Showing 1 words to 3000 words out of 94165 words

Chapter 1 - TA FITA ZAKKA BOOK COMPLETE by Janafty.txt

30 Oct 2024

2105

[8/27, 9:34 AM] Mrs..🤴🏼: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JC8SzIjZ0S39mF7FMmBeWV




*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_


*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*


*BOOK 1*


*Wannan Labarin tundaga farkon sa har karshensa Tukwaici ne kuma Sadaukarwa ne zuwa ga HALIMA YUSUF GWARZO(Besty) Amincin Allah su tabbata a gareki Allahu ya iya miki Halima Allah ya jibanci Lamuranki Duniya da Lahira Ameen*


_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_


*Intelligent Writer's asso*






*🅿️01*


*GUMEL:Jigawa_Dutse*
_Area:Zango Street_
Friday 5:30pm




Ta jikin get din ta fara lekawa so take tagani ko da wani a Haraban gidan duk da tasan ba lalle ta samu gilmawar wani ba yau jumma"a kuma adaidai wannan Lokacin Duka mazan yara da manya suna masallaci inda Baba Mallam ke musu karatun yammah Matan kuma Kowacce tana cikin gida a irin wannan ranakun na Alhamis da jumma"a suke samun Damar Taimakama iyayen nasu Tunda Ranakun makaranta basa samun Lokaci da sun dawo makarantar Boko abinci kadai suke ci sai sallah da Haraman tafiya islamiya in suka dawo kuma Dare yayi sai Sallar mangariba sai zama yin karatun Tsakani mangariba da Isha"i,sannan in an gama sallar Isha"i kowa zai yi aikin makarantarsa,ko kuma wankin kayan makaranta ko Guga da Sauran aikin karfe 10na Dare kowa yake neman makwanci Saboda Kada a makara Sallar asuba da Shirin makaranta ba atashin mutum sau Biyu sau Daya na biyun kuma Da Duka ne zai sa ya tashi wannan Dokace ga Duk wanda yasan Daya Daga Cikin Dokokin gidan BABA MALLAM da BABA SA"IDU.!
Hankalinta ta Dawo dashi tana kare ma anguwan nasu kallo Shuru ba wani Hayaniya ta Mutane yara duk suna gida Manya kuma suna wajen aikinsu Kofar wani masallaci take Hanga Daga inda take tsaye Fuska ta yamutsa ganin Takalma nan Birjit a kofar Hadadden masallacin mai kama da aljannar Duniya.
Daman tasan yau Dole ne akwai karatun yammah shiyasa bata yarda ta Biyo ta gaban masallacin ba ta yanko Hanya duk da nisanta ta gwammace nisan da Haduwa da Zaluman dake cikin masallacin nan yau suyi bandashenta kamar yadda suka Saba..
Karamin tsuka taja tana gyara zaman Bakar Jakar bayan Dake makale a bayanta wacce ta Sagala Hannu Daya Hannun Daya kuma ta sakeshi.
Yarinya ce wacce ashekaru akallah bazata gaza shekaru sha biyar aduniya ba Doguwace wankan Tarwada mai Dauke da wasu manyan Idanuwa da Doguwar Fuska,kallon Farko Zaka mata ayadda take Motsa baki zakasan tana da Surutu da Tsiwa Sanye take da kayan makaranta na Wando mai Ruwan kuka da Farar riga sai Farin Hijabi da Farin Dankwali kafarta Cikin Takalmin makaranta na Combas samfarin na mata da Safa.
Akallon Farko in kayi mata zaka Fahimci yadda ta jigata,Tun daga yadda Fuskarta Duk ta Kode bakinta ya Bushe yadda kuma take tsaye bakin karamin get din gidansu mai kalan brown zakasan tana tantantaman Shiga gidan ne ko kuma tana Tsorom ta tarar da wani da bataso acikin gida.
Ita Kadai taja tsaki kamar Tsaka afili ta Furta"Ni ba tsoron shiga gidan nake ba..Ni AMINA Aminene tsoron Uban wa zan ji..?kwakwazo ne bana so da Hayaniya uwa uba bana son Yaya ta fito ta ganni ita Kadai ce nake gujema Rigimata..!
Tafada Lokaci Daya tana sosa giranta acikin Ranta tana Tunanin ko taje gidansu HANNE ne..?
Da sauri tace"Kai bama zani ba..Saboda wannan uwar yar saka Idon Yaya Abida..!
Tafada Lokaci daya tana Kallon Wani Makeken get din Daga gaba da Gidansu kadan wanda Jikin Gininsa Daya yake da wannan Kayattacen masallacin da na daga kaina naga ansakamai suna da wani Launin Fenti da larabci Cikin Sha"awa da Burgewa.


*SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA MOSQUE..*


Sannan abun mamaki Gabadaya Daga gidan datake tsaye har wanda take kallo mai hade da masallacin Duka suna Layi dayane juna jikin juna Fenti Daya Komai iri haka get dim ma da kofofi kamar duka gidan gidan mutum Daya ne saboda babu abunda ya bambamtasu illah mai jikin masallaci yafi girma da kawatuwa Sabanin da wanda Amina ke Tsaye awajen yake karami sannan bai kai wanchan abubuwan More rayuwa Daga Ginin ba ammh bayanan komai da komai iri Dayane babu abunda ya bambamtasu.
Tagama Tunanin bata da wata manufa yanzu banda tayi shahada ta kutsa kai cikin gida haka kuwa akayi Da karfin gwiwanta ta Tura kofar get din ta Shiga gidan maimakon na Hangi wanchan gidan sai na Fahimci Daga ciki katanga ta raba Tsakanin Gidajen.
Mota Dayace aharaban gidan wata Siyana ce,Motar da ake kai su makaranta ce wani Lokacin in waccan babbar Macapoli din bata da lafiya ko kuma wani abu ya faru daman ko ABA bai cika Parking din motarsa anan ba yawanci yafi ijiyeta a haraban Gidan Baba mallam Saboda yawancin Saukarsa sai ya fara isa chan kafin ya iso anan Ko Yaya JA"AFAR bai cika ijiyar Mota anan ba Komai su sun saba gudanar dashi Bangaran Baba Malam din Daya zame musu tamkar wani bango abun Jigina da alhafarinsu.
Wani kofa naga ta shiga mai Dauke da Dogon Koridin Dayaji Interlock ko"ina,Sannan yana Dauke da Dakuna Hudu ajere suna Kulle da Kofofi
Daga gani Dakuna ne na mazan gidan ko baki indan hakan ta kama,
Kafin inga ta kara ganin wata Kofa Da karfin gwiwanta ta Tura kofar ta shiga sallamar ma acikinta tayi ta Ba kowa a tsakar gidan nasu wanda ba mai Fadi bane Sosai Daga gefenta kuma Ta hangi HAMIDA tana Gaban Famfo botiki ne a Gabanta tana wanke Kayan makarantar.
Dagachan yammh kuma Kitchen ne Babba Daga ganin yanayinsa zaka Fahimci haka sai daga chan Hannun Hagunta kuma Tiolet ne guda Hudu na Waje Biyu na Wanka Biyu na Lalura sannan Daga gabas dinta kuma Jerin Dakuna ne Guda Hudu,Daya yana nesa da ukun wanda ke Rufe Dakin Aba kenan mai Dauke da Ciki da Falo,Sai Dayan kuma Katon Dakin su ne mai Dauke da Falo kadai ammh babba ne Tun zamanin su Yaya Jalila adakin kowa ke cin yayinsa kafin Aure ya Dagasu har zuwa yanzu da suma suka taso suna cin nasu Lokaci.
Sannan Daki na gaba kuma Dakin MAMANMU CE mai Dauke da Ciki da Falo da bayi sai Dakin kurya kuma Dakin YAYA ce shima kamar na Mamanmu haka yake Daga bakin Dakunan anyi Rumfa Babba wanda ya bada inuwa sosai Daga gaban Rufar kuma akwai katuwar Bishiyar Umbroller
Ko"ina agidan yana Tsabtacene duk da Interlock ne aduka Tsakar gidan ammh bai hana ka gansa kal ba ta tabbata Hamida tayi aikinta kenan Saura ita Daga chan kuma wajen bayika igiyace Doguwa Cike da Shanyan irin kayan makarantar Dake Jikinta.
Cikin Lokaci kadan tagama Nazarin Tsakar gidan ajiyar rai ta sauke Yaya bata Tsakar gida tana Dakinta bari ta Lallaba ta shige Dakinsu ta Sauke gajiyarta kafin ta fara amsan Korafin da kwakwason yan gidan nan akanta da Kullim baya karewa kara Hade ranta Tayi saboda bataso wani ya mata mgana ma ayanayin Datake ciki.
Ita Zainab isa zata rainama Hankali..?tasan ta bata shiri da makaryaci mara Cika alkawarin Bata da Mutumcin in aka Shiga harkanta Tasan bata da kudi Ranar ita yau a makaranta ta ari kudin Break dinta..?ranar haka ta Dawo makaranta ko Biyar bata kashe ba Tana ganin Hamida na kashe kudinta itama ko oho haka take duk da karancin Shekarunta bataso ka Roketa abunda take dashi bata baka ba Zainab isa kudin Mashin dinsu na Ranar da zasu koma gida aka Sace acikin aji,ita da kannenta suke zuwa makarantar wata Unity school dake Cikin gari ne taji Tsausayinta yasa ta ara mata kudin Hannunta naira Hamsin ta Hada dana Hannunta da Niyyar Ranar jumma"a zata kawo mata kudinta,Amina tana girmama alkawari mai Saba shi kuma bata shiri dashi yau Zainab isa batazo makaranta ba ita kuma ana tashi Tana ganin Direban su Mallam Idi yazo Daukansu ta Boye tana ganinsu Hamida da jawaad suna ta Nemanta Ya Shamsu nata Muzarai ta Sulale tayi amfani da kudin Breakdinta da bata kashe ba ta hau mashin taje gidan su Zainab isa ai tasan gidan Saboda sun Taba zuwa gaisheta ida yan ajinsu Lokacin data kone da ruwan zafi.
Sai dai kash tana zuwa ta iske gidansu a kulle wani yaro ta hadu dashi nan waje shi yake fadamata Zainab basa nan sun tafi garinsu Zaria yau da Safe.
Ranta ya baci ta Cizi yatsa ta kudira aranta sai ta Gumdumama Zainab rashin Mutumci bata da ko asi ahannunta yasa ta tako a kafarta Tunda anguwan su Zainab Hadeja Road har anguwansu Zango Street.
Ga yunwa ga kishi ga ba sallah ba Salati iya wannan kadai ya isheta batason kuma adameta da wata mgana.
Ko barayin da Hamida take bata kallah ba Duk da tun shigowarta ta Saki abunda take yi ta mike tana kallonta Cikin mamakin karfin Halin Amina.
Sai da taga ta wuceta zata shiga Dakinsu yasa tace"Ke kam Amina ina kikaje an tashi makaranta muna ta nemanki bamu ganki ba..?Anya Amina baki gudun mgana kullum Aba da Yaya mgana suke akanki naga hakan ma kara miki Dadi yake yi..?
Amina tana jinta bataso ta waigo ba, Saboda bazata mata kyau ba Daga ita har Hamidan Tsakaninta da ita Wata Uku Cur..Kamar bata girmeta ba in Na samanta sun mata mgana ta Ragamusu Hamidan bata isa ba
Ganin in ta tsaya tankata zata kara bata Lokaci yasa ta kara Sauri ta saka Hannu kenan ta Daga Labulen Dakinsu Taji Hamidan na Fadin"Tukunna ma ina kike je..?
Ranta ya kara baci ga gajiya ga yunwa ga kuma wani banzan kallon da Ya Zulaihat da ya Zeenatu Dake Cikin Dakin kowacce kan gadonta na katako kamar na yan bording suke jifanta Dashi ta kasa gaba ta kasa baya.
Kamar Daga sama taji Ya Zulaihat na Fadin"Shigo ki fadamana Gidan Uban wa kike je bayan an tashi makaranta..!?


Bata gama Rufe baki ba Yaya Zeenatu ta Dauka da Fadin"Kema kinsan bazata taba fada ba wannan mai Taurin kan tsiya..Duka ne kadai yaran data sani kuma yau sai kin Daku..Domin ba Dadewa Ya Jafar yazo ya Tambaye ki muka Fadamai gaskiya shida Ya Nasir suka shigo kuma yadda suka Fita yau in s suka kama Dukanki sai na Lahira yafi ki jin Dadin Sakarya mara Tunani..!
Ta karishe Fada tana Hararanta kafin ta saki tsaki ta Cigaba da Duba Littafin Turancin dake gabanta Fuskarta Kaf irin na Hamida ne sai dai Amina tafi su haske ammh har Zulaihat din suna kama ta jini ita Amina manyan Ido ta Fisu da rashin jiki.
Har Duhu Amina take gani Saboda yunwa da gajiya ga bacin rai bataso ta shiga Cikin Dakin suna Cigaba da yaba mata mgana tasan sai ta tankasu kuma basu da imani Taruwa zasu yi suce zasu Daketa tasan bmai Centonta sai Mamanmu in ta Yaya ne su kasheta ita kuma bata iya Shuru da bakinta wanda ya fadamata goma sai ta Fadamai ashirin.
Shawaran canza Daki tayi da Niyar Shigewa Dakin Mamanmu ta Saki Labulan Dakinsu tana Fadin"Duka ai baya kisa..Dayana kisa da ko Burbushin Amina ba"a samu ba..Kuma ni ba Sakarya bace Ehe..!
Tafada tana kunkuni Zulaihat Dake Dakin tace"Eh me kike cewa ne..?
Zeenatu Wlh Zaginki tayi..!
Tafada Cikin takaichin yadda Amina take so ta zame musu ciwon kai acikin gidan ko Aba bata ce Amina na jin tsoronsa ba.
Zenatu tayi Falati da Zanen datakeyi wanda Bilogy teacher dinsu ya basu Doguwar rigace ajikinta ta Fice tana Fadin"ki barta bakinta zan fasa wlh..Zatasan wa take ma rashin kunya..!
Tana daga kwancen tace"Uhm..Ki Dirji bakin gudun Reni ammh nasan ko kin gama bakin Amina bazai taba mutuwa ba..!
Tafada Lokaci daya tana girgiza kai aranta take fadin Allah ya shirya Amina
Zeenatu ta fito Daga Dakin Daidai Lokacin da Hamida take fadin"Mgana fa nakeyi Amina..?gwara ki fara fadamin Inda kika Tsaya na samu yadda zan kare ki agaban Ya jafafar yau.!
Azafafe Amina ta Dago Daga Nufar Dakin Mamanmu datayi niyya Jakarta ta Sauke Saboda Jidalin Dake kanta bazata iyasa da wannan nauyin ba,Manyan idanuwanta ta Sauke kan Hamida tana Fadin"Hamida...Hamida..Hamida Sau nawa na kiraki..?
Hamida na yar dariya tace"Kamar sau uku..!
Amina ta tareta da"ba kama bace..Sau uku na kiraki saboda ki gane girman Warning din da zan miki..Hamida ki Fita Daga Rayuwata Wlh..Ina ruwanki da inda naje inace ke bagaki kin Dawo gidan ba..!da kike fadin ki kareni gaban ya Jafar na sakaki ne..?ke kika saka kanki kina kokarin kare abunda bazai taba karuwa ba Hamida Ni Amina wake sona..?Aba kullum Amina mai Laifin ce awajensa Hakama Yaya kowa baya fadamin abun Alheri akaina Daga Mamanmu sai Baba Mallan ke sona..Sai Hajiya Baba da Hanneta bandasu fadamin me yabon Amina..?kinga kuwa ko Icce aka sakama baki haka Lalacewa yake yi ballatana Mutum kamar ni to bari kiji na Fadamiki ni AMINA SA"IDU GUSAU kainuwa ce dashen Allah baki ko Duka baisa yaga karshena ba, ballatana ganin baya na saboda haka ki adana kalaman bakin ki kuma Rufemin Dattin bakin ki in kuma ba Haka ba ki jirani na ci na koshi in Jidali kike nema na Rantse da wanda Raina ke hannunsa kin Tare ni kin sam.u..!
Tafada Lokaci Daya tana Girgiza kugunta kamar wacce take Shirin Dambe,Zeenatu Data fito tsayawa tayi tana kallonta Hamida kuwa cigaba da wankinta tayi tana Fadin"Allah baki Hakuri..Kya yi bayani in kika shiga Hannun Ya Jafar..!
Wani Tsaki taja kafin ta Duka tana Daukan Jakar makarantar tana Fadin"In yazo kada ya bar Amina da Rai..Yau aka saba ko yau za"a kareta Hamida..?da duka na kisa da yanzu Amina ta Dade a kushe..!
Dauummmm...!
Taji Saukar Dunkullen Dumdu abayanta kafin ta karisa mganarta Dumdum dayasa sai da ta Duke kasa kan Jakarta tana bankare baya saboda taji Saukan Dumdum a bazata.
Zeenatu tace"Yauwa Yaya..Don Allah Daketa bari na karyo Iccen Bishiyar Nan ki Daketa da ita tunda tace Duka baya mata komai..!
Tafada tana Nufar Bishiyan Dake Haraban wajen ai ko ba"a Fada ba,Tasan Hannu Dayake ke da wannan Dumdum ba tun yau ba Tun tasowarta bata iya Haddace dukan kowa ba, da an Dageta taji zafi ya Huce shikenan ta manta ammh Duka Daya Duka Daya daga Hannu Dayane bazata taba manta yanayin ba bata Cika Duka ba mai Hakuri ce sai dai In ta saka hannu ta Duma maka Dukanta Har Ka kwana bazaka manta dashi ba Hannu Dayane mai kama da goma
YAYA CE..ita kadai ce Amina bata saba da Dukanta ba kuma Dukanta ne kadai ke saka Fitar Hawaye a Duka Idanuwanta Aba bai duka sai dai Fada Ko su Ya jafar sai dai su gaji su kyaleta zatayi ihu ammh in ka Duba ba Fitar Hawaye ko Daya Amina akwai Taurin rai da kafiya kamar kafuran Farko..!
Dagowa tayi Idanuwanta na Cikowa da Hawaye ta Sauke kan Fuskar Yaya kamar an Tsaga kara yadda kukasan yan Biyu sai dai bambamcin Amina yarinya ce Yaya kuma Shekarun sunja akallah 49 aduniya ammh Hatta Shape din Fuskarsu iri Daya ne tafi Amina Haske sosai ita din Fara ce ammh ba Tar ba.
Cikim bacin rai take kallon Amina rai Daya..Rai kwara Daya da Tunda ta Haifeta bata Huta ba Amina..Amina ta Addabi kowa acikin gida da waje ba inda ta bari ita kadai take so ta jazamusi hawan jini da Ciwon zuciya ita kadai TA FITA ZAKKA..cikin Ya"ya goma sha Biyu Dake gidan kowa ya gama lafiya banda Amina kowa Amina tagaji takai makura ga kauda kanta kan Lamarin Amina.
Tana Kitchen Sanda Amina ta shigo Taje Duba Wani mganin Ciwon Ciki ne Ararrabi Data ijiye Cikinta ke Juyamata take so tasha..Tun Sanda yaran suka Dawo suna Fadin basu ga Amina ba takasa mgana to me zatace...?wannan ai ba karon Farko bane da Amina tataba batan Dabo a makaramta ba,akwai Lokacin da har an baza Cigiya agidan Radio sai gata ta Dawo wai taje Birthday din yar a Jinsu kaninta ake ma Birthday Bakimciki yasa Aba dinsu ya kamata yayi mata Duka ammh baisa ta Daina ba Amina kanta Tsaye take aikata Duk Abunda taga Dama,a kananun SheKarunta Duka ya Zame mata sabo eh mana Gaskiya ta fada Da Duka na Kisa da an kasheta ita kam Tin tana Daukan Amina aljanu gareta har ta yarda ma kanta Lafiyanta Kalau Amina Zakka take so ta zame musu Cikin gidan nan da Zuru"a gabadaya.
Koda ta Haifesu kaf ya"yanta Ba ita take Renansu ba BALARABA ce Mammansu banda Jafar duka ya"yanta ita take Renonsu ta yayesu in ba Fadamaka akayi ba bazaka Taba Cewa Yaya ta Haihu ba Duka yaran Gidan komai nasu Mamanmu Mamanmu Kowa mamammu In kaji Yaya sai in Mamanmu ta sakota Cikin Shirginsu komai na Tarbiyan yaran da komai na Rayuwarsu na Hannunta ne sai In ma ta musu wani abun take sani Daga baya ba ita kadai kaf Dangin Sa"idu suna girmama Balaraba Kuma sun saka mata suna ita mai karamci ce Taci wannan sunan Domin ita Maman kowa ce.
Bazata kyale Amina ta zautataba kullum Kokenta kan kare ma Amina ne,Mganar Rauninta kan Amina ne Koda yaushe Cikin nema mata Taimako take gani take Aminar ba ita kadai bace kullum kalamanta kenan
"Yaya ku daina Ganin Laifin Amina..Adaina Dukar min Ya'a yaya ba Laifinta bane.. ku lura kamar Amina ba ita kadai bane ni dai ina Zargin Aljanu suka taba Amina Tun tana ciki..Yaya bazan taba barci ba sai naga Amina ta dawo kamar kowacce y'a acikin gidan da watarana Zaku yi alfahari da ita..!
Lokacin datake Fadar haka kukane acikin Ranta da Zuciyarta tasha kuka Har da majina kan Amina in ana Dukanta haka zata zo ta tare har ana Samunta tana Fadin"Jafar ka bari..Kada ka sake taba ta nace..!
"Mamanmu ki barni..Ki bari na Illata wannan rayuwar kafin ta kashe mana Uba da Bakaken Hallayarta..!
Rike Amina take ajikinta ta Fashe da kuka tana Fadin"To in bazaka bari ba sai dai ka Hadamu duka ka Dakemu..Ammh bazan bari ku illatamin yata ba..!
Ita ta Haifi Amina ammh wannan Raunin Maman Amina ke Daukansa bata Cika maida kai kan lamarin Amimar ba Tunda bata wata shakuwa Tsakaninsu,ammh yau taji tana so ta Nuna ma Amima ta bar wasu Zukata su Huta ta Duba Raunin Mamarta akanta ko Saboda ita ta sauya wannan Bakin Halin nata.
Kallon Datake mata Da kuma Tuna wasu abubuwan yasa Hawaye suka Cika kwarmim idonta.
Amina na Dafe da baya ta Bude tace"Yaya..ki ts
Bata kai ayaba Yaya ta kaimata mari wannan karon ya Sameta da Karfi Har sai da ya fito da Zulaihat Daga Daki da Gudu Hamida ma ta bar wankin da Sauri ta karisa tana Fadin"Yaya kiyi hakuri..!
Har Zeenatu Dataje Karyo Icce sai gata ta dawo Wlh bada gaske take ba Bata Dauka Yaya zatayi Duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login