KELTOUMAH BOOK COMPELET BY TAKORI

Author :  Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 31

1 to 3K   out of 92.7K words

KELTOUMA









1

Sumayyah AbdulQadir

(Takori)





07030137870 (

whatsapp

only)

GARGADI DA TUNASARWA

Labarin



dake



cikin



littafinnan

da

duk



abinda



ya



kunsa



kirkirarre

ne,

kuma



kagagge

.

An



rubuta



domin



fadakarwa

da

nishadantar

da

mai



karatu

.

Ba’a



yi



shi



domin



cin



zarafin



wani

, ko

wata



ba

, ko

wata



kasa

ko

wani



jinsi

ko yare

na



wata



al’umma



ba

, don haka

idan



kaji



wani



abu

a

cikin



labarinnan

;

suna

ko gari, ko

sunan



kabila

ko

wata



kasa

da

yayi



kama

da

naka

to

arashi

ne

kawai

aka

samu



irinna

fiction.

Gabadaya



sunayen



jarumai

,

garuruwan



cikin



labarin

da

yanki

da

akayi



amfani



dasu



duka



bana



kowa

bane,

kintace

ne

kawai

da

hasashe



na



marubuciyar

,

an



sanya

ne

kawai



domin



kayata



labarin

da

armasa



shi

.

Ba’a



yarda



wani

ko

wata

, ko

wata



kungiya

ko

kafar

yada

labarai

ta

karanta



shi

a

wata



kafa

ta

sadarwarta



ba



tareda



rubutaccen



iznin



marubuciyarshi



ba

.

Yin

hakan



karya



doka

ne,

kuma



abinda



zai



janyo



tuhuma



daga



dokar



shari’ah

ta

hakkin



mallaka

. Fatan

alkhairi

ma

duk



makaranta



littatafan

TAKORI.

-

SUMAYYAH ABDULKADIR

(TAKORI)

1/1/2026





SADAUKARWA

LABARIN “KELTOUMA” SADAUKARWA NE GA DUKKAN ‘YAN AREWACIN KASATA NIJERIYA, WADANDA SUKA SAMU KANSU DA YIN KAURA DON NEMAN MAFAKA GA RAYUWARSU (GUDUN HIJIRA) SANADIN IBTILA’IN TA’ADDANCI A KO’INA SUKE A FADIN KASARMU MAI ALBARKA, NAJERIYA.

-

SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)





1/1/2026



TAKORITES



Kafin

mu

fara



ina



mai



farin



cikin



tallata



muku



kayan



abincin

LAZEEZUN

na

Haj. Aishat Aliyu

Sabuwa

,

Kaduna.



Mai

kamfanin



Lazeezun

Venture and

G

lobal Services.

Khairan

Lazeezun

mai



garin



Danwaken

Lazeezun



mai



dadi

da

gamsarwa

,

garin



kunun



Lazeezun



mai



gardi



da

dakakken



Yajin

Lazeezun



mai



dadin



dandano

.

Kayan nan

na

LAZEEZUN

ina



baku



tabbacin



daban



suke

da

duk



wani



kalar



garin



danwake

ko

garin



kunu

ko

dakakken



yajin

da

kika



sani

,

ni

din



dai

tested



ce

,



kuma

trusted

ce



akan



kayan

LAZEEZUN

.



N

a ci

na



yaba



nida



iyalina

shine



nace



bazan

ci

dadin

nan

nikadai



ba

tare da

na



tallata



muku



Khairun

Lazeezun



ba

.

Kayan

danwaken



Lazeezun

da

garin



kunun



Lazeezun



da

yajin



Lazeezun



suna

nan

suna



ratsawa

a

wasu



daga

supermarkets

din



garuruwan

Abuja,



Kano, Maiduguri, Kaduna kai

har



Janhuriyyar



Nijar

, a



yanzu

haka

garin



danwaken



Lazeezun

da

garin



kunun



lazeezun

da

yajin



lazeezun

sun

fara



tsallakawa



har



ketare

, sun isa UK, Dubai, Egypt, da

Saudiyyah

,

kawai

ki

tuntubi

Haj Aishat Aliyu a

wannan



lambar



waya

(08030802900)

daga



duk

gari ko

kasar

da kike don

dandana



Lazeezun



dinmu



mai



dadi

.

Ban fada

muku



abinda

ban ci

naji



ba

!!!

Madallah



daku

.

Takorinku.

SHIMFIDAR LABARIN

ZURI’AR MARIGAYI GRAND KHADI

Z

uri’ar

Marigayi



Alkalin

Alkalan Tambuwal,

wanda



ake



kira

‘Grand Khadi’,

wato

Alkali Jalloh Ahmad,

wata



fitacciyar



zuri’a



ce



sananniya

,

mashahuriya

,

kasaitacciya

,

kuma



hamshakiyar



zuri’a



mai



fadi

da

girma

a

garin

Sokoto-Birnin Shehu.

Sau da dama in ana

bada



tarihin



zuri’ar

Jalloh Ahmad,

zaka

ji ana

buga



babban



misali

da

tsananin



hadin



kansu

, son

juna

, da

kaunar



junansu

,

har



ila



yau

, ana

bada



kwatance



dasu

da

irin



kyawun



surar

da Allah

yayi



musu



mazansu

da

matansu

.

Allah

ya



albarkacesu

da zaman

lafiya

da

fahimtar



juna

a

tsakaninsu

. Alal

misali

, tun a

zamanin

da can,

an



san



duk



inda



zuri’a



mai



fadi

da

yado

take (extended family), to dole

ake



samun



hatsaniyar

zaman tare

na



yau

da

gobe

, da

yawan



sabani

,

kyashi

,

hassada

,

gutsuri



tsoma



na



yan



ubanci

ko

makamantansu

a

tsakanin



mambobin



wannan

family,

matansu

ko ‘

ya’yansu

, ko

faccaloli

, to amma

yawancin



wadannan



matsaloli

babu

su

a

zuri’ar



gidan



Alkalin

Alkalai.

Anyi

ittifakin



cewa



su



zuri’ar

Jalloh sun

baiwa



irin



wadannan



kananan



matsalolin

baya,

basa



nuna



yan



ubanci

ga

junansu

,

koda

ace

suna



yi

din,

toh

da

hankali

da

tunani

da

ilmi



suke

yin

nasu

,

wato



bana



kyashin



juna

ko

hassada

bane

a’ah

,

na



rige-rigen



samun



cigaban



rayuwa

ne.

“In baka

yi

bani

wuri

in

wuceka

” (a

neman



ilmi

da

neman



na

kai) shine

abinda

Jalloh

suka



sa

a

gaba

.

Zamantakewarsu

ta

yau

da

kullum



mai



ma’ana



ce



kwarai

da

gaske

,

sannan



abar



sha’awa

da

burge



kowa

da

ya



sansu

ko

yaji



labarinsu

.



Akwai



fahimtar



halin



juna



na



hakika

da

kuma



girmama



juna



tsakanin



zuri’ar

Jalloh Ahmadu. Babba da

yaro



kowa



ya



rike



matsayinsa

.



Duk da

cewa



ya’yan

Grand Khadi, sun

fito



daga



cikin



iyaye



mata



daban



daban

,

wato



gidane

da aka

fifita

POLYGAMY, aka

auri



mata



har



hudu



rus

! Aka

kuma



yi



rayuwa

tare,

rayuwa



irin

ta ga

baki

ga

hanci

(

tsakanin



dakunan



matan



gidan



na



wannan



na



kallon



na



waccan

, kitchen din

gida



gabadaya



guda



daya

),

kuma



kowacce

data zo ta

haifi

nata

yaran



gwargwado

, a

karkashin



inuwar



auren



adalin



miji



daya



tamkar

da

goma

a gun

matansa

,

mutum



mai



tawadi’u

da

wanzar

da

adalci

da

kyautayi

a

tsakanin



matansa

.

Kokari

Grand Khadi

lullum

shine

ya



tabbatar

da

farin



ciki

da

hadin

kai a

tsakanin



iyalinsa

.

Matan Grand Khadi Jalloh

hudu

babu

wacce

bai

haihu

da

ita



ba

;

uwargida



itace

Inna Jari

wato

(Jarin

gida

), Yaya

Suwaiba

ta

biyu

,

sai

Hajja Badejo, da

ya



auro



daga



Wurno

, da

amaryarsa

Haj. Hadiza da

kowa

a

gidan



ke



kira

(Maman Nasiba).

Zaman

lafiya

da

hadin



kan

da

ake

dashi a

wannan

family din, ta

ko’ina

ka

hanga

ka

duba



sai



kaga



bazai

rasa

nasaba

da

kasancewar



kusan



duka



iyalin

Jalloh Ahmadu,

ilmin



addini



ya



wadacesu



ba

.

Allah

yayi



ahalin

Jalloh

masana



ilmin

Al-qur’ani ne,

sannan



mafi



yawansu

ta

fannin



abun



duniya



zamu



iya



cewa



mawadata

ne ko

masu



babban



rufin



asiri

.

Ba ga

ilmin



addinin



kadai

Jalloh

suka



yi



shuhura



ba

,

har

da

na



zamanin

,

shi



yasa



ake



zaune



lafiya

a

wannan



babban



gida

.

Kowa ka

gani

a

a



zuri’ar

Jalloh

yanada



abin



yinsa



kwakkwara

,

kusan



har



ya



zarta

dan

uwansa



abun



yi

da

rufin



asiri

, da

wuya

ka

gane



wanda



yafi



wani



nasibi

a

cikinsu

, don

basa



barin



dayansu



yayi



kukan

babu (

ya



nemi



komai



ya

rasa),

ba



tareda

sun

yi



gangami

da

hobbasa



sunyi



rige-rige



wajen



agaza

masa

ba

.

Kenan

tunda



abubuwan

da

ke



haddasa



fitina

a

yawancin

(extended family)

zuri’ar

Jalloh

duk

sun

basu

baya;

kamar



rashin



abun



duniya

, da

rashin



taimakawa



juna

,

rashin



ilmin



addini

,

rashin



abinyi

da

sauransu



sai



ya



zamana



nasu



nakasun

shine ‘competition’ (

gasa

da

juna

),

wanda



ke



faruwa

a

tsakanin



yammatan

family din

kadai

, don

samarin



zurri’ar



duka



masu



dattaku

ne da

halin



girma

, (amma babu

manyan



matsaloli



irinsu



hassada

ko

kyashin



juna

).

Misali

, a

tsakanin



yammatan

Jalloh family,

kowacce



naso

ace

tafi

‘yar

uwarta



iya

ado

na



fita



tsara

, ko tana so ace

tafi



sauran



iya



gayu

da

iya



karkata



daurin



dankwali

, da

iya



shiga

(dressing)

mai



burgewa

, ko son ace

tafi



sauran



yan



uwanta



yawan



kayan



kwalliya



masu

aji. Don

kwalisa



kam

!

Wannan



kowa



ya



shaida

a

jinin



yammatan



gidan

Jalloh take.

Iyayensu



maza



duka



cikinsu



daya

. Wato Jarin

gida



ce

ta

haifi



manyan’ya’yan

Alkali Jalloh,

wannan



ya

kara

taimakawa



wajen



haduwar



kansu

, don

kowanne



shi



ke

da fada aji a

gidansa

,

kuma



abinda



babba



ya



yanke

dole

na



kasan



su

bi.

Mai bin Jarin

gida

a

matan



gidan



wato



Hajiya

Suwaiba,

daga



zuwanta

ta

fara

da

haihuwar

mace,

itace



babba

a ‘

ya’ya



mata

,

wadda



ita



kadai

tayo

gadon

Grand Khadi ta

fannin

profession;

Alkaliya



Shafa’atu

Jalloh

kenan

(Justice

Shafa’atu

), da

suke



kira

(Yaya ‘Yar Dada).

Inna Badejo

kuma

da aka

auro

a bayan

Suwaiba



tazo

ta

haifi



auta

a ‘

ya’ya



maza

,

daya



tamkar

da

dubu



watau

Baffa Attahiru.

Haj. Hadiza

wato

Maman Nasiba

itace



uwa

ga

autar



gidan



gabadaya



mai



suna

Nasiba Jalloh, tana

aure

a Mubi. Maman Nasiba

itace

1 / 31