Author : NIMCEY SARAUTA Category : Romantic Hausa Novels
a kunnansa hakan yasa duk yaji wani iri babu daɗi sam baya son yaga komai ya samu yayan nasa,kallon Hajia yayi yaɗan rausayar dakai yace."plz gida"aikam tace bai isa ba sai nan da sati guda sannan ya ƙara jin sauƙi,raurau yayi da ido kamar zaiyi kuka,haka dai yasa Hajia a gaba da shagwaɓa kala² shi sai an sallameshi haka nan kawai an wani ta kura mutum akan bed kamar mace,haka likitoci suka din gayimai dariya idan ya gaji saidai ya kalli Hajia ya kwaɓe face yace."Hajia kin gansu ko"dariya take tace ."rabu dasu da ɗinta kaima dr ne"to haka dai aka sallami A.j daga asibiti zuwa gida,inda ya hana abar kowa ya shigo gidan sai nan da wani lokaci idan ya huta.
Shekaru wawayene hakanan suka dinga ja kamar hucewar numfashi,abubuwa da yawa sun faru daga ciki har zaɓen farko da akai wanda su A.j basu samu nasara ba suka faɗi sosai,ansha drugs kala² wanda yaja akai a sarar rai kamar hauka sabida yadda ƙwaya tayi aiki wajan matasa,Chairman Ahmada Tijjani Asasa da gyar yasha lokacin da yaje yin zaɓe,sosai Chairman Jazuli ke zuba rashin mutunci yana cin kuɗi hankali kwance babu ruwansa da talakawa da kuma yaran daya bawa drugs wasu har kwanciya asibiti sukai dan haka mutane suka ɗauki ɗamarar sauyi a zaɓe mai zuwa.
Duk tsayin shekarun nan A.j da Mus'ab basu taɓa ganin Anusha ba,duk sanda sukai hutu su kuma basa ƙasar gaba ɗaya.
Hajia ta riga data gama yanke hukuncin ɗaurawa A.j aure da dukkan wacce tayi niya domin ciwon nasa kullum ƙaruwa yake,hakan tasa ta yanke yi masa aure cikin gaggawa babu wanda yasan macen da zata bashi,yanzu haka auren saura kwana ɗaya tak,sosai soyyaya ta shiga tsakin Anusha da kuma teacher Ameen,babu wanda yasan labarin kowa yanzu haka tana da shekara 15 cif da haihuwa inda asalin black skin ɗinta ya ƙara fituwa.
Yau asabar yaune su Anusha sukai hutun zangwan ƙarshe na aji 3 a secondry,yayinda a yaune su Mus'ab suka sauka daga ƙasar itopia,suna zaune a parlour gaba ɗayansu yayinda A.j yake kwance akan cinyar Hajia Mus'ab kuma yake zaune kusa da A.j yana danna lapton,madam Najwa kuma tana kujerar mutum ɗaya ta zabga ta gumi tana kallon A.j,shira suke ƙasa² shida Hajia wacce ita kawai ta kejin abinda yake cewa,buɗe baki yayi zaiyi magana yaji anyi sallama cikin wata cool voice mai sanyi.
_(afuwa da rashin update as soon as na gama SAI NA AURETA,za kuna jina kullum,nagode sosai guys son so fisabilillah💋🌹)_
Comments#
Vote#
Shere#
*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE REASSON BEHIND_
*_NIMCY LUV_*
👸🏻S@r@ut@👸🏻
@wattpad
Nimcyluv
*🐓ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA....!!*
Happy sallah guys😍
Like the colour of silver,
in the night sky,
the new moon rises,
the holy month has past,
the fasting is over,
tomorrow is the great feast of Eid-ul-Fitr.
We will eat spicy chicken,
and mouthwatering pakoras,
I’ll call my neighbours,
and friends on the street,
may the peace of Allah,
and joy of Eid,
be with everyone.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*37↪️38*
Gaba ɗayansu suka ɗago kai suna kallon bakin ƙofa domin ganin wacce take sallama,yayinda A.j ya lumshe idonsa tare da gyara kwanciyarsa bisa cinyar Hajia,wata matashiyar yarinya suka gani wacce a zahiri face ɗintane na yara but a jikin kam zaka iya bata 20years,hannunta ɗauke da wata red trolly ta mata fiya,idonta sai sharning yake sabida fari tamkar zata zubar da kwalla sabida yadda idonta yake da matuƙar haske da girma har wata colour ne cikin kwayar idonta,sosai shape ɗin jikinta ya bai yana cute pink lips ɗinta mai kyauri ya fito sosai sabida yadda jikinta yake dark black, duk cikin 2min Mus'ab ya gana ƙare mata kallo yasu ya gane ko wace but baya iya tunawa hakan yasa yayi ƙasa da kansa yaci gaba da danna lapton,dariya Hajia tayi sannan tace"Oyoyo my beby finally an gana makaranta"ɗan kwaɓe fuska tayi ta kasa cewa komai sai Hajia da take kallo sai kuma ta kalli cinyarta,jinjina kai Hajia tayi kafin tace"bebyn come to me"ɗan bubbuga ƙafarta tayi lokacin da take turo bakinta gaba,da gudu tazu ta faɗa jikin Hajia tayi masauki a cinyarta"auchii"yace jin anbiki kansa."bebyn enmata yaya school"shuru tayi bata ce komai ba wajan 2min tace"Hajia"murmushi Hajia tayi sannan tasa hannu ta zare beby hijab ɗin jikinta nan take gammun da tayiwa gashinta ya warware ya zuba har bayanta haɗe da rabin face ɗinta sannan tace."wat wrong?"hannu tasa tayi mata nuni da A.j wanda gaba ɗaya surutunsu ya dame shi sam bai fiya son magana ba sai yana tare da Hajia amma gashi wannan staranger zata addabe shi,kallon A.j Hajia tayi sannan tace."Meyayi maki?"turo baki gaba tayi sannan tace"Hajia ya tashi daga cinyata"gaba ɗaya Najwa da Mus'ab ne suka ɗago suna kallonta ya salam shine kawai abinda Mus'ab yace lokacin daya gama tuna Anusha,Hajia ce ta kalli A.j wanda yake kwance a cinyarta sannan tasa hannu ta shafi gashin kansa kafin tace."dr tashi mai waje ta dawo"juyowa yayi fes idonsa ya sauka kan Najwa wace take zaune ta lumshe ido sai lokacin ya samu damar ƙare mata kallo,Sosai take fara harta kosa ɗarasa a fari,lips ɗinta black ne maimakon pink hakan ya kara fito da face ɗinta,ganin zata buɗe ido yayi saurin lumshe nasa idon,Anusha kam da baƙin ciki ya kamata ganin A.j yaƙi sauka daka kan cinyar Hajia yasa ta fashe da kuka tare da kai hannunta cikin sumar kansa tana turasa,hakan yasa yayi saurin tashi zaune zuba mata ido yayi kafin yace"black girl"turo baki tayi haɗe da ƙara sautin kukanta kafin ta zabga masa harara tace"eh naji haka Allah yasu ya ganni"ta faɗa tana turo masa baki gaba,zaro ido yayi waje sannan ya girgiza kansa ya miƙe tsaye yabar wajan,Mus'ab ne yasa dariya ya miƙe tsaye shima sannan ya kalli Anusha yace."sorry beby gal,amma da kuɗina da hankali nima ban iya auren black gal wallahi"shuru tayi ta zuba masa ido kafin tayi tsalle tasha gabansa tare da riƙe waist ɗinta rolling sexcy eyes ɗinta tayi tare dayin fari tace."ohh hello ko a dream bana fatan auren farin mutum,than da kake cewa meza kai da baƙar mace insha Allah baƙar macen itane matarka,than waye ya fara gabatar da kiran sallah,ba bilal bane kuma inajin shima baƙine ko?"tana faɗin hakan ta juya tayi shigewarta ɗakin Hajia,baki Mus'ab ya saki galala yana jin rashin kunyar da take zuba masa,babu shakka data tsaya sai yayi mata mugun duka wani irin baƙin ciki ne ya kamashi haka kawai yaji yana son shiga sabgarta kodan yaji ubanta da wannan tunanin yayi cikin ɗakinsa.
A.j na shiga ɗakinsa ya fara cire kayansa saida yayi naked sannan yayi hanyar bathroom,yana shiga ya sakarwa kansa shower sosai ruwan yake dukan kansa zuwa naked body ɗinsa numfashi ya shiga saukewa a hankali,sosai ya kejin damuwa na sauka zuwa zuciyarsa wanda ya rasa dalilin hakan koda Hajia tayi mai zancen Aure bai shiga wannan damuwar ba,amma yanzu duk yana jinsa a bad mood he don't know why,wajan 30min ya ɗauka hannu yasa ya kashe shower wani light blue ɗin towel ya ɗaura a waist ɗinsa ya fito daga toilet,a gaban mirrow ya tsaya ya fara tsane ruwan dake sauka akansa,sannan yasa cump ya tashe gashin sosai ya shafa wani man gashi mai kyau ta kuma ƙamshi,cikin few minutes kansa ya shiga sheƙi da kuma gyalli,cikin sauri yaci gaba da shiryawa saida ya gama komai sannan ya ɗauko body spray ya shiga fesawa jikinsa yana gamawa yayi wajan wadrop ɗinsa nan ya ciro wata shadda dark blue mai ƙanan zane cikin sauri ya saka kayan sannan ya ɗauko babbar riga ta kayan ya saka tare da wata black cap mai zanen blue a jikin sai agowan apple mai black colour with black shoe company adidas,tabbas Ahmad Tijjani Asasa Allah yayi masa baiwar kyau da kuma kwarjini da cikar zati,sam baya da girman kai saida bashi da magana saidai murmushi haka bai fiya zama da mutumin da yake da surutu ba,yana da taimako sosai akan mai buƙatar taimakon,wayarsa ya ɗauka da kuma key ɗin motarsa cikin takonsa na ƙasaita ta kuma taƙama ya fito daga ɗakin nasa zuwa parlour'n gidan kansa a ƙasa yayi hanyar waje yana zuwa compound na gidan yayiwa motarsa key tunkafin ya ƙarasu wajan motar ta buɗe yana zuwa ya faɗa cikin motar saida ya saita waƙar jerusalema ya ɗansa volume kaɗan sannan yayiwa motar key ya fara tafiya cikin nutsawa yake joya kan motar,tun kafin ya ƙarasu getman ya buɗeman dan haka yana zuwa yayi waje kai tsaye Sosai yake sharara gudu akan titi dake bai iya tafiya a hankali ba indai shike drivering motar,few minutes ya isa babban asibitin dake garin Abuja yana zuwa yayi parking a compound na asibitin,tun kafin ya fito wasu ma'aikatan jinya sukayo kansa cikin sauri,shima kallonsu yayi ba tare daya iya ce masu komai ba,ɗan rusunawa sukai sukace."Dr daman tun ɗazu ake jiran zuwanka,wata mace mai cike ce tun jiya bata haihu ba,yanzu ana tunanin aiki zaai mata she is cirtical condition"cikin sauri ya fitu daga motar ya nufi office ɗinsa su kuma suna take masa baya a bakin office ɗin suka tsaya suna jiransa,yana shiga ya cire babbar rigarsa tare da a gogwan dke hannunsa wata safa ya saka a duka hannunsa,cikin saurin ya fito daga office ɗin yana zuwa suka miƙa masa wata green ɗin riga amsa yayi sannan yayi gaba zuwa Emagency room ɗin da matar ke ciki,turus ya tsaya dan tunaninsa zaiga babbar mace sai yaga wata matashiyar mata wacce take da ƙarancin shekaru,da hannu yayiwa sauran ma'aikatan nuni suka kunna na'ora da oxcygen cikin sauri ya shiga aikinsa da kware da kuma zallar tunani irin nasu na manyan likitoci,tunda yazu yasan cewa abinda yake cikin matar ya rasu,cikin few minutes yayi mata aiki ya ciro abinda yake cikin daman tayaya zata iya haihuwa banda abinsu jaririn da bashi da rai tayaya zaiyi yunƙurin fituwa,kabbara sukai ƴan wajen tare da karɓar jaririn,wata ma'aikaciyar jinyace tace."Dr baya motsi jariri"kallonta yayi sannan ya juya ya kalli matar da akaiwa aikin wacce taɗan buɗe ido yace."am sorry to say bebynki babu shi"wani murmushi tayi duk da halin ciwo tace."Allahamdullilah nayi matuƙar farin ciki da kuma jin daɗi mutuwar wannan shegen yaron"a ra zane suka ɗago kai suka kalleta.
*********** *********
Sosai mutane suka cika matsallacin dake nesa da gidansu A.j,a wannan lokacin A.j baya gida yana Asibiti duba marasa lafiya,ta kasance ranar lahadi 4/8/2020 wanda yayi dai² da ƙarfe 11:00am dai², safiya ce mai ciki da tarihi da kuma abin mamaki,gaba ɗaya ƴan wajan fuskarsu ɗauke da murmushi hadda Mus'ab dake gefe yasha ado cikin manyan kaya,a hankali limamin masallacin ya fara addua da kuma gabatar da abinda akazu yi,yayinda da a gidansu Mus'ab kuma kowa yasha kwalliya mai kyau inda Hajia take sanye da wani less mai ɗinki buba mai green colour tana zaune a ɗakinta ita da wasu manyan mutane suna shira,Najwa kam gaba ɗaya ranta babu daɗi domin zuwa yanzu ta tabbatar da ba ita za'a aurawa A.j ba,koma wace tayi ganganci kuma tayi kuskure sannan kuma za tayi ladamar aikata abinda ta aikata,tana zaune a parlour cikin shigarta wacce ta saba wato abaya mai pink colour yayinda tayi rolling ta mayafin abayar,jin anata ɓaɓɓaka dariya yasa na jiyawa ga mamakina sai naga Anusha zaune tana danna wayar Hajia da alama game take,sanye take da wani black siket iya cinyarta sai kuma wata blue t.shirt mai dugwan hannu a gaban rigar an rubuta HAPPINESS anyi mata kitso guda biyu akan wanda ya sauko har gadun mayanta,wata zabura naga sunyi gaba ɗayansu jikinsu na tsuma musamman Anusha wacce idonta ya ciko da gwalla ba komai ya haddasa hakan ba saijin abinda limamin Masallacin ke faɗa.
(tabbas ina farin ciki kuma ina mamaki yadda book ɗinan ke zagawa ko ina,nagode Allah🙏🏻yanzu aka fara wannan book ɗin dan haka ku kakkaɓe zani guys🤟🏻idan baki karanta ba ki nema a wani waje nima kaina bana tarawa a guna taran ake,masu cewa na turo masu daga farko kuyi hkr,masumin barka da sallah nagode duk da ban samu damar dubawa🙏🏻Maman maama gruop zandai na posting sabida naga comments ɗinku yayi ƙasa😕Wattpad ɗina ina maku barka da sallah kuma naga kundaina comments why?😒ina jiran naman sallah na pls😥)
Comments#
Vote#
Shere#
*🤱🏻RAINO ne SILA🤱🏻*
_ADOPTION IS THE REASSON BEHIND_
*_NIMCY LUV_*
👸🏻S@r@ut@👸🏻
@Wattpad
Nimcyluv
*SALON NA DA BANNE🤟🏻*
*👸🏻FADAR NIMCY LUV💘 wannan page ɗin na kune watan zaku ji daɗinsa ina gdy da Comments🤗*
*🌈KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION🌈*
*39-40*
Ƙara sautin kukanta Anusha tayi still idonta naga wayar hannunta amma kana ganin face ɗinta zaiyi showing damuwar da take ciki, ba komai ya haddasa hakan ba sai game over da akai mata sabida duk nacinta na game bata iya game ɗin TAMPLE ba, hakan tasa ta nace shine ta nayi aka cita,wannan dalilin shiya sata kuka dan ji tayi kamar tayi cilli da wayar ta huta amma ba zata iya ba.
Ta rasa maiza tayi domin nuna godiyarta ga Allah daya nuna mata wannan rana mai cike da tahiri da kuma al'ajabi,tabbas idan ba gizo kunanta yayi mata ji tayi Limamin yace.
"an ɗaura auren DR AHMAD TIJJANi ASASA da NAJWA FAROUK akan sadaki dubu hamsin cif"
Wani shu'umin murmushi tayi tare da juyi a tsakiyar parlour Rashin Sani yasa ta bugi hannun Beby wacce taci gaba da game ɗin ganin zuwa yanzu ta fara iyawa.
Wani kallon ta kaici beby ta bita dashi,wani baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarta,ganin Najwa na shirin barin waje kuma bata yi mata magana ba yasa tayi saurin shan gabanta tace.
"ohh hello kee!! bakya ganine ko kuma Allah mai halicce ki da ido ba?"
Murmushi Najwa tayi sannan ta kalli Beby anusha tace.
"kee bana son rashin kunya daga yau anty zaki cemin ba kiji an ɗaura aure na da bro A.j ba"
Wata harara Beby ta zabga mata rolling eyes ɗinta tayi tare da riƙe faffaɗan waist ɗinta tace.
"i don have any prblm with ur marriage kin gane,ina maganar abinda yasa kikai min hauka a nan"
Zaro ido Najwa tayi jin abinda beby tace babu ɓata lokaci ta ɗaga hannu da niyar marinta, cikin sauri ta zille tayi ƙasan ƙafarta tazu hucewa ta jawo sket ɗin jikin Najwa na ciki,dai² lokacin da Mus'ab yake shigowa cikin parlourn, akan idonsa sket ɗin ya faɗo.
Wata irin shewa tayi tare da yin tsalle tana faɗin.
"wallahi babu wanda ya isa ya takani na rabu dashi bare ke"
Tana faɗin hakan tana ja baya cikin Rashin sa'a tayi tuntuɓe da teedyn ta haka tayi baya luu zata faɗi gaba ɗaya far gaba ta cika mata ciki,runtsa idonta tayi da ƙarfi wata ƙatuwar ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da taji ta faɗa jikin mutum ƙara kwantar da kanta tayi akan ƙirjinsa tana sauke ajjiyar zuciya,tana jikin ya fara ta kawa har zuwa tsakiyar parlour sannan ya kalli Najwa yace.
"matar yaya ki daina kula wannan baƙar yarinyar bata da kunya fa"
Yana faɗin hakan ya cillata kan sofa,saurin tashi tayi sannan kwala murya ganin ya kusa shigewa ɗakinsa tace.
"Wallahi bro jikinka daɗi,ka iya ɗaukan mutum dama zama ɗinga goyani kaji"
Wani mugun tsaki yayi tare da faɗin.
"girma babu hankali,wani idan yaga jikin stupid gal ɗinan sai yayi expecting tayi 20 years da haihuwa,mudai Allah ya ƙaremu kada ki ɗauko mana rigima"
Duk maganar da yake faɗa shi kaɗai yake yinta,Hajia yace ta fito a flat ɗinta fuskarta ɗauke da fara tace.
"beby yau ko a tuna dani ko?
Ɗan cuno baki tayi tare tayin shuru bata ce komai ba,Hajia yace tace.
"Najwa fallow me,mai gyara na jiranki a yau zaku koma wancen flat ɗin babu mai zama a gida na"
Tana gama faɗin hakan ta juya itama Najwa binta tayi a baya tana ɓoye farincikin da take ciki.
*******
Tunda ya shigo farƙon layin ya keji gabansa na faɗuwa he don't why haka yaci gaba da dreving motar slowly kamar bayaso,daga nesa da masallacinsu ya fara jin shelar ɗaurin aure,ɗan murmushi yayi sannan a hankali a buɗe bakinsa yace.
"Happy marriage life bro"
He saied it duk da baisan waye yayi auren ba,a karo na biyu ya ƙara jin abinda Liman ɗin ya faɗa wanda baiji ɗazu ba,wani irin wawan birki yaja lokacin guda zufa ta fara keto masa duk da cewa akwai sanyin A.C a cikin motar,runtsa idonsa yayi da ƙarfi sannan ya buɗesu ya zuba akan mutanan da suke fitowa daga masjid ɗin,idon yayi koma red jijiyan kansa ya tashi,sunan Allah kawai yake karantuwa a cikin zuciyarsa,shin mezai kira wannan auren,auren dole ko kuma aure huce takaici shikenan an haɗashi da wacce baya so sabida lalurarsa,to tabbas idan dan haka sukai sunyi kuskure da ƙwara yayi ta zama a haka da ace yasan wannan a matsayin mata,ba zata taɓa samun saba wajan kwanciyar aure,shi ta keso the game is over ta sameshi shikenan,yana gama faɗin hakan ya juya kan motar ya fara tafiya da gudu duk wanda ya ganshi saiya kauce masa sabida yadda yake sharara gudu akan titi few minutes ya iso wani haɗaɗɗan waje kana ganinsa kasan CLUB ne basai anyi magana ba,ko ganin gabansa ba yayi sabida yadda zuciyarsa keyi masa wani irin zafi,da sauri ya rufe motar yayi cikin CLUB ɗin tun daga nesa aka fara bashi hanya dake mutane da yawa sunsan matsayinsa a garin,kuma time 2 time yana zuwa CLUB ɗin,wata haɗaɗɗiyar sofa ya samu ya zauna tare da lumshe idonsa,wani matashi saurayi ne wanda yaci crzy jeans da wani aski mai tsaga yazu wajansa yace.
"Oga me za'a kawo maka?"
Kallonshi yayi sannan ya kawar da kansa gefe bai ce komai ba,ganin hakan yasa yaja jikinsa ya bar wajan,kamar daga sama yaji ana magana kusa dashi,wata sexcy girl ce wacce tasha ƙana nan kaya taci ƙarin gashin na abun mamaki wajansa tazu ta zauna tare da jin gina jikinta a nasa,kallonta kawai yayi yama kasa magana