Showing 1 words to 3000 words out of 46793 words

Chapter 1 - DINYAR MAKAHO Book 1 Complete Document by Ummu Maheer Miss Green txt

10 Jun 2024

2247


ƊINYAR MAKAHO..
(Ta nuna a hannunsa)
UMMU MAHER(MISS GREEN






*SADAUKARWA:*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga uwayen ɗakina guda uku.


1-Hassana ɗan larabawa
2-Nabila dikko
3-Nabiha Aminu.
4-Bintu Umar Abbale


Allah ya ƙara muku lafiya da kaifin ƙwaƙwalwa da kuma basira.


*GAISUWA:*
Ina gaida masoya na ni ummu maher(miss green)aduk inda suke ina gaida marubuta baki ɗaya.
-----------


*BismillahirRahmanirRahim*


1-2


*Noor pov*
---------------------


. . . . . .A hankali nake tafiya ina hawaye,na kalli kayan jiki na duk sun ƙoƙe sun lalace uniform ne na ƴar makarantar secondary,sai dai ina da tsafta sosai badon tsaftar dana ke dashi ba,da babu abinda zai hana munin uniform ɗin.


Jakar hannuna ma irin ta leda ce duk ta yage,kana i'ya hango ƴan tsurarun littattafan dake ciki waɗanda baki ɗayansu basu fi guda biyar ba.




Sandal ne a ƙafa ta wanda shima ya gaji da siɗewa,nacin son makarantata shine yasa har yanzu ban dai na zuwa ba,amman kullum cikin zagi da tsangwama nake awajen ƴan makarantar mu.




Ni Noor na yabi kai na,saboda ni ba ƴar kowan kowa bace amman ina da kyau na nunawa sa'a.
Fara ce ni ƙal,ga dogon hanci,ƙaramin baki,mantan idanuwa,gashi ma ina dashi don har yankeshi nake.




Mutane da dama suna tankani akan kyaun dana ke dashi,sai dai ni ɗin malama ce ta fannin addu'ah.
Don bana taɓa zama ba tare da azkhar ba,tun ban kai ko'ina ba nake sanye niƙab da hijabi.


Ba na taɓa saka mayafi in fita,kullum hijabi nake sanyawa in fita. Kuma idan ma na ce zan saka mayafin ina na gansa,ni a wancen ƙarnin na ɗauka wasu ƴaƴan masu gata ne ke sanya shi,amman fa ni baya burgeni sam don mayafin baya cikin tsari na.




Makarantar na da nisa sosai da gida,haka kuma nake takawa inje,ƴaƴan gata kuwa sai dai a basu kuɗi su hau abin hawa.
Amman ni ko da wasa ma ban taɓa tambayar kuɗin ba,tunda nasan ba samu zanyi ba.




Shiyasa sai inyi daɓe kullum,har in isa makarantar don ni bani da wannan gatan.
Ina zuwa kai tsaye na tsaya wajen da ake assembly.
Duk kunyar kai na ta ishe ni,saboda yawancin ƴan matan duk uniform ɗinsu sabbi ne,idan kuma ba sabo bane to bai wani sha jiki ba.




Amman nawa duk ya yage,yasha manni da kuma fa-ci ga uban humra dana shafa me ƙamshi sai ka ɗauka uniform ɗinma sabbi ne.
Ƴan matan sai kallo na suke suna harara ta,wasu ma har toshe hanci suke wai wari nake.
Duk abinda suke ban taɓa tanka musu ba,amman tabbas abin yana cin zuciyata sosai amman tambayar dana ke yiwa kai na bai wuce,yadda mutane basa gane da arziƙi da rashinsa duk na Allah ne ba.




Sunfi son suga ne kuɗi nan zaki ga suna rawar ƙafa da rawar kai,amman ni a tsarina nafi son kasancewa ta ahakan,don haka jalla rabbi yaso ya ganni.
Ni shugabar makaranta ta wakilta don yin addu'ah,don haka na fito na fara rero addu'o'i kamar wacce aka yiwa wahayi.




Sannan na rufe da suratuk fatiha,wanda na rera ta da sanyayyiyar murya ne daɗi da taushi.
A nitse na yi karatu na,ya tafi da ɗibban jama'a don na iya karatu sosai ga ilimin addini har dama na boko ɗin.




Ni ce nake zuwa ta ɗaya acikin ajinmu,haka ma islamiyya har musabaƙar alƙur'ani me girma nasha cin ta.ayanzu ma haka an saka sunana a cikin gasar alƙur'ani me girma na ƙasa.




Ina komawa gida gabana ya fara faɗuwa sosai,don daman sabo nane matuƙar na fita to idan zan dawo sai naji gabana yana faɗuwa.
Ko don yanayin gidan namu ne oho?ko kuma saboda tsabar tsoro nane oho?.




Kai tsaye ɗakinmu na shige,babu kowa a tsakar gidan Inna Hafsatu ta gama abin cin ranar da take yi na siyarwa.
Yaran gidan mu kuwa duka sun tafi talla,kaf gidanmu babu yaron da yake zuwa makaranta sai ni.
Nima kuma ɗin ba mahaifina ne ya saka ni ba,ƙanin mahaifiyata ne ya saka ni don yaga yadda nake son karatun shiyasa ya sakani.
Yaransa kaf makarantar kuɗi sukeyi,kuma kaf ɗinsu babu wanda ake biyawa ƙasa da dubu talatin.
Amman ni uniform dana je na gaya masa,cewa ya yi wai in lallaɓa da wannan idan zan shiga S.s 1 wato aji huɗu ya canjamin.




Ranar daya faɗamin wannan maganar ƙwana na yi ina kuka,mahaifiyata sai rarrashi na take yi wacce ke ƙwance rai a hannun Allah.
Don komai sai anyi mata,kuma ni ce ke yi mata komai har tsarkin bayan gida dana fitsari.
Mahaifiyata bata da ƙanwa mace namiji ɗaya ne,kuma shima ƙanin tane amman baya taimaka mata da komai.


Ina tuna wannan na shiga cikin ɗakinmu,na hangi mahaifiyata tana cen gefe ƙwance,da alama ma ta yi wani abune a ƙwance kuma ta rasa yadda za ta yi.
Na goge hawaye na na ƙarasa kusa da ita na ɗago ta,ina kuka sosai ta ɗan shafa kai na tana ɗan murmushi wai duk don in ƙwantar da hankalina.




Amman ina kuka yaci ƙarfina sosai,na rungume ta na fara kuka me tsuma zuciyar me sauraro.




Ahankali ta fara magana bakinta yana kakkarwa ta ce.




"Haba Noor bana son kina kukan nan don Allah".


Ɗan murmushi nayi wanda masu iya magana suka ce yafi kuka ciwo,sannan na ce"haba umma ya zama dole in damu fa,shiyasa nace miki ni gwara in daina zuwa makarantar nan,tunda babu wanda zai iya kularmin dake.".


Ina faɗar hakan na fashe da kuka me mugun ciwo.


Kallona mahaifiyata take,sannan ta saka tafin hannunta ta fara sharemin hawaye,duk jikinta ya yi sanyi itama.


Ta rungumoni sosai ajikinta,tana kuka har ruwan hawayenta na taɓa bayana,sai naji zafin hawayenta tamkar zafin ruwan zafi me tafarfasa zuciyar duk wani bil'adama.


"Ya isa kukan haka uwata kinji?bana son kina yawan kuka a shekarunki bai kamata kina shiga irin waɗan nan tension ɗin ba".


"Hmm umma kenan kada ki damu,na riga dana saba da komai wallahi ke dai addu'ah ya kamata ki bini da i'ta sai kiga rayuwata tana albarka."


Shafo gefan kumatuna tayi sannan ta ce"to Allah ubangiji ya yi miki Albarka uwata ya baki miji nagari abin son kowa,me tausayinki akoda yaushe ko da kuwa bayan rai na ne".


Da sauri na kalleta wasu hawayen suka ƙara wankemin fuska sannan na ce"Umma!don Allah ki daina yawan zancen mutuwar nan baki ɗaya zuciyata bata yimin daɗi,please don Allah Umma".


Na faɗi hakan ina fashewa da kuka,Ummana ta ce"Allah sarki Noor mutuwa ta zamar mana dole,ko da cuta ko babu cuta idan mutuwa tazo dole ne ta ɗaukemu,don haka ki cire komai aranki ko da na mutu,ki yi rayuwarki cikin farin ciki,domin ni nasan Allah bazai taɓa tozarta ki ba,yadda na taso bansan iyaye na ba,bansan daga inda nake ba haka na taso cikin rayuwar ƙunci da nadama,na fara tunanin canjin rayuwa sai kuma na haɗu da namiji maras imani,wanda a kullum bai wuce yaga ya ƙonamin rai ba,haƙiƙa duk macen da ta dace da samun namiji nagari ta more rayuwarta duniya da kuma lahira."


Kallon mahaifiyata nake sosai,duk tausayinta ya cikamin zuciyata wasu hawaye masu zafi suna ta zubomin,wata irin muguwar tsanar mahaifina na ƙara ninkuwa a ƴar ƙaramar zuciya,wacce akullum bata ƙunshe da farin ciki sai baƙin ciki.


Na juyo muryar mahaifiyata tana ce wa.






"Haƙiƙa mahaifinki ya yimin ƊINYAR MAKAHO ne,ban taɓa tunanin zai juyamin baya ba,sai gashi ya juya min baya alokacin dana ke mararin kasan cewa dashi,amman ina godewa Allah daya bani ke a matsayin ƴa Noor haƙiƙa ke ƴa ce tagari,me son farantamin akoda yaushe".




Ta shafa kai na sannan ta ce"Allah ubangiji ya yiwa rayuwarki albarka ɗiya ta".




Ta faɗi hakan tana ƙara matseni acikin ƙirjinta tamkar wani zai ƙwaceni.






Haka na wanke mata jikinta tass,ina ɗan jin kunyar yin haka don ko babu komai mahaifiyata ce,aƙwai kunya a tsakaninmu amman babu yadda zanyi ƙaddara ta riga fa ta,sai haƙuri da kuma addu'ah shekara ɗaya kenan da Allah ya jarabci mahaifiyata da lalurar mutuwar ɓarin jiki,rana ɗaya akaga ta daina komai da kanta sai dai ayi mata.




Na shafa mata turare sai ƙamshi takeyi,ina kallonta ina shafa mata tana murmushi tana kallo na,duk sanda nake hidimta mata sai inga tana kallona tana murmushi,idan na tambaye ta ba'asi sai ta ce babu komai.


Naji muryarta tana ce wa"Oh mama na aƙwaiki da son ƙamshi Allah dai ya baki namiji me son turare sai aje ayi ta bulbulawa."


Sosai nake dariya har da tuntsirawa sannan na canja kuma yanayi zuwa kalar kuka na ce"Ayya Umma ni ai na cire babin aure arayuwata,ni babu abinda na sani sai kula dake da son kasancewa dake,yanzu kuma idan nayi aure fa duk bazanyi miki hakan ba,don haka don Allah umma ki daina zancen auren nan ya riga ya wuce."


Kallona ta yi sosai sannan ta ce"Emilli ni fa bana son kina haka fa?idan baki yi aure ba zama zakiyi ina kallon ki kamar tv ko kuwa me?don haka ki dai na ma wannan zancen".


Ta faɗi hakan tana kallona,na yi mamakin faɗin Emilli da tayi don bata fiya faɗar wannan sunan ba,tafi faɗar Mamana amman ba ta faɗar Emilli.




Ƙwaso kayan da mahaifiyata ta ɓata na yi,Inna Hafsatu bata tsakar gida,Sai Inna Saudatu da Ƙawarta Sahura.


Na ɗan raɓa na wucesu zuwa wajen famfo,don yanzu ko sannu na yi mata sai cibi ya zama ƙari,don wani lokacin har gwara Inna Hafsatu da Inna Saudatu, sam ba tada tausayi da imani ko kaɗan.


Wata irin muguwar dariya ta kyalkyale da ita sannan ta ce"hmm ni fa wallahi Sahura ina mamakin wasu mutanen?".


Sahura ta ɗanyi dariya sannan ta ce"ƙawata dame fa?".




"Hmm da abubuwa mana,wai ace mutum ya dinga kashi da fitsari a zaune kamar wata saniya ko kuma raƙuma"?.


Wata mahaukaciyar dariya suka k'elƙele da ita,sukayi tafi abinsu Inna Saudatu na kallo na tana watsomin wata irin muguwar harara.




Jikina ya yi wani irin mugun yin sanyi,ban san sa'adda na saki wani irin kuka me mugun ƙarfi ba.



.i'na kuka i'na wanke kayan mahaifiyata waɗanda ta ɓata,raina duka babu daɗi ahaka har na gama na share wajen tas tas,har na ɗibi kayan zanje in shanya sai kuwa Inna Saude ta ce"Ke!kada ki kuskura ki ɗoramin wannan banzan kayan kashin a kan igiyata,idan ku kun saba da ƙazanta ato ni dai ban saba da i'ta ba,don haka maza wucemin da gani tun kafin in canja miki wannan aljannat fuskartaki."


Kasa cewa uffan na yi saboda abin Inna Saude ya fara i'sata,don dai tasan ko da za tayi rawa akai na bazan ɗago in kalleta ba,shiyasa take tsokana ta salo salo,don dai in kulata wani abu ya faru ayimin wani sharrin.




Sai bayan tafiya ta Sahura ƙawar Inna Saude ta ce"caɓɓijan gaskiya wannan yarinyar idan baku tashi tsaye ba,sai ta hana yaranku aure acikin gidan nan,don haka wallahi tallahi ki tashi tsaye."


Ta faɗi hakan tana wani hararar baya na,Saude Ta ce"ke Sahura ni fa ban gane abinda kike nufi ba?".




"Hmm zaki gani yanzi kuwa,abinda nake nufi shine matuƙar maza na ganin wannan yarinyar to fa babu zaman lafiya,don baza a kalli yaranku a matsayin mata ba,aradun Allah a matsayin maza za'a kallesu,don kin san yadda wannan yarinyar take da shegen kyau kamar aljana,ga diri kamar ita ce ta ƙera kanta,don haka wallahi tun wuri ki tashi tsaye daman."


Ta faɗi hakan tana kallon Saude don tajo me zata ce.




Saude ta ce"hmm kuma kin san Allah ban taɓa wannan tunanin ba?ni dai kawai wani lokacin sai inyi ta kallonta,ina mamakin yarinyar don tun tana ciki muka hanata zuwa duniya,amman kuma sai gashi tazo shiyasa ni abin yake bani mamaki wallahi."






"Hmm ni dai Saude abinda zan gaya miki wallahi guda ɗaya ne,ko da kina mamaki don kin rasa yadda zakiyi da i'ta a'a baza ki barta tazo ta hana ƴaƴanki aure ba,yanzu don Allah ki duba ki gani?ga Safara'u ga Halima ga Aisha,Ga jidda duk ƴaƴanku ne kuma dukkansu babu sa'ar Noor aciki sai Jidda itama Jiddar ta bawa Noor wasu watanni don haka dai ki dage wallahi,don idan ma baki dage ba ƴaƴan Hafsatu sayi aure su bar naki azaune babu mashin shini."




"To yanzu Saude me kike ganin za'ayi?".




"Hmm abu ɗaya nake ganin za'ayi shine muje wajen boka,don mu amso magani akan ya sanyawa maza muguwar tsanarta ta yadda za ta rasa mashin mashini har abada."


Tafi suka sanya da shewa,ni da mahaifiyata muna jiyosu acikin ɗaki,Ina jin Mahaifiyata na ce wa.




"Hmm Allah ya ƙyauta,ya shirya mana zuri'a baki ɗaya ina amfanin son duniya alhali rabuwa zamuyi da ita?ko munaso ko bama so."


Na juyo ina kallon mahaifiyata,tana matuƙar burgeni don ƙwata ƙwata bata damu da rayuwar duniya ba,abinda yake gabanta shine ta bauta mahaliccinmu tamkar yana ganinta.


Ko da take fama da ciwo ko da yaushe acikin bautawa Allah take,rayuwarta baki ɗaya ta tafi ne a bauta.


Na rungumeta ina jin wani irin sanyi araina.




shafa kai na tayi sannan ta ce"wai uwata baza kije islamiyya bane?".


Ɗan turo baki nayi sannan na ce"kai Umma na don Allah ki kyaleni Allah yau bana son tafiya in barki ke kaɗai,alhali babu me kulamin dake ni yanzu ma na dai na zuwa makarantar ma kawai wallahi".


Na faɗi hakan cikin shagwaɓa ni daman gani auta kuma ƴar fari.


Ɓata rai mahaifiyata tayi sannan ta ce"haba mamana don Allah ki daina wannan zancan,saboda me zaki fasa makarantarki akaina?so kike tunda nu banyi ba kema ki taso cikin duhun jahilci ko me?gaskiya ban yarda ba."


"To Umma duk abinda kike so nima inason shi,Allah dai ya baki lafiya me ɗorewa".


Murmushi ta ɗanyi sannan ta ce"to Allah yayi miki albarka ƴata ya haskaka miki rayuwarki ko da bayan rai na".


"Amin".


Na ce ina me rashin jin daɗin kalmarta na mutuwa,duk sanda ta faɗi hakan duk sai inji babu daɗi araina amman babu yadda zanyi don nima na yadda da mutuwa ɗati bisa ɗari tunda ni ɗin na kasance musulma me yadda da ƙaddara me kyau ko mara kyau.


Na shirya cikin dogon hijabina har ƙasa,duk da ya ɗan sha jiki amman duk da haka ina ɗan maleji,wannan ɗin ma dana samu na ƙawata ne Hadiza don itace ta barmin shi da tayi sabon uniform,kusan shekara biyu kenan yanzu ni kuma har yanzu ba'a samu damar yimin sabbi ba.


Don haka nake lallaɓa abina,don masu iya magana sunce guntun gatarinka yafi sari ka bani.


Na ɗakko jakata na rataya,na samu humra na wanda shima Hadiza ce ta bani na bulbulashi don ni aƙwaini da wankan turare,don da ni wata me kuɗice kuɗina duk aturare zai ƙare.


Mahaifiyata tayi murmushi sannan ta ce"oh ni Emilli gaskiya aƙwaiki da son turare, yanzu wannan turaren da Hadiza ta baki har kin kusa ƙarar dashi?."


nayi murmushi sannan na ce"hmm umma ki gane ina son turare ne wallahi".


Ta yi dariya ta ce"gaskiya nafi kowa sanin hakan".


Ba ɗabi'a ta ce yin ƙwalliya idan zan fita ba,don haka ko hoda ban shafa ba amman yanayin fuskata sai ka ɗauka har ƙwalliyar ma nayi yadda ta bada fashion kyau tsantsa.


Na yiwa ummana sallama sannan na tafi,har na ɗaga labule mama tace"ayya Emilli bakici abincin ba?".


Na kalli ƙwanon da aka zubamin abinci,abincin wani ɗan tsurut dashi na ce"idan na dawo naci Umma".


Tasan hali na idan nace zanci to ba cin zanyi ba,saboda haka tace.


"Ato ni dai gashinan duk inda zakije ki dawo kici,don kinsan yau azumi nake".


Na yi murmushi kawai na tafi,don nasan tsokana ta takeyi ba wani abuba don tasan ba lallai inci ba.




ina fitowa na hangi Anty Inna Hafsatu tana abincin dare wanda ta saba yi akowacce rana.


Na wucewa ta don ko na gaishe tama bata amsawa,Bilkisu na gefenta ta zama kamar wata bazawara don ayanzu tana da kusan shekara talatin babu aure,abinda ta sani shine ta fice abinta kuma baza ta dawo ba,wani lokacin sai tayi ƙwana uku har sati sai ta gama yawon ta zubar ɗinta sannan ta dawo.




"Ke!".


na jiyo muryar Bilkisu tana kirana cikin tsawa.


Zuwa nayi na tsugunna agabanta,sannan na ce"Anty Bilkisu gani".


hararata tayi sannan ta ce"ke yanzu har kinyi babban ƙugun da zakizo ki wuce mu muba zauna?ni da mahaifiyata ko?saboda wannan nakasasshiyar mahaifiyar taki ta koya miki baƙin hali ko?".
Sunkuyar da kaina na yi,kalamanta na ƙarshe da ta faɗa sunfi ƙonamin rai na,na share hawaye na sannan na ce"to kiyi haƙuri ban ganku bane".


Ta zabura za ta dake ni,wani da ake kira Ali yazo siyan abinci ya ce"haba Bilkisu wannan fa bai kamata ba,kawai ku samu yarinya ku mayar da ita kamar ja. . . . .




Tun Kafin ya ƙarasa Inna Hafsa ta ce"Kai!!Ali babu ruwanka da shiga tsakaninsu wannan yarinyar da kake ganinta micijin sari ka noƙe ce,ba tada mutunci ko kaɗan ita fa ganin kanta take kamar ƴar sarkin sarauniyar kyau,shiyasa take wani haɗe fuska wai ita isashiya."




Ali ya ce"duk da haka dai babu kyau takurawa mutum don haka gaskiya ku kiyaye".


"To sannu ubana?ina ruwanka da maganar gidanmu?kada ka ƙara sakamin baki acikin duk lamurana idan ba haka ba,zan saɓa maka lamba ato".


Ta faɗi hakan tana wani ya mutsa fuska,ta kalleni sheƙeƙe sannan ta ce"tashi ki bani waje banza wacce ba tada asali".


A razane na juyo ina kallonta,a rayuwata babu kalmar dana tsana irin kalmar 'rashin asali'wacce kullum suke jifa na da ita.


Ni dai nasan kaf ƴaƴan babanmu babu wacce tayi kama dashi idan ba ni ba,nasha tambayar mahaifiyata akan wanene mahaifina?tunda kullum sai nasha irin wannan gorin,amman amsar ɗaya ce shine mahaifina,ta kance min in kalli fuskata in kalli ta mahaifina don inga irin kamannin da mukayi dashi,idan na kalla sai dai in fashe da kuka,saboda ni ban san abinda yasa suke jifana da wannan mummunar kalmar ba.


Ina hawaye na wuce makarantar Islamiyya ba tare dana biyawa Hadiza ba,wanda a kullum na saba biya mata amman yau saboda tashin hankalin dana ke ciki yasa kawai na wuce.ina jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login