Idan Kaya Ya Gaji Book 2 Hausa Novels Compelet by Badiat.doc

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 25

18K to 21K   out of 73.4K words

mun haWu da'ita a tsakar gida kinga kallon banzan da take yi mun kuwa? Taci sa'a yau aka sakeni jikina da sanyi da sai naci abu ta kazan ubanta"
Adama ce muka jiyo tana rangaWa mana kira da ji ba lafiya ba, babu shiri na tsallake abincin na fito da sauri.
Na'ila na gani sha?e da wuyan AWWa'u ga bakinshi na fitar da jini.
Lafiya meya faru Na'ila. Kai kuma meya same ka sarkin yawo?"
Tana jijjiga tace.
"Ai dole kice haka kin koya ma yaro sata. Kamar wannan yaron ace har ya iya shigowa Wakin mutane saWab saWab ya yi sata?"
Da mamaki na kalleta na dawo da kallona gun AWWa'u. Tabbas ya sata ga rashin gaskiya Saro_ Saro tattare dashi na gani. Dama bai dena satar ba kenan?
"Baiwar Allah ai nutsuwa zaki yi ki mana bayani a tsanake ba kizo kina jijjiga ba. In hau kike ji dashi iyayenki ne a gabanki. Ki sake yaron mutane ko?"
Adama tana ?arashe maganarta ta fincike AWWa'u a hannunta. Ni dai numfashi kawai nake ja da fesarwa.
Kudina gasu ya shiga ya satan mun daga shiga banWaki. Allah yasa yana ?o?arin guduwa ni kuma na shigo.
Narantse da Allah in ya kuma shiga yayi mun sata na lahira sai ya fishi jin daWi.
Ko da yake tarbiyyar da aka koya mishi kenan.
Uwarshi ma da ranar Allah aka kamata a mota"
Tana faWin haka naji wani abu ya tsirgamun
Ga yara duk suna wajen sunyi cirko _ cirko.
"Ke dakata ?aramar ?ar balaja'u mai tafe da wando. Ya zaki shigo har Wakin mata kina faWa mata magana.
Sata dai ai ba a kanshi aka soma ba. Kuma da kike cewa an kamata a mota ke a kamaki mana. Ya yi satan kuma ya saci banza"
Ai Labbai bata rufe baki ba Na'ila ta shiga Waga murya tana kwaroroto dan mutane suji dama nasan da biyu, amman Wan kuka shi ke jama uwarshi jifa. Na'ila kowa yasanta ba ?atamar munafuka bace ita da ?awarta Hamida.
A guje ?ar Shuwa ta le?o tana tambayar meke faruwa ai kuwa Na'ila ta faWa mata.
A lokacin har Maman Safara,u ta shigo.
"Uhm Allah ya kyauta. Sata yaro kamar wannan?
Ashe duk ?an canjinan da muke ajjiyewa mu rasa shine yake sacewa.
"Ya sata dan uwarki kiyi abinda zaki yi in baki bar wajennan ba zaki sha mamaki"
Inji Adama.
"Hehehe me zanyi kuwa. Kuji da sakin duk da akai muku itama Lolo tana hanya dan baku isa kun tare mana a gida ba"
Nayi mamakin yadda akayi ?ar Shuwa tasan auren Adama ya mutu, gara ma na Labbai tunda anyi rikici harda motar ?an sanda.
"Ayi ha?uri Labbai dan Allah kada ku sake cewa uffan.
Ke kuma maman Fatima ki koma Sarayinki.
Na'ila tunda dai kinga kuWinki sai kiyi ha?uri duk a taru ayi ha?uri "
Tsaki yar shuwa tayi ta wuce fuu. Adama ta tasanma zagi
Na'ila kuwa saida ta dinga zage_zage tukunna.
Ni tana zage_zagenma na zame na shiga ciki na dira a wuyan AWWa'u kamar Allah ne ya aikoni har gwara kanshi a bango nake yi.
A tunanina ya dena sata tunda muka baro tsohon gidanmu. Sata babu irin wacce AWWa'u bayayi har atampa ya sata ya siyar ya kashe kuWin. Nasan jarabawace tunda guda nawa yaron ma yake.
Su Maman Safara,u ne suka kwaceshi a hannuna duk goshinshi ya fashe, ni kuma sai haki nake yi
Maman Safara,u da Labbai ne suka garzaya dashi kemis ni ko dana shiga Waki sai kuka, na daWe ina rera baitukan kuka kafin nayi shiru. Adama na zaune tana cewa in gode Allah a hakanma,
Su Mardiyya kuwa kowa ya shiga taitayinshi, ban fiye dukansu ba amman inna tashi dukan yaro ni saina fitar mai da jini hankalina yake kwanciya.
Da sallama Labbai ta shigo.
"Lolo ki daure kici abincin ki tuttura nasa Mardiyya ta kawo miki tea wancan yayi sanyi. Kinga biyar har tayi mu samu muje asibitinnan ko?"
Ko magana na kasa yi, ina gani sukai wanka duk suka saka suturuna. Da ?yar nayi ma abincin loma uku tean ne ma na rufe ido na shanye na tashi.
Sallah nayi na sake kayana muka nufi asibiti harda yaran duka, AWWa'u naso barinshi a gida amman da nai wani tunanin dole na ja hannunshi muka tafi asibitin.
Hamida na ciki tana ba Babangida tea muka shigo.
HaWa idanu muka yi dashi na wani haWe girar sama data ?asa na nemi waje na zauna.
Su Adama ma da suke yi mishi ya jiki babu na wacce ya amsa.
Yara dai sun yi mishi ya jiki ya amsa musu ciki _ ciki.
Hamida bata kula kowa ba, babu wanda yabi takanta in banda yara da suka gaisheta.
Jigum_jigum muka zauna na kusan minti talatin.
To Labbai ku taso muje ko magriba har tayi"
Mun tashi kenan muka ga an turo ?ofar an shigo
Mustapha ne ya soma shigowa abokanshi suka mara mishi baya.
Suna ?arasa shigowa nayi ficewata su Adama ne suka tsaya aka gaisa kafin suka fito suka same ni muka wuce gida.
Sai bayan isha muka shiga gidan. A tsakar gidan muka tarar da Kawu Manga da Wawo, da ?ar Shuwa a tsaye tana mi?a ma Wawo key kamar dai na mota ne.
?arasawa mukayi aka gaisa. Kawu Manga yake tambayar meya samu AWWa'u. Kafin in yi Magana mandiya tace.
"Sata ya shiga yayi a ma?ota shine matar tai mishi irin wannan dukan."
Jim yayi muma duk mu kai shiru kamar ruwa ya cinyemu.
"Allah shi kyauta. Ai sai a ci gaba da bashi rubutu yana sha ko Allah zaisa ya dena"
Wawo kuwa girgiza kai kawai yake yi.
A sanyaye mukai musu sallama muka shige Sarayina.
Duk bamu zauna ba Alwala kowa ya shiga yi, saida akayi Sallah suka soma kiciniyar cin abinci kuma.
Ana gamawa yara suka tafi Wakinsu, muma muka kwanta
Ni dai juyi kawai na dingayi har iya awannin da ban isa sani ba.

Washegari:.
Bayan hantsi muka shirya ni da Labbai Adama yaranta sunzo wajenta dama tace ita ba zata je wani asibiti ba.
A can muka tarar da ?ar Shuwa da Hamida, Kawu Manga da Wawo ma suna Wakin muka shigo.
Ba'a ko gaisa ba wasu mata su su biyu suka shigo da ganin kamanninsu uwa da ?a ne, ga yarinya da bata wuce ?ar wata takwas ba a ri?e a kafaWar wannan dattijuwar, wata kyakkyawar matashiya na biye da'ita
"Ohh Babangida ashe haka jiki ya tsananta ji hannunka yadda ya aune"
Inji wannan dattijuwar.
Ni yaron dake ri?e da hannunta ma nake kallo yaro mai kama da Babangida tamkar an tsaga kara.
To su kuma suwaye waWannan na faWa a raina
Bani kaWai ba harsu Hamida wannan Wan yaro suke kallo.
A murya kawai na fahimci Babangida bashi da gaskiya yadda duk ya daburce yana zare idanu.
"Bayin Allah ina wuninku, yaya kuma me jikin?"
"Jiki da sau?i gashi nan"
Hamida ta ba dattijuwar amsa a yatsine.
"Baby yaya ?arfin jikin naka kaga yadda ka rame kuwa? Na kira Mustapha sai yi mun hanya hanya yake yi. Ni kuma ina ganin lokaci yayi da zan bayyana kaina ga iyalinka sabida tsoron halin mutuwa ko dan sabida wannan yaron"
Inji wannan matashiya.
Mu dai duk munyi tsit muna sauraren ikon Allah
Dattijuwa tace.
"Gaskiya ne kam. Ni kaina sai bayan kwanciyarka a asibiti nayi nadamar biye muku da nayi a matsayina na uwa. Yarinyarnan tun sanda labarin rashin lafiyarka ya sameta take cikin damuwa sabida abokanka kab sun kasa faWa mata a wanne asibitin kake."
Babangida ya kalli su Kawu Manga da sukai tsuru_tsuru ya dawo da idanunshi kanmu kafin ya runtse idanunshi tare da dafe kanshi da hannunshi mai lafiyar"
"Hajiya mu bamu gane ba fa. Ku Win su waye ne daga ina?"
Cewar Wawo da kanshi yafi na Kawu Manga daurewa. Ni kam tuni na gane matarshi ce tabbas ko kaffara babu.
"Bawan Allah ka tambayeshi wa?a a bakin me ita yafi daWi ai. Ke Ramatu jeki ki zauna acan baki fiye juran tsaiwa ba."
Kusa dani da ?ar shuwa tazo ta zauna tace.
"Sannunku"
Tana mana kallon banza.
Yauwa sannu"
Na amsa mata.
"Kai Babangida su waye waWannan matan, menene ala?arka da me kiranka Baby?"
Ya daWe sosai yana tauna maganar kafin a sanyaye yace.
"Matatace Kawu kayi ha?uri "
Salati su Hamida suka shiga yi tare da tafa hannaye.
Ni kuwa sai murmusawa nake yi.
Ba ?aramin tashin hankali da damuwa ?ar Shuwa ta shiga ba.
"Matarka, yaronma da cikin duk naka ne kenan naga kamar ciki ne da'ita ai?"
Kai kawai ya Waga ma Kawu Manga.
Shiru yayi yana nazari kafin yace.
"To ai Shikenan babu damuwa tunda dai aure kuka yi.
Waye maWaurin auren to?"
"Baba na shago ne"
Kawu Manga yayi shiru ya kasa cewa komai Wawo kuwa inya kalli Babangida sai ya kalli Kawu Manga.
"Hajiya gara da Allah yasa ku kai tunanin zuwa tun wuri ba har saida lokaci ya ?ure muku ba."
Wannan dattijuwar tace.
"Hala mahaifinshi ne kai ko?"
"E uba nake a wajenshi"
Sai tace.
"Alhamdulillah ga Ramatu itama a bata Waki a gidan mijinsu ta zauna a haWu ayi jinyar Babangida tare da'ita. Gidan da suke ciki ma Wanta ya karSe har ya siyar sakamakon wani iftila'in daya afka mishi.
Ni kuma bazai yiwu taci gaba da zama a gidana ba tunda dai mijinta yana da gida. Dama kuma ba da son ran dangin mahaifinta aka yi auren ba. Ganinta a gida da akeyi sai aka soma tsogumin ko aurenne ya mutu"
Kawu Manga yace.
"To yayi. Ke Sabuwa in zaki tafi ki tafi da wannan baiwar Allahn ta zauna a turakar Babangida tunda a halin yanzu babu inda zata zauna zuwa a sallamoshi"
To Kawu in sha Allah"
Na faWa da ?arfin guiwata.
"Keyn turakar a hannun wacce matar taka yake?"
Babangida tsabar kunya ne, ko meye yama kasa Wagowa ya kalli kowa yace.
"A hannun Maman Fatima na barshi"
Kawu ya dubi ?ar shuwa yace.
"Kin yana tare dake ne, ko yana gida?"
A kumbure tace.
"Yana gida"
Bai damu da kumburinta ba yace.
"In kin koma sai ki ba Sabuwa keyn. Wawo da Ramadan ku taso muje. Matanshi zasui jinyarshi su dinga yin kama_kama"
Ai kuwa suka haWu su uku suka fice, da gani a ?ule Wawo yake ainun dama gashi da faWa.
"To Ramatu da Alkhairi in kin isa gidanki mayi waya ki mana kwatance ko. Babangida Allah ya ?ara sau?i"
"Ameen nagode Mama"
Wannan dattijuwa ta fita Amarya ta bita a baya.
Yaro kuma yana wajen Babangida a yanata mishi kwarance
"Hmmmm. Hmmmmm. Hmmmm"
Shine abinda ?ar Shuwa take ta nanatawa idanunta sunyi jawur dasu. Wallahi ni kuwa raina fes tamkar audiga.
Labbai muje masallaci muyi Sallah sai mu Wau haramar gida ko?"
Na faWa tare da mi?ewa. Kafin mu fita Amarya ta dawo, mu kuma muka fice.
"Lolo haka mijinku yake kamar bunsuru wajen son mace?"
Haba Labbai ai sai dai ki kirashi Ayu baban bunsurun kenan. Ni wallahi abun yayi mun daWi. ?ar Shuwa ai gani take ta mallake Babangida sai yadda tayi dashi. Bata san ya fita cin kai ba, a tafin hannunshi take.
Ya kika ga Amarya kyakkyawa da'ita gashi a doke ba dokuwa zata yi ba ba"
Dariya muka saka.
Har muka isa masallaci bamu dena dariyar ba. Ko da muka idar da Sallah a hanyarmu ta komawa cikin asibiti zancan dai muke yi.
Muna tura ?ofa muka tarar ana gurmi, wai damme Amarya da zuwanta zata shiga tattaSa Babangida a gaban matan gaban goshi. Ita kuma Amarya tace ai mijinta ne itama.
"Ya isheku haka ko, kasheni kuke so kuyi ne kome. Ke Maman Fati me yasa bakya son a zauna lafiya ne?"
?ar dariya ce ta subuce mun da naji yau babu Habibaty sai Maman Fati
"Maman Fati ka kirani yau gatsau Jannaty sabida wannan abun?"
"Wacece Abu? Ai wallahi nafi ?arfin abu ke da gani kinsan ni dake babu haWi"
Da ?yar dai sukai shiru sai da ya daka musu tsawa sannan suka nutsu.
Amarya mu zamu tafi, kin shirya tafiya ne yanzu?"
A wula?ance tace.
"Ni anan zan kwana kije kawai"
Tana faWin haka ni da Labbai muka juya muka fice abinmu.
Ya suka ?are ohon musu dai.



Baba Malam:
Yana zaune a zaure gashi ga Malama Babba da Malama ?arama da Wawo, da Kawu Manga.
Kawu Manga ya kwashe komai ya faWa musu ya Waura da cewa.
"Kai tsaye wajen shi Baba na shago muka je. Ya tabbatar mana shekara Waya da kusan rabi kenan da Waura auren
Wannan shine abinda yake faruwa a gaskiya na kusan cire hannuna akan Babangida koma ince na cire hannun nawa. Shi wanne irin yarone?"
Malama Babba dake ta faman salati sai ta sau kuka.
"Yanzu ashe a duniya akwai abinda Babangida zaiyi ba tare da ya shawarceni ni mahaifiyarshi ba?
Wannan yaro ina zansa ba?in cikinshi?"
"Ai tukunna ma Babba. Ba dai kina bayan rashin gaskiya ba, in dai kuka ne ai bakiyi ba.
A baya irin kunyar da Babangida ya saka mu ta wasa ce.
Bari in faWa miki ki kuma sani batun Sabuwa data maka ku a kotu. Kisa a ranki muddin al?ali ya saki Sabuwa tamkar ke ya saka in baki sani ba ki sani igiyar auren Sabuwa a ?ulle suke tare suke tafiya da igiyar taki auren. Ai sanan kinsan da zaman wannan sharaWin
Kuma daga yau ban amince Babangida ya sake tako ?afarshi ya shigarmun gidana ba.
Na zame shi daga cikin jerin ?a?ana ko mutuwa nayi kada yazo kan gawata."
Salati Kawu Manga ya shiga yi ganin yadda Malama Babba take shiWewa.
"Kawu mu kaita asibiti kada ta mutu. Malama Babba"
Wawo ya shiga kiran sunanta.
Babu shiri suka kwasheta zuwa asibiti cikin rashin hayyaci.
Malam ya runtse idanunshi wasu hawaye masu Wumi suka zubo mishi.
Ya lura Babangida shine zaiyi ajalinshi da ba?in cikinshi. Sai kace shi kaWai aka haifa duk yabi ya fitineshi, bashi da aiki sai jaye_jayen magana tun yana ?arami.
A daddafe ya rarrafa ya shige turakarshi ko gani bayayi.
Jin har an kira Sallah a masallaci Baba malam bai fito bane Idirisa ya shiga turakar ya samu Baba malam a ?asa babu yadda yake.
Kan kace me mazan gidan suka rufu a kanshi.
Su Wawo suna asibiti aka bugo musu waya ana sanar dasu halin da Malam yake ciki.
Babu shiri Wawo ya baro asibitin ya bar Malama ?arama acan da Sa'a da bata jima da zuwa ba.
Malam dai anyi juyin duniya a kaishi asibiti ya?i fur. Dole sai likita aka kira mishi har gida yazo ya duba shi.
Jininshi ne ya hau sosai da sosai.
A wannan rana iyalan gidan Malam Baba basu runtsaba a cikin wannan dare da ya shiga tarihin daren da Babangida ya tashi hankalin kab ahalin gidan. Gashi a wannan karonma silar Babangidan ne.

Babangida:.

Shima yana asibiti jikinshi ya tashi sakamakon fargabar abinda kaje yazo. Yasan matsawar Baba Malam yaji abinda ya aikata tamkar sake rura wutar ?iyayyarshi yayi a zuchiyar Baba Malam. Hatta Malama Babba da a kullum burinta ta kareshi yasan in taji wannan labarin zai ruguza mata zuchiya.
Wannan abunne duk suka taru suka haWe mishi.
Gashi da ?yar ya kori ?ar Shuwa da Hamida a asibitin suka bar Ramatu ta yi zaman jinyarshi na kwana Waya.
"Baby jikinne yake damunkane? Wai garinma yaya kaji irin wannan ciwon ne?"
"Kar ki damu. Ki daure ki kiramun likita hannuna tsami yake yi mun"
Mi?ewa tayi ta fita, yabi bayanta da ido kawai.
Takamaimai ya rasa tunanin me zaiyi ma zuchiyarshi a cunkushe take sosai.
Haka dai wannan daren ya kasance musu dare dubu da Waya
>?#?>?#?

MRS BUKHARI
Babangida yana ruwa

IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA BIYU
SHAFI NA SHIDA
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


GA ?ARIN SHAFI ALLAH YASA ZUKATANKU SUYI SANYI.

SABUWA:.

Haka dai lamura suka ci gaba da tafiya suna jiyawa.
Matan Babangida suka ci gaba da jinyarshi yau wannan ta kwana gobe waccan.
Amarya dai tana turakar mijinta. Yadda na fuskanceta bata da ha?uri kamar zawayi haka take, shi yasa kusan kullum ita da ?ar shuwa sai sun hau sama sun duro, gata da gadara da girman kai.
Ni dai tun daga wannan ranar kafata bata sake taka asibiti ba.
Malama Babba ma har aka sallamota banje ba.
Baba Malam kam naje har sau biyu gida na duba shi.
Shine ma ya sanar dani a tsanake in tattare kayayyakina waje guda, in SaSSalle gado da komai nawa dai. Bai mun bayanin komai ba, nima ban tambaya ba na dai bi umarninshi nida su Labbai mukai ta kaye_kaye. Sai da su Sa'a suka zo gidanne ?ar Shuwa ta rakouu barayina ko zama sun kasa yi.
"Ku haWa kayayyakinku waje guda zaku tashi a gidan. Za'ayi ma gidan gyara sosai ne"
Bata bari na amsa ba suka fice.
Amman jikina yana bani matsala ba tun yau ba, dan na fahimci su Kawu Manga sai kai kawo suke yi hatta motar ?ar shuwa babu. A zuwa na duba Baba malam na ukunne ma na tarar an sallamo Malama Babba sai na shiga na dubata da jiki.
Ta rame ta komaWe sosai.
"Sa'a ku bamu waje inaso zanyi magana da Sabuwa"
Bani kaWai ba harsu Kudidi suma sun yi mamaki. Ni ko kaina cike da tambayar da babu wanda zai iya amsa mun.
Nan duk suka zame suka fita. Cikin gadara Malama Babba tace.
"So nake ki janye wannan shar'ar da kika shigar da ?ara kotu. Na yi miki al?awarin ko nawa kike bu?ata zan baki"
Da mamaki na kalleta sai kawai nayi murmushi nace.
Bazan iya janye wannan ?aran ba, ko da duniya da abinda ke cikinta zaki bani. Takaddar sakina yafi mun komai"
A_a dai kije kiyi tunani nan da kwana biyu kinga lokacin shiga kotu ya kusa. In kika janye zan baki kuWi masu kauri "
Daga sama muka jiyo muryar Baba Malam
"Babu mahalukin daya isa yasa ta janye. Da kike maganar kuWi kuma a ina kika samesu ni bani da masaniya a kansu? Ai dani kika bama kya samu lada.
Ke Sabuwa taso ki kama hanya ki tafi gidanki"
Sum_sum na ficewata ya suka ?are sai Allah.
Ina isa gida a ?ofar gidanmu naga wata ?atuwar mota tana ta loda kayayyakin Waki harda gadona na hango a cikin motar.
Ban gama mamaki ba Labbai ta fito da ?atuwar randa ta cike da kwanuka da su cokula.
Ga Hamida itama a gefe tanata zuba kayayyaki a buhu. Gidan duk ya hautsine
Hannuna Labbai taja muka shiga cikin gidan"
"Kinga muna zaune Wawo ya le?o yace mu fito da kayanmu. Lallai Sabuwa zaku sha gyara. Amman naga gidannan babu abinda ya sameshi sai samannan da ake tadawa"
Jikina a sanyaye nace.
Sunce gyara za'ayi sosai a gabanki fa Sa'a ta faWa mana. Ina Adama fa?"
"Tana ciki tana fito da kaya muje daga ciki"
Ciki muka shiga muka ci gaba da harhaWe kaya.
Motar ma ta cika har sun tafi kai kayan.
Ni ko har mun gama fitar da kab kayanmu waje, har Adama ta share Wakunan, ni da Labbai mun goge komai da komai.
Har wajajen bayan la'asar yara suka shigo suka samemu muna jira, Adama dai tabi motar kaya da suka dawo.
Ma?ota duk an shisshigo dan jin ba'asi.
Da an faWa musu gyara za'ayi mana sai su

7 / 25