NI DA YAYA SADEEQ BY SIDDIQAHTUL KHAIRY YAHYA .doc

Author :  Saddikatulkhair Yahya Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 21

54K to 57K   out of 62.6K words

akwai massalaci anan ne".

Fadeelah dake kokarin fiddo da sabon silifas a cikin akwatin ta tace "eh man ai nan da kike gani babu abin da babu don kinga har da islamiya ma, kuma har sauka ake yi"

Daga haka ban kuma cewa komai ba, Alwala muka je mukai muka tafi masallaci.

To da dare kuwa gaza bacci nai don kuwa banda juyi babu abunda nike, da yike bacci barawo ne ban san sanda ya kwasheni ba

Washe garin tun shida Fadeela ta tada ni, saboda nai wanka tace "idan banyi da wuri ba zan makara gurin zuwa class, to bayan nayo wanka nazo saka yunifom yace dauke ni inda kika barni, neman duniya ban ganshi ba, Fadeela na fadamawa tace" to ke a'ina kika barshi?" nace nan saman akwati na fa na dora shi"

Cikin takaici Fadeela tace "ai kuwa gwara ki daina wahalar nema dan an sace inada sabo bari na baki, amma kin San daya bazai isheki ba dole sai kinje office din shugabar majar kin karbo wani,

Cikin mamaki nace" ikon Allah mutum ba shi ya aje abu ba yazo ya dauka".

Fadeela tace "wannan ba abun mamaki bane bari na fiddo miki kisa kada mu makara.

Bayan ta fiddo min na saka, kallo na tai tace" Siddeeqah kinga yadda yunifom din nan suka miki kyau?"

Ido na zaro waje nace" ke dai kin cika zolaya wallahi"

Tace "daga fadan gaskiya".

Nace "ba wani gaskiya ke dai tashi mu tafi, tunda mun gama shiri,

" To" Fadeela tace min kana ta Mike? muka fito, kitchen muka nufa, bayan mun karbi breakfast din guri muka nema, bayan mun gama ci muka tafi class.

Wannan kenan



NI DA YAYA SADEEQ


" ?%e& (3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE e&?%" `??

No editing

Chapter 31

____Kwanci tashi asarar me rai kuma babu wuya a gurin Allah.


a bangaran su Zuby abinda ya faru kuwa shine,


kwatsam wata rana suna cikin gidan da suke yin mitin, kamar kullum yadda aka saba, manyan mata suka zo suka zabe su suna tsaka da sheke ayar su, mai gadin su taji ana buga get koda ta bude matan yan sanda ta gani da bazata iya shaida a dadin su ba, ture ta sukai suka kutsa cikin gidan kai tsaye, har cikin katon falon suka shiga inda suka ganewa idan su zahiri take suka shiga jibgar su, ko wacce sai da taji saukar kulki a jikin ta tasan cewa an musu cune, haka yan sandan suka tarasu a guri guda, can na hangi Zuby da Lubancy sai raba ido suke, koda suka fito motocin yan Sanda ne sunkai goma Sha biyar da DSP Sadeeq ya ke jagoran ta, haka aka tarkata su aka kai su sell, koda labari yaje kunnen Abban Zuby ba karamin cikin tashin hankali ya shiga ba duk da alokacin baya Nigeria gashi bikin ta da Maheer a lokacin bai huce saura wata uku ba, ba shiri ya dawo nigeria, bai zarce ko ina ba sai gidan sa, da zuwa direct dakin Mama ya nufa koda ya buda kofa take kansa ya fara juya masa, saboda abinda ya gani, Mariya ce kwance bisa kan gado ga kartai har biyu suna kwanciya da ita, take ya fara ambatar innalillahi wa'inah ilaihi rajiun, haka yai ta ambatar sunan Allah, Mariya kuwa bata ji shigowar kowa ba sai alamar fita da taji, hakan yasa tace ma abokan shashan cin nata "su dakata, kamar taji alamar mutun" amma sukai burus da ita suka cigaba da aika aikan su, tuni Abba ya kira yan sanda kiran gaggawa, ba'a dauki wani lokaci mai tsayi ba sai gasu, nan ya nuna musu dakin da su mariya suke haka suma aka tarkato su sai police station, anan Abba ya sake ta kuma ya mata Allah ya isa, saboda ta cuce shi kuma ta cucu rayuwar yarsa, yace taje ta gani taci amanar aure, shiko Sadeeq koda yaga Zuby a cikin su baiyi mamaki ba Saboda abokin sa Maheer ya fad'a masa, kuma dama tun sanda sukai fadan-nan bai kuma koma mata ba, hakan yasa da Maheer yace mai ita zai aura bai ji komai ba, Maheer abokin Sadeek ne tare suka gama secondary school din su dake nan Abuja, abunda ya jawo to nan asirin su shine, Sumayya da ake cewa yar leken asirice, ashe kanwar Maheer ce kuma shi yaturo ta tun kamin ya dawo kasar Kamal makocin su Zuby ya fad'a mai abunda yake zargi akan Zubyn, hakan yasa yace kanwar sa tayi basaja taje, abunda basu sani ba har Video tai musu alokacin kuma ita ce wacce ta jefar da takadda a gurin wannan shakatawar, hakan yasa Maheer sanar wa Sadeeq shi kuma ya hada rundunar yan sanda, yayin da Sumayya ta musu jagoranci ta kai su har bakin get din, kunji ta yadda asirin jigagan yan luwadin ya tonu.


koda DSP Sadeeq yazo yana tambayar matan Dalilin dayasa suke yin wannan mummunar dabiar saboda yanaso ya gama hada bayanai ya mika su kotu,

Daga wacce zata ce kawar tace tai sila sai wacce zata ce mijin ta ne baya bata hakkin ta, haka dai ko wacce da abinda zata ce, abinda ya qara bama Sadeeq takaici harda matasan yan mata da bazasu wuce 18 to 19 ba, Zuby dai ba bakin magana saboda yadda take jin kunya ji take kamar ta ha'ka rami ta burne kanta, acikin su wanda yafi tsayawa Sadeeq a rai shine abinda daya daga cikin su tace wai ita da kishiyar ta ne suke yi a gida, har suka shiga cikin wani group na yan madugo zallah, daga nan aka kara buda musu ido, sosai Sadeeq yaji maganar ta dake shi tsoron matan yanzu ya kara kama shi, Allah abin tsoro mata abin tsoro, lalacewar har ta kai ga kishiya ta nemi kishiyar ta, saboda sun maida aure ba a bakin komai ba, sunyi Fatali da darajar sa sunci mutuncin sa, badon Annabi Muhammad ya roka kar a halakar damu ba, da tuni an dade da kifar damu, saboda duk wani abu da aka halakar da mutane akai muna aikatawa, an halakar da wata Al'umma akan tauye mudu da suke, ku fada min shin yanzu bama tauye mudu? An halakar da wata Al'ummar, akan luwadi, shin ku fada min yanzu bama aikatawa, an halakar da Al'umma da dama saboda yawan sabama ubangijin su, amma ku duba fa maye ba'a aikatawa a wannan zamanin, shan giya caca zina luwadi madugo, tauye hakkin wani zagin shuwagabanni cin amana, rashin yiwa iyaye biyayya, zagin malamai, cin dukiyar maraya, da dai sauran su, Allah ya bamu ikon gyarawa, idan muka gyara muma sai muji dadin rayuwar, haka dai yai ta jinjina lamarin yana yin rubuce rubecansa, a farar takarda, shi wallahi mamakin masu luwadi da madugo yake yi ko mai suke ji a jikin juna, ace wai mace da mace namiji da namiji, masifar tayi yawa dole annoba ta damemu shin ko kun sar masifar da yake haifarwa? Wallahi duk wanda ya mutu yanayi bai tuba ba wuta ce Makomar sa. Dan yanzu abin yayi yawa, iyaye ku saka ido akan yayan ku ku lura da tarbiyar su, ko kawa ce idan tazo wajan yarki kika ga ana shiga daki a rufo kofa wallahi ki bincika, zamani ne Allah ya kawo mu dole sai mun dage mun tashi tsaye akan tarbiyar yaran mu, saboda zaki tabawa yarinyar ki tarbiya rana daya wata shegiyar kawa tazo ta rushe.



To bayan kwana biyu kotu aka mika su, inda Alkali ya yanke musu hukuncin shekara goma sha takwas-takwas a gidan yari tare da horo mai tsanani, akace duk wacce hukuncin bai mata ba zata iya daukaka kara.



ita kuwa Mariya da abokanan fasikancin ta hukunci jifa aka yanke musu har sai sun mutu kasancewar su masu aure kuma sukai Zina, oh ni rayuwa ina zaki damu wai kina matar aure wace irin jaraba ce da bazaki kama kanki ki rike mutuncin ki ba, saboda ki samu Aljannar ki Allah dai ya ganar damu.

* * * * * * * * * *
Bayan wasu shakaru haka Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin hukunci Allah gashi har mun rubuta jarabawar mu ta JSCE,, aminci da shakuwa mai karfi ya cigaba a tsakani na da Fadeela, sosai muke kyautata wa junan mu, dan Ammi komai tare take siyo mana, haka nima komai tare yah Sadeeq ke kowo min idan zai zo min bizitin, haka idan nice naje gida idan zan dawo hutu komai biyu nike zuwa mana dashi, dan sau biyu su Momy da Inna suka zo min, na kyara girma na ban mamaki ni kaina mamakin yadda nai girman nike, idan ka ganni sai kace na kai irin shatakwas din nan, ga wayau na masifa da nai, sosai kama ta da Ammi take kara bayyana, dan dalibai da dama ce min suke diyar firinsifal.

na hadu da Sadiya kanwar yah Farooq a lokacin da yaya Sadeeq yazo min bizitin yasa aka kira ta, itama tun daga ranar muke zumunci amma ita ba hostel dinmu take ba, duk inda ka ganni zaka ga Fadeela da Sadiya haka ake cemana yan ukun Firinsifal, dan da angama karatu muke zuwa ofishin ta, sosai yanzu nike jin turanci dan ko magana da hausa ban fiye yi ba, dan jina nike babbar yarinya.


Senior Jamlah kuwa sun bar makarantar, sunyi candy, kuma koda tana nan ma, ban bari ta dake ni ba, dan kuwa karar ta nakai staff sai dai zagi da tsangwama idan mun hadu, sosai school Momy na Saudat take kula dani, shiyasa ban wani sha wuya ba gashi yanzu har zan barta.


Yau ne muke zana fefar mu ta karshe kuma cikin azumi ne home economy ne ya bada wuya gaskiya, duk wacce ta fito hol zakiga tana goge gumi, bayan na gama na fito na iske Sadiya zaune na jiran mu, nan muka shiga farar yadda fefa tai zafi, muna cikin firar sai ga Fadeela nan itama tace, "wash rabon da fefa ta bani wuya irin na yau wallahi na manta ku tashi muje mu shirya, dan da alamar wasu daliban ma sun fara tafiya".


hostel muka mufa inda a hanya muke ta haduwa da class mate din mu da akazo daukar su , dama duk munyi musayar numbers saboda dayawan wasu daga cikin mu ba nan zasu yi senior ba,



Ahaka muka karasa hostel muka shiga hada kayan mu bayan mun gama muka raka Sadiya itama ta hada nata.

Office din Ammi muka je, da sallama dauke a bakin mu muka shiga inda muka same ta a tsaye tana hada takardu, bayan mun gaishe ta, tana dariya ta kalle ni tace Yata duk kinfi kowa kosawa ko duk zumudin za'a Dande ne? tunda kince acan zakiyi Sallah"


Dariya nai kasa kasa nace, "Allah Ammi ba haka bane kawai kewar gida nike".


Tace "ai na gama ku tashi mu tafi gida daga can sai mu dauki hanyar Abuja"



Dama tuni n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ayi waya da Yah Sadeeq nace ba sai yazo daukar mu ba, Ammi zata kawo mu, dan tace "tana son zuwa ta gaida Inna saboda ina yawan bata kabarin ta"



A tsakar gidan su Fadeelah muka tarar da kannen ta yan biyu wato , Aysha suna kiran ta da little easha sai Aliyu suna ce mai Dady, haka yaran suka taho suka rungume mu dama mun saba dasu dan ina zuwa gidan idan anyi mana hutu yaya bai zo daukana da wuri ba, muna wasa da dariya muka karasa falon gidan, ciki Ammi ta shiga dan ta shirya haka ma Fadeelah, ya rage da gani sai Easha da Dady da Sadiya sai wasa muke, ahaka Ammi ta fito ta iske mu tace "ina Fadeelan?"


Sadiya ce tace "bata fito ba"

"Fadeelah Fadeelah" Ammi ta kwala mata kira, sai gata ta fito itama tayi fes da ita cikin shigar wata atamfa mai tsadar gaske, atamfar tana da kaloli da yawa a jikin ta mai digo digo, yayin da ta yafo mayafi brown, haka jakar ta da takalmin ta duk brown soboda akwai brown a jikin atamfar, duk da Fadeelah ba fara bace amma tayi mutukar kyau, yayin da Ammi ke sanye da doguwar riga yar dubai mai ruwan kasa ta yana mayafin ta fuskarta sanye da siririn gilashin ta na lura bata rabo dashi, dan ga little Easha nan duk sanda zan ganta itama dashi nike ganin ta,


Ammi ta kalli Fadeelah tace "dadi na dake nawa duk sanda aka shirya tafiya kece a baya".



Fadeelah tace "haba Ammi yanzu haka na dade?".


Ammi bata kula ta ba tace "ku tashi mu tafi rana na dad'a yi"

Dama su little Easha a shirye suke saboda haka muka dauki hanyar Abuja, a hanya muka tsaya a restaurant muka siya abinci mukaci, da misalin karfe biyar na yammacin ranar juma'a muka isa makekyan gidan su Khadija, yayin da Ammi tai hon mai gadi ya bude mata ta sulala ciki, gurin faking din motoci tai faking kana ta bude mana kofa, da gudu na fito ina ihu na nufi cikin gidan Momy da Ummi na tarar zaune suna cin kayan marmari a falo, fadawa cinyar Momy nai, itama kamani tai tana min oyoyo, ban tashi daga kan cinyar ta ba sai ga Ammi ta shigo bakin ta dauke da Sallama, koda Momy ta dago kai da Zimmar amsa sallama, sai tai maza ta tureni ta Mike tana fadin "Amina" ita ma Ammi idon ta zaro tace "Aisha" kollon kallo muka fara bin su dashi, ganin kowannen su idon sa na zubar da kalla, a dai dai lokacin Yah Sadeeq ya shigo gidan ganin Momy da Ammi na zubar da kwalla yasa yai turus yana jimami ya karaso falon.


Ganin basu san ma ya shigo ba yai gyaran murya yace "Ammi Momy ku zauna mana lafiya"


Momy ce tai karfin hali tace "dan Allah ku fada min mafarki nike ko kuwa ido na biyu ne Amina ce fa kanwar Daddyn ku goggwan ku Amina ce fa"


Ni kuwa da naji an ambaci Amina mikewa nai zunbur ina dad'a kare mata kallo, a cikin wannan yanayin Daddy da Umar suka iske mu, koda Yaga Ammi take yashiga murza ido yana fadin "Aisha Aisha kina ganin abinda idona yake gani ko kuwa gizo din take min kamar yadda ta saba?"


Momy tace "ba gizo take maka ba Aminan ka ce ita ce"


Take muka ga Daddy ya fadi yana mai sujja ga Allah, bayan ya dago yazo ya rungume Ammi, nan fa dakin ya kaure da koke koke baka jin karar komai sai shash-shekar kuka, harda su little Easha mukai ta kuka wuy-wuy shi kuwa Sadeeq ba hawayan amma idon sa yai jajur, mun dauki lokaci mai tsayi muna yi daga bisani yah Sadeeq ya shiga bamu hakuri, to bayan komai ya lafa Ammi ta samu guri ta zauna,


ni kuwa tashi nai na haura sama, dan na samu nai wanka na canza kaya, dakin Khadija naje dan na amsa mukulli na amma sai naji kofar ta a rufe, hakan ne yasa na nufi ban garan yah Sadeeq, nayi sa'a a bude na samu kofar, koda na shiga ban zarce ko ina ba sai bathroom din sa, ina shiga na hada ruwan wanka, koda na fito kamshin turaran sa dana ji ne ya tabbatar min da yah Sadeeq ya shigo, ina waigawa na gansa zaune a bakin gado, ya kura min ido, kunya ce ta kamin saboda tawul din dana daura dan karami ne ko cinya ta bai gama rufewa ba, na kasa dago kai na kalle shi, shi kuma ya kasa dauke kai daga gareni, hanyar fita bedroom din nayi amma sai naji kofar a kulle gam, jiyowa nai na kalle shi yana Murmushi yace "ina zaki bayan na rufe kofar ai tun na shigo na fahimci kina ciki da naji alamar ana wanka, nasan babu mai shigo min daki sai ke, shiyasa na rufe kofar dama a yunwace na dawo, ashe zan samu mai kore min kishin ruwa na"

Gaba na ne ya shiga buguwa dan yanzu sarai nasan maye aure kuma nasan abinda yake faruwa a tsakanin miji da mata, ji nai kamar an samin shokin na kasa gaba na kasa baya, haushin kaina ya kamani dana shigo bangaren sa, taku naji anayi da sauri na juye tsaye na gansa gaban madubi yana cire kayan jikin sa, gabana ya cigaba da faduwa, na shiga yi masa magiya, amma ko kala bai ce min ba, ya shige bayi abin sa, ya dauki lokaci mai tsayi can sai gashi ya fito da tawul daure a kugun sa, ba karamin kunyar sa bace ta kamani amma shi sai naga ko a jinkin sa, gefe na kawar da kaina saida ya gama shiryawa yazo gabana, kama hannu na yai yazo ya zaunar dani akan bakin gadon, shima ya zauna muna fuskantar juna yace "nasan yau rana ce ta farinciki a gareki, saboda Allah ya amsa adduar da muka dade munayi, ina tayaki murnar haduwa da mahaifiyar ki Siddeeqerh" ni dai ban ce mai kala ba, ya daura da "gashi kuma kin zana JSCE din ki shima ba karamin nasara bane". hannu na ya kama ya fara murza tafin hannu na, nai sauri na kwace ina fadin "maye haka yaya ka buda min kofa na fita kada aga na dade, nasan yanzu sun fara nema na ga yunwa inaji, yace " to ai banga magana ba amma ya jarabawar da dadi ko?"

Nace "eh Alhamdu lillah"

Kirjina naga ya kurawa ido nai sauri na sa hannu na ka kare nace "wai yaya maye haka kasan dai matar wani ce ni amma duk kabi sai kura min ido kake"


Banyi aune ba naji ya hada baki na da nasa yana tsotsa nayi ta kokarin kwacewa amma na kasa saboda yadda ya matseni a jikin sa. Saida ya gaji dan kansa ya sakeni yana maida wahalallan numfashi


Ni kuwa nayi tsuru-tsuru kamar wacce ruwa yaci ta.

Idanuwan sa sun kada sunyi jawur yace " wannan shine Punishment din da zan dunga miki aduk sanda kika kara ambata min wani" yana gama fada ya mike a kasalance ya bude kofar, ina ganin haka na zura a guje, yai saurin kamo ni yace "ke wai har

19 / 21