Showing 1 words to 3000 words out of 163596 words

Chapter 1 - YANCNKI Book Complete by Aisha Bagudu.txt

02 Jun 2024

3340

ο»ΏπŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
YANCINKI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


*NA*


*AYSHA A BAGUDO*


DEDICATED TO
MRS ADAM
(YAR MUTAN KAGARA)


PAGE 1 to 5


......Mota ce kiran honda accord ke sharara gudu akan titin ilupeju dake kan Express din mushi road ,yayinda wata mata ke zaune abayan motar, sanye cikin wasu had'add'un kananan kaya ,wando jeans da Riga pinky, kanta kwance da gashin attachement har gadon bayanta wanda ya sha gyara.


"wata yarinya wace bazata wuce kimanin shekara tara zuwa goma ba, ke kwance a saman cinyar wannan matar ,tana fidda numfashi sama sama tamkar me cutar asma .
kuka sosai wannan matar take hannuta rike da gorar ruwan roba tana shafawa yarinyar a fuskarta, saboda numfashinta dake barazanar d'aukewa daga gangar jikinta .


Cike da matsanancin tashin hankali wannan matar tace "Dan Allah malam ka taka motar nan sosai," kayi sauri dan Allah mu samu mu isa asibiti nan da wuri ,tun kafin wani abu yasamu yarinyar nan nashiga uku takarasa maganar tana sake yayyafawa yarinyar ruwa ,direban yace "Baiwar Allah gudu fa nakeyi sosai ...


ganin numfashin yarinya yayi kasa sosai fiyye da d'azu al'amunta numfashinta na daf da tsayawa ,yasa wannan matar sake yin magana a matukar firgice.
"Dan Allah malam k'ak'ara sauri kar kabari yarinyar mutane ta mutu a hannuna, dan Allah dan Annabi ka k'ara gudu idan yarinyar nan ta mutu zan shiga tashin hankali mara misaltuwa ....


A tsawace direban yace " what are you saying?
"do you want me to be involved in a car accident because of you ?
"da kikewa wa mutane zancen banza...


"Wayyo Allah nashiga uku "wannan wani irin maseefa ne haka, ke kokari samuna?
"me zancewa iyayen yarinyar nan ?


" me zance yasamu 'yarsu?
"Dan Allah malam, ba dan halina ba saboda Allah kayi hakuri kayi sauri..


" see I have already gotten to my speend limit, how much did you me?
"da kike kokarin na kashe kaina akan matsalarku ya ja tsaki tare da meida hankalinsa da natsuwarsa kan tukinsa ...


Numfashin yarinyar sai sake yin kasa yakeyi gabadaya idanunta sun gama birkicewa yasa matar tace "oh my goodness God have mercy on me "malam ,kindly speend up plz !


Direban yace " I can't speend more than this in this area.


cikin zafin rai yacigaba da magana "Oh my God which kind of people boarded my car this morning .


"sai da zuciyata ta gargad'eni akan d'aukarku da zanyi, amman naki bin umarninta "me yasa na d'aukeki da irin me wannan ciwon alhalin ban makance ba ?


"gasky daga yau zan dinga lura da irin mutane da zan dinga d'auka most especial irinki, ko dayake na yi mark din face dinki bama zan sake wautar d'aukarki a motata ba.


Gabadaya matar nan tagama firgicewa ta rud'e iya rud'ewa sai gumi ne ke keto mata ta koina a gabadaya ilahirin jikinta, banda sambatu babu abinda take ", wayyo Allah hummm ...am..am "malam Dan Allah karkaji haushina kayi hakuri ka duba halin da yarinyar nan take ciki ,kayi gudu ko dan gudun abinda zai sameta..


"Dan Allah matar nan karki dameni , ki shafamin lafiya mana "ina kan yin iyakacin bakin kokarina ,I can't kill my self for you..
fly kikeson nayi akan titi ko me ? inji cewar direban .


Muryarta cike da matsanancin kuka tace" bance ka kashe kanka ba, ko kazama tsuntsu akan titi ba ,but at least ka duba yanayin da karamar yarinyar nan take ciki " karkayi silar shigata maseefa da tashin hankali ,na gaya maka idan wani abu yasamu yarinyar nan karshena yazo, domin zan rasa aikina akanta " kaga kalli ga wani traffic can gabanmu ..


"Eh nagani me za'a yi da trafic?


" idan kakaraso gurin ka karya hannunka na hagu .


"Na karya hannuna hagu kuma ya tambayeta a wulakance?


Tace "Eh .


shi kuma sanin da yayiwa hanyar bata da kyau, yasa yaki bin hanyar hagu kamar yadda tace yasoma kokarin bin dama.


tasaka wani irin firgitaccen kara "Ina kuma kake kokarin bi ?
" kai da nace maka kabi hannunka na hagu .


"Wayyo Allah ni dai yau nashiga uka nashiga motar wahala , kana bukatar kabi hannunka na hagu ba dama ba ..


" wai me ke damunki ne wannan matar ?
"baki da ido da hankali ne ko me ?
" bakiga hanyar bata da kyau bane dazaki dinga min ihu akai ,wallahi idan kika dameni zan saukeku anan ku nemi wata motar.


" ni dai Dan Allah ka koma Kabi hannunka na hagu idan baso kake kayi silar rasa rayuka guda biyu ba alokacin daya acikin motarka ba..


" yaya kike son nayi I have told you this road is not good yayi maganar a zafafe ..


ihu da masefa take masa ganin yaki sauraronta sai tuki yake hankali kwance, cikin kankanin lokacin taga ya bullo wata hanya wanda yayi daidai da hospital din, take ta sauke wata irin naunayen ajiyar zuciya "yauwa a she dai kasan abinda kake, ga hospital din da zamu shiga can mun iso ta nuna masa da hannunta "ai na d'auka wawa ne kai bakasan hanya ba shiyasa kaji ina ta maka maseefa "kayi sauri tunda mun karaso plz .


"Dan Allah karki dameni da shirmenki din banza da wofi ,ba gashi kokarin danake yi ba kenan, yayi maganar tare da sanya hancin motarsa Cikin harabar hospital.


matar tace "Ni dai ban nemi jin wani dogon turanci daga gareka ba, ka..ka daidaita tsayuwar motar kawai ,gama daidai tsayuwar motar keda wuya ta bud'e murfin motar da sauri tana ihun kiran"doctor!nurse! "Dan Allah malam taimaka ka fito ka d'aukar min yarinyar nan..
dareban yace " Dan Allah gani nan fitowa karki dameni," ko ni ne ubanta?
yayinda ita kuma tashiga ihun kiran doctor da nurse jikinta na wani irin kirma ta zame Kan yarinyar dake kwance saman cinyarta, ta kwantar a kujera tasoma yunkurin fitowa tana kiran" hhh uhmm tana 'barin jikin fitowa da yarinyar ,a daidai lokacin da shima direban ya fito daga mazauninsa har ya bud'e bayan motar yace " kinga Dan matsa na taimaka miki ,da sauri jikinta na kyarma tabar jikin motar tayi baya .


Direban yashiga kokarin fito da yarinyar yana kai hannunsa jikin yarinyar yaji yanayinnta ya sauya tayi nauyi sosai,yayi saurin cewa " ai sai matso ki d'auketa kin wani tsaya kamar wata dolowa kina kallon mutane .
jikinta na rawa ta matso tasoma kokarin janyo hannayen yarinyar amman ta k'asa sai kyarma take tana kuka. "ki fito daita man kin wani tsaya kina rawar jiki ko ba yarki bace?


Cikin rawar murya tace "zan d'auketa tana sake kai hannuta amman tsoron ganin yanayin yarinyar yasa ta kasa d'aukarta, ta matsa baya da sauri "shikenan abinda nake gudu ne ke shirin faruwa dani.


direban ya dubeta a matukar firgice "naga alamun kina son sakani cikin tashin hankali ba?


" ,ki d'auketa daga cikin motata ki sallameni na kara gaba neman abincina, " kayi hakuri abinda nake kokarin yi kenan sai dai bazan iya d'aukarta ba tayi nauyi sosai .


Wani tunani direban yayi kar fa ya tsaya sanya yarinyar tazo ta mace masa acikin mota yashiga uku,wannan tunanin dayayi yasa ya tattara gbdy karfinsa yasoma janyo hannunwan yarinyar ya fito da rabin gangar jikinta yayin kafafunta ke cikin motar "oya kamata mu fito daita .


fito da yarinyar keda wuya, ta dinga yin wasu abubuwa tamkar macijiya yayinda matar nan sai ihu take tana kuka tana kiran sunan yarinyar "NASREEN dan Allah ki rufa min asiri karki mutu "domin idan wani abu yasameki madam bazata barni a raye ba, kuka take sosai tana biye da bayan direban "look at how she curling like a snake may God have mercy inji cewar direban .


gudu gudu sauri sauri suka iso bakin kofar shiga cikin reception " kin damu mutane da ihu ki matso ki bude min kofa mana .


da sauri takaraso jikin kofar ta bud'e masa kofar suka shiga nurse naganinsu suka yi hanzarin karasowa garesu ,tare da amsar NASREEN a hannun direba, kai tsaye d'akin babban likita suka nufa daita ,suka kwantar daita akan gadon likita dake zaune yana dudduba wasu file dake gabansa,likita ya mike da sauri yana gyara zaman farin medical glass dinsa, ya isa gadon da NASREEN take kwance yasoma kokarin bata taimakon gaugauwa .


********


Tsaye take cike da kamewa da natsuwa a tsakiyar maza ,wanda a kalla zasu kai guda goma zagaye daita sai mata guda biyar ,wad'an da ke karkashin ikonta , acikin conference room. kowanensu sanye yake cikin shigar black suit , yayinda ita kuma take sanye cikin wata had'ad'd'iyar doguwar rigar abaya baka har kasa ,wace akayiwa adon da green stone ajikinta tun daga zaren har duwasu, tayi rolling kanta da mayafin abayar wanda ya fidda ainihin sahihin Shep din fuskarta da sirrin kyawunta.
black hill Shoe ne sanye a kafafunta ,yayinda tsintsiyar hannuta yake d'aure da farin agogon diamond me matukar kyau da d'aukar hankali.
wani irin sihirtaccen kamshi na musamman jikinta ke fitarwa ,wanda ke sanya duk wanda ya shaki kamshin yaji yasamu wata natsuwar ta daban a zuciyarsa.


"me'ad kenan diya ga alhaji idris takai dake karkashin hukumar jahar kano ,alhaji idris takai hamshakin me kudi ne wanda ya rike mukamai daban daban agidan custom har zuwa yanzu dayake matsayin controller k'asa gabadaya .


me'ad kyakkyawa ce ajikin farko ta bugawa ajarida ,mace ce first class me tsananin kyau da kyauwun sura wace ta tattara duk wani abinda cikakken d'a nmj me jini ajika yake bukata daga diya mace.
"fara ce sol ko tabo daya babu ajikinta sannan doguwa ce sosai mara kiba, sai dai takasance irin matan nan ne masu shape din cokacola, wato daga samanta tana da cikar halitta qirji na dukiyar fulanin, yayinda cikinta ke shafe tamkar bata sakawa cikinta komai, daga k'asanta kad'an tana da wani irin Hip's na ban mamaki me tsayawa arai ,tana da doguwar fuska da hanci kamar yadda tsarin jikinta yake, sannan tana da karamin baki wanda ke zagaye pinky lip's , itace ta tattara dukkanin wani kyawun mahaifiyarta hjy Khadija da mahaifinta alhaji idris .


me'ad takasance shiru shiru ce ,kasancewar bata fiyye son magana ba, wanda hakan yasa mutane suke mata kallon me shegen girman kan tsiya da miskila ,sai dai fa idan kashiga track dinta zata zage ta shuka maka rashin mutunci ,sam bata d'aukar wulakacin ko rainin hankali, amman idan bakashiga lamarinta ba, zakuyi shekara dubu babu daita babu ruwanta da lamarin mutu .

babu cikakken d'a namji da zai kalli surar me'ad yace bai ga mace me cikar halitta ba, sai dai ya fad'i son ranshi. manage ce a M I K company's dake cikin ikoyi hotel.


ahankali take jujjuya jikinta tana magana a tsanake cikin harshen tsadadden turancinta " am taking about our new product ," all of you are a ware of the reason ,why we call this crucial and important meeting ,we are here to discuss about the company's new product in this market , the importance of this meeting is the product must to do well in the market ,not just do well.


" The product must be the very best in the market "ina fatan gabadayanku kun fahimci inda zancena ya dosa?


suka kad'a kai ala'mun suna sauraronta sannan tacigaba da magana ahankali.
" so the new toothpaste must be the very best in the market so that ....
kiran wayan daya daga cikin members din dake zagaye daita ne ,ya d'auki kara sauti wanda ya karad'e ilahirin conference room din, har ya katse karshen maganar me'ad wace tayi tsaye sororo tana dubansu daya bayan daya, cike da mamaki da matsanancin 'bacin rai kafin ahankali idanunta ya tsaya cak akan wanda wayarsa ke kara ,tacigaba da kallonsa tamkar zata cinyesa tsabar bacin rai, domin abinda tafi tsana kenan arayuwarta tana magana me mahimmanci ana damunta da hayaniya mara amfani .


A matukar tsorace shima ma'aruf yake dubanta kirjinsa na wani irin lugud'en baguwa da karfi, ya kai hannu ya shafa sumar Kansa sannan ya dane fargabansa yasoma kokarin d'aukar wayar ya manna a kunnensa batare da ya sake duban inda take tsaye ba yasoma magana "kana jina ina meeting karka damu kaje cikin dakin ka duba cikin wardrobe dina idan kagani ka d'auka kawai .


sake ware seyx eye's dinta tayi dan tabbatarwa kanta abinda ke faruwa "mafarki ne ko gaske ?ma'aruf wayar ya d'auka alhalin tana tsaye agabansa.
karewar d'aukar wayar ma ,har sautin muryarsa sun soma shiga cikin kunnuwanta suna mata kuwa , cigaba tayi da kallonsa cike da matsanancin mamaki da tashin hankali, "tabbas ma'aruf yana wasa daita tare da wasa da aikinsa , a daidai wannan lokacin, zuciyarta ce taitamata mata sake sake had'e da tsantsar tsanarsa acikin zuciyarta .


"wannan bashi ne karo na farko dayake mata haka ba, a duk sanda suke taro makamancin haka, akoda yaushe shine mutun na farko dake kokarin break din rule dinta ....
iya hassala tayi domin kuwa zuciyarta har tasoma tafarfasa akan sa, yayinda har lokacin ta kasa d'auke idanunta akansa ,wayarsa yake hankali kwance cike da izza da nuna ita din bakowa bace agabansa ." sai dai duk wannan abinda yake zuciyarsa cike take taf da matsanancin tsoron shugaban tasa......


mmn sudais ce
[11/3, 8:24 AM] El~hajj: πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
'YAN CINKI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—


~NA~


*AYSHA A BAGUDO*


~DEDICATED TO~
MRS ADAM
( YAR MUTAN KAGARA)


page 6 to 10


....."mr ma'aruf takira sunansa cikin zakakkiyar muryarta me dad'in sauraro da kashe jiki ,"can i please just have that phone of you's ......?


cike da jin shi ma wani shegen kansa ne "yace am really sorry ma ,tare da meida wayar cikin aljihun wandonsa ya sunkuyar da kanshi kasa yana duban yatsun kafafunsa .



"can you give me your phone now? ta sake yin maganar a fusace tana tsare gira.


"i said am sorry ya fad'a cike da izza ,runtse idanunta tayi ahankali sautin muryarta ta fito atsawa ce "can you give me ur phone?


ransa a had'e ya ciro wayar daga cikin aljihun wandonsa ya mike mata ta amsa tare da jan dogon tsaki ta d'aura wayar kan table tacigaba da maganar "now this is something I wil like to tell everybody.


"if i smash the phone on the floor because of this stupidty...it's the highest level disrespect for your boss to be talking at a meeting..


"idan ma ba rashin hankali da tunani ba ," ta yaya shugabanku na tsaye tana magana me mahimmanci zaku dinga shigowa da waya, har wani jaki daga cikinku wanda yake ganin shi tsagera ne zai dinga receive Call "let me tell you all ,for the very last time.


"me nace...?


gabadaya suka had'a baki gurin cewa for the very last time ma, amman banda ma'aruf da zuciyarsa ta kusan bugawa tsabar takaicinta.


"a tsawa tace "ina son ku sake had'a baki, ku maimaita abinda nace har kai mrs ma'aruf for the very last time .....
take suka sake maimaitawa ,tayi taku daya zuws biyu " let it be the very.. last time, that i wil cal a metting or you come to the conference room da zaku shigo da wayoyinku kai bama ring din wayoyinku ba ,hatta vibrating banaso jin , kai gbdy ma "i don't want to see your phones okay ..


"yes ma.


ta fuskanci ma'aruf sosai "mr ma'aruf this is ur last warning dakazo min da waya meeting .....


sannan ahankali ta fuskanci gabadayansu tace "akwai millions of people out there looking for jobs.. "basu samu ba ,masu kwalkwaluwa sannan suka san yadda zasu sarrafa tunaninsu da kwalkwaluwarsu acikin kasar nan ba irinku dakikai ba, ku kun samu amman kuke iskanci , abinda yakamata ku godewa Allah dayasa kuka kasance cikin wad'an da ke aiki acikn company nan.


ahankali ta sake juyowa matukar fusace gefen da ma'aruf ke zaune sunkuye da kansa "mr ma'aruf..


ya d'ago da kyar yana amsawa da "yes ma.


"ina gargadinka da wannan iskancin naka ya zama karonka na farko da karshe okay "ina nufin karonka na karshe you dare bring ur stupid phone to my meeting, " idan hkan takasance bazan koreka daga cikin meeting din ba, sai bayan nasa an tozarta min kai ,sannan nayi ratsaratsa da wannan banzar wayartaka sannan zanyi sack dinka daga aiki alright? takasara maganar a matukar hasale ."amshi banzar wayarka daga hanuna ta miko masa wayar tana me lumshe idanunta cike da 'bacin rai ,yasa hannunsa ya kar'ba wayar tare da furta "thank you ma a dakile .


bata tsaya sauraresa ba tacigaba da magana cike da matsanancin bacin rai


"yauwa mukoma kan abu me mahimmanci da muke duscusing before..kafin wannan stupid din ya katse mana hanzari " muna magana ne akan sabbin product dinmu na toothpaste da zasu shiga kasuwa acikin tsakankanin wannan lokacin "atakaice dai duk nasan kusan yadda muke son kasuwancinmu yakasance da yadda contains din fluoride dinmu zasu zo hannunmu ko ba haka ba?


suka had'a baki gurin cewa "haka ne ma.


"there is menthoi in it
"we are hering very good report on that as wel dan haka kowanenku yaje yayi nazari akan tautaunawarmu domin yana da matukar mahimmanci....


can hospital kuwa, gudu gudu sauri sauri teacher chioma take a dogon korido din hospitar , kunnenta mane da waya ,cike da tashin hankali ta cire wayar a kunneta tana dubawa tagani ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login