Idan Kaya Ya Gaji Book 2 Hausa Novels Compelet by Badiat.doc

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 25

15K to 18K   out of 73.4K words

baya saki Waya ya taSa yi mun.
Yau kwana goma cib da sakin da na saka rigimar sai dai in zauna inyi zaman ?a?ana wallahi yau dai a guje da bulala ya rakoni, kun ganni sai makwabta ne suka bani takalmi da mayafi.
Nazo na tarar anata rikici da mijin Labbai "
Ni dai take kaina ya hautsine hawan jinina ya tashi sabida damuwa.
"Hmmm ai Shikenan ke da Labbai duk auren naku dai ya tsinke. Ga dai filin tsakar Wakinnan du ya ishemu, ga wannan mitsiyaciyar itama Auren nata take so ta kaso. Duk ku dawo kuzo mu zauna ciwon zuchiya yai ajalina ga ba?in cikin Maigogul ga naku."
Tana faWan haka ta sau kukan da nayi imani sabida aurenane da zan kashe ba dan mutuwar auren Labbai da Adama ba.
"Rakiya ki dena kuka kada su Hauwa su jiyoki burinsu a kullum bai wuce su gammu a ?asa ba"
"Ke dallah su gammu a ?asan mana ai babu da abinda Hauwa ta isa goranta mun babu iriyar ?ar iskar da bata dashi a Wakinta.
Sama ne ya le?o Wakin Rakiya kina ciki, Adama Sabuwa kune a gidan?"
"Ahh Sama ai kai zamu tambaya kaine a gidan, wai Sama ina ka shige ne?"
Cewar Adama kenan.
Shigowa yayi da ?ar ledar kayanshi ya nemi waje ya zauna. Duk yabi ya lalace
"Ina can kasashen inyamurai neman kuWi Adama. In ka biye ta gidannan da rikicin gidan ina mai tabbatar miki likkafanin da inka mutu da tabarmar da za'a saka daga ?arshe nema za'ayi a rasa in dai gidannan ne.
Ya kuke ya yaran naku?"
Duk muka amsa mishi da lafiya, Rakiya kuwa tagumi tayi.
"Wai lafiya kuwa?"
Kafin a bashi amsa saiga Hauwa ta buWe labule.
"Wai yau muryar wa nake ji kamar Sama'ila dama kana duniyarnan. Yaushe da rabon mu saka a idanunmu?"
Kai ya Wan sosa.
"Wallahi Hauwa balaguro kawai nayi. Na shiga duniya neman kuWi"
HaSa ta ri?e tace.
"Kuma wacce sana'ar ka kama Sama?"
Harara Rakiya ta zabga mata harda jan tsaki.
"Bige_bige ne duk abinda na kama yi nake yi. Amman kamar dai lokacin kirsimeti ina zaga garuruwan inyamurai ina tallen balambalo" Sai da Hauwa tayi dariya kafin tace.
"Ai yafi maka zaman banzan.
Kaga ?aninka ma mijin Layuza ya kaishi shagonshi dake kasuwa yana taya shi aiki."
Sama yace"
"Wai ma'aru kike nufi shine aka saka a kasuwa. Yaron da ko Sera bai kaishi sata ba? Kai Hauwa nifa ina tsoron kada yaje ya kuntaka mishi sata azo ana raba hali"
Ai nan Hauwa ta shiga zage_zage haka ta saki labule.
Sama kuma ya suri ledar kayanshi yakai Wakinsu na langa_langa yayi ficewarshi. Yana wa?e_wa?e. Shi sabida tsabar shaye_shaye bama saka shi a lissafi dan ba kullum yake da hankali ba. Wataran ma sai a wayi gari dashi yaita danna ihu shi kaWai ?wa?walwar ta riga da ta taSu. Ga ?azanta a cikinshi kamar me.
Wayata ce tayi ruri Baba Malam ke kirana.
Da sallama na Waga muka gaisa. Sai yake tambayata lauya yazo kuwa? Nace mishi yazo yanzu ma gida nake son in koma bana jin daWi sai zuwa yamma ko gobe zani asibiti. Da haka mu kai sallama na ajjiye wayar.
Labbai taso mu tafi ni zazzaSi nake ji gashi ban tawo da magungunana ba."
"Bari in biyo ku nima Rakiya sai mun dawo kawai"
Cewar Adama data mi?e. Rakiya ma mi?ewa tayi.
"Nima zan fita nema banci ta zama ba hantsi yayi. Kayi nayi yanzu aka soma"
Tare muka fice mu makai titi, Rakiya tayi saman layinmu sana'ar kayi nayinta.
Muna isa gida na kwanta a kujera sai Labbai ce ta bani magungunana na haWiya naji dama dama.
"Yanxu bari in Waura abinci ki daure zuwa yamma sai mu tafi asibitin ko minti goma ne muyi sai mu dawo"
Kai kawai na Waga ma Adama, dan idanuna a rufe suke suna fitar da hawayen ciwo ga magungunan sun soma Wibana."





GIDANSU BABANGIDA KACIGARI:.



Kawu Manga yana gurfane a gaban wanshi yana yi mishi bayanin yadda suka ?arke a tsakankaninsu da Alhaji Abubakar Baban Bola. A jiya da daddare bayan sun baro asibiti kenan.
Yaso ma tun jiya yazo wajen wan nashi sai dai yace bari ya bari yau tunda Alhamis ce almajirai babu karatu sai rubutu, wanki, da wanke allo.
Wawo na daga gefe yana jinsu.
"Gabaki Wayan dukkan kadarorin yaronnan da muka yi musu kuWi basu kai kuWin da Alhaji Abubakar Baban Bola yake binshi ba, ciki mun haWa da motar shi, da motar Amaryarshi. KuWaWen dake cikin asusun bankinshine bamu san ko zasu isa a cikita bashin da ake binshi ba, a samu a gagganWa a biya wannan kuWaWe domin dai kada a shiga wannan kotu Yaya. Shi Alhajin zamu rokeshi ayi rubutu dasa hannuna da garantonshi, dasa hannun lauyan kamfani takaddun kadarorin duk su zama mallakinshi, ya Wan Waga mana ?afa kafin mu haWa ?an uwa ayi karo karon taimakon wannan yaro.
To babbar damuwata shine Babangida bazai tsira da komai ba daidai da muhalli sai mu mun taimaka mishi da inda zai zauna tare da iyalanshi. Mata har uku ga yara. Muna nema ma wannan yaro alfarma daga cikin gidajen hayar da kake dashi a bashi koda falle_fallene yaran sa dinga bin Wakuna"
Murmusawa Baba Malam yayi daman wajen da yake son azo kenan.
"Manga kenan. Lallai son Babangida ya gama rufe maka idanu. To amman ka sani ni idanuna a buWe suke ras.
Kasan Allah ko haya bazan iya barin Babangida yayi a gidajena ba, balle har ni in bashi muhalli kyauta ya zauna.
Batun kuWi da kake yi, ni fa wannan duk bata shafeni ba in kun mance tattaunawar da mukayi daku anan wajen in yana magana shima bai mance ba, dangane da dukiyar da Babangida yake ta wada?a da'ita, sai auren mata yake yana sakinsu, ba'a wata uku zai kuma jajiSowa kai kuma ka Waura mishi auren. Yaita ma mata Sarin dukiyar mutane, yaita saka suturun alfarma. Sai yanzu data dame mishi ne za'ace inyi wani abun? La babu abinda zance, babu abinda zanyi akai. Kuma ina mai shawartarku da ku bari aje kotu domin al?alai suke da hakkin fitarwa da me hakki hakkinshi, tunda harkar kasuwanci suke yi, Babangida shike juya kuWi. Iyakar shawarata kenan. Ita Shari'a saSanin hankalice sai kuga kun tsira da wasu abun da bakui zato ba.
Ai kana maganane akan gudun zubar da mutuncin gidan ko?
Akwai wani abun kunya da za'ayi kuwa wanda Babangida bai riga yayi bane?
Karfa ka mance Manga..."
"A_a Yaya ya isa dan Allah. Mun gode da shawararka in sha Allah zamu je kotun a yi komai acan
Wawo taso muje mu tattauna"
Cikin gidan suke shirin shiga Baba Malam yace.
"A_a Manga ba dai a cikin gidana zaku tattauna wannan maganar ba. In wajen Babba kuke son zuwa to kai Wawo shiga ka kirawota kuje can gidan Manga ku tattauna amman ba a gidana ba kuwa."
Ba ?aramin mamaki sukai ba. Amman in suka duba girman Malam da girman laifukan Babangida sai sui ma malam uzuri.
Wawo ya shiga ya kira Malama Babba suka haWu dasu sa'a a gidan Kawu Manga akaita tattauna yadda zata kaya daga karshe suka tsaya a matsaya guda ta a bari a shiga kotun ko Allah zaisa Babangida ya tsira da wani abun.
"To amman matanshi kuna ganin a sanar musu halin da ake ciki ko kuwa a bari a ?ar?are zaman kotu?"
Kawu Manga ne yake tambayarsu. Wawo yace.
"Gudun kada a saka su cikin damuwa kan damuwa inaga a bari aga ?arshen shariar tukunna. Kome kika gani Sa'a Kudidi?'"
Sa'a da jikinta yayi murus tace.
"E Wawo hakan yayi kada ayi gaggawar sanar musu tukunna. Mu jira abi komai a hankali. Amman ya batun karar da waccan balagazar ta shigar?"
Usman yace.
"Akan wannan ?arar data shigar Malama gata a zaune ko bacci bata iyayi. Duk halaccin da Baba Malam yaima yarinyarnan gada abinda zata saka mana nan"
Malama Babba ta nisa tace.
"Zaima saketa kowa ya huta. Yaji da Waya. Jira nake a sanarmun da farfaWowarshi tukunna. Ko a wayana zan kirashi muyi maganar. Tunda ya kamata da wani namijin ai dole ma su rabu."
Naja'atu tace.
"Ya kamata yaranma a kaisu asibiti ayi musu gwaji domin a tabbatar da nashi ne Amman malama Babba aurenki fa?'
Kawu Manga yace.
"Gidanku Naja'atu. Nace hakan ki. Yara dai namu ne da gani domin basu da bambanci da yaran Wawo da yaran Sa'a mu kininmu baya Suya. Sannan ke Babba da kike cewa zaki saka Babangida ya saki Sabuwa hala kin mance da sharaWin Yaya ne ko? Abi komai a hankali dai."
Haka dai akaita tattaunawa daga baya suka watse.
Wawo da matarshi suka tafi kai abinci asibiti.


Asibiti:.
Tun sassafe Yar shuwa ta kasance a asibiti. Hamida kuma taje raka iyayenta tasha zasu Wauki hanya.
Tana zaune a doguwar kujerar dake Wakin da Babangida yake kwance tanata tunani a ranta so take tasan menene yake faruwane taga tamkar dangin Babangida da akwai abinda suke Soyewa dai.
"Amman koma menene in tayi wari maji"
Ta faWi hakan a zuchiyarta. A hankali Babangida ya buWe idanunshi ya kalli sama, ya dawo da kallonshi wajen ?ar Shuwa da Ramadan dake zaune a kujerar roba yana gyangyaWi.
"Ramadan ka kira mun Mustapha a waya inason ganinshi"
Ya faWa yana nishi irinna jiki yayi tsanani.
Saida Ramadan ya garzaya ya kirawo ma'aikatan jinya kafin ya isarma da Mustapha sa?on Babangida. Mustapha yace dama suna hanya shi da matanshi gashi nan ?arasowa "
Likita na tsaye a kanshi yana aunashi, ga nurse a tsaye da kwando Wauke da takaddu da magungunan marasa lafiya"
"Malam Babangida ka daure ka rage ma kanka damuwa sabida jininka ya samu ya sakko. Kaga jinin bai sauka yadda ya kamata ba. Tunda dai kai musulmine dole ka yarda da kaddara me kyau ko akasin hakan. Ka duba iyalinka da iyayenka karka kashe kanka a banza yaranka suna bu?atarka a raye"
Dr ya dinga mishi nasiha tare da bashi musalai masu yawa, har da jawo mishi hadisai da ayoyin Qur'ani mai girma.
"Nagode sosai Dr. Komai zai daidaita in sha Allah."
Idanunshi ya runtse zuchiyarshi ke tuka mishi.
Har aka gama wanke mishi ciwon aka sake yima wajen dressing Babangida idanunshi aru??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fe sai ajjiyar zuchiya yake saukewa.
Bawai baya jin zafin ciwon bane har cikin ranshi yake jin motsin zafin. Amman zafin da zuchiyarshi take Wauke dashi ya doke zafin ciwon zafi.
"Yanzu ka samu kaci abinci kasha magangunanka, sai ka daure kayi wanka. Amman sai dai a goge maka jiki da tawul kada a kwara maka ruwa a jikinka.
Magungunan ya mika ma Ramadan, yayi musu sallama ya fita.
"Ramadan taimaka mun in soma watsa ruwan tukunna, ji nake kamar na shekara babu wanka.
Ramadan ya taimaka mishi suka shiga bayan gida, shi ya goge mishi jiki da tawul, ya buWe mishi sabon brush yayi. Alwala ya Wauro mishi ta hanyar shasshafa mishi ruwa ya kuma taimaka mishi suka fito.
Saida yaci abinci, yasha tea, ya haWiyi magungunanshi kafin daga gadon ya soma rama sallolin da ake binshi.
Duk wannan bidirin bakin ?ar Shuwa bai rabu dayi mishi sannu ba. Daidai da sannunta sau Waya bai amsa ba, inda take ma bai kalla ba.
Mustapha da iyalanshi ne suka turo ?ofar suka shigo suma ni?i_ni?i da kayan abinci a basket.
Daga me ciki, sai me goyo, sai me jego a matan Mustapha.
Gaggaisawa akayi kafin Mustapha yace
Dukkanku ku bamu waje zamu tattauna in mun kammala kwa dawo"
Matan Mustapha da Ramadan suka fice, ?ar Shuwa kuma ta gyara zama ita a tunaninta ai duk abinda za'a tauna yana da ala?a dasu.
"Ke me kike nufi da ba zaki fice ki bama mutane waje ba?"
Babangida ya faWa da Waga murya yana zare idanu tamkar zai cinyeta.
"Kayi ha?uri jannaty da bata maka rai da nayi natuba.
Amman kaga yanzu haka daga gida aka turo mun hoton Sabuwa ita da wani a zaune"
A razane ya kalleta yana son ya furta kalma harshenshi ya gaza haWa kalmomin da za'a fahimta.
"Ya haka baiwar Allah, ya ina ganinki da hankalinki zaki faWa ma mara lafiya irin wannan maganar kuma?"
Cewar Mustapha kenan.
"Ka kyaleta wallahi so take zuchiyata ta buga in mutu a raba musu gadon dukiyata ki fice a Wakinnan"
Cikin fushi tayi ficewarta asibitin ma ta bari baki Waya dan ji take da badan Babangida jinya yake yi ba bai isa ya daka mata tsawa bata mayar mishi ba.
"Mustapha yaya kuka ?are dasu Sumy ne da Ramatu, wayata na hannunka ko?"
"Tana wajena dukkansu so suke dole sai sun zo asibitinnan sun duba ka. Kasan Allah da ace dukkansu sunsan a wanne asibitin kake kwance da tuni sun Saro maka aiki.
Amman ni ba wannan ba batun Alhaji Abubakar Baban Bola shi yafi Waga mun hankalina in fa bawan Allahnnan kudinshi za'a biya shi Babangida wallahi dukiyar daka tara kab sai ta ?are kuma bata kai ka biya shi kuWinshi ba. Nace kenan asirin rufin bakin da akayi mishi tsawon shekaru shine ya karye?
Cewa nayi ko zan kuma komawa Inugun ne in samu malamin a sake rufe bakin shi Alhaji Abubakar Baban Bolan?"
Kai Babangida ya shiga girgizawa tunda Mustapha ya soma magana, saida ya jefo mishi tambayar ?arshe ya samu zarafin cewa.
"Kaiya Mustapha bakin alkalami ya bushe. Ai tunda Alhaji Abubakar Baban Bola ya samu baki ya fallasa wannan maganar taje har kunnen Kawu Manga da Wawo kaima kasan tabbas Baba Malam yasan da maganar. To shi in an rufe bakinshi su iyayena da ?an uwana yaya zanyi dasu? Asirina ya riga daya fallasu"
Mustapha ya busar da iska daga bakinshi yace.
"A_a Babangida kacigari karka sare. Har su Baba Malam Win ba sai a sa a rufe musu bakinsu ba? Talauci da tsiyane fa suke shirin tukaroka. Ka bari a sake sabgarnan kaci gaba da dama dukiya"
Hannu ya Waga mishi hakan ya tilastama Mustapha yin shiru.
"Mustapha ba zaka gane bane. Mu ajjiye wannan maganar a gefe ta riga tazo ?arshe mu dawo maganar Sabuwa zuchiyata jinta nake tamkar zata tarwatse Mustapha. Kai a tunaninka wanne matakin ya cancanta in Wauka wanne hukunci zata karSa ita Lolon?"
"Hmm ni a nawa muguntar duk runtsi kada ka saketa tunda abinda take so kenan. Kaga duk bala'i dole ta ha?ura da wannan Wan iskan. Ai tunda takai ?ara kotu kada ka sake ka saketa. Sannan in ka saketa Malama fa sakinta Baba Malam zaiyi"
Dafe kai Babangida yayi yana kallon Mustapha.
"Kotu ta kaini akan me wai?"
Nan Mustapha ya bashi labari. Dariyar da tafi kuka zafi da ?una yayi.
"Zata ga sharri. Lolo zata gane kuranta sai tayi nadamar shigar da wannan ?ara, kazalika sai tayi nadamar tunzurani da tayi. Zata ga makircin lauyoyi kuwa shi kuma farkanta zai sha mamaki wallahi"
Sun daWe sunata tattaunawa da Mustapha kan yadda zasu Sullo ma lamarin.
"Kaga fa wayarta na hannuna amman babu ma chaji farkan nata yaita kiranta tare da tura mata kalmomi daWaWa akan ta kwantar da hankalinta. Tana fitowa daga gidanka zasu yi aure. Duk iyakar runtsi kada ka sake a rabu da'ita wallahi"
Tari Babangida ya soma babu shiri Mustapha yayi shiru da bakinshi. Babangida yayi juyin duniya Mustapha ya bashi wayar Lolo amman ya?i fur ya kaWa ya raya fur Mustapha ya hana wayarnan.
Mikewa yayi yai mishi sallama ya fita akan da yamma inya taso aiki zai zo.
Yana fita Hamida ta shigo ta nemi waje ta zauna a farar kujerar dake gefen gadon.
Babangida kuma yana jingine shiru yanata lissafin halin da zai shiga in Alhaji Abubakar Baban Bola ya ?wace dukiyarshi, ga shariar sabuwa dole tana bu?atar makiran lauyoyi masu yima mutum sharrin da sai ya tsani shari'a. To su kuma ba ?aramin kuWi suke bu?ata ba.
Wani Sangare na zuchiyarshi yanata jaddada mishi ya saki Sabuwa kawai ya huta tunda ba sonta dama yake yi ba.
Wani shashe na zuchiyarshi kuma sai yaji yayi nauyi. Sosai da sosai
MRS BUKHARI

Ina manyan mata masu capacityn suke? ku fito lambarku ce ta fito.
?ar uwa turaren wuta kike nema nau'ika daban_daban masu musulmin ?amshi da kama muhallu? Ba itacen banza masu sanya gida ?auri da hayaki kamar an kunna taohuwar bespa ba.
Matso gasu MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI nazo miki da duk abinda kike bu?ata na ?amshi. Kama daga turarukan wuta irin na gidan alfarma. Zuwa humrori iri daban daban masu musulmin ?amshi da ri?e jiki.
Bugu da ?ari muna da turarukan kaya, na fesawa dana turara kaya.
Muna da kulaccam nau'i daban daban masu gyara jiki da lausasa fata mata, ga kuma ?amshi mai inganci.
Muna da turarukan tsugunno na musamman masu sirri Hajiyata
Muna da room freshener iri_iri
Muna da mopping mix masu kama waje.
Akwai turarukan kafet dana kujeru.
Sannan akwai box _ box setika na Hajiyoyi masu ?yallin goshi.
Muna da Amarya package.
Muna da uwargida package
Muna da maijego package
Muna bayar da sari ko a ?asar waje kike, muna tura kaya
Saudiyya
Nijar
Ghana
Camaron
A duk ?asar da kike kayanmu zai iso miki cikin aminci da yardar Allah.
Hajiya akwai Humrar matan aure wannan ta musamman ce.
Duk wani abu da kika sani na ?amshi babu irin wanda bamu dashi a kamfaninmu.
Muna da turaruka designer na maza da mata wanda kamfaninmu ke bugawa Hajiya babu inda zaki je ki ci karo da mai irin ?amshinki.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI TAZO MUKU DA DUK ABINDA KUKE SO NA ?AMSHI HAJIYA.
KUNSAN KANURI MUNE ?AMSHI DAMU AKE KOYI
SIYAN NAGARI MAIDA KUDI
MUNA MARABA DA MASU SIYAN ?AYA KO SARI.
LAMBAR DA ZA'A SAMENI KAI TSAYE ITACE.
Wa.me/2348179523215
SAI NA JIKU
IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA BIYU
SHAFI NA BIYAR
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

INA MI?A SA?ON GODIYA GA ?AUKACIN MASOYANA NA FA?IN DUNIYA.
MRS BUKHARI TAKU CE.


Sabuwa:.
Bani na farka ba sai ukun rana.
Da hanzari na mi?e amman jiri sai ya mayar dani na koma kan kujera.
Kasancewar yau alhamis yaran suna gida babu islamiyya.
"Sannu ummi kin tashi. Ya jikin?"
Mardiyya ta faWa da salon tausayawa. Su Adama ina jiyosu a kitchen kamar ba basu biyu bane.
Jiki da sau?i Mardiyya ina AWWa'u naga kowa shi banda shi?"
Sadiya ta fito daga kitchen tace.
"Gaskiya Lolo yaranki na da shegen yawo. Yau mune har kogi ammman babu shi babu dalilinshi. Muka dinga zagaye gidajen abokanshi wallahi suma abokan basa nan"
Take na sake shiga sabuwar damuwa dan na lura AWWa'u yana da rashin ji sosai kuma yaron bashi da tsoro sam.
Ni dai ko da nayi wanka nayi Sallah Allah na ro?a akan Allah ya shirya mun AWWa'u ina ro?on Allah kada AWWa'u ya Webo halina ko halin mahaifinshi na sa iyaye a cikin magana "
Kafinma in fito Labbai ta biyo ni da jallof Win taliyar Hausa taji attaruhu da albasa ga kifi an warwatsa.
"Lolo yaya ?arfin jikin naki? Ki samu ki daure kici abinci zuwa yamma mu le?a ?an asibiti. Naga waccan ba?ar kadarar ta dawo daga asibitin

6 / 25