Showing 1 words to 3000 words out of 104570 words

Chapter 1 - SARAKI (The Accused Prince).txt

ummi   

03 Jun 2024

5300

 Ouummey 01 (7/27/2022 3:36 PM )


💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey✍️
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*






PAGE 1️⃣


BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM!!.


Dukka yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki, Ubangijin sammai da ƙassai, Ubangijin talikai, Ubangijin Al~arshi me girma.


Dubun salati su tabbata ga shugaba kuma fiyayyen halitta, Annabinmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.


Wannan littafin mallakar Ouummey (khairert) ne, ba yarda wata ko wani su juya min littafi ba ta kowace siga bata reda yardata ba, duk wanda yai gangancin yin hakan kuwa zai haɗu da fushin hukuma.


Wannan labari ƙirkirarren labari ne dana ƙirƙireshi bisa fasaha da baiwar da Allah yai min, kamanceceniyar suna ko halayya akasi ne kuma arashi ne, fatan za'ayi haƙuri da hakan.


Gareku masoyana masu bibiyar rubutuna da nuna min ƙauna da soyayya, to gani na kuma dawowa gareku cikin salon rubutuna da ya bambanta dana kowa.


Salon yasha bambam da wadanda suka gabata, tafiyar me ƙarƙo ce, tsarin me matuƙar tsayawa a rai ne haka kuma soyayyar me garɗi ce, ina fatan zaku biyo ni sannu a hankali don tabbatar da duk abinda na faɗa.














__________


Dogon ginin me matuƙar girma da faɗi da za'a iya kiransa da gari guda, gidan da ko ba’ace ba Kai tsaye zaka kirasa da gidan sarauta sabida yanda aka tsara ginin ga kyau ga girma had’ida tsawon gini....


Tsugunne a gaban babban mutumin da ya sha naɗin rawanin da ya rufe fuskar sa ruf da ba'a ganin komai sai hancinsa da idanunsa yake, daga ganinsa ko ba'a faɗa maka ba kasan shine Sarkin dayake mulkar wanna babbar masarauta me daɗaɗɗen tarihi gami da ababen mamaki da al'ajabi haɗu da tarin izza da tsantsar mulki me tafiya da tsofaffin al'adu, SARKI MUHAMMED HASHIM II kenan, wanda ya kasance na bakwai a jerin sarakunan da suka jagoranci kuma suka mulki wannan babbar masarauta.


Masarautar DAULATUL NOOR kenan dake garin Giwa a nan kudancin ƙasar Hawarya, masarautar da take cikin manyan masarautu huɗu da suke a faɗin ƙasar


Kamar yadda na fara faɗa a baya, masarautar DAULATUL NOOR masarauta ce me cike da shahararren mulki da iko haɗi da ilimin addini da na zamani, sarakuna bakwai ne suka mulki wannan babbar masarauta kawo yanzu da mai martaba sarki Muhammad Hasheem ke jan ragamar ta.


Sarki Muhammad Hasheem kamili kuma adalin sarki ne da yai suna wajen zartar da hukuncin adalci batareda duba ga girma, kusanci ko muƙamin wanda ya aikata laifi ba, ya kasance sarki jajirtacce kuma mara tsoro wanda hakan yasa bayi da dukkan talakawansa suke alfahari dashi da jin daɗin zama a ƙarƙashin sa.


___


Idanunsa masu matuƙar kaifi da tasirin da yake amfani dasu wajen yiwa mai laifi hukuncin farko ya zuba akan babban ɗansa dake ɗuke gabansa yana mai tsattsare shi da su.


Kaifin idanun mahaifin nasa akan sa baisa yaji wani ɗar ba ko kaɗan dan har yanzu yana akan bakansa na bazai karɓi laifin da aduniya ya tsani mai aikata shi ba, laifin da yake jin da yana da iko se ya hana wanzuwar masu aikata shi a ban ƙasa, sai gashi an wayi gari yau shi ake tuhuma da aikata wannan laifin har ake ƙoƙarin tursasashi wajen ya amsa da bakinsa saidai yana jin ko wuƙa za'a ɗora a maƙoshinsa a raba shi da numfashinsa bazai taɓa yin abinda suke so ba.


Janye idanunsa sarki Muhammad Hasheem yayi daga kallon yaron nasa kana ya maida dubansa ga dubban jama'ar da suka cika fadar tashi dan ji da kuma ganin hukuncin da za'a yankewa YARIMA SARAKI da aka kama da ɗaya daga cikin manyan haramtattun laifin da masarauta ta hana tai kuma Allah wadai da aika tasu.


Gyaran murya mai martaba yayi kana cikin tsantsar izza da ƙasaita ya fara magana a hankali cikin muryarsa mai cike da dattako wadda banda waziri dake kusanshi hatta ɗan sa dake duƙe gabanshi baze ce yaji me mahaifin nasa ya faɗa ba.


Miƙewa tsaye waziri yayi bayan ya gama sauraren jawabin da mai girma sarki yai masa ya dubi al'ummar dake cike a fadar ya fara magana.


"Sanin kowa ne da ke cikin wannan gari me Albarka ZINA na ɗaya daga cikin manyan laifukan da masarauta tai Allah wadai tare da hani da aika tawa Wanda aka tanadar da hukunci me matuƙar tsauri da girma ga duk wanda ya kasance victim ɗin wannan aiki, sai dai kwatsam aka sami YARIMA SARAKI da aikata mafi munin laifin da girmansa ya shafe laifin zina wato FYAƊE". Sauke numfashi waziri yayi sannan ya ɗora


"Bisa hujjoji masu yawa da ƙarfi da aka gabatarwa wannan fada me Albarka, an sami yarima saraki da aikata laifin fyaɗe ga ƴan matan bayi guda biyu haɗi da yi musu barazana in har suka sake suka sanar da koda iyayensu ne, wanda ɗaya daga cikinsu ta rasu yayin haifar cikin yariman yayinda ɗaya ke raye ɗauke da cikin shi na wata biyu a jikinta, haka kuma a shekaranjiya ne aka kuma kama yarima saraki da laifin aikata fyaɗe wa ƙanwar gimbiya Saudat da ta kawowa yayarta ziyara wato gimbiya Husna ta masarautar kangiwa, yariman yayi amfani da ƙarfin sa yayin ɗaukar gimbiya Husna zuwa turakarsa inda ya wulaƙanta rayuwarta, dan haka adalin sarkin mu ya zartar masa da hukunci bayan sauraren dukkan ɓangarorin dake ƙara tareda gudanar da ƙwaƙwaran bincike inda aka sami yarima dumu dumu da aikata wannan Laifuka dan haka a yanzu maga takarda zai karanto mana hukuncin da shugaban mu ya yanke wa mai laifi".


Sauke ajiyar zuciyan dogon surutun da yayi waziri yayi kana ya koma ya zauna haɗi da miƙa wa magatakarda paper ɗin da maimartaba ya bashi.


Fadar tayi tsitt ba abinda kake ji illa sautin Muryar magatakarda data karaɗe ilahirin fadar saboda tsananin zaƙin murya da Allah ya bashi.


"Bayan gabatar da hujjojin da suka bayyana yarima saraki a matsayin mai laifi, wannan fada mai adalci ta yanke masa hukuncin haramtawa yarima saraki zama a cikinta na har abada, ma'ana yarima saraki zai bar cikin wannan masarauta a yau batareda ya fita da ko tsinke da ya zama mallakin masarauta bane,
Wannan hukuncin fada ne,
A ɓangaren hukuncin uba da ɗan sa kuwa maimartaba ya zare yarima saraki daga cikin ƴaƴan da ya haifa haka kuma yana umartarsa da ya ajiye dukkan abubuwan da yasan ya samu ne daga gareshi ciki har da kwalayen takardun karatun da yayi zuwa katin ATM na gidan sarauta har kan kayan sawa, haka ya haramta masa kusantar garin nan haɗi da iyalansa in kuwa yayi hakan to ya tabbatar yana cikin fushin Ubangiji".


Tuni fadar ta hautsine da hayaniya jin hukuncin da maimartaba ya yiwa yarima saraki, da yawa basu ji daɗin shi domin dai basu yarda ze aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba yayinda wani ɓangare na cikin gidan sarautar suke murna da farin ciki da abinda ya faru a lokacin.


Fadawa ne suka tsawatar nan da nan kowa yaja bakinsa ya tsuke dan dukan bafade ba wasa bane.


Tun fara jawabin waziri zuwa ga karanto hukuncin da magatakarda yayi kansa na duƙe batareda ya ɗago ba har saida aka gama hayaniyar.


Miƙewa yayi a nutse kamar yadda ya kasance ɗabi'arsa yasa hannu ya fara zare alkyabbar da ke jikinsa bata reda ya dubi kowa ba ciki kuwa harda mahaifinsa har lokacin kuwa kansa na kallon ƙasa.


Ajiye alkyabbar yayi gaban waziri kana ya duƙa ya cire takalmin da yake ƙafarsa wanda ya kasance mai matuƙar taushi na sarauta shima ya ajiye, hannu yakai bisa kansa ya warware naɗin rawanin dake kansa duk ya zube, hatta da zobunan hannunsa da wata ƴar sarƙa mai ɗauke da tambarin masarautar saida ya cire ya zube, duk wani abu da yasan ya danganci sarauta dake jikinsa haka ya ajiye su a wajen kana ya duƙa yayi godiya ya juya ya fita daga fadar zuwa ainahin part ɗin sa dake gidan sarautar yayinda duk inda ya wuce bayi da barori ke nuna shi suna ƙusƙus ɗin abinda ya faru.


Ko da yashiga part ɗin nasa dukkan katinsa na banki ya ɗebo ya ware na masarauta da nashi na kanshi, bawansa ya bawa ya kaiwa waziri duk katin banda guda ɗaya da yasan wahalar sa da guminsa suka samar da kuɗaɗen dake ciki.


_______


Kanta sade a ƙasa take zubar da hawaye Masu matuƙar ƙuna da raɗaɗi yayinda zuciyarta ke mata azababben zafi, ta rasa me tayi wa maƙiyanta da suka sako mata ɗan ta a gaba , ɗan da ta fiso da ƙauna a cikin ƴaƴan ta, ɗan da bata son taga ko ɗigon damuwa akan fuskarsa sai gashi yau maƙiya sunyi nasara akanta dashi har sun kai ga rabasu tana ji tana kallo ba yadda zata yi.


Sanarwar isowar yarima yasa ta maza ta saka hannunta ta goge fuskarta ta daidaita kanta kafin ta bada izinin shigowar tasa.


Gaban Mahaifiyarsa gimbiya halimatus~sadiya ya durƙusa ya miƙa gaisuwa sannan ya ɗaga hannunta na dama ya ɗora akanshi yana jiran ta saka masa albarka kamar yadda ta saba.


Danne kukan da ke taso mata tayi tareda furta masa albarka kamar yadda ya zame musu jiki kana ta zaunar dashi a gefenta.


Kauda kansa yake yi yaƙi bari su haɗa ido dan yana jin idanunta akansa tana ƙare masa kallo.


"Saraki nah, yau mamin ce ba'a son kalla?


Juyowa yayi ya fuskanceta ya kuma sunkuyar da kansa ba tareda yace komai ba.


"Naji dukkan abinda ya faru a fada, kar kaji komai a ranka mahaifiyar ka ta yarda da kai ta yarda da tarbiyyar da ta bawa ɗan ta dan haka ko kaɗan zantukansu basu sa zuciyata tayi rauni akan yarda dakai ba kaji ɗana".


Wannan karon sosai ya zubawa Mamin tasa idanu kafin kuma ya faɗa jikinta ya rungumeta har lokacin bece ko uffan ba kuma hakan bai dame ta ba kasancewar tasan in yana cikin fushi da ɓacin rai baya magana gudun furta kalaman da basu dace ba.


Shiru sukayi yana kwance akan ƙafarta ita kuma tana shafa kansa har zuwa wani lokaci kafin ya buɗi baki


"Mami ki samin Albarka zan tafi, zan yi biyayya ga umarni da hukuncin me martaba duk da ban kasance mai laifi ba".


"Albarka ta na tare da kai a ko yaushe a kowane hali, ina mai maka nasiha da ka kasance mai gaskiya a duk inda ka kasance, ka gujewa haram duk daɗinta duk babunka, ka nemi halal ɗin ka ko da a wuta ake nema, ka gujewa zaluntar wani dan daka zalunta gwara a zalunceka, ina mai maka nasiha da kaji tsoron Allah ka kiyaye al'aurar ka daga datti da dauɗar zina, kar ka fara ko da hangar gonar da bata kasance mallakinka ba, ka kasance mai tausayin na ƙasa da kai kuma mai taimako da duk ƙanƙantar abinda kake dashi, ka guji zargi domin Annabinmu ya hane mu dashi a ƙarshe ina kuma tunasar da kai ka zama me gaskiya da riƙon Amana, ka kuma kasance mai yafiya, kuma ina so ka lura a duk inda zaka zauna dole zaka samu masoya da maƙiya, to kaso masoyanka ka kuma yi taka tsantsan da maƙiyanka domin ko anan su suka fitar da kai daga gadon ka kuma abin tunƙahon ka, ka girmama kanka kar ka yadda a wulaƙanta domin kai ɗin mai daraja ne, kasa a ranka ina matuƙar so da ƙaunar ka sosai saraki nah".


Goge mata hawayen da ke fuskarta yayi kana ya sake rungumarta kafin a hankali ya zare jikinsa ya sumbaci goshinta sannan ya miƙe ya fice.


Fashewa tayi da kuka dan tasan shikenan sallamar tasu sai kuma watarana in Allah ya ƙaddara saduwarsu in gaskiya tayi halinta......✍️


©️ Khairert


☑️ote
Comments
Share fisabilillah














Ouummey 02 (7/28/2022 3:05 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*














Page 2️⃣
















_________________📖 Tafiya yake a nutse cikin kwanciyar hankali kai baka ce yana cikin damuwa ba alhalin a lokacin inda za'a bincika zuciyar sa to fa sai an tadda ta tafi gawayi baƙi saboda baƙin cikin sharrin da akai masa.


Duk yadda ya tsani kallo yau dole ya haƙura ya kau da kai domin kuwa ya san sai an kalle shin dan yau yasan sharrin da akayi masa ke trending a garin nasu. Tuno da facemarks ɗin da ke cikin aljihun wandan sa yasa ya saki ajiyar zuciya kafin ya laluba ya ciro shi kana ya maƙala a fuskar sa.


Ta ƙofar baya ya fice daga gidan sarautar dan yasan ƴan jarida nacan cike a main ƙofar shikuma a halin da ake ciki bazai so yin magana dasu ba, bawai dan ba shida abun faɗar ba, a'a sai dan yin biyayya ga umarnin mahaifin sa.


Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa Save more Bank dake kusa da unguwar sarki wato unguwar su, ATM ɗin sa ya zaro wanda yake ɗan ajiye kuɗi aciki sa'i da lokaci dan lalura in ta taso, bai san nawa ne ainahin yawan kuɗin ciki ba shi dai kawai yana zubawa ne ashe zai masa amfani a rana irin ta yau.


Dubu Ashirin yai withdrawing kana ya tare ɗan acaɓa ya kai shi tasha sai dai in da matsalar take ba wasu garuruwa ya sani ba a ƙasar ta Hawarya dan kaso mafi yawa na rayuwar sa ba anan yayi ta ba.


Jin wani karen mota na ta maimaita sunan Garin Manya yasa kawai ya nufi motar dan haka kawai yaji sunan yayi masa kuma ya na san zuwa garin.


Kuɗin mota ya biya 10k dan Garin Manya yana arewacin ƙasar Hawarya ne yayin da Garin Giwa ke kudanci dan haka akwai tazara sosai tsakani.
Tafiyar kwana da wasu awanni ce ta kai su garin na Manya, garin da akewa kirari da "BABBA DA YARO KOWA DATTIJO NE, MANYA MASU HALIN MANYAN MUTANE DA MUTUNTAKA, HAWARYA IN BA MANYA KANGO CE!


Sosai Yarima Saraki ke yawatawa da idanunsa kusufi kusufi ganin yadda Garin yake a cike, kowa se sana'ar sa yake ba ruwan kowa da kowa in ba neman arziƙi ne ya haɗa ba, masu dako, masu abinci , masu ruwa har ma da masu shayi duk acikin tashar.


Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin ina zai nufa dan ba inda ya sani a wannan garin, hasalima bai taɓa jin ko sunan ba sai ko yau balle ayi batun zuwa.


Driver ɗin motar da ya sauke su ne ya ganshi har lokacin ya na tsaye yayin da duk ragowar fasinjoji sunyi nasu wuri, bai masa magana ba sai da ya gama ƙare masa kallo tare da nazartar sa kana ya matsa kusa dashi.
Sallama yai masa suka gaisa bayan ya amsa, nan yake tambayar sa ina zashi yayinda take Saraki ya amsa masa da baisan inda zashi ba bashi da kowa a garin arziƙi ya zo nema.


Ƙare masa kallo driver ɗin yayi tun daga sama har ƙasa sai dai shi sam baiga alamar talauci ko wahala a jikin sa ba dan duk wahalar zaman motar da yasha bai hana sheƙi da ƙyallin da fatar sa keyi bayyana ba, sai dai banda haka ba wani kayane mai tsada a jikin sa ba, simple shirt and trousers ne wanda suka ɗan cukurkuɗe saboda zaman mota.


Gyaɗa kansa yayi bayan ya tabbatar wa da kansa insha Allah mutumin kirki ne dan sosai nutsuwa da hankali ke bayyana kansu a tattare dashi, wayar sa ya fito da ita daga aljihu tare da dialing number ƙanin sa ya Kira shi kan yazo yana neman sa.


Kallon Saraki yayi yana masa bayanin ga ƙanin sa nan zai zo ya rakashi inda zai sami wajen zama na haya in Yana so tare da ɗan aikin da baze gagara ba dan dillali ne shi amma na kasuwa.
Cikin yabawa da karamcin mutumin Yarima Saraki yai masa godiya.


Cikin mintuna ƙalilan ƙanin driver ɗin ya ƙaraso, yaro ne matashi dan bai wuce sa'an Sarakin ba, gaisawa sukai kana ya'yansa yai masa bayani, cikin fara'a ya jagoranci Saraki zuwa jerin wasu shaguna dake bakin kasuwar durumi wadda itace babbar kasuwar garin, ya kawo shi nan ne dan yaji sauƙin fita neman kuɗin sa tun da yace arziƙi yazo nema.


Dubu Ashirin da biyar ya biya kuɗin hayar shekara na ɗakin kana idriss ƙanin driver ya rakashi cikin kasuwa dan ya siyo kayayyakin da ze buƙata na rayuwar yau da kullum.
Kayan shayi ya siyo masu ɗan auki, se kayan sawa jeans da t shirt set huɗu, jallabiya guda biyu, silifas guda biyu sai takalmin kwalliya mai ɗan kyau suma biyu, bucket madaidaita biyu sabulun wanka da klin kowanne biyar biyar, sabulu wanka ne ya ɗan so ya basu matsala dan shi da mai tsada ya saba amfani sai dai a wannan gaɓar dole ya karɓi sauyin rayuwar da ya zo masa kwatsahan batare da ya shirya ba, dudu osun idriss yai masa recommending dan haka ya siya kusan guda goma sha biyar, dan shi ɗin kamar kifi yake wajen son wanka, se kuma katifa da suka siya irin wadda ake ɗin kawa rigar nan bayan mutum ya siya, suka siyo net da ɗan ƙaramin carpet da zai wa ɗakin daidai, labulaye suka ɗin ko guda biyu na ƙofa da window se kuma akwati mai sauƙin kuɗi da turarurruka masu ɗan sauƙi suma, kayan abinci ya siya kaɗan kaɗan,macroni rabin carton, sphagetti ma haka, se mudun shinkafa uku se ko wake mudu ɗaya, Maggi Leda biyu, gishiri da kuma kayan spices, Mai kuwa nacikin jarka ya siya dan yace bai yarda da ingancin wannan ɗan ɗurin ba.


Kafin kace me kuɗin hannun sa sun ƙare wadda a banki ya tsaya ya ciri 100k sedai yanzu yan canjin da suka rage a ciki ƙalilan ne, dole ya ciro wasu idriss ya na nuna masa hanya suka siyo 4 plates

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login