Sallah. ______________ Ƙarfe sha biyu sannan suka fito daga Library, dukkan su sunyi wujiga wujiga banda Kisnah dan ita in tasa kanta zata yi abu to fa duk wuyar sa ita bata gani. Motar Kisnah suka shiga suka fita duk da kowacce da tata ta zo, abinci suka fita ci dan basa cin komai na makarantar, EAT WELL restaurant suka je, vip suka shige akayi serving ɗin su abinda kowacce ke so suka ci suka sha kafin suka fito. Kamar ance ta ɗaga kan ta ta sauke idanun ta kansa, zaro ido tayi tana faɗin wow tare da kwass da gudu ta nu feshi, bata yi wata wata ba ta faɗa kansa.....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. *Vote, comment and share fisabilillah* Ouummey 07 (8/1/2022 3:23 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 7️⃣ ___________________📖 Sak saurayin da ta faɗa kan sa yayi dan it's unexpected kafin ya ɗan zare ta daga jikin sa ya ja baya kaɗan, zare Ido yayi ganin ta kafin unbelievably ya nuna ta Yana faɗin sunan ta "Queen, Kisnah". Da ƴar dariyar dake fuskar ta ta furta sunan sa Shima "Deeq". A sittin ya sake fisgota jikin sa ya ƙanƙame yana sakin dariyar farin ciki kamar yadda itama ta kasa rufe bakin ta, ƙara zare ta jikin sa yayi ya tsura mata Ido har se da ta hura Masa iska a bakin sa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya sake rungumar ta, wannan karon da kan ta tai breaking hug ɗin kana ta ja kujerar gefen sa ta zauna tana gyara zaman rigar ta da ta ɗan janye zuwa cikin ta. Zama Shima yayi a kujerar sa ya sake kafe ta da Ido Yana kallo kamar irin Wanda ya Sami film ɗin da ya daɗe Yana jira, ɗan haɗe rai tayi tana dukan table ɗin gaban su "Zaka Fara ko Deeq bayan kafi kowa sanin bana San wannan ƙure kallon ko". "Uhm..hmmm...am..am sorry Kissy, kawai na kasa daina mamaki da jin daɗin ganin ki ne, we missed you so badlyyyy". Ya ƙarashe faɗa Yana Jan ƙarshen kalmar badly ɗin, murmushin ta me cike da aji tayi kafin a ɗan shagwaɓe itama ta mayar Masa da amsa "I missed you people so much also, it's a kinda feeling I gat at that time, I thought of nothing but home, my country, my land, my pride and my happiness, and as you can see am enjoying it here". Gyaɗa kansa yayi cikin yarda da abinda tace "Sure I believe you're enjoying it, but what about we people, you don't have idea how we felt at the time, you leaving without even saying a goodbye is something we didn't expected". "And am sorry for that, nasan in na faɗa muku ba zaku bar ni in tafi ba that's why I choose to just disappear without your consent". "Allah ya shirya ki, so bani labari, how's life here in naija to you bayan nasan kin Saba da rayuwan Canada". "The feeling of living in my home is as sweeter as honey, that's what I lack in Canada, but I missed all those partying, clubbing and dancing like hell though am trying to catch up here". "I see, those girls?. Ya faɗa pointing at su Meenah da suke cin abincin su hankali kwance dan sun Saba irin haka da Kisnah ɗin, "Friends". Ta Bashi amsa a taƙaice, nodding yai Shima without saying anything dan daga yadda ta amsashi ya tuna Kisnah fa bata son yawan tambaya da bin ƙwaƙƙwafi akan personal life ɗin ta, miƙewa tayi tana duban designer and fashionable wristwatch ɗin dake tsintisyar hannun ta "We see some other times Deeq, will be having some lectures now". "No am not letting you off until you gave me ur digits, kaɗan daga aikin ki ki ɓace min a garin nan". Ƴar dariya tayi a gayance da ya bayyana wushiryar ta dake ƙara Maya kyau kafin ta shiga karanta Masa number ta Yana shigarwa wayar sa, hannu ta ɗaga masa bayan ya gama sawa ta wuce wajen su Meenah da zuwa lokacin su ma sun gama ita suke jira, Surayya ce ta ɗauka mata nata abincin da akayi packaging cikin wrapping paper me kyau duk da a cikin wani ƙayataccen takeaway take dan bata Sami cin abincin ba tana ta magana da Deeq. Makarantar suka koma dan suna da lectures biyu kafin su tashi, kamar yadda ya zame mata halayya da ɗabi'a wajen mai da hankali kan karatu yanzu ma haka tayi dan bata sake ko kallon su Hameedah ba se da suka fito daga theatre dan babu interval a jere ne lectures ɗin, wani na fita wani na shiga. Ƙarfe shida biyar saura suka fito, kowa ka kalla fuskar sa gajiya zaka karanto kwance kanta wanda su Kisnah na ɗaya daga cikin su, na lokacin ba abinda take buƙata se wanka dan wani irin danƙo da ƙaiƙayi take jin jikin ta na mata, haka yasa hannu kawai ta ɗagawa su Hameedah da suka ƙarasa wajen motocin su kafin ta shige tata ta fige ta a ɗari ta fice a makarantar. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙarasa gida dan ba ƙaramin gudu ta ɗiba ba a titin, base nace komai ba kun dai san yadda tuƙin ta yake, bata tsaya bin yadda taji parlon nasu yau shiru ba hayaniyar kowa ba ta haure saman ta, tun a nata ƙaramin parlon ta fara cire kayan ta tana watsarwa har ta ƙarasa bedroom lokacin ba abinda ya rage a jikin ta ta faɗa toilet. Sassauƙar ajiyar zuciya ta sauke bayan ruwan sanyin ya ratsa fatar jikin ta ya shige ƙashi da jinin jikin ta, tun tana yarinya Allah ya jarabe ta da son ruwan sanyi wajen yin wanka, ba ƙaramin sanyi za'a yi ba da zaka ga Kisnah ta yi wanka da ruwan ɗumi sedai ko ta gasa jikin ta da na zafi amma fa in ta fito se ta watsawa jikin ta na sanyin nan, abin a jinin ta yake shiyasa da yawan ruwan sama da ake yi yake ƙarewa a kanta dan da taga hadari zata canja kayan ta zuwa rigar wanka ko shimi iya cinya ta fita backyard ta fara wasa a ruwan har se anyi an ɗauke a kanta kafin ta koma ta canja kaya. Shimi ta saka me ɗan tsayi da ta tsaya iya rabin cinyar ta ragowar kuwa na waje se ƙyalli fatar ta take yi tana ɗaukar ido, tun a kallon farko zaka san ba ƙaramin laushi da santsi zata yi ba shiyasa in ta saka kayan da basu rufe mata jiki ba zakaga maza na ta ƙure mata kallo suna tanɗar baki tun bare ma ƴan bariki da suka san sittin mata. Parlon ƙasa ta sauka ta wuce kitchen inda ta sami Rayya tana girki cikin nutsuwa, gaishe ta tayi ta amsa a sake kamar yadda ta saba dan bata kasance cikin masu wulaƙanta ƴan aiki ba. "Ya naji gidan shiru, ina mutanen gidan?". A ladabce Rayya ta bata amsa "Duk basa nan, ɗazu Hajiya babba ta fita da trolley a hannu ita kuma Aunty maigado taje makaranta, yaya Awwaf kuma ........". "Wannan surutu baki Rayya Allah ya yaye miki, kawai se kice min basa nan shikenan amsar tambaya ta, in Kuma na nemi ƙarin bayani se ki faɗa min ina suka je". Dariya Rayya tayi "Da ke kaɗai nake surutun nawa ai Aunty Kisnah, Allah Baki na har ciwo yake yi na rashin magana a gidan nan". "Toh Allah ya yaye miki, nidai yau a gajiya nake bare in biye Miki , zuba min abinci in tafi dan a gajiya nake". "Amma gaskiya Aunty Kisnah wannan yaya Awwaf ɗin ɗan Air ne". Rayya ta faɗa tana zuba mata fried spaghetti da tayi wadda taji kayan lambu sosai, zare kyawawan oily brownish eyes ɗin ta masu kama da na mage Kisnah tayi "Faɗa min me yayi miki ni Kisnah?". Hankali tashe tayi maganar dan ita kan ta shaida ce Awwaf ƙwararren ɗan iska ne da bata fatan ace yayi wa Rayyan wani abu dan bazata so a ce a gidan ta aka ci mutuncin wata ba. "Laah ba fa abin da yayi min kawai dai naji shi yana waya ne yana batsa". Ajiyar zuciya Kisnah ta sauke "Kome yake yi ba ruwan ki, ki kama kanki kin ji ko, bana san ko da wasa in ji wani abu ya haɗa ki dashi bayan gaisuwa, na faɗa miki". "Insha Allah Aunty". Karɓar abincin Kisnah tayi ta juya ta fita daga kitchen ɗin batare da ta kuma cewa Rayya komai ba,da ido Rayya ta raka bayan ta cikin kallon ƙauna, ba ita kaɗai ba duk ma'aikatan gidan haka suke san Kisnah dan bata da raina na ƙasa da ita, bata da wulƙanci balle rashin mutunci, barta dai da yawace yawacen ta, itace bata club, cinema, park, hotel da guest in, kullum tana da gurin zuwa dan bata fiye zaman gida ba se dai in tana da school wacce itace abu mafi muhimmanci a rayuwar Kisnah ɗin. A duk yadda ake mata kallon karuwa ko ƴar iska har yau zuciyar Rayya ta kasa yarda da cewa hakan take, ita tana hango kamewa da mutuntaka a idanun Kisnah ɗin da jama'a suka kasa gani, tana ji a zuciyar ta sunan karuwa be dace da Kisnah ba duk kuwa da ayyukan ta na zahiri sun tabbatar mata da sunan a idanun jama'a sedai ita har yau zuciyar ta takawa aminta da hakan. Plate ɗin abincin ta ajiye kan carpet ɗin da ke tsakiyar ɗakin tare da zama ta ɗau spoon ɗin, shiru tayi cikin don tunawa da wani abu da tayi kafin fara cin abinci sedai ta kasa tunawa hakan yasa ta fara cin abincin ta cike da nutsuwa, sedai tayi kusan spoon uku sannan ta tuna da takeaway ɗin da Meenah ta saka mata cikin mota, ɗan taɓe baki tayi ta cigaba da cin na gaban ta , ko rabi ba tayi ba ta ajiye spoon ɗin tana nishi jin yadda cikin ta ya cika, mamaki sosai ya kama ni dan ba wani abinci bane na zai a gani gaba ɗayan sa, kun dai san yadda ƴan gayu keyin zubin abincin su wai amma a haka rabi kawai taci. Seda ta ɗan huta sannan ta jawo robar natural ginger drink dake ajiye gefen ta wanda ita take haɗa kayan ta ta zuba cikin fridge ɗin ɗakin ta saboda irin haka in taci abincin ta, sha tayi to her satisfaction sannan ta ajiye, laptop ɗin ta ta jawo ta shiga bincike kan harkokin karatun ta wanda tayi zurfi a cikin sa sosai ya kuma ɗauke ta lokaci me tsawo. Se gab da magrib ta ajiye sannan ta canja kayan ta zuwa na training ta fita gudun yamma da take yi duk lokacin da take gida, riga da wando ne sport wears dark blue color masu ratsin fari, rigar ta kamata sosai kamar wadda akayi shaping se dogon wando shima daidai jikin ta da ya tsaya iya ƙasa gwiwar ta, robar ruwa ɗaya ta ɗauka se ƙaramar wayar ta ta zura a pocket ɗin wando, canvas me ɗan tudu fari tas ta ɗaura a ƙafafun ta wanda ya zauna a ƙafar yayi mata matuƙar kyau, kame gashin ta tayi da blue ribbon ta yi masa doughnut da yayi girma sosai a tsakiyar kanta saboda yawa da tsayin gashin, blue band ta saka a kanta kana ta jawo manya manyan headphone ta maƙala a kunnuwan ta ta kunna waƙoƙin ta na india sannan ta fita daga ɗakin tare da rufe ƙofar da key dan bata yarda da kowa na gidan ba bare har ta bar ɗakin ta a buɗe. Yuuuuu masu aikin compound ɗin gidan suka bita da kallo cike da sha'awar yadda tayi kyau cikin kayan ta haska su, batare da kula kallon da suke bin ta dashi ba ta fita daga gidan ta ƙaramar gate ɗin ta fara gudun ta kaɗan kaɗan hankali kwance, sosai ta zagaye layikan bayan su har ta ƙarasa iya distance ɗin da take so sannan ta nufi dawowa gida, lokacin kam tuni an idar da sallar magrib dan har duhu yayi sedai abinka da unguwar masu dashi ko ina haske ne tarwai har kamar da rana dan ko allura ce ta faɗi a sauƙaƙe za'a ganta a wajen. Cillar da robar ruwan hannun ta tayi bayan ta ƙarasa shanye ruwan lokacin har ta kusa ƙara sawa gida hakan yasa ta rage gudun da take yi zuwa joking har ta ƙarasa, a parlo ta tadda maigado zaune da system zaune kan ƙafafun ta gorar sassanyan lemu a ɓarin daman ta na fresh milk a ɓarin hagu. Ko kallon ta Kisnah bata yi ba dan Allah Allah take taje tayi wanka saboda ginin da ta haɗa, ita fa haka take kamar kifanya, akwai ta da son ruwa sosai musamman na sanyi shiyasa a rana se tayi kusan wanka bakwai zuwa takwas, ko yanzu ma wanka tayi tare da ɗauro alwala, komai ba ta saka ba bayan towel ɗin jikin ta ta ɗora hijab ɗin sallar ta wanda shi kaɗai take da hijab ta tada sallah. Yadda take sallar a gaggauce ze shaida wa me kallon ta bata da wadataccen ilimin addini dan komai bata karantawa a sallar ta ke yin ruku'u wanda yake kama da gaisuwar ƙwangen matasan zamani, sujjadar ta kuwa kamar yadda yara ke yi suna leƙowa ta ƙarƙashin nan, cikin mintina biyar ta gabatar da sallar Azahar, la'asar da magrib da ta tara, dama kuma kusan kullum haka take yi, isha kuwa ba kullum take samun yin ta ba, ranaku irin na yau ɗin sosai take fashin isha saboda zata fita club wanda bata dawowa se wajen ɗaya na dare ko biyu in ta kai mata. Wasu sheɗanun kaya ta saka dan tana cikin waɗanda zasu yi rawa yau a club, ba wai tsara mata ranakun da zata yi rawar ake yi kamar yadda ake yi wa kowa ba, itace take zuwa duk ranar da taso, ranar da zata yi rawa kuwa kamar yau shigar da take yi ta daban ce, duk ranar da ta shiga fili kuwa se ta cinye kowa dan ƙwararriya ce akan hakan, wannan yasa ta tara masoya da magoya baya da yawa a club ɗin, kowa dakon ranar da zata zo yake yi, wanda yayi katari da ganin ta kuwa murna zaka ga yana yi kamar wanda akayi wa albishir. Wasu kaya ne da marabar su da tsirara kaɗan ne, guntun wando ne iya matsematsin cinyoyin ta se baza da akayi masa da ta sauko har rabin cinyar tata, rigar kuwa zan iya cewa sunan ta brazier kawai, dan iya curve ɗin bra ne da ita seko baza itama a ƙasan ƙirjin da ya sauka har kan cibiyar ta, hannun kuwa wasu zarurruka ne da ake ɗaure su kamar dai yadda ta tsaya gaban mirror tana ɗaure su, saman ƙirjin ne aka saka net me shara shara sosai da be hana a hango albarkatun ƙirjin ta ba, net ɗin ya kai har saman ƙirjin sosai, ƙafar ta kuwa wani shegen takalmi ne me tsini kamar tsinke, tsananin mamakin yadda za'a iya taka wannan takalmin shi ya daskarar dani waje ɗaya, barima ta gwal ta ciro cikin kayan fashions ɗin ta ta saka a kunnen ta yatsun hannunta kuwa ta wadata su da gold rings uku uku a kowane hannu, sarƙar ƙafa me kyau ta ciro ta zauna kan madubi ta maƙalawa ƙafarta ta dama kana ta zaro wata kyakkyawar jigidi me wani irin sihirtaccen sound ta ɗaura a dirarren ƙugun ta, turarurruka masu matuƙar kaifin ƙamari ta ɗauka ta feffesa a ko ina na jikin ta, kallo ɗaya me kallon ta ze to mata ya kirata cikakkiyar karuwa me licence, sheɗaniya number ɗaya haka kuma wadda shiryuwar ta se Allah..................✍️. *☑️Ote, Comment and Share fisabilillah*. Ouummey 08 (8/2/2022 3:41 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 8️⃣ __________________📖 Box ɗin da take ajiyar keys ɗin motocin ta ta buɗe ta ɗauka ɗaya ba tare da ta tsaya duba wacce bace dan duk motocin ta latest ne, cikin ƙwarewa da iya taka takalmin ƙafar ta take taku ɗaiɗaya har ta fito daga bedroom ɗin ta, fresh kunun aya da ke fridge ɗin ta ta ɗauka gora ɗaya ta fita dashi a hannu, yanzu ma rufe ƙofar tayi bayan tayi resetting password ɗin buɗewa wanda haka take yi indai zata yi amfani dashi wajen kulle ɗakin da password. Sskin baki maigado dake kan dining tayi cikin ƙarewa shigar Kisnah kallo, bawai shigar tata ce ta bata mamaki ba dan ta saba yin wadda ma ta fita, yadda kowane kaya ke mata kyau shine yake sa take kasa riƙe kanta kullum Kisnahn ta fito se ta bita da ido. Yatsu biyu ta ɗagawa maigado cikin salon sheɗanci kafin ta wuce ta gaban ta tana kaɗa mata dirarren ƙugun ta da ya fito fes cikin wando jikin ta though ƴar jacket ɗin da ta ɗora kan kayan ta rufe har zuwa saman gwiwar ta, wata farar dunƙulalliyar mota ce me matuƙar kyau da ɗaukar ido ta buɗe ta saka drink ɗin ta a cikin kafin itama ta shiga ta zauna, warming up motar tayi kafin ta saki horn wa maigadi, da saurin sa ya fito daga ɗakin sa ya ƙarasa gefen gate ɗin, password ɗin gate ɗin ya daddanna gate ɗin ya fara zuge kansa shikuma ya matsa gefe, da mahaukacin gudun da ya zama tsarin ta ta fice daga gidan yayin da megadin ya koma ya sake pressing password ɗin rufe wa, kawu dake tsaye ta can saman benen sa yana kallon komai ya saki wani makirin murmushi kafin ta juya zuwa cikin parlon sa. Wayar sa ya ɗauka dake gefen sofar da yake zaune yai daddanna wasu numbers kana ya kara a kunnen sa, shiru yayi zuwa lokacin da aka ɗaga wayar sannan ya fara magana "Ta fito yanzu wanda am sure ba zata dawo da wuri ba se zuwa 2am dan haka ku bi bayan ta kuga inda tayi, kusan yadda zaku tare ta in ta fito lokacin dare yayi tsakiya kowa na gida, tun yanzu ku ɗau matsaya dan bana son aikin wasa, ban ce kuyi mata komai ba se barazana dan ina so ta tsorata ta bar batun dukiyar ta dake hannuna". Amsar da aka bashi daga can ya sa ya jinjina kai cikin gamsuwa kafin ya katse wayar yana jin sa cikin farin ciki dan ba shida tashin hankalin da ya wuce yaji Kisnah na maganar karɓar dukiyar ta wadda da ita yake ci yake taƙama yake wadaƙa da bushasha shiyasa yanzu ba shi da burin da ya wuce ya mallake ta takowace hanya kuwa. ******* *HIDEAWAY CLUB (The young Anacondas)*. Tun kafin ta ƙaraso bakin gate ɗin club ɗin take sakin mahaukatan horn, da sauri masu gadin wajen suka wangale makeken gate ɗin, ƙaton building ne da tun kafin ka shiga zaka san babban waje ne da ya ƙawatu da kayan alatun rayuwa, ginin tsakiya ne da ya wadatu da gilasai ta ko ina ba abinda yake se ɗaukar ido da reflecting abubuwa, kyawawan fulayoyi da furanni ne shushhuke a compound ɗin club ɗin da ya zagaye ginin club ɗin dake tsakiya. Parking tayi a parking lot ɗin wajen ta kashe motar, da gudu masu gadi da suka rufe gate suka ƙaraso wajen da take suna washe haƙora dan sun san tabbas yau kakar su ta yanke saƙa dan kyauta ne Kisnah take musu ta manya, kamar yanzu buɗe mata ƙofar tayi ta zuro ƙafafun ta kafin a hankali ta fito da gangar jikin, rusunawa sukai da sauri kowanne na gaisuwa da kirari, murmushi ta hau sake musu dan ita kam bata da wulaƙanci haka macece me fara'a da in kaga ta ɗaure fuska to fa an kai ta ƙarshe, gaishe su tayi daga tsaye sukuma suna durƙushe wanda biyu daga cikin su za su haife ta a haife dayan kuwa ya girme mata nesa ba kusa ba, check ta yi signing ta miƙa musu dan bata fito da cash ba, da sauri babban cikin su ya karɓa suna zuba godiya, bata kuma kula wanzuwar su ba ta ɗau wayar ta da goran kunun ayar ta ta rufe motar ta wuce cikin main building ɗin club ɗin. Babban hall ne dake shaƙe da jama'a maza da mata, mostly samari da ƴan mata ne a ciki se kuwa tsirarun manyan mata da maza da tsufa yai wa gardama sukai faɗuwar baƙar tasa. Ihu da sowa club ɗin ya ɗauka baka jin komai se kiran sunan Queen Kissy it's kuwa se murmushi take yi yalwatacce tana ɗaga hannun ta dake riƙe da key ɗin mota, ɗaya bayan ɗaya manyan yaran wajen suka ƙarasa suna rungume ta ba maza ba mata, da ƙyar suka ƙyale ta ta ƙarasa wajen su Meenah dake zaune a permanent VIP seat ɗin su, kujera Meenah ta ja mata ta zauna wanda itace permanent wajen zaman ta se Meenah a gefen daman ta, Hameedah a gefen hagun ta se Surayya da Maleeka a ragowar kujerun wajen da suka kasance biyar se wani haɗaɗɗen madaidaicin table a tsakiyar su. Daga inda suke take kallon ƴan wajen kowa ke sabgar gaban sa gefe ɗaya kuwa ƙaton filin rawa ne da ƴan rawa kowanne na ƙoƙarin son ganin ya nuna tasa bajintar, a nan kan table ɗin su kuwa manyan kwalaben wine ne da Maleeka tayi ordering dan iya kam cikakkiyar mashayiyar giya ce, a rana se ta shanye kusan kwalba uku ko huɗu, a irin wannan ranakun kuwa da suka zo club kafin su tashi tana iya shan biyu, ita kuwa Meenah gaba ɗaya hankalin ta yana kan lemon coke da take jijjigawa dan ƙwayoyin da ta zuba su narke, ita bata shan giya amma tana shan ƙwaya, Hameedah kuwa shisha ce take zuƙa tana fesarwa cike da ƙwarewa se Surayya da ita kuma hankalin ta ke kan mazan wajen, ita bata shaye shaye ko kaɗan se dai akwai ta da son maza, gajeren tsaki Kisnah ta saki tana fincike robar coke ɗin dake hannun Meenah dan a ɗan zaman ta na mintina talatin wannan ce roba ta biyu da Meenahn zata shanye wadda ta shigo ta tarar da wata a hannun ta. Cikin ɗan maye kaɗan da ƙwayar kan saka ta Meenah ta ɗago ta kalle ta, wata shegiyar harara Kisnahn ta wurga mata da ta saka ta komawa ta lafe cikin kujerar ta tana kumshe idanun ta dan tasan ma'anar hararar shine ta shanye iya kason ta na yau. Miƙewa Kisnah tayi ta zare ƴar jacket ɗin jikin ta ta ajiye kan seat ɗin ta tare da wayoyin ta, gorar sassanyan kunun ayar ta ta buɗe ta ɗaɗɗaka har yai rabi kafin ta rufe ta ajiye ta fice daga VIP ɗin ta nufi wajen masu rawar. A take duk masu rawar suka tsaya can kafin suka fara fita ya rage saura wasu uku, nan da nan aka canja kiɗan dake tashi wajen daga American songs zuwa Indian songs, wani irin kumshe idanun tayi tana jin kiɗan na ratsa ta kafin a hankali ta fara takawa ta kai tsakiyar mutum ukun, cikin wani irin salo ta fara kakkarya gaɓɓan jikin ta cikin salon waƙar tana malkwaɗe wa, banda ihu da sowa da tafi babu abinda ke tashi a wajen dan ko shakka babu tafi asalin jarumar da ta hau waƙar iyawa, haka ta dinga yin rawar waƙoƙi da dama kafin ta dakata tace a maida mata American songs ɗin, nan ma haka ta hau yi kai kace ba musulma nace balle ɗiyar hausawa kuma. A nan ta ɓata lokaci har kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare kafin ta fita a wajen, liƙi kam ta sha shi, manyan yaran wajen sun yi ruwan kuɗi kamar a ƙasa ake samo su, daloli da saifa sunyi kuka se ko ƴan dubu dubu dan babu ƙasa da dubun, ko da ta fito kowa ba ta kalla ba duk da ɗumbin mazan dake ƙoƙarin son yi mata magana, maida jacket ɗin tayi jikin ta kana ta zauna kan kujerar ta bayan ta kwashe wayoyin ta da gorar kunun ta ta maida kan table cikin mamakin ina Surayya ta je, takaici ne ya kamata ganin yadda gaba ɗaya daga Meenah har Maleeka suka fita hayyacin su yayinda Hameedah ke ta sambatu cikin maye. Kawar da kai tayi daga duban su ta buɗe goran kunun ayar ta ta kafa kai ta shanye dan sosai take buƙatar jiƙa maƙoshin ta, cillar da robar tayi sannan ta ja wayar ta ta hau latse latsen ta, tsawon lokaci kafin ta fara jin kan ta yana mata nauyi, jijjiga kan tayi cikin son dena jin komai ta cigaba da danna wayar ta, wani irin jiri jiri ta fara ji kafin ta fara ganin bibiyu uku uku, da sauri ta ajiye wayar tana dafa kanta da hannu ɗaya yayinda take mutstsika idon ta da ɗaya hannun. Sedai maimakon ta dawo daidai se ma ƙaruwa da abin yake yi dan har gani take kamar gurin na tafiya, sama ta dawo ƙass, kamar dai tana yawo a cikin gajimare, tashi hankalin ta yayi dan duk iskancin ta bata shaye shaye, ba abun da ta tsana ma a rayuwar ta kamar giya, ƙwayar kuwa ko a asibiti aka bata bata sha duk tsananin da rashin lafiyar da take yi kuwa. Kafin kace me ta rasa hankalin ta gaba ɗaya da har ta faɗa kan table ɗin gaban ta tana wasu irin surutai marasa kan gado gaba ɗaya jikin ta ya saki idanun ta sun juye. Daga can gefen wajen zaman su wasu samari ne da kallo ɗaya zaka musu kasan manyan yara ne saboda irin shigar dake jikin su, cike table ɗin gaban su yake da kayan shaye shaye, tukunyar shisha, ƙwayoyi, kwalaben maganin tari, cocain har ma da wasu da ban ko san su ba, su huɗu ne kowanne kuma da kalar kayan mayen da yake bankawa cikin sa banda ɗaya daga cikin su da yake danna waya yanayi yana duban Kisnah a kaikaice. Wani irin shu'umin murmushi ya saki kafin ya dubi na gefen hagun sa yana miƙewa "Ni na wuce, yau dai tarkon da na ɗana ya kama ɗawisu". Dariya duk suka sake na gefen damar da na faɗin "Kai baaba yau zaka kwashi Gara yacin, ko dai nima nazo na ɗana ne in ka gama". Wata shegiyar harara wanda aka kira da baaba ya sakar masa "Ka jimin ɗan iska, yau ina suhan ɗin taka da har kake kiran in rage maka, to bari kaji till Dawn zan yi dan haka ma kar ku jira ni ku wuce kawai zamu haɗe gobe". Sowa suka sa suna tafawa kafin ya musu sallama ya wuce, wajen su Kisnah ya ƙarasa lokacin tayi nisan da har bata gane waye a kanta, hannu yasa ya shafi fuskar ta yana kunshe ido saboda tsananin taushi da santsin fatar ta, wani irin lashe leɓe yayi da harshen sa cikin salon su na gogaggun ƴan guguwa kafin ya sa hannunsa biyu ya ɗauke ta kamar wata baby doll ya fice da ita daga wajen gaba ɗaya. A tazame Surry dake wani ɗaki ita da saurayin ta suna romance ta fincike jikin ta ganin yadda yau wani namiji ya samu damar taɓa Kisnah har ma ya ɗauke ta a hannun sa, da azama ta fita daga ɗakin wadda dama basu rufe ƙofa ba, to rufewar me zasu yi bayan kowa iskancin sa yake a fili, ko kafin taje har ya saka Kisnah a mota yayi mata key, da gudu Surayya ta koma table ɗin su ta ɗau key ɗin motar ta ta fita itama, tana fitowa compound shikuma Yana fita da motar daga building ɗin, a gigice ta figi motar ta fice kafin masu gadi su gama rufe gate ɗin da ya fita. Hannu ta kai zata yi accelerating motar se kuma ta fasa dan in yasan an biyo shi ze iya gudun da ze tsere mata dan ƙarfin hali ne kawai take yi amma jikin ta a mace yake da abinda saurayin ta ya gama yi mata. Sannu a hankali take bin bayan motar har suka ƙarasa bakin kasuwar durumi in da ta tabbatar ko ihu tayi za'a iya jin ta saboda shagunan masu kwana dake kan titin, ƙara gudun motar tayi taje ta sha gaban shi har ƙiris ya rage bata daki gaban motar shi ba, ajiyar zuciya ya sauke jikin sa na ɓari dan da be yi saurin tsaida motar Ba da se sun daki wanda Allah kaɗai yasan me ze faru in da hakan ya kasance. Ƙurewa motar gaban sa ido yayi cikin son gano waye ya sha gaban sa sedai be yi nasara ba kasancewar motar me baƙin gilashi, cikin motar kuwa hannu na rawa Surayya ta danna kiran jami'an tsaron da ke police station nan gaba dasu kaɗan dan ƙa'ida ne akwai police station gaban duk kasuwannin garin. Cikin Sa'a bugu biyu wani ɗan sanda yai picking call ɗin ta sanar dashi me ke faruwa, take ya shaida mata hadu nan tafe, cikin ɓacin rai baaba wanda asalin sunan sa Sageer ne ya fito daga motar dan ganin wane ɗan rainin hankalin ne ya tare masa hanya, a fusace ya kaiwa glass ɗin motar Surry wani mahaukacin bugu, ganin fa in aka cigaba da haka se iya fasa glass ɗin kuma ya damƙe ta yasa hankalin Surry tashi dan kallo ɗaya zaka yi wa baaba Kasan gawurtaccen ɗan Air ne, tunanin da ya zo kan Surayya yasa da hanzarin tai unlocking motar kana ta buɗe murfin da dukkan ƙarfin ta, take kuwa ya tafi ya daki kan baaba dake jiran a buɗe ya ciwa koma waye mutunci. Faɗuwa yayi gefe kan sa na zubar jini dan ba ƙaramin dukan sa murfin yayi ba Gashi kuma ƙarfen motar me ƙwari ne sosai, a fusace yake neman miƙewa dan cin uban Surry da tana buɗe motar yaga macece, da sauri ta finciko kwalbar lemo da tasha tana hanyar zuwa club ɗin ta jefe shi da ita, take ta same shi a ka ya kuwa fasa ƙara dan sosai kwalbar ta shige shi, jiri ne ya fara ɗibar sa saboda jinin dake zuba wanda har se da ita kanta ta razana, da sauri ta ƙarasa motar da ta fara ƙoƙarin fito da Kisnah daga motar sedai ta kasa dan duk jikin ta ya saki hakan yasa ta ƙara nauyi sosai, da ƙyar Surayya ta tallafo ta jikin ta suka nufi motar ta suna yi suna layi kamar zasu faɗi dan Kisnah tafi Surry nauyi nesa ba kusa ba. Ihu Surry ta saki jin shigar kwalba a gefen cikin ta wanda baaba ya daɓa mata dan baze bari taci bulus ba, sakin Kisnah tayi cikin jan numfashi a wahalce hakan yasa duk suka zube a wajen, tsabar taurin kai haka baaba ya miƙe jiri na ɗibar sa na komai ya ja su su biyun da hannu ɗaya ɗayan na dafe da kan sa, jiniyar motar ƴan sanda da yaji yasa ya sake su ya nufi faɗa wa motar da dan ya tsira saboda be manta kashedin baban da ba na in aka sake kama shi baze sake bailing ɗin shi ba, sedai ko kafin yakai mota tuni wani ɗan sanda ya sakar masa harbi a kafa da ya tilasta masa faɗuwa, da gudu wasu daga cikin ƴan sandan sukayi kan su Kisnah dake sheme a ƙasa bata hayyacin ta ga kuma Surayya dake zubar da jini a sume wasu kuma suka yi kan baaba aka sa masa ankwa a hannu sannan aka sashi a mota.......................✍️. 😭Wayyo Allah Kisnah ta😭 amma gaskiya baaba Allah ya isan mu😭 Surry mun gode miki Allah kuma ya baki lafiya😔. Duk wanda be min jajen abinda ya faru da Kisnah ba aradu bani ba shi eh😏 ©️ Ouummey📚✍️ *Vote, comment and share fidabilillah.* Ouummey 09 (8/3/2022 3:51 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 9️⃣ _______________________📖 Asibiti aka wuce dasu su duka dan ceto ran su musamman Surayya da tafi su jigata. Kula sosai ake basu ganin ƴan sanda ne suka kawo su, dressing akayi wa baaba a kan sa tare da ƙafar sa dan bullet ɗin be shiga ƙafar ba yadai shafe ta ne. Allurai kawai aka yiwa Kisnah da zasu taimaka mata dawowa hayyacin ta da wuri ban da wannan ita kam bata cikin kowane haɗari, Surayya ce dama dai ke cikin matsala kasancewar kwalbar ta shige ta sosai dan se da akayi mata aiki aka cire guntuwar kwalbar da ta karye mata a jiki sannan aka ɗinke wajen, aluran kariya aka yi mata kafin a maida ita ɗakin hutu. Ta can ɓangaren kawu kuwa yana can yana baccin sa hankali kwance da tunanin koma ina Kisnah take zuwa yanzu an kirea mata warning ɗin da ze tsoratar da ita a kansa. Tun farar asuba da ya farka ya dannawa gang ɗin nasa kira batare da ya ko duba lokaci ko gabatar da sallah ba da ake ta kira a manyan masallatan kusa da su, seda tayi ringing ta gama har so biyu basu ɗauka kafin ana uku su ɗauka, be ko amsa sallamar da suka yi masa ba ya fara tambayar su batun aikin sa. "Acan muka kwana oga amma har zuwa ɗazu karfe huɗu bata fito ba kuma kasan ƙarfe uku ake rufe club ɗin, da alamu dai ta lura da muna binta to ta bi wani, hakan yasa dole muka haƙura muka koma maɓoyar mu dan ƴan sanda suna fitowa patrol, sedai a tara gaba". Cikin wani tuƙuƙin takaici da ɓacin rai kawu ya kashe wayar, tsantsan disappointment na wanzuwa kan fuskar sa dan ba abin da ya tsammaci ji ba kenan daga gare su. ************* A hankali a hankali ta fara buɗe idanun ta da take jin sun mata nauyi sosai, dishi dishi take gani dole ta sake maida idaun ta rufe kan ta sake buɗewa, a sannu a sannu har ganin ta ya daidaita ta fara ganin komai normal, ƙarewa ɗakin kallo take cikin tunanin me kuma ya kawo ta asibiti dan a cikakken kallo ɗaya da tayi wa ɗakin ta tabbatar asibiti ne saboda gadajen dake jere a ɗakin, ƙarafan ƙarin ruwa da arin magani da ɗakin ke yi. Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye dan nauyi da ko ina na jikin ta yayi mata, canular ƙarin ruwan dake hannun ta ta fisge har jini na rushing daga inda aka saka allurar amma bata damu ba, band ɗin kanta ta cisge ta ɗaure hannun dashi wanda hakan yasa doughnut ɗin da tayi wa gashin ta bajewa ya kwanta lamɓan a bayan ta. Ƙafafunta ta zuro ƙasa da niyyar miƙewa sedai da sauri ta ɗauke cike da ƙyanƙyamin floor ɗin asibitin da yai jurwayen ƙura, hannu ta zura ta janyo takalman ta da bata san waye ya cire mata ba ta maida abin ta ƙafar ta sannan ta sauka, batare da tsayawa neman inda wani likita yake ko wanda ya kawo ta asibiti ba ta fice daga ɗakin, cikin Sa'a ba wanda ta haɗu dashi cikin ƴan sandan da suka kawo su ko likitan da ya karɓe su dan haka ta fice har bakin titin da ke gaban asibitin, napep ta tsayar ta shiga bayan ta faɗa masa inda ze Kaita, this is the first time of her being a motar haya kowace iri ce kuwa, kalle kalle take a titin har ta gane unguwar da take kafin ta sauke ajiyar zuciya. Tun da ta shigo motar mayen ƙamshin ta da ya kama jikin ta ko da bata saka ba balle ta ƙara wani yake tashi yana cika masa hanci, lumshe idanun sa yayi dan Allah yayi shi mutum me matuƙar so da ƙaunar ƙamshi sedai nata yayi ƙarfi da yawa shiyasa yake tashi sosai dan ko daga nesa mutum ze iya jin sa. Kamar kullum yau ma t-shirt and jeans ne a jikin sa sedai masu ɗan tsada ne dan duk kuɗin da yake samu a sallamar sa tarawa yake yana ƙara sutura dan mutum ne shi me son ƙyale ƙyale a jikin sa, kansa na ƙasa bakin sa na ɗan motsi hannun sa sanye da counter yana pressing alamar dai tasbih yake yi. Tun zaman ta bata san akwai wani a cikin napep ɗin ba se da traffic ya tsaida su daidai gaban wani me ɗan kiosk a gefen titi, ƙishirwar da ta addabe ta yasa ta neman ruwan da zata sha hakan yasa cikin muryar ta da bata gama dawowa daidai ba tai wa me napep ɗin magana dan ba ko sisi a hannun ta "Excuse me drive, bani ɗari biyar mana se in haɗa maka da kuɗin ka in ka kaini". "Ok". Kawai me napep yace tare da miƙo mata ɗari biyar ɗin da ta buƙata, karɓa tayi sannan ta juya side ɗin da ta hango me kiosk sedai wani ne a gefen side ɗin, batare da wata damuwa ba ta miƙawa na gefen nata kuɗin "Help me collect some water please brother". A hankali saraki da idanun sa ke kan counter ɗin hannun sa ya ɗago yana me sauke idanun sa kan hannun ta dake miƙo masa kuɗin, kamar baze karɓa ba se kuma ya saka nasa hannun ya zare kuɗin dake cikin yatsun ta cikin takatsantsan, ta ƙofar wajen sa ya miƙa kuɗin ya karɓo mata ruwan haɗe da canjin kana ya juyo ya miƙa mata, a side ɗin fuskar ta idanun sa suka sauka daidai lokacin da take gyara gashin ta da ya zubo ya rufe mata fuska, wani irin yamutsa fuska yayi ya ajiye mata ruwan nan gefe tare da kuɗin kana ya kau da kansa gefe yana kallon waje. A zuciyar sa kuwa wani irin ƙyanƙyamin ta ne ya cika zuciyar shi ganin gashin kanta da duk a tunaninsa attach ne ta saka ga kuma yatsun hannun ta da tayi wa fixing long nails da suka sha pink jan farce, ko kaɗan be lura da kayan jikin ta ba dan kallo ɗaya yayi mata be sake marmarin kallon ta ba dan ko ba ya ƙyanƙyamin ta shi mutum ne me kiyaye doka da ƙa'idojin da Muslunci ya gindaya, ba wanda ya sake ko tari tun bayan thank you ɗin da tace masa Wanda nodding kan sa kurum yayi. Bakin kasuwar da zeje aka ajiye shi, fitowar da tayi dan ta bashi damar fita yasa har ya lura da kayan jikin ta wanda jacket ɗin da ta ɗora ta suturta, wucewa akayi da ita bayan ya sallama me napep ɗin ya cigaba da takawa da ƙafa dan ƙara sawa shagon su, addu'a kawai yake wa ƴaƴan musulmai cikin ransa da sake godewa Ubangiji da yayi shi musulmi, a nashi hasashen ita ɗin kafira ce shiyasa har tayi wannan shigar ta kuma fito da ita dan su a wajen su hakan bakomai ba ne, shine fa yake godewa Allah da yayi shi musulmi, ya kuma tuna Masarautar su da irin yadda suke da tsauri kan yanayin shiga musamman ta ƴaƴa mata, addu'ar shiriya yayi mata dan duk inda yaga me laifi yakan ƙoƙarta yi masa fatan shiriya. Har ƙofar makeken mansion ɗin ta me napep ya Kaita yana ta mamakin yadda akayi me rayuwa cikin wannan gidan ta iya fita ba mota har ta shiga ta haya, wajen security ɗin bakin gate ta karɓi dubu uku ta miƙa wa me adaidaita, da hanzarin sa ya zari dubu ɗaya yana faɗa mata tayi kuskuren ƙara masa kuɗi, da murmushi kan fuskar ta ta sanar dashi ba wai mantuwa tayi ba tana sane ta ƙara masa tare da masa fatan alkhairi, addu'a sosai yayi mata lokacin har ta shige kafin yaja motar sa yayi gaba. Gaisuwar da ma'aikata ke mata ta amsa a gurguje tana shigewa tanƙamemen falon nasu, bata tsaya duban komai ba ta haye saman ta da gudu dan wanka kawai take san yi shine dalilin barin ta asibitin batare da neman kowa ba, a wannan karon kam ta san dole ta haɗa da ruwan zafi dan gasa kanta, sosai taji daɗin ruwan zafin dan ruwa uku tayi sannan ta fito ta kunna shower ɗin ruwan sanyi dan ɗauraye jikin ta kamar yadda ta saba, shirya wa ta shiga yi bayan ta fito daga toilet ɗin tana ture duk wani tunanin abinda ya faru a ƙwaƙwalwar ta dan tana son samun hutu kafin komai, seda ta shirya cikin three quarter da ya ɗan wuce gwiwar ta hakan be sauka kan ƙafar ta ba da riga t-shirt da ta kama ta sosai, kan bed ta faɗa duk da kuwa tana jin yunwa akan ta fi buƙatar bacci kafin komai. Bacci tayi sosai da se kusan sha biyu ta farka, a gigice ta tashi dan yunwar da ta azalzale ta, slippers ɗin ta masu taushi da akayiwa ado,n gashin damisa ta saka ta sauka ƙasa, da ido kawu dake zaune kan sofa ya bita har ta shige kitchen, da kanta ta dafa noodles shaf shaf sedai kallo ɗaya zaka wa plate ɗin kaji ta burge ka, veggies ne a cikin ta a awadace banda niƙaƙƙen naman da ta zuba, iya ƙamshin ta ka zai shaida maka ba ƙaramin daɗi zata yi a baki ba banda kuma yanda tayi plating abincin, kan dining ta zauna ta fara cin abin ta da zafin sa dan yadda take ji bazata iya jira har ta ɗan give ba bayaga haka tafi son cin abinci da ɗan zafi, ruwa ta kora bayan ta gama kana ta ja kujerar baya ta jingina jikin bayan kujerar ta lumshe idanun ta har taji ta koma daidai kafin ta tashi ta nufi hawa saman ta sedai tuni kawu ya dakatar da ita. "Zo nan daughter, tun safe nake jiran ki farka dan muyi magana se kuma naga yanzu kin taso da yunwa shiyasa ban tare ki ba". Ɗan juyowa tayi ta kalli kawu kafin kuma ta dawo cikin falon kamar yadda yace tayi, kan sofar dake opposite ɗin shi ta zauna cikin salon zaman ta na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gyaran murya kawu da takaici ya cika wa ciki yayi kafin ya ɗan haɗe rai irin ba wasan nan "Jiya a ina kika kwana". Kallo ta ƙure kawu dashi kafin ta saki murmushi silently "A club". Harara yake mata a kaikaice kafin yace "Amma ya akayi mutane na basu ganki ba". Surprisingly ta ƙanƙance idanun ta "Mutanen ka, bangane ba, dama ka sa abi bayana ne?". A ɗan daburce kawu ya gyara zama kafin ya ɗan dake "Yes, sure nasa abi min bayanki a ganar min inda zaki dan yawon ki ya fara damuna". "Oh I see, so an dai tabbatar maka da club naje ko?". "Sosai, sedai ba'a faɗa min inda kika kwana ba bayan ƙarfe uku ake rufe club, ke kuma se to nine na safe kika dawo gida". "Na kwana gidan wani customer na ne, da matsala?". Ta faɗa tana ɗage masa hira ɗaya, baki buɗe kawu ya bita da kallo speechlessly dan duk yadda yake tunanin Kisnah ta nuna masa ta zarce nan. Sama ta haye ganin kawu bai da abin cewa kuma, abinda be sani ba shine ta san yasa an bi bayan ta dan she's very sensitive hakan yasa ta lura da motar dake bin bayan ta duk da cewa a ƙware suke komai, ko da wannan incident ɗin be faru ba dama ta shirya plan ɗin da zata musu sedai kawai suji ta a gida. Zama tayi kan gadon ta tana me tunano duk abinda ya faru jiya da dare da har ta ganta a asibiti, sosai komai da komai ke dawowa kan ta har abinda ya faru da Surry ta bisu, bawai Suma tayi ba a lokacin ko bata jin meke faruwa ba, tana jin komai sedai bata jin karfin jikin ta da bazata iya aikata komai ba haka kuma tana ji da ganin komai ne kamar a mafarki, kamar ba gaske ba, kamar a wata duniyar ba wadda take ciki ba. Hawaye ne suka zubo idanun ta tuno yadda Surry tayi ƙoƙarin ceto ta da abinda ya sami Surryn. Da sauri ta miƙe ta ciri wani pink Hill shoe kalar rigar jikin ta tare da scarf ta ɗaure kan ta wanda majority in zata skul ta ke ɗaurawa, wayoyin ta ta zuba cikin pocket kafin ta fara dialing number Meenah tana gangarowa daga step, a ɗan hanzarce ta katse Meenah dake ƙoƙarin fara tambayar yaya take wanda hakan ya zame wa duk ƴan Click ɗin nasu ɗabi'a tambayar ya junan su suka kwana "Meenah Surry na asibiti fa, mu haɗu can yanzun nan, Ado Muhammad manya hospital, ki sanar dasu Leekha". Bata tsaya jin me Meenahn zata ce ba ta katse wayar ta fita da sauri, a compound ta ɗau wata dark Ash motar ta ta fice da sauri hankalin ta a tashe sanin kome ya samu Surryn fa saboda ita ne. "Wannan anyi sheɗaniyar yarinya". "Ƴar iskar yarinya mara mutunci". "Allah ya shirya amma wannan yarinya bata da tarbiyya". Ire-iren waɗannan kalaman da an wanda ya fisu muni Kisnah ke ta samu wajen mutanen dake kan titin dama na gefe, wasu har dasu tsinuwa wasu kuma fatan shiriya, ita kam tuƙin ta take yi cikin son ganin ta isa hospital ɗin da wuri, a haka ta isa Allah yaso ma gate ɗin a buɗe yake dan haka ta shige, parking tayi ta fita da sauri ko amsa gaisuwar da ma'aikatan asibitin ke mata bata yi ba, kun san halin mutane ina suka ga me maiƙo ko da basu sanshi ba balle ita da sunan ta da hoton ta yayi tambari a gari. Ɗakin da aka nuna mata matsayin na Surry ta shiga da sauri, wani irin ƙarnin magani da warin allura yasa ta kai hannu ta toshe hancin ta, da sauri ta juya ta fita zuwa wajen likitan da ya duba su, bayanin tana son a sallame su ta canja wa Surayya asibiti tayi masa, be ja da nisa ba ya yarda ya basu sallama bayan ya kira ƴan sandan da suka kawo su, cikin tsananin jin daɗin ganin ta ƴan sandan suka yarda da sauri dan sun san tun da suka ga Kisnah to fa yau sun warke, aikuwa alkhairi sosai tayi musu suna ta washe baki, cikin ƙankanin lokaci aka canjawa Surayya asibiti zuwa wata tsadaddiyar private hospital aka canja mata, take a ka kai su wani tanƙamemen ɗaki kamar a gidan su, likitoci suka rufu kan ta aka fara bata kulawar data dace, banbancin asibitin kuɗi dana gwamnati kenan, *KULAWA*! Ƙarar wayar ta yasa ta cire tagumin da tayi tana duban screen ɗin, ganin sunan Meenah yasa tayi picking tare da sawa a speaker.......................✍️ ©️ Ouummey 📚✍️. *☑️Ote, comment and share fidabilillah*. Ouummey 10 (8/3/2022 3:52 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣0️⃣ _____________________📖 "Hasbunallah wani'imal wakeel". Ya faɗa yana dafe kansa, shiru shagon yayi cikin jimamin tsaka me wuyar da ta same su lokaci ɗaya daga sama, dukkan su tagumi ne suka yi da hannu bibbiyu barin ma Alh Musa me shagon. A hankali Alh Musa ya ɗan motsa kafin ya fara magana cikin muryar dake bayyana ainahin damuwar da yake ciki "Wannan abu da ya faru damu rubutacciyar ƙaddara ce da bawa baze iya guje mata ba, na daɗe da sanin muna da magauta da mahassada cikin kasuwar nan kuma abokan sana'ar mu ne sedai ban ɗauka abin ze iya kaiwa har haka ba". Numfashi yaja ya sauke a ɗame kafin ya cigaba cikin ƙarfin hali "Ina me baku haƙuri domin nima ba haka naso ba sedai ba yadda muka iya da hukuncin Allah, ina me baƙin cikin sanar daku na sallame ku gaba ɗaya a yau, Allah ya baku wasu hanyoyin samu ya yiwa rayuwar ku albarka ya saka muku da alkhairi bisa zaman amanar da kuka yi dani da junan ku, duk wanda na ɓatawa a zaman mu ya yafe min dan ɗan adam ajizi ne, nikam baku taɓa min komai ba koma kun min na yafe muku duniya da lahira". Shiru duk sukayi wasu na sharar hawaye, ko a shekaran jiya basu taɓa kawo tunanin haka na iya faruwa dasu ba, sedai in akace kana da magauta da mahassada to fa se kariyar Allah kawai. Abin da ya faru kuwa shine ragowar maƙota da wasu daga cikin abokan kasuwancin Alh Musa ne suka fara fito masa da hassadar su ƙarara dan sun daɗe suna ɓoye ta sedai zuwan Saraki yasa suka kasa riƙe kansu ganin yadda al'amura da kasuwancin Alh Musan suka ƙara bunƙasa, yasan suna masa hassada sedai be ɗauka zasu iya cutar dashi har haka ba, akwai kayan da yayi order Wanda in suka zo ana sa ran ba ƙaramin roba za'a samu ba shine suka yi masa shune custom suka kama kayan wanda bana ƙananan kuɗi bane, kusan dukkan jarin shi ya tattare dan babbar order ce se Gashi custom sun kama kayan a shekaran jiya da daddare, hankalin da ya tashi sedai bisa tunatar war me ɗakin sa yasa ya barwa Allah komai ya cigaba da addu'a dan ko yaran da be sanar dasu ba, a jiya ne kuma abokan kasuwancin nasa dake son ganin bayan shi suka tada ɓallin son ya biya su bashin da suke binsa na kayan da ya karɓa kamar yadda ƴan kasuwa ke yi in sun karɓi Kaya su biya rabi daga baya su cika, be ja da nisa ba ya haɗa ragowar kuɗin hannun da ya basu tare da sauran kayan da ba'a siyar ba, hakan yasa yau shagon ya tashi kusan ba komai a ciki se tsirarun takalman da basu wuce a irga ba, wannan shine dalilin sallamar su Saraki da yayi tun da ba kaya a shagon yana son kwashe ragowar kayan sa ya saki rumfar dan dama suna watan biyan kuɗin hayar sabuwar shekara da za'a shiga ne. A sanyaye Saraki ya ɗago kansa dake sunkuya ya fara tausar megidan nasu da kawo masa hadisai da ayoyin da suka tabbatar da nasara ga duk wanda yayi haƙuri yayi tawakkali ya kuma Ubangiji yadda ya kama ta, wannan ne karo na farko ga duk wanda ke shagon da yaji Saraki yayi doguwar maganar da ta wuce sentence biyu zuwa uku, cike da kewa da tausayi Alh Musa sukai sallama bayan sun taya shi kwashe ragowar kayan sa zuwa gidan sa kowa ya nufi hanyar da ya fito. Ya daɗe zaune a ɗaki yana tunanin da be san inda ze ɓulle masa ba ba'a kan komai ba se kan sana'ar da ze kama nan gaba se dai be san ta Ina ze Fara ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan sunan Idris ya faɗo ransa, tabbas ya zama dole ya sanar dashi abinda ake ciki tunda shine yai masa hanyar zuwa shagon. Without any hesitation yai dialing number Idris Wanda bugu daya ya ɗauka da sallama Muryar sa cike da farin cikin ganin yau Saraki ya kira shi duk da dama yakan kirashi sa'i da lokaci. Gaisawa suka yi kafin a nutse Saraki yai masa bayanin halin da ake ciki zuwa zaman da yake ba abin yi, sosai Idris ya jinanta faruwar hakan ya kuma tabbatar masa da zeje yayi wa Alh Musan jaje kafin a ƙarshe ya ƙarƙare da insha Allah cikin satin nan za'a samowa Sarakin wani aikin. Ajiye wayar Idris yayi a gefen sa kafin ya sanar da yayan sa da suke tattauna batun gyaran motar shi (drivern da ya tuƙo motar da saraki ya hau daga Giwa zuwa Manya) karayar arziƙin da ta sami tsohon maigidan sa Alh Musa, sosai yayan sa shima ya jimanta abin tare da Allah wadai da mahassada kafin ya dubi ƙanin nasa "Maganar aikin abokin ka ina ganin akwai aiki a hannu in ze iya". Da mamaki Idris ya dubi yayan sa "Farawa da iyawa, amma naji daɗi gaskiya, yadda aiki yake wahala yanzu amma har ya samu, gaskiya Ahmad me Sa'a ne". "Bawai Sa'a ba Idris, aikin nan ya daɗe a ƙasa sedai duk wanda aka samarwa da yaji wadda zewa aikin da yanayin tsarin aikin se yace baze yi ba, kasan yanzu jama'ar garin nan sun fi ganewa kasuwanci kan aikin albashi". "Sosai ma kuwa, nikaina bana jin zan iya aikin albashi yaya, amma me yasa ake ƙin karɓa, I mean ya tsarin aikin yake". Numfashi yayan Idris ya saki "Tuƙin mota ne, wata Hajiya ce ke neman driver da ze ding tuƙata duk inda zata, matsalar aikin shine tana fitar dare kuma duk lokacin da zata fitan ze tashi ya Kaita, a taƙaice dai duk min dare, safiya, sanyi, rana ko damina in ta buƙaci zuwa waje shine ze kaita". "Wannan ai ba matsala bane yaya, ai dama amfanin ɗaukar driver ɗin kenan, Ni banga aibun aikin ba". "Aibun shine fitar dare, tana fa ita fita ɗayan dare, biyu, uku, huɗu ko ma dai karfe nawa na dare". Shiru Idris yayi cikin jinjina lamarin aikin dan gaskiya fitar daren matsala ce, daga yanayin aikin ya gane ba hutu ko kaɗan, ka wuni kana tuƙi sannan ka kwana kanayi gaskiya da matsala. "Da matsala kam dan matsala yaya, amma me ze Hana in Masa Magana, in ya fara yaga baze iya ba se a neman masa wani dan na fahimci ba ya san zama haka kawai". "In har ya yadda ni me farin ciki da haka ne dan na sama wa abokina mafita, kasan Inusa aka ɗorawa nauyin samo driver kasancewar da yayi aiki a gidan kuma sun yadda da amanar da kafin daga baya ya ajiye ya buɗe shago a nan kasuwa, yanzu haka kullum se yayi min batun aikin dan baya son suga kamar yana sane yaƙi sama musu bayan duk halaccin da sukai masa". "Ai bari ma kaga in kirashi yanzun nan in sanar dashi, gwara mu sani in ze iya ko kuwa ba se ansa rai ya kasa ba". "Yauwa maza kirashi". Cikin sauri kuwa Idris ya kira Saraki da a ringing ɗin farko ya ɗaga da sallama, a taƙaice Idris yayi masa bayanin aikin da kuma yadda tsarin aikin yake be ɓoye masa komai ba har batun fitar daren kafin ya saura dan jin me Sarakin ze ce, shiru yayi kamar baze ce komai ba kafin ya amsa da ze yi insha Allah, cikin tsananin farin ciki sukai sallama da Idris ya ajiye wayar. Lumshe ido Saraki yayi cikin daɗa jujjuya yanayin aikin a ransa, katse tunanin yayi yana miƙewa ya wuce toilet ɗin sa dake wanke fes yana ƙyalli, alwala yayi ya fito ya ɗora baƙar jallabiya a kan boxers da singlet ɗin jikin sa ya tada kabbara kan sallayar shi. Raka biyu yayi wadda a cikin su ya sauke Suratul baƙara kafin cikin sujjada ya nemi zaɓin Allah kan aikin da aka kawo masa, tasbih ya ɗora ko da ya idar sannan ya buɗe Alkur'anin sa ya ɗora karatun sa da yake sauka duk sati, seda yakai adadin surorin da yake yi kullum kafin yayi addu'a ya ajiye ya kwanta. Da safe ko da ya tashi wasai ya jishi tare da sake jin kwanciyar hankali kan aikin nasa, a safiyar Idris take ya tafi dashi wajen abokin yayan sa Inusa wanda anan za'a sanar dashi adadin albashin sa tare da raka shi gidan da zeyi aikin. ********* Muryar Meenah ke fita daga speaker wayar inda ta shaidawa Kisnah sunje Ado Muhammad Manya hospital ɗin amma basu gan su ba, ɗan dafe kan ta dake mata ciwo kaɗan kaɗan tayi sannan ta bata amsa "Am sorry, na karɓi sallama ne na kawo ta nan get well, ku ƙaraso nan". Ok kawai Meenah tace ta kashe wayar, itama kifa kai tayi kan tata wayar cikin tunanin da ya kasa barin kanta na waye yai drugging ɗin ta jiyan, Surayya ce dama zata iya shiga zargi dan itace bata wajen lokacin data dawo sedai yadda tayi ƙoƙarin kuɓutar da ita dole ze shaidawa me zargin ba ita bace, to waye??? Wannan shine amsar da ta gagara samu gashi bazata iya barin asibitin ta tafi station ba a halin da Surry ke ciki. Cikin wannan tunanin su Meenah suka shigo ita da Leekha da Meedah, cikin nasu tashin hankalin suma suka ƙarasa gaban gadon da Surry ke kwance suna jajantawa, Leekha da Meenah har da hawayen su, Meedah da tafi su karfin zuciya ce kawai bata koka ba sedai itama nata idon yayi jajir, haka suke basa san ko yaya cuta ta sami ɗaya daga cikin su duk da sukan sami saɓani ko jin haushin juna wani lokutan. Kan sofar da Kisnah take suka zazzauna suna tanbayar garin yaya hakan ta faru da Surayya, cikin damuwa Kisnah ta sanar da su duk abinda ya faru, ko kafin ta gama faɗa musu tuni Meenah ta miƙe rai ɓace ta nufi fita daga ɗakin, da sauri Meedah ta bi bayan ta yayinda daga Leekha har Kisnah ba wanda ya dakatar dasu dan bama tsayawar za suyi ba, baki Leekha ta ringa ba Kisnah ganin yadda duk ta damu, se lokacin tunanin sanar da iyayen Surayya yazo musu, Surayya marainiya ce da take hannun yayanta namiji wanda su biyu kaɗai iyayen su suka haifa, yayanta ba mazauni bane haka kuma matar sa bata da mutunci Sam ba ta kuma shiga harkar Surayya hakan yasa ko zata kwanan nawa ba zata neme ta ba se in ita taga dama ta koma, sauƙin abin duk iskancin su basa kwanan waje, duk nisan dare se sun koma gida sedai in sun gaji da zaman gidan sun kama hotel dan hutawa shine fa se sanda suka gama hutun suka koma gida. Cikin sanyin da jikin ta yake take scrolling through contact ɗin ta har ta samu sunan Auntyn Surayya da tayi saving da *matar yaya* kasancewar suna girmama Junan su da ɗaukar iyayen junan su matsayin nasu, ta sami number ɗin ne lokacin da Surry ta kwana tare da ita aka kuma yi rashin Sa'a yayan Surayyan ya dawo ranar shine fa cikin tashin hankalin tsoron faɗan da yayan ce mata Aunty ta kira number Kisnah dan ta yi ta kiran ta Surayya a kashe. Kusan five miscall tayi mata kafin a kan na bakwai ɗin ta ɗauka cike da izza da yanayi na an takura mata take tambayar waye, batare da kula wulaƙancin Auntyn ba dan sarari tasan Kisnahn ce kawai salon wulaƙanci ne ta soma nata bayanin halin da Surayyan take ciki. Sosai hankalin Auntyn ya tashi dan wasan every blame ze koma kan ta ne in yayan Surayya yaji abinda ya faru, hakan yasa tuni ta manta da batun wulaƙanci ta roƙi Kisnah kar ta sanar da yaya gata nan zuwa, kashe wayar kawai Kisnah tayi ta ajiye ta maida idanun ta ta lumshe kamar dai yadda take a ɗazu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sefa Auntyn ta ƙaraso, ba wanda ya kula ta a cikin su ta ƙarasa gaban gadon da Surayyan ke kwance, zare idanu tayi ganin har da ɗinki, cikin tashin hankali take tambayar su garin yaya hakan ya faru da ita, Leekha ce ta bata labarin komai kamar yadda Kisnah ta sanar dasu dan ko buɗe idanun ta ita Kisnah bata yi ba bare ta bawa Auntyn amsa, zage zage ta fara a ɗakin tana blaming Kisnah kan ita ke koyawa Surayya lalacewa Gashi nan ta sanadin ta daraja mata mutuwa, banza tayi wa Auntyn kamar bata jin ta har se da taji ta fara taɓo iyayen ta kafin ta buɗe idanun ta da suka canja kala daga attractive golden brown oily and sexy eyes zuwa brownish color so scary ga me kallon su, tsit Aunty tayi da bakin ta ganin mugun kallon da Kisnahn take binta dashi, duk iskancin ta tana shakkar yarinyar dan tasan ta fita iya shege da sanin malamar rashin mutunci shiyasa tana iya taka su Meedah amma bata taɓa kwatanta yi wa Kisnah ba se yau, yatsar ta manuniya ta ɗaga tana nunawa Aunty hanyar fita wato ta fice ta basu waje, jim tayi kamar bazata fita ba kafin taka uban tsaki tayi waje fuuuuu kamar zata tashi sama. Haka suka ƙarasa wuni wajen Surayya har su Hameedah suka dawo, anan suke shaidawa Kisnah wanda yayi musu wannan aika aikan "Kin tuna wani gaye da i think two months ago yazo wai yana son ki?? Yamutsa fuska Kisnah tayi cikin son tuno Wanda suke magana akai amma ta kasa, ko banza masu cewa suna son nata ai ba iya ƙirga su zata yi ba dan haka ta girgiza wa Meenah kai "Wanda fa kika mara a club da ya rungume ki kina rawa". Cikin sauri ta gyaɗa kai dan shi kaɗai ya taɓa mata haka kaf shekaru uku da tayi tana zuwa hideaway club "To shine ashe ya sa miki drug acikin kunun ayar da kika ake da zaki rawa, he take advantage of us da bama hayyacin mu ya saka ita kuma Surayya dama kina tashi itama ta bi saurayin ta". Shiru Kisnah tayi cikin tuƙuƙin ɓacin ran abinda yaso aikata mata jiya, wato dan ta mareshi shine bari ya yaga mata mutunci ko, aikuwa zata yi maganin sa. "Yanzu me kuka ce ayi masa a station?". Leekha ta tambaya Meedah ta bata amsa da "Mun ce kar a sake a bada bail ɗin shi ko uban waye yazo". Jijjiga kai Kisnah tayi alamar hakan yayi kafin suka tarkata kowacce ta nufi gidan su dan ba'a kwana a asibitin dan suna da masu jinyar patients. Ko da tayi parking ta daɗe Bata fito ba daga motar har se da taji kan ta dake ciwo ya ɗan tafi, tasan ba komai bane illa effect ɗin ƙwayar da yasa mata jiya wadda ita ke ta wahalar da ita dan ba ta taɓa sha ba, a hankali take takawa ba kamar yadda ta saba kullum ba sedai duk da haka cat walk ɗin nan dai take yi wanda haka asalin tafiyar ta yake. Da sauri me bawa flowers ruws ya ƙarasa gaban ta ya ɗan durƙusa hakan yasa ta dakata da tafiyar da take yi ta duba shi "Dama Inusa yace in sanar dake sun zo ɗazu ba kya nan, in ba damuwa zasu dawo gobe shi da sabon driver ɗin da aka samo". Nodding kanta tayi kafin cikin rashin son magana saboda ciwon kanta tace "Zan jira su by 9:30am". Da hanzari ya amsa da ze faɗa musu insha Allah, bata ƙara jiran me zarce ba tayi gaba, a falo ta tadda kawu wanda wunin yau taga ya tsiro zaman falon su maimakon nasa da yake zama da, bata ko ce masa ƙala ba ta haura saman ta ta buɗe ta shige, bedroom ta wuce ta faɗa kan gado tana sakin nishin azaba kafin da ƙyar ta zare takalman ƙafar ta ta haye gaba ɗaya ta ja blanket saboda ɗan sanyi sanyin da taji yana shigar ta..........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. *☑️Ote, comment and share fidabilillah* Ouummey 11 (8/4/2022 4:14 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣1️⃣ _______________________📖 Bargo ta tashi ta ɗauko da ƙyar ta ƙara kan blanket ɗin ta shige ciki. Ranar ko kayan jikin ta bata iya canjawa zuwa na bacci ba ta kwanta dana jikin ta. Sosai tayi bacci saboda ɗumin da ke ratsa jikin ta wanda bata farka ba se to nine, wanka ta shiga tayi ta saka Black straight English gown me ɗan gajeren hannu da ta tsaya iya ƙaurin ta, yau bata kama gashin da ribbon ko sa masa band ba ta sake shi a bayan ta bayan ta taje shi ta masa style me kyau. Turarurrukan ta ta feffesa kafin ta jawo black designer wedge half cover shoe ta saka ta ɗebi wayoyin ta da system ɗin ta da key ta sauka falon ƙasa, kan two sitter sofa ta zauna tana zube wayoyin ta a gefen ta sannan ta jawo Centre table ta ɗora ƙafafun ta kana ta ɗora system ɗin kan laps ɗin ta ta shiga operating hankali kwance. Maigado dake zaune kan dining ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba dan Allah ya sani ta tsani Kisnah beyond expectation, ba ƙaramin ɓacin rai da takaici take ji ba inta dubi gidan nan ta kuma tuno wai mailakin ta ne, yanzu haka da take zaune tana dai cin abincin ne dan bazata iya zama da yunwa ba amma gaba ɗaya tunanin ta yana kan yadda zata yi Mommy ta dawo gidan ne dan su fara planning yadda zasu ɗaiɗaita rayuwar Kisnahn da gaggawa, ga shima wancan banzan yaya Awwaf ɗin ya ɗau ƙafa ya bar gari wai birthday ɗin aboki. Tsaki tayi ta dangwarar da cup ɗin hannun ta ta wuce fuuuuu ɗakin ta, sarai Kisnah ta jita sedai ko kallon ta bata yi ba dan ba itace a gaban ta ba, kacokan hankalin ta yana kan kuɗaɗen da spy ɗin ta da ta ajiye a Companyn gine ginen ta me suna K&C (Kisnah constructions) ya turo mata an nema an rasa ba kuma batun wani bincike akai. Kusan awa ɗaya tana latse latse a laptop ɗin kafin wayar ta da take amsa kiran ma'aikatan gidan ta hau ringing, bata ji kiran ba har se ana biyu dan gaba ɗaya hankalin ta ya tafi kan aikin da take yi, picking tayi dan ganin 0045 wato number me bawa flowers ruwa kasancewar kowane ma'aikaci yana da number base on ɓangaren da yake aiki, haka kuma an bashi phone and sim card Wanda in ya kira wannan number ce zata yi displaying, karawa tayi a kunnen ta tana sauraren bayanin da yake mata kafin ta amsa "Su ƙaraso main falo shi da Inusan kai kuma ka koma bakin aikin ka". Ajiye wayar tayi ta sake maida hankali kan system ɗin, tsurawa screen ɗin ido tayi ganin account details ɗin da kuɗin suka shiga bayan sun fita daga account ɗin Company, sosai ranta ya ɓaci dan wannan ne karo na kusan biyar da aka samu irin haka kuma duk ta bi diddigi wannan account ɗin dai take gani dan haka wannan karon bazata saurara ba se ta gano ainahin me shi. Sallamar da suka yi kafin shigowa yasa ta ɗan ɗago ta kalli ƙofar kafin ta ɗauke idon ta maida screen ɗin, bata amsa sallamar ba dan hakan ba ya cikin tsarin ta, turo ƙofa Inusa yayi ya shigo yayinda Saraki ke bin sa a baya, ƙasa kan carpet Inusa ya nema ya zauna yayinda Saraki yake tsaye dan baya jin ze iya zama ƙasa wani na sama wanda ba mahaifan sa ba (Sarautar ta motsa😜😂). Seda ta ɗan ɗauki lokaci bayan tayi saving komai sannan ta ɗago fuskar ta a sake ta dube su, da hanzari Inusa ya fara miƙa gaisuwa ta amsa fuskar ta da walwala har tana tambayar sa ya family ɗin shi da harkokin sa, amsawa yayi cikin jin daɗin yadda bata wulaƙanta su duk da sun kasance a ƙasan ta kafin ya nuna mata Saraki da bayanin shine sabon drive ɗin da aka samo mata. Kallon ta ta maida inda Sarakin ke tsaye hannun sa cikin aljihu, idanu ta fara bin sa tun daga ƙasa kan kyakkyawar tsaftatacciyar ƙafar sa dake nan sumul kamar baya taka ta zuwa kayan jikin sa har ta kai fuskar sa sedai kallo ɗaya tayi wa fuskar tasa ta ɗauke kanta da sauri saboda wani irin kwarjini da cika ido da taga yayi mata. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye idanun ta na kan Inusa ta furta "Have a seat please, za muyi magana". Bece komai ba ya nemi one sitter sofa ya zauna yana iya ƙoƙarin sa na ganin be yi zaman da ya saba ba duk yakai zaune kan kujera wato harɗe ƙafafu kan juna, irin zaman da yayi kawai seda ya sake sata jin nauyi da ɗan shakka dan zama ne irin na cikakkun jinin sarautar da suka gawurta da isa, izza da taƙama dan ya buɗe gaba ɗaya ya cika kujerar, wannan shine karo na farko da zata ɗauki drive batare da ta ƙare masa kallon tabbatar da tsaftar sa ba kamar yadda ta saba, shiyasa tunda bazata iya duban sa direct ba take satar kallon sa ta gefen ido. Ɗan gyaran murya tayi kafin ta juyo gare shi sedai idanun ta na kan Tvn bayan sa ne dan bata jin zata iya kallon fuskar sa dan a hakama ji take yi gaba ɗaya ya cika falon da girman sa. "Kamar yadda nasan Inusa ya riga da yayi maka bayani, driving ɗina zaka ringa yi to every where I headed to, ban da haka babu wani aiki kuma da zaka dinga yi". Gyaɗa kansa yayi alamar ya fahimta hakan yasa ta cigaba da magana "Zan dinga biyanka 300k every month, zaka kuma zauna a gidan nan ne saboda ina fitar dare ko ince ko yaushe ma zan iya fita so baze yuwu se na tsaya jiran zuwan ka kafin na fita ba, akwai abincin da ake bawa ma'aikata wanda se in sun ga dama sannan za su siya in Wanda aka dafa be musu ba, fatan zaka iya aiki tare da ni". Shiru yayi kamar baze ce komai ba saboda batun zaman gidan da ta kawo sedai kuma be san yaushe ze sami wani aikin ba in ya bar wannan, tunanin hakan yasa shi nodding kansa kafin cikin daddaɗar Muryar sa ya fara magana karon farko tun shigowar sa gidan "In har aikin baze dinga shiga lokutan ibada ta ba I think ba matsala na karɓa". Jinjina kanta tayi cikin tsananin mamaki a ranta, me yake faruwa ne, its as if yana bata condition ne zata ce ko sharaɗi ne oho, sedai haka kawai taji zuciyar ta ta nutsu da yanayin shi na nutsuwa so take ta yarda da sharaɗin nasa "Is okay, in har wannan ne ba matsala, sedai fa aikin ka ze Fara daga yau ne dan yanzu haka ina buƙatar fita". Wannan karon Inusa ne ya bata amsa "Hakan ba matsala bane Hajiya, ai ze iya farawa yau ɗin ma". Miƙewa tayi tana faɗin "Toh shikenan, ku ɗan jira ni". Step ta haye zuwa falon bayan ta ɗau system ɗin ta, zama tayi kan tsadaddun royal chairs da suka ƙawata ɗakin tana sauke numfashi, in her whole life zata iya cewa shine mutum na farko da take jin girma da nauyin sa sosai tun bayan iyayen ta da suka rasu, bata san me yasa hakan ba ko kuwa dan yadda nutsuwa ta bayyana a jikin sa da kuma Muryar sa ne ?, Ko kuwa dan tsananin kwarjinin sa ne bata sani ba. Nannauyan numfashi ta sauke kafin ta maida system ɗin ma'ajiyar ta ta nufi box ɗin da take ajiye keys ɗin motocin ta ta ɗauko shi gaba ɗaya, kana ta ɗauki ƴar mini purse ɗin ta baƙa ta fito bayan ta ɗebo kuɗaɗe masu yawa a cikin wani safe dake gefen wardrobe ɗin ta ta zuba. Wannan karon da key ta rufe ɗakin kafin ta sauko ƙasa, lumshe idanun sa yayi dan ba ƙaramin hawa masa kai ƙamshin ta ya fara ba, duk da ya kasance me son ƙamshi amma be fiya son turare me ƙarfi ba. Gaban kujerar da yake zaune ta tsaya tare da miƙa masa box ɗin, kyakkyawan hannun sa fari tas da shi dake cike da gargasa me ban sha'awa da ta kwanta luf luf ya miƙo dan karɓa, miƙa masa tayi tana sake jinjina tsaftar sa dan fararen aikafun sa dake a yanke very low bako alamun wani abu wai shi datti cikin su. Komawa tayi ta zauna inda ta tashi ta buɗe purse ɗin ta ɗebo kuɗaɗe masu ɗan kauri da bata tsaya irgawa ba ta miƙa wa Inusa "Ga wannan se kayi kuɗin mota, Nagode sosai Inusa, a gaida min da Ramatu dan Allah". "Insha Allah zata ji, nasan da tasan wajen ki zan zo da se tace zata bini". (Ramatu matar sa ce, lokacin da yana aiki a gidan suna zaune ne a biya quarters ita kuma tana girki). Ɗan dariya tayi tana faɗin "Ai mutuniya tace sosai, nayi missing barkwan cin ta". Da haka sukai sallama Inusa ya tashi ya fita Saraki ma ya miƙa ya bi bayan sa, a gefe guda daga cikin compound suka ɗan tsaya, Inusa ya dube shi cikin mutuntaka "Insha Allah zaka ji daɗin aiki da ita dan sam bata da girman kai haka tana da sauƙi da daɗin mu'amala, bata da wulaƙanci sedai in akayi mata to bata haƙura se ta rama, gwargwado tana da alkhairi dan yarinya ce ta gari sedai dake rayuwa ɗan Adam baya taɓa cika cif to itama tana da nata halayyar da basu da kyaun ji balle gani, se ka kula sosai bata san yawan tambaya haka kuma bata san aringa mata shisshigi cikin al'amuran ta, in har zaka tsaya iya matsayin aikin da ta ajiye ka to na tabbatar maka se kafi kowa jin daɗin zama da ita, nasan ka baka da matsala tunda Idris ya shaida min haka sedai tunatarwa tana da daɗi, ka zama me amana dan Allah da kuma ɗauke kai ga duk abinda be shafe ka ba". Ɗan murmusawa Saraki yayi da ba kowa ze gane yayi hakan ba jin yau wai shi ake faɗawa ya zama me amana, sedai ita rayuwa dama haka take kuma beji ko ɗiso na haushin abinda Inusan ya faɗa ba tun da ba sanin shi yayi ba balle ya san halayyar sa "Insha Allah zan kiyaye duka, Nagode sosai". Iya abinda ya iya furtawa kenan hakan yasa Inusa yi masa sallama ya wuce, cikin takun sa da kallo ɗaya zaka masa ka ɗauke shi as mutum me izza da taƙama ya koma hanyar falon da suka baro sedai be ƙarasa ba ta fito riƙe da purse ɗin ta waya kare a kunnen ta tana magana, da hannu tayi masa alamar ya biyo ta kafin tayi gaba, tsananin mamaki ne ya kamashi dan fa ɗazu be kalle ta balle yasan a ya take, shiyasa yanzu da ya ganta haka sanye da rigar da bata saukan mata ba ta kuma kamata sosai haka kan ta a buɗe zata fita se mamaki yake neman daskarar dashi. Ture komai tayi gefe ya bi bayanta ganin har tayi gaba tuni, wajen parking motocin ta suka ƙarasa tayi masa pointing wata black designer car da taji wanki take ta ƙalla da ɗaukar ido ( Allah ya sani ina son baƙar mota a rayuwata😻 ). Wajen motar ya ƙarasa ya saka key ya buɗe kafin ya matsa ya bata waje, ƙarasowa tayi cikin takun ta na ɗaukar hankali yayinda ya ke kallon ta a kaikaice ya ga inda zata shiga gaba ko baya dan fa turaren ta ya fara takura masa yana kuma son fara karantar halayen ta da ɗazu Inusa ya gama faɗa masa, bisa ga mamakin sa gaba ta zauna owner's corner ta rufe murfin dole ya ƙarasa ya shiga driver's seat ya zauna, tada motar yayi bayan ya gama karanto addu'a kamar yadda ya saba tun da can duk da be fiya tuƙa kansa ba tun dawowarsa Giwa. Fita yayi da motar bayan an buɗe gate ɗin ya hau kan titin kafin ya fara tuƙi kamar yadda ya saba cikin nutsuwa ba garaje, ba gudu sosai yake yi ba kuma bawai salo salo yake tafiya ba, yana tsaka tsaki ne, Kisnah da tun da ta shiga motar ta maƙala ɗan gado wato earpiece ɗin ta ta maida kanta bayan kujerar ta kwanta tare da lumshe ido bakin ta na motsi kaɗan kaɗan alamun bin waƙar take yi so bata ji tambayar da yayi mata har uku ba na inda zasu, be ƙara tambaya ba ya sauka gefen titi ya faka motar ya jingina jikin makarin kujerar ya lumshe idanun sa kamar me bacci. Jin shiru kamar ba'a tafiya yasa Hajiya Kisnah buɗe ido, sake ware manyan golden cat eyes ɗin ta tayi tana bin titin da kallo kafin ta juyo ta kalli yadda Sarakin ya baje cikin kujera, mamaki ne ya kamata to me yake nufi da tsayawa da yayi gefen titi ya wani rufe ido, badai bacci yake mata a mota ba ko, tunanin haka yasa ta zare earpiece ɗin ta ajiye kan cinyar ta ta saka hannu ta bubbuga steering ɗin, a hankali ya buɗe idanun sa ya zuba kanta wanda yasa ta janye nata da sauri daga kan fuskar sa ta koma wajen ta ta zauna sosai "Badai bacci kake min ba ko, meye ma'anar tsayawa gefen titi da kayi bayan na faɗa maka ina sauri ne". "Ina zamu je?". Ya faɗa without giving attention kan tambayar da tayi masa ba, ranta fa ya soma ɓaci dan ita bata son rainin hankali ko kaɗan, in be san wajen da zasu ba shine kuma ba ze tambaya ba se kawai ya wani tsayar da ita a titi dan fa Kisnah akwai saurin fusata sedai tayi ƙoƙarin yi masa uzurin Wannan shine karon farko na aikin sa tare da ita bari ta masa uzuri, "Ado Muhammad Manya hospital". Ta faɗa tana maida earpiece ɗin ta sedai wannan karon idanun ta na kan titin ne, cikin zaman kusan wata da yayi a garin ya ɗan sassan gurare dan haka tuni ya ɗau titin da ze kaisu can ɗin, sun kusa isa Asibitin ta bashi umarnin tsayawa gaban wani ƙaton shopping mall dan tana son yiwa Surry siyayya, bakin mall ɗin ya tsaya ta fita, ganin ba shida niyyar fitowa yasa ta ƙarasa side ɗin da yake tare da bubbuga glass ɗin windown, ɗagowa yayi ya kalle ta ɗan tinted glasses ne a motar, ganin itace yasa ya buɗe ya fito hakan yasa tayi gaba tana faɗa masa "Follow me"..............................✍️. Kai SARAKI kafa shiga hankalin ka, haba Ni kaina na fara gajiyawa da halinka balle kuma Aunty na Kisnah, zamu fa koreka fa tam😡😡 ©️ Ouummey 📚✍️. *☑️Ote, comment and share fidabilillah.* Ouummey 12 (8/4/2022 4:15 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣2️⃣ _______________________📖 Gudu take sosai duk da ba haka ta saba tuƙi ba dan tana san isa da wuri, a yanzu bata da burin da ya wuce ta ganta gaban Mommy dan su zata, zafin da zuciyar ta take mata a lokacin ba kaɗan bane. Gaban wani madaidaicin gida ta tsaye tare da yin horn, da sauri me gadin ya buɗe mata mota dan a kwanan nan ya gane ta saboda Wannan shine zuwan ta gidan na uku. Parking tayi ta fito hannun ta riƙe da ledar da tayi wa Mommyn shopping kamar yadda ta turo mata text ɗin abubuwan da take buƙata, bakin madaidaicin falon ta tsaya tare da murɗa handle ɗin ta shiga. Muguwar harara wata kakkaurar babbar mace ta maka mata tana jan tsaki "Yanzu kuma me kika zo yi, Ni kam na shiga uku da wannan takurar, ita uwar ki ta kasa zama gidan ubanki saboda baƙin hali ta zo nan ta tare min kema kuma kin takura min da zirga zirga kamar me neman gafara, to wallahi baze yiwu ba, ko ki ɗauke kafar ki daga gidana ko na tarkata uwar ki na kora ku gaba ɗaya". Zuba mata jajayen idon ta Megado tayi cikin tsananin ɓacin rai da takaici yadda ƙanwar babar ta ke musu cin kashin da ta ga dama dan kawai Mommy na zaune gidan ta, baki ta buɗe zata maida mata martani sedai tuni Mommy da ta fito daga ɗakin yara inda take kwana ta rufe mata baki da hannun ta kafin ta ja hannun Megadon zuwa ɗakin da ta fito. Harara Aunty ta bi bayansu da ita tana sakin ƙananun maganganu sedai ko kallon ta Mommy batayi ba ta shige da Megado dan in tace zata tanka yanzun nan ƙanwar tata me Huna hasiya zata nemi yi mata tijara. Fusge bakin ta Megado tayi bayan sun zauna kan wata three sitter ƙwalli ɗaya dake ɗakin se katifun yaran Aunty Hasiyar, Ido ta zubawa Mommy ganin yadda cikin kwana uku kawai ta fara yin baƙi ga wata ƴar rama da tayi again dan mugunta kawu yayi mata ya faki idon ta ya kwashe ATM cards ɗin ta gashi ƴan kuɗin da ke hannun ta lokacin dubu da biyar ne kawai, nan gidan Aunty Hasiya kuwa ba wani jin daɗi ake ciki ba compared to gidan da ta baro, ba AC se fanka, ba ruwan roba se pure water, ba different dishes se ɗaya da matar gidan taga damar dafawa gashi tun da tazo a wannan three sitter ɗin take kwana dan Aunty tace bata da spare mattress Kuma ragowar na ƴaƴan ta ne sedai tai manage da kujerar. Katse mata tunani Mommy tayi da dafa ta "Yanzu Megado ba zaki sa ubanki yace na dawo ba, kina fa kallon rayuwar da nake ciki gidan wannan shegiyar yarinyar". "Wallahi Mommy ya ƙi ko saurara ta amma abinda nake gani kawai me ze hana ki tattara mu koma, ai ba dole se ya san kin dawo ba ko?". Zaro ido Mommy tayi "Ashe kin manta tijarar ubanki, kaɗan daga aikin sa ma ya iya sakina kan hakan, Ni a ganina kawai zan kira ƴar iskar yarinyar can in bata haƙuri a wuce wajen, ragowar shirin mu kuwa se mu yi shi ta ƙarƙashin ƙasa ko". "Wallahi sake raina mu zata yi Mommy, adai nemo wata shawarar ba wannan ba". "Dole dai ita za'a yi Megado dan fa kin san in har ba ita tace ya dawo dani ba wannan uban naki da baƙin halin sa ze iya bari inyi wata ɗaya ko biyu a gida, ke har fiye ma wallahi". "Ai sam Daddy be yi ba wallahi, Ni ban san me ya kaiki ma auren shi ba tun farko, shi abu ba kuɗi ba, ba ilimi ba, ba wani kuma kyau ba se shegen tsayi kamar me, yanzu dai jini yadda ya cuceni ya gada min tsayi kamar ba mace ba". "Hmm Bari kawai, Ni kaina ban san me yaja ni ba a lokacin, kin san dai ƙaddara amma yadda nake da kyau na da diri a ƙuruciya ai be kamata na ƙare a wajen shi ba, yanzu dai ba wannan maganar ba, bari kiga in kira waccan sheɗaniyar dan in so samu ne in koma gidan nan yau dan wallahi na wahala matuƙa". Mommy ta ƙare maganar tana dialing number Kisnah kana ta cigaba da faɗin "Wai hatta caji fa a gidan nan bani da damar yi se ace in bada caja shiyasa yanzu haka 20% ne kawai dani". "Ai wallahi Aunty Hasiya se ta san ba tada mutunci, banda arziƙin kina gidan ta ita har ta isa ta yi min ko da kallon banza ne balle zagi". Da sauri Mommy ta nuna wa Megado tayi shiru ta hanyar sa hannun ta a bakin Megadon jin wayar na ringing. ************** Cikin mall ɗin suka shiga inda Kisnah ta shiga lodar kaya kamar ba da kuɗi za'a biya ba, cart huɗu ta cika ma'aikata na bin ta dashi a baya dan shi kam Saraki tun da suka shigo ya nemi waje ɗaya ya tsaya. Ɓangaren kayan maza ta koma ta shiga jida kamar ba zata dena ba har se da ringing ɗin wayar ta ya tsaida ta kafin ta ƙarasa kusa da Saraki ta miƙa masa ATM card ɗin ta tayi masa alamar ya bi ma'aikatan suje a biya ita kuma ta tsaya amsa kiran, har yayi gaba ya tuna bata faɗa masa pin ɗin ba dan haka ya koma "Oh sannu fa, ashe kece, to ya hutu fatan kina jin daɗi tare da enjoying zaman". Sentence ɗin da ya shiga kunnen shi kenan da ya iske tana faɗa cikin salo na rainin wayo, shiru tayi cikin sauraren Mommy kafin ta saki dariya "Ke ɗin uwa ta? Wai Mommy nah! Mommy my foot kinji, Baki da wani matsayi wajena sama da na matar kawu na haka sunan ki a bakina da zuciya ta Halima ne ko ba haka gyatumi ya raɗa miki ba". Daga can ɓangaren Mommy ta cika da takaici da ɓacin ran wulaƙancin Kisnah sedai bata da yadda zata yi, nema take dole ta danne komai a ranta, dan haka ta ɗan saki murmushin da be kai ciki ba "Hakane sunana Halima, sedai duk mu ajiye wannan a gefe, dama na kira ne in baki haƙuri dan Allah kisa kawun ki ya dawo dani, na miki alƙawari Megado bazata kuma shiga sabgar ki ba". Jinjina kai Kisnah tayi "Amma nayi mamakin jin kinyi laushi cikin kwana uku, ashe dama ke ɗin kura ce da fatar damisa, damisar kwali me bawa yaro tsoro, anyways tun da kinyi apologizing ki shirya kayan ki ki dawo anjima sedai fa ko da wasa wani raini ya kuma shiga tsakanin ƴarki dani ko ke kanki to tabbas zan sa a yanka Miki red ticket, Kim San dai mijin naki a tafin hannu na yake, byee bye uwar me bed". Katse wayar tayi ta maida kallon ta fuskar sa dan ta lura da tsayuwar sa tuntuni, sosai ta zuba idanun ta kan kyakkyawar fuskar sa wanda tun zuwan ta se yanzu ta iya karfin halin hakan, ƙarewa fuskar kallo tayi sosai ba tare da ta yadda idanun sa ya shiga nata ba kafin ta kawar tana me yaba kyan shi cikin ranta, "The pin". Ɗan juyowa tayi dan sam ta manta na bata faɗa masa pin ɗin ba "1469". Juyawa yayi ya koma wajen accountant ɗin ita kuma ta cigaba da tsayuwar jiran su tana kiran Leekha dan jin ya jikin Surry kafin ta ƙarasa. ************ "Barka da dare Mamin ya Saraki". Cikin murmushin ta me kyau na dattijan ƙwarai ta amsa wa ɗan nata gaisuwar da yayi mata "Barka kadai ƙanin Saraki". Dariya ce ta ƙwacewa Jamal na jin daɗin yadda yau mahaifiyar tasu ta sake har take iya barkwanci "Fatan Abbin Maimartaba na cikin ƙoshin lafiya". "Lafiya lau Mamin mu". Ya amsa mata cikin farin cikin jin ta kirashi da Abbin Maimartaba dan yaci sunan baban takawa ne. "Nazo yi miki albishir ɗin amincewar takawa na tafiya ta dan haka insha Allah nan da kwanaki biyu nake sa ran tafiya". "Naji daɗin hakan yaro na sedai ina jin damuwa kan tafiyar nan taka, nayi istikhara na tsawon kwana huɗu kuma alhamdulillah naji kwanciyar hankali sosai dan da alama Saraki na yana Lafiya dan haka ka bar batun nan dan ina son ganin giccin ka a tare da ni Jamal". "Amma Mami na riga na faɗawa takawa zan yi tafiyar nan har ya amince min, ba kya tunanin ya kawo wani tunani na daban kan fasawar tawa? "Sam ba zaka fasa tafiya ba Jamal, kaje ƙasar da kace masa zaka kayi course ɗin wata biyun under your field daga nan ka dawo kayi aure dan Allah, ina son ganin grandchildren ɗina kafin lokaci na yayi". Da sauri ya ruƙo hannun ta jin tana kawo batun mutuwa da sam baya san ji bawai dan be san dole zata mutun ba se dan yana fatan tayi tsawon rayuwar da zata ga dawowar gudan jinin ta mafi sayuwa a ranta cikin gidan uban sa da aka koreshi, cikin gatan sa kuma tunƙahon sa har ya taka matsayin da maƙiya suka ƙulla masa sharri domin shi. "Insha Allah zan yi kamar yadda kika ce Mamina, ki taya ni da addu'a Allah ya bani Sa'a kinji alfahari na". Hannu ta ɗora kan shi tayi masa addu'a kamar yadda ta saba yayinda cikin ranta ke ɗauke da kewar ɗan ta da yafi kowa kusanci da ita itama tafi kowa kusanci dashi, addu'a tayi masa a ranta kamar yadda ta saba duk ta tuno shi duk dama be taɓa barin ranta ba sedai ta danne kawai. Sallama Jamal yayi mata ya tafi processing duk abinda ke haɗa na tafiyar ita kuma ta cigaba da duba litattafan addu'o'in da ya shigo ya same ta tana yi. Ko da dare ta shirya tsaf dan zuwa turakar takawa kasancewar ita ke da kwana ranar, cikin haɗaɗɗen falon sa da ya kasance bame shiga se shi da matansa da ƴaƴansa ta same shi hannun sa riƙe da jarida yana dubawa, da sallama ta shiga ta zauna kusa dashi kafin ta miƙa gaisuwa. Hannu ya ɗaga mata kasancewar karatun yasha kansa itama bata kuma ce masa komai ba ta shiga zuzzuba masa kayan abincin da ta ƙaraso dashi dan a falon farko ma'aikata ke ajiyewa me girki kuma se ta ƙarasa dashi. Seda ya gama karanta jaridar kafin ya ajiye ya juya gare ta, cikin sakin fuska da walwalar da yake tsintar kansa duk ya kasance tare da ita ya amsa mata gaisuwar da tayi masa ɗazu yana me tambayar ta ya ta wuni. Abincin ta tura gabansa bayan ta amsa shi da lafiya lau, cikin kwanciyar hankali ya soma cin abincin sa yayinda gimbiya Haleematu ta kafe shi da ido dan ɗan ta Saraki take hangowa a tare dashi. Yanayin nutsuwar shi, yadda yake riƙe spoon har zuwa yadda yake tauna abinci duk takawa ya gado hakan yasa yanzu take ganin kamar shine a gaban ta, a dabarance tasaka tafin hannun ta ta goge hawayen rashin ɗan ta da ya zubo mata dan bata so takawan ya lura da halin da take ciki sedai abinda bata sani ba tuni ya gane me take tunani tun sanda ta kafe shi da ido har hawayen da ta share. Ya daɗe da sanin Haleematu macece me tsananin kawaici haka kuma yafi kowa sanin halin ta na haƙuri kuma yafi kowa shaida irin son da take yiwa gudan jinin nata. Tissue ya zara ya goge bakin sa bayan ya gama cin abincin, tashi tayi zata janye kwanakin ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata kusa dashi "Zauna nan Haleematu". Kamar yadda ya umarce ta haka ta zauna dab dashi suna fuskantar juna, a hankali cike da dattako ya ruƙo kyawawan yatsun hannunta ya shiga murzawa a hankali kafin cikin murya me taushi ya shiga mata magana "Me yake damun Haleematu na da har yake sata hawaye da damuwa? Wace irin damuwa ce haka da har gimbiyar Giwa ta kasa daurewa har raunin ta yana bayyana a fili? Shin akwai matsalar da ta shafi gimbiya ta da zata gagara sanar da ni Sarkin ta? Duk yadda taso daurewa kasawa tayi, tsawon watanni biyu na barin Saraki masarauta yau ne takawa ya nuna yasan tana da damuwa duk da ta daɗe da sanin ya fahimci hakan yana dai kawar da kai ne dan kar ya bata fuskar tunkarar sa da batun Sarakin ko yaya sedai abinda ya manta a cikin halayen ta shine tafi kowa sanin sa da iya karantar sa kamar yadda yafi kowa sanin ta da fahimtar ta, ya manta tunda har ya nuna baya son jin komai dangane da Sarakin ita ɗin bazata taɓa kawo masa batun ba saboda tsananin biyayyar ta. Janyo ta yayi jikin sa yana bubbuga kafaɗar ta har tayi me isarta ta share hawayen ta kafin ya ɗago ta "Faɗa min, menene damuwar gimbiya ta". Murmushin da ya tsaya iya saman lips ɗin ta tayi kafin ta bashi amsa "Ba wata babbar damuwa bace, kawai dai zuciya tace bata min daɗi haka ina ji na empty, shikenan" Tsananin tausayin ta ne ya kama shi, dama ya sani ba zata kawo masa batun Saraki ba ko za'a shekara nawa ne kuwa, shi kansa yana kewar ɗan nasa sedai da ya tuno irin laifin da ya aikata se yaji baya ko san jin sunansa balle tunawa dashi, bare kuma ita da yana cikin wanda zasu bada labarin irin shaƙuwar dake tsakanin su, akan ce ƴa mace itace ta uwa mace sedai a ɓangaren Sarakin da gimbiya is different, komai nasa Mamin sa ce, itace abokiyar sa, malamar sa, Auntyn sa, yayar sa kuma mahaifiyar sa haka a gare ta Saraki ne ƙawarta, maman ta, yayar ta, kuma wanta, ya sani in yace kar ta damu ma be mata adalci ba dan haka be sake ɗaga maganar ba se nasiha da wa'azi da ya shiga yi mata har hankalin ta ya kwanta har tayi cikakken murmushin da ya fito tun daga zuciyar ta ba wai iya fatar baki ba. (Allah Sarki uwa, i love U so much my umma💞). ................................ Babbar macece sedai ba wai irin girma sosai ɗin nan ba a kishingiɗe kan tattausan gadon da yasha shimfiɗu na alfarma, a ƙalla bazata wuce shakara 48 ba , daga kishingiɗen da take ta ke girgiza ƙafafunta da suka sha zanen jan lalle irin na zamani fuskar ta ɗauke da ƙasaitaccen murmushi, daga gefen ta kuwa matashin saurayi ne zaune kan tuntun ƙafar sa ɗaya kan ɗaya yana dubanta "Kar ka wani damu da wannan dan ni baya cikin lissafi na ko kaɗan, ko kana manta ka girme mashi ne kuma a halin yanzu kai ke amsa sunan YARIMA ME JIRAN GADO? kana tunanin zan yi sake da sarauta zata faɗa ɗakin Haleema ne bayan ina da ɗa babba? Ko kaɗan dan haka ka kwantar da hankalin ka ka cigaba da rayuwar ka ni mahaifiyar ka RUMANA na maka alƙawarin indai ina raye to sarautar Daular Noor taka ce". Sosai farin ciki da murna suka wanzu kan fuskar sa "Shiyasa nake matuƙar so da ƙaunar ki Ammi na, Allah ya bar min ke ya ƙara miki lafiya me inganci ki ganni zaune kan karaga matsayin sarkin daular Noor, Sarki UTHMAN MUHAMMAD HASHEEM". Ya ƙarasa faɗa sautin Muryar sa cike da tsananin buri da fata wanda itama gareta gimbiya RUMANA hakan ne a ranta. *************** "Ke yanzu Laylah baza kiyi wa kanki karatun ta nutsu bane, shin baki san rayuwar mace nada limit bane, fidabilillah ace kin zauna jiran gawon shanu kin ƙi aure kin zauna jiran wanda baki san yaushe zai dawo gare ki ba, yanzu kin yiwa kanki adalci kenan? Ko kuwa kin manta har Yarima Saraki ya bar masarautar nan be taɓa son ki ba ne?". Hawaye ne masu zafin gaske suka zubo daga idanun matashiyar dake duƙe ƙasan dattijuwar dake magana, kallo ɗaya zaka musu kasan uwa da ƴa ne saboda tsananin kamannin da suke yi, a hankali dattijuwar ta saka hannun ta ta ruƙo kafaɗar ƴar tata "Bawai bana son ki da Saraki bane Laylah, hasalima se na fi kowa san tarayyar ku sedai dole in faɗa miki gaskiya, kin sani kaf masarautar nan ba da wanda na aminta sama da gimbiyar Giwa haka itama gare ta, dan Allah ki cire komai a ranki ki bawa maneman ki dama Laylah, wallahi zaman ki haka ba aure yana damu na". Ruƙo hannun dattijuwar Laylah tayi cikin sakin murmushin da be kai zuci ba, " Ki taya ni da addu'a Ummi na, insha Allah zan yi kamar yadda kika ce, nima ina so in manta dashi sedai har yau na kasa hakan, kullum gani nake kamar ze dawo gare ni amma insha Allah a wannan karon zan ƙoƙar ta". Cikin tausayin autar tata Umma ta ce "A yanzu kam ni Sameera bani da wadda nake wa addu'a kamar ke Laylah, dan haka kar ki damu kinji Allah na tare da ke". Gyaɗa kai Laylah tayi kafin ta miƙa "Bari in je in duba abincin can kar ya ƙone". Ficewa tayi tana saƙa da warwara cikin ranta na yadda zata iya yakice Saraki cikin zuciyar ta....................✍️. Hhhhhhh😂🤣🤣 su Mommy an yi laushi luɓuɓus😜😜. Gimbiya RUMANA, ko ita kuma wacce haka🤔oho🤷 Toooooo faaaahhh😳 ke kuma Laylah daga ina, wata sabuwa inji ɗan caca, #team_saraki Ina tambaya 🤔 ©️ Ouummey 📚✍️. *☑️Ote, comment and share fidabilillah* Ouummey 13 (8/6/2022 9:46 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣3️⃣ _________________________📖ko da suka isa can suka tadda su Meenah and alhamdulillah jikin Surryn da sauƙi sosai dan ta ma farka har suna ta hira da Leekha, kamar yadda ta saba haka tayi wato just ta tura ƙofan ta shige without Salam yayinda Saraki dake bayanta riƙe da ledodin shopping be shiga ba se da yayi sallama ya jira izini tukunna dan ga dukkan alamu gareshi mata ne a ɗakin saboda tashin muryoyin su da ake ɗan ji daga waje. Kujerar gefen gado Meedah ta turawa Kisnah ta zauna suka shiga gaisawa da tambayar ya me jiki kafin ta maida kanta wajen Surayya da tun da Kisnahn ta shigo take ta sakar mata murmushi. "Ya jiki swee swee? Ta tambayi Surry calling her with the name she used to, "Alhamdulillah da sauƙi Kissy, Ina ta zuba ido amma shiru nace to akwai abinda ya tsaida ki, hope dai guy ɗin be miki komai ba ko?". "Sure naso na fito da wuri sedai kuma i have to wait for my new driver da na bawa appointment ɗin ganawa dashi da safen, no kar ki tashi hankalin ki ba abin da yayi min, all thanks to you my swee swee". "Masha Allah, that's what I wanna hear tun farkawana". "And you'll heal faster insha Allah". "We hope so my Kissy, so your new drive brought you here". "Yesso, ai tare ma muke, here he is". Ta faɗa tana juya wa dan nuna mata Saraki sedai wayam bata ganshi ba, miƙewa tayi ta nufi ƙofa tana faɗin "A'ah, ina kuma ya tsaya, i thought tare muka zo kofar ɗakin". Buɗe ƙofar tayi da niyyar fita duba shi se ta tadda shi tsaye hannayen sa riƙe da shopping bags ɗin har lokacin, zaro ido tayi cikin mamaki "So all this while kana tsaye a bakin ƙafa still holding the bags ko ɗan ajiye wa ka huta ma baka yi ba kamar wani soja, tabɗi, okay let's enter". Bece mata komai ba ya bi bayanta cikin ɗakin, be kalli kowacce ba cikin su dan ba wadda ta amsa sallamar da yayi ya ƙarasa gaban Kisnah ya ajiye bags ɗin ya juya ya fita, da ido duk suka raka shi banda Kisnah da hankalin ta ke kan waya tana duba messages a watsapp ɗin ta "Lord of heaven, Ina kika samo cute and handsome guy ɗin nan Kisnah?". Surayya ta tambaya a ɗan ruɗe dan ita fa Allah ya jarrabe ta ko ta ɗorawa kanta son maza zance, idon ta idon namiji me kyau se dai ƙarfin ikon Allah ya hana ta samun shi, hatsabibiyar kanta ce wajen sanin salo salo na kissa da kisisinar jan hankalin maza masu kyau shiyasa yanzu ma tana ganin Saraki taji ya fa yi mata. "Shine sabon driver na". "Driver!!!". Suka yi exclaiming in disbelief, gyaɗa musu Kai tayi in assurance ba tareda ta dube su ba. "Amma gaskiya me kyau ne, Oh my Goddd!! "Baki ƙarya ba Surayya yana da kyau kam sosai". Leekha ta faɗa in support of Surayya's words. Wani irin yatsuna fuska Hameedah tayi ganin yadda Surry da Leekha suka ruɗe da ganin wani banza wai shi driver "Kyan banza kenan, kyan ɗan maciji da baya hana a kashe shi, duk wannan kyan nasa dai sunan sa driver, so disgusting, mtsww". Ta ƙarashe tana tsartar da miyau in disguise, ɗan taɓe baki Meenah tayi tana ɗan jefawa Surry harara "Kin San fa ita Surry anything related to men shine abun yabo a wajen ta, ni duk banga abin zuzutawa ba a guy ɗin dan ba yau muka fara ganin maza masu kyau ba ai". Janyo bags ɗin Kisnah tayi batare da ta tankawa kowa daga cikin su ba ta tura gaban Surayya tana kallon ta "Yau Aunty tazo ne?". "Tazo amma bata daɗe ba ta tafi, dama zuwan nata bana Allah bane shiyasa tun da yaya yace mata ze Kai wata be dawo ba se ta tafiyar ta meaning ai dai kafin ya dawo na warke". Jijjiga kai Kisnah tayi tana miƙewa ta fara tafiya "Bari naje police station naga yadda zanyi da wancan ƙaramin ƙwaron, in na fito da wuri maybe na dawo akasin haka kuma se gobe insha Allah". "Allah ya yarda, but what about test ɗin da zamu yi gobe ga kuma abinda ya faru kinga ba zan samu zuwa ba". "Karki damu, I'll handle that". "Goodluck then". Yatsu biyu ta ɗaga musu ta ƙarasa ficewa daga ɗakin yayinda Meenah da Hameedah suka bi bayan ta dan mata rakiya zuwa wajen mota Leekha kuma ta zauna tareda Surry. Zaune a cikin motar suka same shi yana sauraren karatun Alkur'ani da aka saka gidan radiyon Sa'a FM, buɗe mata ƙofar baya Hameedah tayi take kuwa ta girgiza mata kai ta saka hannu ta buɗe gidan gaba ta zauna tare da maida murfin ta rufe, sauke glass ɗin tayi tai waving ɗin su daidai lokacin ya tashi motar suka bar wajen. "Durumi police station zamu je". Ta faɗa tana lumshe ido saboda yadda karatun Alkur'anin cikin ƙira'ar Sheikh shureim ke ratsa jikin ta har tana jin kamar ta dawwama tana saurara, wani irin shauƙi da nishaɗi take jin yana shigar ta from nowhere da ya tilasta mata lumshe ido tare da kwanciya cikin kujerar, karon farko tana zaune cikin mota without her daily headphone a kunnen ta. Cikin wannan yanayin suka ƙarasa gaban ƙaton ginin police station ɗin wanda bama ta san sun kawo ba seda ya ƙwanƙwasa glass ɗin kusa da shi kafin ta ɗago ta dube shi, ɗage mata gira yayi kafin ya nuna mata station ɗin da idon sa, saurin kau da kai tayi dan jin yadda jinin jikin ta ya tsinke da signal ɗin da ya mata. Hannun ta na ɗan rawa ta buɗe ƙofar ta fice da sauri tare da mai da ƙofar ta rufe, ɗan jingina tayi jikin motar har ta samu ta daidaita nutsuwar ta kafin ta buɗe side ɗin da ta fito ta ɗau purse ɗin ta da ta manta, batare da ta dube shi ba tace ya fito su shiga. Fitowar yayi kamar yadda tace yayi gaba tana bin shi a baya har cikin station ɗin, dogon baƙin kakkauran ɗan sandan dake kanta ya fito da sauri yana welcoming ɗin su dan polisawa kaɗan ne zasuce basu san fuskar Kisnah ba, ko ba domin tsiwar ta da yadda ake kawo report ko ita tasa a kama wani ba, ba wanda ke cikin garin Manya daze ce be san K&S drinks ba, K&S table water, K&S couture, K&S textiles, K&S Furnitures, K&S shopping Mall, K&S flour and food stuff Wanda duk itace mamallakiyar su a yanzu. Da sauri police ɗin yayi leading ɗin ta to office ɗin D.P.O dan jin ƙorafin ta, kai tsaye ta shiga office ɗin without any knocking or neman izini, a fusace dpo ya miƙe dan ganin wane shegen ne ya shigo masa without excuse se kuma yai arangama da Kisnah, da sauri ya washe baki yana mata maraba "Welcome Madam Kisnah, have a seat please". Ya faɗa yana tura mata ɗaya daga cikin kujerun dake gaban table ɗin sa, ɗan ɓata fuska tayi kafin kuma ta zauna tana ɗan sakin fuska, da sallama Saraki dake bayan ta ya shigo wanda dpo ne kaɗai ya amsa masa banda Madam ɗin da tayi kamar ma bata ji ba, shima kujera dpo ya nuna masa wadda ke kusa da Kisnah ya zauna. Gyara zama Kisnah tayi tana ɗora hannayen ta kan table ɗin dpo "Nazo ganin sheɗanin da ya nemi shiga hanya ta ne day before yesterday". Da sauri dpo ya miƙe yana faɗin "Bari a kawo shi Madam". Ficewa yayi yana bawa wani kurtu umarnin kawo Sageer wajen sa, da sauri kurtun ya amsa yana wuce wa ciki inda aka rufe Sageer, ɗaɗɗaure cikin sarƙa hannu da ƙafa aka fito dashi kamar wani gawurtaccen ɗan fashi ko makashin jama'a dan da ƙyar ma yake iya tafiya, gaba ɗaya kamannin sa sun canja kai baka ce Sageer ɗin nan bane haɗaɗden gaye me ji da wanka. Karɓar sarƙar dpo yayi ya iza ƙeyar sa cikin office ɗin sa wajen su Kisnah, jan kujerar ta baya tayi tana jefawa Sageer mugun kallo lokacin da dpo ya gurfanar dashi gaban ta. Shiru tayi tana bin shi da kallo kafin ta daddage ta sheƙa masa kyakkyawan marin da se da ya hantsila saboda ƙarfin sa, ƙafar ta takai ta kuma shurin sa yayi baya ya bugu da bango, hakan be mata ba ta tashi ta bishi tana duka da ƙafa faɗi kawai take "How dere you, I said how dere you". Sosai baki da hancin Sageer suka fashe dan ya daku da takalmin Kisnah da ya kasance me tsini sosai, dukan sa kawai take dan duk ta tuno ƙazamin hannun sa ya taɓa jikin ta se taji kamar ana hura mata wuta a zuciyar ta, ga kuma raunin da yayi wa Surayya da take asibiti sanadin shi, dpo na zaune kan kujera ko pim bece mata kan dukan da take wa Sageer ɗin ba wanda a ƙa'ida hakan ya saɓawa doka, se ma aikin sa da ya cigaba da yi hankali kwance kai kace baya wajen. "Stop it, I said stop it". Tsayawa tayi cak kamar wadda aka dannawa pause kafin a hankali ta juyo ta dubi Saraki dake tsaye bayan ta wanda shi ya daka mata tsawar, kafe shi tayi da ido kafin a hankali ta girgiza kanta "Baka san me wannan annamimin yayi min ba that's why you're saying I should stop, had you know what he did cewa ma zaka yi in ƙara masa". "Whatsoever, dukan yayi yawa, can't you see he's bleeding, don't you get a heart in your chest?". Cikin ihun masifa ta shiga bashi amsa dan ranta ya kai maƙura wurin ɓacin cewa ta ƙyale Sageer da yayi, har yana wani faɗa mata whatsoever, kamar ita, lallai ma! "I don't care, nace I don't bloody care if he'll loose all of his blood here, this stupid guy use his worthless dirty filthy hands to touch me with his dirty intention, he attempted to rape me after drugging me which without Surayya he would have succeed, can't you understand, nace can't you see Surayya is there laying on sick bed because of this stupid brat, he intends killing her if not Allah has saved her she would have been in her grave since yesterday, and you're here saying I should leave him, tell me how can I leave this devil". Be kalle ta ba ya juya ga dpo da tuni shima ya miƙe tsaye yana rarraba ido tsakanin su a ransa yana ayyana 'this guy must be her brother or boyfriend' Dan if not one of the two baya tunani akwai someone that has the gut ya ma Kisnah tsawa like this giving her orders. "Take him to hospital, he's unconscious". Da sauri dpo ya ƙarasa gaban Sageer dake kwance ƙasa wanwar har lokacin hancin sa na fidda jini ya fara jansa kafin ya kira ƴan sanda ɗaya ya kama masa suka ɗauke shi, juyawa yayi ga Kisnah da ta kafe shi da idanu, kallo ɗaya yayi mata yasan ta kai maƙura gurin ɓacin rai, kujerar ta da ta ture garin dukan Sageer ya jawo mata "Seat". Banza tayi masa dan fa takai wuya, ɗan shiru yayi kafin ya ɗan rage kausasa Muryar da yai ya sake faɗa mata "Saet Please". Kamar bazata zauna ba se kuma ta zauna tare da kau da kanta daga gare shi tana huci, zama yayi a kujerar da ya tashi shima "He attempted raping you saboda kin sa kayan da basu dace ba? Okay hakan is nothing, you live your life as you wish, Amma bakiyi tunanin ya mutu ba saboda dukan da kike masa bayan akwai harbi a ƙafar sa ga kuma dukan da police ɗin suka masa, ba kya tsoron ya mutu a hannun ki? Ko baki san duka zunuban sa zasu koma kanki bane, why not ki Kai shi court a yanke masa hukunci daidai laifin sa? Yes he's a devil for what he did but what if you decide to forgive him? Do you know the reward, ehm? The prophet said whoever forgive someone Allah will also forgive him, do you think you've no sin? No! We all sinned because we're bin Adams and we'll all like Allah to forgive us, didn't you want to be among?". Ya ƙarashe cikin sigar tambaya, sosai taji jikin ta yayi sanyi with his speech, a hankali ta girgiza kanta alamun she want, ajiyar zuciya Saraki ya sauke a ɓoye ganin ta karɓi nasihar sa "So forgive him please, leave him for the sake of Allah, in har halin sa ne hakan kuma be tuba ba se kiga Allah yayi punishing ɗin sa one way or the other, will you pls forgive him?". "Na yafe masa". Ta faɗa so cool hoping Allah will forgive her also. Sosai yaji daɗin yadda bata da taurin kai sosai, he pray Allah ya shirya ta dan ya fara yadda da abinda Inusa ya faɗa masa ɗazu, now he believed she's simple yadda be yi tsammani ba. "Akwai abinda muke jira ne?". "Yes, ka faɗawa dpo nace a sake shi". Gyaɗa kai yayi ya fita daga office ɗin, bakin ƙofa suka yi kiciɓis da dpo so kawai se ya dawo ciki shima dpon ya shigo, cikin sauke ɗan numfashi saboda doguwar maganar da yayi ya kalli dpo "You released him, ta yafe masa". Da sauri dpo ya kalle ta daidai tana miƙewa tsaye, gyaɗa masa kai alamar hakane kafin ta fice daga office ɗin, fita shima Saraki yayi cos se ya buɗe zata shiga motar dan yayi locking motar. Jingina jikin motar ya same ta dan haka tun kan ya ƙarasa yayi unlocking car ɗin using smart Lock na car ɗin, jin alamun yai unlocking yasa ta buɗe ta shiga ta zauna kalaman shi na sake yawo a kanta, shiga yayi shima ya zauna tare da rufe ƙofar ya tada motar suka hau kwalta, ƙwaƙƙwaran motsi bata yi ba har suka kusa isa gida traffic ya tsaida su, ɗan buɗe ido tayi ta kalli titin ganin yadda ababen hawa suka cika ko ina alamun an tashi kasuwa, daga can tsallaken titi ta hango wani tsoho tukuf duƙaƙƙe yana takawa a hankali hannun sa saƙale da buhu, ɗan sake buɗe ido tayi ganin kuɗaɗen sa da ya samo sadaka (not sure) na zubewa ta wata ƴar huda jikin buhun, kallon traffic ɗin gaban su tayi taga suna da sauran kusan 20 count downs kafin a sake su dan haka ta ɓalle murfin motar ta fita da sauri. Ƙarar buɗe side ɗin ta ya sa ya juyo dan ganin ina zata, kan idon sa ta kukkurɗa tsakanin motocin har ta ƙarasa wajen tsohon da yake tafiya kamar yaron da yanzu yake koyon tafiyar, "Sannu baba, kana ta zubar da kuɗin ka a ƙasa baka sani ba". Ɗan tsayawa tsohon yayi kafin ya juyo ya kalle ta a hankali ya kuma kalli hannun ta da ta kwaso masa kuɗin Naira hamsin se ashirin biyu, da ƙyar ya buɗe bakin sa da haƙora da yawa sun zube "Nagode jikata, kinga ban ma kula buhun ya ɓule ba, Allah yayi albarka kinji". "Ameen kakana, kawo in maida maka kuɗin in Kuma gyara maka ya dena zubewa ko". Ta faɗa tana karɓar buhun nasa ta jirkita shi zuwa side ɗin da be huje ba kafin ta ɗan nannaɗe bakin ta miƙa masa "Gashi kakana, kaga an kusa sakin hannu ga kuma magrib ta kusa, ko zaka zo mu kaika gida tunda a mota nake kaga dare ya kusa". Karɓa tsohon yayi yana sakin tattausan murmushi a fuskar sa da duk ta mokaɗe "Nagode jikata, Allah ya saka da alkhairi ya yi miki albarka, Bama se kun kaini ba dan nazo gida, kin ga kwanar nan ita zan shiga". "Allah Sarki, to Allah ya ƙarasa da kai gida lafiya kaka, bari inje kar a saki hannu". "Allah ya shirya mana ku ya kawo miji nagari". Da sauri ta amsa da Amin tana tafiya har ta ƙarasa wajen motar su, buɗe ƙofar tayi zata shiga se kuma ta juya inda ta bar tsohon, yana nan kuwa tsaye kallon ta, hannu tai masa waving kafin ta shige jin an bada hannu, ɗauke idon sa Saraki yayi daga kanta ya maida kan steering yaja motar, haka ta dinga leƙa window tana kallon tsohon da ya cigaba da tafiya a hankali fuskar ta ɗauke da murmushi har ya shige layin da ya nuna mata kafin ta koma ta zauna daidai tana sauke ajiyar zuciya. Horn yayi a katafaren gate ɗin kafin gate ɗin ya buɗe ya shiga da motar har wajen parking, kashe motar yayi bayan ya gama daidaita parking ɗin hakan yasa Kisnah kwasar wayoyin ta da purse ɗin ta ta fita, zagowa tayi daidai shima ya fito yana kulle motar yaa miƙa mata key ta tsaya tana kallon shi batare da ta karɓa ba "Ai kai zaka cigaba da riƙewa tunda kai ke driving ko". "No zan je gida in kwaso kayana tukunna gobe na dawo". Ɗan shiru tayi kafin ta gyaɗa kai tunda yau bazata fita da dare ba "Okay kaje da ita amma ka shigo da wuri dan ina da class by 9, wannan ragowar bags ɗin na bayan mota naka ne". Batare da ta jira me zece ba tayi gaba kafin ta ɗan tsaya tace "Thanks". Ta cigaba da tafiya har ta shige falon..........................✍️. My Kisnah Allah yasa kina da rabon shiriya 🥺. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 14 (8/7/2022 9:40 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣4️⃣ ___________________________📖 Zaune a falon ta tadda Mommy da Maigado suna hira while watching TV, kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kai ta cigaba da tafiya heading to the staircase, cikin danne takaici, baƙin ciki da tsanar da tayi mata Mommy tace "Welcome back". Hannu kawai ta ɗaga mata ta haye sama dan har yanzu jikin ta a mace yake ga kuma gajiyar dukan da tayi wa Sageer, dole tana buƙatar wanka yanzun nan ma kuwa. Unlocking door ɗin tayi ta shige locking it back ta ciki kafin ta ƙarasa ta zube wayoyin ta kan sofa ita kuma ta wuce bedroom, undressing kanta tayi as usual without using towel ta ƙarasa bathroom ɗin tayi wanka sosai da cold water batare da damuwa ba kana ta fito yanzu kam ɗaure da towel se wani da tayi tying kanta ciki saboda jiƙewar da gashin ta yayi, goge kan tayi sosai kafin ta jefar da towel ɗin ta ɗau dogon brush ta shiga combing hair ɗin, dole gobe in ta fito test ta wuce saloon dan kan ya fara damun ta, in aka wanke se ayi mata ko kalba ne ko twisting sedai taje ta ga Wanda zata zaba. Cikin wannan tunanin ta gama busar da kan da hand dryer ɗin ta sannan ta koma gaban wardrobe ta ciro sleeping dress ta saka dan bata jin zata kuma fita daga ɗakin nan se kuma gobe. Kwanciya ta nufi yi dan ta gaji sosai so take ta huta ko kaɗan ne kafin ta tashi ta sake karatun test ɗin da zasu yi gobe se kuma ta tuna bata fa yi sallah ba yau, dafe goshin ta tayi dan wallahi ta gaji maƙura, haka dai dole ta tashi ta koma bathroom ta ɗauro alwala ta fito, hijab ɗin sallar ta tasaka ta hau duddungura sallar, nan da nan kuwa tayi ta gama tun daga Azahar la'asar har magrib ɗin da aka idar yanzu (wa yaga me shaf shaf😂🤣) kafin ta cire hijab ɗin ta bi lafiyar gado. Bacci tayi har goma na dare kafin ta farka sedai bata tashi ba se da ta ɗan sarara har taji daidai dan ba'a son daga farkawa bacci mutum yace ce tashi, toilet ta shiga tayi brush tare da wanke fuskar ta sannan ta fito ta ɗau littatafan school ɗin ta tare da laptop other than that da tayi amfani dashi da safe, laptop ne me kyau da kana gani kasan ce yi tsada bayan sa ɗauke da tambarin K&S wanda purposely sabida karatu take amfani dashi ta koma falo kan sofar da ta ajiye wayoyin ta. Ɗauke su tayi ta zuba kan center table ɗin ɗakin kafin ta zauna tana ajiye system ɗin kan ƙafar ta, cike da ƙwarewa da tsantsan iyawa take pressing keyboard ɗin wanda baka jin ƙaran komai a ɗakin se nasa. Sosai ta maida hankali kan research ɗin da take yi har ta samu abinda take so kafin ta janye system ɗin ɗan gefe kaɗan da ya ita ta ɗau ƙaton littafin lauyoyi ta cigaba da going through. A ƙalla tayi spending 5 hours tana karatu wanda bata lura lokaci yaja haka ba se da ta kalli agogo mistakenly, zare kyawawan oily cat eyes ɗin ta tayi kafin kuma ta dafe baki ganin har 3am, da sauri tai shutting down system ɗin ta ajiye tare da books ɗin ta wuce bedroom da gudu, kan bed tayi tsalle ta faɗa tana tura hannun ta ƙarƙashin pillow ta jawo photon ta ta rungume a chest tareda covering kanta with duvet, ƙarfi da yaji ta hana kanta tunanin komai dan haka cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi gaba da ita. Ƙarar buɗe gate ne ya farar da ita daga baccin ta me daɗi (kun san ga every student daɗin baccin asuba daban ne😂), ɗan juyi tayi dan se taji kwata kwata baccin be ishe ta ba, she wants more and more, har ta rufe ido dan komawa kalman test tai ringing a mind ɗin ta hakan yasa ta zabura da sauri tana kai kallon ta kan designer wall clock ɗin ɗakin "Oh my God". Ta faɗa tana durowa daga gadon da sauri har tana neman faɗuwa ta dai samu bata faɗin ba, bathroom ta faɗa a gurguje dan It's 5 mins to eight, wardrobe ta buɗe ta janyo wata straight English gown kusan similar to ta jiya sedai wannan bata kamata sosai ba kuma ta kai mata ƙasa sedai tana da tsaga sosai ta baya dan ya kai har wajen gwiwar ta, da sauri ta zura rigar bayan ta saka bra da pant ɗin ta, faɗin yadda silver gown ɗin ta mata kyau ma is a total waste of time, scarf ta janyo silver me ƙyalƙyali ta ɗaura saman kanta sedai gashin ta ya fito ta tsakiyar sa duk da ta nannaɗe shi amma seda yakai ƙasan wuyan ta. A gurguje ta ɗebi wayoyin ta da kayan rubutun ta ta fice ko breakfast Bata iya tsayawa yi ba dan shirinta kaɗai ya cinye fiye da 40mins, bata sami kowa a falon ba ta wuce compound cikin sauri wanda takalmin ƙafarsa silver color me tsini be hana ta yi ba, tsaye tayi tana bin compound ɗin da kallo sosai ganin bata ga Saraki ba, wajen da ma'aikata ke zama in sun gama aikin su, gurin yasha grass carpet me kyau ɗauke da tables manya da kyawawan kujeru gefen su flowers ne masu kyau da ke fitar da sassanyan ƙamshi, tun da Khamees shugaban ma'aikata ya hango ta ya miƙe da sauri har ta ƙaraso, gaishe ta ya soma sedai bata kula hakan ba ta shiga tambayar sa "Ehm wannan sabon driver ɗin be zo bane?". "Wai Saraki? Yazo amma ya ɗan fita yana amsa call yanzun nan". "So sunan sa Saraki kenan?". "No baba me gadi ya kirashi da hakan dan yace abubuwan da yake kaman tafiya,magana, miskilanci da izzar shi kaman na yaran sarauta shi yasa masa Saraki amma sunan shi na gaskiya Ahmad ne". "I see". Kawai tace ta juya daidai lokacin Saraki ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo, da ɗan sauri ta ƙarasa tana masa alamun ya fito da mota. Farar mota ya ɗauko ganin kayan jikin ta is way related to farin, da sauri ta buɗe ta shiga kana yai hanyar gate da kafin ya kai ma gate ɗin ya buɗe kansa ɗan tuni nasu gadi suka saka password ɗin ganin fita zasu yi, seda suka hau kan titi sosai kafin ta ɗan dube shi a kaikaice tace "Good morning". Ya ɗan yi mamakin jin ta gaida shi sedai ya dake ya amsa da "morning" batare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tuƙin sa, itama bata kuma cewa komai ba ta buɗe littafin kan cinyar ta ta cigaba da dubawa. Bakowa yasan halayen Kisnah sosai ba se close friends ɗin ta dake tare da ita kusan ko yaushe wato su Meenah, ba wani abu bane gare ta gaishe da wanda ya girme ta tun bare ma in ya kama girman sa, eh tana da tsiwa da rashin kunya amma fa ga wanda ya siya da kuɗin sa ma'ana wanda ya takale ta ko ya zubar da girman shi. "Where are we heading to?". Batare da ta ɗago ba ta bashi amsa dan karatun ya sha kanta "Federal University, Manyan". Cikin ƙaton gate ɗin school ɗin ya wuce wanda tun ɓullowar motar ta security suka buɗe amma mamaki suke na yadda yau bata yi horn ba kamar yadda ta saba ga kuma yanayin driving ɗin cikin nutsuwa. Bakin department ɗin da ta dinga kwatanta masa har suka ƙara so yayi parking tare da kashe motar, buɗe side ɗin ta tayi ta fice bayan ta kwashi litattafan ta, rufe ƙofar da ta bari a buɗe yayi yana lumshe idan sa cikin karanta suratul Kahf da be samu yayi ba yau saboda baccin da yaci ƙarfin sa. Tun daga nesa ta hango su Meenah wannan karon su uku dan babu Surry da ke asibiti, ƙarasowa sukayi gare ta suka amshi books ɗin hannun ta suka jera tare zuwa cikin theatre ɗin, row ɗin tsakiya suka shiga kuma layi na farko suka zazzauna kafin suka fara gaisawa a tsakanin su, karɓar littafin hannun Meenah tayi ta shiga yi musu bayanin abinda tayi researching jiya wanda take tunanin za'a iya tambayar su, sosai tayi musu ƴar ƙaramar tutorial Wanda har se da lecturern ya shigo sannan ta rufe littafin ta miƙawa Leekha, karɓar Leekha tayi ta haɗa da nata da nasu Meenah ta fitar dashi can gaban theatre ɗin sannan ta dawo, miƙewa duka suka yi jin malamin na faɗin each line mutum biyu yake son gani dan gurin akwai girma sosai, fita Kisnah da Leekha suka yi suka bar Meenah da Hameedah na sake spacing tsakanin su. Tunawa da Surayya yasa ta fasa budar saman theatre ɗin ta wuce wajen malamin dake tsaye yana jiran su gama gyarawa "Good morning sir". Juyowa yayi ya dube ta yana amsa gaisuwar Tata "Good morning, fatan dai lafiya". "No sir, nazo yin report ne concerning Surayya kabeer da ba zata samu damar zuwa yin test ba saboda rashin lafiya, yanzu haka tana kwance gadon asibiti sir". "And where's her relatives da basu zo sun yi reporting ba se ke". "Her brother is presently in Canada for business Kuma ba ta da kowa bayan shi, matar sa kuma hate...oh Is just personal sir, but you can confirm, tana Gare well hospital, room 13, Dr Ibrahim nura ne ke handling case ɗin ta". Gyaɗa kai yayi cikin yarda da batun nata kafin yayi wa Surayya fatan samun lafiya da tabbatar mata da zai organizing team ɗin bincike aje a dubi Surayya a kuma tabbatar da in bata da lafiya da gaske, nodding kanta tayi tare da masa godiya ta juya neman inda zata zauna. Bin bayan ta sir Kashim yayi da ido cikin yaba kyan ta tare da mata fatan shiriya, if not sabida ayyukan ta he would have marry her fan sosai take da kyau take kuma burge shi sedai yasan ko hauka yake baze kai ta gidan su sunan wadda yake so ba duk da shiɗin ba saurayi bane dan yana da mata har da ƴaƴan su biyu. Cikin jin daɗi take ta amsa questions ɗin cike da nutsuwa dan alhamdulillah ba abinda bata sani ba cikin wanda aka tambaya, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama ta sake bi through kafin tayi submitting ta fita, da idanu majorityn ƴan class ɗin suka bita da ido har ta fice, su fa har yau gani suke bata da wani ƙoƙari kawai tana siyan marks da jikin ta a wajen malamai though yawancin su zasu bada shedar ita bame zuwa office ɗin malamai bane se in ta zama dole. Duk wani abu related to karatu lokacin ta take bashi cikakken shiyasa bata wasa da zuwa makaranta, ƙarya kaga ta makara dan tun fara karatun ta har zuwa yanzu da take 400l zata iya irga iya makarar da tayi haka bata yadda rashin fahimta ya shiga tsakanin ta da wani malami shiyasa kawo yanzu malami ɗaya ne suke ƴar tsaka dashi, shikuma haka kawai ya ɗau karan tsana ya ɗora mata, tun tana kau da kai da ido a kanshi dan bashi girman shi na malami har ya ƙure ta tayi masa rashin mutunci shiyasa shi kuma duk hanyar da ke disga ta ko ya kayar da ita a course ɗin ita yake nema, yanzu haka akwai assignment ɗin da aya bayar Wanda individual ne kowa da questions ɗin sa, har zuwa yau da za'a yi submitting jibi ta kasa fitar da amsar, tayi tayi har ta haƙura ta cigaba da normal routine ɗin ta sedai deep down abin na mintsinin ta a rai, bata taɓa samun wata matsala ta carry over, spill over ko resit ba se gashi yanzu ƙarfi da yaji malamin na neman kai ta ƙasa. Cikin wannan tunanin ta ƙarasa ta shiga motar se dai bata rufe ƙofar ba, jiran su Meenah zata yi sedai bazata iya tsayuwar cikin ranar da ake yi me zafi sosai ba shiyasa ta shiga motar, hannu takai ta ƙara ƙarfin AC ɗin kana ta kwanta cikin kujerar ta ta shiga tunanin ta wace hanya ya kamata ta ɓullowa malamin. Tayi nisa cikin tunanin har bata ma san tana hawaye ba dan ita kam kacokan fari cikin rayuwar ta ta ɗora shi ne kan karatun ta, shine number one priority a rai da zuciyar ta shiyasa yanzu da matsala ke neman Kunno Kai duk hankalin ta ya tashi, bawai bata da yadda zata yi da malamin bane dan ko yanzu taso ya bar makarantar tabbas za'a masa transfer haka kuma ko A tace tana so tana da yadda zata samu ko da baya so kuwa se ya bayar sedai tana da wani principle ɗaya, sam bata son alfarma a karatun ta, bata son hanya ko wani abu, tana so ne ta bugu ƙirji tace ta sami kwalin ta ne da ƙoƙarin ta da zufar ta, wannan shine aƙidar ta shiyasa ba ta tunkari kowa da batun ba. A kaikaice Saraki ke kallon yadda take hawayen wanda alamu ya nuna koma meye ya sata kuka ba ƙaramin matsayi gare shi ba a ranta haka kuma ba ƙaramin so take wa abin ba, to ko dai malpractice tayi aka koro ta daga hall ɗin ɗan be ga wanda ya fito ba har yanzu bayan ita, taɓe baki yayi yana ayyana hakan ne ma dan yadda wannan take yasan ba wani abu ta iya ba balle ta tsinana dole seda satar amsar. Ƙarasowar su Meenah ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi ta maza ta saka hannu ta share hawayen idon ta dan bata taɓa nuna karaya ba gaban su yanzu ma kuma bazata fara ba shiyasa bazata bari suga hawayen ta ba, ɗan kallon Saraki tayi ta gefen ido hopping be ganta tana kuka ba se ma taga idanun sa a kunshe suke hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya. Fita tayi daga motar ta tsaya jikin ƙofar dake buɗe har lokacin tana facing su Hameedah dake tsaye kusa da ita, congratulations suka shiga yiwa juna na sauƙin da test ɗin ta musu kafin suka dinga thanking ɗin ta, murmushi kawai take musu batare da ta amsa ba dan tana cikin damuwa sosai, Meenah ce ta fara lura da hakan ta matsa sosai ta ruƙo hannun ta "Kina cikin damuwa Kissy I can read it on your face, me ke damun ki pls". Ɗan ajiyar zuciya ta sauke tana sake danne raunin ta "Kema kin sani, me ze sani damuwa bayan CON005, wallahi har yanzu na kasa fitar da assignment ɗin nan, dama na daɗe da sanin malamin nan ya tsane ni shiyasa ya tsiro da Wannan assignment ɗin ɗan ya samu damar laƙabin carryover, ko Baki ji wai shine matsayin C.A da test gaba ɗaya ba?". "Nikaina na kasa gane damuwar malamin nan da ke Kisnah, amma me ze Hana kiyiwa Deen magana nasan dole ze saka ya fita hanyar ki". "Bana buƙatar connection a karatuna Leekha, I want to earn my certificate with my brain ba money ba, Dan haka ba wanda zan faɗa wa, Allah See's everything and will surely give me a way out". "Then Goodluck Mrs brain". Hameedah ta faɗa kamar cikin wasa but cike da isgilanci da farin cikin yau dai ta ƙarewa uwar iyayin basira, murmushi kawai Kisnah tayi dan ba tun yau ba tasan Hameedah is jealous of her sedai bata damu ba dan tasan tuni ta yiwa Hameedar zarra nesa ba kusa ba. "Hope you guys duk kun gama naku?". "Just some little corrections". Meenah ta faɗa "Already finished". Leekha itama ta faɗa "Since yesterday". Inji Hameedah, gyaɗa kai Kisnah tayi kafin ta juya dan shiga mota Wy "Wish all of you success, will be going, see you tonight a cinema". "See yha dear, byee". Suka haɗa baki wajen faɗa, ita kuma tai ya nasu tare da rufe murfin tana gyara zama. 'So wannan ce damuwar ta kuma the reason behind her tears, so this is how she loved her studies, he pray she get an alternative, ko ba komai she's doing good here'. Tashin motar yayi tare da yin reverse ya fice daga makarantar haka ma Meenah da Leekha Hameedah kuma tace she get something to do..............✍️ ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 15 (8/7/2022 9:41 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣5️⃣ _______________________📖 "Kai ni K&S drinks". "You show me the way". Nodding tayi ta shiga nuna masa hanya har suka ƙarasa, horn yayi security dake bakin gate suka fito dressed in blue black uniform of theirs, ko da sun ga motar tace basu fasa checking ɗin motar ba sannan aka basu hanya suka wuce first gate, ko a second and third gate ma seda aka sake duba su kafin a basu hanya suka wuce. Ƙaton building ne da girman sa ya zarce misali da ba ma zan iya misalta shi ba, just ku auno shi a idanun ku. Da sauri ɗaya daga cikin securityn ya ƙaraso ya buɗe mata ƙofar ta fito sannan ya maida ya rufe ta tunkari main building ɗin Company ɗin. A hankali Saraki ya juya ya dubi litattafan ta da ke ajiye kan seat ɗin da ta tashi kafin ya sa hannu ya janyo su ya buɗe ya shiga dubawa, sannu a hankali yake bin rubutun yana karantawa kafin ya fara flipping through pages ɗin, bin paper ɗin da ta faɗo yayi da kallo kafin ya ɗauka ya warware, question ɗin assignment ɗin da take batun ta kasa ce dan gashi nan bayan sunan ta, admission number, department, course code da kuma question bata rubuta komai ba, Sunan ta ya koma sama yana maimaitawa cikin tunani to ya akayi ya canja ya koma Kisnah, to kodai nickname ɗin ta ne Kisnah kamar yadda yaji ana kiranta?". "Sakeenah Safwan". Ya sake maimaita sunan kafin ya maida hankali kan question ɗin, ƙaramin cute smile ya saki ganin question ɗin ba wata me wahala bace amma har take kuka akai, kamar wanda ake controlling ya samu kan sa da ɗaukar pen ya ɗora kan plain sheet ɗin ya soma rubutu, sosai ya maida hankali kan rubutun da yake yi, seda ya cika plain sheet ɗin gaba da baya ya kuma zarar wata da ta ɓullo ta cikin textbook ɗin ta, wasa wasa seda ya cika plain sheet uku sannan ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya, bin rubutun yayi da ido yana karantawa har ya kai ƙarshe kafin ya ninke takardun ya maida mata cikin ƙaton exercise book ɗin ta kana ya cigaba da karanta textbook ɗin. Sosai ta ɗauki lokaci supervising all the workers kafin ta fito dan tafiya gida cikin gamsuwa da aikin da suke yi, tun daga nesa da ya hango ta ya rufe littafin ya ajiye mata inda ya dauka tare da kunna motar, shigowa tayi tana karɓar file hannun ma'aikacin da ya rako ta dasu Sannan ta rufe ƙofar. Jan motar yayi zuwa waje wanda a nan ma seda aka sake checking ɗin motar tasu kafin bar su su wuce, yanzu kam gida suka yi yayi parking a lot ɗin su ta fita, har ta fara tafiya se kuma ta tsaya har ya fito shima "Kaje wajen Khamees me kula da ma'aikata ya nuna maka ɗakin ka". Gyaɗa mata kai yayi taci gaba "Help me with these files please, sun min yawa ga books again". Karɓar files ɗin yayi a hannun ta ita kuma ta riƙe littattafan suka nufi ƙofar falo, yanzu kam ta tadda su Mommy har ma da ƙawayen ta biyu a falon gaban su cike da drinks da kayan snacks hakima Maigado a gefe riƙe da waya ta maƙala earpiece a kunnen ta, shiga tayi falon without excuse kamar yadda ta saba yayinda Saraki ya dakata bakin ƙofar yana jiran ta kai books ɗin hannun ta ta dawo ta karɓi files ɗin, jin bata ji takunsa a bayan ta ba yasa ta juyo ta dube shi yana tsaya ta masa izinin shiga "Come in Mana, ya ka tsaya a nan". Ɗan shiru yayi se kuma ya shiga thinking ta sanar da na ciki za'a shigo, shiru duk suka yi Mommy da ƙawayen ta suna binta da kallo har ta kai tsakiyan ɗakin tana niyyar ƙarasawa saman ta sannan ta juyo, ganin Saraki tsaye yasa ta dakata tare da dawowa kusa da ƙawayen Mommy "Excuse me, join those two a three sitter ɗin ki bashi wajen ya zauna, ya gaji so baze iya tsayuwar har na hau sama na sauko ba". Sosai fuskar matar ya nuna ɓaci rai sedai kafin tayi magana Mommy tayi saurin tarar ta "Haba Kisnah, ai se ya zauna a kan rug ko ko bashi ne sabon driver ɗin ki ba?". "Yes shine se aka yi yaya?". "He supposed to wait outside, ba daraja bace ace muna zaune sama jere driver ma na zaune, its so disgracing, hakan ze iya sa ya dinga girman kai kalla fa ya shigo muna zaune amma ko gaida mu be yi ba". "So sannu Nana, Nace sannu Nana Asma'u uwa ta, to yaƙi ya tsaya a wajen kinji akwai abinda zakiyi ne, kina wani maganar ba daraja bace to hell with the daraja, ke har wani daraja gare ki, to bari kiji wallahi Ya Saraki da kike magana akai ya fiki daraja nesa ba kusa ba ya kuma fiye min ke da duk abinda ya shafe ki so dubu, in bazaki iya zama inda yake ba You better pack your belongings and move back to where you return from dan nan gida nane bana gyatumin wani bane haka ba na mijin wata ba so I have the right nayi yadda naso a kuma lokacin da naso, da zaki wani ce be gaishe ku ba to ya gaida ku yace ya gaida wa, gayyar munafukai?, Mtsww, Ya Saraki have a seat please". Ta ƙarashe looking at Saraki da har lokacin ke tsaye, without saying a single word ya zauna inda waccan ta tashin bisa dole, farko be yi niyyar zama ba sedai kalaman Mommy kan shi yasa yaji Yes se fa ya zauna duk da response ɗin da Kisnah ta mata ya burge shi sosai, dukkan su seda suka sake kallon shi lokacin da yakai zaune, ba Mommy ba har Kisnah da Maigado da se lokacin ta ɗago kanta daga pressing phone ɗin da take. Zama ne irin na cikakku Kuma gawurtattun ƴaƴan da jinin sarauta ke circulating through their veins, tsantsar izzar dake tare dashi da kwarjinin da zaman ya ƙara masa yasa duk suka kau da kansu a kanshi kusan a tare, juyawa tayi ta haye saman ta yayinda su Mommy duk sukai wani irin shiru kafin ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta ƙawayen ta na rufa mata baya. Barin dannar wayar Maigado tayi ta maida full attention ɗin ta kan Saraki da yake nan zaune idanun sa a lumshe, ko da be buɗe ido ba yana jin yawon idanu cikin jikin sa hakan yasa ya buɗe idanun towards direction ɗin da yake jin gaze ɗin, a bazata hakan ya zowa Maigado shiyasa har ya kamata dan bata tsammani ze buɗe ido lokacin ba, kallo ɗaya yayi mata ya janye idanun sa ya sake lumshe su itama kuma da sauri ta maida naga kan waya sedai ta kasa cigaba da abinda take. Ƙarar takalmin Kisnah yasa Maigado kai kallon ta can, har tayi wanka ta canja rigar jikin ta zuwa wando three quarter da t-shirt mara nauyi ta saki gashin kanta da bata samu zuwa saloon yau dan gyarashi ba, ɗauke kanta tayi zuciyar ta na ɓaci ta maida kan wayar ta sedai ta kasa haƙura hakan yasa ta shiga satar kallon dukkan su biyu dan sosai taji baƙin cikin fitowar Kisnah da wannan shigar da haka kawai zuciyar ta ke faɗa mata zata iya burge Saraki da ita. Zama kan one sitter gefen Saraki Kisnah tayi kafin ta saka hannu ta ɗauke files ɗin da ke kan cinyar sa da yasa ya buɗe idon sa kan ta, ajiye files ɗin tayi gefen ta kafin ta ɗauko bundle ɗin 1k ta ɗora masa inda ta ɗau files ɗin, kallan kuɗin yayi kafin ya maida kanta cikin sigar kallon tambaya "Gashi nan ka siya kayan amfanin da babu a ɗakin ka ka kuma ƙara kaya, haka ake bawa kowani sabon ma'aikaci da ze Fara aiki a gidan nan, ba wai dan raini ko wani abu ba se dan kyautatawa". Da farko so yayi yace baya so sedai yadda ta ƙare bayanin yasa ya fasa hakan wanda da alama ta fahimci yana son rejecting shiyasa ta ƙarasa a tausashe. "Thanks". Ya faɗa yana miƙewa bayan ya ɗau kuɗin itama ta ce masa "thanks also for the drive". Fita yayi yana mamakin ta a ranshi, jiya ma haka tace masa thanks yau ma gashi ta kuma, to akan me zata gode masa bayan aiki yake mata kuma biyanshi zata yi, a karo na biyu ya kuma ganin hali me kyau tattare da ita. Khamees ya samu da batun ɗakin kamar yadda yace ya kuwa rakashi part ɗin ma'aikata har ƙofar da aka saka tag ɗin sunan sa Ahmad dake can nesa da part ɗin su Kisnahn. Bin ɗakin yayi da kallo cikin yaba tsarin ɗakin, ƙatuwar katifa ce me matuƙar taushi sabuwa dal cikin ledar ta se three sitter sofa daga gaban katifar kalar ash ita ma me kyau da ita, madaidaiciyar wardrobe me murfi biyu itama kalar ashe da ratsin fari a kusurwar ɗakin se curtains Suma Ash color se ƙaramar plasma TV dake jikin bango tare da kayan DVD da DSTV a ƙasan ta kan kyakkyawan ƙaramin glass TV stand, sosai yaji daɗin ganin har da Ac akwai a ɗakin dan baya shiri da zafi ko kaɗan. Ƙarasawa yayi ƙofar toilet da ya hanga acan gefe ya buɗe ya shiga, fari tass ɗin tiles ne a banɗakin tun daga ƙasa har jikin bangon sa gaba ɗaya sedai na ƙasan manya ne na jikin bango kuma madaidaita, ba wani tarkace bane cikin toilet ɗin illa hand shower, water closet, tap, sink, mirror, bucket se ƴar cupboard me ɗauke da towels masu kyau, sabon brush and new sponge, se cleaning apparatus a gefe. Ƙaramar low cut broom ɗin ya ɗauka ya zuba car wash me ƙamshi da ya gani cike cikin jarkokin faro manya har uku a ƙasan ya shiga sake wanke toilet ɗin duk kuwa da cewa a wanke yake, seda ya tabbatar yayi masa yadda yake so kafin yasa ruwa ya ɗauraye sannan ya tuɓe ya yi wanka da ruwa dan be siyo soap ba kuma babu sabulu a toilet ɗin, ɗaure da ɗaya daga cikin sababbin towel ɗin ya fito ya zauna kan sofa, wani ƙaramin towel da ya ware yanzu dan goge jiki yasa ka ya tsane ruwan jikin sa kafin ya maida jeans da rigar da ya cire ya ɗau key ya fita zuwa motar da suka fita jiya da ya kwaso kayan sa a ciki. Fito da kayan yayi da gaba ɗaya yayi wa leda biyu dan basu da wani yawa, kala goma ne gaba ɗaya se toothpaste ɗin sa da sabulai da mayukan sa ya kai ɗaki kafin ya dawo dan rufe motar idanun sa suka sauka kan shopping bags biyun da ta bari cikin mota ta kuma ce masa nasa ne, kamar ya bar su ya maida mata se kuma kalaman Mami suka dinga dawo masa kan sa kamar lokacin take faɗar su "Ka Dena irin haka Saraki, sheɗan kawai ke maida alkhairi in an masa, ko mai ƙanƙantar abun da aka baka ko kuma girman shi ka karɓa ko dan wanda ya baka yaji daɗin baka raina shi ba balle abin hannun sa ko da bazaka yi amfani dashi ba kuma kayi godiya dan ya tabbatar kaji daɗi kuma ka yaba, ita kyauta tana zuwa ne da kyautatawa bawai raini ba kamar yadda kai kake gani, wanda ya baka kyauta bawai ya raina ka bane a'a yayi appreciating wani abu da kayi masa ne ko kuma dan ƙauna kawai dan akwai mutane da yawa a gari amma be bawa Kowa ba se kai , ka min alƙawarin zaki dinga karɓar kyauta indai bata zo ta sigar raini ko isgilanci ba". Be manta kalaman da ya faɗa wa Mami ba a lokacin which is "I promise you Mami nah". Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaukan bags ɗin ya nufi ɗakin dan be ga raini ko isgilanci tattare da Kisnah ba, wardrobe ɗin ya buɗe ya shiga jera kayan sa wanda be daɗe ba dan set goma ne, jeans da t-shirt ya cira ya saka kafin ya koma ya fara jera kayan da Kisnah ta siya masa, ko bai faɗa ba Allah ya sani kayan sun burge shi dan irin su ya saba sawa da ma wanda suka fisu, designer Kaya ne masu matuƙar tsada da kyau ta siya masa har kala sha biyar se wrist watch guda uku, silver, golden se black. Godiya da addu'a yayi mata sosai a zuciyar sa tare da mata fatan shiriya daga dukkan abinda take aikatawa na ba daidai ba, kan katifar ya kwanta bayan ya shimfiɗa bed sheet ɗin da ya gani cikin wardrobe which is so clean se ƙamshi ma yake. Kwanciya yayi cikin tunanin Mamin sa da ya saka shi gaba da yake ta faman dannewa sedai yanzu kam ya kasa, shaƙuwar sa da Mami daban ce da ba kowa ze gane ba, ƙaunar da yake mata bazata faɗu, itace ƙawar sa, yar sa, ƙanwar sa, haka kuma mahaifiyar sa shiyasa yanzu duk wanda ya sanshi a baya ya ganshi yanzu yasan ƙarfin hali ne kawai yake yi amma he's not well. Haka ya cigaba da kwanciya har lokacin da akai knocking ƙofar shi ya tashi ya buɗe, ma'aikaci ne sanye da uniform ya ɗora rigar girki a kai se apron a kansa da zata shaida ɗaya daga cikin cooks ɗin gidan ne, miƙa wa Saraki plate ɗin hannun sa yayi yana sakin masa murmushi, karɓa yayi yana sakin masa murmushi shima kana ya koma ɗakin tare da rufe ƙofar. Kan sofa ya zauna hannun sa riƙe da plate ɗin yana bin abincin da kallo kafin yasa hannu ya janye foil paper da aka rufe plate ɗin dashi, fried rice ce da ta yi kyau sosai a ido se rabin kaza a gefe da spoon shima nannaɗe cikin tissue, ɗaukar spoon ɗin yayi tare da ajiye plate ɗin gefe bayan ya maida foil ɗin ya rufe, toilet ya shiga ya sake wanke spoon ɗin thoroughly kafin ya koma ya zauna ya ɗau plate ɗin, bisimilla yayi ya fara cin abincin a nutse wanda yake nan ba yabo ba fallasa, wato dai ba wani daɗi gare shi sosai ba amma fa baza ace bashi da daɗi ba, ƙarar waya da yaji yasa yayi pausing hannun sa riƙe da spoon ɗin da ya ɗebo abincin, jin ƙarar sosai a ɗakin yasa ya ajiye spoon ɗin ya miƙe tsaye ya fara neman inda wayar take dan ba tasa bace take ƙarar dan ita tana gefen sa. Can gefe ya hango landline kan wani ƙaramin fridge da be lura dashi ba tun da ya shigo, ƙarasawa yayi ya ɗau wayar tare da yin sallama, Muryar Kisnah yaji cikin maganar da ta sa ta kira shi batare da ta amsa masa sallamar ba. "You get ready we're going out tonight, pls help me check if one dark blue car of mine is clean". Ajiye wayar yayi bayan ya gama sauraren ta batare da ya amsa mata ba dan shima bata amsa masa sallamar da yayi ba ai, komawa yayi ga abincin sa ya ƙarasa cin iya yanda ze iya dan shi kam a dole yaci abincin dan shi fa be san wani abinci related to foreigners, yafi ganewa natural traditional dishes ɗin mu na Hausa shiyasa Mami da kanta take masa girkin sa. Fridge ɗin ya buɗe ya ɗau bottle water da ya gani batare da ya kalli drinks ɗin wajen ba sannan ya fita duba motar da tace, its clean amma dai yace a sake goge ta kar tace ba'a yi mata daidai ba. Ɗakin ya koma ya zauna a sofa looking at he's watch dan ganin ina lokacin sallah yayi, sedai to his utmost surprise se ma yanzu ƙarfe ɗaya yayi, alwala ya shiga toilet yayi kafin ya fita zuwa masjid ɗin da ya gani gaba da gidan, sallar Azahar yayi tare da azkhar ɗin bayan sallah kana ya dawo gidan, bacci yake son yayi sosai kafin la'asar dan kansa wani irin ciwo yake masa wanda yasan ba komai bane yaja illa damuwar da yake ciki da yawan tunanin da yake ga kuma ayyukan da jikin sa be saba da su ba duk da wata kusan biyu kenan da yake yin wasu kafin wasu su ƙaru jiya...................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 16 (8/8/2022 6:49 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣6️⃣ ________________________📖 Sallar Isha ya idar a masallaci amma be dawo ba se da ya gama duk tasbih ɗin da ya saba, fitowa yayi a hankali ya saka takalmin sa ya nufi komawa gidan yana me duba agogon hannun shi, its 8:45 pm. Yana shiga compound wayar da aka kawo masa ɗazu me kyau da ita madaidaiciyar Android kamfanin Samsung matsayin wayar da ake bawa kowane ma'aikaci da sim da komai ta fara ringing, ɗan kallon screen ɗin yayi kafin yai sliding ya amsa "Ya Saraki ka fito da motar gani nan fitowa" "Okay" yace yana ending call ɗin tare da ƙarasawa ɗakin sa ya ɗauki key ɗin motar da kuma kuɗin da ta bashi ɗazu dan yana son yin siyayya. Warming up motar yayi kafin ya matsa da ita kusa da flat ɗin nasu ya kashe yana jiran fitowar ta. Cikin wata dark blue ɗin guntuwar gown iya ƙasan gwiwa kaɗan ta fito, rigar tasha adon silver stones masu matuƙar kyau se ɗaukar ido take tana walwali, gashin kanta parke cikin blue ribbon se ta sake shi ta baya kana ta ɗora p-cap akai, kyakkyawar farar ƙafarta kuwa sanye take cikin dogon blue Hill shoe da igiyoyin sa suka kai har kusan rabin ƙaurin ta, kyawawan hannun ta saye da agogo shima dari blue se ɗayan da ta sakawa siririyar sarƙar hannu ta kuma ƙawata yatsun ta da zobuna. Tun da ta fito ƙamshin ta ya cika ko ina a harabar gidan har ya kai ga hancin Saraki da ya saukar da glass ɗin side ɗin sa, girgiza kai kawai yayi yana mata addu'ar shiriya dan tabbas saka irin waɗannan turaren dole ya haddasa fitina a ban ƙasa. Tun a ɗazu da ta kira shi da Ya Saraki yaji wani irin abu ya tsarga masa, ba abun da yazo ransa a lokacin face ƙanwar sa ɗaya tilo da ita kaɗai ce mace dake kiran sa da sunan, hakan yasa yaji a ransa kamar ita ɗin ce ta kira shi sedai yasan ba itan bace, tun a lokacin yaji a ransa wata ƙanwar ce ya samu, ƙani, ƙanwa, yaya mace, wa namiji kai har ma iyaye ana iya samun su a duniya base wanda kake da blood relation ne kaɗai family ba, a hadisai da ayoyi da dama Allah da Manzon sa sun nuna mana so da ƙaunar juna, sun nuna mana duk wani musulmi ɗan uwan musulmi ne dan haka ya amshe ta as ƙanwa kamar Miemie da suka fito ciki ɗaya da baze iya barin any harm yaje gate ta ba, haka baze so yaga rayuwar ta ta lalace ba, he'll treat her as an elder brother that will protect his little sister ko ta wane hali sedai yasan for now ba komai zece dole ze yi magana kan se ta gyara ba dan abun ya riga ya shiga jikin ta da dole se an bi a hankali. Cikin wannan tunanin yayi nisa da har be san ma ta ƙara so har ta shiga ba se da ta bubbuga bayan kujerar da yake kai tana kiran sunan sa "Yaa Saraki mana, am late fa". Buɗe ido yayi a kanta kafin ya bi shigar jikin ta da ido sannan ya janye ya maida fuskar ta da ba wata kwalliya banda lip balm se mascara da eyeliner, kauda Kai yayi ya maida gaban motar yasa hannu ya kunna sannan ya nufi gate suka fice, seda suka hau titi sosai kafin ya ɗan kalle ta a kaikaice "Zaki makara? Makaranta zaki je?". "Wane irin makaranta a wannan late hours ɗin, clear screen cinema za muje". Jijjiga kai kawai yayi ganin bata ma fahimci baƙar magana ya faɗa mata ba, be kuma cewa komai ba har suka ƙarasa, be shiga parking lot ba ya tsaya a gefe kaɗan da gurin dan fita yake son yi "Ya ka tsaya a nan, kaga fa zan daɗe kawai ka shigar da ita parking lot kar muyi blocking wasu". Hakan da ta faɗa se ya tuna mata dasu Abeed da gaba ɗaya ta manta da batun su wanda ta san for sure suna nan a kulle dan in har bata sake su ba ba wanda ya isa yasa a sake su, dole yau insha Allah zata sa a sake su dan badan ta manta ba da tun kwana uku da ka masu zata sa ayi freeing din su. "Zan je Mall in dawo, ko ba daɗewa zaku yi ba?". Ya faɗa mata "Gaskiya zamu daɗe ina tunanin ma se to 1 Film ɗin ze ƙare, kasan fa Film biyu zan kalla, Film ɗin sharukhan me suna Ra one se kuma na Ajay devgan shikuma sunan sa Action Jackson". Yadda take maganar cikin farin ciki ze shaida maka she drive pleasure talking about Hindu films talkless of watching it. "You enter, Bari inje in dawo". "Safe drive". Ta faɗa tana fita daga motar bayan ta buɗe safe ɗin ciki ta ɗau ledar crackers biyu, juya motar yayi ya fita daga cinema ɗin yana bin titi hopping to see a nearby Mall dan baya so yayi nisa, wani madaidaicin mall da ya gano yasa ya ƙarasa yai parking tare da shiga, ɓangaren takalma ya fara shiga ya zaɓi masu kyau guda biyar kafin ya koma ɓangaren turare nan ma ya zaɓi madaidaita dan wanda yake amfani dashi da is worth 350k duk ɗaya shiyasa yanzu sedai manage. Kayan ƙamshin toilet ya siya ya haɗa kafin ya siya sabulan wanka da mayukan kai, a taƙaice dai 2k ce kawai tai ragowar cikin 100k ɗin da ya fito da ita. Payment yayi aka masa bagging kayan security suka kai masa mota ya shiga ya koma cinema, Yana yin parking ya duba watch ɗin sa only to see 9:50, he's wandering how he'll be waiting cikin mota har to one kamar yadda tace. Rufe glassan yayi gaba ɗaya kafin ya ƙure ƙarfin Ac ɗin motar ya saukar da kujerar sa baya ya kwanta sosai bayan yayi connecting wayar sa da Bluetooth ɗin motar ya saka karatun Alkur'ani mai girma in low tune, tun yana bin karatun har bacci ya sace shi . A can cikin cinema kuwa kallo suke yi hankali kwance oganniya a tsakiyar da'ira tana taunar crackers ɗin ta har aka kusa gamawa aka zo waƙar kusan ƙarshe, sedai me tace bata san zance ba lokacin da waƙar ta ƙare ai se a dawo da ita baya ta kuma kalla, kusan gaba ɗaya mutanen wajen sukai mata caaa kamar zasu cinye ta da baki suna faɗin bata isa ba suna da abun yi, sosai in charge ɗin cinemar hankalin sa ya tashi dan yana samu da Kisnah ba kaɗan ba ga kuma ƴan kallo da suka customers ɗin sa ne, ko da aka kira shi rarraba ido ya hau yi tsakanin su dan be san side ɗin wa ze ɗauka ba. "500k". Kisnah ta faɗa as the sum da zata biya in aka maida mata baya, da sauri wani matashi yace "1mil". "2 mil". Ita ma ta faɗa, shiru wancan yayi se wani ɗan magidanci da ya tashi da sauri "2.5 mil". Ya faɗa ganin yadda wancan yayi shiru "3 mil". Ganin kowa yayi shiru alamun ya sallama yasa dole aka maida mata baya ta kuwa miƙe ta hau cashe rawar ta ba tare da ta damu da mutanen dake wajen ba, wayar ta ta miƙawa Meenah tace tayi wa managern wajen transfer ɗin 3 million ɗin sa shikuwa se washe baki yake cikin farin ciki, irin haka na cikin dalilan da yasa suke son zuwan Kisnah wajen. Ana gama Ra one aka fara Action Jackson, kamar dai yadda ta faɗa basu tashi ba se five mins after one, ita kanta a lokacin a gajiya take sedai tana cike da farin cikin kallon da tayi da ma na sa'insar da suka yi da mutanen. "Amma Kisnah 3 million sabida kawai maimaita kallon waƙar 5 minutes? Haba this is way too much". Hameedah fa ta fara kaita ƙarshe da iskancin da take mata fa, bata manta jiya yadda ta ringa kushe Ya Saraki ba har da wani kiran shi mere driver, dole ma ta taka mata birki wallahi. Ƙanƙance golden brown eyes ɗin ta tayi cikin duban Hameedah "Meke damuwar ki da rayuwa ta ne Meedah, batun yau ba fa kike min shisshigi da rainin hankali ba, ko dan kinga ina ƙyale ki shiyasa kika sami guts ɗin faɗa min kowace banzar magana tazo bakin ki, yanzu da na biya 3 million nawa kika cika min, nawa nai maula ina kuka Hajiya Hameedah me kuɗi taji tausayi na ta bani na cika, kin san i hate nonsense ko, to wallahi tun yanzu ki shiga hankalin ki dan ina raga miki ne being my friend if not ke in an ce kiyi dering Kisnah You won't even start, mtsww". Da sauri Leekha da Meenah suka fara bata haƙuri yayinda baƙin ciki da ɓaci rai ya cika Hameedah, ganin ta dan Kisnah ta fisu kuɗi da kyau yasa take musu rashin mutunci yadda ta ga dama sedai ba yadda zata yi haka ta bata haƙuri itama kafin ta juya wajen motar ta tashi ga ta wuce gida. Tsaki Kisnah ta raka bayan motar Hameedah dashi kafin ta ɗagawa su Meenah hannu alamun bye, da sauri Leekha ta tare ta "Amma dai zaki wajen Surry gobe ko, kinga duk yau baki leƙa ta ba". "Munyi waya da ita ɗazu kin san tana da fahimta so i brief her about that assignment, dole ba inda zani gobe saboda wuni zanyi kan shi in gani in Allah zesa in iya yi". "Hakane, Allah ya sa ki iya ɗin". "Ameen bye, Meenah ki gaida Momma, Leekha ki gaida Adda". "Za su ji insha Allah, sweet dreams Queen". Murmushi ta sake musu kafin ta ƙarasa wajen motar ta, knocking tayi ta ji shiru, ta sake yi nan ma shiru, wannan karon dagewa tayi ta ƙwanƙwasa da ƙarfi da yasa Saraki farkawa daga baccin da yake yi da ba wani daɗin sa yake ji ba dan a takure yake. Zama yayi sosai hana gyara rigar jikin sa da ta tattare kafin yayi unlocking motar yana tada kujerar da ya kwantar, jin ƙarar buɗewa yasa ta buɗe murfin ta shiga tana faɗin "sannu". Which he answered using body language. Rufe ƙofar tayi yayin da ya ɗau goran ruwan dake gaban motar ya fita ya wanke fuskar sa dan wartsake wa sosai, ajiye robar yayi inda ya ɗauka ya ciro kyakkyawan farin handky ɗin sa a aljihu ya goge fuskar sa kana ya rufe motar ya tashe ta tare da yin reverse ya fita daga cinemar. Tafiya suke shiru kamar kurame se karatun Alkur'ani da har yanzu yake yi be kashe ba, time to time yake ɗan kallon ta ganin yadda ita kaɗai take sakin smiles kamar wata zararriya sedai be yi magana ba har suka kusa ƙarasawa gida, "Please yi parking gaban wancan restaurant ɗin". Ɗan kallon restaurant ɗin gaban su yayi kana yayi parking kamar yadda tace, fita take neman yi sedai tuni ya dannawa motar lock hakan yasa ta kasa buɗe murfin. Juyowa tayi ta kalle shi irin na tambayar why ɗin nan, haɗe rai yayi yana kallon ta shima "A haka kike nufin zaki shiga wannan gurin?". Duban jikin ta tayi taga dai bata yi komai ba, fes take kamar yadda ta baro gida dan haka ta maida idanun ta kan shi "Ai banyi datti ba ko". "Bani kuɗin ki faɗi me zaki siya". Ba tayi musu ba ta miƙa masa wayar ta "Ban fito da kuɗi ba yau, ga wayata nan ka musu transfer ta nan, 7139 is the pin, kilishi nake so na 15k guda biyu kaga 30 kenan ko?, Se strawberry ice cream cup huɗu, ayi ledan wrap ɗin kilishin with two cups ko wanne". Gyaɗa mata kai kawai yayi tare da double tapping phone ɗin dan duba in da security sedai babu dan haka yayi unlocking car ɗin ya fita. Sake kallon kanta dan ganin ko dai dagaske akwai abinda tayi da yasa yace bazata shiga wajen ba sedai har lokacin bata ga komai ba, shrugging kafaɗarta tayi koma menene tunda dai ze siyo mata ai shikenan. Kamar yadda tace haka ya siyo, two wrap ɗin kilishi se four cups of strawberry ice cream, buɗe bayan motar yayi ya saka kafin ya shiga mazaunin sa yana miƙa mata wayar ta, karɓar tayi tana faɗin "Thanks Ya Saraki". Smile ya sake mata da yasa ta zaro idanun ta tana juyowa gaba ɗaya ta zubawa fuskar sa ido "Did you just smile Ya? Oh my God kaga kuwa yadda kayi kyau, Lord of universe ni Kisnah". Sosai ta bashi dariya yadda tai maganar wholeheartedly, yanzu ya kuma fahimtar wani abu a tare da ita, she's Frank and open, tana yin abu da iya gaskiyar ta ne ko me za'a yi mata kuwa, kalli dai yanzu abinda tayi kamar wata yarinya ƴar 12-13 years. "Dan Allah smile again Ya Saraki, ina son sake ganin your cute dimple pls". "Shut up, I don't smile you're dreaming". Kwaɓe fuska tayi "Dreaming without sleeping, Allah nidai I see you smile". "See, mafarki kawai kika yi, so nawa mutum be yi bacci ba yake mafarki ma, i too experience that sometimes". "Ban taɓa ji ba amma, kenan nima yanzu nayi mafarkin kana murmushi, amma gaskiya fa kayi kyau a mafarkin". Girgiza kai kawai yayi ya cigaba da tuƙin sa yana tunanin shekarun ta nawa da take da rashin wayo haka, kalla yadda yanzu yayi fooling ɗin ta kuma ta yarda. 'she's just a little spoiled girl'. Ya ayyana a ransa. Cikin haka suka ƙarasa gida ta fito daga motar tareda buɗe baya ta ɗau leda ɗaya wanda ke ɗauke da kilishin da two cups na icecream ɗin ta bar ɗayar a ciki "Ga naka nan Ya, thanks and Good night". Ya Masa rasa me zece se kawai ya tsaya yana kallon ta, da gaskiyar mutane da ke cewa baka sanin halayyan mutum seka mu'amalan ce shi, kamar dai yarinyar nan, a kallon farko mutum ze concluding zata yi girman kai da ɗagawa, rashin mutunci da dis respect, wanda shima a haka ya kalle ta da farko, sedai yanzu sam ba haka yake gani tattare da ita ba. Maganganun Inusa ne suka dawo masa kansa ranar da ya kawo shi gidan, gyaɗa kai yayi cikin yarda da abinda Inusan ya faɗa kafin ya sa hannu ya ciro ledar ya ɗauka ya wuce ɗakin sa. Ajiye ledar yayi ya ciro icecream ɗin ya saka a fridge haka kilishin dan baya jin wata yunwa yanzu, komawa kan sofa yayi ya zauna tare da jawo wayar da aka bashi yai mata texting "thank you"....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 17 (8/8/2022 6:50 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣7️⃣ _______________________📖 Daga wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugun sa se ƙarami a kansa da yake tsane gashin sa har ya tabbatar ya gogu kafin ya cire ya ajiye, kan mattress ɗin sa ya zauna tare da janyo jakar da ya zuba kayan mayukan sa ciki ya fito da wanda za shafa ya shafe jikin sa da shi kafin ya ciro mayukan gashin sa kana ya miƙe ya ɗauko madaidaicin mirror ɗin da ya siya tun yana zaune a shago ya ajiye kan sofa ta yadda ze iya ganin komai sannan ya shiga mulke gashin kan sa da su ɗaya bayan ɗaya kafin ya ɗau comb ya shiga taje shi kana yayi styling ɗin shi, sosai gashin yayi kyau ya kwanta kamar wani Balarabe. Wardrobe ya ƙarasa ya ciro wata Black shadda da ya ɗinka tun yana kasuwa tare da Alh Musa, ba wata me tsada bace amma ba ƙaramin kyau tayi masa ba kamar ka sace shi ka gudu, links ɗin sa ya saka a hannun rigar tare da na wuya, farar hular da ya siya yake haɗa shaddar da ita ya ɗauko yasa tare da takalmin da shi kuma Alh Musa ne ya siya masa ranar da ya fara saka shaddar yace ga takalmin ya haɗa dashi se ya fi kyau. Fatabarakallah Ahsanul khaliqeen, kyan da Saraki yayi cikin shaddar ba me faɗuwa da baki bane just imagine it yourself, turarukan da ya siyo jiya ya jawo yana feffesawa dan jin ƙamshin kowanne har ya sami wanda yayi masa ya feshe jikin sa gaba ɗaya kafin ya ajiye ya ɗau daddumar da ya ɗora kan sofa tun kafin ya shiga wanka ya feshe ta da turare itama dan yau juma'a, wayoyin sa ya kwasa ya fita tare da ɗiban canjin 2k ɗin sa na jiya ya fita bayan ya saka wayoyin sa a aljihu. Sosai ma'aikatan gidan suka dinga yaba kyan da yayi shifa'u sedai yayi musu murmushi tare da faɗin ya gode har ya fice daga gidan pray mat ɗin sa rataye kan kafaɗar sa. ****************** "Wannan gayun se ina kuma auta". Murmushi Laylah ta saki jin auta da ummah ta kira ta dashi wanda se tana san tsokanar ta take faɗa, juyawa tayi ta dubi umman da ke zaune kan stool ɗin mirrorn ɗakin Laylahn "Allah umma yau tsokana kike ji kawai, bayan kin san zance gaida Mami ne". "Oh na manta, ashe za'a je gaisuwar surukai ne, to ai ba kya tafi haka ba dama ina da saƙo wajen gimbiyar bari in baki ki tafi mata dashi". Umma ta faɗa tana fita daga ɗakin yayinda ita kuma ta cigaba da gyara ɗaurin ɗankwalin shaddar da take yi, sosai ta ɗaura shi ya zauna kai kace kafa mata shi akai, kallon kanta take yi tun daga sama har ƙasa tare da yabawa da adon nata, turare ta ɗauka me sanyin ƙamshi ta fesa dan bata manta ba Ya Yarima ya taɓa mata faɗan saka turare me ƙarfi. Mayafi ta ɗauka da ya hau da kayan jikin ta ta yafa tare da fita daga ɗakin nata daidai lokacin umma ta fito daga nata ɗakin hannun ta riƙe da leda me dan girma ta miƙa mata "Gashi ki kai mata ki kuma ce ina gaishe ta sosai da sosai". "Insha Allah umma nah, se na dawo". "Allah ya dawo dake lafiya autar umma kuma surukar gimbiya". Da sauri Laylah ta fice daga gidan cikin jin kunyar umman fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin surukar gimbiya da umma ta kira ta dashi, driver ta saka ya kaita sashen gimbiya Haleematu dan da tazara sosai tsakanin sashen matan sarki dana waziri wanda ita ɗin ɗiya ce wajen wazirin sarki Muhammadu Hasheem II. Da sallama ta shiga turakar gimbiya Haleematu dan tuntuni ta zama ƴar gida da bata neman iso kafin shiga, kan kilisar ta ta sake ta zaune cikin kyakkyawan adon ta dake ɓoye ainahin shekarun ta ya sa ayi mata kallon batakai haka ba alhalin tana cikin shekarun dattijan taka ne yanzu. Da farin ciki gimbiya Haleematu ke amsa gaisuwar Laylah da ta zube gaban ta, ba ƙaramin farin ciki take yi ba a duk lokacin da tayi tozali da yarinyar dan tana ganin ta ne kamar Sarakin ta wanda ba dan wannan ƙaddarar ta sharrin maƙiya ba da tuni yanzu ana batun bikin su ne, Allah ya sani tana son yarinyar saboda irin soyayyar da take gwada wa Sarakin ta wanda ita in har zaka so Saraki to fa ka gama mata komai a duniya. Baya ga haka ita ɗin ɗiyar aminiyar ta ce da bata da kamar ta a duk faɗin garin Giwa da kewayen ta, ga kuma babanta da ya kasance ɗan uwan me martaba kuma wazirin sa me dattako da sanin ya kamata. Karɓar ledar hannun Laylah tayi kana ta sallama kuyangin ta suka shiga hira da Laylahn irin hirar uwa da ɗiyar ta har lokacin Sallah yayi, ko da gimbiya ta shiga yin Sallah ɗakin ta itama Laylah ɗakin kusa da na gimbiyar ta shiga ta gabatar da Tata sallar kana ta fito ta wuce personal kitchen ɗin gimbiyar dake nan falon ta. Abinci ta dafa mata me rai da lafiya tare da lemukan gargajiya da ta san gimbiya tafi son irin su dan ƙarin lafiya da ƙarfin jiki kana ta kwaso ta jera su kan ledar cin abinci da ta shimfiɗa gefen kilisar gimbiyar. Ko da Mami ta fito taga aikin da Laylah tayi ba ƙaramin daɗi taji ba ta dinga saka mata albarka a ranta tana fatan Allah ya dawo mata da Sarakin ta lafiya ayi bikin su dan fa tabbas ɗan nata be fa mata bayan Laylah. Cikin so da ƙauna da kuma shaƙuwar dake tsakanin su suka ci abincin tare suna ɗan taɓa hira jefi jefi har suka gama Laylahn ta kwashe kwanikan zuwa kitchen ta kuma wanke su tare da gyara kitchen ɗin tas. A ranar kam ma'aikatan sashen gimbiya hutu suka yi dan Laylah ce ta sake gyara sashen tare da haɗe shi da sassanyan turaren wuta me shiga rai kana ta shiga ɗakin gimbiyar ta gyara mata wardrobe kafin ta gyara ɗakin gaba ɗaya. Waɗannan halayen na Laylah ke kuma ƙara wa gimbiya son ta Dan duk sanda tazo gidan tofa bata da zama ta dinga hidima da gimbiyar kenan har se ta koma nasu kafin ta huta wanda yanzu ma haka ne. Ko da ta tashi tafiya kaya sosai mami ta haɗa mata har ledoji biyu tare da godiya da sa albarka har suka rabu. Cikin farin ciki ranar Laylah tayi bacci wanda duk take gidan Mamin hakan ke faruwa dan sosai hankalin ta yake kwanciya da ƙaunar da Mamin ke mata har take ji a ranta bata da sauran matsala sets jiran dawowar Saraki dan ta san tabbas fa bashi da wata mata se ita Laylahn gimbiya. *********** Zaune take cikin kyakkyawan garden din ta ta barbaza takardu a gefe gabanta kuwa laptop ɗin tace haka kuma hannun ta riƙe da wayar ta, wannan zaman duk na yin assignment ɗin CON005 ne sedai har fiye da mintina Talatin da zaman nata ba abinda ta fahimta haka ko kan pen bata saka a paper da sunan rubutu ba, dafe kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya cikin tsananin damuwa dan zuwa yanzu kam bata san ya zata yi ba wallahi, tayi tayi amma ta kasa gashi ita bata san wani senior ɗin su ba a department ɗin law balle taje ko ɗora ta a hanya ayi, hasalima ko ƴan level ɗin su ba kowa ta sani ba balle ayi maganan saman su. Cikin karaya ta miƙa hannu ɗan sake duba question ɗin a karo na ƙarshe taga ko zata fahimci me za'a yi dan Allah ya sani daga wannan karon in har bata gane ba to ta haƙura ta bar wa Allah kawai, ta tafi da carryover ɗin ta gyara next year. Zaro takardar tayi se taga wasu takardu sun faɗo tare da ita, ɗan tsira wa takardun ido tayi ganin su ɗauke da rubutu alhalin ita tasan bata ajiye paper me rubutu ba se kuma ta kauda kanta ta ɗau wadda take buƙata a lokacin sedai ganin ta itama cike da rubutu yasa ta ɗan yi turus gaban ta na faduwa kafin kuma ta shiga warware ta da sauri har hannun ta na rawa. Cikin sauri ta shiga bin paper da ido wadda ta tabbatar tata ce dan ga sunan ta da ragowar information ɗin ta da ta rubuta nan jikin paper, kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi jikin ta ya ɗau rawa kafin ta shiga karanta jerarren rubutun da akayi shi cikin ƙware wa layi bayan layi duk da kuwa takardar bame layika bace Dan plain sheet ce, tsaf ta karanci rubutun gaba da baya sedai ganin be ƙare ba yasa da sauri ta ɗauko papers ɗin da suka faɗi ɗazu ta hau neman continuation ɗin ta ɗora karatun, wasa wasa nan da nan ta gama karantawa kuma se lokacin ta fahimci me malamin ke nufi amma saboda tsabagen mugun ta yadda yayi twisting question ɗin ba za ka taɓa kawo abinda yake nufi ba kenan. Tsananin murna ne ya kamata har da hawayen ta sosai ta ninke takardun ta maida cikin textbook ɗin ta se kuma ta shiga tunanin waye ya amsa mata question ɗin, ita dai in bata manta ba har jiya da ta shiga test bata rubuta ko A ba bayan question, kuma tun da ta fita da littafin ba wanda ta bawa haka kuma tun da ta dawo dasu ta kai ɗaki bata kuma ɗauko su ba se yanzu haka kuma ba wanda ke shigar mata ɗaki balle tace. "Yaa Saraki". Sunan yai ringing a mind ɗin ta, ɗan shiru tayi kafin kuma ta shiga gyaɗa kanta cikin yadda da shi ɗin ne yayi mata dan tun a motar ta bar littafin da zata shiga test se jotter kaɗai ta shiga dashi ta koya wa su Meenah abin da tayo research haka kuma da ta shiga Company a mota ta bar su gaba ɗaya wanda tun da ta ɗebe su daga motar da suka dawo daga Company bata kuma fito dasu ba se yanzu, to in bashi bane waye yayi mata, aljanu ko wa? Kai shine ma, wallahi shine. Da sauri ta kwashi takardun ta fita daga garden ɗin ta shigo ta main falo kafin ta sake fita da gudu gudu ta ƙarara compound ɗin tana ƙwala masa kira, sosai ta ke kiran shi not minding yadda ragowar workers suke binta da kallo, Isa me bawa flowers ruwa ne ya shaida mata ai yaje masallaci, bata ji daɗi ba dan ta so ta sake shi yayi mata confirming shine ta kuma gode masa sedai zata jira ya dawo. Juya wa tayi zata koma ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo da sallama a bakin sa, da sauri ta juya dan da ɗan karfi yayi sallamar hakan yasa itama ta ji, da gudu ta nufe shi wanda shi dan be lura da tahowar ta ba se ji yayi an faɗa kan sa da ƙarfi, ƙamshin turaren ta ne yasa ya gane ita ce ya kuwa yi saurin janye jikinsu a yana istigfar a ransa yan kuma haɗe fuska a fili. Sakin baki tsirarun ma'aikatan dake kaikawo a compound ɗin suka yi suna bin su da kallo kasancewar da yawa sun tafi sallar juma'a, bata ko bi ta kan su ba ta ɗago tana kallon Saraki da ya haɗe rai cif sedai ita ko a kwalbar rigar ta dan bata ma san abinda tayi ya haɗe rai ba kuma dama ya saba kusan ko da yaushe haka yake haɗe rai in Yana tare da ita so shiyasa ma bata wani damu ba. "Yaa kai kayi min assignment ko, daama wallahi na kasa yi kaga tun da safe nake zaune amma ko fahimtar question ɗin ban yi ba, Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ya ja da ran iyayen ka, Nagode sosai, kai ban ma san ta ya zance maka Nagode ba wallahi". Ta faɗa sounding very very happy, addu'ar da tayiwa iyayen sa a ƙarshe ya sa ya ɗan sassauta haɗe ran da yayi yana kuma tausar kan sa da ita hakan a wajen ta bakomai ba ne and he promised to transform her so be kamata ya dinga haɗe rai haka ba dole ta nasiha ce yi mata musamman irin wannan lokutan da take cikin farin ciki. "Kalli, ƙafar ki ko takalmi babu kika fito". "Yaa bazaka gane farin cikin da nake ji ba, I feel like in yi ta rawa har se na gaji". "So in kikayi rawa se a san kina farin ciki kenan? Wat of kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ki gode wa Allah da yakawo miki ɗauki lokacin da kika yi giving up? A tunani na hakan se fi ko?". "Sure hakan zan yi riƙe takardun nan bari kaga in ma je inyi yanzu da sauri". Ta faɗa tana sama sa takardun a hannun sa kafin tayi cikin gida da gudu, girgiza kai yayi ya wuce ɗakin sa bayan ya sake haɗe rai ganin yadda gana ɗaya ma'aikatan compound ɗin suka saki aikin su suka maida hankalinsu kan su. Zama yayi kan sofa bayan ya shigo ɗakin ya cire hular kansa ya ajiye tare da pray mat ɗin kana ya wuce wajen fridge dan ciro ruwa se kuma ya ci karo da ledar kilishin jiya da cups ɗin icecream, fasa ciro ruwan yayi ya ɗauki cup ɗaya na icecream ɗin ya koma kan sofar ya shiga sha a hankali har ya ƙarar kafin ya jefa cup ɗin cikin ƙaramin waste bin dake gefen ƙofar ɗakin. Bum yaji an faɗo Masa ɗaki without taking excuse hakan yasa ya ɗago da sauri dan ganin waye se kuma ya ci karo da fuskar ta tana sake masa kyakkyawan smile, ɗan yamutsa fuska yayi dan Allah ya sani ya fara takura "Me kika zo yi nan". "Ya kai fa nazo nema, kaga tun da kayi min assignment ɗin dama akwai test ɗin da Zamuyi gobe kuma kaga akwai abubuwan da ban iya ba acikin shine na ɗauko ka koya min, laah na manta ban faɗa maka ba nayi sallar na godewa Allah kamar yadda kace". Ɗan dafe kansa yayi saboda tsabar surutunta da har ta fara samasa ciwon kai "Ki kwashi litattafan ki gobe na koya miki". "Yaa ai gobe ne test ɗin fa". "To kai na ciwo yake, ya zan miki ne, a'ah". Jikin ta ne yayi sanyi jin yace kan sa na ciwo, kwashe takardun ta da ya ajiye kan sofa a gefen sa tayi tare da juyawa zata fita "Sorry yaa, ban sani bane Allah ya baka lafiya". Dan tsaki yayi kafin ya dakatar da ita "A ina zamu yi karatun dan ba dai a ɗakin nan ba". Da sauri ta juyo cikin farin ciki se kuma ta ɗan rage fara'a "Baka ce kanka na ciwo ba". "Out in bakya buƙata". "To muyi a garden ɗina ko main garden gashi can ta gefen gate". "Meet me there a main garden ɗin by 3pm". Da sauri ta amsa da toh kafin ta fita cikin jin daɗi....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 18 (8/9/2022 8:06 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣8️⃣ ______________________📖 Kamar yadda yace haka ta sake shi a main garden ɗin gidan by 3pm suka soma karatun, ba ƙaramin yabawa ƙoƙarin ta yayi ba a zuciyar sa ganin duk abinda ya koya mata take ta ke kwashe shi dama akace kabar abinda zuciya ke so. Itama a nata ɓangaren haka tai ta yaba yadda yake mata bayani dalla dalla cike da ƙwarewa da sanin malamar karatu, sosai ta kasa daurewa har ta kai ga furta masa abinda yake yawo a ranta "Yaa wai ya akayi ka iya karatun mu haka sosai, ko dai kaima law ka karanta?". Shiru yayi mata a lokacin dan be san amsar da ze bata ba, be shirya sanar da wani asalin sa ba haka ne shirya tattauna personal life ɗin sa da outsider ba Kai koma insider ɗin ne he's not interested balle kuma ita da yanzu ne yake kan sanin wacece ita. "Amma kuma me yasa baka nemi aiki ba tun da nasan ka gama karatun ka da alama". Ta sake faɗa dan ta ɗau shirun sa as yes eh law ya karanta "I was withdrawn from the school". Ya sami bakin sa da faɗa dan alamu sun nuna Yes cikakkiyar lawyer ɗin za'a yi a wajen, shikuma ba ya san duk abinda ze kawo ta zarge shi kan abinda ba haka bane. "Eyya, so sad amma akan me?". Ta sake tambaya further Dan dai tasan baze yiwu ace akan bashi da ƙoƙari bane se dai something different da take son sani dan daga yadda yake mata bayani ta tabbatar a lokacin da yana makaranta ba za'a rasa sashi cikin gifted and talented students ba. "Don't wanna talk about it now". Gyaɗa kanta tayi cikin nuna fahimta kafin tace "I understand, maybe later ko?". Ɗaya mata gira kawai yayi dan ya fahimci in ba haka yayi mata ba ba ƙyaleshi zata yi ba alhalin taɓo maganar makaranta da karatu da tayi yasa yaji incident ɗin da ya faru ya dawo masa sabo Dan if not because of it da tuni i yanzu yana zaune in his own office handling office stuffs. Ba su tashi daga karatun ba se da aka kira Asr prayer hakan ma dan ya tashi ne ba yadda zata yi dashi dan in ta ita ne bata ƙi sukai har magrib ba yana koya mata tana kuma ƙiriniyar tambaye tambaye abinda babu ruwan ta be kuma shafe ta ba. Kashegari har bakin ƙofar lecture hall ɗin su ya kai ta tare da mata addu'ar fatan nasara abinda ya saka Kisnah dakatawa ta ƙura masa ido for a while kafin ta gyaɗa masa kai idon ta na kawo ƙwalla, abu ne tunda ta taso zata ce ba wanda ya taɓa damuwa da yi mata wato fatan alkhairi da nasara in zata yi assignment, test ko exam. To wa ma take dashi bayan kawu da family ɗin sa? Se ko abokan Abbu da ta manta rabon da ta taka ƙafarsa gidan su haka suma tuni suka dena damuwa da neman ta tun bayan wani cin mutunci da kawu ya yi musu lokacin da ya kaita England karatun primary ita kaɗai shikenan duk suka zare hannayen su a kanta. Kawu da matar sa Mommy kuwa.. hmmm.....bata masan ya zata kwatan ta su ba, ta wani ɓangaren the two are perfectly synonyms of each other, in other views Kuma su ɗin antagonist wa juna. Suna da matuƙar close similarities ta ɓangaren tsananin son kuɗi da kwaɗayi sedai suna da bambanci wajen tsananin son ƴaƴa da Mommy ke dashi da kuma hassadar da bata ma iya ɓoye ta, munafunci da baƙin ciki kuwa wajen Mommy har na siyarwa akwai, to taya ma zata yi wani tunanin samun fatan nasara ga matar da a kullum so take taga bayan ta ko kuwa ga kawu da kullum hankalin sa na kan yadda za sami kuɗi ta kowace hanya. Bayan su waye a cikin rayuwar ta? Ƙawayen ta, yes ƙawayen ta, taya zata fassara su? Da wa zata fara a ciki? Meenah da ba inda ta dosa a rayuwar ta ban da son holewa, ita dai tayi ta watsa ƙwayar da indai da ita to fa bata da matsala, ko kuwa da Leekha da tsabar shan giya har ya taɓa mata hanta seda akai mata aiki ko kuwa Hameedar da ƙiri ƙiri take iya fahimtar ƙyashi da hassadar ta cikin ido da Muryar ta har ma da ayyukan ta, dama dama Surayya, duk da mugun son mazan ta tana son karatu haka ta kan yi magana ta cikakkun masu hankali in taso bayan ita gaba ɗaya ragowar ukun ita ce ta sauya rayuwar su kan son karatu, a dole suke yin shi ba dan sun so ba shiyasa basa taɓa damuwa da wata matsala a karatun nasu wanda duk aka samu akasi ita ke yin tsayin daka har se ta tabbatar komai ya koma daidai kuma yana tafiya yadda ya kamata. Ajiyar zuciya tayi kafin ta saka yarda ta ɗauke ɗigon hawayen da ya sauka daga idon ta tana ƙarasa shigewa hall ɗin, sama sama ta gaida da ƙawayen nata kafin ta maida hankali kan littafin da ta shigo dashi wanda ta fara rage karatun exams ɗin da zasu fara ne next week insha Allah, tana jin su suna hira sedai bata ma maida hankali ba balle ta fahimci akan mene suke hirar. Cikin haka halitta ɗaya da zata iya kalla tace ta tsana a duniyar ta ya shigo cikin hall ɗin, ita bame damuwa da shiga shirin mutane bace shiyasa kafin kaji ta furta ƙi ko so abu ne da ake daɗewa sedai wannan ta furta masa kalmar ƙi da tsana so adadin da harshe baze iya ƙirgawa ba kuma ba dan komai ba se dan yadda yake nuna mata tsananin ƙiyasta ta ban mamaki da shigar da bawa ruɗani dan ko kallon banza bata taɓa gwada yi masa ba har se da shi da kansa ya siya da kuɗin sa, MALAM SAMINU kenan, shine malamin da ke ɗaukar su course ɗin CON005 haka kuma mutumin da ya ƙirƙiro wani assignment dan kawai don ganin ya kaita ƙasa sedai Allah Alhakeem baze taɓa bashi nasara ba a kanta. Cikin haɗa murya ɗaliban duk suka shiga furta gaisuwa a gare shi, be amsa ba se da ya ƙare musu kallo har idon sa ya sauka a kanta kafin ya ɗauke kai ya amsa musu, cikin ƙankanin lokaci suka shiga aiwatar da abinda ya tarasu wato lecture, ko da ya dakata shiru yayi yana bin su da kallo kafin ya fara jefo tambayar da kusan rabin ɗaliban suka ɗaga hannu sedai gaba ɗaya ya tsalle su ya nuna Kisnah da kanta ke ƙasa, taɓo ta Leekha tayi tana mata magana a hankali da yasa ta ɗaga kan ta ta dubi Leekhar sannan ta maida kan malamin, sake maimaita mata question ɗin yayi cikin son ganin ya tozarta ta takowace hanya. Miƙewa tayi ta fara magana amma mutumin nan yace baya ji dana haka ta fito gaban board, bata ƙi ba dan hakan a wajen ta ba sabon abu bane, takawa tayi cikin yanayin tafiyar ta yayinda kusan duk wani ido ya dawo kanta, doguwar riga ce me kamar baya sedai wannan anyi shaping ɗin ta ta yarda ya ta kamata tsam haka kuma me makon ta ɗaura ɗan kwali kan gashin ta da tayiwa bun se kawai ta naɗa shi in v style ta yadda tsakiyar ke waje kuma ba ƙaramin fito da fuskar ta ɗaurin yayi ba. Gaban board ta tdaya kamar yadda yace kafin ta fara bayani cikin nutsuwar ta har ta kai ƙarshe sedai ko kafin ta rufe bakin ta ya sake jefo mata wata haka yai tayi mata cikin son dole se ya ruɗa ta sedai har yanzu wannan mutumin be san wace Kisnah ba, ta kuma ji daɗi sosai dan yawancin tambayar da yake yi jiya sunyi makamantan su da Ya Saraki jiya shiyasa dole ya haƙura ransa a jagule da ɓacin ran rashin nasarar da yayi. Ko da ze fita nan ya fara karɓar assignment ɗin da ya bayar kafin yasa kai ya wuce cike da fatan samun damar ta a nan ɓangaren. Da farin ciki sosai a fuskar ta ta fito suka wuce theatre ɗin da zasu yi test wacce take opposite da hall ɗin da suka gama lecture, cikun taimakon Ubangiji shima be bata wahala ba tayi ta gama ta bayar ta fice. Buɗe ƙofar motar tayi ta zauna yanayin ta kaɗai ya isa bayyanar da farin cikin da take ciki a lokacin, batare da ya tambaye ta ba ta shiga sanar da Saraki duk yadda komai ya wakana daga test ɗin har yadda suka yi da M. Saminu a lecture hall, shi kansa yaji daɗin yadda ta fita kunyar jama'a dan mutane irin su Kisnah da suka yi ƙaurin suna idon kowa a kansu yake. Cikin kwanakin da suka biyo baya sosai ta ajiye partying dasu clubbing dan fuskantar exam ɗin ta wadda daga ita se project da zasuyi shikenan sun gama degree ɗin su gaba ɗaya se zama jiran result da zasuyi shiyasa gaba ɗaya bata son jin wani abu me sunan matsala dangane da karatun nata. A kwanakin sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Saraki da Kisnah saboda kusan kullum tare suke wuni suna karatu wanda shima ba ƙaramin pleasure yake driving cikin hakan ba dan kina komai hakan na tuna masa da memories ɗin karatun sa. Ranar da zasu Fara exams ɗin sosai ya saka ta ta kusan kwana a pray mat dan ba ta sassafe bace se ƙarfe sha ɗaya tukunna shiyasa ta sami damar yin Bacci ta Sami peace of mind. Yau ma kafin ta fita addu'o'i ya mata sosai cikin mata fatan dawwamammiyar nasara kafin ya sata karanta wasu addu'o'i kafin ta fita daga motar, itama bata wani damuwa take yin duk abinda yace dan zaman su na kwanakin yasa ta saba da yadda yake da yawan addu'a dan har sallama yanzu takanyi sa'i da lokaci kafin ta shiga waje. A wajen sa hakan ma nasara ce shiyasa be fita takurawa da se ta canja komai a lokaci guda ba dan yasan hakan ba me yiwuwa bane kuma baya san taga kamar takura ne shiyasa yake bi da ita a hankali yadda zata yi komai cikin ra'ayin kanta ba tursasawa ba haka kuma ya fahimci in yace ce tursasa itama ɗin ba kanwar lasa bace ba tanƙwaruwa zata yi ba. Cikin ikon Allah tayi jarabawar ta ta gama lafiya tare da taimakon Saraki da kacokan yanzu ta ɗau duk wata girmamawa ta bashi, Ya sama Ya ƙasa take kiran shi haka yanzu ya san abubuwa kaɗan kaɗan game da ita da wasu daga cikin dukiyar ta wanda da kanta sanar dashi dan samun solution kan matsalolin ɓatan kuɗi da ta nemi shawara a wajen shi. Bayan dogon nazari ya bata solution ɗin da da taimakon Ubangiji se gashi an yi nasarar gano me wannan account ɗin da kuɗaɗen nan suka shige, wani ƙaramin ma'aikaci ne dake da post ɗin gyara files, mamaki ya kama su kamar me da tunanin taya ya kasance shi, tawace hanyar har yake samun access haka, dole akwai wani behind his shadows sedai anyi yin duniya mutumin ya faɗi wa ya sashi ya kafe kan ba kowa, dole aka miƙa shi kotu aka yanke masa hukuncin shekara biyar a prison tun da ya kasa biyan tarar da aka yanka masa ta miliyan uku, sosai Kisnah yaji tausayin sa har tana batun zata ce ta yafe sedai tuni Saraki ya dakatar da ita dan irin su dole se ana hukunta su dan ba wai ze Dena bane ko tace ta yafe ɗin. Kayan abinci yasa ta siya ta kai gidan mutumin da a kallon farko da tayi wa gidan ta daɗa tabbatar da tabbas wani ne ya sashi dan ɗaki ɗaya ne a gidan se kitchen da toilet ɗin da aka zagaye da kwano, jijjiga kai kawai tayi kafin ta saka almajirai aka shiga da kayan abincin da suka ciki booth da su. Godiya ba kama hannun yaro matar sa ta shiga yi ita da ƴaƴan ta mata biyar se maza biyu dan dama cikin matsalar abincin suke. Yanzu ma zaune yake kan ɗaya daga cikin kujerun office ɗin ta na K&S shopping mall da ke gaban table ɗin ta wanda shine karo na farko da ya shiga office ɗin shima bisa dagiya da magiyar da tayi ta masa har da guntun hawayen ta, laptop ɗin da take aiki da ita a office ne ta turo gabam sa kafin ta zagaya ta gefen sa ta shiga yi masa bayani tana daddanna keyboard ɗin. Kwanan nan aka nemi wasu kaya aka rasa a mall ɗin kuma an rasa ta ina suka bi suka sulale daga cikin mall ɗin, kaya ne bana ƙananan kuɗi ba dan kusan rabin ribar da aka samu a wannan shekarar cikin mall ɗin suka sa suka yi order sedai kwana uku da zuwan kayan aka nemi kusan rabin su aka rasa, abinda ya jawo babbar matsala kenan aka shiga binciken ina kayan suka yi sedai har yau an kasa ganowa shiyasa tana gama exam ta maida hankalin ta kan mall ɗin ɗan yana cikin best kadarorin ta da take matuƙar so dan purposely dama ita aka buɗe wa tun iyayen ta na da rai. Yanzu ma bayanin duk ma'aikatan dake cikin mall ɗin take masa da post ɗin kowanne da kuma albashin da yake ɗauka a duk wata, ɗaya bayan ɗaya ya fara scrolling through list ɗin har ya gama kafin ya ajiye mouse ɗin ya fuskance ga sosai. "A yadda na bi bayanan duk ma'aikatan ban ga komai ba sedai akwai strategy da zamu bi, for now ki sa a tara su gaba ɗaya a ɗakin meeting in kuna dashi in babu kuma su taru a tsakiyar mall ɗin bayan an sallami kowane customer". Gyaɗa kanta tayi da sauri kafin ta ƙarara wajen landline ɗin dake kan table ɗin ta ta daddanna wasu numbers ta kara a kunne, bata tsaya amsa sallamar da yake mata ba bare gaisuwar da ta biyo baya "Ka sa a sallami kowane customer da yake cikin mall ɗin nan da mintina goma ya zama ba kowa a ciki sannan ka sanar da kowane ma'aikaci ya hallara a meeting hall in next 30 mins". Ajiye wayar tayi ta juyo gare shi "Na sanar dasu Ya, what next?". "In suka taru Zamuyi addressing issue ɗin tare da yin barazana sosai kafin mu examining facial expressions ɗin su, insha Allah zamu iya gano criminals ɗin ta haka". Faffaɗan murmushi ne ya wanzu saman fuskar ta kafin ta sara masa gani da ƙamewa tana faɗin "Salute you sir". Girgiza kansa kawai yayi dan yanzu ya fara sanin halin ta na surutu da barkwanci dan har ya dena damuwa, ƙarkari ya bata amsar abinda yaga ze iya Wanda baze iya ba kuma ya kalle ta kawai..........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 19 (8/10/2022 10:16 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 1️⃣9️⃣ _____________________📖 Kamar yadda ta bada umarni haka akayi, 30 mins after manager ya kirata yana tabbatar mata da duk ma'aikatan na hall kamar yadda tace ayi, amsa masa tayi da gata nan zuwa ta ajiye wayar tana kallon Saraki "Yaa suna wajen mu kaɗai ake kira". Nodding head ɗin sa yayi yana miƙewa tare da gyara rigar yadin kuftar jikin sa da akayi wa plain ɗin ki sedai ba ƙaramin amsar shi yayi ba kamar a sace a gudu, yana cikin set goma da ya ɗin ka cikin kuɗin albashin sa na farko da ya ɗauka two weeks back, yadi kala huɗu se shadda huɗu boyle biyu. Clutch ɗin dake haɗe da rigar jikin ta ta ɗauka kan table ɗin da ta ajiye ta farkon shigowar su ta bi bayan sa ɗan tuni ya fita. Bakin ƙofar ta tadda shi dan haka itama ta tsaya sedai kafin ta kai ga tambayar me yasa ya tsaya ya riga ta nuna hanya tare da faɗin "You lead me". Bata yi musu ba tayi gaba ya biyo ta a baya dan ta san be san wajen ba to mutumin da ya fara shigowa mall ɗin yau taya de san ɗakin meeting ɗin su. Ƙaton ɗaki ne da kana shigar da zaka sheda na meeting ɗin ne saboda ƙaton table ɗin da ya zage yi ɗakin duk girman sa kuwa se kujeru dake jikin sa wanda a yanzu ma'aikatan wajen ke zaune a kai se kujera ɗaya da ba kowa dake gefen dama ga kujera guda ɗaya tal dake can gaba tana facing table ɗin wadda itace akayi purposely sabida ita. Miƙewa gaba ɗaya ma'aikatan suka yi cikin nuna girmamawa, kujerar da manager ke kai wadda ke gefen daman ta ya miƙe da sauri ya koma cikin ma'aikatan dan akwai two vacant seats, tun kafin ma ya nemi wajen zama ta ƙarasa da sauri ta zauna kan kujerar da manager ya tashi kafin cikin muryar ban girma ta nuna masa kujerar da ita tayi supposing ta zauna. "Please have your seat sir". Shiru yayi cikin Binta da kallon bangane me kike nufi ba yana sake haɗe rai, haɗe hannayen ta tayi alamun Please tana sake roƙon sa da ido, harara ta yayi kafin ya maida duban sa kan ma'aikatan da wasu suka sunkuyar da kai yayinda wasu suke bin su da ido kamar television mamaki rubuce ƙuru ƙuru kan fuskar su. Ɗan gyaran murya yayi kafin ya zauna yana fuskantar su kafin a hankali ya shiga bin su da ido cikin son ƙayyade adadin su wanda be wani sha wahala ba ya ƙirge su, su 35 ne ma'aikatan ciki dan uniform ɗin su ya banbanta da na securities da suke 10. Cikin sassanyan Muryar sa ya soma da gaishe su gaba ɗaya Good afternoon all". Ɗan shiru yayi ya basu damar amsawa kafin ya cigaba "Mun taru a nan bisa dalilin da ba na haufin kowa ya sani, wanda be sani ba ma ina farin cikin sanar dashi a yanzu cewa mun taru a nan ne kan dalilin ɓatan kaya da muka fuskanta sati da ƴan kwanaki da suka wuce, ba wai mun tara ku a nan dan binciken wanda ya ɗau kayan bane, a'a mun tara ku a nan ne dan sanar da ku mun yi nasarar gano wanda yayi hanyar ɓatan kayan wanda alhamdulillah muna kan tunanin tura case ɗin court........". Ya ɗan dakata cikin bin fuskar kowanne da kallo har idanun sa yayi nasarar sauka a inda ya dace dan yayinda ragowar kowa ke garin ciki da godewa Allah kan nasarar da aka samu me aikin yaƙe kawai yake yi haka kuma ga duk wanda yasan malamar aikin lawyer kallo ɗaya ce masa ya dasa alamar tambaya akan sa da kuma look ɗin da idon sa ke fitar wa. "Sedai kafin mu miƙa me wannan aiki court zamu bashi dama, zamu bashi dama ta ƙarashe wato dawo da kayan salin alin ba tareda kowa ya sani ba haka batare da mun tona masa asiri ba". Haɗe rai sosai Saraki yayi har fiye da yadda Kisnah tasan yana yi dan a wannan ɓangare sam baya wasa haka baya san wasa baya kuma san ayi masa wasan wanda irin wannan jajircewar ta samar masa da girmamawa da kuma ɗaukaka a cikin ƙankanin lokaci, a yanzu da yake zaune ba yana hango kansa ne zaune cikin mall ba ƴana hango kansa ne cikin court trying to find out a hidden truth. Direct ya sauke duban sa gefe kujerar da mutumin yake wadda ba kowa kanta ya kuma kausasa murya sosai alamun ba wai wasa yake ba "Ƙin amfani da damar da muka bayar ze sa mutimin ya fuskanci hukunci me tsananin tsauri wanda bana jin ya taɓa fuskanta a kaf rayuwar sa, ba zance kar me laifin ya gudu ba se dai ma nace Allah ya bashi sa'ar hakan wanda hakan shine baban kuskure na ƙarshe daze yi a rayuwar sa dan daga yanzun nan da muke zaune tare da ku anan Yana under supervision ɗin security agencies daban daban, gare ku ragowar maaikata, kusani ba wai an ɗauke ku aiki an ƙyale ku kowa yayi abinda ya ga dama bane, dukkan shige da ficen ku dama information ɗin family ɗin ku duk muna samu dan haka wanda ya tsaya yai aiki tsakani da Allah will receive two reward, one here from us a duniya and the other from Allah a nan duniya ko a lahira, wanna shine iya abinda zan iya cewa kan wannan batu, Allah ya ƙara muku lafiya da ƙarin gwiwar yin aikin ku kan gaskiya da Amana ya kuma ɗaukaka wanna waje". Da Amin kowa da ke cikin hall ɗin ya amsa har da Kisnah dake zaune tana kallon shi cikin jin daɗi da burgewa, yadda yayi addressing issue ɗin ba wanda baze yarda cewa dagaske bane sun kama me laifin tuntuni bayan yar awa ɗaya da ta wuce lalube ne suke yi cikin duhu sedai bata san ko yanzu ya gano criminal ɗin ba kamar yadda manufar meeting ɗin take. Cikin shan jinin jiki ma'aikatan suka fita gaba ɗaya kowa na zargin kowa sedai masu gaskiya ba su wani damu ba se masu ɗan tsatsa a zuci na rashin gaskiya suke shan jinin jikin su ya saura iya manager da Kisnah se Sarakin da ya miƙa a lokacin ya fara tafiya cikin takun sa na isa ya doshi hanyar fita "Yaa pls ka jira ni, lissafi kawai ze yi min se mu tafi". Kisnah ta katse shi da sauri ganin yana gab da ficewa "Ina mota". Iya abinda ya faɗa kenan ya fice batare da jiran me zata ce ba. Cikin sauri suka yi lissafin da ya tsaida su wanda na kayan da akafi so ne cikin watan da ya wuce dan ganin ko za'a sami damar ƙara wasu tunda ana son su, takardun da zata cike kafin a shigar da file ɗin kundin fitar da kuɗi ta karɓa hannun managern da sauri tana faɗin zatai signing a gida se ta kawo masa daga baya. Kishingiɗe kan kujerar driver yake kamar kullum yau ma ya saka wani cassette din wa'azi ne na wani babban malamin garin inda yake wa'azi kan irin tarin zunubin da ke cikin fitar da tsiraici, da sallamar da yanzu ta zame mata dole indai zata kusanci inda yake ta shiga cikin motar, gyara zaman sa yayi yana tayar da motar har lokacin yana cigaba da saurarar wa'azin, shiru duk sukayi yayinda motar ke tafiya smoothly kan shimfiɗaɗɗen titin da ba'a daɗe da zuba masa sabuwar coal tar ba, a kaikaice yake kallon ta ta ƙasan ido cike da son ganin jikin ta yayi sanyi da irin azabobin da malamin ke faɗa sedai kwata kwata ma ya lura hankalin ta baya nan yana can wani waje ne da be sani ba dan yadda ta kafe glass ɗin motar da ido bata ko ƙiftawa irin dai mutun yayi nisa a duniyar tunanin nan, be ji daɗin hakan ba dan saboda ita ya saka wa'azin ko ta rage wasu daga cikin shigar banzan da take yi, hannu ya miƙa ya canja wa'azin zuwa karatun Alkur'ani mai girma dan ya lura saurarar sa na kashe mata jiki sosai. Juyowa yayi gaba ɗaya da san dawo da ita daga tunanin ya ɗan yi gyaran murya kafin yace "Wa kika fahimta matsayin me laifin da yayi wannan aika aikan?". Se da ta sauke ajiyar zuciyar firgita da ta ɗan yi kafin ta kalle shi itama "Ban fahimci kowa ba dan dukkan su basu bada wata ƙofa ba duk da bakowa nake iya ganin sosai ba". Gyaɗa kan sa yayi tare da yin shiru na tsawon mintina kafin ya yanka "Ni na gane shi". Da sauri ta karkato sosai har kamar zata bar kujerar ta zuwa tasa tana magana cike da zaƙuwa "Wane ne yaa, wace number ce a gefen ƙirjin sa?". Ta tambaya cike da curiosity kasancewar kowane ma'aikaci akwai identity number jikin rigar sa ta gefen ƙirjin sa ta dama haka kuma akwai sunan sa a bayan rigar haka kowanne ana bashi uniform set uku ne dan gudun matsala kamar ƙonewa, yagewa ko jiƙewa. Kallon ta yayi for some seconds kafin ya ɗauke kai be bata amsa ba kamar yadda yaga ta zaƙu ta ji, kwaɓe fuska tayi ganin abinda ya mata kafin cikin sakkakiyar murya ta furta "Yaa Saraki mana". Harara ya juyo ya wurga mata ya sake maida hankalin sa kan titi, da sauri ta saki dariya kamar wata zararriya, jin taki denawa yasa ya juyo ya kalle ta hakan kula ya a dariyar ta ƙaruwa. "Dama haka ka iya harara yaa, tabb wa yaga harira sunan wata mata". Murmushi ne ya so ƙwace masa se dai ya danne ya ƙi ko kallon ta hakan yasa ta cigaba "Haka ma fa ɗazu a hall ka harareni kuma guess what, wallahi ka iya sosai dan har wani kaɗawa fa gashin ifon ka ke yi". "013". Ya faɗa da sauri cikin son ta bar zancen hararar dan se ya ji yana ɗan jin kunya, aikuwa da sauri ta tsayar da dariyar ta tana zuba masa ido "Number criminal ɗin kenan 013". "Amma taya akayi ka gane shi yaa, 013 sunan sa Adams kuma physically mutumin kirki ne". "Ki bincike shi sosai though ma yadda na karanci facial expression ɗin sa he's so scared and na tabbatar ze dawo da kayan kamar yadda nace". Girgiza kanta tayi tare da gyaɗa shi at once dan tasan tun da ya faɗa ɗin to Allah ya bashi ikon gano shi ne, batare da kuma sun sake cewa komai ba suka ƙarasa gida yayi parking ta fita, kamar yadda ta saba ta jingina jikin murfin side ɗin ta da ta rufe har ya kulle motar ya zagayo ɗan yi side ɗin ɗakunan su "Good night yaa, have a nice sleep". "Fi Amanillah". Ya amsa ta dan yasan tun da ta daɗi haka to ba zata kuma fita ba yau se gobe shiyasa tun yanzu ta masa bading bye, amsa matan da yayi yasa ta juya ta wuce flat ɗin su dan It's to 3 rana tayi yawa a compound ɗin. Kwana biyu bata fita ko ina ba se ana ukun da ta shirya cikin shagalalliyar shigar da munin ta yakai wadda ya kwana biyu be ganta da irin ta ba, yau ɗin suna da babban taro ne dan yau Surry take birthday party ɗin ta wanda ya wuce satin da ya wuce da bata sami damar celebrating ba saboda ba'a sallame ta ba se shekaranjiya shiyasa suka shirya grand party na murnar birthday da kuma samun sauƙin ta dan yanzu ba kowa ne ma ze ce tayi ciwo ba se su da suka sani haka kuma samarin Surryn ba ƙaramin kashe kuɗi sukai ba wajen ƙawata shi dan yayi looking so big and classy. Shigar da suka yi yau ɗin special ce, komai na jikin su kuɗi ne barin ma Kisnah da iya rigar da ta saka 2.3 mil tayi order ɗin ta kuma tare da ribbon ɗin ta take zuwa, takalmin da tasa kaɗai 310k ne se sun har ɗin ta me kyau da ta siya a K&S 50k Dan designer and fashionable ce sosai. A ƙalla dai kayan da ta sanya wa jikin ta kama daga kan riga, takalmi, hat, chain, earrings, rings, watch, leg chain and glasses sun tasar wa 4mil. A kallo ɗaya zaka yi mata kasan Yes ta haɗu, so breathtaking dan tsayawa faɗar yadda baƙar rigar me walwali ta haska ta ɓata lokaci ne, kamar wata ƴar tsanar turawa ɗin nan da ake decor da su sedai gashi Sarakin namu yaya ga Kisnah sam shigar bata yi masa ba, dan rigar a tsage take tun daga ƙasa har rabin cinyoyi haka kuma ta gefe biyun ma tsaga ce har inda ta tsakiyar ta tsaya haka ma tsakiyar bayan rigar daga ƙasa. Daga sama kuwa ba ƙaramin kama ta rigar tayi ba kuma siraren hannu biyu gare ta se zaren da ake ɗaurewa ta baya haka kuma wuyan buɗaɗden wuya ne ta gaba da baya da yasa ake hango saman ƙirjin ta sosai ta baya kuma har tsakiyar bayan a buɗe yake. Kallo ɗaya yayi mata tun fitowar ta ya ɗauke kai cike da takaici, takaicin yadda ƴar musulmi gaba da baya ke irin wannan shigar ba kuma a gidan ta ba a'a sedan fita wasu su gani su yaba da sunan wani abu wai party, ɗaya daga cikin manya manyan abubuwan dake ƙara yaɗa ɓarna da fasali a ban ƙasa. Tun da ta shigo motar take washe baki tana jiran taji yace mata tayi kyau sedai taga ko kallon ta be yi ba hakan yasa ta kasa haƙuri seda ta tanka "Yaa ba kace nayi kyau ba". Ta faɗa tana ɗan jujjuyawa daga zaunen da take cikin motar ita a dole se yaga adon nata "Yaa baka ji bane?, Nayi kyau ko". Ta sake faɗa jin be tanka mata ba, se a wannan karon ya ɗago ya kalle ta cikin watsa mata mugun kallon da yasa take taji jikin ta yayi sanyi "Kyau? A cikin wannan mummunar shigar kike neman kyau". Shiru tayi dan bata san amsar da zata bashi ba sedai ita sam bata ga aibun shigar tata ba, ita bata wani ɗau saka irin wannan kayan a komai ba dan ta ɗau hakan a matsayin tsarin rayuwar ta haka kuma kamar yadda Bature ya faɗa kowa yana da right yayi living life ɗin shi as he wish dan haka ita ba me sa ido bace akan rayuwar wasu so bata san itama a fiye sa mata idon. "Amma Ya Saraki yau birthday ɗin Surayya ne, tayi missing exact date ɗin saboda rashin lafiyan da tayi yanzu kuma ta samu sauƙi shiyasa ka shirya wannan partyn da murna biyu, jin daɗin warkewar ta da kuma birthday ɗin kaga kuwa dole ne muyi shiga me kyau dan taya ta murna ko?". "Shine se kun bayyana tsiraici za'a san kuna farin ciki, inda zaki kyautawa kanki da kin koma kin canja wannan rigar to something more decent and better". Ɗauke kanta kawai tayi ganin bafa ze fahimta ba ita kuma bata shirya bin wani tsarin sa ba na daban wanda ya zaɓawa kansa dan haka kawai itama ya barta da nata. Ganin yadda ta ɗauke kai yasan nufin ta bazata canja ɗin ba so se be sake cewa komai ba kawai ya tashi motar ya fita daga gidan sedai a lokacin fuskar sa kamar wani mala'ikan ɗaukan rai tsabar yadda ya haɗe ta, har suka je be sake kallon gefen da take ba haka itama dan taga in tayi sanyi neman sa ta dole yake yi. Sosai partyn yayi musu daɗi ya kuma ƙayatar dasu, su Madam Kisnah ansha rawa kamar za'a cire ƙugun a yar, liƙi ne tayi kamar ba gobe haka itama an mata kamar a buɗe wani banki da kuɗin, basu tashi ba se after one Dan saura kaɗan two tayi. Ko da ta fita da ƙyar ta gano inda ya ajiye motar ta ƙarasa, yanzu ma kamar ɗazu ba wanda yace wa ɗan uwan sa uffan har suka kai gida duk da dai ita Kisnah cike take tam da labarin da take son bashi na yadda event ɗin ya tafi sedai ganin ba fuska yasa dole ta haɗiye kayanta. Tun daga lokacin kuma ya shiga fushi da ita, ze kaita duk inda take so batare da query ba haka kuma kome zata yi ya daina cewa komai, sosai take cikin rashin daɗin fushin nasa sedai ta rasa ta yadda zata fara bashi haƙuri dan expression ɗin sa is not helping at all, so biyu tana gwada shiga motar Ba tare da sallama ba amma ko kallon ta be yi ba balle ya harare ta yadda yake yi a baya har se ta fita tayi. Yanzu ma jaye da babban trolley ta fito alamun dai zata yi balaguro, tasowa yayi ya buɗe booth ɗin tare da ɗaukar trolley ɗin ya saka a ciki kana ya rufe, be kalle ta ba ya ƙarasa ya buɗe side ɗin driver ya shiga tare da maida murfin ta rufe, kamar mata laka haka ta ƙarasa nata side ɗin ganin yadda yayi tafiyar da ya bar ta ko arziƙin kallo ɗaya bata samu ba daga gare shi.....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 20 (8/11/2022 10:39 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣0️⃣ ______________________📖 Manyan hamshaƙan mata ne ƴan gayu cikin shigar da kana kallon su kasan sun kai sun isa sun kuma tumbatsa dan gwala-gwalai ne kawai ke ta walwali a jikin su, zaune suke a falon gimbiya Rumana gaban su cike da kayan ciye ciyen da kama gani kasan mutane ne na musamman gare ta haka masu matuƙar daraja. A hankali wata farar mata a cikin su ta ɗago ta kalli gimbiya Rumana dake zaune cikin su ana hira tana kai kyakkyawan slice of apple bakin ta "Amma Rumana bakya tunanin mijin nan baki yace ce bawa yaron can Jamal sarautar nan, ni kam se naga kamar hankalin sa ya fi karkata ga yaran ɗakin kishiyar ki ko da yake ba laifin sa bane a fili yake sun fi uthman nutsuwa nesa ba kusa ba". "Haba Aunty Siyama, wannan wace irin magana ce haka, wace nutsuwa ce aka fi uthman ɗin da zan iya rantse miki baya wani shashanci, masu nutsuwar kuma ai a hakan dai a ka kori ɗaya daga cikin su kan aikata babban alfasha ko". Sarauniya Rumana ta faɗa da little ɓacin rai a harshen ta "Alfashaar da kuka laƙaba masa ke da husna? Ko an faɗa miki ban san komai akan hakan bane, kawai na zuba muku ido ne dan nasan ba laifi kika yi ba wajen fighting Nasara wa ɗan ki, mu ajiye wannan maganar mu dawo kan wadda muke yi yanzu". "Bana tunanin ya isa yayi hakan dai uthman shine gaba da yaron, dama wancan da aka kora ne gaba dasu gaba ɗaya shiyasa ban kwantar da hankali na ba se da na tabbatar da fitar da cikin masarauta ta sigar da shi da ita har abada dan ko cikin ta be isa shigowa ba haka Sarauta sedai yaga anayi". "Hakan yayi kyau, sedai kin san dole uthman yayi aure ko da ba'a taɓa sarki mara mata ba". "Takawa ma yayi magana akan hakan kuma insha Allah ina kan tunanin mafita dan yace baze bada sarauta yanzu ba har se sunyi aure yaga irin kamun ludayin kowannen su ta fuskar riƙe iyali tukuna". "Kina da hankali kuwa Rumana, naji kina maganar su, bayan kamata yayi yace uthman kawai anya ba wata a ƙasa kuwa?". "No ba komai Aunty Siyama, kinsan shikansa Jamal din ya girma yanzu dan he's 28 shiyasa yayi pluhralizing Amma ba wani abu ba". "Na gane" Juya wa sarauniya Rumana tayi ga ɗaya ƴar uwar ta su da tun da suka fara maganar bata ce ko uffan ba se danne danne da take yi a faskekiyar wayar hannun ta "Wato har yanzu dai kina nan da halin miskilancin naki Khadijah, kina ji muna ta hira amma ko kallon mu ma ba kiyi ba, lallau Abu Sufyan yana ƙoƙarin zama dake". Murmushi Khadijar tayi "Hirar taku ce ba irin wadda zance komai a kai bace Aunty, abinda kuke magana akai kun san ba daidai bane haka abinda kuka aikata ke da husna, sedai ba zan iya tona muku asiri ba kasancewar ku ƴan uwa ne, amma fa bazan fasa faɗa muku ba a kullum ku ji tsoron Allah". "To ustaxiya, mun ji kuma mun gode". Ɗan murmushi kawai tayi ta cigaba da latse latse a wayar ta yayin da suma suka cigaba da tasu hirar. ************** Gudu sosai motar take yi kasancewar titin ba wasu motoci da yawa se tsirarun na matafiya, shiru cikin motar ba alamun akwai me rai dan baka jin ƙarar komai se sautin nunfashin su dake fita a hankali a hankali se ko sautin karatun Alqur'ani mai girma da aka kai volume ɗin kusan can ƙarshen ƙasa. Chatting take yi tana zaune a kujerar ta sa'i da lokaci bakin ta na sakin murmushi alamun tana enjoying chatting da koma waye take yi ɗin, ringing ɗin wayar ya saka fuskar ta ƙawatuwa da faffaɗan murmushi ganin sunan Deeq kan screen ɗin, picking tayi tare da kangawa wajen kunnen ta "Deeeeeeeq". Ta faɗa a hankali dariya na ɗan kubce mata, daga can ɓangaren akace "Kar ki wani kira suna na bayan kin shoshala min rashin m, Allah queen baki da kirki". "Am sorry my Deeq, Allah na manta ne a lokacin hankali na yayi makaranta kasan dama na faɗa maka daga can muke, nasan ka fi kowa sanin halina ta wannan ɓangaren". Ta faɗa da ragowar sautin dariya cikin muryar ta "Sosai ma kuwa na san ki ciki da waje, from cover to cover so sedai in ba wa wasu labari". "Yauwa my Deeq na San ka yi min uzuri ko?". "Sosai ma kuwa Queen, kin taho ne?". Ɗan duban titi tayi kafin ta gyaɗa kan ta "Muna hanya tuntuni, I think be fi ragowar three hundred kilometers ba mu ƙaraso, su Surayya sun ƙaraso ne?". "Eh na bar su sun shige ɗaki zasuyi freshen up". "Then Sena ƙaraso ko?". "Ok bye, I love you". "I love you too babe". Ta faɗa tana katse kiran, a hankali ta gyara zaman ta tare da miƙa hannun ta baya ta ɗauko ƙaton headphone ɗin ta dake cikin medium handbag din ta tayi connecting da wayar ta tare da maƙala shi cikin kunnen ta ta ƙure ƙarar sa cikin waƙar koi mil Gaya ta cikin Film ɗin koi mil Gaya ɗin na jarumi Hrithik Roshan da jarumai pretty zinta sannna ta kwanta sosai cikin kujerar ta lumshe idanun ta tana bin waƙar a hankali. Ɗan kallon ta yayi a kaikaice cikin takaicin yadda ta ƙwama uwar earpiece tana sauren waƙoƙin banza na wai arna can da ba lallai ta san me suke faɗa. A haka ya cigaba da gudu kan shimfiɗaɗɗen titin da yasha sabuwar coal tar har suka kusa fara shiga birnin sawariya da duk wannan gudun yana amfani da Google map ne dan shi ne taɓa sanin akwai garin ma a ƙasar ba, ko da yake shi banda garin su Giwa da maƙwabtan su ba inda ya sani dan kusan ba anan yayi rabin rayuwar sa ba. Tun daga nesa ya hango ƙarin ginin resort ɗin da kusan duk da gilasar aka yi shi, gini ne me girman gaske haka me matuƙar tsawo dan a ƙalla ze yi hawa hamsin, kyawawan furanni masu fitar da sassanyan ƙamshi zagaye dashi haka kuma dogayen bishiyun kwalliya suma sun kewaye shi hakan yasa hatta iskar wajen kusan ta musamman ce. A bakin gate security suka tare su demanding for their approved card Wanda ake turawa duk wanda yayi booking resort ɗin wanda su ze nuna kafin a bar shi ya shige, card ɗin na ɗauke da sunan wanda yayi booking, photon sa, adadin kwanakin da ze yi lastly floor number and room number. Dole tasa ya tashe ta tare da nuna mata securities ɗin ta window ɗin ta, da sauri ta tashi zaune sosai tare da gyara zaman ta ta janyo wayar ta ta shiga ta nuna musu card ɗin ta seda suka duba suka tabbatar kafin su tambayi na Saraki shima ta nuna musu kafin a aka basu hanya suka shige. Parking yayi gurin da wani security ya nuna musu dan komai nasu a tsare yake shiyasa ma suke da ƙayyadaddun adadin da suke approving zaman su a wajen, ko da kuwa mutane nawa ne sukai booking in dai adadin su ya cika sedai su bawa mutum haƙuri ya tara a gaba hakan yasa babu wani hayaniya ko kace nace, so classy and peaceful. Fitowa haka yi daga motar customer service biyu suka ƙaraso da sauri, ɗaya ya ɗau ƙaramar jakar kayan saraki ɗayan kuma ya ja trolley ɗin Kisnah, key service suka biya suka karɓi card ɗin da zasu dinga locking and unlocking ƙofofin ɗaku nan su kafin su nufi elevator, a tenth floor suka fita inda nan ne ɗakunan nasu suke, bakin ƙofar wani ɗaki suka tsaya ta saka card ta buɗe ɗakin sannan suka shiga, dakatar da ma'aikatan tayi daga ajiye jakar ta tare da faɗin su jira zasu ƙarasa mata da tata nata ɗakin, card ɗin ta miƙawa saraki tana faɗin "Yaa ga card ɗin ƙofar ka, bari in ƙarasa in yi wanka na gaji da yawa". Wannan karon kasa yin shiru yayi dan tun daga compound ɗin wajen ya fahimci dole se ya saka ido a kanta dan yadda yaga mutane na al'amuran su kai tsaye dan majority ma'aurata ne da suka zo yawan shaƙatawa da kuma hutawa se ko samarin da kan ɗauko ƴan matan su dan holewa wanda baya raba ɗayan biyu itama wani ta biyo. "Ina ɗakin naki yake?". "Room 50, kamar apartment yake ɗan yana da parlour Wanda zamu yi sharing da su Hameedah se kuma bedroom da kowa na da nashi ɗauke da toilet a ciki". Gyaɗa kansa yayi kafin ya shige nasa ya rufo ƙofa ita kuma tayi gaba har ƙofar nasu ɗakin da duk a sake floor ne, bakin ƙofar suka ajiye mata trolley ɗin tayi musu godiya suka wuce ita kuma ta buɗe ƙofar ta shiga. Sosai su Meenah suka nuna farin cikin ganin ta wanda da ƙyar ta samu ta zame zuwa bedroom ɗin ta tayi wanka ta saka shorts iya cinya se guntuwar shimi ta bi lafiyar gado. A can ɗakin saraki shima wankan yayi dan ya gaji sosai kasancewar be taɓa dogon driving ba se yau shiyasa gajiya ta rufe shi. Wanka yayi fito da bathrobe a jikin sa kafin ya zauna kan gadon ɗakin ya jawo jakar sa ya zage ya ɗau shorts da jallabiya ya saka yayi sallar zuhur da ta same su a hanya kana ya cire jallabiyar ya kwanta. Bacci tayi me daɗi kafin ta tashi ta fita parlor ɗin taci abinci sannan suka shiga hirarrakin su irin na ƙawaye. Ƙarfe bakwai da ƴan mintuna suka fito shirya kowacce cikin irin tata shigar suka nufi spa ɗin da ke wajen, ƙwataccen guri ne da ko a cikin resort ɗin iskar cikin sa ta banbanta da ta ko ina saboda madaidaitan bishiyun da aka kakkafa suna rausaya wa sunan fitar da tattausar iska da ta haɗe da ƙamshin fresh sea ɗin gefen wajen. Kan kujerun da ke zagaye da table ɗin me ɗan girma suka zazzauna ana ta hira kafin daga bisani Kisnah tayi shiru da bakin ta ɗan tuni hankalin ta ya koma kan ruwan da yake ɗan motsi garai garai dashi gwanin burgewa, rabon ta da waje irin wannan shekara biyu kenan, da a lokacin tana Canada kusan duk week tana hanyar bakin beach da spa Sabida mayatar son ruwa da Allah ya jarrabe ta dashi, farkon zuwan ta nan lokacin tana level one ne da suka samu hutun first semester tazo tayi sati ɗaya ta koma lokacin tun kan ta san su Hameedah, dan har gwara Surayya da Leekha ta san su tun lokacin sedai ba wani good times suke ba ana dai hi hi ne, farkon alaƙarsu da Surayya tun wani group assignment da ya haɗa su ne daga nan kuma se suke dan gaisawa sosai har suka ɗan saba, Meenah kuwa se suna level two suka haɗu lokacin da ita Meenahn ta Sami carry over a first semester ɗin su tana kuka gaban notice board ɗin da aka kafe musu, sosai ta bawa Kisnah tausayi a lokacin dan haka ta ƙarasa ta ɗaga ta da alƙawarin insha Allah zata dinga koya mata course ɗin da ta faɗi har tayi catching up ƙarkari dai ta sa a ranta zata yi, Hameedah kuwa cousin ɗin Meenah ce da tayi joining ɗin su later farkon second semester, daga baya ne Leekha ta shiga cikin su sosai dan farko sedai ɗan gaisuwa. Tapping ɗin ta da Surayya tayi yasa ta ɗago da sauri tana mata kallon tambaya "Wane irin tunani kike yi haka Kisnah, anata kiran wayar ki nima ina ta miki magana amma shiru baki jini ba". "Ringing Kuma, amma ban ji ba?". "Ta ina zaki tafi, Allah yasa wata bata faɗa tsakiyar kogin da ba mataimaki gabas da yamma ba balle kuma kudu da arewa". "Wane irin kogi kuma wace ta faɗa? Ban gane ba". "Gaya min, wane me sa'ar ne haka ya sami damar sace wannan zinariya zuciyar ta kyakkyawar budurwa kamar queen Kisnah ta?, dan da alama queen ɗin mu ta faɗa cikin makauniya kurma ..........". "Kuma gurguwar soyayya ko, dan nasan abinda zaki faɗa kenan". Dariya suka saka duka dan sosai Kisnah tafi sakewa tayi wasa da dariya da Surayya duk cikin friends ɗin nasu kuwa, Leekha kuma, hmmm yarinyar tayi dan baza' a taɓa zama a zagi Kisnah a gabanta ba ta sani ita kanta in Kuma akayi kuskuren haka to bayan matakin da ita Leekhar zata dauka se ta kuma sanar da Kisnah ɗin, Meenah kuma tana gwada mata kulawa fiye da kowacce cikin ƙawayen nata sedai ita tasa sakin jikin ta sosai da ita duk da cewa ba wai tana ɗari ɗari da ita bane sedai ba kamar yadda ta sake da Surayya ba, Hameedah kam ba a magana dan tun da ta gane halin ta ta ci maganin zama da ita. Ringing ɗin wayar yasa ta mida hankalin ta kan screen ɗin tayi picking tana kaiwa kunne "Hello Queen". Deeq ya faɗa daga can ɓangaren, da murmushi ta amsa da hi "Kin ƙaraso ne?". "Tun ɗazu, har na huta mun ma fito da su Meenah, muna spa". "Okay Bari in ƙaraso". "K". Tace tare da kashe wayar suka cigaba da hirar su da Surayya. Tun daga nesa da ya hango ta yake ta sake mata murmushi har ya ƙaraso kusa da su, miƙewa tayi suka rungume juna kafin ta janye jikin ta ya ƙara sa kusa da su Meenah sukayi shaking hands da dukan su Sannan ya dawo wajen ta. Kujerar kusa da ita ta right side ɗin ta ta ja masa dan ya zauna yayinda Surayya take left side sedai be zauna ɗin ba se kallon kujerar yayi ya maida kallon sa kanta Yana marairaicewa "Please kissy muyi tseren nan da muke yi da boat a Canada, Allah i missed those moments like hell". Ɗan shiru tayi tana kallon sa kafin ta juya ga ruwan da dama tun ɗazu take hasaso shiga cikin sa sedai tana dannewa yanzu kuwa da ya faɗa se taji hakan kawai take so, miƙewa tayi yayinda Surayya ta tambaye ta ina zata ta faɗa mata, da sauri itama fa miƙe tace zata yi, kallon kanta Kisnah tayi cikin ƙarewa shigar ta kallo, doguwar t-shirt ce irin me saukowa har gwiwar nan se ɗan bumpshort da ta saka se ko farin canvas ɗin da ta sanya a ƙafar ta, gashin ta nannaɗe cikin style ɗin bun ta ɗora p-cap, gaban Leekha ta ƙarasa ta ɗau cardigan ɗin da Leekhan ta cire ta maƙala a jikin ta dan tasan dole sanyi ze iya damun ta kafin suka nufi wajen jiragen su ukun...............✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. _The two hardest things to say in life are hello for the first time and goodbye for the last._ Ouummey 21 (8/11/2022 10:40 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* ________________________________ Page 2️⃣1️⃣ ________________________📖 Wajen jirgin suka ƙara sa nan Surayya ta karɓi ɗaya ta biya nata kuɗin a lokacin su kam ɗan ƙaramin receipt ɗin da yayi payment tuntuni ya nuna, guda ɗaɗɗaya kowa ya shiga shi kaɗai, seda kowa ya gama shirya wa kafin Deeq ya irga ɗaya, biyu, uku inda yana cewa ukun kowacce tayi pressing start button na jikin jirgin haka shima suka shiga gudu cikin ruwan suna kwana kwana riƙe da steering da suke controlling direction dashi. Gudu suke sosai dan kowa ya ƙurewa nashi ido cikin son yaga shi yayi winning Wanda se sun Kai wani ɗan ƙaramin mountain dake gefen ruwan daga can nesa sannan zasu juyo, cikin ƙwarewa Kisnah take murɗa steering dan duk cikin su ta fi su iya wa dan lokacin tana Canada babbar gasar tseren jiragen ruwa take yi kuma so uku tana winning, yanzu ma duk ta kere musu tuni se debate ɗin ya koma tsakanin Deeq da Surayya dan da ya wuce ta take dagewa ta zo ta wuce shi haka shima yaƙi bari ta wuce shi, suna cikin haka har Kisnah takai ta juyi ta zo ta gota su tana musu dariya sedai tana wuce su kuma nata jirgin ya mutu, cak jirgin ya tsaya cikin ruwan ya ƙi gana yaƙi baya haka tana tsaye tana faman danne danne dan ya tashi sedai fafur ya ƙi a haka har Surayya tazo ta wuce ta haka ma Deeq suna ta mata dariya da gwalo. Sosai ta cika tayi fam kamar zatai bombing a lokaci guda, haka tana ji tana gani Surayya tayi winning sannan Deeq ya kawo mata wani jirgin ta bar wannan a cikin ruwan, tana direwa daga cikin jirgin ƙarar ta ta shige cikin lallausan yashin dake bakin sea ɗin , zare kafar tai ta cigaba da tafiya tana cire cardigan ɗin Leekha da ta ara, tun kafin ta ƙarasa take wurgawa Surayya dake mata dariya harara, ajiyewa Leekha rigar tayi a gabanta kana ta koma kujerar ta ta zauna, dariyar da Surayya ta fashe da ita yasa ta ji kamar ta rufe ta da duka har se ta huce haushin da take tura mata. Zumbur ta miƙe daga kujerar ta hau zubawa Surayya masifa sedai ko kula ta ba tayi ba sema rawa da ta hau tiƙawa tana waƙar winner, I'm the winner. _winner, I'm the winner_ _winner, go laugh at looser_ _looser, go shout at the winner_ Haka take ta maimata wa ana ta musu dariya hakan ya sake ƙular da Kisnah ta juya fuuu zata wuce, Deeq da yafi kowa sanin yadda ta tsani taga an cinye ta a tseren ya maza ya ruƙo hannun ta, a fusace ta juya kamar wadda zata kai duka ya maza ya rungume ta ƙam a jikin sa wanda yasa ta shiga sauke ajiyar zuciya tana lafewa a jikin nasa daidai lokacin da Saraki ya ƙaraso wajen dan tuni ya tashi yai sallar magrib ya jira yayi ta isha kafin ya fito ya na ɗan zazzagaya wajen wanda ya hango ruwan ta cikin glass ɗin dake fuskantar ruwan dan haka ya fito dan zuwa bakin ruwan kamar yadda yake matuƙar so ya kuma saba a da sedai tun da ya fara tunkaro wajen yake jin kamar Muryar ta tana bala'i da ya ƙaraso sosai kuma ya tsince ta rungume cikin ƙirjin wani saurayi ta saka hannu ta zagaye shi Kamar yadda shima yayi mata. Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idon sa ya cigaba da tafiyar sa har ya ƙarasa bakin sea ɗin ya zauna kan rairayin wajen yana saka ƙafafun sa cikin ruwan, lumshe idon sa yayi cikin jin daɗi lokacin da sanyin ruwan ya ratsa fatar ƙafar sa, wani memory me matuƙar daɗi na yawo cikin kansa, its a family memory, family moment da suka yi spending shi da Mamin sa da Jamal har ma da Miemie lokacin da suka kai masa ziyara America inda yayi karatun sa har ma ya fara aikin sa kafin mahaifin sa ya matsa masa da batun komawar sa gida ashe ƙaddara ke kiran sa, ƙaddarar da be san da wane suna ze kira ta ba abinda ya sani itace ƙaddara mafi tsauri a rayuwar sa sedai yana fatan Allah ya bashi ikon cinye jarabawar da ya masa. Ya daɗe zaune a wajen dan har be san lokacin da ya ɓata ba a wajen se da yaji saukar hannu kan kafaɗar sa kafin ya buɗe idanun sa da ya rufe tun da ya zauna a wajen, janye idanun ta tayi daga duban da take wa fuskar ta saboda tasirin nasa idanun da take ji cikin nata da bazata iya daurewa ba. Hannun ta da ta ɗora kan kafaɗar sa yabi da kallo kafin ya maida kan fuskar ta hakan yasa tayi saurin janye hannun ta kuma fara magana dan kare kanta "Ina ta maka magana ne baka ji ba shiyasa na am am shine na ɗan taɓa ka". Janye idanun sa yayi ya maida kan ruwan da ke motsi kaɗan kaɗan ga kuma fresh air dake busawa a hankali a hankali, gurin so peaceful haka yanayin me saka nishaɗi da nutsuwa ne, kamar daga sama ta jiyo shi yana faɗin "Har ya tafi ne?". Ɗan kallon sa tayi amma se taga hankalin sa baya kanta, tunani ta tafi na wa yake nufi kafin ta tuno da Deeq "A'a yaje ɗakin sa he's spending 2 weeks here too". Bece mata komai ba haka itama bata kuma cewa komai ba suka cigaba da zama a wajen har kusan sha ɗaya na dare kafin ya miƙe sannan ita ma ta miƙe, wayar sa da ya ajiye a wajen ya sunkuya ya ɗauka ya juya ze wuce tayi saurin kiran sunan sa "Yaa Saraki". Cak ya tsaya a wajen da yayi yaki biyu sedai be juyo ba hakan yasa ta sha gaban sa da sauri tana ƙwalƙwal da ido tare da langaɓar da kai "Am sorry Ya, Dan Allah kayi haƙuri". Shiru yayi yana kallon fuskar ta kamar me son gano wani abu a cikin ta kafin ya magantu "Sorry? For what? Me kika min na haƙuri kuma?". "Ni dai am sorry please". Jijiga kansa yayi "A sani na ana bada haƙuri ne in anyi laifi, nikuma ban san kinyi wani laifi ba". Ya faɗa yana shirin ratse ta ya wuce, da sauri ta maza ta ruƙo hannun sa "Amma Ya fushi fa kake sani shiyasa na baka haƙuri". "Fushi akan me, kawai se in kama fushi ba Amin komai ba kamar mahaukaci, Ni bana fushi da ke". "Allah ya fushi kake yi". Wannan a ɗan kausashe ya fisge hannun sa "Na faɗa miki ni bana fushi dake so Please leave me alone, I wanna sleep". Ya faɗa yana yin gaba da sauri, itama da saurin ta biyo shi tana share hawayen da ya zubo mata "Am sorry for that night yaa, am sorry for the dress, am sorry for everything please". Ta faɗa Muryar ta na breaking saboda kukan da ya taho mata, tsaya wa yayi jin abinda take faɗa, sosai yaji daɗi a ransa ganin ta san abinda tai kenan tunda gashi ta faɗa da bakin ta sedai not so easy like this, baze haƙura da sauri ba ko dan gaba dan haka se ya ɗan yi ƙaramin tsaki ya juyo a masifance "See I have nothing to do with your night partying or whatever and also your dressings, this life's so simple, so easy and you have the right to live your life as you wish, as you want and as you plan, am not your father nor your brother, we have no any blood ties or something, am only driver, a mere driver whom you paid to serve you, and am doing that, you also payed me, so I have nothing to do with your life, please am sleepy, make you go live me rest". Ya ƙarashe cikin pidgin Yana wuce wa gaba ya bar ta a wajen sororo tana bin bayan sa da kallo har ya ƙure mata kafin ta sulale ƙasa, ba kuka take ba dan kafin abu yasa ta kuka ana daɗe wa, tasowar ta batare da kowa a tare da ita ba da sunan family yasa ta zama strong, very strong da ba ƙaramin abu ke sa hawaye forming a idon ta ba, hakan yasa yanzu ma bata yi kuka ba se dai tana jin zafi, zafin yadda ya faɗa mata magana, yadda ya tafiyar sa ya barta jama'a na kallon ta duk da tasan kowa a wajen sabgar sa yake ba wanda ya damu da wani amma ta ji haushi ta kuma ji zafi. A hankali ta tashi tana kakkaɓe yashin jikin ta kafin tayi making up mind ɗin ta, he said she should leave him and she'll, he said she should live her life as she want Kuma zata yi amd she'll show no concern to him or everything related to him, zata nuna masa she had a heart a ƙirjin ta, a very strong heart. Da wannan tunanin ta koma ɗakin su inda ta same su zaune anata raha da dariya. Zama tayi cikin su itama dan ba zata ɓata ranta saboda shi ba ehe, nan sukai ta kallo ana hira har se to one kafin Deeq ya musu sallama ya tafi nasa ɗakin suma kowa ya shige bedroom ɗin sa. Kashegari da safe ko da suka shirya motar Deeq suka shige suka fita gaba ɗaya, yawo sosai suka sha dan ya zazzagaya da su wurare sosai, they had a lot of fun together, sun yi hotuna sosai haka basu suka dawo ba se after twelve hakan yasa ranar basu haɗu ba gaba ɗaya. Washegari basu fita da wuri ba se two da su Hameedah suka matsa mata shiga cinemar dake cikin resort ɗin wai kallon wani American Film, sam ita bata ra'ayin anything Hollywood Amma haka dole suka takura mata shiyasa kawai ta haƙura ta bisu se gashi to her surprise film ɗin ya burge ta over. Two hours film ɗin yayi lasting kafin suka fito duk ta gaji ga yunwa da take ji se dariya suke mata wai Madam food amma ko kallon su bata yi ba ta faɗa restaurant ɗin gurin ta nemi table ta zauna tare da kiran waiter ta ticking abinda take so kafin ta koma cikin kujerar ta lafe tana jiran a kawo. Sosai ta maida hankalin ta kan abincin har ta cinye French rice ɗin kafin ta koma kan grilled chicken ɗin ta hau ci, hannu ta sa ta kuma ɗauki wani part ɗin zata kai baki kamr an ce ta ɗago suka haɗa ido, sosai ta haɗe rai ta ɗauke nata idon daga kan sa ta cigaba da cin abincin ta, shima ganin haka se kawai yayi smiling Yana ƙara sa plate ɗin gaban sa. Tissue ta saka ta goge hannun ta kafin ta dau wayar ta tana niyyar miƙewa taji zaman shi kan kujerar gefen ta "Good evening beautiful". Ko kallon sa bata yi ba ta ƙarara tura wayar ta cikin aljihu ta juya zata tafi yai azamar ruƙo hannun ta wanda yasa dole ta tsaya kafin kuma tai masa kallon da yasa ya sakar mata hannun ta ba shiri. Ita tarasa wannan wane irin mayen mutumi ne, tun jiya da suka haɗu dashi a park ya nace mata, ko kallon shi ta ƙiyi akan hakan be sa ya fasa Binta duk inda tayi ba, zata iya rantse wa har a cinema da ta kula da kyau se ta ganshi. "Am sorry pretty, ba binki nake yi ba nima nazo hutu resort ɗin nan ne, You know aikin banki da takura shiyasa tun da nasamu na gudu shine na ɓuya a nan dan kasan ba wanda ze san ina nan". "Ni zan sanar kana nan ko dan ka Dena takura min ai". Dariya yayi ya biya suka jera suna fita daga restaurant ɗin tare "Am sorry kar ki faɗa Please, kinga Daddy yasan ina nan se yayi kilishi da namana yasin, oh Rabb mu Dad is fire wallahi". Dariya ya bata sosai ganin yadda yake wani malƙawaya hannu yana kwatanta wa da yadda ya haɗe rai wai kamar yadda Dad ɗin sa ke yi. Shima dariyar yayi suna tafe yana mata hira har yake faɗa mata yana room 52 ne, jijjiga kai tayi jin ɗaki biyu ne kawai ya raba su, ASAD as he said his name was, is a handsome guy me cike da barkwanci da fara'a hakan ke daɗa ƙara masa kyau, cikin some minutes se gashi yasa Kisnah ta saki jiki dashi though dama bata da wuyar sabo sedai in ba'a iya zama da ita ba. Seda ya rakata har ƙofar ɗakin su ta shige kafin ya wuce nasa cike da tuna mata da alƙawarin haɗuwar su a playground za suyi basket ball...........✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️ Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 22 (8/13/2022 8:50 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣2️⃣ ________________________📖 ƙarfe bakwai yau ma suka shirya suka fice sedai tun a hanya suka raba hanya dan su football za suyi ita kuma za suyi basketball da Asad. Sport wears ne a jikin su, Hameedah da Surayya suna team ɗaya #team_red yayin da Meenah da Leekha suke team ɗaya #team_blue haka suka raba kan su based on color ɗin sport wears ɗin nasu. Ita kam Kisnah Black sport wears ta saka wandan daidai gwiwa rigar me ɗan tsayin hannu shima iya gwiwar hannun se scarf da ta saka ta ɗaure kan ta da be iya rufe gashin ba gaba ɗaya, takalmin ƙafar ta kuma fari ne tas kamar dai na jiya. Tun da ta doso filin Asad ya sake ball ɗin hannun sa ya kafe ta da ido, ya Salam this girl is really pretty, her eyes, her lips, her eyelids, her skin, her curves, her hair........her her her Kai! She's just perfect, really perfect in all ways. Dafa kafaɗar sa da tayi yasa yayi firgigit ya dawo hayyacin sa, kallon fuskar ta yayi kafin ya sake mata smile itama ta maida masa hakan ya kuma saka shi yarda she's just perfect, dan the way she looks when she smiled is so muah. Ɗauko ball ɗin tayi dan taga alamar shi yana can cikin tunanin abin da bata san meye ba, gaban sa ta dawo riƙe da ball ɗin kafin ta kalle shi "Ready?". Ɗan murmushi ya saki da ya sashi looking so handsome Dan shima kyakkyawa ne, "Very ready". Kallon sa take yi kamar ba zata jefa ball ɗin ba kafin ta mamaye shi ta jefa ball ɗin ta kuma bita da sauri, da sauri shima bita yana son ƙwatar ball ɗin sedai ta ƙi bashi dama daga ƙarshe ma ta buga uban tsalle ta jefa a basket ɗin shi kafin ta dire tana ƙyalƙyala masa dariya har da rawar ta. Haɗe rai yayi irin yaji haushin nan yayinda cikin ransa farin ciki yake yi ganin yadda take walwala, godiya yake wa Allah da ya haɗa su dan daga cikin dalilan guduwar nasa daga gida har da batun matar aure da ake takura masa dashi. Cikin wannan tunanin da yake yaga ta jefo mishi ball ɗin ya kuwa cafe kafin shima ya shamma ce ta ya fara buga ball ɗin towards ɓangaren ta, da sauri ta bishi suka shiga bugawa har tayi nasarar ƙwace wa ta koma garin sa da wasan ya biyo ta da sauri tana ta kubce masa har ta daka tsalle zata jefa ya ruƙo ta ta kuwa faɗo ball ɗin tayi gefe ya matsa gurin da sauri ya riƙe, cikin ɗan ɗaga murya Kisnah ke faɗin "Allah You cheat, wannan cheating ne, ai dai ba a haka kawai se a ruƙo mutum". Dariya yayi mata haɗe da gwalo ya tafi ragan ta da ball ɗin sedai yana zuwa jefawa itama ta tafi da sauri ta jawo shi ya kuwa yi baya har suna yin gware kafin ya faɗi, da sauri ta ɗauke ball ɗin ta jefa net ɗin shi, kwaɓe fuska yayi ita kuma ta hau yar fa hannaye "Kaga maganin me yin cuta a wasa, Gashi nan na cinye ka wobul (tayi masa gwalo), kuma na tashi wasan tafiya zanyi football". "Allah baki isa ki tashi ba, se da kika ga kin cinye ni zaki tashi Allah a'a sedai mu cigaba". Da sauri ta ruga da gudu tana barin basketball field ɗin heading to football field, da ɗan gudu gudu shima Asad ya bita trying to catch her sedai tuni ta shige cikin masu yin football ɗin da ta ga suna da yawa ba iya su Meenah bane, dole ya haƙura ya koma ya samu seat ya zauna Yana maida nunfashin wasa da kuma gudun da yayi. Da sauri ta shige field ɗin ta ɗauke madaidaiciyar ball ɗin da suke bugawa, tsayawa duk sukai suna kallon ta kafin Surayya ta nufe ta "Meye haka Kissy, please give us our ball ki tafi kema ki cigaba da basketball ɗin ki". "Mun gama ai, nazo yin football ne da ku". "Then Zaki shiga team ɗin mu ne dan mune seven in number su kuma eight, guys queen Kisnah is joining us, she'll be in our club, so the game will be restarted". Aikuwa haka kowa ya koma club ɗin shi aka fara afresh, sosai suka maida hankali kan game ɗin kowa yana trying to score for his team, game ɗin ba ƙaramin daɗi tayi musu ba da at last aka tashi 3-1, su Kisnah 3 su Meenah 1 dan fa Surayya ba ƙaramar ƙwalluwa bace a football game. Kan tables ɗin da ke gaban field ɗin suka zazzauna kowa na maida numfashi kafin su fito da ruwa suka hau sha, ko da suka sha ruwan haka suka cigaba da tsokanar juna, ana tsokanar su Meenah su kuma suna depending if not because, if not of, har goma kafin su tashi suka tafi ɗaki. Tare da Asad Kisnah ta jera suka wuce floor ɗin yana ta bata labari, his school life, family drama and more tana ta dariya. Ko da suka je ƙofar ɗakin haka suka taya bakin entrance ɗin suka cigaba da hira har suka shiga firar Indian films tana ta lissafa masa fina finan da ta kalla shima haka "Kin kalli mother India?". "No, Amma naji ana yayi kyau so after na bar nan zan neme shi in kalla". "Yayi kyau over wallahi, ai ina dashi, go and freshen up Nima kafin nan nayi wanka na huta se kizo mu kalla". "Okay, yanzu kuwa dan har na fara zumuɗi, yauwa room nawa ma?". "Wai har kin manta?, Jiya fa na gama faɗa miki". "Kai dai tuna min ina sauri in wanka". "Room 52 girl". "Ok, see yha soon Mr Man". Ta faɗa tana shigewa ɗakin nasu shima ya wuce nasa, a falon ta tadda su Surayya duka suna zaune da alama har sun yi wanka dan sun cire sport wears ɗin, bedroom ɗin ta ta nufa zata shige Meenah ta dakatar da ita da sentence ɗin ta "Wai Kisnah a ina kika samo mutumin nan da yau gaba ɗaya ya ɗauke hankalin ki daga kan mu da ma Deeq, dan gwara ma Deeq ya je unguwa ze dawo amma daga jiya da muka zo wajen nan zuwa yau a falo kaɗai muke samun zama dake daga mun fita shikenan se kuma mun ganki". "He's a friend, don't mind". Haka ta faɗa kafin ta wucewar ta ciki, da ido suka rakata har ta ƙarasa shigewa kafin Surayya tayi saurin canja topic ɗin Leekha na karɓa mata dan kar ma akawo wani batu kan Kisnahn. Wanka tayi kamar yadda tace masa ta canja kayan ta zuwa guntun wando iya gwiwa da ƴar ƙaramar rigar sa da bata ƙara sa sauka kan cikin ta sosai ba ta kitse jelar kanta tare da kame ƙarshen da ɗan ƙaramin band yadda ba zata since ba dan sosai kan ke da santsi. Gaba ɗaya nan ta baro wayoyin ta dan bata san tana kallo ana damun ta da kira shiyasa ma ba zata tafi da ko ɗaya ba, adai falon ta kuma tadda su har yanzu suna zaune se dariya suke yi alamun hirar tana kai musu yadda suke so gaban su cike da kayan ciye ciyen da drinks kala kala. "Se na dawo". "Ina kuma zaki yanzu?". Wannan karon Leekha ta tambaya, ɗan kallon Leekhan tayi cike da jin haushin yadda suke wani titsiye ta kamar wata ƙaramar yarinya sedai sanin ba halin Leekhan bane hakan se ta mata uzuri yau ɗaya dai "Ɗakin Asad, akwai Film ɗin da zamu kalla tare a system ɗin shi". "Why not shi yazo ku kalla a nan?". Hameedah tayi interrupting sedai ko kallon ta Kisnah bata yi ba ta dubi Surayya "Mind joining us?". "No, am feeling somehow sleepy, kya bani labari". Gyaɗa kanta tayi tana ɗagawa Meenah yatsu biyu "Se na dawo babe". "Hope you enjoy the movie". Meenah ta amsa mata sannan ta fice, tana fita Surayya ta miƙe ta musu good night ta shige bedroom ɗin ta haka ma Leekha ya saura Hameedah da Meenah, juyowa Hameedah tayi tana kallon Meenah da wani expression on her face yayinda Meenahn ta kau da kai kamar bata gani ba ta mata sallama ta wuce, dole ba dan ta so ba itama ta wuce nata bedroom ɗin dan ba yadda zata yi bayan ta kashe ƙwan ɗakin. Knocking biyu Kisnah tayi Asad ya buɗe mata ƙofar ɗauke da murmushi a saman fuskar sa yana sanye da three quarter da farar t-shirt da ta kama jikin sa sosai, itama smile ta Masa tare da shiga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe. Kan doguwar sofar dake ɗakin ta zauna tana ɗan miƙe legs ɗin ta, be zauna ba ya wuce wajen fridge ɗin ɗakin ya zubo musu dambun naman dake cikin wani rufaffen madaidaicin container ya Kuma ɗauko drinks ya kawo ya ajiye kan Centre table ɗin da ke falon ya koma ya ɗauko glass cups masu kyau guda biyu ya ajiye sannan ya koma ya ɗauko system ɗin sa dake kan bed kana ya dawo ya janyo table ɗin gaban sofar a hankali kafin ya zauna kusa da Kisnah yana danne danne cikin system ɗin kafin ya ɗago ya dube ta "Ready?". Yesssss". Ta faɗa prolonging the 'S' sound. "Here we go". Ya faɗa yana starting film ɗin sannan ya ɗora kan table ɗin suka shiga kalla. Tun kafin ayi wani nisa sosai Kisnah ta fara kuka dan sosai Film ɗin yake da abun tausayi, lallashi ne Asad ya sha shi dan kamar wata ƙaramar yarinya haka ta koma, wasa wasa ba Film ɗin ya ƙare ba se after 2 dan it's a 3 hour film, ko da aka gama bata tafi ba wani Indian comedy na Rani Mukherjee me suna Aiya ya saka mata dan lightening mood ɗin ta, cikin ƙanƙanin lokaci kuwa se gashi tana sheƙa dariya kamar ba ita ce ta sha kuka ba, a hankali a hankali bacci yake fisgar ta dan yau ta gaji sosai har ma dai yayi nasarar sace ta gaba ɗaya, gyara mata kwanciya Asad yayi ya cigaba da kallon sa har se da Film ɗin ya ƙare wanda lokacin it's to five am sannan ya fara tashin ta a hankali. A hankali ta fara buɗe idanun ta ta sauke kan sa, murmushi me sanyi ya yi mata kafin cikin cool and low tune ya Fara mata magana "Hey sleeping beauty, it's subhi, kije kiyi sallah a ɗakin ki, okay?". Out of sleep ta gyaɗa masa kai kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa sedai dake ba sakin ta baccin yayi ba se ta kasa har se da ya riƙe ta helping her to stand ya kaita har bakin ƙofa sannan ta zare jikin ta tana lumshe masa ido alamun zata iya tafiya, waving ɗin ta yayi ta fita kafin ya maida ƙofar ya tafi toilet dan yin alwala. Tafiya take a hankali har tana ɗan layi na bacci har ta wuce ɗakin su bata sani ba , daidai lokacin Saraki ya fito dan tafiya masallaci kamar yadda ya saba dan a can yake karatun Alkur'ani tare da nafilolin sa kafin exact lokacin sallah yayi, sosai yayi mamakin ganin ta a wannan lokaci and to his utmost surprise kamar ma layi take alaman bata cikin hayyacin ta sosai. Kamar ya wuce ta sedai ya kalli ƙofar ɗakin su da ta wuce a baya sosai dan shi yana room 45 ne su suna 50 amms har ta wuce ɗakin nasu tama gota nashi, da sauri ya ƙara sa inda take tare da ruƙo ta dan dakatar da ita, a hankali ta juyo dan fa baccin ne sosai a kanta, ganin shi yasa ta ɗan ware sleepy eyes ɗin ta da suka canja kala zuwa golden brown saboda bacci "Yaaaaaaa". Ta ja sunan sosai abinda ya sa Saraki kuma shaida ba'a hankalin ta take ba "Yaaaaaaa ɗakiiii zaaani". Cikin takaici ya juya ta zuwa hanyar da ta baro hakan yasa ta buɗe idon sosai ta gan a bakin room 43 ma take "Kaga ban ma san na wuce ɗakin bama, am toooo sleeeepyyy". Bece mata komai ba har lokacin sedai cikin ransa cewa yake taya zata san ta wuce tunda bata cikin hankalin ta? Har bakin ƙofar ɗakin nasu ya rakata kuma be tafi ba seda yaga ta shiga cikin parlon kafin ya juya ya koma hanyar da ya baro heading to the elevator. A falo ranar Kisnah ta kwana dan baya iya kai kanta ɗaki ba saboda nauyin baccin dake kanta, se after seven ta tashi ta koma bedroom ɗin ta ɗora baccin ta daga inda ta tsaya. Ƙarfe goma ta farka ta shiga wanka sannan ta shirya bayan ta fito, yau kam ba laifi Canadian gown ta saka da yakai mata ƙasa dan har yana jan ƙasa ta baya ta sake gashin ta bayan ta taje shi tare da shafe shi da mayukan kai masu ƙamshi ta feshe shi da turaren gashi ta ɗora masa sun hat me kyau sosai kalar brown Wanda gown ɗin jikin ta milk and brown ce haka takalman ƙafar ta milk heels ne. Ƙarar wayar ta yasa ta ƙara sa inda ta watsar dasu jiya da dare ta ɗaya wadda take ƙarar ta kai kunnen ta ganin sunan Surry "Mun fita kina bacci Queen, in Zaki biyo mu muna highway mountain". "Okay, I'll see in zan zo ɗin". "Okay". Surry tace tare da kashe wayar. Zama ta ɗan yi tana tunanin ta bisu ne ko kuwa tayi zaman ta? "Garden". Kamar daga sama haka sunan ya faɗo cikin ranta, da sauri kuwa ta miƙe dan a rayuwar ta tana matuƙar son guri me korayen ciyayi da bishiyoyi shiyasa tun tana yarinya Abbi yayi mata ƙaton garden a gidan su. A hankali a hankali take takawa kan corridor ɗin ɗakunan dan sosai marbles ɗin ke da santsin da in batayi taka tsantsan ba ze iya tiƙa ta da ƙasa saboda tsinin takalmin ta, gyaran muryar da taji a bayan ta yasa ta ɗan waiga hakan yasa suka yi four eyes da Saraki da ya fito dan zagaya wa saboda jiya gaba ɗaya a ɗaki ya wuni shiyasa yanzu yake buƙatar fresh air "Good morning yaaa". Gyaɗa mata kai yayi alamar amsawa dan yanzu kam ya sauko daga fushin da yake yi dan ganin abinda ya faru jiya yasan da beyi fushi ba da ko yaya ba zai bata space ɗin kwana wani waje ba dan zata kasance ƙarƙashin idon sa ne. "To where?". "Garden, won't mind joining me please, am lone". "Okay". Ya ce mata dan haka suka jera suka cigaba da tafiya, daɗi sosai Kisnah ta ji ganin ya dena fushi da ita haka itama se ta ajiye alwashin ta a gefe. A tare suka shiga elevator ɗin ɗan yana da faɗi sosai, a third floor suka sauka dan akwai garden me kyau a floor ɗin kafin ta masa jagora zuwa garden ɗin da tun 2 years back ta haddace hanyar shiga cikin sa though an samu sauye sauye a resort ɗin.................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 23 (8/17/2022 8:10 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Assalamualaikum warahmatullah ɗauka cin masoya littafin *SARAKI* daga kowane group most especially*SARAKI FANS CLUB* ina godiya sosai da addu'o'in ku ga ƴar uwa ta , Allah ya saka da alkhairi ya bar ƙauna, Allah kuma ya jiƙan dukkan musulman da suka riga mu gidan gaskiya, marasa lafiya Allah ya basu lafiya, mu da muke da ita Allah ya kara mana ya bamu ikon gode, masa Ameen summa Ameen. Once again, nagode Allah ya bar zumunci da ƙauna 🥰. Page 2️⃣3️⃣ _______________________📖 sunkuyar da kanta tayi ƙasa ganin irin kallon da yake watsa mata na rashin yarda kafin ta sake ɗagowa sedai wannan karon idon ta ya ɗan sauya launi "I swear to God ban Sha komai ba, so nawa zan faɗa maka bana shaye shaye ne yaaa"?". Ta ƙarashe maganar ranta na suya, a rayuwar ta taƙi jinin shaye shaye shiyasa kullum cikin yiwa su Hameedah faɗa take yi, ita magani ko na rashin lafiya in har ba kwantar da ita tayi ba bata taɓa shan sa, duk kuwa irin ciwon kan da zata yi ko ciki sedai ayi mata allura dan magani is her perfect enemy. Ɗan furzar da iska yayi daga bakin sa kafin a hankali yayi magana batare da ya kalle ta ba "What about haɗa hanyar da kika ringa yi jiya da na ganki, me ya kawo shi?". "Bacci ne a kai na sosai saboda na gaji sosai jiyan kuma ban samu hutu ba shiyasa bacci yaci ƙarfi na but am in my sence". "Then daga ina kika fito a lokacin dan nasan ba yadda za'a yi ki fito daga ɗakin ku at that time in har kina hankalin ki kamar yadda kika ce, to me ma zaki fita nema?". "Ba daga ɗakin mu na fito ba, Asad ya taso ni daga ɗakin sa da nayi bacci yana faɗa min lokacin subh prayer yayi". Ta faɗa da ɗan nuna gajiyawa cikin Muryar ta dan wallahi ban dashi ɗin bata ga wanda ya isa ya tasa ta gaba haka yana mata irin wannan tambayoyin bata ci masa mutunci ba. Sedai ta rasa me yasa she's very and very tolerant when it comes to Saraki abinda bata ɗauka wajen kowa se shi yayi mata bata damu ba, kalli dai yadda yayi fushi har ta je bashi haƙuri yana wani yaga ta abinda ta tabbatar da wani ne da se taci masa a lokacin kuma bata jin zata sake kallon shi da mutunci se gashi shi yayi duk kuwa da ta ji haushin abinda yayi mata amma da ya saki fushin se taji ba zata iya share shin da tace ba. "Naje kallon Film ne ɗakin sa and I over slept there shine ya tada ni na fito har muka haɗu". Ta faɗa da ɗan sauri ganin be amsa bayanin da ta yi masa ba se ma zuba mata ido kawai da yayi yana kallo wanda se da ta gwammace da bulala yasa ya dake ta da hukuncin da yake mata da idanun sa. "Na fahimta and dama I thought so, sedai Sam be dace ba a bisa tsarin musulunci mace baliga ta shiga ɗakin namijin da ba muharramin ta ba har ta kai irin lokacin da kika kai saboda gudun sheɗan and Kuma mutane ma zasu iya miki wata kallon na daban dan ba wanda yasan dalilin zuwan ku ɗakin kamar yadda ni kika min bayani yanzu, so pls kar ki sake hakan, okay?". A hankali ta gyaɗa masa kanta tana auna zantukan sa cikin ranta, ita bata ga abin wani rashin dacewa ba tunda ba wani abu suka yi ba a ɗakin, kallo fa kawai tayi se kuma bacci ya kwashe ta and he woke her up, to meye a cikin hakan?, Babu komai! And mutane, who cares about them da abin da zasu ce? Sun daɗw ba su ce ba she didn't give a damn, Amma tun da yace hakan insha Allah zata yi ƙoƙarin dainawa dan dai ta riga ta saba. Zama suka cigaba da yi bakin pool dake ciki garden ɗin ƙafafun ta cikin ruwan shi kuma yana kallon ruwan ƙafarsa a tanƙwashe, fira suke yi jefi jefi wadda a hankali yake sako mata nasiha cikin hirar wadda alamu suka nuna suna tasiri a ranta. Basu bar wajen ba se da aka kira zuhur, masallacin dake resort ɗin ya wuce bayan yace taje tayi sallah a ɗakin su, sallar tayi ta zauna jiran shi kamar yadda yace mata, 30 minutes after se ga Knocking ɗin shi, wayar ta ta ɗauka ta riƙe a hannu kafin ta nufi ƙofar ta buɗe, ɗan ja baya yayi ya bata hanya ta fito sannan suka sake fita daga resort ɗin zuwa parking lot, motar ta dake nan a rufe masu kula da wajen suka yaye musu, tass take ba ko alamar datti dan da alama kullum ake buɗe ta a goge a kuma mayar a rufe. A hankali motar ke tafiya kan titin dake wajen yayinda motar tayi shiru ba abinda ke tashi se karatun Alkur'ani se ko sautin Muryar sa dake bin karatun can ƙasa, daga kan kujerar da take zaune take ɗan kallon shi a kaikaice cikin yanayin burgewa dan yadda bakin sake motsawa yana bin karatun cike da ƙware wa ba ƙaramin burge ta yayi ba. Da haka ya ƙarasa da ita highway mountain wajen su Meenah, yana ajiye ta ya juya dan se six zasu bar wajen and now it's only to 2, ya kawo ta ne dama dan kar ya wuce ɗakin sa ta tafi wajen Asad yake kowa ne oho, sedai yasan ba yaron da ya gansu a bakin spa bane dan ba haka yaji ta kira wancan ba though be riƙe sunan ba. **************** Ranar juma'a ce, ranar da ta kasance farin cikin dukkan wani musulmi dake faɗin duniya, kamar yadda yake al'ada a ƙasar Hausa sanye kusan kowane magidanci, tsoffi da yara suke da sabon kayan su, ba wai se lallai sabo fil da ba'a taɓa sawa ba a'a har da waɗanda ya kasance irin ƙasan akwatin nan wato masu kyau da ba'a saka su sosai ba irin dai na sallah ko wani sha'ani. Falo ne me matuƙar girma da aka ƙawata da kayan ƙawa da alatun sarauta, matuƙar girman falon ya isa a yi bedroom biyu a cikin sa kai har ma da toilet in da za'a zauna a tsara. Falon Maimartaba Sarki Muhammad Hasheem II kenan da yake zama tare da iyalin sa gaba ɗaya a dukkan ranaku irin na yau wato juma'a da kuma asabar dan samar da shaƙuwa da ƙauna tsakanin sa da ƴaƴansa da ma matan sa gaba ɗaya. Zaune yake kan ɗaya daga cikin manyan leather seats da suka ƙawata falon ya hakimce ciki irin zaman da ya kasance sabon sa sedai yau ba rawani ko wani abu da yayi wa ƴaƴan sa shamaki da kyakkyawar fuskar tasa, hasalima sanye yake cikin baƙar jallabiyar da ta saukar masa har kan dunduniya kansa a buɗe ba ko hula yayin da yatsan tsakiyar hannun sa na dama ke sanye da counter yana lazimi jefi jefi kuma yana sauraren hirar ƴaƴan nasa, gefen daman sa ya kalla a nutse inda gimbiya Haleematu ke zaune ya sakar mata tattausan murmushi "Gimbiyar Giwa kin kuwa ji abin da ƴaƴan ki ke taunawa a kai?". A ɗan nutse ta gyara zaman ta tana sake masa nata murmushin "Naji su sarki na, ai dama na daɗe ina faɗa maka ƴaƴan nan naka kunyar su da sauƙi tun bare ma wannan baban namu". Ta ƙarashe tana ɗan hararar Jamal dake cikin ƴan uwan sa biyu da suka rage a gidan, yarima uthman da princess wadda asalin sunan ta kausar ne. "Ayya Mami ayya, Allah ni Ina da kunya, Allah yasa Abiy yaji ya Uthman ne yake magana bani ba ko Maama?". Da sauri sarauniya Rumana ta gyaɗa kanta cikin goya wa Jamal baya tana ƴar dariya "Sosai ma kuwa babana, duk laifin na wancan yaron ne amma dake uwar sa bata son laifin sa ai kaga mu an maƙala mana". Dariya kowa dake falon yayi ganin yadda Yarima Uthman ke ɓata fuska sedai kafin yayi magana princess ta riga shi da sauri "Kowa ya tsaya, Abiy kawai ka sa in raba wannan gardamar kasan nafi kowa iya raba faɗa". Da sauri Abiy ya gyaɗa kansa har lokacin da murmushin jin daɗin ganin haɗin kan iyalin sa a fuskar sa "Sosai ma princess, na baki dama dan nasan kin fi kowa iya hukunci a nan ciki kuwa har da ni". Cikin farin ciki princess ta ƙarasa wajen Abiy ta ɗan rungume shi kafin ta janye ta tsaya tana ƙarawa Uthman da Jamal kallo kamar me yin tsakani yayinda falon ya ɗauki shiru kowa na jiran jin me zata ce yayinda Jamal da Uthman duk kowa yayi irin nasa kalar tausayi da fuskar dan tace bashi bane. "Ina ganin a ɗaga bikin kawai Abiy zuwa lokacin da zan gano waye ya faɗi yadda yake so tsarin bikin ya kasance se a saka sabuwar rana ko?". A zabure duk suka hayayyaƙo suna faɗin "what" kusan a zabure, gaba ɗaya Abiy dasu Mami suka saka dariya kafin cikin dariya princess take cewa ai duk sun faɗa tun da gashi nan sun shiga tashin hankali dan za'a ƙara lokacin bikin. "Come on my princess". Abiy ya faɗa yana buɗe mata hannu cike da ƙaunar ƴar tasa da sauri ta faɗa ya rungume ta yana tapping bayan ta kamar me lallashi, murmushi me faɗi ne wanzu saman fuskar sarauniya Rumana ranta yayi fari ƙal ganin yadda Maimartaba yake nuna son autar ta a gaban kowa baya ko jin kunya sedai farin cikin ta se ya ɗara haka da uthman yake wa wannan ƙaunar, nevertheless a haka ma taji daɗi. A hankali ta tashi daga jikin baban ta ta koma kusa da mami ta zauna kafin ta ruƙo hannayen Mamin suka yi musayar murmushi a tsakanin su. A hankali murmushin fuskar sarauniya Rumana yake fading har ya ɓace ɓat, in da akwai abinda taƙi jini a rayuwar ta ya biyo bayan alaƙar autar ta da gimbiya Haleematu, ta rasa wane irin sakaci tayi da har shaƙuwa irin wannan ta shiga tsakanin su haka sedai ta danganta hakan da sakewar da tayi mata kasancewar ta auta, a baya bayan nan Allah kaɗai yasan irin ƙoƙarin da take wajen ganin ta janye ƴar ta daga Haleematun sedai hakan ya faskara, zata iya cewa ƴartan tafi sabawa da kishiyar tata fiye da ita wanda hakan ba ƙaramin ciwo yake mata ba, shekaranjiya yarinyar ta dawo daga hutun dolen da ta tura ta gidan iyayen ta duk dan ta samu ta raba tsakanin su sedai tana dawowa a shekaranjiya ko sassan ta bata je ba ta wuce na Haleeman hakan kuwa ya ƙona ranta sosai sedai ita yarinyar ko a jikin ta. Hira suka cigaba da yi cikin kwanciyar hankali da farin ciki, daga Maimartaba har Mami zuƙatan su na ɗauke da kewa da wani giɓi sedai duk sun yi ƙoƙarin danne ta ta yarda ba wanda ya gano hakan cikin ƴaƴan su. Hira ce suke yi kan shirye shiryen bikin su Jamal da Uthman ɗin da za'a yi couple of weeks ahead, sati biyu kenan da saka date ɗin bikin which is choosen to be four weeks, yanzu haka suna batun ginin da ake kan ƙara sawa inda amaren zasu zauna ne wanda ke cikin gidan sarautar. Seconds pass by turning into minutes and minutes to hours, hours to days and days to weeks. Cikin hukuncin Ubangiji aka ɗaura auren Yarima Jamal Muhammad Hasheem II da amaryar sa gimbiya Fadeela Lamiɗo Turaki, Yarima Uthman Muhammad Hasheem II da amaryar sa gimbiya Sulaim Ibrahim, bidiri sosai ake sha cikin garin Giwa dama maƙwabtan ta, buki ne ake irin na ƴaƴan gata kuma ƴaƴan Sarauta, baka jin tashin komai se na kiɗan ganguna, busar sarewa da kuma algaitu. A taƙaice dai se da akayi sati ana biki kafin aka kammala komai aka ɗauko amare daga nasu garuruwan, Sulaim ƴar abokin Maimartaba ce ta maƙotan garin su wato garin hayi, gimbiya Fadeela kuwa yar wan Mami ce Wanda shine sarkin garin su yanzu wato masarautar Fulde. Kowace amarya se da aka fara kai ta ga gimbiya Haleematu kafin aka kai ta wa sarauniya Rumana sannan aka rakata sashen ta daga can, manya manyan sassa ne masu girma daidai gwargwado wanda tun daga ginin zaka san mazauna cikin sa matasa ne masu ji da zamani dan duk wani kayan ƙawata gida na zamani akwai shi a dukkan part ɗin biyu da suka kasance iri ɗaya har fenti se bambancin kayan ƙawar ɗaki da aka zubawa kowacce. Sashen na kallan juna se dai da tazara me ɗan yawa a tsakani, tun washegarin kawo su suka shiga gaida surukan su inda suka haɗe a nan aka gaggaisa, sedai a kallon farkon gimbiya Fadeela ta gane gimbiya Sulaim zata yi jin kai da izza dan se wani fuffusgar kai take yi tana basarwa wanda hakan halin uwar ta ne ta ɗauke tsaf shiyasa sam basu da jituwa da mami sedai Maama wato gimbiya Rumana wanda tsabar kissa da iya ƙulla tuggu yasa jinin su ya kwanta da juna shiyasa ko da batun auren da me martaba yake wa Uthman ya sake tasowa ta zauna ta faɗakar da ɗan ta irin matar da take buƙatar ya aura wadda take ganin Sulaim takai duk yadda taso, da hilla da komai ta saka masa son Sulaim a ransa aka kuma yi Sa'a itama ta karɓe shi wanda lokacin tuni soyayyar Jamal da Fadeela tayi nisa se kawai aka nema wa kowanne auren wadda ya kawo tunda duk basu da wani aibu. Matsayin matar wa Fadeela take girmama Sulaim sosai hakan yasa har ta so ta raina ta seda mijin ta yayi jan ido tare da gargaɗin fadeelar kafin abin ya dakata se Kuma aka koma ƴar kowa ba ruwan sa da kowa, dukkan su sha'anin gaban su suke ba me shiga harkar wani se ko ƴar gaisuwar da bata wani tsayi tsakanin su in sun haɗu wajen iyayen. A hankali rayuwa na tafiya Sulaim ta janye daga jikin gimbiya Haleematu dan hatta gaida tan da take yi se ta daina zuwa se sa'i da lokaci in ta daɗaɗa mata bisa zuga da kitsar da uwar mijin ta tayi mata ita da mahaifiyar ta. Ko kaɗan abin be ɓatawa Haleematu rai ba dan tun farko da ta gane halin yarinyar taji sam ta fice mata a rai se dai tana ɓoyewa dan gudun ɓullowar ɓaraka cikin alhali, bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen zaunar da ɗiyar ta Fadeela ta mata nasiha me ratsa jiki tare da ƙara tunatar da ita sanin girman na gaba da ita tare da girmama su, muhimmanci kau da kai da son zaman lafiya domin alhamdulillah ta sami Fadeela har ma fiye da yadda ta san ta dan yarinya ce me hankali da sanin ya kama ta. Tun zuwan Fadeela gidan sarautar suka ɗin ke da Laylah dan dama se hali yazo ɗaya ake abota, tun farkon ganin ta da ita a kilisar Mami Mamin tayi mata bayanin ta da matsayin ta na surukar ta matar Sarakin ta insha Allah, da haka ta fara jan Laylah a jiki se gashi tuni sun ɗinke dan Laylah akwai saurin sabo ga kirki kamar me...............................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 24 (8/18/2022 9:27 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣4️⃣ ________________________📖 "Karka damu Alh Haladu, ban yi wannan tafiyar ba se dan neman mafita kamar yadda kace min shiyasa nabi duk procedure ɗin da ka sanar da ni wajen samun takardun nan, ina tabbatar maka kwanan kusa zamu mallaki dukiyar da muke ta wannan wahalar a kanta, dan dama mu muka cancance ta ba wata ƴar sa can daban ba, kai abokin sa ni kuma ɗan uwan sa ko ba haka ba?". Kawu ya faɗa yana ɗagawa Alh Haladu gira cikin sakin murmushi me faɗi, murmushi shima Alh ya saki yana amsawa kawu "Sosai ma kuwa Sama'ila, ban manta ba lokacin da Safwan na raye haka muka sha wahalar haɓaka dukiyar shi yana zaune taƙamar sa arziƙin sa ne kuma har ya mutu ba wani abu muka amfana dashi ba, kaga kamar ni ba abinda na samu tattare da shi se wani ɗan ƙaramin Companyn robobi, shikam wancan banzan me ruwan ustazai ko Company ɗin be tsira dashi ba se gida da gwangwanin motar da yake ciki kaga kuwa yanzu dan mun nemi haƙƙin mu ai ba laifi muka yi ba ". "Sosai ma kuwa........" Kawu ya amsawa Haladun yana ɗorawa da "............yanzu kaga wannan takardun sune makaman mu, muddun muka samu tayi signing akai magana ta ƙare, a da ina ta tunanin hanya mafi sauƙi da zan mallaki dukiyar na rasa amma haɗuwa ta da kai ta buɗe min kai sosai, kaga ba batun kashe ta kamar yadda da na ke hasashen yi kaga yanzu se ta rayu". Gyaɗa kai cikin gamsuwa Alh Haladu yayi "Haka za'a yi sedai kasan da zafi zafi akan daki ƙarfe, yanzu daka huta se ka shiga Company ka haɗa cikin takardun da ya zame mata dole ta sa hannu, sedai sefa ka kula dan kar ta gane, kai ta kowace hanya ma Karka bata damar karanta takardun, a ɗauke mata hankali da wani abu me muhimmanci gare ta ta yarda zata saka hannun batare da ta san ta saka ɗin ba". Sosai suka cigaba da tattauanawa kan tafiyar da suke ganin zata ɓulle musu har tsawon wani lokaci kafin Alh Haladu ya bar gidan kawu zuwa nasa. **** Rayuwa suke cikin jin daɗi a resort ɗin, kullum da wajen da zasu fita suje cikin garin Sawariya, garin da masana suka tabbatar babu wanda ya kaishi ababen tarihi da jin daɗin rayuwa a kaf ƙasar Hawarya shiyasa kowa da ya ɗan Sami chance to fa burin sa yaje garin yayi spending wasu lokuta dan jin daɗin rayuwar sa da ziyarar wajejen tarihi. Kwanan su na shida kenan a garin kuma kullum se sun fita bisa jagorancin Asad da Deeq dan shi Asad ɗan asalin garin ne shi kuma Deeq yana yawan zuwa dan a nan ƙanwar mamar sa ke aure. Yau da dare kam zaman haɗa kayayyakin su suka yiyyi dan gobe ne zasu bar resort ɗin saboda dama seven days suka yi booking, sun so yafi haka sedai dole suka haƙura dan Kisnah ta sanar dasu dole zata maida hankali kan batun dukiyar ta cikin ɗan hutun da suka samu kafin su ɗora batun project. Manyan shopping bags da suka shiga one of the biggest mall na garin sukayi siyayya, da yawan su tsaraba ce suka yi wa family ɗin su ban da ita da Surayya, ita kam yawancin kayan wa Saraki ta saye su seko kayan yara da ta siya da yawa dan tana son leƙa gidan marayun d ta daɗe bata je ba saboda makaranta da abinda ya faru da Surayya, ragowar kuwa duk nata ne se wasu set ɗin Egyptian jallabiya da ta ga kwana biyu Megado na yawan amfani dasu, burge tan da suka yi yasa ta ciran mata dan har ta auno su a jikin ta, ban da ita kuwa bata ɗaukawa kowa ko tsinke ba. Ranar basu kwanta da wuri ba saboda hotuna da suka ringa zagaye resort ɗin suna yi, a lokacin kam se da Kisnah ta kasa daurewa ta shige swimming pool ɗin da ke wajen, rabon ta da pool ta manta dan tun farkon dawowar ta da ta shiga wani ashe is not that conducive ta ɗan yi fama da rashin lafiya shine fa Abba Hameed ɗaya daga cikin abokan baban ta and the one she respect much ya hana ta swimming se gashi yau ta kasa daurewa seda tayi. Ba ƙaramin daɗin pool ɗin taji ba dan se ayyana wa take a ranta da ta san haka yake da tuni kullum se ta shiga. Kashegari dai suka tarkata ina su inasu suka bar garin Sawariya zuwa garin Manya cike da kewar kyakkyawar rayuwar resort ɗin se dai ga Kisnah ta ƙudure tana kammala project ɗin ta to fa se taje tayi watanni a can. Ƙarfe ɗaya da rabi na rana suka shiga garin Manya haka kuma suna shigowa gari sukayi sallama da Kisnah dan su gaba ɗaya a motar Meenah suka yi tafiyar ita kuma daban ta zo a tata, Yana yin parking a lot ma'aikatan gidan suka dinga zuwa yi mata sannu da zuwa tana amsa musu cikin sakin fuska da fara'a, taji ba daɗi ganin bata ruƙo musu komai ba se kawai ta fiddo ragowar kuɗin handbag ɗin ta wanda suke da ɗan kauri ta miƙa wa Khamees tace ya raba a bawa Kowa. Sabuwar godiya suka dinga yi mata har ta samu ta kufce zuwa cikin gida, bata tadda kowa a falo ba haka bata bi takan tambayar ina suke ba ta shige ɗakin ta da sauri saboda gajiyar jikin ta ba kaɗan bace. Wanka ta sake yi kamar ba ita ce tayi har wanka biyu ba a resort ɗin kafin su taho, riga mara nauyi ta aka tabi lafiyar gado tana ƙure gudun Ac ɗin ɗakin ta da taji bata kai mata ko ina kamar dai ta samu matsala ne. A can ɓangaren Saraki shima wanka yayi ya canja kaya sedai shi masallaci ya fara shiga ya bi jam'in zuhur ɗin da lokacin ta yayi kafin ya dawo shima ya haye mattress ɗin sa yayi ɗai ɗai ya shiga baccin gajiyar tuƙi da na zaman motar da yayi. Kiran sallar da ake yi na la'asar ne ya tayar dashi daga baccin, nauyin da yaji jikin sa yayi masa ya sa ya sake wanka da ruwa me ɗumi kana ya fita Masallacin. Ko da aka idar ya dawo cikin ragowar ma'aikata ya zauna yana amsa sannu da zuwan da tambayar gajiyar da suke masa kafin ya cigaba da sauraren hirar da suke a tsakanin su batare da ya tsoma musu baki ba ƙarƙari yayi murmushi in sun yi abin dariya har wajejen shida kafin ya koma masallaci ya shiga karatun Alkur'ani har aka kira magrib. Se a lokacin Kisnah ta sami farkawa tana sauke ajiyar zuciya na daɗin da baccin yayi mata tana kuma ɗan yamutsa fuska na jin yadda ko ina na jikin ta ya mata nauyi kamar wadda tayi wani aiki na daban, wanka tayi da ruwan zafi sosai ta haɗa jikin ta kana ta ɗauka da ruwan sanyin da ya zame mata dole ta fito. Se a lokacin ta tuno da batayi sallar Azahar ba har zuwa magrib hakan ya sa ta koma ta ɗauro alwala ta zura hijab ɗin sallar ta kan towel ɗin jikin ta ta tada Sallah, kamar yadda ta saba gabatar da sallar ta haka yau ma tayi ta ƴar faki ba yawa se lada, lol. Gaban wardrobe ɗin ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka kafin idanunta ya sauka kan tulin tarin sutturar dake shaƙe kamar zasu yi magana, bin su tayi da ido tana tunane tunane a ranta dangane da kayan, ya zama dole tayi sauyin wardrobe and wannan karon ba zata ɓata kuɗin ta wajen siyan native dress ba da iya saka su take ba dan ba ɗaya daga cikin native dress kana daga atamfa, shadda, ko lace da ta taɓa sawa wnada in bata kuskure ba kusan shekarar su ɗaya yanzu cikin wardrobe ɗin. Gyaɗa kai tayi tana yadda da shawarar da ta zo mata kafin ta ciri wani robber jeans ta saka tare da ƴar ƙaramar t-shirt ta gyara kan ta cikin yamutsa fuska dan se taje gyaran ka gobe insha Allah. Gyara ɗakin tayi a gurguje dan yayi ƙura kawai gajiyar da tayi ɗazu ce bazata bar ta tsayawa gyara shi ba kafin ta kwanta, tass ta gyara ɗakin ta saka abun zuƙe datti tai cleaning ɗakin tare da mopping ɗin shi da electric mopper, haka ma falon ta zuwa mini kitchen ɗin ta da bata amfanin komai dashi se sa'i da lokaci in ta Kai mata. Ƙasa ta sauko bayan ta gama aikin ta da ita dama ke yi duk bayan kwana biyu dan bata yarda wata me aiki ta shigar mata ɗaki tun bayan ɗauke ɗauke da ake mata a ɗakin, zama tayi kan 3 sitter dake falon ta ɗora ƙafafun ta masu ɗauke da soft bedroom slippers tana kishingiɗa. Sunan Rayya ta fara kira da ɗan ɗaya Muryar da ya saka gaban Mommy faɗuwa dan bata san yarinyar ta dawo ba shiyasa yanzu da taji Muryar ta hankalin ta ya tashi, da sauri ta tashi daga kan royal seats ɗin dake personal falon ta ta fito har ɗan kwalin kan ta na faɗuwa saboda tsabar sauri, so take kawai taje ta ganta da idanun ta ta tabbatar ita ɗin ce ko kuwa. "Ki kawo min something mara nauyi na ci, am so hungry, and ki haɗo min da milkshake". "Okay Aunty". Rayya ta amsa Kisnah tana nufar kitchen daidai lokacin da Mommy ta faɗo falon da sauri, turus ta tsaya tana kallon Kisnahn, kenan dai da gaske ita ce ta dawo ɗin, wani irin ɓacin rai ne ya rufe ta dan sati ɗayan da yarinyar bata tare da su ba ƙaramin daɗi suka ji ba, hankalin su kwance suke abinda suka ga dama cikin jin daɗi da walwala da rashin tunawa ƙarƙashin wata fa suke cin arziƙi shine kawai zata wani dawo rana tsaka, to wallahi bazata saɓu ba wannan karon shawarar ƙawayen ta zata ɗauka, duk hanyar da zata kautar da Kisnah daga rayuwar su se ta bita ko dan ita da ƴaƴan ta suji daɗin rayuwa. Kallon da ta kafe ta dashi cikin tunanin anya lafiyar ta ta faɗo haka kamar an jefo ta kuma ta zo ta tsaya waje ɗaya kamar wata sojiya se huci take yasa Mommy ta dawo hankalin ta ta shiga kame kame tana yaƙe wanda a fili kowa yake iya gane wannan fara'ar bata kai ciki ba haka kuma damuwa da ɓacin ran ta gasu nan rubuce kan dattijuwar fuskar ta. "Sannu da zuwa, fatan kun dawo lafiya". "Lafiya, fatan kuma mun same ku lafiya". "As you can see". Mommyn ta faɗa tana shigewa dan ta kasa dannar kan ta shiyasa ta shige tun kafin tayi abinda zata dawo tana dana sanin ɓata shirin ta. Da kallo kisnah tabi bayan har ta shige kafin ta ɗaga kafaɗa irin ko oho ɗin nan, abincin ta da Rayya ta kawo ta shiga ci hankali kwance tana yi tana sipping milkshake ɗin har ta gama kafin Rayyan ta kwashe kwanikan zuwa kitchen ita kuma ta cigaba da kallon da ta kunna take yi. Seda aka kira isha kafin ta koma ɗakin ta, sallah tayi ta koma gado ta shiga chattinga a twitter tana ta murmushi dan the site and it's patronizers are so entertaining, tana gamawa da nan ta koma Instagram ta shiga posting hotunan da suka yi lokacin da zasu bar resort ɗin, within minutes sega likes da comments kamar me, tana son instagram sosai dan mutanen ciki na nuna mata ƙauna,wuyar ta tayi posting photo yanzu zaka ga likes kamar ruwan kuɗi. Shiyasa so da yawa ita hau social sites ɗin ta takan manta da kowa dake tare da ita ne dan bata tuna komai se followers ɗin ta dake patronizing ɗin ta, tasan da ace wata business woman ce ita da cinikin da zata dinga yi ba kaɗan bane dan kamar jiran ta suke ne, kaya kuwa haka zaka ga ana tambayar pls abu kaza nata a ina ta siya da abubuwa irin haka dai. Kashe wayar tayi ta aje bayan tayi offing datar ta ganin har ta shafe kusan awannin uku a online, wanka ta sake ta canja kaya zuwa nighties ta kwanta bayan ta kashe hasken ɗakin tare da janyo photon ta a under pillow ɗin ta ta rungume ƙam a ƙirjin ta tare da rufe jikin ta da comforter ta rufe idanun ta, tunanika sosai yake zo mata a lokacin sedai tana fighting ɗin su dan bata son abinda ze shiga barcin ta balle har yasa ta kasa samun bacci me nutsuwa......................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 25 (8/19/2022 10:30 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣5️⃣ Not edited ❎ ________________________📖 Da ɗan hanzari take shiri dan ta makara, a so samun ta ta fita tun 9 dan saka ido sosai akan companies ɗin ta sedai baccin da ya rinjaye ta yasa dole ta makara. Dogon palazo jeans ta saka a jikin ta da t-shirt ta ɗora jacket akai, sun heart ta saka me kyau a kanta tare da Black shafe, sosai tayi kyau yau looking so responsible ba kamar sauran rana ku ba. Wayar ta ɗaya ta ɗauka wadda take amfanin da ita ko yaushe leaving the other a ɗaki sannan ta sauko, girgiza wa Rayya da ke mata tayin breakfast Kai tayi dan bata da wannan time ɗin yanzu. Tun a resort gaba ɗaya hankalin ta ya koma kan dukiyar ta ne, matsalolin da companies ɗin ke fuskan ta ne suka fi damun ta dan haka dole ta maida hankali dan ba zata bari wahalar Abbun ta na shekara da shekaru ya tafi a banza ba dole ta dawo hayyacin ta. A bakin farar motar ta tarar da Saraki yana jiran ta kamar yadda ta sanar dashi ya fito da mota gata nan fitowa, da sallama ta shiga motar abinda ya sashi ɗago kai da sauri ya kalle ta cikin tsananin mamaki, kafin tafiyar su resort ta kan yi masa sallama a duk inda ta same shi dan baya ko kallon ta in bata yi sallamar ba haka kuma so da yawa ze tursasa ta fita daga motar in har bata yi ba se tayi ta shigo, amma daga lokacin da suka sami saɓani yayin birthday party ɗin Surayya ta ajiye a gefe haka shima lokacin yana fushi ba ya ce mata se tayi se gashi yanzu ta bashi mamaki. "Good morning yaaa, ya gajiya, we're late pls muje". Janye kan sa yayi daga kallon ta yana gyaɗa mata kai alamun amsawa kafin yayi wa motar key suka fita daga gidan cikin addu'ar sauka lafiya daga workers ɗin. Shiru tafiyar tasu kamar ko yaushe dan da wuya kaji tashin sauti cikin motar duk sanda suke tafiya haka in ba wai na karatun Alkur'ani ba se ko wa'azin da yakan sa da yawan lokuta se kuma in maganar da ta kama tsakanin su. "Yaa Please akwai maganar da nake so muyi in mun ƙarasa office, Dan Allah Karka ce a'a". Ɗan shiru yayi kamar me tunani kafin ya amsa mata da "K". Haka suka cigaba da tafiyar kurame dan yau be sa ko ɗaya ba daga karatun har wa'azin har suka ƙarasa, kamar dai kowane daga cikin companies ɗin wannan ma seda akayi screening ɗin su irrespective of wai me company ɗin ce da kan ta, wannan doka ce ta tun mahaifin ta na raye dan gudun afkuwar matsala ko tashin hankali se dai a yanzu ga Kisnah ita bata ga wani amfanin hakan ba tunda a haka ba'a fasa handama da rashin gaskiya a cikin ma'aikatan ba. Wajen da take ajiye mota ta nuna masa ya yi parking kafin suka fito suka jera zuwa cikin babban building ɗin, gaisuwar da receptionist ɗin ke musu ta amsa tana mamakin irin kallon da biyu daga ciki suka bi Saraki dashi. Pretending gaisawa da ma'aikata tayi hakan yasa ya ɗan yi gaba kafin ya tsaya jiran ta tun da be san kan wannan Company ɗin ba, da wannan damar ta yi amfani wajen ƙare masa kallo dan san sanin dalilin kallon da receptionist ɗin suka bishi da shi. Baƙin dogon jeans ne a jikin sa se long sleeve shirt Fara tas ƙafar sa sanye da baƙin brogues da ya sanya, ba ƙaramin kyau yayi ba cikin shigar tun bare gashin kan sa dake ƙyalli wanda ya fito ta ƙasan beret ɗin da ya sanya wa kan sa, se yanzu ta gan dalilin da ya sanya suka wani watsa masa ido kamar zasu cinye shi da su, bata san me yasa ba se ta tsinci kan ta da jin haushin su wanda ya tursasa mata juyawa ta jefa musu wata ƴar iskar harara kafin tayi ƙwafa ta wuce inda ya tsaya suka nufi lifter. Haushi sosai ya cika ta se cika take tana batsewa har suka shiga office ɗin, zama yayi kan kujerar dake gaban ƙaton table ɗin yana bin ta da kallo yadda take ta kumbura fuska kamar wadda aka zaga, kau da kan sa yayi yana ayyana may be ita da employees ɗin ta ne. A hankali yake zagaye idanun sa cikin office ɗin sa yana jinjina girman gurin dan kuwa yaci ayi madaidaitan offices kusan huɗu ko uku, tsaruwar office ɗin ta burge shi dan ba'a wani cika tarkace ba amma yayi kyau sosai, ga kuma tsaftar da ya gani na wajen dan duk da bata cika shiga office ɗin ba amma a share suka tadda shi yana tashin ƙamshi. Zama tayi ita ma kujerar dake gefen sa ta juya ta yadda zatai facing ɗin shi kafin ta soma magana cikin sanyin murya da fatan ya yarda da batun da zata kawo masa. "Kamar yadda kaga gidan mu nasan ko ban faɗa maka komai ba kasan kawu da Mommy ba iyaye na bane, kawu ƙanin Abbu na ne da nake rayuwa tare da su currently, ba ni da wa bani da ƙani ni kaɗai ce wajen parents ɗina, kwanakin baya kasan kaɗan daga cikin matsalolin da na ringa samu daga wasu cikin companies ɗina hakan yasa na yanke shawarar yin amfani da ƙanƙanin lokacin da nake dashi kafin mu fara project dan kula da harkokin kasuwanci na sedai bazan iya ni kaɗai ba dole se da taimakon wani, Please Yaya kayi min favor ɗin karɓar aiki tare da ni, na yarda da kai nasan ba zaka cuce ni ba, ina buƙatar ka sosai cikin tafiyar kasuwanci na Yaa, alamu sun nuna akwai masu son ganin bayan dukiya ta dan haka suke min zagon ƙasa, nayi iya ƙoƙari na wajen ganin nayi tracing ɗin su sedai na kasa samun dama". Kallon ta kawai yake tun da ta fara magana har ta ƙarasa kafin yayi ajiyar zuciya "And what about shi kawun, ina ce shike kula da komai na companies ɗin?". "Shine yaa, amma bana gane komai a abubuwan da yake jagora, a lissafin shekarar da ya gabata da akayi lissafin shekara me makon ace an sami riba se ma kuɗin Company da ya dulmiya, kuɗi ba ƙanana ba fa, haka ma wannan shekarar da muke ciki yanzu muna wata na huɗu ne amma kullum cikin cases ake na ɓatan kaya, kuɗi, rashin maida hankalin ma'aikata and many more problems, beside this kawu ya Fara manyan ta dole se ana taimaka masa banda haka ma kaga companies ɗin kusan biyar ne dole baze yiwu ace mutum ɗaya ke controlling abubuwan su ba in kuwa akace haka za'a yi dole a ringa samun matsaloli kamar yadda muke fuskanta yanzu". A hankali ya ɗan gyara zaman sa cikin kujerar kafin ya kalle ta sosai "Kin taɓa ganin an ɗauki mutum aiki ba takardu? Ko kuwa a ina za'a nemo takardun da za'a saka cikin file ɗina? Kin dai san dole a buɗe min file kamar kowane ma'aikaci ko, that aside, se wa ya dinga driving ɗin ki?". "Is not a big deal Yaa, se na nemi new drive shikenan, maganar takardu kuma ai Company ɗin na wa ne ina da right ɗin kawo duk wanda na yarda dashi ko da kowa ne yarda ba in as much as na yarda ni shikenan". "Okay will get to think about it". Ya faɗa yana ɗan relaxing cikin chair ɗin, marairaice fuska tayi dan Allah ya na gani so take ta san matsayar da suka cimma wa ko hankalin ta ya kwanta, yanzu kam she has no peace of mind seeing her father's hustle been wasted "Dan Allah fa nace tun farko yaa, Abbu na yasha wahala kafin ya kafa companies ɗin nan yaa bana son wahalar sa ta tafi a banza, ka taimaka pls". "Tun da kin matsa then fine na amince amma ina da sharaɗi". Cikin murnar da ta cika ta ta matsin da sauri kamar zata faɗa masa tana washe baki "Naji daɗi sosai yaa, ban damu da sharaɗin naka ba dan zan yi komai in har zaka yarda, faɗa min meye sharaɗin". Ɗan jan fasali yayi kafin ya tsare ta da idanu "Sharaɗin ba wani me tsauri bane, kawai ban yarda da batun ɗaukar new drive bane, I'll be driving you and also be working, and the last shine you'll be dressing decently and abandon clubbing, that's all". Shiru Kisnah tayi yayinda duk wata murnar ta ta koma ciki, she's just thinking of how can she stopped clubbing at once, abun ya riga ya shiga jinin ta haka in ma barin ne tasan sedai ta rage bit by bit Kuma haka ya kamata yace in ma baya san clubbing ɗin se yace ta rage ba ta daina ba. Ɗauke kan sa Saraki yayi tare da ciro phone ɗin sa ya shiga pressing kamar ma hankalin sa baya kanta yayinda yake kallon ta a kaikaice praying internally Rabb yasa ta yarda da sharaɗin sa dan haka kawai abun ya zo masa ganin yadda ta damu da dukiyar yasan wanna ne kaɗai hanyar da ze bi wajen daƙile clubbing ɗin ta though ta kwana biyu bata je ba sedai yasan saboda exams da kuma tafiyar da suka yi ne yasan tana gab da cigaba da zuwa tunda sun dawo yanzu. Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tare da neman seat ɗin da ta tashi ta koma ta zauna tana me cigaba da tunani, a hankali kamar wadda akayi wa dole ta furta "Na amince". Ɗagowa yayi ya kalle ta ya ɗan yatsuna fuska irin kamar an takura masa ɗin nan "See ba dole bane ba fa, naga duk kin wani yi sanyi, abin nan zaɓin ki ne, you've the choice dan haka in Baki yardan ba i don't give a damn, dama zan yi saboda Abbun ki da kika sako, so in ranki be kwanata ba a bar maganar". Da sauri ta girgiza masa kanta tana ƙoƙarin more damuwar kan fuskar ta dan kar ya fasa, she have no hope in Bashi ba so she won't let him go "Na yarda fa yaa, ba wai ina kokonto bane in adai kawai tunanin yadda zan daina clubbing rana ɗaya bayan am used to it though da wahala amma zan yi hakan insha Allah, I'll do it for Abbu na surely". Sauke ajiyar zuciya yayi a ɓoye tare da yin hamadala yana godewa Allah da ya bashi damar fara saita ta kan hanya cikin sauƙi, he pray one day ta zama yarinya ta gari insha Allah. Gaban computer ta dake office ɗin ta koma ta zauna tare da typing abun da be san me take rubuta wa ba se dai hannun ta da yake jin suna motsa keyboard ɗin cike da ƙware wa, tashi tayi ta ƙara sa gaban printer da ke cikin office ɗin ta ciri wata takardu guda uku ta dawo kujerar da ta tashi wadda take opposite ɗin sa ta zauna tare da tura masa papers biyu "You sign this papers, wannan ta farkon takardar ɗaukar ka aiki ne, ta biyun kuma takardar oath na yadda da dukkan wasu rules and regulations na company ne, ragowar takardun ka kuma zamu je court muyi affidavit ɗin ɓatan documents, ina tunanin shikenan ko". Shiru yayi yana kallon ta kafin a hankali ya motsa bakin sa "I thought ƙarya haramun ne a musulunci ko". Kallon shi tayi sosai wannan karon cikin ƙosawa da halayyan nashi na yau "Haba mana yaa, ai ni dai nayi ƙaryan ba kai ba ko, to zunubin a kaina, haba mutum kamar me wanna ko liman albarka". Ta ƙarashe ƙarshen sentence ɗin can ƙasa ƙasa kamar me ƙunƙuni Murmushi yayi dan sarai yaji abinda ta faɗa so ya kalle ta yana ɗaga gira "Miss kamar kina magana ko?". Wanna karon sosai ta ɓata fuska dan Allah ta gaji da gaske "Ni ba abinda nace fa". "Oh i thought magana kika yi". Girgiza masa kai kawai tayi dan ta fahimci neman magana yake ita kuma bazata biye masa ba balle har ya sami abin fakewa yace ba zai karɓi aikin nan ba dan ina hakan ta faru bata san kuma ha zata yi ba. She really need to have a partner da zasu yi joining hands wajen ya ƙar ma ha'in tan companies ɗin ta su kuma ciyar dashi gaba se dai bayan Sarakin bata ganin akwai wani da zata iya yarda dashi a kan batun. Turo mata takardun da yayi gaban ta tare da ƙarar ajiye pen ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, hannu yasa ta ƙara sa jan takardun gare ta kafin ta bi su da kallo kana ta ajiye ta dube shi "A zahiri gaskiya yaa ban san wane matsayin zan baka a Companies ɗin ba dan kaga ina buƙatar ka kusan a duk Companies ɗin, me kake ganin ya kama ta a yi?". "You decide ai ko, you're the CEO here". Kallo kawai ta bishi dashi, ta sani yana sane yake abin da yake dan ya ƙure ta ta tanka and she won't Dan haka se ta yi murmushi "Hakane and I'll let you know whatever my decision happens to be later". "Patiently waiting".....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah Ouummey 26 (8/20/2022 8:39 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣6️⃣ _________________________📖 Tare suka zauna a office ɗin suna ayyuka sedai ana kiran sallah ya dakata daga aikin da yake yi na bin record ɗin spendings na watan da ya wuce da ta nemi a kawo nata shine fa yake bin lissafin dan ganin ko daidai yake. Da kallo ta bishi kafin ta kautar da kanta ta cigaba da shigar da bayanan da take cikin laptop ganin ya shiga toilet, be daɗe ba ya fito fuskar sa jiƙe da ruwa haka hannun rigar sa a nannaɗe yana ƙoƙarin saukar dashi da alama dai alwala yayi. Ɗagowa tayi ta bishi da kallo jin fitowar sa sedai unfortunately idanuj ta ya sauka kan tsintsiyar hannun sa da yake ƙoƙarin sauke hannun rigar, wow kawai ta iya furtawa cikin ranta ganin yadda wasu kyawawan baƙin gashi suka kwakkwanta suka nannaɗe a jikin fatar hannun nasa, sosai ta kasa janye idanun ta kan hannun dan tana matuƙar son taga mutum na da gashin hannu da ƙafa, da sauri ta bi ƙafafun sa da kallo taga nan ma yana dashi ko kuwa sedai taga wandon sa a sake yake hakan yasa ta kuma maida kanta kan hannun nasa da ya gama sakin ɗaya ya koma ɗayan Jikin shi ne ya bashi ana kallon sa dan haka ya ɗago dan yasan ita ce tun da su biyu ne a office ɗin, kanta kuwa ya sauke duban sa yaga yanda ta kafe hannun sa da kallo har bata ƙi ƙiftawa, sake bin trace ɗin in da take kallon yayi ya tabbatar hannun sa take kallon se ya bar ƙoƙarin sauke sleeve ɗin da yake ya ɓoye hannun a bayan sa hakan yasa ta farga ta maza ta gyara zama tana maida kanta kan system ɗin cike da kunyar da bata taɓa tunanin tana da ita ba. Ficewa yayi ya tsaya bakin office ɗin ya gama gyara hannun rigar kafin ya wuce masallaci, ko da aka idar se da ya tsaya yayi addu'o'in sa kamar yadda ya saba kafin ya dawo har lokacin kuma tana kan aiki cikin system ga tarin tulin takardu gaban ta "Miss lokacin sallah yayi, You leave the work kije kiyi se ki dawo ki cigaba". Cak ta tsaya da aikin da take tana bin shi da kallo cikin tuno ita yaushe rabon ta da yin Sallah da rana irin haka, ita fa sallar ta se dare yayi take haɗe su duka tayi a lokaci ɗaya tayi ta huta dan ita bata san wannan gutsire gutsiren da ake yi, a yi ɗaya yanzu ayi wata anjima shiyasa take haɗe nata. "Zan yi duka in na koma gida, hankali na baze kwanta ba se na gama shigar da informations ɗin nan". Ɗan zato ido yayi yana kallon ta "Excuse me, bangane se kinje gida ba, sallar ce se kinje gida ko aikin?". "Haba sallar dai, aikin nan ai bazan bar office ba yau se na ƙara sa shi bari ma in ƙara maida hankali ka gani". Mamaki ne ya kusan kar shi daga zaunen da yake, sallar take batun se taje gida Sannan zata haɗa, La hula wala quwwat, wannan wace irin rayuwa ce, anya yarinyar nan na da ilimin addini ko yaya a tare da ita kuwa? Baya tunanin hakan ko da dai hakan be kamata ya zama abin mamaki ba in yayi duba da ɗabi'un ta da kuma ayyukan ta zuwa kan shigar ta, in yayi rantsuwa baze yi kaffara ba yarinyar nan bata ma san me ye addinin ba kwata kwata, ita dai kawai tana amsa sunan musulma ne amma kuwa iyayen ta sun cuce ta cuta mara adadi. Haɗe ran sa yayi sosai dan ma kar ta samu wani fuskar yi masa musu ko wata magana "Ki tashi kije ki yi sallah nace kar ki bari ranki ya ɓaci". Sakin aikin tayi ta tsaya kallon shi cikin son yin magana sedai yadda ya haɗe gabas da yamma kamar wanda ke jiran ƙiris ya rufe ta da duka yasa ta miƙe tana ture system ɗin da ƙarfi har tana kusan faɗuwa, toilet ta nufa tana maganganu ƙasa ƙasa wanda bai jin me take faɗa ta shige. Alwala tayi sedai gyaran dake cikin alwalar ba kaɗan bane, fitowa tayi tana goge fuska da towel ƙarami tare da nufar wani ɗaki me kyau me matsakaicin girma da akayi shi dan hutawa in an gaji da aiki ta shige, da ƙyar ta sami ƙaramin veil ta naɗa shi a kanta tayi Sallar. Baki buɗe Saraki ya bita da kallo ganin ko minti biyu cikakku ba tayi da shiga ɗakin ba amma har ta fito kuma wai tana nufin tayi Sallah "Kam bala'i". Ya furta batare da ma yasan yayi ba, lallai this girl is unbelievable, tabɗi, lallai Yana da aiki a gaban shi amma for now Bari ya ƙyale ta kar tursasawar tayi yawa har ta fara jin haushin sa tun da suna tare da sannu ze gyara ta ne da izinin Ubangiji. Ɗauke kan sa yayi daga kanta ya cigaba da aikin sa itama haka har se can wani lokaci kafin ta ture system ɗin tana tura baki "Yunwa nake ji sosai yaa". Ko kallon ta be yi ba ya cigaba da aikin sa, to ban da ma rainin hankali d ta faɗa masa me take nufin yayi mata, ko tana nufin ya fita ya siyo mata abinci ne, ashe ko zata wuni da yunwar. Ganin yadda yayi banza da ita yasa itama ta share shi ta janyo wayar ta, order ta bayar sannan ta jingina da kujerar da take kai tana rufe idanun ta, ba ƙaramin gajiya tayi ba wallahi, ga gajiyar tafiyar jiya bata gama sakin ta ba ga ta aiki da ta kuma rafke ta se take jin kamar ba ita ba dan rabon ta da aikin wahala irin haka tun tana level two kafin daga baya taji gaba ɗaya zaman Companies ɗin ya ishe ta ba ta so ta maida ragamar kula da komai hannun kawu. Knocking ɗin da ake a ƙofar yasa ta miƙe ta ƙara sa tareda buɗe ƙofar dan shi kam ko motsawa be yi ba balle ta sa ran yaje ya buɗe, deliveryn restaurant ɗin da tayi order ne yayi handing mata packs ɗin ya juya dan tayi musu payment online. Gaban sa ta ajiye Masa pack ɗaya ta wuce da ɗaya wajen ta ta ajiye, fridge ta buɗe ta ciro goran ruwa biyu da lemo ta ajiye masa nasa ta ajiye nata gaban ta, ba tare da damuwar komai ba na wai yana zaune ta buɗe pack ɗin ta ta soma cin fried sphagetti with veggies da pepper soup ɗin ta hankali kwance tana yi tana sipping drink ɗin ta har ta ƙoshi kafin ta tattare komai ta ajiye a gefe ta ɗau ruwan ta sha to her satisfaction. Duk abinda take yi yana sane sedai be maida hankali kan ta ba dan yasan dana ta saba cin abinci in public so cin abinci gaban sa baze gagare ta ba. Messenger ɗin ta ta kira ta bashi ragowar da ta rage tace a bawa me so ta cigaba da aikin ta, wasa wasa basu bar office ɗin ba se after six, gudu sosai Saraki yayi ranar dan baya son missing magrib prayer da ake ta kira a masallatai, ko da yayi parking be fita ba se da ya sake jaddada wa Kisnah tayi sallah da ta shiga gida fiye da so uku sannan ya wuce a hanzar ce zuwa masallaci. Ko da ta shiga wanka ta fara yi tare da canja kayan jikin ta da suka takure ta, gajeran wando ta saka da ya wuce cinyoyin ta se ƙaramar riga me kamar shimi tana yi tana tunanin yanda zata dena saka irin wannan kayan ta koma saka wasu, tuno da yace tayi Sallah yasa ta miƙe tana ɓaɓɓata fuska kamar yana gaban ta ya zurma hijabin tayi ƴar fakin ta kamar yadda ta saba. Kan bed ta faɗa dan kam yau bacci zata yi da wuri dan ta huce gajiya ta kuma tashi da wuri gobe, da kayan jikin ta ta kwanta bayan tayi offing light tare da locking ƙofar ta, within minutes tayi bacci abin ta. A can ɓangaren Saraki kuwa be dawo gida ba seda akayi sallar Isha, wanka yayi ya canja kaya zuwa jallabiya mara nauyi ya zauna kan sofar ɗakin ya buɗe pack ɗin abincin sa na tun office dan shikam kasa ci yayi a can, gani yake kallon sa zata dinga yi. Seda ya cika cikin sa ya kwashe ragowar ya saka a fridge sannan ya zauna zuwa lokacin da abincin ze faɗa masa, tunanin ta ne ya faɗo masa a lokacin "Allah yasa tayi Sallar". Ya faɗa a fili dan yasan kaɗan daga ayyukan ta taƙi yi ɗin, wanda tayi ma takura mata yayi to wanna da baya nan kuwa ai se abinda Allah yayi kawai. Murmushi yayi tuno dramar su a office ɗin yau, ya sani she's so simple compared to girls of her age Kuma masu kyau da dukiya irin nata, ya sani da wata ce baya jin de iya tanƙwara ta cikin sauƙi haka bayan shi ɗin ba komai ne gare ta ba se mere driver Wanda yake mata aiki take biyan shi haka kuma yasan Allah ne yaso ta da shiriya shiyasa ya sa ta zama mara girman kai balle wulaƙanci though yakan ga tayi wa wasu sedai yawanci ba talakawa bane masu kuɗi ne wanda ya fahimci kodai sun shiga gonar ta ko kuwa sun wulaƙanta kan su. Kwanciya yayi tare da karanto addu'ar bacci ya shafe jikin sa kana ya lulluɓa yana rufe idanun sa a hankali hopping bacci ya ɗauke shi kar ya kuma shiga wata duniyar tunanin da yake ta hana kan shi faɗawa a kullum. ******* "Wai Awwaf me kake nufi da zaman da kayi a wajen ƴan iskan abokan ka bayan kasan ina jiran ka mu fara namu takun kan waccan ƴar iskar, in Kuma ka fasa ba zaka iya bane ka faɗa min in yi introducing wanda ze iya cikin tafiya ta". Da sauri ya miƙe zaune yana hankaɗe matashiyar dake kwance kan sa, Muryar sa har tana rawa ya fara magana "Haba Mommy wane irin bazan iya ba, kin kuwa san yadda nake burin mallakar yarinyar nan da har kike batun kawo wani, to wallahi bari kiji in kika yi hakan se na tona asirin kowa ya sani, gwara ma ki jira ni dan nan da kwana uku zamu dawo, ina dawowa kuwa ba ɗaga ƙafa zan yi ba dan nasan tun yanzu kun riga kun shirya yadda komai ze kasance". "Are You threaten me?, Lallai har yanzu baka san wace uwar ka ba, ka wuce kwana ukun da kace ka gani in komai be faru ba, sedai kaji ana yi shashasha kawai". Mommy ta katse wayar tana huci dan kalaman Awwaf ɗin na wai ze Tona asirin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, zaman tayi a kan kujera tana jefar da wayar, da sauri ƙawar ta Jamila dake zaune ta cafe tana matsowa kusa da Mommyn "Haba sadiya, meye abin fushi haka a maganar yaron nan, kin fa san su samarin nan in suka ga sun girma se haƙuri, kawai lallaɓa shi za muyi ya dawo dan plan ɗin se ya fi tafiya dashi dan nikam yanzu bana yadda da saka bare cikin aiki na kin san mutanen yanzu ba amana, kalli fa yadda yaron can Nuhu ya ci amanar Hajiya Talatu, yanzu gashi ta sanadin sa tayi biyu babu, shiyasa duk abin naka gwara shi ɗin dai, so ki kwantar da hankalin ki dan Ni nasa zamu yi Nasara, tabbas zamu lalata rayuwar Kisnah ni na faɗa miki". Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da wani zazzafan huci "Duk yadda zan kwatanta miki yadda na tsani yarinyar nan Jamila ba lallai ki game ba, kin san dai yadda muka sha fama da rayuwa cikin talauci har Allah ya kashe iyayen ta muka dawo zama tare da ita cikin daula, ina faɗa miki yarinyar nan bata taɓa bari na na samu kwanciyar hankali ba tun ma tana yarinya har se da baban Maigado ya kai ta England karatu sannan na sami sauƙi muka sami damar rayuwa cikin jin daɗi da walwala muka huce duk wani haushin abubuwan da talauci ya sa mana a da, zan iya ce miki ban taɓa shiga cikin damuwar da na shiga ba shekaru huɗu baya zuwa yau wato dawowar yarinyar kenan, ban san wane irin banzan tunani ne ke damun baban Maigado ba amma saboda tsabar baƙin ciki yaƙi kai Maigado ƙasar waje karatu, ki ga dai yadda ita wannan ta yi kyau ta ƙaro aji ga wayewa shiyasa samari kamar ana mata wahayi dan ma ita bata saurarar su ita kuwa Maigado fa, duk da ta samu waye wa da aji amma ai ba kamar waccan ba haka kafin kiga saurayi ɗaya ya biyo Maigado da sunan aure wallahi se a fi watanni zuwa shekara, sedai an ayi rayuwa a ji daɗi sauƙi na ɗaya ita sam ba hakan a gaban ta amma da ya kike zaton tashin hankalin da zan shiga, yanzu fa ki kalla wai ta koma zuwa Companies ɗin ta zata dinga kula dasu manufar ta a hankali a hankali ta ƙwace komai nata dake hannun baban Maigado, ta yaya hankali na ze kwanta in har ban ga na Kai ta ƙasa ba fisabilillahi". Sauke numfashi Jamila tayi tana gyara zama sosai tare da fuskantar Mommy "Shiyasa nace miki da ki yarda Awwaf ya aure ta, a ganina ta haka ne kawai zamu sami nasara a kanta, kinga maganar Companies ko d ta ƙwace wa take dashi da zai kula mata dasu dole dai mijin t zata ɗora a kan komai so kinga sun dawo hannun mu dai haka kuma ta nan ne kaɗai zaki sami damar musguna mata ki fanshe duk tarin tashin hankali da damuwar da ta jefa ki a ciki ko ba haka ba?". Shiru Mommy tayi dan ita kam Allah ya sani bata jin zata taɓa yarda ta bar ɗan ta auren yarinyar da ta san karuwa ce, ita da take fatan samun tsarkakkun jikoki da sirika me mutunci se ta yadda a kwaso mata kaska, to amma kuma duk batun Jamila na akan hanya, bari dai zata yi tunani taga wanne ne fi mata in ya kama auren se ta haƙura amma fa se ta tabbatar ta hana ga haihuwa dan bata buƙatar zuri'a daga gare ta. Juyowa tayi ta kalli ƙawar ta kuma ƴar uwar ta da ta zuba mata ido dan jin me ta yanke "Kin kawo shawara me kyau dan haka zan yi tunani Jamila, kafin dawowar Awwaf zamu tsayar da batu ɗaya". Jinjina mata kai jamilar tayi ta reda sauke murya tayi mata raɗar da ta sa suka saki dariya tare da tafawa....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 27 (8/20/2022 8:40 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣7️⃣ ________________________📖 yau kam tun shida ta tashi, wanka tayi ta canja kayan ta zuwa fararen sport wears ta fice training, jogging taje tayi ta dawo sannan ta wuce gym ɗin da ta saka a ka haɗa mata a wani ɗaki dake gefen personal garden ɗin ta, bata fito ba se after 8, a gurguje ta koma ɗaki tayi wanka ta zauna ta gyara jikin ta tare da shafa mayukan ta na jiki da na ka. Tsaye tayi gaban wardrobe ɗin tana bin kayan ta da kallo cikin tunani kayan da zata saka, Muryar sa ce ta shiga maimaita kanta cikin ƙwaƙwalwar ta kamar lokacin yake faɗa ".......and the last shine you'll be dressing decently and abandoned clubbing, shikenan...........". Ɓata fuska tayi kamar a lokacin yake gaban ta yana faɗa mata, sake kallon wardrobe ɗin tayi tana maimaita 'decent dress' a ranta sedai a idanun ta duk kayan ta a decent dan ita bata ga illar su ko aibun su ba. Sauke idanun ta tayi kan wani Pakistan me matuƙar kyau, pusha Pink, ciro shi tayi ta warware tana bin shi da kallo, sosai ya burge ta da adon da akayi masa most especially na rashin nauyin sa, nan da nan ta zura shi a jikin ta kafin ta ƙarasa gaban mirror ta sha ga bin kan ta da kallo tun daga sama har ƙasa. A hankali tayi sighing ganin yadda yau mata kyau sedai she's feeling uncomfortable sosai dan bata taɓa saka irin su ba, ita kam kayan ga kullum different designers English wears ne, da su ta buɗe ido kuma da su ta saba shiyasa duk lalacewar su ita bata gani. Sake kallon kayan jikin ta tayi, rigar ta sauka har kan cinyar ta, wandon kuma ya buɗe sosai har yana fitowa ta tsayar gefe da gefen rigar yayin da ta tsuke da ƙafa se mayafin kayan dake hannun ta da bata san ya zata yi dashi ba dan bata jin zata yada shi ko a mafarki kuwa. Turare ta fesa tare da kama gashin ta in chignon style ta ɗora masa sombrero ta fice bayan ta watsa phones ɗin ta cikin clutch kalar platform ɗin ƙafar ta wato blue. Mommy dake zaune kan sofa tana kallon movies ta bi ta da kallo baki sake ganin kayan jikin ta, ba tare da ta kalli Mommy ba ta nufi ƙofar fita se kuma ta dakata tana dafe kan ta haɗu da faɗin "Ouch, Allah yasa ban manta ba yau". Da sauri ta koma falon tana ƙwalawa Rayya kira wanda yasa Rayyan fitowa daga kitchen da sauri tana amsa mata "Please follow me akwai kayan da zaki taya ni sakko dasu, tun jiya ya kamata na fito dasu but na mance". Saman suka koma tana gaba Rayya na bin ta a baya ta buɗe ɗakin suka shiga, kallon ɗakin kawai Rayya take tana sake ware idanu dan zata iya rantse wa tun da take bata taɓa ganin haɗaɗɗen ɗaki irin na Aunty Kisnah ba, ɗakin is just so wow masha Allah, tana can admiring ɗaki har bata ji maganar da Kisnah take mata ba se da ta taɓa ta "Am sorry Aunty, na shagala wajen admiring ɗakin ki har ban san kina magana ba". "Ke kam kullum ai a haka kike, Allah ya shirya ki kawai, ni ɗaukar mun wannan bag ɗin ki kai min ƙasa ki dawo yanzu Please". Da sauri ta ɗauka tayi ƙasa duk da jakar da nauyi amma bata fi karfin ta ba, seda ta sauke bags shida kafin suka ƙare Kisnah ta rufe ɗakin suka sauka gaba ɗaya, zaune suka sami Mommy a inda take sedai yanzu gaba ɗaya hankalin ta baya kan kallon da take yana kan haɗaɗɗun bags ɗin ne, ficewa Kisnah tayi batare da tayi mata wani bayani ba kan kayan se can suka dawo falon tare da wasu ma'aikatan gidan uku. Bags biyar ta nuna wa ma'aikatan suka ɗauka suka fitar dasu waje yayinda ta kalli Mommy "Wannan bag ɗin ta Maigado ce, tsarabar resort ce kuma na manta ban bata ba tun jiya yanzu kuma am in hurry ba zan iya jira har ta fito ba se ki bata, am off". Ta faɗa tana ficewa abin ta zuwa compound ɗin gidan inda aka ajiye ragowar bags ɗin kusa da blue ɗin motar da zasu fita da ita "Yaa wannan Black bag ɗin taka ce tsarabar resort ne". Ɗagowa yayi ya kalle ta ita kuma tana wa ma'aikatan da suka fito da bags ɗin magana akan su saka ragowar cikin Booth. Kallon ta kawai yake yana admiring shigar jikin ta, yadda tayi kyau cikin kayan abu ne da ba za'a iya yiwa kallo ɗaya a kau da kai ba musamman ga irin shi da basu taɓa ganin ta da wau kayan ba apart from English wears da take sawa. Sosai tayi masa kyau a ido kamar ya ɗauke ya ɓoye, se ta koma sak kamar Indians ɗin in ka cire sombrero ɗin da ta saka sedai hakan se ya bada wani style na daban. Juyowa da tayi bayan ta gama magana da ma'aikatan yasa ya ɗauke idanun sa da sauri daga kan ta yana istigfar a ransa dan yasan ya saɓa ƙa'idar kallon da Musulunci ya sharɗan ta, kallon bag ɗin gaban sa tayi taga har lokacin tana nan ko matsara da ita bata yi ba "Mudi ɗauki jakar nan ka kaiwa yaa ɗakin sa, yaa bashi key ɗin Please". Be san me ya faru ba se samun kan shi yayi da miƙa key ɗin wanda ita kanta seda hakan ya bata mamaki dan bata yi tunanin ze bayar ɗin ba ta dai faɗa ne. Ɗaukar jakar Mudi yayi yakai ɗakin kamar yadda tace ɗin sannan ya dawo masu da key ɗin, karɓa tayi ganin Sarakin kamar hankalin sa baya kan su dan se miƙa masa key ɗin ake amma kamar be san ana yi ba. Bubbuga jikin motar tayi hakan yasa shi buɗe idon sa da ya rufe ya zuba su kan ta, da sauri ta kautar da nata idon dan jin yadda gaban ta ya faɗi da kallon nasa "Muje yaa kaga ba Company muka nufa direct ba, kar muyi latti". Buɗe murfin motar kawai yayi ya shiga batare da yace komai ba dan ko ya buɗe bakin be san me zai ce ba dan duk wasu kalaman bakin sa sun gudu tuni. Shiga itama tayi ta zauna a seat ɗin ta ya tada motar suka fita daga gidan, har suka hau titi ba wanda ya kuma magana a cikin su se shine ya kai hannu ya kunna tafsir ɗin Suratul mu'umin daga bakin Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (rabimahul lah). "Yaa ba Company muka nufa direct ba, zamu fara zuwa Al~araby orphanage and home of the disabled". (ƘASAR MU A YAU). Ta faɗa da sauri ganin ya ɗauki hanyar Company "Okay". Yace bayan ya samo Muryar sa da ƙyar kafin ya yi amfani da Google map na motar ya nemo location ɗin orphanage ɗin sannan ya ɗau hanya. Orphanage ɗin da ɗan tazara da inda suke dan a ƙalla 30 mins ne ya kai su, tun daga gare security ɗin wajen ke ta gaida su dan sun san Kisnah farin sani, wajen na daya daga wajejen da take matuƙar son zuwa watannin baya dan tana driving pleasure being with the kids. Office ɗin Dr Imam khaleed suka nufa bayan sun fito daga motar wanda shine ainahin me orphanage ɗin haka kuma dama ta saba se ta fara zuwa sun gaisa kafin ta wuce wajen yaran duk da ba ko yaushe yake zama a orphanage ɗin be se ya samu dama amma yana ƙoƙarin shigowa kullum dan duba buƙatun yaran though akwai manager a gidan dake handling komai in baya nan sedai yau da take sauri ba zata iya tsayawa gaisawa dasu ba dan they have a lot dake jiran su a Company. Cikin fara'a da mutunta juna suka gaisa da Imam khaleed dake ta Jan Saraki da hira wanda sedai yayi ta masa murmushi se ko amsar da bata gagara ba har suka yi sallama suka fito bayan sun sanar dashi security za su shigo da tsarabar yaran wadda Auntyn su tayi musu kamar yadda suke kiran Kisnahn. Fuska cike da farin ciki yake ta yi musu godiya ba wai dan sun kawo abin da babu a gidan ba a'a se dan kulawa da ƙaunar da take nuna wa yaran a ko yaushe, bags ɗin da ke Booth securities ɗin suka fitar kamar yadda aka umarce su kana suka nufi office ɗin shugaban su dashi su kuma suka ja motar suka fita. Duk da bata samu ganin yaran ba dan rashin zaman da bata yi ba haka suna lokacin sun shiga school amma fara'ar dake fuskar ta bata tafi ba ko kaɗan, a kullum in ta shiga gidan ji take kamar tana tare da family ɗin ta ne kuma family ɗin Nanar ta, ba ta fatan lokacin da zata daina ziyartar yaran a rayuwar ta dan wannan shine babban burin Nana har ta yi mata nisa dan haka ita kuma ta ɗauka wa kanta alƙawarin cigaba da kula da farin cikin Nana har ƙarshen rayuwar ta. Har suka ƙara sa masana'antar fuskar ta na ɗauke da wannan fara'ar, da walwala da komai ta gaida da duk ma'aikatan wajen kafin suka haura office ɗin ta, yau ma aiki suka sha kamar ba zasu tafi gida ba har se da aka kira magrib kafin suka bar building ɗin, yau ɗin ma haka ya tsaya a kanta tayi dukkan sallolin akan lokacin su tun daga Azahar har zuwa magrib da suka yi a nan kafin suka wuce gida. Cikin kwanakin haka suke kan ayyuka da kuma tsare tsare da suke ganin ze daƙile duk kan wata ta'asa dake faruwa a Company ɗin ta kuma kawo cigaba, alhamdulillah kuma an yi nasara sosai dan a kwanakin da suka biyo baya ba'a sake jin wasu ƙorafi akan ɓatan kuɗi ko kaya ba, haka ma ma'aikata dolen su suka mai da hankali kan aikin su dan ba wanda yake son a kore shi ko a rage masa matsayi kamar yadda Saraki ya tsara mata tayi threaten ɗin su. Izuwa yanzu komai Masha Allah inda a ƙarshe Kisnah ta bawa Saraki post ɗin personal assistant ɗin ta haka kuma next kin ɗin ta wanda ze iya shiga office ɗin ta ya gabatar da ayyuka ko da bata nan. Sannu a hankali suke ƙara shaƙuwa batare da ɗayan su ya ankara ba dan kusan ko da yaushe suna tare da juna, a office suna tare, a mota ma haka Kai hatta da gida dan da yawan ayyukan da basu ƙarasa a office ba haka zasu tattaro shi su kawo gida su zauna kan sa har se sun ga komai yayi dadai. Zuwa yanzu kam alhamdulillah dan little by little kisnha ta bar yin shigar da take na rashin tsari, duk da ba wai tana saka atamfa ko shadda ko lace bane sedai tana saka decent dresses, so da yawa takan saka jeans da t-shirt Amma se ta ɗora mata kimono dake kai mata har ƙasa kuma ta ɗaura yafa scarf, hatta da straight skirts in ta saka se ta nemi jackets, after dresses ko overcoats ta ɗora musu hakan yasa ya fitar da kusan rabin wardrobe ɗin ta ta bawa Rayya wasu ragowar kuwa duka ta bawa Maigado dan native wears ne ita kuma ta sake sabon zubi da ta zauna tayi online shopping daga England sune take amfani dasu yanzu. Duk da Maigado taji daɗin kayan amma hakan bashi ya hana ta yin baƙin ciki da takaici ba dan ita a gare ta ƙasƙanta ta Kisnah tayi da har zata bata kaya, alhalin kayan ko ɗan kwali bata taɓa ɗaura wa na daga cikin su, ranar haka suka zauna suka kashe lokaci wajen shirya plan ɗin tarwatsa Kisnah wanda dawowar Awwaf kaɗai suke jira komai ya fara tafiya kamar yadda suka tsara dan tuni Mommy ta amince da shawarar Aminiya kuma ƴar uwar ta da Jamila na auren Awwaf ɗin da Kisnah (ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta😏). ***** Sati na uku kenan da fara aikin su tare kamar yadda a office ɗaya suke zama sedai an fitar masa da nasa table ɗin a side ɗaya na cikin offices ɗin ta dake kowanne Company, a yadda suka tsara duk tana zama a kowane Company ne tayi kwana biyu, ma'ana tana komawa kowane Company ne duk bayan kwana takwas, in taje K&S drinks yau da gobe to jibi da gata kuma se taje K&S construction, next is K&S couture......haka haka har ta zagaya duka sannan ta kuma dawo wa farko wanda suka fara da K&S constructions. Yau ma zaune suke a K&S drinks, kowa na fama da keyboard na system ɗin shi, a cikin drinks ɗin da aka fitar last week ne aka samu wasu gurɓatattu wanda kusan an rasa rayuka kimanin goma sha uku sanadin shan lemon hakan yasa mutane yin bore har suna batun maka kamfanin a kotu, wannan yasa hankalin su ya tashi da son ganin sun daƙile wannnan ɓarakar da ta ɓullo ta hanyar gano wace iriyar ƙwaya ce ko poison aka saka haka kuma taya ya ƙwayar ta shiga cikin wasu daga drinks ɗin yayin da wasu kuma babu tunda ko da case ɗin ya ɓullo aka dawo musu da goods ɗin daga wholesellers ɗin su an yi tasting majority dan har su sun sha kuma babu komai a ciki, sosai abin ya ɗaure wa jami'an binciken dake kan al'amarin kai wanda hakan ne yasa aka dakatar da batun shiga kotu har se an kammala bincike. A hankali ya miƙa hannun sa ya ɗau hankerchief ɗin sa dake kan table ya goge gumin kan goshin sa kafin ya tura kujerar sa baya cikin sauke numfashi. "A cikin ma'aikatan gurin nan aka haɗa baki akayi wannan abun, waye Emeka maji?". Tsayar da abun da take yi cikin computer ɗin tare da maida hankalin ta kan sa "Yana ɗaya daga cikin in charge masu kula da quantityn ingredients ɗin da ake zubawa yayin haɗa drinks ɗin". Ta faɗa tana ƙure shi da idanu cikin son ƙarin bayani "Come closer". Da saurin ta kuwa ta bar seat ɗin ta zuwa table ɗin sa tare da jawo kujera ta zauna next to him, juyo mata screen ɗin system ɗin sa yayi yana mata playing vedio ɗin da yai pausing, shiru tayi ta zuba wa screen ɗin ido tana kallo cikin tsananin mamaki da rashin yarda da abinda take ganin har short video ɗin ya ƙare...........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 28 (8/20/2022 8:41 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Ouummey 26 (8/20/2022 8:39 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣6️⃣ _________________________📖 Tare suka zauna a office ɗin suna ayyuka sedai ana kiran sallah ya dakata daga aikin da yake yi na bin record ɗin spendings na watan da ya wuce da ta nemi a kawo nata shine fa yake bin lissafin dan ganin ko daidai yake. Da kallo ta bishi kafin ta kautar da kanta ta cigaba da shigar da bayanan da take cikin laptop ganin ya shiga toilet, be daɗe ba ya fito fuskar sa jiƙe da ruwa haka hannun rigar sa a nannaɗe yana ƙoƙarin saukar dashi da alama dai alwala yayi. Ɗagowa tayi ta bishi da kallo jin fitowar sa sedai unfortunately idanuj ta ya sauka kan tsintsiyar hannun sa da yake ƙoƙarin sauke hannun rigar, wow kawai ta iya furtawa cikin ranta ganin yadda wasu kyawawan baƙin gashi suka kwakkwanta suka nannaɗe a jikin fatar hannun nasa, sosai ta kasa janye idanun ta kan hannun dan tana matuƙar son taga mutum na da gashin hannu da ƙafa, da sauri ta bi ƙafafun sa da kallo taga nan ma yana dashi ko kuwa sedai taga wandon sa a sake yake hakan yasa ta kuma maida kanta kan hannun nasa da ya gama sakin ɗaya ya koma ɗayan Jikin shi ne ya bashi ana kallon sa dan haka ya ɗago dan yasan ita ce tun da su biyu ne a office ɗin, kanta kuwa ya sauke duban sa yaga yanda ta kafe hannun sa da kallo har bata ƙi ƙiftawa, sake bin trace ɗin in da take kallon yayi ya tabbatar hannun sa take kallon se ya bar ƙoƙarin sauke sleeve ɗin da yake ya ɓoye hannun a bayan sa hakan yasa ta farga ta maza ta gyara zama tana maida kanta kan system ɗin cike da kunyar da bata taɓa tunanin tana da ita ba. Ficewa yayi ya tsaya bakin office ɗin ya gama gyara hannun rigar kafin ya wuce masallaci, ko da aka idar se da ya tsaya yayi addu'o'in sa kamar yadda ya saba kafin ya dawo har lokacin kuma tana kan aiki cikin system ga tarin tulin takardu gaban ta "Miss lokacin sallah yayi, You leave the work kije kiyi se ki dawo ki cigaba". Cak ta tsaya da aikin da take tana bin shi da kallo cikin tuno ita yaushe rabon ta da yin Sallah da rana irin haka, ita fa sallar ta se dare yayi take haɗe su duka tayi a lokaci ɗaya tayi ta huta dan ita bata san wannan gutsire gutsiren da ake yi, a yi ɗaya yanzu ayi wata anjima shiyasa take haɗe nata. "Zan yi duka in na koma gida, hankali na baze kwanta ba se na gama shigar da informations ɗin nan". Ɗan zato ido yayi yana kallon ta "Excuse me, bangane se kinje gida ba, sallar ce se kinje gida ko aikin?". "Haba sallar dai, aikin nan ai bazan bar office ba yau se na ƙara sa shi bari ma in ƙara maida hankali ka gani". Mamaki ne ya kusan kar shi daga zaunen da yake, sallar take batun se taje gida Sannan zata haɗa, La hula wala quwwat, wannan wace irin rayuwa ce, anya yarinyar nan na da ilimin addini ko yaya a tare da ita kuwa? Baya tunanin hakan ko da dai hakan be kamata ya zama abin mamaki ba in yayi duba da ɗabi'un ta da kuma ayyukan ta zuwa kan shigar ta, in yayi rantsuwa baze yi kaffara ba yarinyar nan bata ma san me ye addinin ba kwata kwata, ita dai kawai tana amsa sunan musulma ne amma kuwa iyayen ta sun cuce ta cuta mara adadi. Haɗe ran sa yayi sosai dan ma kar ta samu wani fuskar yi masa musu ko wata magana "Ki tashi kije ki yi sallah nace kar ki bari ranki ya ɓaci". Sakin aikin tayi ta tsaya kallon shi cikin son yin magana sedai yadda ya haɗe gabas da yamma kamar wanda ke jiran ƙiris ya rufe ta da duka yasa ta miƙe tana ture system ɗin da ƙarfi har tana kusan faɗuwa, toilet ta nufa tana maganganu ƙasa ƙasa wanda bai jin me take faɗa ta shige. Alwala tayi sedai gyaran dake cikin alwalar ba kaɗan bane, fitowa tayi tana goge fuska da towel ƙarami tare da nufar wani ɗaki me kyau me matsakaicin girma da akayi shi dan hutawa in an gaji da aiki ta shige, da ƙyar ta sami ƙaramin veil ta naɗa shi a kanta tayi Sallar. Baki buɗe Saraki ya bita da kallo ganin ko minti biyu cikakku ba tayi da shiga ɗakin ba amma har ta fito kuma wai tana nufin tayi Sallah "Kam bala'i". Ya furta batare da ma yasan yayi ba, lallai this girl is unbelievable, tabɗi, lallai Yana da aiki a gaban shi amma for now Bari ya ƙyale ta kar tursasawar tayi yawa har ta fara jin haushin sa tun da suna tare da sannu ze gyara ta ne da izinin Ubangiji. Ɗauke kan sa yayi daga kanta ya cigaba da aikin sa itama haka har se can wani lokaci kafin ta ture system ɗin tana tura baki "Yunwa nake ji sosai yaa". Ko kallon ta be yi ba ya cigaba da aikin sa, to ban da ma rainin hankali d ta faɗa masa me take nufin yayi mata, ko tana nufin ya fita ya siyo mata abinci ne, ashe ko zata wuni da yunwar. Ganin yadda yayi banza da ita yasa itama ta share shi ta janyo wayar ta, order ta bayar sannan ta jingina da kujerar da take kai tana rufe idanun ta, ba ƙaramin gajiya tayi ba wallahi, ga gajiyar tafiyar jiya bata gama sakin ta ba ga ta aiki da ta kuma rafke ta se take jin kamar ba ita ba dan rabon ta da aikin wahala irin haka tun tana level two kafin daga baya taji gaba ɗaya zaman Companies ɗin ya ishe ta ba ta so ta maida ragamar kula da komai hannun kawu. Knocking ɗin da ake a ƙofar yasa ta miƙe ta ƙara sa tareda buɗe ƙofar dan shi kam ko motsawa be yi ba balle ta sa ran yaje ya buɗe, deliveryn restaurant ɗin da tayi order ne yayi handing mata packs ɗin ya juya dan tayi musu payment online. Gaban sa ta ajiye Masa pack ɗaya ta wuce da ɗaya wajen ta ta ajiye, fridge ta buɗe ta ciro goran ruwa biyu da lemo ta ajiye masa nasa ta ajiye nata gaban ta, ba tare da damuwar komai ba na wai yana zaune ta buɗe pack ɗin ta ta soma cin fried sphagetti with veggies da pepper soup ɗin ta hankali kwance tana yi tana sipping drink ɗin ta har ta ƙoshi kafin ta tattare komai ta ajiye a gefe ta ɗau ruwan ta sha to her satisfaction. Duk abinda take yi yana sane sedai be maida hankali kan ta ba dan yasan dana ta saba cin abinci in public so cin abinci gaban sa baze gagare ta ba. Messenger ɗin ta ta kira ta bashi ragowar da ta rage tace a bawa me so ta cigaba da aikin ta, wasa wasa basu bar office ɗin ba se after six, gudu sosai Saraki yayi ranar dan baya son missing magrib prayer da ake ta kira a masallatai, ko da yayi parking be fita ba se da ya sake jaddada wa Kisnah tayi sallah da ta shiga gida fiye da so uku sannan ya wuce a hanzar ce zuwa masallaci. Ko da ta shiga wanka ta fara yi tare da canja kayan jikin ta da suka takure ta, gajeran wando ta saka da ya wuce cinyoyin ta se ƙaramar riga me kamar shimi tana yi tana tunanin yanda zata dena saka irin wannan kayan ta koma saka wasu, tuno da yace tayi Sallah yasa ta miƙe tana ɓaɓɓata fuska kamar yana gaban ta ya zurma hijabin tayi ƴar fakin ta kamar yadda ta saba. Kan bed ta faɗa dan kam yau bacci zata yi da wuri dan ta huce gajiya ta kuma tashi da wuri gobe, da kayan jikin ta ta kwanta bayan tayi offing light tare da locking ƙofar ta, within minutes tayi bacci abin ta. A can ɓangaren Saraki kuwa be dawo gida ba seda akayi sallar Isha, wanka yayi ya canja kaya zuwa jallabiya mara nauyi ya zauna kan sofar ɗakin ya buɗe pack ɗin abincin sa na tun office dan shikam kasa ci yayi a can, gani yake kallon sa zata dinga yi. Seda ya cika cikin sa ya kwashe ragowar ya saka a fridge sannan ya zauna zuwa lokacin da abincin ze faɗa masa, tunanin ta ne ya faɗo masa a lokacin "Allah yasa tayi Sallar". Ya faɗa a fili dan yasan kaɗan daga ayyukan ta taƙi yi ɗin, wanda tayi ma takura mata yayi to wanna da baya nan kuwa ai se abinda Allah yayi kawai. Murmushi yayi tuno dramar su a office ɗin yau, ya sani she's so simple compared to girls of her age Kuma masu kyau da dukiya irin nata, ya sani da wata ce baya jin de iya tanƙwara ta cikin sauƙi haka bayan shi ɗin ba komai ne gare ta ba se mere driver Wanda yake mata aiki take biyan shi haka kuma yasan Allah ne yaso ta da shiriya shiyasa ya sa ta zama mara girman kai balle wulaƙanci though yakan ga tayi wa wasu sedai yawanci ba talakawa bane masu kuɗi ne wanda ya fahimci kodai sun shiga gonar ta ko kuwa sun wulaƙanta kan su. Kwanciya yayi tare da karanto addu'ar bacci ya shafe jikin sa kana ya lulluɓa yana rufe idanun sa a hankali hopping bacci ya ɗauke shi kar ya kuma shiga wata duniyar tunanin da yake ta hana kan shi faɗawa a kullum. ******* "Wai Awwaf me kake nufi da zaman da kayi a wajen ƴan iskan abokan ka bayan kasan ina jiran ka mu fara namu takun kan waccan ƴar iskar, in Kuma ka fasa ba zaka iya bane ka faɗa min in yi introducing wanda ze iya cikin tafiya ta". Da sauri ya miƙe zaune yana hankaɗe matashiyar dake kwance kan sa, Muryar sa har tana rawa ya fara magana "Haba Mommy wane irin bazan iya ba, kin kuwa san yadda nake burin mallakar yarinyar nan da har kike batun kawo wani, to wallahi bari kiji in kika yi hakan se na tona asirin kowa ya sani, gwara ma ki jira ni dan nan da kwana uku zamu dawo, ina dawowa kuwa ba ɗaga ƙafa zan yi ba dan nasan tun yanzu kun riga kun shirya yadda komai ze kasance". "Are You threaten me?, Lallai har yanzu baka san wace uwar ka ba, ka wuce kwana ukun da kace ka gani in komai be faru ba, sedai kaji ana yi shashasha kawai". Mommy ta katse wayar tana huci dan kalaman Awwaf ɗin na wai ze Tona asirin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, zaman tayi a kan kujera tana jefar da wayar, da sauri ƙawar ta Jamila dake zaune ta cafe tana matsowa kusa da Mommyn "Haba sadiya, meye abin fushi haka a maganar yaron nan, kin fa san su samarin nan in suka ga sun girma se haƙuri, kawai lallaɓa shi za muyi ya dawo dan plan ɗin se ya fi tafiya dashi dan nikam yanzu bana yadda da saka bare cikin aiki na kin san mutanen yanzu ba amana, kalli fa yadda yaron can Nuhu ya ci amanar Hajiya Talatu, yanzu gashi ta sanadin sa tayi biyu babu, shiyasa duk abin naka gwara shi ɗin dai, so ki kwantar da hankalin ki dan Ni nasa zamu yi Nasara, tabbas zamu lalata rayuwar Kisnah ni na faɗa miki". Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da wani zazzafan huci "Duk yadda zan kwatanta miki yadda na tsani yarinyar nan Jamila ba lallai ki game ba, kin san dai yadda muka sha fama da rayuwa cikin talauci har Allah ya kashe iyayen ta muka dawo zama tare da ita cikin daula, ina faɗa miki yarinyar nan bata taɓa bari na na samu kwanciyar hankali ba tun ma tana yarinya har se da baban Maigado ya kai ta England karatu sannan na sami sauƙi muka sami damar rayuwa cikin jin daɗi da walwala muka huce duk wani haushin abubuwan da talauci ya sa mana a da, zan iya ce miki ban taɓa shiga cikin damuwar da na shiga ba shekaru huɗu baya zuwa yau wato dawowar yarinyar kenan, ban san wane irin banzan tunani ne ke damun baban Maigado ba amma saboda tsabar baƙin ciki yaƙi kai Maigado ƙasar waje karatu, ki ga dai yadda ita wannan ta yi kyau ta ƙaro aji ga wayewa shiyasa samari kamar ana mata wahayi dan ma ita bata saurarar su ita kuwa Maigado fa, duk da ta samu waye wa da aji amma ai ba kamar waccan ba haka kafin kiga saurayi ɗaya ya biyo Maigado da sunan aure wallahi se a fi watanni zuwa shekara, sedai an ayi rayuwa a ji daɗi sauƙi na ɗaya ita sam ba hakan a gaban ta amma da ya kike zaton tashin hankalin da zan shiga, yanzu fa ki kalla wai ta koma zuwa Companies ɗin ta zata dinga kula dasu manufar ta a hankali a hankali ta ƙwace komai nata dake hannun baban Maigado, ta yaya hankali na ze kwanta in har ban ga na Kai ta ƙasa ba fisabilillahi". Sauke numfashi Jamila tayi tana gyara zama sosai tare da fuskantar Mommy "Shiyasa nace miki da ki yarda Awwaf ya aure ta, a ganina ta haka ne kawai zamu sami nasara a kanta, kinga maganar Companies ko d ta ƙwace wa take dashi da zai kula mata dasu dole dai mijin t zata ɗora a kan komai so kinga sun dawo hannun mu dai haka kuma ta nan ne kaɗai zaki sami damar musguna mata ki fanshe duk tarin tashin hankali da damuwar da ta jefa ki a ciki ko ba haka ba?". Shiru Mommy tayi dan ita kam Allah ya sani bata jin zata taɓa yarda ta bar ɗan ta auren yarinyar da ta san karuwa ce, ita da take fatan samun tsarkakkun jikoki da sirika me mutunci se ta yadda a kwaso mata kaska, to amma kuma duk batun Jamila na akan hanya, bari dai zata yi tunani taga wanne ne fi mata in ya kama auren se ta haƙura amma fa se ta tabbatar ta hana ga haihuwa dan bata buƙatar zuri'a daga gare ta. Juyowa tayi ta kalli ƙawar ta kuma ƴar uwar ta da ta zuba mata ido dan jin me ta yanke "Kin kawo shawara me kyau dan haka zan yi tunani Jamila, kafin dawowar Awwaf zamu tsayar da batu ɗaya". Jinjina mata kai jamilar tayi ta reda sauke murya tayi mata raɗar da ta sa suka saki dariya tare da tafawa....................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. Ouummey 29 (8/21/2022 10:30 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 2️⃣9️⃣ _______________________📖 Yau ma Ka&S drinks suka nufa maimakon K&S Furnitures kamar yadda su kawu suka yi hasashe dan bata jin zata iya tafiya ta bar gurin nan a yadda yake sedai a maimakon su zauna duka su biyu se ya ajiye ta shi ya tafi construction company ɗin dan cikin zuwan da suka yiyyi tare ya fahimci yadda wajen yake tafiya se a bin da ba'a rasa ba. Cikin farin ciki kawu ya ƙaraso cike da jin daɗin ze gabatar da aikin sa hankali kwance sedai lokaci ɗaya fara'ar nan ta ɓace ɓat lokacin da yayi ido biyu da Saraki zaune kan kujerar sa cikin office ɗin Kisnah. Be sami zarafin cewa komai ba yaga Sarakin ya miƙe dan lokacin suke da meeting da wani Company da zasu basu kwangila, cikin ɓacin rai kawu ya juya gida dan ji yayi ma sam baze iya zama cikin Company ɗin ba. Cikin kwanciyar hankali aka gama meeting ɗin komai ya tafi daidai, sedai a maimakon Saraki ya bari a saka rabin kuɗin aikin da aka yi da su zasu biya cikin account ɗin banki se ya bayar dana Kisnah dan haka kawai yake jin something is fishy a nan ɗin ma dan haka ya ɗau wannan matakin wajen daƙile koma meke shirin afkuwa. Tana zaune tana aikin ta can a office ta ji ƙarar shigowar alert phone ɗin ta, ajiye aikin tayi tare da jawo wayar, mamaki ne ya cika ta ganin uwar kuɗin da ya shigo cikin account ɗin ta ko da ta duba sunan se ta ga sunan Company ɗin da suke batun karɓar kwangila wajen su ne, kenan hakan na nufin an daidaita shine suka yi half payment ko me, Yes haka ne ma, to amma me ze sa a saka kuɗin cikin account ɗin ta bayan akwai na Company?. Shiru tayi tana jujjuya lamarin cikin ranta se dai ganin ta kasa ganewa se ta ajiye shi a gefe dan ta san dole Saraki ze mata bayani. Tuno da sunan sa ya sa ta kalli wajen zaman sa cike da kewar sa tana tuno yadda suke wuni tare tayi ta masa surutu yaƙi kula ta in ma ta dame shi ya haɗe rai shikenan ya kashe bakin maganar se ta shiga taitayin ta. Tuni yadda ta rungume shi da yadda yayi reacting se kawai ta tuntsire da dariya tai tayin abin ta ita kaɗai kamar wadda ciwon hauka ya kama kafin tayi shiru ta cigaba da aikin ta tana sakin smiles kamar zararriya. Hankali kwance ta cigaba da ayyukan ta tana me jin farin ciki cikin ranta. A can ɓangaren Saraki shima aikin can ya cigaba da dubawa yana tabbatar da kasancewar komai a muhallin sa. Kawu kuwa da baƙin ciki ya cika wa rai yana komawa gida number Alh Haladu ya kira telling him all that happened, shima sosai ran sa ya ɓaci ganin yadda yarinya ƙarama take neman wahalar dasu tun bare ma shigowar wannan ɗan iskan yaron cikin rayuwar ta kamar an ƙara mata ƙwarin gwiwa ne. Nazari ya zauna yayi dan neman hanyar ɓullo musu tsawon lokaci kafin ya saki dariyar farin cikin samun wani solution ɗin, da sauri ya ɗau wayar sa ya shiga kiran Kawu da ringing ɗaya tayi ya ɗauka kamar dama jira yake. "Kana ji ko Sama'ila, yanzu abinda za'a yi maza ka tafi Company ɗin furnitures, Zan turo mutane na da fake currency zasu siya set ɗin full three bedroom flat, amfanin da zuwan ka ze yi shine tabbatar da an karɓi cash ba transfer ba, na sani duk da haka ba durƙusar da gurin ze yi ba amma dai ai asara asara ce kuma ina da wanda zan tura wa kayan ya saye su daraja dan kayan gurin duk latest ne kuma ba ƴan ƙasar nan ba". Shima Kawu washe baki yai duk da ba haka yaso ba, yaso ace wancan maƙudan kuɗaɗen kwangilar ne suka shigo account ɗin su sedai ba komai sa rage zafi. Haka kuwa akayi, mutanen Alh Haladu suka yi shiga me kyau suka ɗau manyan motoci da kana gani kasan sun cika sun timbatsa, tarba me kyau manager ɗin wajen yayi musu aka gaggaisa kafin suka kawo batun siyan kayan da ya kawo su wanda a daidai lokacin Kawu ya ƙaraso. Ciniki aka yi suka zaɓi kaya masu matuƙar tsada da kyau kafin akayi lissafi kuɗi ya tashi kusan miliyan 50 dan fa set ɗin 2 parlor and 3 bedrooms suka zaɓa, ana gama lissafi babban Alh cikin su yace yana zuwa ya koma mota ya ware adadin kafin ya ɗauko jakar da kuɗin ke ciki zuwa gasu Kawu, manager ya so yin magana sedai ganin yadda Kawu ya karɓe kuɗin da sauri yasa dole ya rufe bakin sa, buɗe jakar Kawu yayi gaban kowa ya fito da kuɗin aka ƙiƙƙirga aka tabbatar sun kai kafin aka shiga loda musu kayan cikin babbar motar da suka zo da ita. Ana gamawa suka yi sallama da kowa suka ɗau hanya Kawu na ta washe baki haka shima manager yaji daɗin cinikin dan sun tabbatar musu da suna dawowa nan da two days akwai mansion ɗin su da zasu sawa furnitures Kuma a wajen su za'a siya komai. Manager Kawu ya bawa kuɗin kan yaje yakai bank in ya tashi aiki shi ze wuce K&S couture, da haka yabar manager ya fita daga building ɗin yana dariya a ranshi ga kuma farin cikin kuɗin da zasu samu har miliyan 50, ko ba komai yasan ke tashi da twenty five millions. ********** Ƙarfe biyar ya tashi daga aiki ya wuce wajen Kisnah tare da kiran ta ya shaida mata yana waje, ba ɓata lokaci ta fito suka wuce, sun kusa ƙara sawa take faɗa masa "Yaya yau ina da zuwa cinema by 8pm, za'a haska Film ɗin jarumi sharukhan Chennai express". Ɗan kallon ta yayi ta gefen ido yaga yadda take ta washe baki tsantsan farin ciki rubuce ka fuskar ta, be san ta wace hanya ze sami damar hana ta zuwa cinema ba ayanzu Amma he pray Allah ya kawo masa wata damar da ze yi hakan ko da nan gaba ne. Gyaɗa mata kai yayi tunda bashi da wani option se hakan, gaban wani suya spot tace ya tsaya, atm ɗin ta ta miƙa masa tana lissafa masa abinda take so ya siyo ɗin, fita yayi bayan ya gama sauraren ta batare da ya karɓi atm ɗin ba, komai da ta lissafa se da ya siyo ya kawo mata sannan ya shiga motar ya cigaba da tuƙin sa, kaɗan kaɗan take kallon sa tana sakin murmushi, kusan so huɗu kenan indai zata siya abu se ya siya mata batare da ya bi takan kuɗin ta ba kuma tana jin daɗin hakan. Suna ƙara sawa gida ta ɗauki ledar ta tare da yi masa godiya ta fice daga motar cike da farin ciki, bata ƙarasa flat ɗin ba suka haɗu da Awwaf, bata ko kalle shi ba kamar yadda ta ke masa tun da taga ya fara neman raina ta wai har ze kalle ta yace yana son ta, gaba tayi ta bar shi a wajen sedai kafin ta ƙara taku uku taji an janyo ta an rungume, fisge jikin ta tayi daga gare shi tare da ɗagowa cikin zafin rai da tsananin baƙin ciki da takaicin abinda yayi mata ta haske fuskar sada kyakkyawan marin da se da ya ɗauke masa jin sa na wasu sakanni. Ƙara masa take ƙoƙarin yi se kuma ta fasa ta shiga nuna shi da yatsa ta fara masa masifa da cin mutuncin da duk wanda ke compound ɗin ke iya jiyo ta dan dama suna tsaye a compound ɗin ne ta hanyar shiga flat ɗin su "Wane irin ɗan akuya ne kai da har rashin kunyar ka takai ka kai ƙazamin hannun ka jikina da wata manufa, nace waye kai da har kake da wannan guts ɗin ko an gaya maka ni ɗin sa'ar kace ko kuwa sake war da ka samu ce tasa har kake tunanin ni ɗin daidai nake da kai bari ka kawo min raini, to bari kaji wallahi wanda ya isa da kai ma be isa ba balle kuma wani banza kamar ka, an warning You for the first and last time, na rantse da Allah duk sanda ka kuma gwada irin haka se ranka ya ɓaci fiye da yadda kake zato, wannan ɗin ma Sa'a kaci na dubi matsayin mahaifiyar ka wajen ƙanin uba na if not wallahi matakin da zan ɗauka kan ka ko da kuɗi aka baka akace ka kuma trying this nonsense ba zaka kuma ba, pathetic peace of trash kawai, mtseww". Ta ja tsaki kafin tayi gaba cikin ɓacin rai, Mommy dake tsaye tana kallon komai ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba sedai sanin ba abinda zata iya yi ko cewa yasa bata ƙarasa wajen ba ta juya ta shige falon ganin Kisnah tayo hanyar. Ko kallon Mommyn bata yi ba ta nufi steps zata wuce ɗakin ta se kuma ta dawo ta tsaya gaban Mommyn tana jijjiga jiki tsabar bala'in da yake cinya dan ji take kamar ta koma in da ta bar banzan ta rufe shi da duka "Haleema ki jawa ɗan ki kunne akaina, be san wace ce ni bane da alama shiyasa har yake ƙoƙarin kawo haukar iskancin sa kaina,to salin alin tun kafin in bayyanar masa a ainihin Kisnah ta ya fita a hanya ta in Kuma ba haka ba wallahi zan bi takan sa, har shi waye da ya isa ya kai ƙazamin hannun sa jikina, waye shi waye ya tsaya masa eye, ke kin San ni kin San abinda zan iya dan haka zaki iya gargaɗin sa, dan in ya kuma ban san iya abinda zan aikatawa banza ba". Tana ƙare isar da saƙon ta ta wuce sama da ɗan gudu gudu har ta haye, ƙofar ma seda ta san tana fushi dan yadda tayi banging ɗin tada akwai wani a kusa ba ƙaramin ciwo zata ji masa ba. Kayan jikin ta ta fara ciccire wa tana watsar wa har se da ta cire komai na jikin ta kafin ta ƙarasa toilet, ruwan sanyi ta sakar wa jikin ta ta tsaya a ciki har se da ta ji ranta yayi mata sanyi kafin ta yi wanka ta fita, tsane jikin ta tayi da towel sannan ta zura guntuwar red gown iya gwiwa ta warware chignon ɗin da tayi wa kanta ta maida shi French plait ta saki jelar a bayan ta. Ledar ta da ta shigo da ita ta fito parlo ta ɗauka tare da nufar mini kitchen ɗin ta, plate ta ɗauka ta wanke duk da fess yake ta goge da duster sannan ta juye abin cikin ledar a kai, lumshe ido tayi cikin zaƙuwar fara cin gasasshiyar kazar wadda ta sha kayan haɗi kamar me, take cikin ta ya fara kukan yunwar da ta yo guziri daga office dan yau bata yi launch ba aiki ya ɗauke mata hankali. ******** Juyawa yayi da ledar hannun sa ya wuce ɗakin sa bayan yayi locking motar, yaji daɗin yadda tayi wa Awwaf sosai dan hakan na nuna ta fara sanin ciwon kan ta kenan, a ganin sa da da kanta take rungume maza yanzu kuma tana fighting masu rungumar ta haka ma Nasara ce. Poor Saraki be san ita Awwaf ɗin ne ta raina wa hankali ba ba wai dena rungumar maza tayi ba duk da an daɗe hakan bata faru ba tun da kullum tana hanyar office to a ina zata gan wanda ta sani balle har ta runguma? Wanka yayi ya canja kaya kafin ya zauna kan ledar sa shima ya shiga aika ta ciki, sosai gashin ya yi masa daɗi abaki dan haka yake ta lumshe idanu, abin dariya har ya cinye ma be san ya cinye ba seda yaji ledar ƙwalam kafin yayi murmushi ya tafi toilet ya wanke hannun sa. Kitabul kaba'ir ɗin da ya fanso recently ya ɗauko ya shiga dubawa, lokacin da aya baro gida yayi nisa sosai sedai kwana biyu da yayi be duba ba ya ɗan samu tangarɗa so ya koma baya ya shiga karanta wa cikin ransa. Seda akayi kiran sallar magrib ya ajiye ya yi alwala ya fita zuwa Masallaci akayi sallah tare da shi har Isha sannan ya fito, da jallabiyyar jikin sa ya ɗau key ɗin motar da suka dawo da ita ya fita dan kai ta cinema Kamar yadda tace. Cikin shigar jeans da half tigh shirt ta fito sedai ta saka brown overcoat a kai ta ɗora sou'wester a kanta ƙafar ta sanye da brown wedge shoe da ya mata masifar kyau. Buɗe motar tayi ta shiga dan shi dama tuni ya shige ciki ita kawai yake jira, tana shiga ya tashi motar suka fita daga gidan bakin ta ɗauke da addu'a. Suna ƙarasawa ya yi parking a lot ɗin wajen tare da kashe motar yana jiran ta fita. Karkatowa tayi tana kallon shi cikin ɗan marairaice fuska "Yaya pls mu shiga tare da kai kaima ka kalla, kaga fa kai kaɗai zaka zauna a nan ɗin har kusan 3 hours". Da mamaki sosai ya kalle ta "Kin taɓa gani na ina kallon Film bare ma irin wanda kuke kalla, I don't have that time to waste, ke dai kije ki kalla abin ki, kuma ai ba yau na fara zama ni kaɗai na jira ki ba ko?". "Yaa ba fa romantic film bane it's a sport movie, Dan Allah kaji". "Ki dena haɗa ni da Allah fa dan ba inda zani, am here zan yi night azkhar ɗina, you go and watch se ki bani labari later". Duk magiyar da tayi masa ƙi yayi yakan yasa tayi fushi ta fice tana banging Masa ƙofar, murmushi yayi dan yasan haushi taji, shikam be taɓa shiga cinema ba wai kallo kuma baze fara yanzu ba, gwara a gida yana kallo sosai amma cinema ba da shi ba. Kwantar da kujerar yayi ya kishingiɗa sosai a kanta ya shiga tasbih ɗin sa a hankali patiently waiting for her...........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fisabilillah. Ouummey 30 (8/21/2022 10:31 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣0️⃣ ________________________📖 Ƙarfe sha ɗaya suka fito a tare su biyar ɗin suna tafe suna mata ƙorafin dena fitowar da tayi dan rabon ta da party da club tun kafin su je resort which is three weeks da dawowar su yanzu, har Gara cinema tun da gashi yau ta zo. "Ni fa tun kafin tafiyar mu resort na fahimci wancan driver ɗin nata ya ɗauke mata hankali, ban san wane irin asiri yayi mata ba wai ta bashi aiki a Company kuma a office ɗin ta ta yadda kullum suna tare, ban sani ba ko kin soma irin halin Surayya ne shiyasa ne ko kuma meye oho". Sosai maganganun Hameedah suka yi wa Kisnah zafi, wato a wasan dare take so tace mata ta fara bin maza shine ta wani dake, da alama dai zargin ta take da Saraki, da ƙyar ta samu tayi controlling kanta dan kar tayi something stupid wa Hameedar, cikin irin wannan ƙorafe ƙorafen na su suka ƙarasa wajen motar ta ta ɗan jingina tana kallon su "Am sorry guys, Kuma kusan dole ce zata sa na bar zuwa partying da clubbing, am sorry to say na bar clubbing, har abada ne ko kuwa ban sani ba se abin da gaba ta haifar, for partying da zuwa cinema kuwa rashin lokaci ne yasa bana zuwa, abubuwa da yawa sun faru a Company da dole ana buƙatar attention ɗina, as you can see sabida yawan abubuwan dole se da na samo me taya ni dan ni kaɗai bazan iya ba, amma cinema kam insha Allah ko next movie da ni za'a kalle shi". Jijjiga kai Surayya tayi cikin yarda da abinda ta faɗa kafin suka haɗa baki ita da Leekha wajen faɗin "I believe you dear, Allah ya taimaka ya bada Nasara, worry not okay?". Dariya duka suka saki ganin yadda suka haɗa baki kafin Meenah itama ta dafa kafaɗar Kisnah "All the very best dear, Allah ya taimaka, we all are with you kinji". Gyaɗa kai Kisnah tayi cikin farin cikin irin yadda suke nuna mata ƙauna, ɗan siririn smile Hameedah ta saki saying "Wishing you lots of lucks". Murmushi itama tayi mata tare da nodding head alamar amsawa. Jikin ƙofar side ɗin da take zama ta matsa ta shiga knocking a hankali, shiru be buɗe ba, ɗan ƙara ƙarfin knocking ɗin tayi nan ma shiru, matsowa Meenah tayi ta saka key ɗin motar ta ta shiga ƙwanƙwasa glass ɗin tsawon lokaci kafin yayi unlocking car ɗin ya fito hannun sa riƙe da gorar ruwa, zagayo wa wajen sa Kisnah take ƙoƙarin yi dan ganin ko lafiya yake suke ta Knocking ko kuma bacci yayi sedai tuni Hameedah ta riga ta isa wajen ta fara magana cikin sigar rashin mutunci tana watsa masa wani kallon banza "Wannan wane irin wulaƙanci ne malam zaka kama ka wani rufe ƙofa ka bar ta a waje se faman bugu take kamar wani taka, ko kuwa dan kaga ta danƙa maka keys ɗin motar ne yasa kake feeling taka ce or what, ban da tsabar rashin iya samun guri irin na talaka har kai ka isa ka bar mu tsaye tsawon wani lokaci kamar wasu bayin ka ko masu yi maka maula, me kake dashi, waye kai, waye baban ka kuma waye ya tsaya maka, ko da yake ba laifin ka bane ita ce ta sake maka har kaga damar ta shiyasa ka rai nata, banda tsabar rashin ilimi da.............". Razananniyar tsawar da Kisnah ta sake mata cikin kiran sunan ta ce ta dakatar da ita daga cin mutuncin da take wa Saraki da ya gama wanke fuskar sa da ruwan robar hannun sa sedai be kai ga mayar wa ba ya jingina jikin motar yana sauraren ɗibar albarkar da Hameedah ke masa sedai be ko ɗago kai ya kalle ta ba yana dai sauraren ta. Da wani irin zazzafan taku Kisnah ya ƙara so inda Hameedar take tsaye tare da ɗaya hannun ta cikin son sauke mata kyakkyawan mari sedai a karo na farko Saraki ya riƙe hannun ta, da sauri ta waiwaya ta kalle shi tana son ƙwace hannun ta sedai be saki ba sema girgiza mata kai da yayi alamar kar ta mare ta tare sake mata hannun, "Ƙyale ta, kar ki dake ta". Ya faɗa xan ƙasa cikin murya irin ta wanda be daɗi da tashi daga bacci ba, juyawa tayi ga Hameedah da ta tsaya speechlessly watching at Kisnah kamar ta sami TV "Da ka bar ni na koya mata hankali yaa, na daɗe ina tolerating iskanci da baƙaƙen maganganun ki gare ni amma ke baki gane ba, danne rai na nake kar nayi miki rashin mutunci amma You keep pushing me to the wall, to tau na kai ƙarshe da iya shegen ki ko kin ɗauka ban da hankali ne ban fahimci zagin da kika gama yi min ba yanzu, ko kin zata ban fahimci nufin ki we have an illegal dirty affair da ya Saraki bane a kalaman ki, na daure na share ne kawai saboda ƴar uwar ki gata nan.......". Ta faɗa pointing at Meenah dake nan tsaye kamar an dasa ta saboda tsabar tashin hankali ".......if not sabida ita wallahi da tuni nayi maganin ki, and ki sani Yaa da kike kira da driver ya fi mun ke sau adadin da za'a kuma bani zaɓi, je mau be mere driver a wajen ki amma ni a wajena shine mutum na farko da nake ganin matuƙar girma da darajar shi dan haka duk wadda a cikin ku take ganin ba zata iya girmama shi ba to na haramta ko magana tayi masa ehe, zulwajahaini kawai ƙaramar ƙwaruwa, ke iskancin ki na gangan ne yarinya, da ace kin isa kin cika kin kuma tumbatsa ba soka min magana da hassada a ɓoye zaki yi min ba fitowa zaki yi gaba da gaba ki tare ni ki faɗa min ni karuwa ce, ko an gaya miki dan kin yi hakan zan damu ne, ko kin manta ba yau na fara jin an dangan ta ni da sunan ba, kuma tun da ake faɗa kin taɓa ganin na damu, eh ni karuwa ce amma me aji dan ni maza da kan su suke bina bani nake bin su ba, na san abinda kike wa hassadar ke nan kuma dai se haƙuri na riga nayi miki nisan da ko hange na ba zaki iya ba balle ki kamo ni, mara mutunci kawai". Zuwa yanzu hawaye kawai ke kwarara a fuskar Hameedah cikin baƙin cikin irin cin fuska da tozarcin da Kisnah tayi mata amma fa a ganin ta dan duk da dare ne seda aka samu masu tsayawa kallon abinda ke faru cikin waɗanda suka fito daga gidan kallon. Ita kuwa Kisnah tana gama faɗar abinda ta ga dama wa Hameedah ta shige mota tare da maida murfin ta rufe, batare da ya dubi kowa ba shima Saraki ya shiga side ɗin da ya kamata ya rufe, cikin kankanin lokaci ya tashi motar suka fita daga cinema ɗin suna barin su Surayya da suka zama so speechless tsaye kuma daskare a wajen. Tafiya yake a hankali kamar baya so time to time yana kallon gefen da take zaune tana fidda huci har lokacin kamar wadda zata ci babu. "Relax, kwantar da hankalin ki pls, ni ban ma ga abin tashin hankali a maganar da ta faɗa ba, kema kin san gaskiya ta faɗa am just a mere driver to you Kuma be kamata na rufe mota na bar ki waje kina Knocking ba alhalin kina matsayin mamallakiyar motar, uhm to meye ta faɗa da zafi kuma". A hanzarce ta juyo ta kafe shi da ido tana jefa masa kallo me kama da harara cikin jin haushin abin da yace "To da kake driver ita ta ɗaukar min aikin, ko ita take biyan ka, ina ruwan ta in ma kwana nayi ina knocking da zata wani kama zagin ka, motar ta ce ko mun haɗa kuɗi da ita mun siya ne". "To shikenan baku haɗa kuɗi kun siya ba, amma ni a ganina da baki kula ta ba, mace me class bata faɗa any how Kuma bata tsayawa ihu da kowane kalan mutane, wanda suka isa da wanda basu isa ba, and pls ki rage saurin marin da kike yi, da an miki abu se ki hau kai mari hakan ma is not good most especially ga maza, ba class ɗin ki bane". Ajiyar zuciya ta saki fushin ta na ɗan raguwa saboda yadda yake magana cikin kwantaccen harshe da taushin murya "Zan dena insha Allah, Amma for Hameedah dole nayi magana dan ta ƙure ni ne, na daɗe da sanin tana min hassada da baƙin ciki akan komai, ko kasan murna tayi lokacin da na kasa assignment ɗin CON005?, kuma na gani na gane amma na nuna ban san tana yi ba, yanzu haka da muka fito wasu banzan maganganu take faɗa tsakanin ni da kai wai shine dalilin da na baka aiki a office ɗina dan kullum mu kasance tare, shima na danne rai na to kuma meye ruwan ta da kai, shiyasa na ci mata dan gobe kar ta kuma min dan wallahi in ta kuma se ta gwammace rungumar transformer kan matakin da zan ɗauka kanta". Ɗan murmushi ya saki ganin yadda take masifa kamar har yanzu Hameedar na gaban ta "On her behalf, she's really sorry Miss, zata kiyaye gaba". "Better for her". Ta faɗa tana kau da kanta gefe, a hankali a hankali yake ɗan mata hira though ba iyawa yayi ba amma ya ƙoƙarta dan ganin ya sauke mata fushin da take har se da yaga tayi ƴar dariya kafin ya ƙyale ta. Yana yin parking tayi masa sallama tare da wuce wa cikin gida shima ya fice zuwa ɗakin sa. Kashe gari da tashin hankalin fake currency ɗin nan suka tashi, sosai suke ta kan bincike amma ko trace ɗin mutumin da ya sayi kayan ba'a samu ba, hankali fa ya tashi manager ya shiga cakwakiya dan bank ɗin da yaje depositing riƙe shi suka yi suka handling ɗin shi wa hukuma kan zr damfare su da kuɗin ƙarya, ba ƙaramin kuɗi Kisnah ta zuba ba kafin aka sake shi. Duk wanda yaga kawu kuwa ze yi zaton shine ainahin me dukiyar dan yadda yayi wujiga wujiga dashi ya fita kamannin sa wajen neman yadda za'a yi ayi tracing mutumin, kai kamar ma yafi ita Kisnahn damuwa dan se ita ta koma tana kwantar masa da hankali kafin asamu ya ɗan daidaita dan har suma biyu yayi. Cikin wannan tashin hankalin aka kawo takardun hannun jari da wani Company ya zuba a K&S flour and food stuffs wanda dole ana buƙatar signing ɗin ta kafin ayi documenting a Kuma ba wa su waɗancan copy ɗin su. Da wanna damar kawu yayi amfani wajen haɗawa da fake takardun ownership ɗin nan ya kai mata tayi signing sedai ba shi ya kai mata direct ba manager ɗin ta ya bawa ya kai, bata tsaya duba komai ba ta yi signing a duk inda akace tayi tare da bawa Saraki ajiya kan ya bawa manager in ya dawo karɓa ita kuma ta wuce station dan fa bank ɗin sun ƙi haƙura suna batun shigar da ƙara dole ana buƙatar ta dan ganin ko za'a iya cimma maslaha in suka zauna. Gyara takardun yake yana girgiza kan sa ganin yadda gaba ɗaya ta ajiye takardun a hargitse kafin ya shiga jera su ɗaya bayan ɗaya yana ajiye kowacce inda ta dace ta hanyar karanta heading ɗin jiki har yakai kan ta ownership ɗin, cikin matuƙar mamaki ya ciro su har guda huɗu ya ajiye a gefe ya ƙarasa gyara waɗan can kafin ya shiga karanta su ɗaya bayan ɗaya, in akace mamaki to an rage matsayin yanayin da yake ciki, wani irin tsoron Allah ne ya ratsa shi a zaunen da yake ganin tsantsar rashin tsoron Allah, mugunta da kuma ƙarfa ƙarfar da wasu da suka daɗe da kwashe kayan su gaban manzon Allah suke yuƙurin aikatawa. Takardar shedar mallakar kamfanoni ɗaiɗai har huɗu ne, K&S construction, K&S flour and food stuffs, K&S Furnitures, se K&S drinks, Kuma wai mugun se da ya duba manyan da suka fi girma, bunƙasa da kawo riba, dafe kansa yayi cikin tunanin waye me wannan aiki dan duk yadda aka yi wanda yasan ciki da bai na Companies ɗin ne da wannan aiki, kuma baya tantama shine boss ɗin Emeka, shine ƙashin bayan asarar da akayi yau haka kuma shine yake assasa duk wata asara dake ta afkuwa cikin kamfanonin a kwanakin nan. Seda gaban sa ya faɗi da sunan kawu ya faɗo ran a, da sauri ya girgiza kan sa telling his mind it's impossible, yes impossible ace wai kawu ne behind all this evil act, no be ma yarda ba, taya ma ze zama kawu bayan shine ke kula da duka dukiyar tun kan ta girma kuma dukiyar tai ta haɓaka batare da wata matsala ba se yanzu, beside haka ma kalli fa tashin hankalin da kawun ya shiga a ɗazu, Bama shi bane, baze zama shi ba, ya sake jadda dawa a ran sa, to waye??? Yana cikin wannan tunanin har manager ya shigo be sani ba dan ya daɗe yana knocking Amma ba amsa so yayi tunanin ma ba kowa bari ya shigo ya ɗau takardun kawai ya wuce dan su kawu na jiran sa kasancewar da sanin sa aka bashi takardun ya aka bayan sun masa alƙawarin maƙudan kuɗaɗe. Wani irin mazari jikin manager ya ɗauka ganin takardun a hannun Saraki yana jujjuya su tare da sake karanta su kamar wanda aka bashi aikin haddar su dan se da ya zamana ya haddace every single word dake kan papers ɗin nan, a hankali manager ya fice daga office ɗin batare da ya bari Saraki ya lura da shi ba, jiki na rawa ya zaro wayar sa ya shiga sanar da kawu halin da ake ciki bayan ya sami waje ya laɓe wanda daidai lokacin Saraki da yaga fitar sa ya biyo bayan sa da takardun a hannu ya na neman sa dan ya bashi tun kan yayi nisa. Daidai wajen elevator yake jiyo magana ƙasa ƙasa dan haka ya ƙarasa a hankali ya ɗan laɓe dan jin waye ke waya haka cikin rawar murya alamun rashin gaskiya ga kuma ɓuyan da yayi wajen da yake tunanin ba wanda zeje dan elevator ɗin tsoho ne an dena amfani dashi so bame zuwa ta wajen se ta kama. "Kayi haƙuri Alh ba laifi na bane, na kai takardun kamar yadda kace wallahi ban san yaya akayi aka samu wannan matsalar ba, kuma alamu sun nuna ita bata karanta ba tunda ta saka hannun wannan sabon ma'aikacin nata ne na samu yana dubawa". Shiru yayi alamun saurare daga ɓangaren da yake kafin ya cire wayar faga kunnen sa yasa handsfree da alamun baya ji sosai kenan sedai ya rage Muryar yakai ta can ƙasa "Lallai manager baka san da wa kake wasa ba , bari kaji in faɗa maka wallahi ko da wasa naji sunana ya fito a wannan batun se ka gwammace mutuwar ka kan rayuwar da zan sa kayi, kar kuma ka manta da nasan gidan ka, ƴaƴa huɗu ga kuma tsaleliyar mata, Har yau Sama'ila na ke kuma kasan abinda zan iya aikatawa". Gumi manager ya shiga sharewa jin kawu ya kashe wayar sa, da sauri Saraki ya lallaɓa ya bar wajen sedai tuni manager ya ganshi dan yaji sautin takalmi kamar ana tafiya a hankali, wani tashin hankalin manager ya Kuma shiga haka kuma be yi ƙasa a gwiwa ba ya sake kiran kawu ya sanar dashi. ****** "Ya zama dole su mutu a yau dukkan su, daga ita har ɗan iskan yaron dake neman zame mana barazana, a yau zasu mutu base gobe ba dan a kan dukiyar nan zan iya yin komai akan kowa, dama na kawo waccan hanyar ne dan mu bar ta da ranta tunda kuma bata san hakan zata tafi tabi mattacen uban ta yau". Gyaɗa kai kawu yayi cikin yarda da batun Alh Haladu kafin ya zaro wayar sa ya shiga danna kira, within minutes aka ɗauka ya kuma bada umarnin kisa ga duk wanda ke cikin motar su Kisnah bayan ya bada lambar motar ya kuma haɗa da location ɗin da suke da kuma duk Possible titin da zasu iya bi su kai gida. ******* A rikice ta dawo K&S furnitures saboda kiran ujilar da Saraki yayi mata, a parking space ta same shi tsaye yana jiranta fuskar sa ɗauke da wani yanayi, komawa mazaunin ta tayi ya shiga driver's side tare da tashin motar ya fice, seda ya hau kan titi kafin ya ɗora mata takardun a kan cinyar ta, da kallo ta bisu kafin a hankali ta ɗauka ta shiga karantawa, cikin tashin hankali ta ɗago cikin don yi masa magana sedai ko kafin ta kai ga hakan wata babbar mota ta zo ta daki tasu, hantsila wa motar su ta shiga yi kafin cikin ikon Allah ta tsaya daidai hakan yasa wata babbar motar yowa kan su sedai tuni Saraki da ya fahimci an shirya musu ne ya figi motar cikin wani irin azababben gudu hakan ya sa itama babbar motar rufa musu baya..............................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, comment and share fidabilillah. Ouummey 31 (8/22/2022 9:20 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣1️⃣ ________________________📖 Tsawon lokaci suna zuba azababben gudu kan shimfiɗaɗɗen titin garin har suka fara ficewa daga cikin ainahin garin suna dosar daji ka, juyawa yayi ya kalli bayan sa ta cikin mirror ɗin motar, wani irin ƙure speed yayi ganin har lokacin babbar motar na bin su a baya itama cikin nata gudun. Cikin tashin hankali ya kallo gefen da Kisnah take zaune kamar mara rai tsabar shock da ruɗanin da take ciki "Ki ɗaura seat belt ɗin ki da sauri, am increasing the speed now dan za su iya cimma na". Se lokacin ta saki wani Gwauron numfashi kafin a gigice ta kalli bayan su lokacin tazarar dake tsakanin su da babbar motar Ba wata me yawa bace, hannu na rawa ta shiga ƙoƙarin saka belt ɗin wanda se da ƙyar ta iya saka shi, aikuwa take ya ƙure gaba ɗaya speed ɗin motar ya shiga tsufa azababben gudu, fit fit haka motar take wucewa kamar walƙiya hakan yasa nan da nan suka yi wa babbar motar ɗan nisa duk da alamu ya nuna shima matuƙin ta ya ƙure nasa gudun, haka suka ringa shige dajijjika kamar ba zasu ƙare ba amma ba su da alamun tsayawa, to su tsaya yin me ma. Zaro ido yayi cikin sabon tashin hankali lokacin da ya kula da tankar mai da ta tare titin da alamu ta lalace ne a tsakiyar hanya kuma be lura ba se da ya zo daf, cikin ɗimuwa ya shiga ƙoƙarin ganin ya tsayar da motar amma inaa taƙi tsayawa saboda mugun speed ɗin da ya ƙure, hasbunallah wani'imal wakeel kawai ya shiga maimaitawa dan ya tabbatar se sun haɗu da wannan tankar haka kuma da sauri ya sa hannu ya fisgo Kisnah cikin jikin shi ya rungume cikin son kare ta ko yaya ne. Wani irin ƙara ce ta tashi lokacin da motar su ta daki wannan tankar haka kuma tayi baya kamar wadda aka tura da mugun gudu kafin ta shiga hantsilawa tayi gefen dajin dake Wajen, seda ta jujjuya sosai kafin ta tsaya, mintuna ƙalilan Saraki ya fara ƙoƙarin ganin ya fito daga motar cikin dauriya da son ganin mutanen cikin waccan motar basu iske su a wajen ba dan yasan yin hakan tamkar ƙarshen rayuwar su ne yazo. Da ƙyar ya iya fita daga cikin motar kafin ya samu yin dabarar da murfin ɓangaren sa ya buɗe ya zaro Kisnah da take a sume jini na bin fuskar ta, kallon ta ya tsaya yi cikin tunanin yadda de yi da ita dan tabbas baya tantama hannun sa na dama a karye yake dan yana iya jin yadda yake masa lilo haka kuma yayi masa nauyi sosai, ƙarar dosowar babbar motar wajen su yasa da sauri ya saka hannun hagun sa ya ciciɓata da ƙyar ya saɓa ta a kafaɗar sa kafin ya shiga gudu da ita ta cikin duhun ciyayi da bishiyun gonar da suka faɗa, be ko yi wani nisa ba motar su ta kama da wuta hakan yasa ya dakata gami da juyowa ya kalle ta. Yadda take ci da wuta ya saka shi furta alhamdulillah dan yasan ba dan rahamar Allah ba da tuni suna cikin motar yayinda wutar zata tashi ta cinye dukkan wata tsoka da ƙashi na jikin su. Jin kamar sautin Muryar mutane yasa ya juya da sauri ya cigaba da tafiya da ita cikin tsananin dauriya dan ba ƙaramin jin jiki yayi ba, wani irin jiri jiri yake ji sanadin dokuwa da kan sa yayi lokacin da motar ke tumble sedai aka ce wai shi gudun ceton rai da ban ne wanda hakan ne yasa har yake iya daurewa dan ganin sun tserewa magautan su. ***** Can ɓangaren ƴan hirer killers ɗin da kawu ya turo kuwa suna ƙarasowa gab da wannan tanka suka tsaya tare da firfitowa dan sun hango ta tunda nesa, wajen da motar su Kisnah ke ci da wuta suka ƙarasa don tabbatar da su ne ɗin ko wasu ne sedai number motar su dake kan ci da wuta ta tabbatar musu da sune dan ga tambarin KS nan dake bayan duk wata mota tata, duk da ganin motar na ci da wuta basu fasa bincika gonakin dake gefe gefen hanyar ba dan tabbatar da sun mutu basu sami kuɓuta ba. Ganin basu ga wani alama dake nuna sun kuɓuta ba yasa suka koma motar su suka zauna har se da gaba ɗaya motar ta ƙone ƙurmus kafin suka juya bayan sun ɗauki hotunan motar lokacin da take kan ci, number motar da kuma lokacin da ta gama ƙonewa gaba ɗaya. ******* Gudu sosai yayi kafin ya fara tafiya a hankali kan sa na juya masa saboda tsabar jirin da yake ɗiban sa, tun yana iya tafiya har ya kasa ya nemi ƙarƙashin wata bishiya da yake ganin ta dishi dishi ya kwantar da Kisnah tare da zama kusa da ita yana maida numfashi ɗai ɗai cikin tsananin azaba da jigata. Da hannun sa me lafiya ya dafe kan sa da yake jin kamar ana masa ihu a ciki, tun yana gani dishi dishi har ganin sa ya ɗauke gaba ɗaya ya daina gani da fahimtar komai. ********* A hankali ta fara buɗe idanun ta tana yi tana rufewa tare da buɗe wa saboda yadda take gani uku uku har ganin ta ya daidai ta. Cikin mamaki take bin wajen da take kwance da kallo, jar ƙasa ce sosai akayi ginin da ita dan gata nan a fili ana iya ganin ta, haba ɗaya ginin da akayi da ita be fi kamu biyar ba se kuma wasu karare ko yayi zata ce ne da aka haɗa aka tashi ɗaki dashi, a ɗan tsorace ta nemi miƙewa sedai da sauri ta dafe kanta tana faɗin "Wash". Saboda zafin da ya ziyarci kan nata a daidai lokacin ne kuma komaɗaɗɗiya kuma yamutsattsiyar mata ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da wani ƙoƙo, wata irin zabura Kisnah tayi da har yasa taji kamar kanta ze faɗo saboda nauyi ga kuma zafin da ya ziyarce ta sedai bata ko kula hakan ba ganin wannan aljanar tana nufo ta. Da sauri matar ta ƙara sa matsowa wajen Kisnah tana ajiye ƙoƙon hannun ta kan wani ɗan tudu dake gefen su, da hanzari ta saka hannun ta da ƙashi ne kawai da fata ba ko ɗigon tsoka (a ganin Kisnah ) ta ruƙo ta ganin tana neman fita daga ɗakin, wani irin ihu Kisnah ta saki jin matar ta riƙe ta haka kafin ta sami zarafin magana matar ta shiga yi mata magana cikin wata gurɓatacciyar Hausa da ba wani ganewa take ba "Kayi haƙuli yalo, baka da lashiya magani nak kawo maka kashi". Ai ina Kisnah bata ma tsaya ta saurare ta ba balle ta fahimci me take son cewa se ƙoƙarin ƙwace hannun ta kawai take tana zarar idon tashin hankali, cikin zuciyar ta kuwa bata bar tunani ya akayi ta zo hannun wannan aljanar ba, ganin fa bazata tsaya ba gashi maganin na neman bushewa yasa matar ta ɗan ɗaga murya ta ƙwala kiran "Bingel". "Na'am". Wata ƴar matashiya ta amsa tana shigowa cikin ɗakin, kallon ta mayar tayi kafin tayi mata maganin cikin wani irin yare aikuwa da sauri yarinyar ta ƙaraso ta kai nata hannuwan da bambancin su dana tsohuwa zance ko dattijuwa ce kaɗan ne, aikuwa se gashi sun danne Kisnah ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi, sosai mamakin yanda waɗan nan matan masu matuƙar siran ta kamar me suka iya danne ta haka har takasa motsi. Ƙwaryar da matar ta shigo da ita ta janyo ta dangwalo wani koren abu cikin wata leda kamar mai kamar kuma ruwa me ɗan kauri ta shiga shafawa Kisnah kan goshin ta zuwa cikin kan ta kaɗan, runtse ido kawai Kisnah ta ke yi cikin tsananin zafi dan yarinyar da aka kira da Bingel ta danne mata baki da tafin hannun ta ɗaya saboda tsabar ihun da ta ke kurma musu. Seda suka gama shafa mata maganin kafin Bingel ta cire hannun ta a bakin Kisnah, da sauri kuwa ta tofar da miyan da ta tara jikin rigar Bingel ɗin sedai ko kallon ta bata yi ba balle ta nuna ta ji haushi se ma wata ƙwarya da bata san yaushe aka shigo da ita ba da Bingel ɗin ta miƙawa matar nan suka kuma matse mata baki suka ɗura mata kafin suka sake ta, a tamanin ta duro daga kan abinda suka kwantar da ita da bata ma tantance mene ne ba ta shiga kakarin amai sedai ko ɗigo hasalima wahalar da kanta kawai tayi dole haka ta haƙura ta koma ta zauna tana hararar Bingel dan ita dattijuwar suna gama ɗura mata maganin ta fice. Murmushi Bingel ta sake ma Kisnah da yasa tayi kamar wata zombie a idanun Kisnah duk da kuwa Bingel kyakkyawar bafulatanar daji ce sedai a idanun Kisnah ita bata ga wani kyau ba se ma tsorata ta da take yi. A can wajen ɗakin kuwa dattijuwar na fita ta tadda wani yamutsattsen farin bafulatanin daji sedai yafi matar nan kyan gani sosai, murmushi ta sake masa da dole wanda be saba ganin su ba ya tsorata sedai a wajen su su murmushi ne hakan, da ɗan sauri dattijon ya matso kusan matar "Nene Ina fatan kin shafa mata kuma tasha maganin". Ya faɗa cikin cikakkiyar Hausar sa da tafi ta su matar da ya kira Nene nesa ba kusa ba, gyaɗa masa kai Nene tayi tana nuna masa ƙwaryar hannun sa "Ƙin sha yalon can yayi sheda muka masa danna ni da Bingel, na shafa ma mun sha masa, aradu yalon kwai ƙarfin kai arɗo". Ɗan murmushi arɗo yayi cikin fahimtar matar tasa, taurin kai shine ƙarfin kai a wajen su, kallon ta yayi yana faɗin "Tun da ta sha ai da sauƙi, yanzu ki haɗo min wani na bawa yaron can dan shi har yanzu be farko ba kuma da alama ya fita shan wahala". "Tau arɗo". Ta faɗa tana shiga wata bukka nan gefen inda suke tsaye, tsawon lokaci tana ciki kafin ta fito da ƙwaryar da ta shiga a hannun ta ta miƙa wa arɗo, karɓa yayi ya juya ya shige wata bukka da ke ɗan nesa da wadda Kisnah ke ciki seda ya duƙa sannan ya iya shiga ciki, itama kamar waccan an yi mata ginin jar ƙasa kamu biyar kafin aka ƙara sa da asabari da kuma ya yume ya yumen su. Kwance kan wani gadon kara da aka shimfiɗawa wani tsumma na hango Saraki, gaba ɗaya kamannin sa sun canja dan ƙafar sa ɗaure take da wani tsumma bayan an zagaye ta da karare haka ma hannun sa na hagu, da sallama dattijon ya shiga ɗakin yana ƙara sa gaban Saraki ya tsaya tare da bin sa da kallo na wasu daƙiƙu sannan ya ajiye ƙwaryar hannun sa ya ƙara sa wajen Saraki, hannu yasa ya ɗago ƙafar ya shiga kallon tafin ƙafar da yayi jajir dashi ga kuma alamun cuwuka sosai a jiki, hannu yasa ya lakato wani mai cikin wata ƴar jakar fata dake jikin sa ya shiga shafawa a tafin ƙafar, seda ya shafe ko ina kafin ya saki ya matsa yana taɓa ƙaurin sa da yake ɗaure da kararen, se aya taɓa sosai sannan ya gyaɗa kansa tare da yayyafa wani farin Ruwa kan gurin sannan ya tashi. Wajen hannun ya matsa ya kama hannun ya jinjina shi cikin nasa kafin ya ajiye a hankali bayan ya ɗan jijjiga shi, a hankali ya sunkuya ya kai bakin sa ya shiga tofa abinda ban sanu ba kan hannun, koren magani irin wanda aka shafawa Kisnah ya lakata ya shafa masa shima a kansa kafin ya tashi ya fita bayan ya sake bin sa da kallo. ****** A can wajen su kawu kuwa duniya sabuwa bayan sun ga hujjojin da yaran su suka basu na shedar mutuwar su Kisnah, wani ɗan ƙwarya ƙwaryar liyafa ranar suka yi a tsakanin su shida Alh Haladu. Seda aka kwana aka wuni da faruwar lamarin kafin ya shigar da ƙorafi kan ɓatan Kisnahn yana me nuna tsantsar damuwa da tashin hankali Wada da ƙyar ƴan sandan suka sami lallaɓashi ya bar police station ɗin bayan an barbaza jami'ai cikin garin manya dan nemo inda take. Ranar farin ciki wajen su Mommy kamar sallah ko ma fiye duk da so tayi su wulaƙanta rayuwar ta sedai ko a hakan ma duk ɗaya dan haka ta shiga addu'ar kar Allah yasa Kisnahn ta bayyana, haka ƴan sanda suka ɗin ga shiga lungu lungu neman ta amma ko alamar ta, ba wani club, hotels ko cinema dake garin manya da jami'ai basu shiga neman ta ba amma duk ba wani labari, cikin ƙanƙanin lokaci gari ya ɗauka da batun ɓacewar Kisnah, kiran wayoyin da ake wa su Meenah da su Surayya na wai jaje yasa suka san meke faruwa a ranar kuma suka haɗu gaba ɗaya suka tafi gidan su Kisnahn sedai ba ƙaramin rashin mutunci Mommy ta shuka musu ba dan ko barin su su zauna bata yi ba ta shiga jifan su da munanan kalamai har tana neman ɗora musu alhakin ɓatan Kisnahn, al'amarin be musu daɗi ba haka dole suka tarkata ƙafafun su suka fice daga gidan sedai basu koma gida ba neman ta da suka shiga yi a wuraren da suka san suna zuwa. A kwana na uku da ɓatan ne kawu ya shigar da batun wai yana zargin driver ɗin ta ne ya sace ta, nan fa lamari ya canja aka shiga neman Saraki ruwa a jallo sedai rashin sanin inda za'a iya samun sa ya sa dole aka taƙaita binciken bayan an saka jami'ai a ko wani titi dan bincike duk motar da tazo wucewa. Ranar da suka kwana biyar da ɓata ne aka samu rahoton samun ƙonanniyar motar su da suka fita a cikin ta, jami'an bincike aka ɗauko suka shiga aikin su a daidai wajen da aka ga motar kafin daga baya suka sanar da cewa motar ta kama da wuta ne sanadin dukan tankar mai da ta tare hanya wanda ya dukan yasa murfin gidan man ɓalle wa abinda ya haddasa tashin wuta a motar kenan bayan ta hantsila har so biyar. Al'amarin ya girgiza da yawa cikin jama'a dan zuwa wannan lokacin babu wani mazaunin garin manya da maƙoftaka da bai san da ɓatan the CEO na K &S companies ba, ranar kawu kam a asibiti ya kwana saboda yadda ya dinga sumewa ana yayyafi masa ruwa daga ƙarshe kuma ya dinga sambatu kamar wani zararre dole aka dangana dashi asibiti. Duk yadda Mommy ke ƙin Kisnah seda ta ɗan yi sanyi sanadin mutuwar kafin kuma daga baya ta watsar ta shiga fantamawa cikin nera, su Maigado kuwa duniya sabuwa babanta ya zama me kuɗi. Seda kawu yayi kwana uku a asibiti kafin aka sallamo shi lokacin ya dawo daidai sedai ba uhm balle uhm uhm sedai yayi ta kallon mutane, dole a ka rufe Companies ɗin K&S har zuwa lokacin da kawu ze dawo hayyacin sa ga kuma jimamin mutuwar mamallakiyar wajen da ma'aikatan ke ciki. ******* Seda Saraki ya kwana shida be san wa ke kan sa ba kafin ya farfaɗo, zuwa lokacin kuwa tuni ciwukan ƙafar sa da yaji sanadin gudu cikin daji yana taka ƙayoyi sun fara warkewa, zuwa lokacin kuwa har Kisnah ta saba ganin su Bingel dan ta daina tsoron su sedai kuma bata kula su haka kuma bata iya cin abincin su sedai a bata fura da nono kullum........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 32 (8/24/2022 10:07 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣2️⃣ _______________________📖 Zaune take a bakin bukkar ta kan wata tabarmar kaba tana bin Bingel da ke kwanto shanu da garken su ke can gefen bukkokin su da kallo, yadda take iya kwance su ta na shafa jikin su ba tare da tsoro ba ba kuma tare da su shanun sun wa Bingel ɗin komai ba ya matuƙar ƙayatar da ita, ba tun yau ba in taga Fulani na kora shanu abin ke burge ta da cika ta mamakin yadda suke iya controlling ɗin su, yanzu kuwa da take ganin hakan a gaban ta sosai se take jin kamar itama ta gwada sedai kuma tana tsoro. Sanye take da kayan saƙi irin na Fulani, ƙaramar riga da bata sauka kan cikin su ba se zanin saƙi ɗaure a jikin ta shima be ko kai ƙaurin ta ba, gashin kanta ya wani barbaje kamar be taɓa ganin gyara ba, ƙafafun sanye da wani tsohon silifas da arɗo ya samo mata da ƙyar cikin garin su dan ta ƙi yadda ta saka irin takalman su. Da sauri ta miƙe ganin Bingel na shirin ficewa da shanun bayan ta gama yi wa Nene magana cikin bahagon yaren su da ya kasance fulatanci sedai na su fulatancin ba irin na gamagarin Fulani bane, nasu na Fulani daji ya sha banban da ragowa. "Ki tsaya ni, nima zanje". Tsayawa Bingel tayi tana kallon Kisnah kafin ta juya ta kalli babar ta, gyaɗa mata kai Nene tayi alamun su je tare tun d tana so. Ba yau ne ta fara fita kan ta ba ɗan kwali ko hula ba haka ba yau ta fara fita da kayan da basu rufe mata jiki ba shakka yasa ko kaɗan abin be dame ta ba ta fice a yadda take, ita matsalar ta ɗaya da kayan nauyi ga kuma zani da bata saba sawa ba da yake bata matsala wajen tafiya shiyasa ma in ta tashi take ɗaure shi can sama dan da ƙyar yake kai wa gwiwar ta, ɗaurin zanin kuwa dole ya bawa wanda yaga yadda ake yin sa dariya dan kawai cukurkuɗa kayan ta take ta cusa tayi gaba abinda, to ta ina zata fara wahalar da kanta, dole dai su ɗin zata saka tun da nata gaba ɗaya sun ɓaci da jini haka wasu guraren duk sun yayyage. A hankali suke tafiya da Bingel yayinda shanun suke gaban su, kalle kalle take hannun ta riƙe da sandar da ta saka dole Bingel ta ɗauko mata itama wai zata taya ta kula da shanun, sosai garin ya burge ta ganin ko ina cike yake da korayen ciyayi, daga inda take ta hango kogin dake gaba da su sosai wanda da alama nan zasu tsaya da shanun, aikuwa suna kaiwa wajen taga duk shanun sun tsaya haka kuma sun fara ƴan ciye ciyen su, seda ta juya bayan ta sannan tasan ashe sun shiga daji sosai dan bata ma iya gane ta wace hanya suka kawo nan ɗin ba. Ɗan kallon Bingel tayi kafin ta juya ta shiga bin wata hanya da taga wasu kyawawan tsuntsaye na tafiya a jere a jere a sama, sannu a sannu take bin tsuntsayen tana irga adadin su har tayi nisa bata ankara ba, seda ta gaji kafin kuma ta juyo dan komawa wajen Bingel sedai sam ta rasa ta hanyar da ta shiga wajen, hanyoyi ne da yawa gasu nan haka yasa ta daburce ta rasa ina zata bi, tsayawa tayi cikin tunanin wace hanya zata bi daga ƙarshe dai ta zaɓi bin hanyar dake right hand ɗin ta, without any second thought ta shiga tafiya tana me fatan Allah yasa hanyar daidai ta ɗauka, seda ta ɗan yi nisa kafin tafara jiyo muryoyin mutane da kuma ɗan kukan shanaye ƙasa ƙasa aikuwa cikin azama ta ƙara sauri wa tafiyar ta dan ta isko wajen dan tun da ta jiyo kukan shanu ta san ta dawo wajen Bingel. Wasu Fulani samari ta gani kowanne riƙe da sanda a hannun sa suna tsaye suna magana da ƴar dariyar su suna nuna wani ɗan uwan su da ke duƙe ƙarƙashin wata sanuwa yana shan nonon ta, zaro ido Kisnah tayi ganin abinda yake yi kafin ta fara yamutsa fuska cikin ƙyanƙyami, wani irin amai ne ya tuƙo ta ganin yadda ruwan nonon ke biyo wa ta gefen bakin sa aikuwa nan ta duƙa ta shiga amaye ƴar guntuwar fura da nonon da yayi saura a cikin ta, kakarin aman ne yasa hankalin samarin ya dawo kanta gaba ɗaya har wanda ke ƙasan saniyar, sakin shanuwar yayi ya fito daga ƙarƙashin ta ya tsaya yana ƙarewa Kisnah ta kallo a lokaci ɗaya yana lashe ragowar nonon dake gefen bakin sa da harshen sa, da sauri ragowar samarin suka yi kan Kisnah sedai kafin su ƙarasa Bingel da ta biyo bayan ta neman ta ta riga su, ɗan duƙar da kai tayi ta gaida su kafin kuma ta zuba gwiwoyin ta a ƙasa ta gaida ɗaya saurayin dake tsaye yana kallon Kisnah. Jinjina mata kan da yayi yasa da sauri ta koma wajen Kisnah ta bata ruwa ta wanke bakin ta ta miƙe ita kuma Bingel ta rufe aman da ƙasa kana ta ja hannun Kisnah dake tsaye tana hararar saurayin dan su tafi "Wacece wannan?". Tambayar da saurayin yayi mata kenan cikin Yaren su, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa ta shiga bashi amsa "Baƙuwa ce da Arɗo ya tsinto cikin gona kwanakin baya". "Shi arɗo ya manta da al'adar mu ne da kuma sharaɗin da wassai ya kafa mana a wannan garin da har ze karɓi baƙuncin budurwa, ko kuwa yana son jamana bala'i da masifa ne?". Da sauri Bingel ta tare shi dan jin abinda yake faɗa "Ai ba budurwa bace lamiɗo, matar aure ce da mijin ta aka tsince su, ya sami rauni ne sosai shiyasa baya iya fitowa". Wani kallo saurayin da aka kira lamiɗo ya bi Kisnah dake tsaye tana kallon su cikin rashin fahimtar abinda suke cewa dan da Yaren su suke magana (kuyi hqr fa, banjin fillanci balle in yi muku😝). "Ki cewa arɗo ya shigo fada ƙarfe biyar na yamma". Da toh kawai Bingel ta amsa musu kafin ta ja hannun Kisnah suka wuce yayinda lamiɗo ya raka su da mayatatttun idanun sa. Tafiya suke cikin dajin shiru ba me magana, to ita Kisnah ba gane Hausar su take ba haka kuma bata fahimtar Yaren su, har gwara su in tayu magana suna ganewa, tunani kawai Bingel ke yi na dalilin da ze sa lamiɗo yace arɗo yaje faɗa yau bayan yau ɗin ba ranar fadanci bace, to ko dai be yadda baƙuwa matar aure bace ba ko kuma meye, da wannan tunanin a ran Bingel suka ƙarasa wajen da tabar shanun ta ranar bata bari ta kai lokacin da take tashi kiwo ba ta kora shanun ta suka kama hanyar gida. Suna zuwa gida bata kula Nenne dake mata barka da dawowa ba dan bata gane me tace ba duk inda cewa da Hausa ta faɗa se kawai ta ɗaga mata hannu tare da gyaɗa kai alamun amsawa ta wuce bukkar da aka ajiye Saraki a ciki. Zaune ta sake shi kan gadon shi na kara da aka shimfaɗa wa wani tsumma, da sauri ta ƙara sa ta zauna gefen sa tare da kai hannu zata taɓa nashi me ciwo ya kautar da sauri yana hararar ta "Ina kika shiga da se yanzu zaki shigo, wato a garin da baki san kowa ba ma bazaki daina yawo ba ko?". Karyar da kai tayi cikin son Kare kanta "Yaa ba fa yawo naje ba, I was so bored staying alone, su ba iya yarena sukai ba duk da suna ganewa amma ni ko fahimtar su bana yi sedai fa in ta zama ina bin su da kallo shiyasa yau na bi waccan yarinyar kiwo, kuma baka ga garin ba wallahi me kyau and their atmosphere is so wow banda Kuma beautiful look na garin". Girgiza kan sa yayi kawai, ya sani dole da ma zata gaji tunda ko abokin fira bata da, haka kuma bata saba da zama waje ɗaya ba haka ma wani ƙalubalen ne shiyasa ma be yi mata wani faɗa sosai ba. "And a haka kika fita ba". Kallon kanta tayi kafin ta ɗan taɓe baki "To su irin kayan su kenan, suma haka suke yawo kaga kuwa ba laifi na bane, ni bacci na zo yi dan bana iya bacci a wancan ɗakin ina jin tsoro, can't wait ka samu sauƙi mu bar dajin nan if not Allah mutuwa zan yi, bana iya cin komai se fura da nono fa yaa, kuma basa sa sugar se zuma ni kuma bana so" Ta ƙarashe tana kaiwa kwance gefen sa, kallon ta kawai yayi bece komai ba, to me zece mata, kar tayi bacci? Bayan yasan a halin da take tana buƙatar baccin sosai dan gudun abinda ka iya faruwa da ita. Ya ji daɗi da bata kasance mutum me saka abu a rai ba dan da wata ce ya tabbatar har yanzu ba zata saki ranta ba saboda abinda su kawu suka aikata kuma hakan ze iya sawa ta kamu da ciwon depression Wanda ita ma Kisnahn ya San tana fama dashi ko da ba yawa sedai dole ta damu, her only family turns out to be her worst enemy, abin is not easy at all. Kamar yadda tace kuwa bacci ta shiga yi abin sa yayinda yake zaune Yana tasbihi a ransa, a rana ɗaya fa Allah ya canja musu yanayin rayuwa, yanzu dai dubi da rich, beautiful, sexy and fashionable Kisnah kwance akan gadon kara rabin jikin ta kwance kan tabarmar kaba, wa ce taɓa yadda 8 days back in aka ce masa zata yi rayuwa a irin wannan wajen, waze yarda in akace masa zata saka irin wannan kayan, waze yarda in akace masa her long black silky hair ze yi wannan busu busun ba gyara? Sure life is unpredictable and Allah is the all doer. Rufe nasa idon yayi lokacin da tunanin rayuwar sa ta baya ta faɗo masa, ba iya Kisnah ba shikansa be taɓa kawo rayuwa a irin wannan wajen ba balle har da karaya a left hand da kuwa gocewar ƙashi a ƙafar dama banda ƙananun ciwuka duk da alhamdulillah daga gocewar ƙashin har ciwukan sun warke se karayar hannun da ake fata itama a sami dacewa. Ƙarfe huɗu arɗo ya shigo gida kafaɗar sa saɓe da fatanya hannun sa riƙe da wani duƙunƙunen nan buhu, da sauri Nene dake aikin cura fura ta ajiye ta ƙara sa ga mijin ta ta karɓi buhun hannun sa tana masa sannu da zuwa. Be amsa ta ba seda ya kai zaune bakin bukkar sa kafin ya amsa yana mata sannu da nata aikin, ruwa Bingel ta kawo wa mahaifin ta tare da rufaffiyar ƙwarya da ke cike da damammiyar fura da aka wadata da zuma ta ajiye masa, albarka ya sa mata kafin ya fara zubawa cikin sa furar. Seda ya shanye tas sannan ya miƙe ya ɗau gwangwanayen da suke alwala da zagaya wa dasu ya wuce can bayan bukkokin su da suka ɗan rufa matsayin matsuguni ya rage marar sa kafin ya dawo ya shiga alwala, seda ya gama ze fita Bingel ta tare shi da saƙon lamiɗo "Arɗo, lamiɗo yace kaje faɗa da yammaci". Tsayawa arɗo yayi cikin fargaban dalilin da ze sa ace yaje fada bayan yau ba ranar fadanci bace, juyowa yayi ya dubi ƴar sa sosai kafin ya tambaye ta me ya faru da ake neman sa bayan yasan be aikata kowane laifi ba, take Bingel ta sanar dashi duk abinda ya faru lokacin da suka fita kiwo da Kisnah, shiru arɗo yayi yana tunanin me kiran ke nufi, shi dai yasan yarinyar matar aure ce duk da be tambaye ta ba ko mijin se dai a yanayin da ya tsince su shikam ya gane ma'aurata ne amma kuma tabbas lamiɗo da baffa arɗo kallo ɗaya suka yi wa mace suke gane budurwa ce ko matar aure, sosai dai kan sa ya ɗaure ya kasa fahimta hakan yasa ya fice da niyyar in yayi Sallah ya wuce fada dan jin dalilin kiran. Lamiɗo ɗa ne ga Sarkin ƙauyen Banda (ƙauyen su Bingel) da ake kira baffa arɗo, baffa arɗo Dattijo ne ko ma ace tsoho dan a ƙalla yayi shekara saba'in da wasu ƴan kai, duk cikin ƴaƴan sa ba wanda ya gado shi kwabo da kwabo a kamanni kamar lamiɗo, hakan yasa ya ɗau duk wata soyayya da kulawa ya aza kan lamiɗo da ya kasance auta. Shekaru Ashirin baya aka taɓa samun wani irin annoba da basu taɓa ganin kamar ta ba cikin ƙauyen, gaba ɗaya amfanin gona ya lalace, shanu suka murmutu, ƙoramai da koguna suka bubbushe, tashin hankali ya samu mazauni cikin rayuwar su aka shiga fafutukar neman sauƙi, cikin haka ne suka sami wani malami wai shi wassai da ya buga musu ƙasa sannan ya sanar da su dalilin wannan annoba "Kun yi baƙuwar budurwa garin nan shekara ɗaya baya wanda itace musabbabin wannan annoba dan yarinyar mayyace haka kuma baƙaƙen rauhanan jikin ta sun nemi cutar da rauhanan da suka kafa wannan gari, sanadin wannan faɗa tsakanin su ne ya jawo wannan annoba sedai ina muku albishir da rauhanan mu sun yi nasara kan nata dan yanzu haka ta mutu, sedai akwai sharaɗi, dole duk baƙuwar da zaku yi takasance matar aure, in har kuma budurwa ta shigo dole a mallaka wa lamiɗo ita na tsawon kwana bakwai dan rauhanai sun zaɓe shi matsayin sarkin wannan gari bayan mahaifinsa ya shuɗe, haka kuma zan bashi maganin da yana ganin budurwa ze gane ta da kansa shida baffa arɗo dan gudun yaudara irin ta mutane, dan za'a iya samun wanda ze sauki budurwa kuma yace matar aure ce, hakka ba sabon halayya bace ta ɗan Adam, da ita aka halicce shi". A lokacin ba wanda ya ja da hakan tunda dai ba wai ƴaƴan su mata akace su dinga bayar wa ba haka kuma tun daga lokacin ma babu wanda ya kuma yadda ya sauki baƙuwar budurwa se sau biyu da hakan ya faru kuma duk se da aka aiwatar da sharaɗin boka wassai aka kaiwa lamiɗo su turaka tsawon sati ɗaya kafin ya sallame su......................✍️. Ƙaƙa ƙara ƙaƙa!!!! Wata sabuwa in ji ɗan caca, ga Kisnah ga lamiɗo ga Kuma Saraki, shin me kuke tunani bayan an tabbatar wa da lamiɗo cewa Kisnah budurwa ce? Shin kuna tunanin Saraki ze Bari a mallakawa lamiɗo Kisnah ne na tsawon kwanaki bakwai? Shin kuna tunanin Kisnah da Saraki zasu bar ƙauyen Banda ne ko kuwa?. Ni dai nasan...............ban san komai ba😝😂. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 33 (8/24/2022 10:08 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣3️⃣ *Wannan PAGE ɗin sadaukarwa ne gare ku my best commenters* *Itx_ammin_halimatou* *Maman nabeehat* *Maman Mu'awiyah* *Mom Islam* *Mom misra*. *Amina tijjaney* Zainab Habib* *زينب* *Ihsana* *Real bloom* *Da ma duk wanda ban ambata ba ina godiya da ƙauna, saraki da Kisnah sunce a faɗa muku You Are really amazing and loving* _________________________📖 "Mun sami labarin ka sauke budurwa a gidan ka arɗo, ko za mu iya sanin dalilin hakan?". Da sauri arɗo ya gyara zaman sa yana share zufa da hannun rigar jikin sa da taci datti kamar ba gobe "Allah yai maka tsawan kwana na tsinci wasu matasa biyu mace da namiji kwana takwas da suka wuce, a yanayin da na tsince su suna tsananin buƙatar taimako, a nawa idanun se na ga kamar ma'aurata hakan ne ma yasa na ɗauke su ba tare da wani tunani ba, yanzu haka ita macen ta sami lafiya har ta iya fita jiya shine suka haɗu da lamiɗo, shi kuma namijin yana jinyar karaya ne a hannu duk da cewa hadda gocewar ƙashi a ƙafa amma tuni wanann ya warke, tun ɗazu da aka sanar dani abinda ya faru da har lamiɗo ya nemi na zo fada nasan nayi kuskure, nayi kuskuren ɗaukar matasan matsayin mata da miji haka nayi kuskuren rashin sanar da kai labarin su, a yimin afuwa baffa arɗo, hakan ba zata sake faruwa ba nayi alƙawari". Gyaɗa kai kawai baffa arɗo ya dinga yi har arɗo ya gama bayanin sa kafin ya amsa shi "An maka afuwa arɗo sedai kasan ya zama dole a miƙa wannan budurwa ga lamiɗo yau ɗin nan ba se gobe ba dan kaucewa fushin rauhanai". "Yanzu za ayi hakan baffa arɗo, ina komawa gida zan rakota gare ka se a miƙa ta ga lamiɗo, Allah ƙara tsawon rai ina godiya da sassaucin faɗa gare mu". ****** Cikin rashin daɗin rai arɗo yake taka ƙafar sa kan ƙasa a hanyar sa ta komawa gidan sa, be taɓa sanin yarinyar budurwa bace da baze ɗauko su ba badan komai ba se dan guje mata shiga turakar lamiɗo sedai aikin gama ya riga ya gama dan ba yadda za iya tsallakewa umarnin baffa arɗo da boka wassai, dolen dolen sa ya kai ta ga lamiɗo dan hakan ne zaman lafiyar su daga shi har su. Ko da ya ƙarasa gida zaune ya samu su Bingel da Nenne cikin fargaba, yana shigowa suka bishi da kallo cikin son bayani sedai bece komai ba har Nenne ta kasa daurewa ta tambaye shi da baki, shiru yayi na wasu lokuta kafin ya buɗe baki ya fara musu bayanin abinda ke akwai cikin rashin daɗin rai, fargaban su ce ta ƙaru jin abinda ke faruwa dan Allah ya saka musu ƙaunar Kisnah cikin zuciyoyin su, ba zasu so abu makamancin haka ya faru da ita ba sedai ba yadda zasu yi. Arɗo ya daɗe zaune wajen ƴar sa da matar sa nan ƙofar bukkokin su dake kusa da kusa da juna kafin ya yi ƙarfin halin miƙewa ya shiga ɗakin da Saraki yake dan ya sanar dashi abinda ke faruwa kuma dama Nenne ta sanar dashi Kisnah na tare da Saraki a ɗakin. Da sallamar da ya koyo a birni da yake kai kaya ya shiga ɗakin fuskar sa ɗauke da damuwa ƙarara, da sauri Saraki ya buɗe idanun sa da ya rufe yana kallon shi tare da ƙoƙarin gyara zaman sa "Sannu da shigowa arɗo, sannu da zuwa". Be sami zarafin amsawa Saraki ba ya samu waje ya zauna daga gefen damar Sarakin yayinda Kisnah ke gefen dama, shiru suka yi a ɗakin ba wanda yace komai kafin arɗo ya daure ya tambayi jikin Saraki "Ya jikin naka?. "Da sauƙi arɗo, ina iya motsa hannun ma a hankali baba". "Angodewa Allah, Ina maka fatan samun sauƙi cikin sauri". Da Amin Saraki ya amsa suka sake yin shiru na tsawon lokaci "Kayi haƙuri Ahmad, ban ɗauka za'a sami matsala ba da zaman ku a nan shiyasa ban sanar daku wani abu ba dangane da garin namu sedai gashi wata matsala ta Kunno Kai da tafi ƙarfin magance wa ta, ban san ya zan maku bayanin abinda ya faru ba dan shigowa ta ɗin nan daga gidan baffa arɗo nake wato me garin mu". Zuba masa ido Saraki yayi cikin son matsalar da yake maganar tana son faruwa, fatan sa ɗaya Allah ya sa ba a fitar yarinyar can bane taje ta jawo musu wata maganar, shikam be san ya ze yi da ita ba, in suka bar nan ina zasu je, har yanzu ma basu san takaimaimai a wane garin suke ba su dai sun farka sun gamsu a wannan ƙauyen kuma be wani damu da ya tambayi ina bane tunda ba lafiyar barin garin gare shi ba. "A shekarun baya munyi fama da wata annoba sanadin wata budurwa mayya da ta shigo mana, a cikin neman masu maganin da muke ne Allah ya kawo wassai garin nan da ya zama sanadin samun sauƙin al'amuran har muka dawo muka cigaba da rayuwa kamar da sedai ya kafa mana wasu sharuɗa da muke rayuwa a wannan ƙauyen akan su, sharaɗin shine ba karɓi baƙuncin budurwa mara aure ba in kuwa hakan ya faru to za mu miƙa ta ga Sarkin gobe lamiɗo auta ga Sarkin yanzu ya tare da ita a turakar sa na tsawon sati ɗaya. Kayi haƙuri a lokacin da na tsince ku na yi zaton mata da miji ne shiyasa ban ji ko ɗar ba na ɗauko ku zuwa wannan garin, a fitar da yarinyar tayi jiya suka haɗu da lamiɗo kuma ya gane budurwa ce ba matar aure ba saboda wassai ya basu maganin da zasu dinga gane budurwa da matar aure shi da baffa arɗo dan gudun yaudara, yanzu haka baffa arɗo da lamiɗo suna jira ne na miƙa wannan yarinya ga turakar lamiɗo a yau, shine nazo na sanar da ku". Kallon sa kawai saraki yake yana fassara dukkan bayanin sa tare da miƙa shi matatar bayanai wanda cikin lokaci kaɗan ya fahimci me arɗon yake nufi, in akace tashin hankali to kaɗan kenan, taya ze yarda haka ya faru? Ta ina ze iya zuba ido har hakan ta kasance? To meye ma amfanin guduwar su daga waɗancan makasan, meye banbancin wannan sharaɗin da bindiga hannun ƴan ta'addar kawu, in hakane ma gwara da ace tsayawa yayi aka kashe su gaba ɗaya, a ganin sa waccan mutuwar ma tafi sauƙi kan wannan batu dan mutuwar tsaye ne kawai. A hankali ya juya ya dubi inda take kwance tana bacci peacefully, baccin da kana gani zaka san ta kwana biyu bata samu irin shi ba. Dawo da duban sa yayi ga arɗo dake zaune ya duƙar da kai ƙasa, abubuwa da yawa ke zuwa ransa sedai ya rasa wanne ze yi, me ze yi da zai cece ta, ya sani baze yiwu yace zasu bar garin ba dan bashi da isasshiyar lafiyar tafiya dan har yanzu ba wai hana taka ƙafar sa bane an dai kunce ɗaurin ne, to idan ma zasu tafi ina zasu nufa su da basu san a ina suke ba haka kuɗi fa, su da basu da ko sisi dame zasu tafi, dole ya ajiye ma wannan batun dan ba mafita bace. "Yanzu babu wata mafita ga hakan arɗo dan bana tunanin zan iya yadda da wannan sharaɗin na garin ku". Girgiza kai arɗo yayi cikin son tabbatar wa "Kayi haƙuri samari amma babu wata mafita se hakan". Sake yin shiru suka yi ya rufe idanun sa cikin karanto duk addu'ar da ta zo bakin sa, fatan sa Allah ya bashi wata mafita da zata kange wannan matsalar dake neman kutso kai rayuwar su banda kuma wadda suke ciki. Tunani yake yi sosai har yayi zurfin da be san lokacin da arɗo ya tashi Kisnah ba, ƙoƙarin fita da suke yi ita da arɗo ya sa ya farga haka kuma a lokacin ya yanke shawarar da yake ganin ita kaɗai zata kore wannan musiba dake neman danno kai gare su, da sauri ya dakatar da arɗo dake neman bin bayan Kisnah da ta riga ta fita "Zan je fada arɗo, Ina son na biku dan Allah". Tsayawa arɗo yayi cikin ɗan ƙure shi da kallo kafin ya girgiza kai "Ta ina zaka iya bin mu Ahmad, har yanzu ba wai ƙafar ka ta gama lafiya bane". "Kayi haƙuri amma dole na biku bana, akwai abinda nake san sanar da Sarkin ku". Ganin ya dage yasa arɗo nemo me amalanke ya biya shi sannan suka kama Saraki suka taimaka masa ya shiga kafin shima da Kisnah suka shiga me amalanken ya ja, tsakanin su da gidan Sarkin akwai tafiya sosai sedai gare su ba wata tafiya bace, rashin lafiyar Saraki yasa ya biya amalanke da da ƙafar su zasu taka su je. A ƙofar fada suka sauka nan ma arɗo da me amalanke ne suka taimaka wa Saraki zuwa cikin fadar Kisnah na bin su tana ƙare wa gurin kallo. Ginin ƙasa ne gaba ɗaya ba kamar nasu dake da su asabari da yayi ba, ƙaton fili ne da aka ahimfiɗe shi da tabarmin kaba se daga can nisa bukkokin iyalin sa suke an zagaye wajen da asabari. Zaunar da Saraki suka yi me amalanke yayi gaisuwa ya fita waje yana jiran su gama ya mayar dasu dan kuɗin zuwa da komawa arɗo ya biya, Hausar da sarki suka yi kafin arɗo ya shiga yiwa sarki bayani "Gasu nan baffa arɗo, su ne matasan da na tsinta, ga macen da lamiɗo ya gani ga kuma namijin nan". Kallon su ɗaya bayan ɗaya baffa arɗo yayi kafin ya aika aka shiga cikin gida kira masa lamiɗo, ba jimawa ɗan aiken ya dawo tare da lamiɗon da tun da ya shigo idanun sa na kan Kisnah yana Binta da wani mayen kallo saboda yadda jikin ta yake luƙwi luƙwi ba alamun rama ga laushin da ya san fatar ta zata yi uwa uba ga diri, duk gaisuwar da suka masa hankalin sa baya gare su ya amsa sa'annan ya kai zaune gefen baban sa. "Kije gare shi yarinya, zaki kasance dashi a turaka na kwana bakwai". Arɗo ne ya fassara musu abinda baffa arɗo ya faɗa dan su ba jin Yaren su ke ba sedai shi baffa arɗo yana jin Hausa mayarwa ne ba ya iya yi, wani kallon rainin hankali Kisnah tayi musu sedai kafin ta buɗe baki ta faɗi abinda tayi niyya Saraki ya riga ta "Allah ya ƙara masa tsawon rai wannan yarinya da ake magana a kanta tana amsa sunan matata ne dan kafin mu sami hatsarin da yayi silar shigowar mu garin ku an riga na biya sadaki da komai na aure kawai ana jiran lokaci ne se wannan ƙaddarar ta afku". Da wani irin sauri Kisnah ta juya gare shi tana kallon shi baki buɗe ido zare sedai tunda ya fara magana yawun bakin ta suka ƙafe hakan yasa ta kasa furta komi se bin shi da kallo shikan ƙin kallon ɓangaren da take yayi dan yana jin yawon idanun ta a cikin jikin sa, shima ba a san ran sa ze Fadi hakan ba sedai ba yadda za yi wannan ce kaɗai mafitar da yake hasashen zata hana faruwar abinda ke gab da aukuwa. Gyara zama baffa arɗo yayi yayinda lamiɗo ya ɗago da sauri yana aikawa Saraki mugun kallo da ƙananun idanun sa Magana baffa arɗo yayi cikin Yaren su yayinda arɗo ya ke fassara musu "Baffa arɗo yace in dai haka ne to sedai su baka zaɓi biyu kuma dole ka zaɓi ɗaya a ciki ka yarda?". Gyaɗa kai Saraki yayi duk da be san wane irin zaɓi bane amma ya tabbatar ze samu na ɗauka a ciki insha Allah "Yace ko ka yarda a ɗaura muku aure yanzu a nan dan mu dole haka sharaɗin mu yake budurwa bata zama mana se ta kwanta da lamiɗo ko kuma in ba zaka aure ta yanzu ba to tabbas lamiɗo ze wuce da ita". Arɗo ya ƙare fassara wa Sarakin yana bin shi da kallo dan jin wanne ya zaɓa. "La'iha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimeen". Addu'ar da saraki ya shiga maimaita wa kenan cikin ransa dan tabbas yana cikin tsaka me wuya da dole ya nemi taimakon Ubangiji. "Kayi shiru yaro, ka amsa mana da abinda ka zaɓa dan Musan abinda ya dace a yi. Bashi da zaɓi da ya wuce buɗe bakin sa yayi magana, a lokacin, a lokacin ne kuma ƙaddara ta buɗe sabon shafi a rayuwar sa, shafin da be san da wani irin suna ze Kira shi ba abu ɗaya ya sani shine ƙaddara ke juya rayuwar sa a lokacin kuma bashi da wani zaɓi illa ya bata dama tayi duk yadda taso dashi da rayuwar tasa. ******** Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke yana me runtse idanun sa, bit by bit ya shiga tuno rayuwar sa tunda ga yarinta, zaman sa da mahaifiyar sa da irin so, ƙauna da shaƙuwar dake tsakanin su, ƙannen sa da halin kowanne a ciki, tafiyar sa karatu ƙasar waje, rayuwar sa a ƙasar da ba tasa ba, gama karatun sa da fara aikin sa zuwa dawowar sa, farin cikin da ya kasance a ciki na zama tsakanin iyayen sa da suke so da ƙaunar sa ga kuma ƙannen sa masu biyayya gare shi, Laylah da irin son da take nuna masa duk da ya nuna be gane ba, yarinyar da ban da yau be sake tuna ta an tun da ya baro masarauta dan je has no feelings for her ko kaɗan, shigowar Husna masarautar da kuma yadda ƙaddara ta fara nata sharafin da rayuwar sa, shigowar sa garin manya, haɗuwar sa da idriss, zaman sa kantin Alh Musa, shigowar Kisnah rayuwar sa ko shigar sa rayuwar ta ze ce, yarinyar da be san da me ze kwatanta haɗin da ƙaddara tayi musu ba, abu ɗaya za iya cewa shine ya ɗauke ta kamar Miemie ƙanwar sa ne, kulawa da kariyar da yake bata duk domin wancan matsayin ne se gashi lokaci ɗaya ƙaddara ta yi juyin masa da wancan matsayin ta bata wani matsayi da be shirya masa ba a yanzu, matsayin da yake ganin bata dace dashi ba haka kuma matsayin da be san da wane ido zasu dinga kallon juna dashi ba domin sa. Wani irin nauyi yake ji a ransa da baya tantama nauyin bana komai bane se na gungumemen kayan da aka aza masa a kai, taya ze iya fara riƙe ta, da me ze kula da ita, be shirya ba , sam be shirya ba, ba tsarin sa kenan ba, ba lissafin sa ba kenan haka kuma a tanadin sa bane hakan. Abinda saraki ya manta shine ita ƙaddara ba ruwan ta da tsarin sa, shirin sa, tanadin sa, lissafin sa ko burin sa...................! "Alhamdulillah, aure tsakanin Ahmad da Sakeenah ya ƙullu, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba ya tabbatar da kasancewar ku tare har abada". Kalaman limamin ke ta maimaita kansa a kunnen sa haka kuma idan har ba mantawa yayi ba a lokacin kalmar *Ameen* ta suɓuce daga bakin sa wanda ba ita yayi niyyar furtawa ba har zuciyar sa sedai be san me yasa harshen sa ya canja masa akala ba. A hankali ya juyar da kansa yana ƙare wa sabuwar bukkar da aka canja musu kallo wadda aikin baffa arɗo bane, sannu a hankali yana yawatawa da idanun sa cikin bukkar har idanun sa ya faɗa kanta, ita ɗin dai da komai yake faruwa sanadin ta, ita ɗin dai da ta yi sanadin buɗe sabon babi wa rayuwar sa rayuwar sa, bacci take, bacci fa bayan shi gashi nan ya kasa ko da runtsa idanun sa a dalilin ta kuma a sanadin kare ta. Haka Saraki ya ɓata daren da ya kasance daren auren su cikin tsananin tunani, tunanin mafita game da wannan bahaguwar ƙaddarar tasu, tunanin mafita kan wannan auren nasu da be san da tunanin da ze kira shi ba, be samu sauƙin nauyin da zuciyar sa tayi ba seda ya samo *mafita*, mafitar da yake ganin itace daidai kuma abinda ya dace. Sake kallon wajen da take kwance yayi yana watsa mata zazzafar harara ganin yadda take bacci hankali kwance batare da ta damu dashi wane halin yake ciki ba a sanadin ta...........................✍️. Wihuhu🤸🤸🤸🤸🤸 anzo wajen 💃💃 wallahi anzo💃💃💃. Saraki ya zama na Kisnah Kisnah ta zama ta Saraki 💃💃💃💃. 🎶🎵Ai wannan bikin gidan mu neeee🎶🎵 🎵🎶Ɗaurin auren yayan mu neeee🎵🎶. Ku zo mu taka team #sarakisna. 🎶💃biki yayi biki ashe da dangi muka kuriiii🎶 matan garin mu ba'a nuna musu komai💃💃💃 🎵🎵Daga munji ɗan kiɗan sa se rawa, sama mata💃💃. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 34 (8/25/2022 9:56 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣4️⃣ ________________________📖 Hasken da ya ratso ta tsakankanin asabarin ɗakin ya haske masa fuska yasa ya fara motsa idanun sa a hankali har ya buɗe su gaba ɗaya, kallon ɗakin ya shiga yi kafin ya zabura cikin son miƙewa sedai tuni ya koma saboda zugin da ya ratsa hannun sa ya kai tsakiyar kansa. Seda ya ɗan yi mintuna a kwance kafin ya yunƙura ya zauna a dabarance, hasken da ya shigo ta duk wata kafa ta jikin asabarin ya tabbatar masa da gari ya daɗe da waye wa har rana ta fito gashi ko sallah be yi ba, takaici ne ya kama shi dan baze iya tuna yaushe ya makara sallar asuba ba, haushin sa ya fi ta'alkaƙa ne kan rashin baccin sa da wuri ne ya ja masa makarar wadda duk sanadin tunanin mafitar wannan ƙaddararren auren da aka ɗaura masa jiya ne. Duban gefen da yasan take kwance yayi ya ga bata nan, kenan ta tashi ita tayi sallah amma shine ko ta tashe shi, ƙwafa yayi yana me jin zafin hakan a ransa. Daga zaunen da yake yayi gyaran murya cikin babban sauti dan haka yake yi se arɗo ya shigo ya taimaka masa zuwa matsuguni kafin ya dawo dashi yayi alwala. Nenne da ke zaune tare da Kisnah tana taya ta mulmula furar da take curawa wadda sana'ar tace ta juyo gyaran muryar Saraki hakan yasa ta dubi Kisnah da ta maida hankalin ta kan furar gaba ɗaya "Tashi yalo mijin ka na kila". Tsayawa da abinda take Kisnah tayi ta shiga kallon ta dan bata fahimci me take cewa ba, sake maimaita wa Nenne tayi amma ita bata gane komai ba se miji kawai, seda ta nuna bukkar su tana sake maimaita mata daidai lokacin kuma da Saraki ya sake yin wata gyaran muryar kafin ta gane me take nufi. Miƙewa tayi da sauri ta ƙarasa bukkar tare da shigewa dan tun ɗazu take cikin jimiamin rashin farkawar tasa kasancewar tun da suka zo ƙauyen ya farfaɗo bata taɓa ganin yayi nauyin bacci irin wannan ba. Bata lura da kallon da yake mata ba ta ƙarasa gaban gadon karar da yake kwance ta kai zaune "Yaa lafiya kuwa yau irin wannan bacci haka, Allah har kasa hankali na ya tashi". Ko kallon ta be yi ba ya sake yin gyaran murya shi a dole yana neman arɗo "Yaa arɗo fa baya nan, yau tun sassafe ya fita gona, ya shigo baka tashi ba so se ya tafi". Se a lokacin ya kalle ta, arɗo baya nan to wa ze taimaka masa yau gashi yana son zagayawa dan fitsari yake ji saboda magungunan da baffa arɗo ya bashi ya sha a can da kuma wanda ya taho dasu yasha kafin ya kwanta. "Bari in kawo maka ruwa kayi alwala se kayi sallah". Ta faɗa tana miƙewa zata fita, da sauri ya tsayar da ita dan ji yake kamar marar sa zata yi bombing "Zan yi fitsari tukunna". Tsayawa tayi tare da juyowa ta kalle shi, ze yi fitsari tabɗin, to ita yaya zata yi mishi ga baffa baya nan. "Bari in faɗa wa Nenne in ji ko za'a sami wani da zai taimaka maka to". Wani banzan kallo ya watsa mata jin wani wai se ya tsaya an samo wanda ze taimaka masa, kawai tace so take ya saki fitsarin a nan mana "Malama in zaki zo ki taimaka min na je bayi ki zo in Kuma ba so kike na sake shi a jiki na ba, salon gulma kawai". Dariya ce ta ciyo ta ba kaɗan ba ganin yadda yake magana yana ɓaɓɓata fuska at the same time yana mutsu mustu da alamu dai da gaske fitsarin ya matse shin. Gaban gadon ta matsa tare da miƙa masa hannun ta, se ya gama hararar hannun kafin ya kama da nashi ya fara ƙoƙarin miƙewa ita kuma ta saka ɗayan hannun ta tallafe nasa me ciwon, da ƙyar ya samu ya iya miƙewa dan ba wani ƙwari gare ta ba har kusan faɗo masa tayi. A hankali yake taka ƙafar sa me ciwon yana bada ƙarfin sa ga mara ciwon ita kuma ta saƙalo hannun ta a ƙugun sa yasa hannun sa me lafiya ya zagaye wuyan ta har suka ƙara sa wani ɗan ƙaramin sabon makewayin da aka yi musu shi jiya wanda duk aikin baffa arɗo ne, ba kamar nasu arɗo ba nasu ginin jar ƙasa ne gaba ɗaya se asabarin da aka rufe saman dashi haka kuma a gefen bukkar su aka yi shi da ke da ɗan nisa da tasu Nenne. Se da ta shigar dashi banɗakin kafin ta fita bayan ya zauna kan wani ƙaton dutse dake ciki sannan ta koma ta zubo masa ruwa a gwangwani ta tura masa ta koma gefe tana jiran sa. Ɗan gyaran muryar da yayi ya shaida mata ya gama dan haka ta shiga ta kama shi suka fito se wani hahhaɗe rai yake kamar wanda aka doka ko aka zage shi, se da ya zauna sosai kan gadon sa kafin ta kalle shi cikin tsokana "Yaa ya Zamuyi ina kashi ya matse ka kuma baffa baya nan?". Ta faɗa tana saka yatsa a baki irin wai tana tunanin kamar dai yadda yara suke yi, kunya ce ta kama Saraki ganin yadda yarinya ƙarama take neman raina shi, dariya tayi ganin yadda ya sake matse fuska kafin kuma ta haɗiye kayar ta saboda mugun kallon da ya jefa mata "Am sorry Yaa, Kai ne kake ta wani haɗe rai bayan fitsari kawai kayi kuma ai nima ina yi ba, to meye abin ma damuwar bari in kawo maka ruwan alwalar". Tana faɗa ta fice da sauri fuskar ta ɗauke da murmushi dan Allah ya sani ya bata dariya ba kaɗan ba. Inda yake zaune ta kawo ƙatuwar ƙwaryar da yake alwala a ciki tare da wani gwangwanin cike da ruwa, a hankali ya matsa bakin gadon ya tara hannun sa ta shiga zuba masa ruwan yana alwala, yana gamawa ta ɗauka ta fice dashi ta zubar kana ta dawo ɗakin, ganin yana Sallah ta juya ta fita wajen Nenne. Ko zama bata yi ba Nenne ta tura mata madaidaiciyar ƙwarya rufe da faifai tare da mata alamun ta kaiwa Saraki, ɗauka tayi ta koma bukkar su inda ta tarar ya idar yana zaune yana azkhar, ajiye masa tayi tare da neman guri ta zauna nan kusa da shi, tana zaune ya ƙarasa azkhar ɗin tare da yin addu'a sannan ya dube ta "Meye kuma?". Da ido ta nuna masa ƙwaryar da ta ajiye a gefen sa "Nenne tace in kawo maka". "Bakin kawo ba, to me kuma kika tsaya jira". Kwaɓe fuska tayi tana fatan Allah yasa ya yarda dan ita fa bata ƙoshi ba, su Fulani haka suke da ƙauron hannu, ƴar fura da nonon ma da za'a bata ba za'a bata a wadace ba kamar ta wani roƙa. "Rage min zaka yi Please Yaa, Allah Ni kam ban ƙoshi ba". Bece mata komai ba ya miƙa hannun sa na hagu da yake da lafiya ya ɗau ƙwaryar tare da buɗe wa ya ɗau ludayin ciki ya ɗebo ze Kai Baki se kuma.ya dakata yana kallon ƙwaryar da hannun sa, a jiye ludayin yayi ya zubawa furar ido kafin ya ɗago ya kalli Kisnah dake zaune tana bin shi da kallo, shi kam Allah ya jarrabe shi a kwanakin nan, hannun dama a karye ko da wanne ze ci abinci yau oho, dama arɗo ke zama ya bashi gashi kuma yau baya nan. "Lafiya yaa, ko hannun ne yake ciwo?, Ka fama ƙafar ka ne?". Ta jero masa tambayoyin ganin yadda ya tsaya yana kallon ƙwaryar hannun sa kamar me neman wani abu a ciki, be amsa ta ba se ƙwaryar da ya miƙa mata ta sa hannu ta karɓa kafin ta juyo Muryar sa very low "Feed me". Ɗan zaro ido tayi tana buɗe baki, ganin abinda yayi yasa shima ya zaro mata nasa kyawawan idanun "Hannun dama na akwai ciwo I can't eat or drink with left hand, is haram in Islam, so Mrs is not as you think". Ya ƙarashe yana tsuke baki kamar ƙaramin yaro abin kuwa ba ƙaramin burge Kisnah yayi ba, hannu ta sa ta dafe bakin preventing herself bursting into laughter. Gyaɗa kai tayi tare da ɗaukar ludayin ta ɗebo furar tare da nufar bakin sa saying "Haaa, oya buɗe bakin". Seda ya harare ta kafin ya buɗe bakin sa ta saka masa ya shiga sha, ɗebo wa tayi ta kai bakin ta itama ta sha tana lumshe ido dan se taji kamar tasa ta fi daɗi kan wadda aka bata, sanin neman magana take yasa be ko kalle ta balle yayi mata maganar sha masa da take yi. Haka suka cigaba da sha su biyu, in ta bashi ta bawa kanta har suka shanye kafin ta sa harshe ta lashe lips ɗin ta, da sauri Saraki ya kawar da kai ganin abinda take yi ya nemo wani ɗan tsumma a gefe ya goge bakin sa kafin ya jingina jikin jan bangon su. Fita tayi da ƙwayar ta ajiye kana ta dawo da maganin sa da Nenne ta bata ta kawo masa, be yi musu ba ya karɓa yasha ya koma ya jingina yadda yake kafin ta kawo maganin ya rufe idanun sa ya shiga tunani, shikam ya gaji da zaman nan da yake yi waje ɗaya, gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa saboda zaman ga kuma son barin garin da yake yi saboda yanayin cimar su da kuma wajen zaman su, yasani ciwon jikin sa baya rasa nasaba da kwanciya kan gadon karar da yake yi kullum ga kuma wuni zaune waje ɗaya, taya jikin sa baze yi ciwo ba. Abincin su, hmmm wani daban shima kenan, be ga laifin Kisnah ba da tace ba zata iya cin komai na cimar su ba se fura da nono wanda dama shi ne main food ɗin su, se ku ganyayyaki, zogale, rama, kai abubuwa dai da bai taɓa sanin akwai su ba balle ya san sunan su, bawai ya raina musu bane ba, ya sani suna iya ƙoƙarin su wajen kula dasu, ko ɗauko su da arɗo yayi wani abu ne dan a yadda yanzu duniya ta lalace ba kowa ne ze iya kasadar ɗaukar su ba batare da yasan ko su waye su ba, mugaye ne ko mutanen kirki, kawai dai basu saba da wanann yanayin rayuwar ba adopting ɗin shi cikin sauƙi abu ne me wuya a gare su, addu'ar sa ɗaya Allah ya bashi lafiya da gaggawa su bar garin dan ko a wajen shi ba'a samu matsala ba ya tabbatar a wajen ta se an samu. Nauyin da yaji a ɓarin hangun sa yasa ya buɗe ido yana kai duban sa wajen, itace kwance a jikin sa kan ta a gefen kafaɗar sa ragowar jikin ta kan gadon shi tana bacci, sosai yake mamakin saurin baccin da take yi yanzu sedai daga baya ya dena, to in bata yi bacci ba me zata yi, ita ba waya ba balle ta danna, ita ba abokin fira ba gashi tun jiya ya gargaɗe ta da kar ta kuma fita, dole kuwa ta yi bacci ai. Zame ta yayi ya kwantar ya cigaba da tunanin sa har be san lokacin da shima baccin ya ɗauke shi ba. Muryar Nenne dake ta magana a bakin ƙafa ya farkar dashi dan bashi da nauyin bacci, motsawa yayi yana gyara zaman sa tare da yamutsa fuska jin hannun ya sake saboda nauyin da ya bashi da yana bacci, gyaran murya yayi saboda har lokacin Nenne bata dena magana ba, ajiye kwanon hannun ta tayi tana faɗin "Nashe ga nan abinshin ku bakin danga". Da toh ya amsa mata dan ya gane me take son cewa, ga abincin su nan a bakin ƙafa, hannu yasa ya shiga bubbuga kafaɗar Kisnah dake kwance dan taje ta ɗauko kwanon da Nennen ta ajiye, buɗe idanun ta da suka sauya kala saboda bacci tayi a kansa tana bin sa da su dan son jin dalilin tashin ta "Ki tashi ki ɗauko kwano ga shi can bakin ƙofa and ki duba min kamar lokacin Sallah yayi". Zaune ta miƙe tana yin miƙar da ta sa Saraki kau da kan sa da sauri ganin fitsarar da take yi gaban sa ba ko kunya, se da tayi son ranta kafin ta miƙe tana tafiya a sanyaye ta ɗauko kwanon ta dawo ta ajiye sannan ta fita, gwangwani ta ɗauka ta ɗauraye bakin ta sannan ta shiga bukkar Nenne dan ta gama cure furar ta shiga ɗaki. "Lokacin sallah yayi Nenne?". Gyaɗa mata kai Nenne tayi tana mata murmushi itama ta maida mata tare da fita zuwa tasu bukkar ko ɗaki zata ce dan dai tasu ginin ƙasa ne gaba dayan ta se asabari a sama da aka rufe saman dashi. Gaban shi ta zauna tana ɗan jingina jikin kafaɗar sa dan jikin ta ba wani ƙwari saboda baccin da tayi, ture ta yayi daga jikin sa hakan yasa ta shiga ƙunƙuni ƙasa ƙasa, haɗa idon da suka yi yasa ta kwaɓe fuska "Ai dai ba abinda nace". "Buɗe kwanon nan". Matsawa tayi gaban akushin da ke ajiye ta buɗe shi, yamutsa fuska tayi ganin abinda ke ciki kafin ta maida ta rufe, kallon shi tayi tana faɗa masa me ke ciki ganin yadda ya bita da kallo................................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 35 (8/25/2022 9:57 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣5️⃣ _________________________📖 kallon kwanon yayi ya kuma kallon ta yana tunani me ye something atrocious ɗin da tace, "In gani". Matsar da kwanon tayi gaban sa yasa hannu ya buɗe, zubawa zogalen da yasha haɗi yaji ƙuli ƙuli yayi kyau ido yayi, so this is something atrocious a wajen ta kenan, ɗago wa yayi ya dube ta se kallon sa take tana ɓata fuska, miƙa mata kwanon yai ta karɓa tana neman rufewa ya tare ta "Bani naci". Zaro ido tayi waje jin abinda yace, shin be ga meke cikin kwanon bane da zece ta bashi, ko kuwa dan yana jin yunwa ze ci, in kuwa hakane yanzu zata je ta maida wa Nenne su dai kawai a basu furar su sha. "Yunwa kake ji ko yaa, bari na maida mata abin nan nace a bamu fura kaji, dama nasan kaima bazaka iya cin wannan trash ɗin ba". Dakatar da ita yayi daga fitar da zata yi "Wannan ɗin nake son ci, in ke a wajen ki trash ne to ni a wajena yafi ye min all that luxurious dishes, ko kin manta da background ɗina ne, being with you doesn't make me as you, you're rich and am not, you're from a high class family and am from from a middle class family, so you go and get the fura, as for me this is what I want but don't forget we have no any relation with these people, they're only helping and yet they are trying their best with all they have, if you won't appreciate it I think you shouldn't curse it". Cak ta tsaya a inda take tana sauraren sa, sosai jikin ta yayi sanyi da kalaman sa, 2 mins back ba taga aibu a cikin maida zogalen ba amma yanzu kam da ya faɗa mata wannan words ɗin se taji sam bata kyauta ba, ta sani wannan shine cimar su and shine abinda suka basu, in ta koma tace a canja is like ta Raina musu, bata gode ba kuma ta raina wa ƙoƙarin su. A hankali ta dawo ta zauna in da ta tashi ta saka hannun ta ta ɗebo zuwa bakin sa, buɗe wa yayi ta saka masa ya shiga taunawa knowing ba zata ci ba sedai ga mamakin sa she feed herself also kuma duk yadda taso ganin wani baƙon reaction akan abinda bata saba ci ba be gani ba dan bata nuna masa komai ba ta shiga taunawa har ta haɗiye though deeo down tana dannewa ne amma ji take kamar tayi amai. Haka suka cinye zogalen tass kafin ta ɗebo masa ruwa yasha ya kuma yi alwala, kallon ta yayi lokacin da ta koma ta zauna, fasa tada sallar yayi ya dube ta "Ke ba zaki yi sallar bane?". "Zanyi da magrib". Ba abin mamaki bane a wajen sa jin hakan daga gare ta sedai abin haushi ne dan be manta not more than 10 days back da suke tare a Company yana ƙoƙarin saka ta yin Sallah a kan lokaci duk in lokaci yayi amma shine har zata ce masa wai zata yi da magrib, a yanda ya ke ji kaman ya rufe ta da duka wallahi se dai Allah ya taimake ta hannun sa be da lafiya "You get up go and pray ko se ranki ya ɓaci, mara hankali kawai". Tun tsawan da ya daka mata tayi wuff ta fice daga ɗakin sedai jin last word ɗin da ya faɗa ya mata ciwo, itace mara hankali, mara hankali fa ya kirata, is he in his right sense kuwa ko ko dan bata nuna masa kalar ta bane, ko kuwa gaskiyar Hameedah ne ta sake masa da yawa, aikuwa in haka ne ze san da ita yake wallahi. Cikin ɓacin rai tayi alwalar ta koma bukkar su ta yafa wani baƙin saƙi da Nenne ta bata wai mayafi tayi sallar, tana idarwa ta matsa can gefe ta zauna ya shiga tunani, tunanin iyayen ta dama rayuwar ta gaba ɗaya! *SAKEENA SAFWAN* Sunan mahaifin ta Alh Safwan Yaƙoub, asalin su mutanen ƙasar Congo ne dake maƙwabtaka da tasu, cirani ya kawo shi ƙasar Hawarya inda ya bar ƙanin sa ɗaya tal da yake dashi a can gida Congo, mahaifin su Safwan wato Yaƙoub manomi ne me ƙaramin ƙarfi wanda yake da mata biyu, A'i da suke kira Inna se kuma Inna lami da ainahin sunan ta Sakeena ne. Inna A'i ita ce mata ta farko wajen Malam Yaƙoub da aka yi masa auren ladan noma da ita, shekara huɗu da auren amma bata taɓa ko ɓarin wata ba balle a yi batun haihuwa hakan yasa iyayen Malam Yaƙoub sake nemo masa auren Sakeena wato ladi. Shekarar farko ta auren bata ƙare ba se da ciki jikin ladi, wata goma cif cif ta haifi ɗan ta namiji, sati na zagayowa kuwa aka raɗa masa suna Safwan, Safwan na isa yaye Inna A'i ta karɓe shi daga hannun ladi ta cigaba da rainon sa cikin tsananin soyayya. Shekarar Safwan uku Allah ya azurta Inna A'i da samun nata rabon wanda ba ƙaramin murna ladi da malam Yaƙoub suka yi ba, aka raini ciki cikin tsananin kulawa har zuwa haihuwar sa itama ta haifi nata namiji yaci suna Sama'ila da sati ya zagayo. Haihuwar Sama'ila yasa malam Yaƙoub maida wa ladi Safwan ganin babu ɗa ko ɗaya a wajen ta ita, a wannan shekarar kuma Inna ladi ta yi ɓaci har so huɗu d hakan ya tasar wa da malam Yaƙoub hankali aka shiga neman magani. Ciki na biyar ɗin da aka samu kuwa ya zauna da taimakon Ubangiji sedai ko da aika haife shi be zo da rai ba, bayan wannan se da ta sake yin biyu suma suna mutuwa kafin haihuwar ta tsaya gaba ɗaya. Safwan da Sama'ila sun tashi tare duk da kana ganin Safwan zaka san shine gaba da Sama'ila dan gaba ɗaya ya gado malam Yaƙoub wajen ƙirar jiki irin ta cikakkun jaruman maza yayinda a kamannin fuska kuwa ya haɗe kamannin iyayen biyu hakan ya sa ya tashi da tsananin kyau dan duk iyayen sa ba baya. Sama'ila a nasa ɓangaren shima kyakkyawa ne duk da shi mahaifiyar sa ya gado, tun a yarintar su Safwan mutum ne meson neman na kansa yayinda Sama'ila ya kasance me son jiki wanda hakan ne yasa basa shiri sam da mahaifin sa malam Yaƙoub dan in Safwan ya damƙi aikin gona abin se sam barka yayinda Sama'ila ze yi kwance a ɗaki ko ya tafi wajen matasa tsaran sa wasa. A haka rayuwa tayi ta tafiya har Allah ya ɗauki ran Inna ladi lokacin haihuwa dan ta sami wani cikin daga baya, cikin alhini aka yi mata sutura aka kaita makwancin ta rayuwa ta cigaba da tafiya har lokacin da suka zama samari. Lokacin ne kuma Safwan ya hana baban su Malam Yaƙoub zuwa gona shi ya cigaba da yin noman suna samun abin da zasu ci har ma su siyar da wasu su sami kuɗin ɓatar wa. Kwatsam wata rana Malam Yaƙoub ya tafi gona wai duba aikin Safwan, dake aka cein ajali yayi kira dole a amsa, a gonar wani baƙin miciji ya sari malam Yaƙoub da yayi sanadin ran sa dan kafin a man gan shi har rai yayi halin sa. Wannan mutuwa ta malam Yaƙoub ya saka Inna A'i da ƴaƴan sa su Sama'ila cikin tashin hankali, sedai dole haka ba yadda suka iya su ka saka haƙuri da dangana cikin ran su suka cigaba da rayuwa, sedai kuma lafiya tayi wa Inna A'i ƙaranci dan haka take yau lafiya gobe babu, tsananin son abin duniya da buri da ya nuna kan sa cikin halayyar da rayuwar ɗan ta Sama'ila ya sa kullum cikin yi masa nasiha take da bashi misali da ɗan uwan sa sedai dake yayi nisa sam baya jin kira sedai ya amsa mata da toh kurum amma ba abin da ya fasa, shine yau satar akuya, satar kaza gobe damfara kai abu dai iri iri. Ana haka ne kuma itama aka wayi gari babu Inna A'i, bayan rasuwar ta ne aka yi rabon gado inda Safwan ya haɗe kan kuɗaɗen sa ya shiga duniya cirani bayan ya bar amanar gonar sa da ya shuka auduga hannun wani abokin baffan sa Malam yaƙoub. Ƙasar Hawarya garin Manya nan ne malam yaƙoub ya yada zango inda ya shiga fafutuka da ɗan abinda yake hannun sa, shoe shiner, yalo, kayan miya duk malam Safwan ya sai da har yazo ya sami aikin gadi a wani babban Companyn sayar da auduga. Rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a haka yana aikin sa yana kuma leƙa gida in ya sami fama, amfanin gonar sa kuwa a can yake saidai wa ya biya ma'aikata da suka kula da ita ya kuma san wa Malam Umaru abokin baban sa wani abu har zuwa lokacin da yaji wasu mutane na batun ai masu Company suna neman audugar da zasu siya amma kwana biyu wahala take yi dan wadda aka samu baya da wata yawa, jiki na rawa Safwan ya yake bawa ma'aikacin da ya kawo masa labarin batun tasa audugar da yake nomawa, mutumin be yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar da ɗaya daga cikin manyan ma'aikatan batun Malam Safwan, aikuwa cikin kwana uku suka haɗa committee aka je da malam Safwan aka gano gonar, sosai suka yi farin ciki da ganin noman sa dan duk cikin wadda aka samu ɗin ba wadda ta kai ta Malam Safwan kyau da yawa, take suka siye ta a tsaye suka bashi kuɗin. Wannan kuɗaɗe su sukayi sanadin barin Safwan harkar gadi ya tarkata kuɗin sa ya koma gida ya shiga noman auduga haiƙan bayan ya ƙara siyen manyan gonaki har biyu ya adana ragowar kuɗin sa cikin banki. Noman auduga fa ya karɓi Safwan dan har rige rigen siya ake tsakanin manyan kamfanoni dan yana bayar da ita da sauƙi ga kuma kyau da take da, sannu sannu gonakin Safwan suka yi yawa dan ya shiga sahun masu yawan gonaki a garin su yayinda Sama'ila ya na can yabi abokai yawon holewa da kuɗin gadon sa. Kuɗi da sun fara zauna wa Safwan hakan yasa ya bar noma sedai yana da amintattun yaran da ya ɗora suke kula masa da komai shikuma ya tarkato ya dawo garin manya da tulin kuɗin sa ya shiga gina nasa kamfanin na sarrafa auduga, sannu a hankali gini ke tafiya yayinda kasuwar auduga ke daɗa bunƙasa, cikin ikon Allah kuwa se ga Company ya kammala, an ɗau dogon lokaci yana aikin zubawa Companyn injinan aiki da duk abubuwan buƙata kafin komai ya haɗu da taimakon abokin da yake ganawa n yafi ɗan uwa a wajen sa wato Sulaiman wanda shine mutumin da yayi masa hanyar arziƙin tun farko dan shine mutumin da ya sanar da masu Company nan batun audugar Safwan ɗin tun farkon lokacin da suke nema. A farkon buɗe Companyn an sa masa suna SC textiles ne wato Safwan Congo fan yace duk da yake zaune a garin manya dake ƙasar Hawarya to fa ƙasar sa ta haihuwa dai har ila yau Congo ce, cikin ikon Allah Company ya dinga haɓaka, komai suka fitar se an siya kamar me cikin ƙanƙanin lokaci Safwan ya sake buɗe SC couture da ake zuba ɗin kuna kamar ba gobe ya ɗora abokinsa Malam Sulaiman matsayin me kula da komai. A kuma shekarar ne Allah ya nufe shi da sauke farali yaje yayi aikin hajji ya bar shi as shekara me zuwa ya biyawa Malam Sulaiman shikuma ya zauna ya kula da harkokin su, haka kuwa akayi malam Sulaiman ya tafi aikin hajji ya dawo a matsayin Alh Sulaiman dan tuni Safwan ya koma Alh Safwan. Shekarar da ta zagayo Alh Safwan ya buɗe Companyn SC drinks and table water, a lokacin kam gurare kaɗan kaɗan ne a garin manya da ba'a san shi ba saboda akwai shi da taimako ga tausayi hakan yasa kullum yana hanyar gidan marayu da nakasassu kai tallafi. A zuwan da yayi wata rana ne ya haɗu da Nana Asma'u, budurwar da ta canja masa duniyar sa gaba ɗaya, daga workaholic da Alh Sulaiman yake kiran sa zuwa real Safwan, yaji sha'awar ajiye iyali shima yayi settling down sedai zuwan sa garin Congo dan sanar da baffannin sa ya tarar Sama'ila yayi aure, ya auri wata bazawara me ɗa ɗaya suna cikin matsin da ƙangin rayuwa ɗan Sama'ila dai bashi da sana'ar yi, be baro garin ba se da ya wadata ƙanin sa da duk abinda suke buƙata shi da iyalin sa ya kuma jari. Tare da iyayen sa suka dawo garin aka nema masa auren Asma'ul husna wajen Sarkin garin da shine babban kowa na garin balle kuma ƴaƴan gidan marayu. Ba'a ɓata lokaci ba aka yi bikin su bayan wata ɗaya dan haka ƙa'idar su take basa sa lokacin aure da tsawo, soyayya ce sosai tsakanin Safwan da Asma'u dan ba wanda ke tare dasu da besan wannan ba. Basu taɓa haihuwa ba har suka shekara biyar, zuwa lokacin duk hanaklin su a tashe yake sedai shi Safwan yana ƙoƙarin dannewa dan lallashin matar sa, asibitocin da suka je ba zasu ƙirgu ba sedai ko ina faɗa musu ake lafiyar dukkan su ƙalau lokaci ne kawai be yi ba, a shekarar ne kuma matar Sama'ila ta haifi ƴa mace bayan namijin da ta haifa ya rasu, ranar suna Sama'ila ya sanya wa yarinya sunan wata tsohuwar budurwar sa da yake tsananin so wato bilkisu, anyi ɗauki ba daɗi kafin matar sa Haleema ta haƙura da batun sunan ta shiga kiran yarinya da Maigado dan bata tunanin zata iya ambaton ta da sunan bilkisu. Se da Safwan da Asma'u suka cika shekara tara da aure kafin Allah ya azurtata da juna biyu, kwatanta yadda suka ɗauki cikin a ransu ɓata baki ne, sun yi kuka sun yi dariya sun yi murna sun yi sadaka sunyi kyauta at long last suka dira a ƙasa me tsarki dan nuna godiyar su wa ubangiji, ko da Safwan ya tashi dawowa can ya bar Asma'u bayan ya ajiye mata masu kula da ita har huɗu dan yace a ƙasa me tsarki zata haihu dan ɗan ko ƴar su Sami tubarakin ƙasar. Wata sha ɗaya sannan Asma'u ta haifi santaleliyar ƴar ta mace me matuƙar kamanni da duka iyayen ta biyun, dogon gashi da suffar jikin ta sak Asma'u ce yayinda tsayin ta da kamannin fuskar ya kasance na Safwan, murnar da wannan ahali suka yi a lokacin bame misaltuwa bace, nan suka shiga kula da ƴar su da taci sunan kakar ta wato Sakeena da suke kira da Kisnah cikin so da ƙauna bayan sun tarkato sun dawo garin Manya. Haihuwar Kisnah ya zowa Alh Safwan da matsanancin buɗi dan a shekarar ya samu nasarar buɗe manyan Companies ɗin sa har uku da tashi ɗaya ya sanya musu sunan ƴar sa wato K&S FURNITURES, K&,S CONSTRUCTION, K&S FLOUR AND FOOD STUFFS, haka kuma ya bi duk ragowar Companies ɗin ya canja musu suna zuwa K&S. Duk wani mazaunin garin manya ya sani ya kuma shaida irin soyayyar da Alh Safwan je wa gudar ƴar sa Kisnah dan tun da tayi wayo da ita yake zuwa ko ina in ka cire wajen aiki, a kuma lokacin ne ya haɗu da Alh Haladu wanda ya ɗauka ya bawa matsayin manager dan takardun sa sun kai, soyayyar da Alh Haladu ke nunawa Kisnah ce ta saka Alh Safwan sake masa har suka dawo abokai ya danƙa masa kula da K&S drinks and table water da K&S flour and food stuffs saboda aminci yayinda har lokacin suna tare da Alh Sulaiman. Wata rana da ta kasance baƙar rana wa ahalin, ranar da ta kafa baƙin tarihi a zuƙatan su da ma rayuwar su gaba ɗaya..........................✍️. Me ya faru a wannan ranar, wane tarihi ne baƙin tarihin......amsar ku na wajena😍. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 36 (8/26/2022 9:51 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣6️⃣ _________________________📖 ƙarfe tara na daren ranar they were sitting a falo having fun with her parents as always, she was just 5 a lokacin, ranar Abbu kamar yadda take kiran mahaifin nata be fita aiki ba yadda ya saba ko da Nana as she called her mom ta tambayi Abbu dalilin ƙin fitar he answered her with "Am going no where today sweetheart, will be spending the day with you and my cute, beautiful and charming princess". Ko da take yarinya lokacin ba ƙaramin daɗi ta ji ba da abinda Abbu yace, she really loves her Abbu as you loved her haka ma Nanan ta, kasancewar only daughter ɗin su yasa suke pampering ɗin fiye da zato sedai hakan be sa sun kasa tsawata mata ba, in har tayi ba daidai ba suna nuna mata sedai in a cool way da zata ji a ranta Yes she's wrong, bata yi daidai ba. Ranar they wore the same dress with there Nana, blue black Arabian gown that fits their complexion dan dukkan su farare ne sedai Kisnah tafi Nana dan ita Nana hasken ta me duhu ne ba irin na Kisnah ba da ta gado Abbu. Sun yi yawo gurare da ba zata iya tuna adadin su ba, sun ci from all they want, sun siyo duk abinda suka so daga me amfani har zuwa mara amfani, a ranar duk abinda tace yi mata kawai ake ko da wanda basu saba yi mata ko barin ta tayi ba a baya. Tjey spent the day together kamar yadda Abbu yayi alƙawari dan se after 7, ko da suka dawo wanka kawai sukai tare da Sallah sannan suka kuma biye mata suka cigaba da shiririta da kayan wasan ta har almost 9 Wanda ƙa'ida lokacin baccin ta nine ɗin ne, sedai ranar bata san me yasa Abbu keep saying Nana ta bar ta ba while Nana tayi insisting she should sleep saboda tana da school kasancewar gobe Monday. Abbu follows them to her room da suka shiga Nana zata yi mata shirin bacci, its not odd Abbu follow them Dan sometimes shi yake canja mata kayan ka but se jikin Nana yayi sanyi ganin ya karɓi ragamar shirya princess ɗin tasu as they called her majority of times, gefe Nana ta koma ta na kallon su kawai while he dress her happily suna dariya, she's having some kinda bad feelings and it's just recently, se take ganin kamar something is about to happen, kamar akwai wani obstacle da ze zo ya shiga tsakanin wannan father-daughter love ɗin, sedai ta danne wishing all that's about to happen ya canja zuwa khair. Ko da Abbu ya gama shirya ta be tafi ba se ma ya sami gefen bed ɗin ta ya zauna, bayan yayi mata addu'a se kuma ya shiga sake tsokanar ta suka shiga wasa da pillows ɗin bed ɗin maimakon ya sata tayi bacci, tears rolled down Nana's cheeks haka kawai, she keep staring at them tana jin wani abu a jikin ta, something me kama da kewa, kewa irin me cin ran nan, sincerely she's missing them while gasu a gaban ta, da ƙyar ta iya daurewa ta share hawayen ta tana sakin broad smile da ya kai har tsakiyar zuciyar ta ganin gaba ɗaya hankalin su baya kanta, they were busy playing and seeing them like this is all she have and want at the same time. So da yawa in ta kalli relation ɗin ƴar tasu da mahaifin ta mamaki kan kamata, tare take wuni da ita a gida in ba school amma a fili yake ƴar tasu ta fi shaƙuwa da mahaifin ta sama da ita sedai kuma mamakin baya zuwa ko ina yake ɓacewa dan tasan akwai manyan dalilan da zesa hakan faruwa. To Abbu Kisnah has always been his first priority and she's still har yanzu, kafin ta shiga school ko ina zashi da ita yake zuwa hatta da office, seda tayi da ƙyar sannan yake tafiya office ya barta, lokacin tashi nayi kuwa haka ne ajiye komai duk muhimmancin sa ya taho gare su kuma tun a compound ze Fara ƙwala Kiran princess yayind ita kuwa duk baccin da take kira ɗaya yake yi ta farka ta fice da sauri neman mahaifin nata, and one more thing baya taɓa shigowa gida be ruƙo mata wani abu ba, a rubuce yake kullum akwai abinda ze siyo ya kawo mata and that helped in bringing the level of shaƙuwar su so high. Weekend kuwa is never a leisure time wa Abbu tunda aka Kisnah ta fara wayo, he spent every of his weekends trying to pleases her and make her happy ta hanyar kaita gidajen wasa, adventure palaces, shoppings da ma gurare da dama. Yasha haɗa musu tafiya to outside Hawarya ƙasashe masu irin kayan tarihi na yara ɗin nan duk dan jin daɗin ƴar sa wannan ma ya taimaka sosai wajen samar da shaƙuwa da fahimta tsakanin ta da mahaifinta. For Nana kuwa daga baya ƙin bin su gurare ta dinga yi dan gajiyar da ita suke yi su kuwa ko a jikin su shiyasa tace ta dena binsu se wajen da itama take son gani, ko da yarinyar ta fara zuwa school majorityn lokuta Abbu ke dressing ɗin ta dan ko Nana ta zo haka ne persuading ɗin ta akan ta tafi ta yi girki ze taya ta shirya princess Shirin da sometimes har se ta gama girki su basu gama shi ba sun ɓige da wasa se ta shigo su kwakkwaɓe fuska suna bata haƙuri. Zaman sa me kuɗi be sa yace ya ɗau driver was ƴar sa ƙarama da bata san komai ba, da kansa yake kai ta ya ɗauko ta in Kuma aiki yayi masa yawa ya kira Nana taje ta ɗauko ta, wannan gatan yasa Kisnah zama very happy and active, a lokacin mutane da yawa na mata kallon ƴar turawa ne saboda ƙibar da tayi tana yarinya ga kuma kyau da fari kamar ka sace ta. Gyaran muryar da Nana tayi yasa ya kallo gefen ta daidai yana ɗaga pillow ze buga wa Kisnah da ta ke ɓuya, hararar wasa ta masoya Nana ta jefa masa hakan yasa ya sake pillown hannun sa da sauri ya riƙe kunnuwan sa dan se lokacin ya tuna ashe barci suka kawo Kisnah tayi, "Am sorry my life". Abbu ya faɗa while holding his two ears "Nana Abbu is sorry please". Kinsha ta faɗa itama tana riƙe da kunnuwan ta kamar yadda Abbun ta yayi, girgiza kanta kawai Nana tayi dan ta saba da irin wannan halin nasu, ba dama ɗaya yayi laifi se su haɗe mata kai su dinga bata haƙuri har se taji she have no option but to forgive them. "Oya bid her goodnight and move to our room". Nana ta faɗa in serious tone dan in ba haka tayi wa Abbu ba he won't mind spending the night with princess gobe kuma ya makara aiki haka itama princess din ta makara school. Be yi abinda ta ce ba se ya fice daga ɗakin, bin shi tayi da kallo tana sakin smile dan tasan yayi fushi kenan tun da ta kore shi daga wajen princess, ƙara sawa gadon yarinyar tayi ta zauna bakin gadon ta shiga tofa mata addu'a kamar yadda suka saba duk kuwa da cewa Abbu yayi mata amma ƙa'ida ne itama se tayi mata, tana gama ta saka yarinyar ta haɗe palms ɗin ta kafin ta saka ta ta karanta Suratul nas, Suratul falaq and Suratul Ahad da kanta tare da ayitul kursiyyu sanan ta umarce ta ta kwanta ta ja mata blanket kan cikin ta tare da mata offing light ta kunna mata qur'anic recitation a mp3 ɗin ta da aka siyo purposely sabida hakan da kuma ƙara koyan karatun da take yi. Seda ta jira tayi bacci kafin ta bi bayan Abbu ɗakin su inda ta same shi kwance kan gadon su har yayi wanka ya canja kaya zuwa na bacci sedai da alama yayi nisa a tunani dan be ko ji shigowar ta ba, bata ƙarasa gare shi ba seda ta yi wanka ta shirya sannan ta hau gadon har lokacin yana yadda ta same shi da farko, hannu ta miƙa ta cire masa tagumin kafin ta fara tambayar sa damuwar sa a tausashe. Shiru yayi kamar baze faɗa mata ba kafin kuma a hankali ya janyo ta jikin sa ya nufi baki yayi magana dan basa taɓa ɓoyewa junan su komai duk kuwa da ɓacin ran da maganar zata haifar sun gwammace su fuskanci hakan su kuma tare ko ma mene ke ƙoƙarin shiga tsakanin su. "I'm having some strange feelings Husna, Ina jin wani iri a jikina, yanayin kamar irin wani abu mara kyau na gab da faruwa, irin feeling ɗin da na ringa ji lokacin da zanyi rashin inna har ma da baffa na, bana son barin ku Asma'u but it's like something bad is about to happen sedai ban San akan wa ya ba, nidai fatana ko meye kar ya shafi princess, Husna I can't hold myself in wani abu ya taɓa min yarinya, bazan iya ɗauka ba, i pray koma meye ya tsaya a kaina dan............". Da sauri Nana ta rufe masa baki dan tuni ya daɗe da karya mata zuciya da kalaman sa, she too is experiencing the feelings sedai yanzu da ya alaƙanta yanayin da mutuwar Inna da baffa se abin yayi tasiri a rai da zuciyar ta gaba daya har take jin kamar zata rasa su ne, kamar...kamar.... bata fata! Kamar wanda ya dawo hayyacin sa yayi saurin gyara yanayin fuskar sa trying to hide something to her karo na farko tun fara rayuwar auren su 15years back, kumatun ta ya ja Yana sakin dariya lokacin da take faman sharar hawaye "See this woman, are you crying for good, tabɗi amma dai anji jiki dan dama gwada ku nake na ga extent to which kike son mu ni da princess ɗina nad thank God you love us this much". Ya ƙarashe yana mata cakulkuli, dariya take tana kai masa duka tare da magiyar ya bari amma yaƙi seda ya galabaitar da ita sannan ya kwanta gefen ta yana dariya ita kuma tana nishi, seda suka mutu kafin ya soma magana "Ko me kika ga ya faru da bawa rubutacce ne Husna, dan haka mu kwantar da hankalin mu muyi addu'a tunda ba zamu iya sauya ƙaddara ba, now let's pray and sleep ma'un safwanu". Ya ƙarashe in a joking tone dan yasan ta tsani ya kira ta ma'un nan, aikuwa seda ta mintsine shi kafin ta fara addu'a shima ya shiga yin tasa, tana gamawa ta shafawa kanta ta shafa masa shima yayi as she did sannan suka kwanta rungume da juna cikin blanket, shiru suka yi har ta fara gyangyaɗi kafin tai firgigit ta ce masa "I love You". "I love You more ma'u na". Ya faɗa kissing her forehead, and that's the end of their conversation bacci ya kwashe ta, seda ya tabbatar tayi bacci kafin ya zare jikin sa ya koma ɗakin princess, dim light ya kunna sannan ya kwanta a gefen ta yana staring at her face kamar wanda aka bawa aikin zana ta har bacci ya ɗauke shi. Ƙarfe biyu da rabi na dare Nana ta tashi fitsari, ko da ta je ta dawo bata ga Abbu ba ɗakin Kisnah ta nufa ta kunna wuta, kamar yadda tayi zato kuwa nan ta ganshi kwance kusa da princess ɗin tasa, kamar ta tashe shi se kuma ta ƙyale shi ta koma ɗakin su ta kwanta dan gadon baze ishe su su uku ba balle ta kwanta tare da su. Ko minti uku ba tayi ba ta fara jiyo ƙara kamar ana dukan glass ɗin upstairs ɗin su da yake daga stairs ɗin zuwa saman su akwai glass days zagaye gurin da dole se ya buɗe sannan mutum ze hawo. Da sauri ta sauka daga gadon ta koma ɗakin Kisnah kafin ta shiga tashin Abbu cikin firgici, a razane ya buɗe idon sa dan yana cikin wani mummunan mafarki ne ta tashe shi, bata ko lura da yanayin saba ta shiga sanar da shi abin da ke kan faruwa, shima cikin tashin hankali ya saka hannu biyu ya sunkuci Kisnah suka zagaya suka fice ta ƙofar baya, Nana daga ita se rigar baccin jikin ta inda Allah ya so ta ma me kauri ce kuma haɗe take da wando suma duka haka. Gudu ya shiga tsugawa a kan titi yayinda terrorist ɗin suka rufa musu baya dan wanda aka bari zagaye da gidan sun sanar da na ciki fitar su Abbu, haka suka dinga tsere da motar terrorist ɗin har daga ƙarshe suka kai ga harbin tayar motar, cikin ihu Abbu da yaji ƙarar da tayar tayi alamar fashe wa ya ke bawa Nana umarnin ficewa daga motar ita da Kisnah, cikin ruɗewa Nana ta sungumi Kisnah da ta farka tuni ta jefa ta window, cikin son tseratar da ƴar ta ta jefa ta gurin da bata san ina bane ita dai kawai fatan ta ta tsira. Tun daga wannan jefawar da Nana tayi mata ta suma yayinda su kuma su Abbu motar su ta shiga karantawa tana juyawa har ta shige cikin daji kafin ta tsaya sanadin bishiyar da ta tokare ta, mintuna kaɗan kuma ta tashi da wuta gaba ɗaya (abinda kawu yaso yiwa motar su Kisnah kenan da suka gudu se kuma ba sukai ga harbin ba suka daki wannan tankar). Duk da ƙananun shekarun ta a lokacin se da tayi kuka ba kaɗan ba domin a islamiyyar su ana faɗa musu in an mutu ba'a dawowa haka kullum Nana na faɗa mata in ta mutu ba zata sake ganin ta ba se gashi yanzu ana faɗa mata Abbu da Nanan ta sun mutu, a yadda taji labari daga baya ko gawar su ba'a samu ba wuta ta cinye komai. Bayan bakwai ne kuma kawu ya tarkato suka dawo gidan da zama, bayan sadakar arba'in ne kuma ya shiga batun ya kamata ta koma makaranta amma ba zata cigaba da karatu a ƙasar nan ba dan wai ta samu ta manta memoryn mutuwar su Abbu...................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 37 (8/27/2022 12:37 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣7️⃣ __________________________📖 England kawu ya shirya kai ta batare da shawara da kowa ba dan tuni ya babbake kan dukiyar ta dan yace bata da wanda ya fishi a lokacin kuma ba wai ta mallaki hankalin ta bane so ze kular mata da komai zuwa ta girma, ko sati da karɓar ragamar Companies ɗin be yi ba ya sauke Alh Sulaiman daga kan duk abinda yake jagoranta ya canja manajojin da ya ga dama. Ana ya gobe ze kaita England Alh Sulaiman ya same shi har gida kan be dace ya kai yarinya ƙarama ba wata ƙasa ita kaɗai bayan bata da kowa a can, ƙasar da komai namu ya sha banban da nasu kama daga kan al'adu, addini zuwa wayewa sedai tuni kawu yasa ƙafa yayi fatali da maganganun Alh Sulaiman suka rabu baran baran bayan kawu yayi masa cin mutunci wanda wannan ne yasa Alh Sulaiman ɗin yin fushi be kuma magana ba akan duk abinda ya shafi Kisnah dan kawu ya faɗa masa ƴa dai tasa ce dan haka baya san shisshigi da kalan dangi. Haka kawu ya kaita makaranta yayi mata registration ɗin komai ya danƙa ta hannun shugaban makarantar da sunan ze dinga turo masa kuɗin komai na buƙatar karatu amma bazata dawo gida ba har se ta gama karatun ta zuwa matakin ƙaramar secondary. Haka kuwa akai kawu ya dawo gida manya ya bar Kisnah garin da bata da kowa a hannun baturen da be san Allah ba, kamar yadda yace bata dawo manya ba kuwa seda ta gama primary gaba ɗaya sedai batun ilimin addini kuwa babu shi dan tun da ta bar manya ba wanda ya kuma tuna mata akwai abin bautawa da gaskiya wato Allah balle kuma akai ga su karatun Alkur'ani da hukunce hukuncen addinin Islam sedai a karan kanta ta riƙe yin Sallah dan sallah ce abu ɗaya da Nana ta fi jaddada mata fiye da komai hakan yasa duk zamanta a can bata manta da yin ta ba sedai yadda zata yi tan ne bata iya ba so take yin duk yadda taso kawai. Dawowar ta da ƙyar kawu ya barta ta yi wata biyu a gida lokacin tana shekara goma ya kuma maida ta ƙasar Canada inda tayi karatun secondary gaba ɗaya har ta fara University kafin kuma tashi ɗaya ta gudo ta bar ƙasar shine haɗuwar su da Deeq a restaurant ɗin nan yake faɗar ta gudu ba sanar wa sedai suka neme ta suka rasa. Dawowar ta ta nemi admission a nan manya state University department ɗin law inda kuma a nan ta haɗu da duk ƙawayen ta kamar yadda muka ji a baya . *Wannan shine tarihin Kisnah* (Mun dawo labari). Shessheƙar kukan ta da yaji ya ƙara ƙarfi fiye da baya yasa ya juyo ya kai duban sa gare ta, daga zaunen da take ta ƙara takurewa kanta tsakankanin cinyoyin ta tana kukan ta da ya ɗan ƙara ƙarfi dan ta daɗe tana yin sa sedai be kai ƙarfin na yanzu ba. Mamaki ne ya kama shi ganin yadda jikin ta yake rawa sosai kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi a tsakiyar hunturu, gaba ɗaya se yaji jikin sa yayi sanyi, me ya same ta da take kuka haka, bata da lafiya ne ko me? Kamar wanda aka tunawa haka kalmar mara hankalin da ya kira ta ya dawo kansa, to ko shi take wa kuka? Amma in ze tuna an kira ta da kalmar da tafi wannan muni kuma be ko ga ta damu ba balle har ayi batun yin kuka? To amma in ba hakan take wa kuka ba ai ba abinda aka yi mata haka kuma iya sanin sa lafiyar ta ƙalau. Kawar da kansa yayi daga kanta se kuma yaji baze iya ba, kiran sunan ta yayi a hankali sedai ko ɗagowa bata yi ba balle ta amsa hakan yasa ya sake kiran ta wannan karon cikin ɗan ɗaga murya, a hankali ta fara sassauta kukan har sautin ya dena fitowa gaba ɗaya sedai hawaye kafin kuma ta ɗago kanta gaba ɗaya ta sauke jajayen idon ta da kuka ya rina ya sauya musu kala. Seda ya ɗan firgita ganin yadda kyawawan fararen sexy eyes ɗin ta suka koma kala mara daɗin kallo, kafe shi tayi da su taƙi janye wa har lokacin kuma hawayen ta basu tsaya ba se shine yayi ƙarfin halin kau da nasa kafin ya shiga mata magana cikin sanyaya Murya "Lafiya?, me ya same ki?, Wani abun akayi miki?". Girgiza masa kai tayi alamar a'a dan tasan ko tace tayi masa magana ba iyawa zata yi ba yadda Muryar ta ya dishe haka kuma bata saba faɗawa kowa damuwar ta ba bata kuma jin zata fara yau, a kaf rayuwar ta tana barin damuwar ta a ranta ne dan ba wanda take dashi da zarai sharing dashi, a haka ta taso har girma shiyasa hakan ya zame mata ɗabi'a yayinda take samar wa kanta mafita irin wadda taga ta dace, bata san me zata ce an yi mata ba tunda ba'a yi mata ɗin ba shiyasa kawai ta zaɓi girgaza masa kan. "In dan mara hankalin da na kira ki ne kiyi haƙuri raina ne ya ɓaci a lokacin amma na san be dace na faɗa miki hakan ba so na janye ta ki ɗauka ban ma faɗa ba, kinji?". Ya faɗa cikin sake sanyaya Murya, girgiza kanta ta sake yi a karo na biyu kafin ta buɗe baki tayi magana cikin dasasshiyar murya ganin yana ɗorawa kansa alhakin laifin da be aikata ba, tasan ta ji haushin sa akan kalmar haka har tayi fushi kuma ba wai ta janye ba ne sedai ita ba abinda ya sata kuka ba kenan, Allah ta tuba kalmomi nawa aka faɗa mata da suka fi wannan muni kuma bata damu ba balle ta ɗorawa kanta wahala har balle kuma dasu yin kuka. "Duk da naji haushin kalmar amma ba shi ya saka ni kuka ba, i just feel like crying shine nayi". Tsura mata ido yayi trying to read her facial expressions and emotions and he succeeded, ya karanto damuwa akan fuskar ta haka yayi sensing kewa a Muryar ta sedai be san damuwa da kewar akan mene bane ba gashi itama she's not trying to unveil koma meye, a yau ya kuma fahimtar wani daga cikin halin ta, tana da zurfin ciki when it comes to bayyana damuwar dake ranta sedai kuma bata da zurfin ciki kan nuna so, ƙauna ko ƙi ga duk wanda ya siffantu da ɗaya daga cikin, misali bata ji nauyin Meenah ba lokacin da ta cinye wa Hameedah mutunci haka bata ji kunyar Mommy ba Lokacin da ta ƙare wa Awwaf tanadi sedai gashi a yanzu ta kasa bayyana masa damuwar ta. Ajiyar zuciya ya sauke cikin son calming ɗin ta dan har lokacin hawaye keep rolling down her cheeks "Komai yayi zafi maganin sa Allah ne haka kuma bawa baya taɓa gujewa ƙaddarar sa, bawa nagari shine wanda ya amshi ƙaddarar ya shiga ƙoƙarin ganin ya cinye jarrabawar sa ta kyakkyawar hanya, in kin ji zuciyar ki bata miki daɗi se ki yawaita ambaton Allah se ki ji sauƙi ba wai ki zauna kukan da bazai miki maganin komai ba". Yana lura da yadda ta saka hannu t hau goge hawayen daga kan fuskar ta da ta ɗa tasa tsabar kuka har ta goge su tsaff kafin ta miƙe "Bari inje wajen Nenne". Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin kuma be hana ta ba dan yasan hakan ze iya taimakawa mood ɗin ta, sedai tsawon mintina da fitar tata amma ya kasa samun nutsuwa, tunani kawai yake what could be damuwar ta, ko zaman su a nan ne damuwar, ko kuwa zogalen da ta ci ne yake damun ta, but in haka ne ai be ga wani sign na rashin lafiya a tattare da ita ba . Ranar haka ta wuni so moody, ba wani farin ciki balle walwala, sam baya ji daɗin ganin ta a haka dan ba hakan ya saba gani tattare da ita ba, ita ɗin me fara'a da walwala ce a ko yaushe ko da kuma t ɓata rai ba ya kaiwa this long dan ba saki rai ta koma daidai ba har kusan bayan kwanaki biyu, ko yaushe se dai ta zauna tayi shiru cikin tunani wanda da ita ke damun sa da surutu har se yaji ya gaji. Cikin ikon Ubangiji ƙafar Saraki ta warke ras cikin sati biyu da suka biyo baya kuma zuwa wannan lokacin tuni Kisnah ta saki ta koma yadda take baya, surutu kam da tsokana se abinda ya ƙari, yanzu kam ta sake cikin su Nenne da Bingel dan yawanci tare suke zuwa duk in da Bingel ɗin zata dan tuni ya yarje nata fita tun lokacin da ya ganta cikin damuwar nan. Sannu a hankali hannun sa ke samun sauƙi har yana iya yiwa kansa ƙananan abubuwa kamar ɗaukar ludayi, ɗaukar gwangwani, cin abinci da sauran abubuwa marasa nauyi da ba zasu takurawa lafiyar hannun ba. Zuwa wata biyu da suka ƙara kuwa gaba ɗaya hannun ya warke tas dan ba abinda baya yiwa kansa kamar dai lokacin da babu abinda ya faru, duk yadda yaso ya dinga taya kawu aiki ƙi arɗo yayi yana faɗin hannun sa be gama warke wa ba, seda ya ƙara sati biyu kafin arɗon ya yarda suka dinga tafiya tare, duk da cewa be saba da aikin wahala ba amma he's trying to adopt to his new environment saboda so yake Kisnah ta kuma samun new lesson na rayuwa kafin su bar garin. Kamar yau da ya dawo da yamma which is past five, duk da basu da agogo amma suna iya predicting lokaci ta hanyar amfani da yanayin garin, fitowar rana, yin zafin, yanayin raguwar hasken ta, fara faɗuwar ta zuwa gushewar ta gaba ɗaya. A gajiye yake yau tiɓis dan wani yanki arɗo ya shata masa a matsayin gurin da de noma shi kaɗai iya kaci kawai arɗon ya dinga supervising ɗin shi yana gyara masa in da ya kuskure, gurin ya ɗan jima ba'a yi noma a cikin sa ba shiyasa se da yayi aikin gyara shi har na tsawon kwanan uku which today ne cikon na ukun, se kuma a fara gyaran ƙasar wato yi mata kunya kunyar da za'a zuba seeds ɗin. Ƙarewa ɗakin kallo yake cikin son tabbatar da bata nan duk kuwa da yasan dama zata iya bin Bingel, ganin dai bata nan ɗin yasa ya shiga cire rigar jikin sa da ta kasance irin ta Fulani nan arɗo ya siya masa har set ɗin kayan uku, wanka yake san yi sedai matsalar baze iya wankan tafi ba haka kuma ba su da sabulu wanda arɗo ya siyo musu da ya shiga birni ya ƙare dan sati biyu kenan da siyo shin ga kuma waccan yarinyar da tun da ta ƙyalla ido taga sabulun ta dawo yin wanka so biyu a rana madadin ɗayan da take yi, gashi nan ta ja musu sabulun ya ƙare da wuri duk da ma ba wani sabulu me kyau bane irin koren nan ne me yin furkaki in ana wanka, gashi ba yanzu arɗo ze Kuma shiga birni ba which means dole su cigaba da yin wanka da ruwa kawai. Haka ya ɗibi ruwan a cikin gwangwani huɗu ya kai banɗakin nasu ya watsa kawai yana ɓata fuska ganin yadda jar ƙasan ke fallatsan masa a ƙafafun sa, Allah ya sani shima ya gaji dole ma su bar garin nan kwanan nan, da ya gama shukawa kawu seeds ɗin zasu tarkata suyi gaba dan ya gaji da irin wannan rayuwar, da ya bari ne akan ta ƙara samun life lessons sedai a yanzu kam baze iya daurewa ba dan se ya ga ma ita wadda yake yi domin ta kamar bata damu ba tunda yanzu ko me aka bata ci take yi haka baya tunanin yanzu akwai wata kusurwar da za'a shiga a ɓatar da ita a garin, ɗebo ruwa a rafi kuwa tuni ta zama ƙwararriya dan yanzu tare suke cika abubuwan ajiyar ruwan su da Bingel, kiwo kuwa fita take da shanun ita kaɗai kuma taje ta dawo. Ƙawayen Bingel kuwa kusan duk nata ne itama duk da ta girme musu sosai dan su basu fi 13-14 years ba dukkan su ita kuwa tana cikin 20yrs ɗin ta ne. Yana fama canja kaya ko furar da aka ajiye masa be kalla ba ya fita neman ta dan seda ya ce mata kar ta fita dan jiya saura kaɗan wani maciji ya sare ta Bingel ta ganshi ta kashe shi amma shine saboda tsabar rashin jin magana ta kuma saka ƙafa ta bar gidan salon ta ja masa tashin hankali, a yanzu da ya shirya barin garin in not more than a week baze so abinda ze sa su wuce kwanakin da ta ƙidaye ba amma in bata da lafiya ai dole a haƙura da tafiyar abinda baya jin ze iya kenan. Duk wajejen da yake sa ran ganin ta ya dinga bi yana dubawa sedai ba ko alamar ta, tun yana tafiya da tunanin ze ganta har ya gaji ya tsaya, tunani yake tun da bata daji ina kuma take? Sunan rafi da yayi ringing a kanshi yasa ya juya moving towards the direction da ze Kai shi can ɗin, ƙaton ruwa ne da har ba'a ganin ƙarshen sa dan a yadda arɗo ya bashi labari babban ruwa ne da ya ratsa ta cikin garuruwa ko ace ƙauyuka uku bayan nasu, ƴan mata ne birjik a wajen kowacce riƙe da tulun ɗibar ruwan ta yayinda gefe kuma samari da dai ƴan matan masu wanka na yi kowa dai na abinda ya sa kan sa. Daga gefe kaɗan ya hango ta zaune a bakin rafin ta zura fiye da rabin ƙafafun ta cikin ruwan tana wasa dashi, kan buɗaɗɗen gashin ta ya sauke idanun sa takaici na kama shi dan ko jiya seda ya sake mata maganar fita ba ɗankwalin nan shine yau da ta ga ya fita da wuri ta fito a hakan, gurin nasu ya fara dosa dan su waje huɗu ne zaune a wajen suna hira yayinda gogar take ta dariya da alama labari ake bata......................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 38 (8/27/2022 12:38 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣8️⃣ _________________________📖 Ɗaya daga cikin ƙawayen Bingel ce ta fara ganin shi aikuwa ta washe baki da sauri tana faɗin "Kwarankwatsa ga kaɗo me shau nan yana zuwa, Bingel ka gani shi ne ko?". A zabure Kisnah ta miƙe tsaye bayan ta zare ƙafafuwan ta daga cikin ruwan ta shiga zarar ido na rashin gaskiya dan tasan laifin ta, yace kar ta fita ta fita yace kar ta kuma fita ba ɗan kwali kuma bata saka ba, to amma me ya biyo ta ya mata dan duk fitar da take be taɓa biyo ta ba se yau. Damƙar da yayi wa hannun ta ya saka ta ɗago ta ɗan kalle shi cikin alamun rashin gaskiya, haɗewar da ta gani kan fuskar sa yasa lokaci guda cikin ta ya bada ƙara, ƙululu, sosai ta tsorata dan zata iya cewa bata taɓa ganin ɓaci ran sa ba irin na yau shiyasa ta shiga neman abinda zata faɗa dan kare kanta in sun kai gida. Be gama shan takaici ba se ganin yadda duk inda suka wuce se kaji ana mata magana daga maza har mata, wani me neman wajen zaman ma tasowa yayi daga inda yake zaune ta sha gaban su da sauri yana faman washe baki "Kaɗo kana lahiya, yau baka jo ka karɓi lemon ka ba". Ya faɗa yana miƙa mata wani ƙaramin buhu me kamar leda da yake cike da fruits, a yadda Bingel tace mata ɗan ƙanwar Nenne ne shiyasa ta sake masa fuska suke gaisawa yayinda shi kuma hakan yake sa shi cikin farin ciki yana yi wa mazan garin kurin kaɗo kyakkyawa yana kula shi kamar yadda suke kiran ta, Saraki kuma kaɗo me kyau, tun daga lokacin da ta nuna tana son fruits shikenan kullum se ta tsinko mata ya bata ita kuma duk in ta kai gida ta gyara ta sha ta ajiyewa Saraki in ya tambayi ina ta samo cewa take ita ta tsinko ko Bingel, to yau da wuri suka gama kiwo shiyasa basu haɗu ba shine fa ya bata yanzu da ya ganta. Wani irin ƙululu cikin ta ya bayar amma se ta dake ta sa hannu ta karɓa tana mishi godiya shikuwa se aikin dariya yake yana faɗin gobe me yawa ze samo mata. Figar hannun ta Saraki yayi suka yi gaba batare da ya bari sun ƙarasa shirmen su ba suka bar isuhulle tsaye yana ɗaga mata hannu tare da faɗin ta fito da wuri fa gobe. Da sauri ta saka hannu ta dafe garin su na ƙasa wanda ba dan tayi haka ba tabbas da ƙasa zata faɗi saboda turo tan da yayi da ƙarfi. Ko gama tsayuwa daidai bata yi ba ya ƙara so gaban ta yana huci kamar wanda ya haɗiyi garwashi idanun sa sun sauya launi saboda ɓacin rai, ƙanƙame jikin ta tayi jikin bangon ɗakin kamar zata koma Cikin sa saboda fargaba da tsoron Sarakin, kallon ta yake yana tuno yadda ta zagaye gari kanta buɗe ga shashancin da take yi da mazan garin, ɓacin ran da ya sake tuƙo shi yasa ya dunƙule hannun sa ya kaiwa garun da take tsaye jikin sa nauyi, runtse idanun ta Kisnah tayi jikin ta na ɗaukar rawa dan ta zata ita ze nausa sedai da suari ta buɗe idon jin ƙarar zubar ƙasa a bayan ta, zaro ido tayi waje ganin yadda gurin yayi rami yar ya fasa waje, da sauri ta juyo ta dubi hannun sa da duk ya kukkuje yana fitar da jini. Ɗagowa tayi da niyyar yi masa magana sedai ya riga ta buɗe baki "How dere you, eyeh nace how dere you in Baki umarni ki ƙi bi, ban ce kar ki fita ba shine tsabar raini ki ka saka ƙafa kika fice and to make it worse ba ma ɗan kwali dan ki nuna min ban isa ba bazan faɗa miki kiji ba, kina tafe kina shashanci da mazan gari ko?". Kai ta shiga girgiza masa da suari alaman ba haka bane kafin da ƙyar tayi summoning courage ɗin yin magana "Allah ba haka bane yaa, banga zanin da nake sawa a kaina ba shiyasa kuma..........". "Will you shot your stupid mouth ko sena kwaɗa miki mari a gurin?". Tsawar da ya daka mata ya katse abinda take son faɗa ta maza ta saka hannun ta ta ƙara taushe bakin ta, mugun kallo ya cigaba da yi mata kafin kuma ya saki ƙwafa ya matsa inda buhun kayan marmarin da ta shigo dashi ya faɗi ya ɗauka ya fice. Ajiyar zuciya ta saki tare da zame wa ta zauna a gurin tana dafe ƙirjin ta da hannu, dama haka yake? Abinda ta shiga tambayar kanta kenan kafin kuma ta jijjiga kai, amma fa ya bata tsoro, tayi zaton dukan ta ze yi irin yadda taga jikin sa na rawa saboda ɓacin rai. Bata san ze ɗau zafi har haka ba da bata fita ba ɗan kwali ba, ganin ba yau ta saba fita hakan ba kuma a gaban sa tun suna manya yasa bata ɗauki fitar ta ba scarf a komai ba bayan haka ma suma matan garin basa sa komai a kan su suke ficewa, to me ze sa yaji haushin ta ita, ta ƙarshe tananin ta tana tura baki. A can waje kuwa Nenne Saraki ya bawa kayan marmarin yace nasu ne kar a taba dasu suna dashi a ɗaki ta kuwa karɓa tana godiya, can wajen zagaye bukkar su ya fita ya zauna dan in ya koma ɗakin su a yadda yake ji ze iya sa mata hannu and baya fatan hakan ya fara faruwa tsakanin su tun yanzu, a rayuwar sa ya ƙi jinin namiji me dukan mace dan a ganin sa rashin tunani ne da hauka so ba ze so ya zama one ba . Haka ya zauna wajen yana kallon yadda kowa yake al'amuran sa batare da sa ido ko wani ya damu da wani ba har duhu ya kawo jiki amma ko tunawa da yunwar cikin sa be yi ba dan tuni ɓacin rai yasa ya manta da ita. Seda yayi sallar magrib nan waje cikin wani ɗan fili da suka yi wa gini kamu bakwai da bulon su na ƙasa da sunan masallaci kafin ya shiga gidan, kan tabarmar kabar da ya tadda arɗo ya zauna suka shiga tattauna batun seeds ɗin da ze noma a filin da aka bashi, sunyi nisa a batun gonar kafin ya shigo da batun tafiyar su nan da kwana biyar, shiru arɗo yayi yana bin shi da kallo yayinda shi kuma ya sunkuyar da kan sa ƙasa har arɗon yayi magana "Anyi muku wani abu na rashin kyautawa ne Ahmad da kake batun tafiya?". Da sauri ya ɗago yana sakin murmushi wa arɗo ganin yadda duk tsohon ya damu "Ko kaɗan arɗo, sedai kamar yadda na sanar da kai kuma ka gani haɗari ne ya kawo mu zama da ku, kuma alhamdulillah ku ɗin mutane ne na gari dan kun karɓe mu batare da sanin ko su waye mu ba haka batare da neman komai daga gare mu ba, kayi haƙuri arɗo sedai zamu tafi ne dan iyayen mu suna can cikin tashin hankalin rashin sanin ina muke da kuma wane yanayi muke amma ba wai dan kun gaza damu ba, a zamanin nan bana tunanin za'a samu mutane masu matuƙar karamci irin ku arɗo". Murmushin jin daɗin yabon da aka yi musu arɗo ya saki yana gyaɗa kan sa at the same time cikin yarda da batun Ahmad ɗin, "Hakane Ahmad, daɗin zama yasa na manta da ya kamata iyayen ku su san halin da kuke haka su san kuna raye, ban ji daɗin jin zaku tafi Ku bar mu ba amma hakan ya zama dole, kar ka damu Allah ya kaimu ranar". Da Amin saraki ya amsa masa suka cigaba da hirar su har Nenne ta kawo musu abinci da ya kasance kwaɗon rama ne, tare suka saka hannu suka ci suka sha ruwa sannan suka ɗora firar, basu tashi a wajen ba seda arɗo yayi wa Saraki sallama kan yaje ya kwanta sannan ya tashi ya shiga bukkar su ba dan yaso ba. Duk hirar da suka yi Kisnah na jin su dan takarar dake tsakanin bukkar su da ta su arɗo ba me nisa ba ce dan ana iya jin komai dake wakana a waje , ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin batun zasu bar garin in five days time, Allah ya sani tana rayuwa ne kawai cikin nuna all is well alhalin ba haka bane daurewa kawai take amma she is not used to all in the environment, kiwo da zuwa rafi ne kawai abinda tasan tana yi da zuciya ɗaya yake kuma sata nishaɗi da farin ciki se kuma da green view of the palace shima is something lovable to her. Jin ze shigo ɗakin yasa ta takure jikin ta waje ɗaya tare da kwanciya kan buhun da take zaune, baccin ƙarya ta nuna tayi har lokacin da na gasken ya ɗauke ta gaba ɗaya a yadda take, ko kallon inda take be yi ba ya wuce wajen kwanciyar sa ya gyara shimfiɗar sa duk da a gyare take ya zauna tare da karanto addu'ar baccin sa ya shafa yakai kwance abinsa. Ya daɗe kafin bacci ya iya ɗaukar sa saboda kayan jikin sa, kullum haka yake fama dan shi be iya bacci da kaya a jikin sa ba most especially riga sedai a nan dolen sa ya kwanta da ita tunda an haɗa shi kwana guri ɗaya da wannan yarinyar, bayan haka kuma rigunan su masu nauyi ne saboda na saƙi ne. Asubar fari yayi Sallah tare da sammakon tafiya gona, cikin kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya ya maida hankalin sa kan gonar dan so yake yayi ya gama dasa irin su tarkata su bar garin dan ya ishe shi, har kwana uku basa wani good times da ita dan fushi yake sosai, iya gaisuwa ke shiga tsakanin su kawai, in ta gaishe shi ya amsa mata da lafiya shikenan. Ganin yadda ya ɗau fushi yasa ta kama kanta ta tsaya iya matsayin ta bata wani shisshige masa kamar da, in ya dawo yana ɗakin zata fita waje gurin su Nenne tayi zaman ta se dai in an kawo musu abinci sannan ta kai ɗakin su ci dan a kwano guda Nenne ke haɗa musu abinci, haka zasu zauna cin abincin shiru bame cewa komai, in sun gama ta ɗauka ta fita da ƙwarya to akushin ta cigaba da zamanta cikin su se lokacin da Nenne ta kore ta tukun take musu sallama ta shiga taya shirin bacci ta kwanta. Ciki kwanaki huɗu kamar yadda yayi fata ya gama shuka seeds ɗin gaba ɗaya wanda ba abinda arɗo yayi a ciki se gyara masa in da ya kuskure har aka gama. Ranar kam basu dawo da wuri ba duk da da wurin ya gama amma se arɗo ya ɗauke shi suka dinga zagaya gonakin da da kuma na maƙwaftan sa yana ganin yadda shukokin suka yi kyau sosai, nan suka ɓata lokaci har bayan isha kafin suka dawo, ko da suka shigo gidan ruwa kawai ya watsa tare da canja ya fita wajen arɗo dake zaune kan tabarmar sa dake gefen su Nenne, Bingel da Kisnah. Tare suka cigaba da hirar gaba ɗaya cikin farin ciki da kuma kewar su Kisnah da zasu bar garin gobe, kayan marmarin da su arɗon suka shigo dashi Nenne ta gyara ta ajiye wa Saraki da arɗo tare a gaban su su ma su uku nasu a haɗe. Basu tashi daga zaman ba se kusan karfe goman dare sannan akayi sallama kowa ya nufi ɗakin sa, gyara masa shimfiɗar sa tayi lokacin yaje banɗaki sannan ta koma ta gyara tata da tsurar buhu ne se zanin saƙin da yayi laushi saboda shan ruwa da take haɗawa ta kwanta a kai. Ko kafin ya shigo tuni tayi baccin ta dan ita kam bata da nauyin yin Bacci, wuyar ta ta kwanta tuni zata yi baccin ta abin ta, haka damuwa bata hana ta bacci shiyasa yanayin rayuwar ta ya zo mata da sauƙi dan irin cases ɗin da suka wanzu a rayuwar ta ba kowa ce zata iya ɗauka ba, sedai ba fa wai bata damuwa bane a'a abin dai na zuwa mata da sauƙin ne dan rashin bacci ma babbar damuwa ce dake assasa cututtuka da dama. Kashegari da wuri suka shirya dan akwai tafiya sosai kafin su shiga cikin gari, basu ɗau komai ba da yake sunan nasu dan ba abinda zasu yi dashi ko sun ɗauka ɗin, se a lokacin ne kuma arɗo ya kawo wa Saraki kayan sa da ya tsince shi da su a jikin sa, be yi zaton kayan zasu sake amfanuwa ba se gashi an kawo masa su a wanke, faɗar farin cikin da yayi a lokacin ɓata baki ne, kayan ya koma ɗakik su ya canja yana yiwa arɗo godiya yana fitowa kuwa se suka ga kamar bashi ba dan se ya canja musu sosai a cikin shigar, ita kanta Kisnah se taga yayi mata wani irin kyau dan har ta fara sabawa da ganin sa cikin shigar fulanin dajin. Nata kayan Nenne ta bata suma an wanke har da ɗin ke guraren da suka yage sedai a idon ta ba zasu sawu a jikin ta ba dan haka kimonon kawai ta ɗauka ta ɗora kan saƙin jikin ta tare da scarf ɗin ta duk da shima ya sha ɗinki. Cikin matuƙar kewa Kisnah tayi sallama dasu Bingel da Nenne kamar kar su rabu, shaƙuwar kenan, amalanken da arɗo ya tarar musu suka hau aka shiga loda musu tsarabar da su arɗo suka basu, ƙwaryar zuma me kyau guda biyu haka fresh sabon nono ƙwarya uku se curin fura dake cikin wata ƙwayar daban. Haka me amalanken yaja suna ɗagawa juna hannu dasu Nenne dan shi arɗo se ya kaisu tasha, seda suka fara biyawa gidan baffa arɗo suka yi masa sallama shima ya basu tasa tsarabar ta kayan fruits har buhu biyu sannan suka tafi, duk inda suka bi haka ake ta ɗaga musu hannu dan kaɗan kaɗan ne basu san Kisnah ba kasancewar ƙauye kowa ya san kowa har suka yi nisa da mutane suka fara shiga dokar daji. Kamar yadda arɗo ya faɗa tafiyar ba kaɗan bace dan se da rana ta ɗaga sosai sannan suka kai tasha, akori kura ne da yawa a wajen matsayin motocin tafiya, dole haka su Kisnah suka ɗane bayan ta aka loda musu kayan tsarabar su, anan suka yi sallama da arɗo bayan ya sanar dasu sunan kauyen nasu wato Bina, haka kuma yana can cikin jihar Makwan ne, daga Kisnah har Saraki ba wanda yasan wani gari wai shi Makwan sun dai amsawa arɗo da sun gane ne kawai, da motar zata tashi kuwa Kisnah har da kukan ta na rabuwa da arɗo kafin motar ta tashi suna ɗagawa juna hannu su dashi har suka ƙule. Tafiya ce mata daɗi dan hanyar duk kwazazzabai ne bata da kau dama kuma ba wai kwalta ce ba a wajen birji ne, se kusan yamma kafin suka sauka a wani babban ƙauye da a can cikin sa ne ƙauyen su arɗo yake wato Bina, nan ma sallah kawai suka yi suka sake neman tasha suka hau Mota zuwa cikin garin Makwan da ɗan guzurin da arɗo ya bashi da kuma wanda baffa arɗo ya ƙara musu. Basu shiga cikin garin Makwan ba se karfe shida na yamma a yadda yaji direban motar na faɗa, ko da mota ta tsaya rasa ina zasu nufa suka yi tunda basu san ko ina ba a garin hasalima wannan ne karon su na farko na jin sunan garin da ma kasancewa a cikin sa..............................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 39 (8/27/2022 9:32 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 3️⃣9️⃣ ________________________📖 wani tunani yayi kawai ya tsayar musu da napep yace ya kai su nearby hotel amma ba me tsada ba, beso kashe kuɗaɗen hannun sa ba sedae ba yadda ze yi dan ba su da wajen zuwa in ba can ɗin ba. Kamar yadda yace wa me napep ɗin haka ya kai su wani middle class hotel, room ɗaya me ɗan girma ya kama musu ya karɓi key suka wuce. Suna shiga ta wuce toilet da sauri, ruwa ta tara ta shiga wanke jikin ta kamar me wadda ke shirin canja fata, se da tayi kusan saɓi biyar kafin ta haƙura ta fito shima dan knocking ɗin da Saraki ya dame ta da yi ne, ɗaure da towel me matsakaicin girma ta fito abinta se kanta da yasha wanki shima naɗe a ƙaramin towel, da sauri ya kau da kansa tare da bata hanya ta wuce ko a jikin ta, da sauri ya faɗa toilet ɗin ganin ta zauna kan dressing mirror gyara jikin ta, mayukan da ta gani ta dudduba ta ɗau wasu biyu ta shafa ɗaya a jikin ta ɗayan kuma a gashin ta sannan ta ɗau set ɗin comb ta tashe kanta bayan ya ɗan sha iska dan gurin basa ajiye hand dryer, seda ta gama shirya wa kuma ta tuno bata ma da kayan da zata saka dole haka ta koma ƙaton bed ɗin ta zauna jiran ya fito ya samo mata kayan da zata saka. Shima a ta can wankan yayi har round uku dan tsabar dauɗar da ya tara a Bina jikin sa har wani ƙaiƙayi ƙaikayi yake masa, bathrobe da ya hango yasa ya ajiye towel ɗin da ya ɗauko dan ɗaurawa ya ɗau ledar sabuwar bathrobe ɗin ya farke tare da zurawa ya ɗaure sannan ya fita bayan ya goge sumar sa ya ajiye towel ɗin a nan. Be lura da ita ba ya ƙarasa kan mirror ya fara neman man da ze shafa, ganin be ankare da ita ba yasa ta kira sunan sa a hankali "Yaaa". Juyowa yayi ya dube ta at the same time ya kawar da sauri ganin ta ɗaure da towel har lokacin, towel ɗin da a ganin sa be rufe komai na jikin ta ba, "Meye haka kike zaune ba kaya? "Ba ni da kayan da zan saka yaa, nawa kasan masu dauɗa ne I can't wore them again". Shiru yayi dan.yasan gaskiya ta faɗa, shaf ya mance da batun kayan da zasu canja shiyasa be ko yi batun siya ba, ajiyar zuciyar rashin mafita ya saki kana ya miƙe zuwa toilet inda ya ajiye kayan da ya cire ya fito dasu yana lalubar aljihun sa dan ya ɗebo ragowar kuɗin da suka rage musu da baya tunanin sun wuce 6k. Sak yayi jin hannun sa ya taɓo wani card me ɗan kauri kamar ID kamar kuma complimentary card know Kuma................! Kai baya ma tunanin the last one, zaro kuɗin yayi gaba ɗaya tare da card ɗin, abin da ya gani ne ya daskarar dashi a tsaye, ganin yayi tsaye yana bin kuɗin hannun sa da kallo yasa ta kiran sunan shi har kusan so biyu amma be san tana yi ba, seda ta ɗaga murya sosai sannan yayi firgigit ya juyo ya kalle ta, hannun sa ta kalla sannan ta maida kan fuskar sa "Yaa meye a cikin kuɗin da ka kafe su da ido har baka ji kiran da nayi maka ba kusan so uku?". Da sauri kamar wanda ta tunatar dashi ya sake maida idon sa kan kuɗin, ganin har lokacin card ɗin na nan yasa ya kai hannu ya ɗauka jikin sa na ɗan rawar murna, taso wa tayi cikin son ganin abinda ya ɗauka da shine yasa ya kafe kuɗin da kallo cikin tunani, zaro ido tayi ganin atm card ne a hannun nasa haka kuma bata yi wata wata ba ta fisge da iya ƙarfin ta, ATM card ɗin sa ne wanda suka je bank tare ya buɗe take saka masa albashin sa a ciki, tsabar ruɗewa da farin ciki bata san sanda ta faɗa jikin sa ta ƙwaƙumeshi cikin bashi zazzafar runguma ba, wani irin shock ne me azababben ƙarfi ya ratsa jinin saraki, a daidai wannan lokacin baya tunanin in an tsaga jikin sa za'a ga jini tsabar daskarewar da yanayin yasa yayi. Gaba ɗaya kuɗin hannun sa zubewa suka yi a ƙasa dan ba shida wani sauran ƙarfin riƙe su yayinda rawar da jikin sa ke yi ta tsanan ta kamar wanda aka jonawa wutar lantarki, to her kuwa ko a jikin ta, tana gama murnar ta ta sake shi ta tsugunna tana tsince kuɗin da ya zubar, har ta gama tsincewa yana nan daskare be ko iya ya motsa ba seda ta miƙe sannan ya iya ƙarfin halin juya mata baya da sauri dan baya son ko kaɗan taga damar sa. Drawer dake gefe taje ta zauna tare da janyo landline ɗin wajen ta danna kiran customer care tunda ba waya a hannun ta balle tayi online shopping, ma'aikaciyar customer care ɗin ta zo ta bata kuɗin hannun ta 6k ɗin ta lissafa mata abubuwan da zata siyo musu na kayan sawa sannan ta nemi guri ta zauna bakin bed ta juya da nufin yi masa magana sedai wayam taga wajen ba kowa se ATM card ɗin da ke ƙasa, cikin rashin damuwa ta ƙara sa ta ɗau card ɗin ta koma wajen ta ta zauna. A cikin toilet kuwa ya daɗe tsaye dafe da mirror ɗin wajen kafin ya iya dawowa hayyacin sa, he's totally out of word, be San me ze Kira recent scene ɗin ba, yanayin da ta shiga some minutes back was so unpredictable, be San da wane yanayi ya akaƙanta shi ba haka be san da sunan da ze Kira what he just experienced some minutes back ba, yanayin baƙo ne a gare shi dan ze iya rantse wa be taɓa samun contact da mace kamar yadda ya faru a tsakanin su ɗazu ba, it happened so sudden and unexpected, Kai baya jin ko yayi bayani akwai wanda ze fahimci abinda yaji a jikin sa ɗazu. Cold shower ya sake kansa na tsawon lokaci har se da yaji ya koma daidai kafin faruwar abin, bathrobe ɗin da ya cire ya sake maida wa kafin ya gimtse fuska ya fita dan ma kar ta ga fuskar dawo masa da abinda ya wuce. Bata lura da yanayin fuskar sa ba ta shiga lissafa masa abubuwan da ta aika a siyo musu, da kai kawai ya amsa mata tambayar da tayi masa na ko hakan da tayi yayi daidai. Be daɗe da fitowa ba matar da ta aika ta dawo ta kuwa miƙe da saurin ta ta nufi ƙofa with minding cewa towel ne kaɗai a jikin ta, bai san me yasa ba haka kuma be san tunanin da yake ba a lokacin da ya sha gaban ta cikin sauri yana faɗin ta koma shi ze amshi saƙon cikin kau da kai, ɗan tsai tayi cikin mamakin me ze sa ya hanata karɓar aiken se kuma ta matsa baya ta koma bakin bed ta zauna yayin da shikuma ya karɓo ledar ya zo ya ajiye mata a gaban ta kana ya sunkuya ya buɗe ya ɗebi nasa ya wuce toilet Dan shiryawa. Itama nata ta fitar ta shiga sanyawa cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin kar ya fito bata gama ba, doguwar rigar bacci ce me ɗan kauri da ta kai mata gwiwa se wandon ta iya cinya, gaban madubi ta ƙarasa ta ɗau ɗaya daga cikin turaren dake wajen ta shiga fesawa a jikin ta duk da ba taste ɗin ta ba ne amma ta ji daɗin ƙamshin dan rabon ta da yi tun ranar da ta bar gida suka haɗu da wannan accident ɗin. Fitowa yayi shima sanye da nasa kayan baccin, dogon wandon bacci da rigar sa me gajeran hannu, ba ƙaramin kyau kayan suka yi masa ba da har yasa Kisnah kasa janye idanun ta a kan sa ta shiga bin shi da kallo duk inda yayi, yana sane da kallon da take bin shi sedai yaƙi kallon inda take balle yace ta daina dan baya son kallon ta tun bayan kallon farko da yayi mata bisa kuskure lokacin da ya fito daga toilet ɗin, sosai tayi masa kyau sedai yana kallon ta incident ɗin ɗazu ne ya dawo idon sa shiyasa yake gujewa kallon ta. Knocking ɗin da aka sake yi yasa ta kalli ƙofar sedai bata yi ko yunƙurin tashi ba, wannan karon ma shi yaje ya buɗe ya karɓi abinda bata san me ne ba dan rufe yake cikin leda, godiya yayi wa wanda ya kawo ya rufe ƙofar sannan ya dawo cikin ɗakin ya janyo Centre table ɗin dake ajiye ya ɗora ledar hannun sa kafin ya zauna bakin bed ɗin ta ɗaya side ɗin. "Ki buɗe ki ɗau abinci ki ci". Iya abinda ya faɗa mata kenan ya tashi ya nufi wata kusurwa ta ɗakin tare da shinfiɗa daddumar da bata san inda ya samo mata ba ya tada sallah, buɗe ledar tayi ta ɗan leƙa take away biyu ta gani alamun ita ɗaya shima haka. Nata ta ɗauka ta buɗe ta shiga ci tana lumshe ido, fried rice ce da aka wadata da veggies, da a da ne cewa zata yi taste ɗin abincin be mata ba dan a zahirin gaskiya ba wani daɗi ke gare ta ba sedai yanzu dake ta daɗe rabon ta da irin cimar se ta ji duk duniya ba abincin da yakai na gaban ta daɗi, sosai taci ta ƙoshi dan takeaway ɗin irin me biyun nan ne so abincin da yawa, tana gamawa ta far wa rabin gasasshiyar kazar dake kan abincin sannan ta kora ruwan roba, hamdala tayi ciki godiya ga Allah karo na farko a rayuwar ta, wani irin mutuwa jikin ta yayi taji ba abinda take buƙata a lokacin kamar bacci sedai sanin bata isa tayi shi batare da tayi sallah ba yasa bata ko kwatanta kwantawa ba ta jira har ya idar kafin ta ciri hijab ɗin dake cikin ledar wanda ita ta saka aka siyo shi ta hau kan pray mat ɗin ta tada Sallah. Da wannan damar yayi amfani ya buɗe nasa pack ɗin abincin ya shiga ci a nutse, kamar yadda Kisnah taji like bata taɓa cikin n abincin da ya kai wannan daɗi ba shima haka, they spent good 3 months five days suna shan fura da nono se ko zogale da yaɗiya se kuma fruits sanda suka samu, to ba dole yanzu su having this feeling ba. Ko kafin ya gama ci ta idar haka kuma ba wani azkhar ko tasbih ta cire hijab ɗin ta bar shi a wajen dan tsananin baccin da ke rinjayar ta, can tsakiyar bed ɗin ta haye tana sakin ajiyar zuciyar missing this kinda laushi da taushi da tayi ta shige blanket kafin ta iya ce masa good night. Baya san abinda ze sa shi kallon ta balle har wancan ƙaddararren scene ɗin ya dinga dawo masa shiyasa be kalle ta ba balle yaga wajen da ta kwanta ya amsa mata da night kawai. Se da ya gama cin abincin ya tattare wajen ya shiga toilet ya ɗauraye bakin sa ya fito ya nufi kwanciya sannan ya ga yadda ta raba gadon biyu ta kwanta a tsakiya, sororo ya tsaya yana kallon ta dan shi duk a tunanin sa ta ɗau blanket ne ta kwanta a ƙasa, rasa ma wane irin tunani ze yi yayi dan shima baccin yake ji gashi babu ko ƴar kujera a ɗakin balle ya kwanta, tsurar tiles ne a ƙasan se ɗan ƙaramin carpet a bakin gadon wanda ko ƙafar mutum huɗu baze ɗauka ba, haka dai yayi ƙarfin halin janye blanket ɗin da ta lulluɓa ya shimfiɗa a ƙasan ya kwanta sedai be ko yi mintuna goma ba ya miƙe jin kwanciyar ƙasan fa bazata yiwu ba saboda sanyin tiles ɗin ga blanket ɗin ba wani me kauri ba to a bikin da middle class hotel. Sake kallon ta yayi kafin yayi ƙundunbala ya runtse idanun sa ya hau gadon yasa hannu ya tura ta one edge na gadon yana kiran Allah a ransa kamar wanda se taɓa aljana ko wata halittar daban. Har wata ƴar ajiyar zuciya yayi ganin ya matsar da itan sannan shima ya kwanta can ɗaya edge ɗin gadon yana haɗe tafukan sa ya shiga karanta addu'ar bacci, yana gamawa ya shafe jikin sa gaba ɗaya sannan ya ɗan zura ƙafafun sa cikin blanket ɗin da ya maida mata, tsaki yayi ya miƙe ya zauna tare da karanto sabuwa addu'ar bacci sannan ya ɗan matsa kusa da ita kaɗan ya ɗaga blanket bayan ya rufe idanun sa ya tofa mata dan sam baze yi kuskuren kai hannu jikin ta wai shafa mata addu'a ba. Mintuna kaɗan kuwa bacci yayi gaba dashi shima, kiran farko na sallar asuba ya farka dan akwai masallacin gefen hotel ɗin kasancewar gurin na musulmi, seda ya ɗaura alwala kafin ya tashe ta ta hanyar bubbuga gefen gadon sannan ya fita, yana fita ta koma ta kwanta abinta har aka idar da Sallah ya dawo ya tadda ta haka, aikuwa toilet ya shiga ya ɗebo ruwa ya watsa mata, ta kuwa tashi a firgice tana zare ido, ganin sa tsaye kanta ya sa ta tashi da sauri dan zuwa toilet dan tasan dalilin hakan. Tana alwala tana gungunin ya takura mata har ta fito sannan tayi shiru tare da ɗaukar hijab ɗin ta da yake kan daddumar da ta ajiye shi tun jiya ta tada Sallah. Tana idarwa ta kuma neman gado, be hana ta ba dan yasan sun kwaso gajiyar da suke buƙatar baccin sedai shi baze samu damar yi ba dan yanzu haka ya tambayi ɗaya daga cikin securities na hotel ɗin inda ze samu ɗakin haya ya kuma sanar dashi ɗaki baze gagara ba a garin dan haka se haɗa shi da ɗaya daga cikin dillalan da ya sani ko za'a dace shine da ze fita anjima kaɗan. Ƙarfe tara ya fita daga ɗakin yayinda har lokacin take kan barci, be tashe ba se kawai ya kulle ta ta waje bayan ya ajiye mata breakfast ɗin ta, gida kusan huɗu suka je da dillalin kafin a dace da samun wanda yake so wato mara mutane da yawa, ɗaki ne ɗaya sedai da ɗan girman sa haka kuma su uku ne a gidan ba kamar ragowar da ke da mutane sama da biyar ba, seda ya tabbatar wajen yayi masa sannan suka fita suka ƙara sa wajen P.O.S ya cire kuɗin hayar shekara dubu talatin da biyar ya biya shikuma ya bashi key ɗin. Daga nan machine ya tare ya hau bayan ya faɗa masa ya kai shi nearby kasuwar robobi, suna zuwa ya sallame shi shikuma ya shiga siyan ƴan kayan robobi da yasan zasu iya buƙata, butoci, buckets, drum, cups, Parker and dustbin, mopper da broom dan tiles ne a ƙasan ɗakin. Seda ya siya duk abinda yake ganin zasu nema na roba a wajen kafin ya biya kuɗin ya sami me napep ya ɗaukar masa ya kai gidan sannan ya kuma komawa kasuwar Kayan abinci nan ma ya siyan musu me ɗan yawa sannan ya biya ta ƴan katifu ya siya guda ɗaya ƙatuwa dan in yace ze siya biyu to ze ci ƙarfin kuɗin bankin nasa alhalin kuma yana son ya smai ɗan jarin yin sana'a. Yana kai wa gidan ya koma hotel ɗin ya ɗauke ta dan ya samu tayi wanka ta karya tana kwance ne kawai, suna shiga tabi gidan da kallo a lokacin ne kuma mata ɗaya da suka tarar ta fito suka gaisa sannan ta koma bayan ta faɗa musu ɗayar tayi tafiya amma gobe zata dawo. Tare suka shiga gyaran ɗakin bayan ya share ita kuma tayi mopping duk da ba wai yayi bane dan bata wani iya ba, ba laifi ɗakin yayi kyau sedai babu labule babu kuma risho ko gas na girki haka babu kayan plates da spoon ga uwa uba kuma tukunyar da food flask, dole yace ta Masa list ɗin abin da babu ta kuwa yi bayan ta aro pen da paper wajen matar gidan ta tace sunan ta Saudah, haka ya karɓi list ɗin ya kuma fita siyowa ita kuma ta zauna tana bin ɗakin da kallo cikin jin haushin rashin toilet a ciki, gidan madaidaici ne da ke da soro biyu babba da ƙarami se tsakar gida me ɗan faɗi, kitchen a gefen dama se toilet a kusa da ƙofar shigowa se kuma nasu ɗakunan da ke jere sedai da ɗan tazara kaɗan tsakanin ƙofofin su kasancewar ɗakunan da girman su, daga jikin ɗakin Kisnah akwai ɗan ƙaramin corridor da tun da ta ganshi tasa a ranta nan zasu ajiye kayan ruwan su. Be dawo ba se yamma suka kuma shiga gaganiyar saka curtains ɗin masu matsakaicin tsada se dai suna da kyan su ba laifi. Yana gamawa yace ta sa masa ruwan ɗumi a ƙaramin gas ɗin su me kai uku da ya siyo fitar sa ta ƙarshe yayi wanka, bata ƙi ba ta fita ta cika ɗaya daga cikin sababbin pots ɗin d aya siyo da ruwa ta matsa dan kunna gas sedai yaƙi kamawa, da ta gaji se kawai ta koma ɗakin ta faɗa masa yaƙi kamawa, seda ya fito ya gwada mata yadda ake kunnawa sannan ta gane akwai banbanci da nasu na gida...................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 40 (7/28/2022 3:05 PM ) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 4️⃣0️⃣ _______________________📖 Ruwan na tafasa ta shiga ƙoƙarin juye shi cikin bucket sedai ta kasa kuma bata san kiran shi dan taga yadda ya gaji sosai, tana ta kokawa da tukunya har ruwan ya zubo mata a ƙafa bata lura ba se zafin da taji ya ratsa kwanyar ta, ai ba tasan sanda ta saki tukunyar da ta ɗauka ba tana sakin ihu at the same time, a gigice ta fito daga ɗaki jin ihun ta haka ma maƙociyar ta saudah, inda take durƙushe riƙe da ƙafar ya ƙarasa da sauri tare da kaiwa tsugunne yana ƙoƙarin riƙo ƙafar tata dan ko be tambaya ba tukunyar da ta faɗi can gefe da kuma ruwan da suke malale a ƙasa ya shaida masa abinda ya faru, fatan sa Allah yasa ba ta ƙone sosai ba. Se da ƙyar ta cire hannun ta daga kan ƙafar da tayi jaa sosai na azaba, hawaye kawai take yi dan ko sautin kukan babu dan bata taɓa cin karo da irin wannan azabar ba a kaf rayuwar ta se yau, gefe saudah ta tsaya tana mata sannun da bata iya ta amsa ba se Saraki ne ya amsa mata kafin ya tayar da Kisnah tsaye ya saka a gefen jikin sa suka shige ɗakin su. Duk da suna cikin tashin hankalin ƙonewar da tayi amma hakan be hana wani baƙon yanayin kasancewar Kisnah cikin jikin sa ziyartar sa ba sedai be maida hankali ga hakan ba buƙatarsa kawai ya zaunar da ita ya duba mata ƙafar, Allah ya taƙai ta dan fatar bata tashi ba sedai ƙafar da ta yi jajur, duk da gajiyar jikin sa haka ya kuma miƙewa ya fita yaje ya siyo mata ointment da zata shafawa wajen da kuma pain killers da zata sha dan kashe zugin. Kallon sa take yi tana jin wani shauƙi da farin ciki ganin sa duƙe gaban ta yana shafa mata ointment ɗin a ƙafar ta cikin kulawa da takatsantsan, tausayin sa ne ya kama ta ganin duk yau be zauna yana ta zirga zirgar ganin komai nasu ya kammala, wankan da ze yi yaji daɗi ma be samu ba ga abin da ya faru, duk se taji tana jin haushin kanta, yanzu da tana shiga kitchen sosai ai da ta iya juye ruwan zafi da kuma bata ƙara sashi ya wahala ba. Yana gama shafa mata ya ajiye man ya ɗau pain killers ɗin ya miƙa mata biyu, dafe gaban kansa yayi tuno ba ma su da ruwan da zata sha maganin, suna da ruwa a drum ɗin su da ya kira me ruwa ya zuba musu sedai yasan baze yiwu ta sha magani da shi ba, to amma ai a Bina ruwan da suke sha wannan sedai a kira shi ruwan roba a kan sa, tuno hakan yasa ya miƙe ya ɗau cup ɗaya cikin kayan su ya fita ya wanke sannan ya zubo mata ruwan a cikin sa ya dawo, bata yi musu ba ta karɓa duk da tsanar da take wa magani amma haka ta rufe ido ta shanye dan bata san ƙara masa wani gajiyar na ƙin shan maganin ta kan wadda take tattare dashi. Ajiye cup ɗin yayi a gefe ya fita wajen da incident ɗin ya faru ya tarar har saudah ta gyara wajen ta ajiye musu tukunyar a gefe haka ta goge wajen, godiya yayi mata a ransa sannan ya kuma zuba wani ruwan ya ɗora da kansa, ruwan na tafasa ya juye ya sirka ya kai toilet ɗin, tsayawa yayi yana kallon toilet ɗin cikin ɗan ƙyanƙyami dan a rayuwar sa yaƙi jinin toilet mara inganci, a ganin shi gwara toilet ɗin su na Bina dan shi ƙasa ce haka kuma da kansa yake gyara shi kullum so biyu a rana kuma hankalin sa a kwance yake sanin su biyu kawai ke amfani dashi akasin wannan. Sam ji yayi baze iya shiga ba se kawai ya ɗau bucket ɗin ya maida ƙofar ɗakin su ya shige tare da zama kan katifar su nesa da inda take zaune. Bata kawo komai ba ganin ya zauna a tunanin ta someone is using the bathroom shine yake jira sedai ganin har ya fara bacci yasa ta bubbuga katifar tana kiran sunan sa "Baccin ai ze fi daɗi in kayi wankan, nasan ma zuwa yanzu na cikin toilet ɗin ya fito". "Na fasa". Cikin mamaki ta dube shi cikin son dalilin fasawar "Amma saboda me, kalla fa ka gaji da yawa You need to take a warm bath se ka fi jin daɗin jikin ka, ko kuma dan incident ɗin da ya faru ɗazu ne, kayi haƙuri Please Allah ban iya bane amma naga yanda kayi and next time zan yi daidai, an sorry please". "The toilet is not clean". Ya bata amsa yana lumshe idanun sa, bata ce masa komai ba se miƙewa da tayi ta ƙarasa inda ya ajiye musu detergents da su toilet wash da ya siyo musu ta ɗau robar wasu ɗin, disinfectant da kuma toilet freshener ta fita, be san ta fita dan baccin da ya fara ya ci ƙarfin sa. Duk yadda take jin zafin taka ƙafar haka ta daure dan bazata iya kallon shi ya zauna da tarin gajiyar da yake ciki ba bayan all he's going through is because of her, Kai abubuwan hannun ta tayi ta ajiye gefen toilet ɗin kaɗan sannan ta koma corridor ɗin da drums ɗin su ke ajiye ta ɗau empty bucket ta zuba ruwa sosai ta fara ƙoƙarin ɗauka sedai nauyin da ta ji yasa ta ajiye tana yarfe hannun ta, kwaɓe fuska tayi dan all these are new to her, bata Saba da irin wannan rayuwar ba sedai bata jin zata fasa wanke toilet ɗin, da ƙyar ta iya kai bucket ɗin bakin door na toilet tana sauke numfashi tare da kallon palms ɗin ta da suka ɗan yi ja, numfashi ta sauke cikin faɗa wa kanta zata iya ta juya zuwa ɗakin su ta ɗauko daya daga cikin brooms ɗin da ya siyo ta ɗauko me ƙwari ta jujjuya a hannun ta (tsintsiyar kwakwa), banɗakin ta koma ta tura ƙofar, yamutsa fuska tayi itama dan itama ta ga rashin clear ɗin da ya faɗa, tunani take ta ina zata fara wanke wa se kuma tunanin kar ta ɗebi germs a kayan ta yasa ta ajiye broom ɗin ta tsugunna ta tattare ƙasa wandon fakistan ɗin jikin ta har zuwa kusa da gwiwar ta sannan ta ɗaure rigar a ƙugun ta se kuma ta tsaya kallon broom ɗin kamar zata fashe da kuka dan siri sirin saman ta san baze iya wanke toilet ɗin nan ya fita ba. Saudah dake tsaye ta window ɗin ta tana kallon ta ce ta fito kamar zata yi wani abu, motsin ta yasa Kisnah kallon wajen suka haɗa ido se ta ɗan sake mata ƙaramin murmushi, maida mata saudah tayi tana ƙarasowa kusan ta "Lafiya kike tsaye bakin banɗaki haka". "Ehm ina son wanke toilet ɗin ne but nasan wannan broom ɗin won't clean anything, ya zan mata pls". Ƴar dariya saudah tayi kafin ta shiga ɗakin ta ta fito da wata wuƙa kana ta karɓi tsintsiyar hannun Kisnah ta shiga datse ta a ranta tana mamakin yadda zata ce zata wanke toilet ɗin da bata ko daɗe da gama wanke shi ba, tana rage ta tana tambayar Kisnah yayi amma se tace a'a a sake datsewa har seda aka kai tsintsiyar kusan rabi kafin tace yayi mata ta karɓa tare da yiwa saudah godiya ta wuce toilet ɗin ita kuma saudan ta shiga gyara wajen . Ajiye komai tayi a gefe na tunanin bata saba ba bata kuma taɓa yi ba ta zuba toilet wash a floor ɗin tare da detergent tare da disinfectant ta zuba ruwa ta shiga wanke shi da iya ƙarfin ta, kusan saɓi uku tayi wa floor ɗin kafin ta ga yayi mata daidai a idanun ta ta saka ruwa ta ɗauraye sannan ta sake feffesa disinfectant da kuma toilet freshener, take kuwa scent ɗin toilet ɗin ya canja ba kamar ɗazu da yake fitar da wari kaɗan kaɗan ba. Bucket da broom ɗin ta maida corridor ɗin su sannan ta koma ta kwashi ragowar disinfectant, toilet wash da toilet freshener dan detergent kam se da ta ƙarar dashi tas, ajiye kayan tayi inda ta ɗebe su cikin wani ƙaramin basket sannan ta matsa wajen da yake kwance, hannu ta kai da niyyar tashin sa se kuma ta maida ta zuba wa fuskar sa ido cikin yi masa kallon ƙurilla a karo na farko tun da suke tare. Kallon sa take tana admiring duk wani abu na fuskar sa da idon ta ya kai kan sa har ta sauke duban ta kan ɗan siririn baƙin gashin da ke saman bakin sa da be haɗe da madaidaicin gashin dake haɓar sa ba, jajayen laɓɓan sa ta ƙurawa ido kafin kuma ta kawar da kai da sauri tana ɗan matsawa baya jin hannun ta ya fara mata ƙaiƙayin son shafa gaba ɗaya fuskar sa tun bare ma gashin haɓar sa, ɗan gyaran murya tayi cikin kunyar kanta da ya kamata sannan ta shiga bubbuga pillown da kan sa ke kai tana kiran sunan sa. A hankali ya buɗe idanun sa dake cike da bacci ya zuba a kanta yana kallon ta, kallon da ya haifar da wani electrification a cikin jikin ta gaba ɗaya sedai ta kasa kawar da kanta duk da abinda take ji dan kyan da idanun sa suka masa a lokacin baze bar ta ta janye ɗin ba, rufe idon da yayi yasa tayi firgigit cikin tuna abinda ya kawo ta dan haka ta sake kiran sunan sa, wannan karon bata kalli fuskar sa bata shiga masa magana Muryar ta a sanyaye dan tun kallon farko da yayi mata komai na jikin ta ya saki. "Ka daure ka tashi kaje kayi wanka, na kai maka ruwan toilet". Maida idanun yayi ya rufe dan baya jin ze iya tashi a lokacin saboda daɗin da baccin yayi masa "Lokacin Sallah fa yayi ma, gashi can naji kamar ana kira a masallaci". Ta faɗa da sauri dan tasan abinda zata ce kenan ya tashi ba musu, aikuwa dai tar ya buɗe idon sa yana kallon ɗakin su da yake da ɗan duhu kafin ya miƙe ya zauna na wasu sakanni Sannan ya tashi ya ɗau buta ya fita, ruwa ya zuba na alwala sedai yana buƙatar amfani da banɗaki dan fitsari yake ji, takaici ne ya kama shi na tuno yanayin banɗakin na ɗazu, be san me yasa masu gidajen hayar garin nan basa yin toilet a ɗaki dan duk gidan da suka je kafin nan suma toilet a waje yake kuma guda ɗaya, be yi shiru ba lokacin ya tambayi dillalin ko ze iya samun ɗaki me haɗe da toilet sedai amsa ya bashi da su basa toilet a ɗaki sedai in gidan kai ne. Ɗaki ya koma ya fara fitar da kayan wankin toilet dan gwara ya wanke ta shiga a tsaftace duk kuwa da gajiyar da yake tare da ita har lokacin, bata ce masa komai ba ya fita daga ɗakin hannun sa ɗauke da robobin sedai yana dosar wajen ya hango floor ɗin very clean and neat ga Kuma ƙamshi da yake yi, tsaye yayi yana bin toilet ɗin da kallo kafin ya juya zuwa ɗaki da sauri. Ajiye robobin yayi cikin baskets ɗin su ya shiga bin Kisnah dake zaune da kallo, a ƙafar wandon ta da hannun rigar ta ya tsayar da kallon sa ganin yadda suka jiƙe, basket ɗin kayan wankin toilet ya ɗauka ya shiga bubbuɗe su yana dubawa, alamun an yi amfani dasu da ya gani yasa ya tabbatar itace ta wanke. "Wa ya saki fita wanke toilet bayan kin San da ciwo a ƙafar ki kuma ba iya wanke irin wannan kikai ba, what in kika faɗi fa". Yaso ya bata dariya sedai kuma ta ji daɗin kulawar sa "Taya bazan je wankewa ba bayan ka kwanta a gajiye baka yi wanka ba saboda rashin kyan toilet ɗin, nikam ba zan iya barin ka kwanta haka ba". Sosai kalaman ta suka yi tasiri a ran shi haka kuma yaji daɗin concern ɗin da ta yi showing Masa sedai be nuna ba ya bar abin a ransa "Rashin yin wanka na is none of your business, ƙafar ki ya kama ta ki maida hankali ta warke ba yin abinda ba'a saki ba". "Ciwo na is none of your business, wankan ka ya kamata ka maida hankali kayi ba damuwa akan ciwon da ke jiki na ba". Ta bashi amsa cikin jin haushin rashin appreciating effort ɗin ta. Murmushi ne yayi escaping a lips ɗin sa jin ta maida masa da amsa daidai abinda ta faɗa masa, be kuma cewa komai ba ya fita daga ɗakin ya wuce toilet ɗin bayan ya ɗau mini basket ɗin wankan su dake ɗauke da sponge, soao, shower gel, da turaren wanka. Ba kaɗan ba yaji daɗin wankan duk da ruwan ya Salamce ba kamar lokacin da ya sirka shi ba da zafi sosai, ko da ya gama se yaji kamar ya sauke wasu nannauyan kaya a jikin sa, fitowa yayi hannun sa riƙe da bucket ɗin ruwan basket ɗin wankan a cikin sa jikin sa sanye da baƙar jallabiyar da ya shiga da ita a hannun sa. Gaba ɗaya se yaji shi so uneased feeling kamar kowa na kallon shi dan be saba hakan ba, be ji sauƙin abin ba se da ya shiga ɗakin su sannan ya sauke ajiyar zuciyar relief. Tashi tayi ta fita daga ɗakin ganin ya ciro kaya ze saka amma ya ƙi sawari ya tsaya kallon ta riƙe da kayan a hannunsa, lokaci ta bashi sosai sannan ta koma ɗakin dan tasan ya isa ace ya gama shiryawa, jallabiya ya ɗora kan three quarter ɗin da ke jikin sa ya ratse ta ya nufi fita "Ina kuma zaka je yaa". Ta tambaya da sauri, ɗan tsayawa yayi tare da kallon ta "Ita kuma sallar wa ze yi min?, ko bake kika faɗa min an kira ba?". "To wasa nake ai, na faɗa ne dan ka tashi kayi wanka, shugaban an iya baƙar magana". Ta ƙarashe can ƙasa kamar me gunguni. Bece mata komai b aya koma cikin ɗakin ya zare jallabiyar jikin sa ya ajiye kan jakar kayan sa kana ya nemi waje yayi zaune kan carpet ɗin dake tsakiyar ɗakin ya rage daga shi se three quarter da t-shirt mara nauyi da ta kama shi a jikin sa. Tana ganin ya koma ɗakin ta fita ta shiga neman abinda zata ɗora musu girkin dare, jallof sphagetti take son yi sedai basu da kayan miya da vegetables ɗin da zata haɗa dasu, komawa ɗakin tayi ta dube shi yana zaune "Zan ɗora girki yaa amma babu kayan miya da sauran abin buƙata". Shiru yayi yana tunanin wane girki ta iya da har zata ce masa ba kayan haɗi, shifa ko da ya siyo kayan abinci ba wai nufin sa ta dinga girki ba dan yasan ba abinda ta iya, ya siyo ne dan ya dinga dafawa da kansa, yayi musu breakfast, lauch da dinner, in Kuma ya fara fita sana'a se ya dinga musu breakfast da dinner launch Kuma se ta dinga siya. "Ki bar girkin se gobe yau zan siyo abinda za'a ci gobe kuma se ki min listing duk abinda babu se a siyo". Ya faɗa yana kaiwa jingina, bata ƙi ba ta koma ta zauna bayan ta mayar da abubuwan da ta fito dasu da wanda zata yi aikin girkin dasu. Haka suka cigaba da zama shiru kowa da tunanin da yake a ransa har aka kira magrib ya fita, kamar yadda yace haka ya shigo da ledar da yayi musu takeaway da zasu ci da dare bayan yayi sallar isha a masallaci................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah. Ouummey 41 (8/28/2022 8:55 PM) 💠💠💠💠💠💠💠💠 *SARAKI (the Accused prince)* 💠💠💠💠💠💠💠💠 Daga Alƙalamin Ouummey Wattpad @Ouummey *Marubuciyar;* *1; HAƘORIN DARIYA* *2; ƘASAR MU A YAU* *3; BA NI DA LAIFI* *4; Loading......SARAKI (the Accused prince)* ______________________________ *PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞 ```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``` /https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *P.W.A✍️* _________________________________ Page 4️⃣1️⃣ _________________________📖 kan katifar su ka kwanta su biyun sedai kowa yana edge ɗaya na each side, dukkan su sun daɗe bacci be ɗauke su kowa da irin kalar tunanin da yake a ransa kafin Sarkin iya sata ya ƙwamushe su. Yau ma seda ya tada ta da asuba sedai be fita ba se da ya tasa ta gaba tayi alwala tare da saka hijab ta zauna kan dadduma sannan ne ya fita, zama tayi jiran ayi kiran sallah na biyu ta gabatar da sallah kamar yadda yace mata sedai ta ƙi yin nafilar da yace ta yi maimakon zaman jira dan kar bacci ya ɗauke ta. Tana idar da sallah ta cire hijab ɗin ta ninke ta maida jakar kayan ta ta koma katifa ta kwanta cikin sake sabon bacci, ko da ya dawo ya same ta kwance be yi yunƙurin tashin ta ba dan jikin sa ya bashi tayi Sallah, kan daddumar da ta bari ya zauna ya shiga yin azkhar ɗin sa ya gama ya ɗora da tasibihan da ya saba sannan ya tashi ya zare doguwar rigar jikin sa ya ajiye tare da mayar musu da ƙofar ya rufe ya wuce kan mattress ɗin ya kwanta a wajen sa tare da lulluɓa, mintuna kaɗan kuwa bacci ya ɗauke shi dan har yanzu yana ɗan jin gajiyar aikin jiya a jikin sa. Hayaniyar yara dake tashi a tsakar gidan ya hanata bacci yadda take so dole ta haƙura ta tashi ta zauna tare da duban wall clock ɗin da ya taho dashi jiya bayan Isha da ya je siyo musu abinda zasu ci, ƙarfe tara da mintuna uku na safe amma shi ne har yara sun tashi a baccin su gashi itama sun hanata nata da iface ifacen su da duk bata saba dashi ba, ita a gida in ta kwanta bacci ba wanda ke tashin ta har se ta gaji ta tashi dan kanta, to ina ma suke da yaran da zasu dinga irin wannan hayaniyar. Tsaki taja tana ayya na sam gidan haya be yi ba a ranta, kallon gefen da Saraki yake tayi taga shi baccin sa yake hankali kwance da alama ma be san ana wata hayaniya ba balle har ta dame shi, buta ta ɗauka ta buɗe ɗakin ta fita tana hamma a hankali, drum ɗin su ta buɗe ta ɗebi ruwa cikin butar dan zuwa toilet sedai tana zuwa bakin toilet ɗin ta ja ta tsaya ganin yadda aka yi masa kai baka ce shine wanda ta wanke jiyan nan ba, wani irin ɓaci ranta yayi da bata san sanda ta doka uban tsaki ba ta juya zuwa ɗakin su bayan ta dangwarar da butar a ƙofar shiga ɗakin. Fitsari take ji sosai ga kuma wanka tana son yi amma a yadda toilet ɗin yake ta gwammace tayi fitsarin a jikin ta da ta shiga, takaici yasa kawai ta fashe da kuka dan fitsarin ya matse ta. Kukan ta ne ya tashe sa daga baccin da yake yi, be miƙe ba seda ya saurara sosai yaji kukan a ɗakin su ne, zaune tsakiyar carpet ya ganta ta haɗa kai da gwiwa tana gurzar kuka kamar ƙaramar yarinya, dafe goshin sa yayi cikin tambayar kansa yanzu kuma me aka yi mata da take wanann kukan da sassafe, kallon ƙofar su yayi da haske ya ratso ta jikin labulen lu, shi dai yasan seda ya rufe ƙofar daze kwanta dan haka kenan ita ta buɗe ta fita, kenan a wajen akayi mata abinda yasa take kukan hala, ganin tunani baze kaishi ba yasa ya tambaye ta da Muryar sa irin ta wanda ya tashi da bacci "Ada dai nasan kina da jarumtar rashin yawan kuka sedai naga alama a kwanakin nan kin koma raguwar ƙarfi da yaji, yanzu kuma me akai miki kike kuka haka kamar wata ƴar baby?". Seda ta ja hanci kafin ta buɗe baki tayi magana cikin sautin kukan da har lokacin bata dena ba "Ba toilet zan shiga ba, kuma duk an ɓata shi kamar ban yi wahalar wanke shi ba jiya kuma ni fitsari nake ji sosai". "Kawai ki ce kina son yin kashi kuma sun ɓata meye na sako kin wanke shi jiya in ba salon dama kiyi min gori ba kin wanke min toilet nayi wanka, Allah ma yasa ni ban sa mutum ba". Ta sani so yake ta bar kukan shi yasa ya tsokane ta sedai bata jin zata saki ranta in ba fitsarin nan tayi ba dan ji take marar ta ta wani ɗaure kamar zata fashe. Fita yayi daga ɗakin ya ɗau bucket ɗin wankan su ya cika da ruwa kana ya dawo ɗaki ya ɗauki basket ɗin wanke toilet ya fita, da sauri ta tashi ta bishi daidai lokacin da ya zare jallabiyar jikin sa da ya saka lokacin da ze fito ta karɓa da sauri shi kuma ya shiga wanke toilet ɗin tana tsaye bakin ƙofar riƙe da rigar sa, seda ya wanke toilet ɗin fes kafin ya ɗauraye sannan ya karɓi rigar sa ya zura ya fito ta maida ƙofar ta rufe da sauri dan kamar ma fitsarin ya fara zubowa taji, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta gama fitsarin tayi tsarki sannan ta buɗe ƙofar zata fito sedai taci karo da ruwa a bucket ɗin su tare da kwandon wanka bakin ƙofar, zagaye wa tayi ta wuce zuwa ƙofar ɗakin ta ɗaya labulen tana tambayar sa ruwan wankan sa ne wancan sedai amsar da ya bata yasa taji wani abu na ratsa zuciyar ta game dashi "No naki ne, ki maza kije kiyi wankan kafin nan nawa yayi zafi se in yi in kika fito, in Kuma kika bari suka sake ɓatawa ba wanke miki zan yi ba tam". Murmushi ta saki na farin ciki kafin ta juya ta koma toilet ɗin ta shigar da ruwan da kwandon ta rufe ƙofar ta shiga wanka tana lumshe ido saboda zafin ruwan da ke ratsa ta, duk da ta fi son wanka da ruwan sanyi amma wanan ta san zai taimaka wajen tafiyar mata da gajiyar gyara ɗakin da suka yi dan gwara shi yayi wanka tun jiyan ita kuwa se yanzu ne za tayi . Dogon hijab ɗin da ta saka ta ɗora kan towel ɗin da ta ɗaura a jikin ta ta buɗe ƙofar ta fito hannun ta riƙe da bucket da basket ɗin su a ciki, a ƙofar su ta ajiye ta shige ɗakin da ƴar guntuwar sallama a bakin ta, miƙewa yayi ya bi ta gefen ta ya fita zuwa juye nasa ruwan yayinda ita kuma take kiciniyar cire hijab ɗin jikin ta dan ta shirya. A nutse ta kammala shafar ta sannan ta ciri wasu riga da skirt da ta gani cikin jakar kayan da yace mata ta ta ce ta sanya, skirt ɗin baƙi ne daya sauka har kan ƙaurin ta se rigar sa ja da tayi mata cif cif a jiki, gyara gashin ta tayi ta sa masa ribbon ta zazzage jakar cikin neman abinda zata rufe gashin ta dan so take ta fita ta nema musu abin da zasu karya, se da ta birkice kayan duka kafin ta samo ƙaramin baƙin veil ɗin wata Arabian gown me sauƙin kuɗi da ya haɗa mata a kayan, mai da ragowar tayi ta rufe jakar sannan ta yafa veil ɗin da ya tsaya iya kafaɗun ta ta fita bayan ta ciri kayan tea a gurin da suka adana kayan abincin su, gas ta kunna ta ɗora ƙaramar tukunya ta zuba madaidaicin ruwa tare da jefa Lipton ɗin a ciki ta rufe ta zauna kan ƙaramar kujerar robar da ya haɗo cikin kayan robobin da ya siyo musu tana jiran shayin ya tafasa. Tana zaune ya fito daga wanka ya nufo ɗakin, gaban ta ya tsaya yana ƙarewa shigar ta kallo kafin ya juya bayan su dan ganin ko akwai me ganin su, ba kowa se yaran da ke ta wasan su a tsakar gidan da suka yi wa kaca kaca kasancewar weekend ba boko se islamiyya ita kuma se da rana, fisgo hannun ta yayi daga zaunen da seda ta miƙe haka kuma ba ɓata lokaci ta faɗa kan ƙirjin sa dan fisgar ba ta wasa ya mata ba, cikin ɗakin ya jata suka shiga kafin ya saki hannun ta ya shiga bin ta da kallo, ran sa ya matuƙar ɓaci ganin ta zaune a tsakar gida da wannan shigar a jikin ta bayan ta san basu kaɗai bane a gidan sedai yanzu da ya gama ƙare mata kallo se ya nemi faɗan da ya shigo da ita ze mata ya rasa dan ba ƙarya kayan sun matuƙar amsar ta haka sun fito da hasken ta sosai, ba ƙaramin kyau tayi masa ba shiyasa ya manta da faɗan da ya shirya yi "Lafiya yaa, tea fa nake dafawa Dan mu karya, am hungry sosai". Ta tambaya ganin bece mata komai ba se kallon ta da yake yi hakan yasa ya tuno da faɗan da yayi niyya dan haka ya watsa mata harara "Wai me yasa bakya jin magana ne, so nawa zan faɗa miki babu kyau fita da irin shigar jikin ki amma dan taurin kunne kin ƙi denawa, yanzu dan Allah dubi fa yadda kika fita bayan kin san akwai wasu mazan da basu dace su ganki a haka ba". Kallon kanta ta sake yi tun daga ƙasa har sama kafin ta dube shi "Yaa kalla fa kayan jiki na ba inda yake buɗe a jikina se fa hannu na kawai, and se fa da nasa veil a kaina fa, kuma iya ƙofar ɗaki na fita ba waje ba". "Ba inda yake buɗe amma ba curve ɗin da be bayyana ba a jikin naki zaki tsaya yi min musu, meye amfanin veil ɗin naki, da baki saka ba gaba ɗaya ze fi, tunda da baki fita ba ai seki sa himma yanzu ki fitan na manta ne ba yau kika fara tallan jikin ki ba kin saba, You go ahead ki nuna halin ki anan ɗin ma kinji". Ya ƙarashe a zafafe jin tana neman raina masa hankalin wai ba waje ta fita ba, to me ya hana ta fita wajen se taji daɗin da take so kowane low class ya kalle ta ai dama ta saba. Ita ba me damuwa da abinda mutane suke faɗa a kanta bace shiyasa bata taɓa ɓata ranta dan an kira ta karuwa sedai bata san me yasa ba a duk lokacin da shi ya faɗa mata magana se taji rayuwar ta ya ɓaci kamar dai yau, gaba ɗaya walwalar da ta tashi da ita se ta neme ta ta rasa, bata kuma ce masa komai ba kamar yadda be kuma kallon ta ba ya juya ya zauna kan katifa yana shafa mai a jikin sa, dogon hijab ɗin da ta shiga wanka dashi ta zura jikin ta ta fita wajen gas ɗin, tea ɗin ya tafasa ba so ɗaya ba dan gashi nan yayi kala sosai, madaidaicin tea flask ɗin su ta janyo ta saka cup ta dinga ɗiba tana zubawa a ciki har ya kusa cika sannan ya ƙare ta sauke tukunyar ta ajiye a ƙasa dan dama ta kashe gas ɗin. Ɗauraye pot ɗin tayi ta maida ɗaki sannan ta koma ta shigar da flask ɗin ciki ta ajiye tsakiyar carpet ɗin su, cups ta ɗauka ta fita ta ɗauraye suma ta kai kusa da flask ɗin sannan ta ɗauko gwangwanayen kayan madara da ya siyo jiya da dare tare da bread ta ajiye, cup ɗin da ya fi girma ta ɗauka ta tsiyaya masa tea ɗin ta saka cubes ɗin sugar huɗu ta zuba masa madara da bournvita sannan ta kai masa gaban sa da yake zaune kan carpet kusa da katifar su ya shirya cikin jeans dogo da t-shirt. Duk abinda take yi yana kallon ta haka kuma mamaki ne ya hana shi magana na yanda ta haɗa tea daidai, tambayar kan sa ya ringa yi a ina ta koya kafin kuma ya bawa kansa amsa da ai ba wani wahala zata iya haɗawa dan alamu sun nuna ita ke haɗawa kanta. Nata ta haɗa ta koma gefe ta shiga sipping a hankali zafin shi na ɗan ƙona ta sedai ko kaɗan ba wannan zafin ne a gaban ta ba dan zafin maganganun da ya faɗa mata ɗazu sun ninka wannan so ba iya ka, ko rabi bata yi ba taji shayin ya fita a kanta ta ajiye dan dama haka take, indai ranta a ɓace yake bata iya cin abinci shiyasa ba ta ko kalli gefen da bread ɗin yake saboda tasan ba zata iya ci ba. Tunanin rayuwar ta ta shiga yi da yadda ta taso ba wani me kwaɓa, komai tayi kawai daidai ne a wajen kowa, bane ce mata yi, bari, gyara ko makamancin haka shiyasa take duk abinda taga yayi mata daidai a ranta, yanayin shigar ta kuwa abu ne da yabi jinin ta, tun da tayi hankali da masu irin shigar ta buɗi ido ta kuma rayu a tsakiyar su under supervision ɗin Mrs Andrew Smith Wanda itace matar shugabar makarantar da kawu ya danƙata a hannun sa, bata san meye al'adar ta ba, bata san meye daidai da ba daidai a addinin ta ba tunda bata da wani ilimi a kai shiyasa tayi adopting gaba ɗaya culture ɗin su da ma wasu da yawa daga cikin ra'ayin su da yanayin rayuwar su, sallah ce kaɗai ta banbanta sunan ta da kasancewa kafira wanda da za'a bi diddigi ita kanta sallar ba tabbas ɗin tana amsuwa dan kwata kwata ko kusa ko alama ba ta yinta yadda Annabi ya koyar, to bata da ilimin hakan shiyasa kawai dai tana yin ta ne. Hawaye ne suka cika idanun ta dan tasan da iyayen ta basu rasu ba da bata kasance cikin irin wannan rayuwar ba balle har ya ringa samun damar yi mata gori da baƙaƙen maganganu. Cin bread ɗin yake yana korawa da tea kamar a ɗan gaggauce dan yana so ya zagaya yaga wace irin sana'a ze kama da zata fisshe shi, har ya gama tana zaune inda take cikin rashin daɗin rai, seda ya ajiye cup ɗin hannun sa ya miƙe sannan itama ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauke cup ɗin ta fitar waje ta dawo ta shiga gyaran ɗakin cikin sanyin jiki, katifar ta fara gyarawa ta karkaɓe bedsheet ɗin ta maida ta gyara sannan ta mai da kowane abu inda ya kamata kafin ta ɗau tsintsiya ta shiga shara, seda ta gama ta kwashe da ƙyar dan bata iya ba haka kuma bata jin ko son Kiran sunan sa balle tace ya koya mata, ruwa ta kawo tayi mopping floor ɗin iya yanda ta iya sannan ta maida carpet ɗin da ta naɗe tare da fesa room fresheners kala biyu. Seda ta gama komai sannan ta ɗauko ƙaramin jotter da biro da ta karɓa jiya wajen saudah ta shiga rubuta masa duk abinda basu dashi na girki da ragowar amfanin yau da gobe, miƙa masa paper ɗin tayi bayan ta duba taga komai yayi, be tambayi ta me ce ba ya karɓa ya bi abubuwan da kallo kafin ya gane na meye. Da "adawo lafiya". ta bishi da ze fita daga ɗakin duk da bece mata fita ze yi ba alamun fushi yake da ita, yana ficewa ta tura ƙofar ɗakin amma bata saka lock ba ta koma kan katifa ta shiga share hawayen da ta ke ta dannewa kar su fito a gaban sa..........................✍️. ©️ Ouummey 📚✍️. ☑️Ote, Comment and share fisabilillah.