Idan Kaya Ya Gaji Book 2 Hausa Novels Compelet by Badiat.doc

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 25

1 to 3K   out of 73.4K words

??????>?? ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????)

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????~0Table????????JData
????????????????????? P?B? KSKS?~!_???????tt? ? ? ? q ? ??5<? ?$$$$$$$$&$? ?;*t? ? $$? ? ? ? $e?? e$? $e? $$? ?  ?B`????BNormal$a$KHOJPJQJaJ!_LP%?7?JZDm??????????l?D?h*?&?9D>&DzXf?qV? ?????????
???Z??,&!?3hJ>\xn?y\?v???????.??H??`P*|1D~T?an?x@???????l??????Z?X/?C?K?_(nz???b??????????v"6<|Rrb\x???X??r?@??IDAN KAYA YA GAJI....
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA BIYU

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI



LABARI MAI DA?IN SAURARE

*Abinda ya faru shine*
*Jiya da daddare da misalin ?arfe bakwai na dare wata lamba ta kirani cikin ikon Allah na Wauka sabida ban fiye Waga waya ba nafi gane a turo mun sa?on karta* *kwana.*
*Sai tace dani*
*"?ata dan ALLAH hutun da kika ce zaki yi na* *tsawon kwana goma yayi yawa ki daure zuwa monday in dai da hali kici gaba da rubutun dan* *ALLAH. In ina karanta littafinki ina samun nishaWi sosai. ?ata Ubangiji Allah ya huwace miki baiwar tsara rubutu da fikrar hausa sosai. Ni tsohuwar ma'aikaciyar jarida ce, nafi shekara talatin ina karance karancen littattafan hausa irin nasu Ado gidan dabino, Balaraba Ramat, Anty Bilki funtua* *Amman ?ata salon rubutunki ya bambamta da na ragowar marubuta. Hausarki, sunayen jarumai, da* *yadda kike amfani da daWaWWun kalaman hausa, bugu da ?ari sunayen littattafanki sunfi komai burgewa."*
*Mun yi maganganu da'ita sosai na yaba na kuma yi mata godiya dattijuwace sosai.*
*Na yi mata al?awarin monday zanci gaba da posting da izinin Allah.*
*Maigidana daya dawo* *masallaci na bashi labari sai ya umarceni da yau lahadi in soma posting Win kawai.*

*Mamana gashi na* *soma posting sabida girman soyayyar da kika nuna mun*
*Masoyana a duk inda suke da bazarsu nake taka rawa. In babu ku babu BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI.*

001





SABUWA:.


Hannu na saka zan amshi ledar da Khalid yake mi?o mun ina murmushin cusa haushi. Ban aune ba naji an warce ledar tare da tunkuWeni gefe naje na faWi na dauje hannuna.
Babangida ashe ya fito a mota da gudu kamar mayunwacin zaki.
"Dan ubanki waye wannan, wanne kwarto fasi?in ma?iyin Allah da manzonsa ne wannan. Au ashe Sabuwa har yanzu baki dena bin maza ba da gasken dai duk fitar da kike yi maza kike bi?"
Da sauri na mi?e ga mutane har sun soma taruwa"
"Malam koma me kake tunani bai kamata ka shiga Waga murya a hanya haka ba. Matarka ce fa, ya zaka tunkudeta haka"
Karku daWa kar ku raga iyakar abinda Khalid ya faWa kenan Babangida ya kucuneshi ya soma cunkusa mishi manyan ashariyar da kamar a bakin tasha aka haifeshi yana yi yana jijjiga Khalid idanunshi kamar gauta.
Ka sake shi Babangida, zanma baya"""
Hannu yasa ya zabga mun mari, ya sake marina bakina ya fashe.
Ya sake Waga hannu kenan Khalid ya ri?e hannun gam jikinshi na rawa yace.
"Kar ka sake dukanta in kai baka san darajarta ba ni nan nasan darajarta. Baby ashe Wan balaja'u kike aure ban sani ba, madoki wanda baisan darajarki ba?"
Habawa Khalid bai rufe baki ba Babangida ya runtumashi da ?asa, dambe ya kaure kica_kica jama'a suka haWu kamar ya?i mata sai tittiWowa suke yi sada gidajensu.
Da kyar aka raba faWannan Babangida ya shiga labartama jama'ar da suka taru.
"Matatace fa kwarto ya kawota har gida, har yana mata siyayya fa, saina kasheki Sabuwa wallahi, shima sai ya mutu. Mutuwa nima zanyi uban kowa ya huta. Yana faWan haka ya cabke wuyana ina kakari yana dukana. Da ?yar aka SanSare Babangida a jikina. Duk ya fasa mun wuyana.
A guje na faWa motar Khalid, ana in fito naki fitowa Babangida kamar zai haukace haka yake ji. A guje ya gangara.
"Malam ja motarka ka bar wajennan dutse yaje Wakkowa zai ragargaje maka mota"
Da sauri Khalid ya buWe motar ya shigo, yana ma motar key muka hango Babangida da ?aton dutse a hannunshi, habawa a guje muka hau titi har muka kusan kaWe wata baiwar Allah mai ciki, dutsen da Babangida ya harbo ya fashe ma Khalid gilashin bayan motarshi.taratsatsatsa
Gudu muke yi Babangida na binmu a mota.
Ka kaini gida Khalid, na gama auren Babangida na gama zama dashi kenan har abada."
"Amman babu matsala Baby jini ne yake zuba a bakin ki da hannunki fa muje asibiti"
Idanu na lumshe na waiga Babangida na biye damu a mota.
A_a ka kaini gida kaga biyo mu yake yi, in kuka kuma haWuwa zai iya maka komai"
?wafa yayi yace
"Rabu dashi bai isa yayi miki komai ba, ni kuma daidai nake dashi. In yana jin shi tataccen Wan iskane ni ubanshi ne a iskanci"
Idanuna na runtse ina kuka mai ciwo yarana kawai nake tunowa kada wannan labarin tozarcin ya iskesu shin Yaya zasu ji musamman Mardiyya da Aminu?
Ajjiyar zuchiya nayi dana tuna ?arshen zamana da Babangida ne wa'adin ya cika, wannan abinda ya faru kaWai na cancanci ya sakeni, dama banje inda naje domin a kwato mun hakkina ba.
Ban buWe idanuna ba sai a ?ofar gidanmu, Khalid na tsayawa Babangida ya fito a mota da kanshi ya buWe motar ya fincikoni yana neman dukana. Jikinshi yana rawa.
Dira nayi a wuyanshi na shiga dukanshi tako ta ina, haukacewa nayi duk inda na samu naushi nake yi, idona ma a rufe yake.
Ashe an cika a layi anata tsogumi, Rakiya da Adama ne suka Sanbareni a jikin Babangida. Wanda a tsaye kawai yake jikinshi na rawa, idanunshi na hawaye.
"Kayi hakuri dan Allah Babangida. Rashin hankali ke damunta ne shi yasa"
Murmushin takaici yayi kawai idanunshi sun ri?ide yace.
"Kamata nayi da wani Wan iskanta fa ya kawota har gida. Dake baku bata tarbiyyar arziki ba shi ya kawota gida. Ni zata daka harta zubarma da jini? Kuma ku wani fito kuna bani ha?uri wallahi saina kasheta.
Sabuwa amman wallahi sai kinyi Wan da kace ba'a haifeki ba. Komai yazo ?arshe kurun?us shi kanshi mai Waure miki bayan yau dai zai sallama zamana dake yazo ?arshe"
To se me IDAN KAYA YA GAJI GAMMO MA YA GAJI.
Tuni nabi hanyar nemo ma kaina mafita.
Me za'ayi da aurenka auren ?addara wawa jahili da?i?i kawai"
Ina faWin haka na shige cikin gida ina kukan fitar rai. Duk wannan bidirin Hamida fa tana tsaye ake yinshi abun yafi ?arfin tunaninta ne.
Rakiya da Adama ya suka ?are oho ga mata duk an fito kallo sai ri?e baki suke yi.
"Ke Lolo wai dama dake akeyi ne, eh ya naga jini a jikinki yana gudana ne wanne Wan abu ta kazanne?"
Cewar Gaza da bansan ya fito daga firzin ba.
Babangida ne ya dokeni ya tara mun mutane a unguwarmu da ?yar na iso gida Gaza kaje ka ramamun wallahi bazan Yadda ba"
Mi?ewa yayi tare da neman hanyar waje tar da cewa.
"Kutumar dumadu lahira ga ba?o"
Maigogul ne ya taso a guje ya bishi, ni kuma na zube a tabarma ina kuka kaina kamar zai fita.
Ni dai ina jiyo ihu daga waje, Hauwa ma da gudu ta fita tana salati.
Wani yanayi na shiga wanda nake shiga in ?unci yaimun yawa nafi awa uku bansan meke faruwa ba, kaina sai jujjuyawa yake yi, ga maganganu a kaina ina ji can kuma saina dawo hayyacina.
"Sabuwa sannu. Rakiya kinga ta samu kanta Alhamdulillah"
Cewar Maigogul dake bakin gadon da nake kwance.
"Sannu Lolo, daure ki tashi ki watsa ruwa Rakiya ko Adama su kaiki gidanki. Kinga uban mijinki ma yanzu yabar gidanan"
Da ?yar na buWe bakina nace.
Narantse da Allah bazan koma gidan Babangida ba sai dai sama da ?asa ta haWe"
"Babu inda zata je. In akayi wasa fa sai in ?arashe Babangidan uban kowa ma ya huta. Ya sabida rashin sanin darajar kai Dattijo kana ganin yadda ya cire imani yaima yarinya duka ace kuma ta wani koma. Babu inda zata je in dai ni Gaza ina numfashi. Uban mijinta ai bashi yake aurenta ba, bafa sonta yake yi ba. Wallahi domin rufin asirinsune kawai yake lallaSa Lolo nine ubanta daga yau"
Maigogul yace.
"To duka ai ka rama mata saranshi fa kayi Gaza. Kuma ai kana ji yace fa da wani namijin ya ganta. Tsinannen halinsu ashe bata dena ba. Dole ya doketa ai, kana gani uban mijin ya biyo bayanta yadda muka yi dashi data farka za'a mayar da'ita"
"A_a Maigogul ni ina ganin a dakata da batun komennan har komai ya lafa tukunna. Duba da irin saran da Gaza yayi ma Babangida "
Cewar Rakiya, ina dai jinsu da masu cewa in koma da masu cewa in bari ?ura ta lafa duk dai, basu san hukuncin dana Wauka bane amman in tayi wari zasu ji a lokacin nayi musu bayani.


Babangida:.
Yana tafe a mota jini na Wibanshi Hamida tana gefe tana salati.
"Abban Usama kabi komai a hankali ka gode ma Allah daya tuna asirinta. Ohh ace mace da aurenta tana bi kwararo kwararo bin maza, mu muna zaune zata kwaso mana cuta. Babu mamaki ma infection Win dake damun mu duka gidan ita taje ta Webo mana"
Idanu ya lumshe ?wa?walwarshi na hasko mishi hoton Khalid da Sabuwa data shige motarshi.
Babu shiri ya tsaida motar a gefen titi yana haki.
Malama Babba sai kiran wayarshi take yi.
"Kada ki Wauki wayar Wauko wayarki ki kira mun Mustapha ki bani shi"
Ya ?arashe maganar tare da cije leSenshi na ?asa.
KafaWarshi sai jini take yi, ga saran da Gaza yayi mishi ya shiga sosai har wajen ya soma kumbura.
Hamida ta mi?o mishi wayarta Mustapha nata
"Hello Hello"
"Mustapha kazo ka kaini asibiti dan Allah"
Nan yaima Mustapha kwatanceN inda suke ba'a jima ba sai gashi acaSa ya saukeshi. Ganin yadda jini ya Sata kayan Babangida da motar ma da yake ciki saiya tashi hankalinshi. Sai da Mustapha ya kira wani kofur abokinsu ne ya shige musu gaba a asibiti kafin aka karSi Babangida, a lokacin jini ya Webeshi ko gani bayayi ga zuchiyarshi kamar ana soyawa dan ?una a sume akayi cikin Waki dashi.
"Wai meya faru hakane, rikici ne ya haWasu da wani kome?"
Hamida ta kwashe labari tsab ta labartama Mustapha. Hankalinshi yaji ya tashi ainun yasan yadda Babangida yake da matu?ar kishi wannan dambarwa yanzu aka soma, shi kuma wannan farka ko a ina yake sai sun nemoshi.
"Bani kiga wayoyin nashi in ri?e mishi. Su Baba Malam sun san me ake ciki kuwa?"
Wayoyin ta mi?a mishi.
"Wannan ba?ar wayar Maman Mardiyya ce lokacin da abin ya faru ta faWi shine na take ta.
Banyi tunanin su Malama Babba sun san halin da ake ciki ba yana da kyau a sanar musu. Yau munga tozarci da abun kunya. Babu kunya ta kule motarshi shi kuma yaja suna shirin guduwa"
Kai kawai Mustapha yake ta jinjinawa. Kiran Malama Babba ne ya sake shigowa wayar a karo na barkatai. Mustapha ya Wauka tare da karawa a kunne kana yayi sallama.
"Muryar Mustapha kamar nake ji. An kashe mun Babangidan ko? Wallahi sun jawowa kansu bala'i dan bazan yarda ba."
"A_a bai mutu ba Malama ki kwantar da hankalinki muna asibiti yanzu dai aka shiga dashi, saran dai ya shiga sosai.
"Shikenan gamu nan zuwa asibitin hankalin kowa a tashe yake"


GIDAN SU B HOUSE

Sauke wayar Malama Babba tayi a kunnenta.
"Malam kaji wai suna asibiti da Mustapha abokinshi. Sai muje ko? Ka kira Wawo yazo ya kaimu"
Jim Baba malam yayi tare da dena rubutun da yake yi a allo yace.
"Ki je ki kira Ramadana yazo mu je, Wawo yana wajen aiki ai ba sai an rabo shi da wajen aikin ba. Allah dai ya kyauta tsuntsun dai da yaja ruwa shi ruwa kan doka, kuma duk wanda yasai rariya yasan zata zub da ruwa"
Kuka Malama Babba ta kuma fashewa dashi tace.
"Anya malam kana ?aunar Babangida kuwa?"
Girgiza kai yayi yace.
"Ko kaWan. Da ana canja Wa da tuni na canja Babangida daga tsatsona. Kaf haulata babu mai muguwar Wabi'ar Babangida."
Shigewa ciki tayi tana kuka. Baba Malam kuma ya shiga tunano baya
Sallamar wani bawan Allah mai saye da surt ce ta katse tunanin Malam Baba.
"Ameen wa'alaikas Salam. Bawan Allah daga ina?"
"Daga kotu al?ali Muhammad Muhammad ya rubuto sammaci yace in kawo gidannan. Surukarka Sabuwa ce ta shigar da ?aran Wanka Babangida kacigari. Wannan sammacinne ranar zaman kotun yana jiki Malam zaku gani.
Sai a daure a halarci kotu kuma dan Allah a tabbatar takaddar taje hannunshi."
Salati Malama Babba ta saki wacce fitowarta kenan Ramadan na ri?e da hannunta.
"To Shikenan wannan takadda in sha Allah zata je hannunshi, kuma da zaran lokaci yayi zai zo, da kaina zan kawo shi"
Hannu Baba Malam ya saka ya karSi takaddar. Ya juyo ya zuba ma Malama Babba da Malama ?arama idanu, can ya dubi Ramadan yace.
"Kayi musu jagora kuje asibiti. Akwai inda zani yanzu daga can zan biyo"
Malama ?arama na son magana amman tana tsoro dan Malam kaifi Waya ne.
Dole haka suka wuce asibiti shi kuma ya nufi gidansu Sabuwa a karo na biyu.
Sallama yayi a bakin ?ofar gidan dan ya rasa yaro Wan aike"


SABUWA:.
Fitowata daga wanka kenan, Rahama da su layuza duk sun zo, gasu Sadiya anata mayar da zance. Na jiyo sallama tabbas Muryar Baba malan ne. Maigogul ne ya fito daga Wakin Hauwa.
"Yauwa Lolo ki daure ki shirya in mayar dake.
A cikin gidannan babu uwar abinda zaki tsinta. Zawarawan gidan ma neman makafa suke yi balle ke da mijinki yake da rufin asirinshi, mu kanmu dake fa muka dogara. Ni dai na faWa miki wallahi Allah sai kin koma"
Fu ya fice, nima na shiga Wakinmu a hankali, zancan ake dai ta tattaunawa, kowa yana da damar faWin albarkacin bakinshi da duk abinda yake so yace.
Mai Rakiya ta mi?o mun mai gurguwa babu ko murfi duk datti cikinshi.
Kaya kawai na zura, goduwar rigar kanti da Sadiya ta ajjiye mun.
"Rakiya ke da Lolo kuzo, ku zo da tabarma"
Gabana ya yanke ya faWi, Rakiya tayi saurin mi?ewa ta fice, Adama ta bi bayanta da tabarma, ni ko sai da Maigogul ya le?o yai mun dakuwa.
"Ungo nan. Kaga ne mun ?ar nema zaki fito ne ko saina shigo nayi miki Sarin makauniya"?
Bakina a ture na suri mayafin rigar jikina na fita. Dukkansu suna kan taburma ni suke jira. A hankali na isa na nemi waje gefen Adama na zauna kaina a ?asa.
Gyaran murya Baba malam yayi yace.
"A kwanakin baya Sabuwa tazo mini da batun in amince Babangida ya saketa, na rarrasheta na bata ha?uri ta koma gida. To a wannan karon nasan tabbas rigima ce ta kaure a tsakaninsu, rigimar da ta lafa shekaru fin goma. Yanzu haka ga takadda daga kotu an turo mana Sabuwa ta maka Babangida a kotu, shine nazo inji ba'asin musabbabin abinda ya haWa rikicin, da dalilin yin ?arar"
Nan dukkansu suka shiga sallallami, Maigogul kuwa yin?urawa yayi ya kawo mun wani wawan dukan da zafinshi ya jima yana ratsa tsokokin jikina.
"Zauna Maigogul abi komai a hankali Sabuwa fa tana da gaskiyarta.
"Wacce gaskiya malam bata da hankaline da zata maka mijinta a kotu dan ubanta, dame ya rageta ba dai hakuri akeyi ba. Da ba'a ha?urinnan ai da itama fa ba zata zo duniyar ba"
Maiduguri ne yake magana duk a daburce da halama lamarin ya doke su sosai. Rakiya dai sai tafa hannayenta take yi kaina na ?asa ina Wigar hawaye. Gaza daga can gefe yana ma Rahine wanka yace.
"Kaga ?ar gari. Wallahi baki taSa burgeni irin yau ba"
"A_a ai mata uzuri shekaru goma sha ba kwana goma bane ba. Nasan abubbuwa da dama da ku baku sanshi ba dangane da tafiyar aurensu.
Amman menene dalilin rikicin?"
Maigogul ne ya zage ya labarta mishi yadda abun yake.
Idanu ya runtse ba tare da yaso jin gaskiyane ko ba gaskiya bane. Yace
"Batun shigar da ?aran akan menene shi kuma Sabuwa?"
A mugun sanyaye nace.
Saki nake nema Malam Baba kayi ha?uri"
Da sauri ya Waga mun hannunshi akan in yi shiru, mu?ut na haWiye maganata.
"Sabuwa zan miki tambayoyi ki amsa mun su ki daure ki kuma dena kuka."
Ina shesshe?an kukan ba?in ciki da tsagwaron tantagaryar nadama na gyaWa mishi kaina.
"Kin shirya rabuwa da Babangida kin tabbatar, sannan kin shirya zawarci da kaucema kuskure da kauce hanyar da akabi a baya, sannan Sabuwa ki sani Shari'a zata iya baki ?a?anki, to in bata baki su ba kin shirya ha?uri, sannan zaki karSi duk halin tagaiyara ko tozarci da ?as?ancin da zaki gansu a ciki? Dan daga ranar da kika rabu da Babangida daga lokacin duk tallafin da nake yi zai ?are, hatta Islamiyya sai an biya musu zasu je balle boko da ba tawa bace. Hatta ubansu yabar sake shigo mun gidana. Sabuwa!"
Ya kirani da murya ta gaske.
Bakina na rawa na amsa.
"Kin shirya ma duk waWannan lissafin da nayi miki, da waWanda tunanina bai kawo su ba?"
Rakiya tace.
"Babu ma Kotun da za'a shiga Malam dan Allah maganar nan a barta Sabuwa dai ba ita ta haifo kanta ba, ni da Adama da daddare zamu rakata gidanta. Sannan shima Babangida a bashi ha?uri da abinda ya shiga tsakaninsu da Gaza. Shaye_shayenshi yayi bata faWa mishi gaskiya ba ko maigogul?"
Ta tambayi Maigogul dake hararata. Da sauri yace.
"Sosai ma. Kaga muma fa in yayo shaye_shayenshi ya dibga sai yazo yace uwar tashi zai zane, ko kaji ma ya kirata da matarshi. Ayi ha?uri "
Malam Baba yace.
"Assha Allah ya kyauta. Ai Maigogul duk wannan fa ba damuwa bace, addinin Musulunci addinine mai sau?i, nima da kaina ina sulhunta aure, wasu ma in abun ya?i sai in turasu kotu daga ?arshe kaga an rabu. Sabuwa ki amsa mun tambayoyina duk kin karSa?"
E Baba malam na karSa babu damuwa"
Idanunshi ya runtse tare da ri?e kanshi yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi.
Sautin Wura ashar na Maigogul kawai kake ji a wajen sai zagina yake yi yana mangareni. Gaza kuma ya taso shima ya tsaya akan Maigogul sunata faWi in faWa.
"Maigogul dan Allah kabi komai a hankali duk wannan bashi bane. Ke Sabuwa da daddare ki shirya Rakiya da Adama su mayar dake Wakin ki, kije ki zauna har aga menene sakamakon ?arshen shari'a. Ki sani da aure a kanki shi wannan bawan Allah kar ki sake haWuwa dashi, aji tsoron Allah Sabuwa"
Da sauri na Wago jin ya ambaci in koma Wakina, magana nake son in yi amma nauyi da kwarjininshi yasa dole na sunne kaina ?asa ina hawaye.
"Ji mana kai Dattijo bafa eh zata wani koma ba in faWa maka gaskiya"
Baba Malam ya dubi Gaza yace.
"Abi komai a hankali Sabuwa ta koma Wakinta har sai an gama Shari'a"
Mi?ewa yayi yai mana sallama ya fita.
Dawa Allah ya haWa su Maigogul in bada ni ba.
Nan wannan yace wannan, wannan yace wancan akaita zagina tare da aibantani. Har Sadiya tana duban tsabaragen idanuna tana cewa dama in Babangida ya sake ni ita ya aureta duk bala'i zata zauna. Gaza shima ya saka tijara shi yana bayana.



ASIBITI:.

Isowar su Malama Babba ke da wuya aka fito da Babangida daga Wakin ?aramar tiyatar da akayi mishi a hannunshi, a gadon marasa lafiya aka wuce dashi zuwa

1 / 25