NI DA YAYA SADEEQ BY SIDDIQAHTUL KHAIRY YAHYA .doc

Author :  Saddikatulkhair Yahya Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 21

15K to 18K   out of 62.6K words

nayi koda na bude Umar ne hannun sa d'auke da jaka da takalmi da gyale duka masu ruwan madara
Yace "Momy tace in kawo miki ki saka idan? kin shirya ki fito".

Kar 'ba nayi takalmin irin mai tsinin nan ne ni kuma banason irinsa koda nasa tafiya d'aya buyu na turgud'e

Wata yar karamar jakace kalar dai ta amare a hannu na rike ta, yayin da gyalan na yafa sa a saman kaina.


A gaskiya ina son kwalliya a rayuwa ta saboda haka nike tafiya ina taku d'ai-d'ai duk da ban iya tafiya da takalmin ba lokaci zuwa lokaci ina turgud'ewa Amman hakan bai hana ni yin yanga ba, naman ta da wani lamarin aure

Afalo nasami su Momy duk sun shirya

"Momy wai ina zamu haka?". Na fad'i? haka ne sanda nike zama kusa da Inna

"Abuja". Momy ta bani amsa

zaro ido na nayi nace "Abuja kuma Momy shine zaku tafi da ni?".

"Eh" kawai tace min narai-narai nayi da ido 'kwalla na zubo min Daman koda nai wanka banyi kwalliya ba ko hoda ma ban shafa ba, saboda haka na cigaba da yin kuka na ina share 'kwallar da bayan hannu na

Inna ce ta kama? hannu na tana matsar kwalla, ba tare da tace min komai ba

Cikin kuka nace "Inna kada kibari atafi dani mana Inna nasaba dake, bazan iya rabuwa ba dake ba, nasan wannan tafiyar ba irin wacce na saba yi bane saboda haka jiki na ke bani, nidai gaskiya bazan je ba".

Cikin sanyin murya Inna tace "to ba gasu Khadija ba acan kuma akwai su Jiddah, baki da damuwa zaki saba kuma duka 'yan uwan ki ne".

"Siddi'ka inaso na ingan ta miki rayuwa ne, saboda 'Karami yace min idan ban bar ki kinyi karatu ba nan gaba dani zakiyi kuka".

Ina sharar 'kwalla nace "Inna ni ba zanyi kuka dake ba ki yarda dani da iya gaskiya ta nike magana".

Daga haka bata 'kara ce min komai? ba

Momy ce ta kama hannu na ta yima Inna sallama ina kuka ina kallon Inna haka na baro ta

daman driver mu yake jira a bakin 'kofar fita naci karo da Ladiyo data ke 'ko 'karin shiga gidan mu

A d'an tsora ce ta kalleni sai tayi baya

Bance mata komai? ba nashi ga mota idan ta naga ya kawo 'kwalla kuma ta bani tausayi,
ganin haka nayafito ta da hannu aikuwa da gudu tanufo ni

"Siddi'ka ina zaki haka ko sallama babu?".

"Birni mana".

"inda kike zuwa?".

kai kawai na d'aga mata

"Amma shine? wannan karan ko sallama babu?".

"nima bansan da tafiyar bane? ladiyo kuma karatu zanyi a can d'in ba yanzu zan dawo ba".

"Karatu fa kika ce Siddi'ka, mai zakiyi da makaran ta?".

"Nima bansan me zanyi da ita ba? Ladiyo amma dai an cemin tana da mutu'kar amfani kuma nan gaba zai temaka min zanji matukar dad'in karatun".

Cikin sanyin murya Ladiyo tace "to? Allah ya bada sa'a Siddi'ka don Allah kada kimanta dani".

Tabani tausayi sosai nasan kaf kauyen nan Ladiyo ba tada kama ta kuma nima banida kamar ta
Wata ran ma ni zanyi tsoka na amma sai inja mata duk da haka bai sa ta rabu dani ba

Nace "Bazan manta dake ba Ladiyo zan dawo gare ku Ina yi miki fatan alkairi kema".

"Ki shiga gurin Inna kice injini taba ki kayan sawa na gabaki d'aya".

"To" tace tayi min? godiya mukayi sallama ta shige gidan mu

A lokacin su Khadija sun shiga mota driver yaja muka d'au hanya


NI DA YAYA SADEEQ
? ? ? ? ? ? ? ? ? ??
(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

? ? ? ? ? ? ? ?? Chapter 10

? ? ? ? ? ? ? ? GARIN ABUJA

?? _______bamu wani tsaya akan hanya ba Dan Momy tace "duk mai uzuri yayi ha'kuri har sai munje gida saboda ance mata hanya babu kyau". Da misalin 'karfe 3:25pm muka isa garin birnin tarayya Abuja, tun daga unguwar zaki san ba irin unguwar nan ce ta kowa da kowa ba sai d'an wane da wane tunda ga wajen gidan Daddy zaki san gidan manya ne saboda ko fulawowin kansu da aka zagaye gidan dasu abin kallo ne, ba sai ka shiga daga ciki ba, yawancin gida jen un'guwar ginin gidan sama ne, idan ki kaga wannan sai kiga duk yafi kyau, amma kina ganin wani sai kice wancen bai kai wannan ba to haka dai gidajen unguwar suke, na wane yana wane na wane,

Ba yau na saba zuwa ba amma har yanzu? na kasa ri'ke sunan un'guwar Saboda ita kan ta sunan un'guwar na 'yan gayu ne kuma da turan ci ne >??
Gidan su Khadijan ma yana d'aya daka cikin 'ke rarrun gida jen saman dake un'guwar, shiyasa nike son zuwa saboda ina son bene a rayuwa ta

Driver d'in mu yayi? horn adaidai bakin 'katon get din gidan

Mai gadi ne ya le 'ko ta 'karamar 'kofa ganin motar Momy ne yasa shi saurin bud'e get motar mu ta sulala cikin gidan mai gadi ya maida get ya rufe

Daka bisani yazo da gudu ya bud'e wa Momy cikin ladabi yake yi mata sannu? fuskar Momy a sake? ta amsa masa "mun same ka lafiya?". "Lafiya lau hajiya". Mai gadi ya fad'a yana sadda kansa 'kasa "masha Allah babu dai wata matsala ko?". Momy ta kuma tambayar Habu mai gadi, yace "eh Hajiya babu wata matsala komi yana tafiya daidai".

"A kwai kayan mu a bayan mota kashigo mana dasu ciki? kaida Idi". Da "to" suka amsa su duka

A kasalan ce muka fito daka cikin motar muka shiga cikin falo ko waccen mu tasan d'akin ta dan haka muna shiga ko wacce tayi inda tasan nan ne dakin ta yake

A sama d'akin danike sauka yake don haka na haura abina amma dana murd'a hannun 'kofar sai naji a kulle yake gam

'Dakin Khadija dake kallon nawa naje shima a kulle yake sai dai naji motsi da alamar ita tuni tana ciki 'kwan-'kwasa 'kofar na shiga yi, daga can ciki tace "waya?".

"Siddeeqah ce". nabata amsa

Jim kad'an sai gashi ta bud'e 'kofar jikin ta d'aure da tawul da alamar har ta cire kaya wanka zata shiga

"Khadija mukul-lin d'aki na nazo ki bani".

"To" tace ciki ta komo sai gashi ta fito hannun ta rike da mukullin na amsa nayi gaba a bina

"Matar yaya a huce gajiya lafiya". tace min, da gudu na na juyo dan na doke ta amma sai ta maida 'kofar ta rufe tana dariya

~&~&~&~&~&~&~&~&~&~&~&
A bangaren Sadeeq kuwa yana barin d'akin Inna bai zarce ko ina ba sai gidan abokin sa Farooq bai kirasa a waya ba amma yayi sa'a saboda ya same sa ne yana 'kokari fita, nan dai ya bashi hannu suka gaisa Farooq yace "yanayin ka ya nuna kamar kana cikin damuwa, kuma ba ka saba zuwa gida na a irin wannan lokacin ba, kodai kai da mutuniyar taka ce? Saboda nasan labarin gizo baya? wuce na 'ko 'ki, da fita zanyi na gaji da zaman gidan, amma tunda kazo mu shiga ciki ka fad'a min abinda ke tafe da kai".

To bayan sadeeq ya shiga cikin bedroom suka wuce, saboda yanayin tsarin gidan irin me ciki da falo ne sai bayi da kitchen kuma duka haka gidajen kusa dashi suke saboda duka gida ne na yan sanda, wasu ma da matan su a ciki shima Sadeeq da nasa dan yana da Inna shiyasa bai damu da kwanan nan ba, kusan unguwa ce guda aka bar ma 'yan sanda ita, shi yasa da wuya kaji ance wani abu ya faru a cikin ta ko kamar ace anyi fashi ko an sace wani, saboda a zagaye take da masu tsaro kamar barikin sojoji shima Sadeeq saboda ansan shine kuma akwai nasa 'ban garan a ciki shiyasa da yazo ake bude mai get ya shigo abin sa

Kan gado Sadeeq ya fad'a yana maida numfashi, Farooq ya zauna a kan wata kujera dake bedroom d'in yace "ba ba kaifa nike jira kace wani abu mana ka wani baje a kan gado sai kace wata mace".

Tashi Sadeeq d'in yayi ya zauna ya shiga jero ma abokin nasa d'anyen hukuncin da su Daddy suka yanke, Farooq ya san Sadeeq ba zai ta'ba yi masa irin wasan nan ba musamman ma da yasan cewa Sadeeq da Siddi'ka babu jituwa a tsakanin su saboda haka ya gyara zama yace "Alhamdu lillah gaskiya naji dad'in wannan had'in kuma da kace d'an yan aiki wallahi sunyi dai dai, Ko ba komai zaka daina tsangwamar Siddi'ka, kuma sha'kuwa mai 'karfi zata shiga tsakanin ku, saboda haka ka tashi muje a d'aura auren da mu a kwai wata? sabuwar shadda na da nasa aka d'inka min da niyar yau in sata to sai bayan na anso ta daga wurin taila na canza ra'ayi".

Kwanciya Sadeeq d'in ya gyara a kan gadon yace "d'an iska mayen mata to ai sai kaje in yaso d'aurin auren ma sai ayi da kai, amma ni nan daka ganni babu inda zani wallahi, wai ni za'ama aure kamar wani 'karamin yaro, arasa ma wa za a had'a ni da ita sai 'yar 'karamar yarinya wacce ko gama sanin inda yake mata ciwo batayi ba".

Dariya ce ta kama farooq saboda haka yay ta da rawa abin sa saida ya gama ya fara lallashin a bokin nasa akan ya tashi ya shirya suje d'aurin auren, amma Sam Sadeeq yace "bai san da maganar ba". Farooq yana ji yana gani dole ya 'kyale shi amma ba dan ransa yaso ba

?

Wayar sadeeq d'in ce ta hau ringing cikin hanzari ya d'auko wayar daga aljihun sa ganin sunan Hisham yana yawo akan screen d'in yasa shi jan dogon tsaki yace "kagani ko Farooq abinda nake gudu kenan yanzu haka kira na yayi ya cemin ashe nayi aure ko gayyata babu". Kiran ne ya katse, yayi saurin kashe wayar gabaki d'ayan ta wannan dalilin ne yasa da Daddy ya kira wayar Sadeeq d'in yaji ta a kashe

Sadeeq ya ci gaba da cewa "ai ni yanzu na shiga uku Daddy ya gama jamin abun kunya a gari, ni ba mai laifi ba da sai na ringa yawo da abun fuskar da zan sauya kama".

Farooq dariya harda ri'ke ciki yace "wallahi aiki ya ganka yanzu ma aka fara nidai d'an kallo ne, saboda ko na baka shawara ba lallai ne kayi amfani da ita ba amma bari na gwada baka".

Sadeeq yace "wallahi Farooq na tsani yarinyar ne ji nike da ma na mutu na huta da dai nayi rayuwa da ita amatsayin mata ta".

"Kana ruwa aboki na, to kai wai me yarinyar nan tayi maka ne haka da ka tsane ta".

"haba Farooq wai har kana bu'katar 'karin bayani, bayan komai a bayyane yake, kasan nafi san na auri wayay-yiyar mace mai aji da yanga wacce ta gama digiri dinta in so samu ne ma ta fara aiki koda kuwa wani iri ne sannan kuma kada shekarun ta suyi 'kasa da 25 to ko bata da masifar kyau in dai tana da wa'innan abu buwan da na lissafa maka zan aure ta".

Zai ci gaba da magana Farooq ya dakatar dashi ta hanyar fad'in dakata malam "ai na d'auka ka bar wannan banzan tunanin da kasa a ranka zaka ro'ki Allah ne yayi maka za'bi mafi alkairi ashe ba haka bane, to ina so kasan har yanzu Siddi'ka yarinya ce ba a haka zata ci gaba da rayuwa ba ko kana da ya 'kinin cewa baza ta canza ba? Ya fad'a yana kallan Sadeeq d'in".

"Eh Farooq". Sadeeq yace yana d'aga murya "bazata canza ba a haka zata gama rayuwar ta>?? saboda irin zuciyar uban ta gare ta, kuma bugu da 'kari rashin jin maganar ta yayi yawa, kaf 'kauyen Dande babu wanda bai san ta ba ko ina idan na wuce kallo na ake ana nuna ni kamar anga barawo saboda an san ni yayan ta, nasan ma dan suna jin tsoro na ne da tare ni zasu dunga yi, nafisan yarinya natsats-tsiya mai kunya".

"Hhhmmmm Sadeeq nidai shawara ta anan ita ce kabi komi a hankali kada kayi gag-gawa, amma ni banga laifin Siddeeqah ba rashin jin magana da kace yarinta ce take damun ta, wataran idan akace tayi zata ce ba tayi ba, sharri ake mata".

"Sa'ar Jiddah ce fa mai yisa Jiddah bata yin duk wa'innan abu bu wan da Siddi'ka keyi?".

"To ai Sadeeq kasan yara kowa da kalan 'kuruciyar sa idan ka bibiya a kwai abinda ita Jiddahn ta keyi Siddi'ka kuma koda kud'i akace tayi ba zata yi ba, kuma idan ka lura Siddi'ka goyan kaka ce duk abinda tayi sai ace daidai tayi ba a nuna mata tayi kuskure, amma da ina tabbatar maka da sai tafi Jiddah han kali".

Ta'be baki Sadeeq yayi yace "wallahi ina raga mata ne saboda gwaggo Amina, amma yanzu tunda ta shigo gona ta zan koya mata darasi=?"? zan nuna mata tayi babban kuskure da Daddy yace zai aura mata ni bata ce A a ba".

Kafad'ar sa Farooq ya daka sannan yace "Allah ya bawa mai rabo sa'a". Ya fice a d'akin

~&~&~&~&~&~&~&~&~&~&~&
? ? ? ? ? GARIN ABUJA

Koda na bud'e d'akin na same shi a tsaftace kamar yadda nayi zato saboda duk zuwa haka nike samun shi

Da sallama d'auke abaki na, na shiga sannan na maida 'kofa ta na rufe da d'an mukulli Kan gado na fad'a ina maida numfashi, wash nagaji matu'ka
Baccin gajiya ya d'auke ni ba tare da nayi sallar la,asar ba daman sai da muka yi azahar agida muka taho

Hankali na kwance ni keyin bacci na na manta dawani auren yaya sadeeq da yake kaina.

A cikin bacci na nayi? wani mummunan mafarki wanda ban taba yin irin sa ba tun da nike arayuwa ta, ban fahimci me mafarkin ya 'kunsa ba tsabar rud'anin dake cikin sa.
A firgice na farka amma nakasa yin salati saboda ban saba ba, ina ta zaro ido na alamar tsoro nakasa firta koda kalma d'aya ina son in tuno abinda nagani acikin mafarkin amma na kasa, sai wani masifaf fan ciwon kai daya saukar min a lokaci daya, sosai tsoro ya shigar min har banason nayi motsi saboda sai naga kamar za a kama ni.

Bugun zuciya ta ne ya 'karu yana bugawa da sauri da sauri sakamakon buga 'kofa ta da naji anayi

Kara du'kun-'kune? kaina nayi a cikin bargo,? daka waje naji ana fadin "Ummi ce ki bud'e".

Jin muryan Ummi da nayi yasa nayi? han zarin saukowa daka kan gadon jiki na 'bari na bud'e mata 'kofar ta shigo, rungume ni tayi? tana ihu Bata lura da yanayin da nike ciki ba turanci ta fara su burbud'a min bayan tasan bawani ji nike ba amma tsabar iya yin Ummi takeyim shi Jin ban rungume ta ba kamar yadda muka saba yasa tasake ni, tana kallo na

tace "sisi kamar bakya hayyacin ki meke damun ki".

"Bacci na tashi". nace mata bansan maye dalilin 'boyewa Ummi gaskiyar abinda yasa yanayi na sauyawa ba

"Haba koda naji". ta fad'a tana kama hannu na, muka fito daga d'aki na, d'akin ta muka shiga wanda ya kasan ce a tsaki yar nawa da na Khadija

"Amma yakamata kiyi wanka sisi kicanza kayan jikin ki, kin ma yi kokari da kika yi bacci dasu a jikin ki ni yaushe zan iya".

"Ai ke ki ka ce Ummi? ni kin san na saba ko a kauye kayan da nasa dasu nike yin bacci duk sabun tar su bana sauyawa izuwa na bacci duk da ina dasu".

Wata uwar 'kara ta saki a razane na kalle ta "la fiyan ki 'ka lau kuwa Ummi?".

"lafiya ta lau sisi naji kin anbaci kauye ne kinsan ni da 'kauye amana don Allah yi ki fito wanka kizo ki bani labarin Dande".

Ban kuma cewa da ita komai ba, na nufi bayin wankan ta masha Allah shine abinda na fad'a bayan na bud'e bayin naga ko mai na cikin bayin fari ne 'kal kamar a zuba abinci a kasan a lashe saboda yadda kasan tayil din ke she'ki ga wani sihir taccen 'kamshi da yake tashi,

A han kali na d'aga 'kafa ta na shiga bayin duk da banyi addu'a ba amma na shiga da 'kafar hagu cikin kwamin wankan na shiga na kunna famfon ruwan zafi da na sanyi na dad'e a cikin ruwan d'umin sannan na fara wanka ina gamawa na d'aura tawul din dana gani rataye.

Ina fitowa ana kiran sallar magriba saboda haka na koma ciki na d'auro alwala na fito

A gefen gado nasamu Ummi? zaune tana buga game a laptop

Saida ta dube ni tace "gaskiya sis kin dad'e sai kace kina? canza fata gashi kuma kina nan yadda kike".

Ban kula ta ba na nufi durowar kayan ta saboda suna yimin dai dai, bayan na bud'e na ga wata doguwar rigar yadi mai laushi me run madara fitet ce ba tada wani kwalliya amma duk da haka d'in kin nada kyau,
ban wani damu da saka bra ba nafi sa haf bes, sif d'in haf bes din na bud'e na ciro d'aya sannan na bude na fant na d'auko sabo wanda na gansa da 'yar takar darnan a jiki alamun ba a sa ba, da yake duk nasan inda suke harda na siket din ciki haka na fiddo duk abinda nikeda bu 'kata

Sannan na nufi gaban madubi na zauna kan kujerar dressing mirror na fara shafa mai ina gamawa na d'auki tura rukan ta masu 'kamshi da tsada na fesa a jiki da kaya na duk kuwa da wasu ba akaya ake fesawa ba amma saboda ni ban sani ba haka nai ta fesawa, saboda a lokacin Ummi ta shiga bayi, doguwar rigar na saka na dakko dadduma don rama sallahr da ake bina sannan inyi wacce muke cikin? lokacin ta.

Ina cikin yin sallar Ummi ta fito daman dad dumar na kar kata ta yadda mutane biyu zasu iyayin salla akai

Ko da na idar ban wani tsaya yin addu a ba na cire hijabin

Na sauko kasa na tarar da duka 'yan gidan kowa y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ana nan harda Aunty Bilkisu da yaranta guda biyu Samahir da Shakran, Khadija da Umar ga Momy sai Jiddah da ke

6 / 21