daƙilar tab. Gaisheta na shiga yi, batare data ɗago ba ta amsa min. Kusan mintuna biyu muna zaune kamar masu neman gafara sannan ta ɗago tana cire eyeglasses ɗin idonta da bana raba ɗayan biyu na ƙara gani ne. A kaina ta zube idanun nata, sai kuma ta ɗan saki murmushi. “Ƴammata sorry fa. Tunda mukazo ban sake waiwayarki ba ko? Nayi busy ne da yawa.” “Ba komai Mama”. Na faɗa kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hanuna ta cikin hijjab. “Ohkay, yanzun ma bani da isashen lokaci. Maman Nana kije da ita wajen Sunusy ya gwadata a ɗinka mata uniform itama. Sauran kayan da zata iya buƙata kuma sai ki shirya zuwa anjima kuje shopping. Zata cigaba da zama a hannunki kafin tasan aikin da zatayi”. “To Hajiya in sha ALLAHU yanda kikace haka za'ayi. ALLAH ya ƙara nisan kwana da rayuwa mai albarka”. A hankali ta amsa da amin. Jin godiyar da Mama tayi nima sai nayi godiyar. Duk da kuwa wani irin abune mai masifar nauyi ke neman riƙe min ƙirji. Ban san a wace kalar rayuwa kuma na jeho kaina ba. Lallai na tafka kuskure. Inama Kano na nufa abina. Kai anya kuwa kuskuren nawa ba daga baro asibiti bane da nayi. (Tun daga baro gidan mijinki dai a Kano) wani gefe na zuciyata ya ayyana min. Jinai tsigar jikina yay wani irin tashi sama. A saman lips na maimaita kalmar “Miji”. (Kai ina ai bazan taɓa zama matar kowa ba sai Mansoor in ALLAH ya yarda).. “K! waye wannan kika hayo mana har sama da shi?!”. Muryar dana tabbata naji irinta a jiya ta faɗa cikin daka mana tsawa dai-dai muna sauka steps na biyun ƙarshe. Ganin yanda Mama Balki ta dakata da sauri cikin nuna shakka ya sani mamaki. Cike da girmamawa da sauke kai ta furta “ALLAH ya huci zuciyarki Aunty Azizat. Dama mun cika umarnin Aunty Mama ne. Dan itace ta buƙaci ganinmu”. Fuska ta wani yamutse tana balla mana harara. Da alama dai bata da abincewa. “K kuma uwar miye kike wani kallona? Shegiya mai kama da mayu!!”. Ta sake faɗa a fusace tana wani ware idanu a kaina sosai cike da nuna tsagwaran tsanar da ban san laifin dana mata ba. Duk yanda naso jin na bata girma a matsayin wadda na shigo gidansu da kuma girmata da tayi a shekaru dan zata iya kaiwa sa'ar Yaya Musaddiq amma sai naji hakan ya gagareni. Sai ma tsareta nai da idanu ina ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa.... Tauuuu!!! Naji saukar wani shegen azabebben mari asaman fuskata babu zato babu tsammani. A take ta rashin jin ya yunƙuro, bamma san lokacin dana ɗaga nawa hannun ba na sauke mata nawa yatsun biyar nima a saman fuskarta dake fara sosai a dama da haggu kuma. Daga gani kasan akwai ƙarin farin kanti dan har wani yellow-yellow takeyi. Tamkar mutuwa ta ratsa gidan haka yay wani irin tsittt na wuccin gadi. Kafin tai wani irin zuba min ido like wadda tai suman tsaye. Bama ita ba hatta da Mama Balki wani irin waro idanu tayi da ɗaura hannuwa duka a saman kai bakinta buɗe. Cike da dakiyar nan tawa da taurin kai na watsar da su tamkar banga komai ba na raɓa zan wuce. Dai-dai nan ta wani saki kururuwa da girgiza tamkar tsohuwar dodanniya ta damƙo min hijjab ta baya. Sai kawai ji nai an shaƙureni tare da jawoni baya. Tabbas da banyi azamar damƙe hijjab ɗin ta gaba ba da zamesa da sauri babu abinda zai hanata kaini ƙasa a wajen. Idan kuwa na faɗi zan iya buguwa, idan ma da tsautsayi zan iya rasa rayuwata. Gaba nayi gaba ɗaya, dan yanda ta fisga ni kuma na fisge sai yay kamar an hankaɗoni ne. Na gama sallamawa babu makawa a wannan gaɓar sai na kai ƙasan mayen marbles ɗin nan mai tsananin sheƙi da ɗaukar idanu tamkar zakaga fuskarka a cikinsa. Dan haka na runtse idanuna gaba ɗaya ina mai ambaton sunan ALLAH da sallamawa baki ɗayana...... ★★★★ Cikin mintuna ƙalilan Halime ta dawo ɗauke da tray. Haka kawai take ji bazata iya tsallake umarnin Abba ba. Duk da tana jin shakkar uwar ɗakinta tasan ta ƙetare umarninta. A hankali ta dire tray ɗin a gaban Abba dake zaune a dining. Tun fitowarta kuma yake famar binta da kallo ta gefen ido tamkar zai cinyeta. Ƙoƙari barin wajen take yi tamkar mai raɗa ya furta, “Baza'a zuba min ba?”. Duk shirmen Halime sai da taji zuciyarta ta tsarga. Hannunta na rawa ta shiga zubama Abba abincin. Ta kammala tana ƙoƙarin barin wajen ya katseta da faɗin, “Uhhm Kinga zo mana”. Nan ma ƙiri tai tana kallonsa, kafin cikin sanyin jiki tai ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa. Amma sai yay saurin girgiza mata kansa da mata nuni da kujera. Gabantane ya sake faɗuwa. Tai masifar waro idanu waje tana jijjiga masa kanta alamar dai bazata iya ba. Ƙyaleta yay, cikin gyara yanayinsa ya ce, “Minene sunanki?”. Ganin yanda yaci serious ya sata nutsuwa itama. Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa masa da, “Halime”. “Halimatussa'adiyya kenan?”. “Eh ta faɗa a hankali”. “Ina ne garinku?”. “Ƴan tumaki”. Ta bashi amsa kai tsaye. “Ƴan tumaki?”. Ya maimaita da ɗan waro idanu a kanta a tunaninsa shaƙiyanci ne. Amma sai a mamakinsa yaga ta jinjina masa kai na tabbatarwa. Kasa haƙuri yayi sai da ya furta “A wane state ne?”. Girgiza masa kai tayi da faɗin, “Katsina ne. Amma dai muna kusa da Musawa”. Jin sunan Musawa ya sashi fahimta Katsina state kenan ɗin dai da gaske. Humm mutanenmu da ganganci, ka turo yarinya mai cikar halitta jiki kamar wannan aikatau har wata jiha. Cigaba yay da faɗin, “Miyasa kike aikatau?”. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla. cikin rawar murya ta ce, “Inna ce tace Baba ya turani na samo kuɗin kayan ɗakin aurena”. “Ita Innar mamanki ce?”. “A'a gwaggona ta rasu tun ina ƙarama. Matar Babana ce, amma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Gwaggona. Bayan ta rasu aka aurama Babana ita dan ta riƙemu ni da ƙanina. Sai dai kuma ta tsanemu, kullum cikin mana mugunta take, gadonmu ma da Gwagginmu ta barin mana duk ta cinye. Gashi Baba baya iya cemata komai, shima tsoron masifarta yake ma”. Haka kawai yaji wani abu mai nauyi ya tsikarar masa zuciya. Tamkar walƙiya hoton Maman su Samraah yazo masa a cikin idanu. Da sauri ya ture zancen zucin gefe ya cigaba da faɗin, “ALLAH ya gafarta mata. Toke kina da saurayi ne da aka turoki samun kuɗin kayan ɗaki?”. Ƙasa ta ƙara yi da kanta sosai alamar jin kunya. Wasa ta farayi da yatsunta sannan cikin in ina ta ce, “Duk wanda yazo wajena Inna korarsa take yi. Tace saina haihu a gida ɗan shege ko zata bari nayi aure. A hakan ma sai su Lami sun gama yin nasu auren”. Sosai zuciyar Abba ta sake raunana da tsinkewa. Da ƙyar ya iya furta, ”Wacece ita Lami ɗin?”. “Ƙanwata ce ita ta haifeta da su Lailah”. Kasa sake magana Abba yayi tsahon lokaci. Sannan yace ta tashi taje ta cigaba da aikinta. Shima sai ya miƙe dan ya gagara cin abincin kuma ya koma ɗaki. Shirin fita yayi zuciyarsa na masa kaikawo. Bai wani jimaba ya kammala ya bar gidan batare da ya sake neman Halime ba.... Duk yanda Abba ke son yaƙar zuciyarsa game da abinda take ƙwaɗaita masa hakan ya gagara. Tun yana iya danne al'amarin har yana son fin ƙarfinsa. Yakan rasa sukuni a duk ranar da baiga Halime cikin idanunsa ba. Al'amarin tun yana bashi mamaki har ya koma bashi tsoro. Dan haka kawai yanzu rana tsaka zai baro kasuwa yayo gida dan kawai yaga Halime. Tun Mom na masa uziri idan yace mantuwa yayi harta fara tsarguwa da tunanin ya saka mata ido ne akan yawan yawon da take kwana biyun nan. Hakan ya sakata ɗan nutsuwa a waje guda. Yayinda shi kuma Abba zaman nata a gida ya zame masa takura. Dan idan tana nan ko giccin Halime baya gani saboda yanda take jin tsoron saɓa umarninta. A haka da ƙyar akai kwana huɗu. A daren cikar na biyar ya gagara haƙuri ya nufi gidan abokinsa Alhaji Sadisu mai-agogo. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Alhaji Sadisun. Shiko ya dinga dariya yana tsokanar Abba har sai da yaga ya ƙulu sannan ya bashi haƙuri tare da bashi shawarar yanda ya kamata suyi dan ganin komai ya tafi dai-dai. Sosai shawarar tayima Abba kuwa. Ya tafi gida cike da farin ciki.... ★★★ Wata irin ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin na faɗa kan abu mai taushi saɓanin inda na gama sadaƙarwa zan faɗi. Rawar tsorata dana riga nayi jikina keyi, dan haka na sake ƙanƙame abinda na faɗawar ina mai sake matse idanuna dake a kulle. Sai dai me, wani kalar wakitawa ƙitjina da zuciyata sukayi a lokaci guda, a take tsigar jikina ta fara mimmiƙewa. Gabana ya sake faɗuwa jin yanda wajen ya koma tsitt tamkar babu wani rai mai numfashi. Gaba ɗayan numfashina ne ya ɗauke daga illahirin gangar jikina nima, tare da wata irin girgizawar zuciya taban mamaki. Sake ƙanƙame abinda na faɗawar dai na sake yi. Wani irin jifff!! Ƙirjina ya sake bugawa a karo na biyu jin tabbacin mutum ne, mutum ɗin kuma daga ji ba jikin mace bane, sannan ƙamshin dana shaƙa na neman jirkice min tunani gaba ɗaya. Ga tsitt ɗin da wajen ya ɗauka lokaci ɗaya tamkar an tsaida numfashin kowa da komai na gidan. Sassauta riƙon da naima koma minene na fara yi, sai kuma na shiga ɗago kaina a hankali ina ƙoƙarin buɗe idanuna. Akan farin riga armless ta sport wear fara tas na fara saukewa. Sai ƙaton damtsen hannu dake a murɗe sosai fari mai ɗan duhu kaɗan dan fatar batai irin tas ɗin nan na mahaukacin fari ba. (Jikin namiji) zuciyata ta ayyana min, dai-dai da bugar hancina da ƙamshin turarensa ya sake yi. Cikin wani irin sauri da shiga tsananin tashin hankali na ɗago gaba ɗayana na sauke idanuna akan fuskarsa.........✍️ _🥺🥺Hukumar tawada da alƙalami tace a tafi yajin aiki.🥱_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* [03/05, 2:58 p.m.] +234 907 711 8052: *_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_ __________ Toh Nazo maku Da kayan arziki Kudai kunsan mata sai da gyara Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne Muna da Shedaniyar gumba Gumba mai saying Garin mai kabbara Mai dalalan miyau Wayyo dadi Mai bunsuru Dan jarida Soyayya dole Bakin kyalle Tadire ta girke Gumba mai likkafani Maza taye Zumar kwakwa Zumar ridi Zumar dabino Zuma mai ma'ul ijaba Farin jini Mallakoki Gumba kalla kalla da dai sauran su A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba Ga kuma maganin slimming Gyaran nono Maganin hips Maganin Kara kiba Da dai sauran su Kayan mu tested and trusted ne Muna maraba da masu siyan Daya ko sari Muna Nan cikin garin kaduna Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah Ni ce taku har kullum AMINA GACHI 07034404975 CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE KADUNA Phone no 07034404975 ____________ .......Ƙamshin turarensa mai armashi daya bigi hancin Halime ya sata ɗagowa a zabure. Hakan yay dai-dai da isowar Abba inda take. Aiko suka kusa cin karo. Tsalle tayi baya jikinta na rawa. Tako tafi zata zube ƙasa yay saurin riƙota. Rawar jikinta ce ta ƙaru sosai sai faman zazzare idanu take tamkar bazazzage a hannun kanawa (😂😜lol). “Please kinga calm down nutsu”. Abba ya faɗa da sauri ganin yanda duk ta gigice. Kasa nutsuwar tai, sai ma mutsu-mutsun son ƙwacewa da take kawai daga hannunsa. Sakinta yay, aiko ta kwashi tsintsiyarta ta zura da gudu hanyar kitchen dan nan ne kawai takema kallon wajen ɓuya. Murmushi Abba ya saki mai haɗe da ƙaramar dariya yana girgiza kansa da jinjina wawtarta. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai kauri zuciyarsa na sake tabbatar masa da yanayin dake son hawa kansa batare daya shirya ba. Dan duk yanda yake son ƙaryata zuciyar tasa hakan ya gagara. Dole ya haƙura a yau tare da tabbatar da da gaske fa son yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba yake. Lallai yasan shima ya taro match babba, mai aikin gidansa fa. Randa Jalilah tasan wannan sirrin nasa sai abinda ALLAH yayi ai. Maybe yankan raguna zata musu shi da yarinyar nan.... 📯📯📯📯📯 Zancen Bahijja ya tabbata. Dan kuwa bata dawo ba sai bayan sallar magrib. Haka ta shigo idanunta balo-balo alamar taci kuka. A take zuciyata ta motsa. Sai dai bance da ita komai ba ganin itama ta dake tana min murmushi. Dan cike da kulawa ta shiga faɗin, “Lah baki je falo ba bayan gasu A'i can duk sun dawo su tun ɗazun. Su Mama Balki ne kawai su sai anjima saboda girkin masu gidan kowa da abinda yake so. Balle ma Uncle Boss yana gida aikin yafi tsamari kodan gayyar yaransa”. Dariya sunan data faɗa ya bani, wai Uncle Boss. Amma sai haka kawai naji gabana ya faɗi, cikin ƴar in ina nace, “Waye Uncle Boss kuma?”. Numfashi ta sauke mai nauyin gaske. Sai kuma tai murmushi da faɗin, “Uncle boss shine gidan dama ƙarfin ikon kidan baki ɗaya. Shine babban ɗa a gidan kuma. Bari dai kada na shagala da yawa banyi sallar magriba ba, har an kusa isha'i. Kuma Malam da anyi isha'i idan ka makara zuwa makarantar dare duka yake yi”. Da kallo kawai na bita dan babu abinda na fahimta a zancen nata. Sai kawai na cigaba da lazimina harta fito ta kabbara salla ban sake cewa komai ba. Tana idarwa ana kiran sallar isha'i. Dan haka muka tashi a tare muka kawota. Muna idarwa ta miƙe ɗauke da Alkur'ani tace na taso muje wajen karatu. Ban musa mata ba na tashi na bita kuwa. Mun samu duk kusan ƴammatan nan sa'anninta suma sun fito, a tare muka rankaya waje. Can muka nufa cikin wajen wasannin nan dake ƙwanyar da hasken lantarki tamkar rana. Hakama tsakar gidan yake tako ina. Ga hasken ya sake ƙawata gidan tamkar ba'a duniya ake ba. Mun samu malam har ya iso, dan haka babu wani ɓata lokaci muka zazzauna a ƙatuwar dardumar dake shimfiɗe a wajen. Yayinda shi kuma yake zaune a saman kujera abinsa. Kamilun mutum dattijo. Dan shekarunsa da gashin fuskarsa zuwa kansa dake fari fat ya isa tabbatar maka da shi ɗin ba yaro bane ba. Mun gaishesa a tare, ya amsa mana da kulawa kafin a fara karatu babu ɓata lokaci dan kowa ya riga yazo. Naji daɗin karatun, duk da kuwa nayi sauka tuni. Kusan awarmu ɗaya da rabi dan sai takwas da kusan arba'in muka tashi. Sai dai yanata kallona amma baiyi magana ba balle tambayar dalilin shigowar baƙuwar fuska ajin karatunsa. Can sashen muka koma, sai dai wasu basu zauna ba suka shiga canja uniform wai zasu koma can sashen su ƙarasa ayyukansu, ciki kuwa harda Bahijja da tafi kowa rawar jikin komawa. Sun bani matuƙar tausayi, amma dai bance komai ba dan bani da abin cewar. Shiru babu wanda ya dawo a cikinsu ni dai har na fara hamma saboda sabon barcin wuri da nayi tun fil azal. Mama Balki data rigasu dawowace tace naje na kwanta. Babu musu na miƙe na wuce ɗaki kuwa, dan ni kaina nasan ina buƙatar barcin, amma ba lallai tunanin dake danƙare a zuciyata ya barni yinsa ba. Koma dai yaya ne zanyi yaƙi da zuciyata wajen ganin na yisa kodan na samu nutsuwar fuskantar abinda ke gabana. Dan Alhmdllh, ɗan zuwa islamiyyar nan ta ɗazun da nayi sai nake jin kamar yanayin da nake jin kaina sanda nake a gidan Hajiya ya fara sakina... A hankali na buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi irin na mai barci. Akan Bahijja na sauke su. Da mamaki nake kallonta. Ta sakar min murmushi da nuna min agogon ɗakin. Sosai na waro idanun waje mamaki fal raina na ganin asubahi. Kenan nayi barci sosai yau. Tab ɗi, abinda na daɗe banyi ba a rayuwata. Dan ko kwanciya asibitin da nayi ni shaida ce akan allurar da suke min ke bugar da ni bawai normal barcina ba. Bayan mun idar da sallar asuba muka gaisa da Bahijja. Itama A'i dake faman ɗauke min kai gaisheta nayi. A mamakina sai naga ta amsa da sauri har ma abin nata ya bani dariya. Amma sai na danne banyi ba sai dai guntun murmushi kawai. Alkur'ani na ɗauka na fara karatu, yayinda A'i ta shiga wanka, ita kuma Bahijja ta fara ƙoƙarin gyara mana gadajenmu. Ina nan zaune harta kammala tace na koma saman gado zatai shara. Hakan kuwa nayi, tana kammala shara A'i ta fito, a gurguje ta ƙarasa morping itama ta shiga wanka. Bata jima ba kamar A'i ta fito. Su dukansu shiri sukayi a cikin Uniform ɗinsu wankakku harda guga dan na fahimci suna dasu ne da yawa ba ɗaya bane. Suna kammalawa harda fesa turare, na fahimci hakan kamar yana cikin dokar aikinsu a gidan zama cikin tsaftar jiki. Fuskar Bahijja da murmushi ta kalleni. “Sis.. mu zamu wuce aiki. Ki kwanta ki hutama ranki kafin a kawo break fast. Tunda kinga har yanzu ba'a sanar da aikin da zakiyi ba, ALLAH dai yasa ba tafiya dake aunty Mama zatayi ba”. “Waye aunty Mama?”.
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN