Idan Kaya Ya Gaji Book 2 Hausa Novels Compelet by Badiat.doc

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 25

9K to 12K   out of 73.4K words

da Dr daga Wakin. Wawo ne ya nemi a sake ma Babangida Waki, a saka shi a I P U nan da nan aka maidashi abinka da kuWi harma kulawar da ake bashi aka ninka.



SABUWA:.
Mu dai muna ta zaune mu na Wan taSa hira da Labbai.
Daga shigarsu Hamida wajan Babangida har fitowarsu, kama zuwansu Kawu Manga da fitowarsu, da sake ma Babangida Waki duk ina zaune ina buga lissafine kawai.
Bamu muka bar asabitin ba har saida muka yi isha, muka tattare kwanukan abincinmu wanda Ramadan ne kaWai yasha farfesun mukai musu sallama muka tafi.
A nan muka baro Kawu Manga da Wawo.
Hamida,tun yamma ta dawo gida ita da ba?inta. ?ar Shuwa da ?annenta ?ila nan kwana dan naga basu Waura haramar tawowa ba.
Ko da muka shiga gida munyi tulis da gajiya tara da kusan kwata muka shigo.
Mardiyya ce ita kaWai a zaune a falo tana ta karatun Alqur'ani. Tana ganinmu ta mi?e.
"Ummi kun dawo. Ya jikin Baba"
"Jikin Babanku da sau?i. Ina su AWWa'u?"
Labbai ta bata amsa.
"Allah ya ?ara sau?i. Su Aminu tun Wazu sukai bacci. Ummi Wazu AWWa'u daga zuwa masallaci yabi abokanshi rafi da daddare da ?yar muka ganshi. Dana dakeshi shine ya zageni"
Kai kawai na girgiza wannan yaro baya ji sam. Kullum ina mishi adda'ar shiriya.
Hmm barni dashi gobe da safe zaki ga yadda zamu kwashe. Kije ki kwanta muma a gajiye muke."
Sallama tayi mana ta wuce Wakinsu.
Ni na wuce ciki kai tsaye zuwa banWaki dan in watsa ruwa ko zanji daWi, Labbai kuma kitchen ta nufa dan ta sama mana abinda zamu ci.
Ina zaune ina shafa mai wayar da Baba Malam ya bani ta soma ringing. Nadai san lauyan da akace zai kirani ne.
Dagawa nayi da sallama a bakina.
"Ameen wa alaikis salam. Sunana barrister Ahmad Ahmad. Ina magana da Sabuwa ne wacce ta shigar da ?arar mijinta tana neman ya saketa?"
Idanuna na lumshe a hankali wani irin zazzaSine yake hudani sosai.
E nice ina wuni?'
Na bashi a takaice.
"Lafiya lau. Gobe inaso ni dake mu haWu dan mu tattauna dangane da Shari'ar da zamu soma. Sabida musan yadda zamu bullowa lamarin dan shari'a a tsakankanin mata da miji sharia ce mai rikitarwa.
Inason jin jawabai daga gareki."
To Shikenan a ina zamu haWu, ko zanje gidan iyayena sai ka sameni acan. A unguwar Zai suke"
"Yauwa hakan yayi. Kije zanzo da misalin karfe takwas na safiya sai kiyi iya ?okarinki kafin lokacin ki rigani isowa."
A haka muka daddale na sauke wayata.
"Kixo muci abinci. Indommie da dafaffen ?wai na dafa mana sai tea"
Bakinta cike da ?wai take maganar. Ni tean kaWai na sha na watsa magungunana.
"Lolo na fahimci kamar bayan ciwon Babangida kamar akwai wata matsalar kuma. Amman ke me kika fahimta?"
Ta kafeni da idanunta tana son taji ta bakina.
Toh ni nafi tunanin ciwon nashi ne, ko dalilin ciwon nashi. Amman banyi tunanin wata matsala ba"
"Amman da gaske ne Lolo da wano Babangida ya kamaki, ko dai ba?in zargine da jan kishi dake damunshi?"
Numfashi naja tare da cewa.
Da gaske ne Labbai. A mota yaga an saukeni da ledar shopping. Iyakar abinda kaWai ya gani kenan"
Tambaya take son sake jefo mun na katseta.
Dan Allah ki barni inji da abinda yake damuna. Koma menene aurenmu yazo ?arshe ko ya ganni ko bai ganni ba ba shikenan ba?"
Gado na haye na rufe idanuna zuchiyata da jikina nata mu?ur?usata. Bansan sanda nayi bacci ba. Zage_zagen da Labbai naji tana ta yi a wayane yasa na farka naga gari har yayi shaa. Da sauri na shiga banWaki na Wauro alwala sabida tsabaragen jarabar da take ta faman yi a waya ni dai sai a Wakin yara nayi Sallah. Su kuma sunata wanka da shirin makaranta.
Sai kallonsu nake yi ina tausaya musu. Bansan yaya zasu fuskanci rayuwa ba, ban kuma san wacce iriyar rayuwa zasu yi bayan bani a tare dasu ba. Ban kuma isa cewar a bani yarana ba, domin nasan Babangida na da hujjojin da zai gabatar a kotu yasa a hanani ri?on ?a?an. Nima ina cikin damuwa da tsoron kada in ri?esu tarbiyyarsu ta lalace duk da bazan iya rayuwar gidanmu ba nafi son in kama haya in zauna ko zan nutsa.
AWWa'u zo nan"
Na faWa da murya mai kauri. Da sauri yazo wajena dukanshi nayi niyyar yi, hannuna daya kama yasa zuchiyata tayi sanyi abinka da uwa.
Wato jiya dan bana nan shine AWWa'u kayi tafiyarka yawo har saida aka nemoka ko? Sannan ka zagi Adda AWWa'u na ro?eka da girman Allah kabi Allah kabi duk abinda Adda zata ce maka ka Wauketa tamkar uwa.
Har da kai Aminu, dake ma Malama da kike muttsuka idanu."
Duk sai akai dariya baki Waya na dinga yi musu nasiha.
Kafin na mi?e na fita zuwa kitchen dan anan na jiyo Suruntun Labbai.
Doya da ?wai take ta soyawa. Tana yi tana Wure_Wuren ashar harda sharar hawaye.
"Se me dan kace in yi zamana a gidanmu. Ni da sakina kayi da yafi mun Wan gidan ta?i zama ta zauna kawai.
Ke kiji mun wannan maras mutuncin Habu, daga na Wan tambayeshi kuWi nera Wari biyar fa. Shine ya zage ya shiga yi mun Wiban albarka, har yana cewa in zauna a gidanmu in ubana ya koya mun tarbiyya na koma.
In kaya ya gaji gammo ma ya gaji. Babu inda zan koma sai dai ya aiko mun da takaddata dukan ya isheni.
Nifa yanzu in ba mai kuWi ba bazan kuma aure ba.
Jibeki ko dukanki akeyi zaki ci kuka ki toya ?wai ki kunna ac ga tv ga suturu.
Mufa a dakemu mu fito mu tu?a tuwo miya lami, da safe kokkone ko sigari babu wacce take da kuWine zata sai masa, kosai, ko ?ar tsala fa"
Dariya na kwashe dashi, itama dariyar ta saka.
Ke dai yi maza ki sallamesu, mu ki juye mana namu a kula maci a gida sauri nake yi kinga har bakwai tayi.
A gurguje muka gama komai muka fito tare da yaran
Karfe takwas saura minti goma muka isa gida.
Nanma muka tarar maigogul yana yima su Rakiya tujarar daya saba. Duk suna tsaye ya faWa su da faWa, Rakiya ta zageshi tas.
Wani abune ya tokareni a wuyana banko kallesu ba nayi shigewata ciki.
Su Sadiya duk suna ciki sunata karyawa harda Uzairu zuchiyata. Da magazin. Ko wanne cikinsu da abinda yake ci, dan kowa da kudinshi ya siya.
"Labbai kafin ki zauna zo ki karSo mun waina"
Cewar Rakiya data le?o.
"Ga ?wai da biredi da doya Rakiya zai ishemu ki shigo"
?wafa tayi ta shigo ta baro Maigogul da Hauwa suna ci gaba dayi.
Mu kuma muna karyawa su Sadiya sunata hirarsu. Uzairu zuchiyata yace.
"Ashe dambarwar tsiyar da akayi kenan ke Lolo? Uhm ai wallahi Gaza yayi mun daidai. Allah ne ma ya so shi bama gidan wallahi da raunin yafi haka."
Magazin yace.
"Wanne rauni? Ai kasan Allah da ace inanan to sai dai gawarshi. Nifa da har ubanshi daya tako gidannan saina tsinke mishi agara Allah"
Danna ?wai yayi a bakinshi wanda ya gutsura a cikin kular gaban Labbai.
"Ai ?arshenta Rakiya a gidan gyaran hali zata ?arke rayuwarta in dai bata dena wannan shegiyar sana'ar kayi nayin ba. Mata sai sayen kayan sata"
Tana jin Maigogul ya faWi haka zuruf ta fita dawa Allah ya haWata in ba dashi ba. Uzairu zuchiyata a guje ya bita yana aikin dariya.
Nidai lauyana daya kirani na rakici Labbai nace tazo muje.
A lokacin da muka fito har gidan ya soma Winkewa da maza da mata ?an ban hakuri maigogul ya tuSe rigarshi ya doka da ?asa zai doki Rakiya, ita kuma anata ri?eta akan yana dukanta zata rama.
Ficewa muka yi a wajema matan unguwa duk an firfito anata gulma harda mahaifiyar ?ar Shuwa.
"Mutanen banza gida sai kace karnuka. Ni na taSa ganin jahilai irin wannan gidan kuwa? Kamata yayi wallahi a koresu a wannan unguwar domin zasu lalata mana tarbiyyar yara"
Allah sarki inji mahaifiyar ?ar shuwa kenan fa. Wai me bunu a ?un?uru ke kai gudunmawar gobara. Wacce kalar karuwace bata da'ita a gidan nata. Su kansu masu gulmar ko wanne nada guntun kashinshi, sai dai dake ance lefe tudu ne, kahau naka domin kayi le?en na wani. Allah dai ya basu sa'a dan Magazin zai iya fitowa nasan ya watsasu.
Wani mutum ne naga ya fito daga farar motarshi, yana saye da surt ba?a?e da ba?in gilashi, ya nufomu.
Nanfa kallo ya koma kanmu gulma a kyauta.
"Kece Sabuwa ko?"
Ya tambaya yana nuna ni da manuniya"
E nice sannu da zuwa. Ga dakali mu Wan gangara mu zauna"
Na nuna mishi dakalin ?ofar gidansu Babayo muka ?arasa muka zauna, muka sake gaisawa.
MRS BUKHARI

Sanya

IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA BIYU
SHAFI NA HU?U
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI



https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA




Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa=??? Ko kimin mgn ta=?G? 08093932955





"Zanso insan menene dalilinki na shigar da ?arar mijinki ya sake ki, shin wanne hujja kika ri?a a matsayin babban dalili, sannan in ba'a kotu ba bazai iya sakin ki bane?"
Kaga lauyoyi duka wannan tambayoyin lokaci guda aka watso mun. Kuma ya kafe ni da ba?a?en idanunshi yana jiran amsa.
Dalilin da yasa na shigar da ?aran shine bana sonshi, duk kwanan duniya ?ara tsanarshi nake yi.
Hujjata shine.
Ya dena ciyar damu, baya shayar damu, baya mana sutura, baya biyan kuWin makarantar yara, baya mu'amalar aure dani.
Sannan tambayarka ta uku tsawon shekaru sama da goma ina faWin ya sake ni yana cewa ni dashi mutuwace zata raba, kuma badan yana sona ba sai don mugunta kawai"
Kanshi ya jinjina yace.
"Yana cin zarafinki ne, ko zarafin iyayenki, sannan yana dukanki ne?"
Babu wanda bayayi daga cikin abinda ka lissafo. Babangida ya wuce tunaninka, wata iriyar ba?ar zuchiya gareshi."
Shiru yayi yana nazari can ya jefo mun wata tambayar.
"Auren dole kuka yi ko Auren soyayya kuka yi?"
Bazan ce auren dole ba, ba kuma zance auren soyayya ba. Babangida yayi mun irin soyayyar da babu mahalukin da zai iya yi mun ita a duniya.
Daga baya ne komai ya lalace.
Amman karka tambayeni dalilin lalacewar domin bata shafi shari'ar ba"
Murmusawa yayi kawai kafin yace.
"Iyayenki suna bayanki ne akan shari'ar kamar yadda Baba Malam yake bayanki?"
Kai na girgiza nace.
A_a basa bayana kona mis?ala zarratin."
Mijin Labbai ne yazo ya wuce mu, Labbai tayi tsaki ta bishi da harara.
Barrister Ahmad Ahmad yace.
"Baba Malam menene hala?arshi dake?"
Shine mahaifin mijin nawa"
Har a jikinshi saida mamaki ya bayyana ba'a iya fuskarshi ba.
"Ban gane ba. Kina nufin Wanshi kika maka a kotu kuma ya Waukar miki lauya, yake ta jaddadamun inji tsoron Allah in yi iyakar yina a ?wato miki hakkinki Babangida ya sake ki?"
Tabbas mahaifinshi ne"
"Toh Malama Sabuwa ni zan wuce in ma akwai wata tambayar zan bugo miki waya saimu tattauna. Ki kuma zauna da shirin fuskantar Shari'a ki sani kuma saSanin hankalice, tamkar macece da ciki, kinga sanin abinda zata haifa sai Allah. Na barku Lafiya"
Ya mi?e da sauri ya tafi.
Nayi shiru a zaune a dakalin Labbai tace.
"Wai kinsan tunda kuka fara magana da lauyannan ?annen ?ar Shuwa da mahaifiyarsu suke ta faman sunturi kuwa?"
Baki na taSe nace.
Ina ganinsu sunata wucewa kamar ?awayen Amarya.
Naga Malam Habu ya wuce"
"Malam ko buzuzu? Dallah tashi mu tafi ni.
Aurene ni dashi ya ?are"
Ashe yana tawowa duk abinda Labbai tace a kunnenshi.
Yana ?arasowa buWar bakinshi sai cewa yayi.
"Aure kam ya ?are, domin ni ba lusari bane da zan zuba idanu ina kallonki da aurena kina bin maza kamar yadda aka kama Sabuwa ba, yanzu ma ba gashi na kama ku ba.
Na sake ki saki guda, dama dai kwaWayine irin namu na maza shi yasa na auro karuwa"
Naji zafin maganganun Malam Habu sosai. Musamman karuwa daya cema Labbai.
Kafin in ankara Labbai ta cukumeshi tana ihu tana kwaroroto.
Wallahi kafin ?iftawa da bismillah sai ga jama'a sun taru.
Malam Habu ya dinga cauWama Labbai carbi yana jefo manya manyan maganganu marasa daWin saurare a kanmu.
Sama da ?asa Allah baisa na iya cewa komai ba.
Cikin munafukan da suka taru na kutsa na fincike Labbai a wuyan Malam Habu na jata kiyyy har cikin gida.
A lokacin ?urar cikin gidan ta lafa, Rakiya ma wanki take yi, Hauwa na kwalima.
"Wai menene dama daku ake???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? hayaniya ne Labbai.
Ni naji matan Malam Habu sunata Wuma zagi ta katanga.
Kafinma mu bada amsa muka jiyo zagin.
Turmi Labbai ta hau sukaita zagi in zaga da iyalan gidan Malam Habu ta karanga
Da ?yar na fige Labbai muka shige Waki.
Yaran gidan sukaita jifa daga gidansu zuwa namu.
Dawowar Gaza yasa komai ya lalace. Yana shigowa aka jefo ?aton dutse ya sauka a ?afar Rakiya.
A guje ya shiga gidan Malam Habu, Labbai ta bishi da gudu da wu?a a ?ugunta.
Hmmm abu dai babu arziki duk matan gidan shigewa Waki sukai suka kulle. Gaza ya saka ragunan Malam Habu gabas ya dinga yankasu.
"?an abu ta kazan uba. Ku shiga ku Webo kayanku mu tafi. Yasin duk matar da muka haWu a hanya sai dai ta canja hanya in ba haka ba saina farWeta."
Haka mukaita jide kayan Labbai muna ficewa dashi.
A guje Rakiya ta shigo.
"Gaza matsa dale katanga ka wuce ga Malam Habu da kwalawa. Take katanga maza"
Ragunannan daya yanka ya suri biyu ya yaSa a kafaWa suna yararin jini ya haye turmi ya dire bayan lungu.
Yana direwa kwalawan na shigowa a guje.
Jin muryoyin ?an sanda yasa iyalan Malam Habu fitowa.
"Kaga ta'asar da yayi mun ko?
YallaSai ku wuce da waWannan matan dukkansu, kuma wallahi sai an biyani ragunana raguna kusan takwas a yanka mun su sabida rashin tarbiyya Gude a mayar mun da kayan Labbai ciki"
"A_a Malam ka rabu dasu kawai tunda dai mai rabawa ta raba.
Wallahi ina jiye mana bala'in da zai biyo baya.
Ni dai Malam ka dangana kawai. Tunda kai ka yayiSo mana dama yaran gidan farare. Meye bamu faWa maka ba?
Kar ka bari a tafi dasu, muna da yara mata kada Gaza ya turo yaranshi sui ma yaranmu fyaWe a banza da wofi"
Tana faWan haka sai jikin Malam Habu yayi sanyi.
Take yaja ?an sandannan waje, ya suka ?are sai Allah.
"Labbai maza kwashe kayanku ku tafi"
Cewar Gude da ciki ya Wuri ruwa. Rakiya tace.
"Ai ba sai kince ba. Wallahi kinyi ma kanki Alamnashara Gude da zaman unguwarnan ya gagareku.Yanzunma sai fa mun so rigimarnan zata lafa.
Labbai ku kwashe kayan mu wuce miji goma ba uba goma bane. Ku Wakko mana ?atuwar tinkiya in dai da Bismillah ya yanka"
Dukkanmu muka haWu muka kwashe kayannan Labbai kuwa saida ta kinkimi ?atuwar tinkiya ta fice tana ta zage zage unguwa ashe ta cika ta batse sosai da sosai.
Ohhh Allah rayuwarmu tana cikin garari. Shin haka rayuwarmu zatai ta tafiya babu sauyi ne?"
Muna shiga gidan muka tarar Adama tazo tana zaune da takadda akan kujerar tsugunno tana gani munata shigo da kaya babu wanda ta kula.
"Adama ke kuma fa wai?"
Cewar Uzairu zuchiyata daya jingine katifa.
"Hmmm kai dai muje daga ciki tukunna"
Ta bashi amsa tana shigewa.
Tare muka Wunguma muka shiga Wakin duk ?an matan basa gidan dakin kaca_kaca babu shara, kwanukan da suka ci abincinma duk yana baje a tsakar Wakin. Ga uban suturu a a ?asa.
"Adama wannan wai takaddar asibiti ce, ko kema dai sakin naki akayine duk kika wani yi laushi? Allah na tuba da irin wannan aure ba gara zawarci sau dubu ba? Jebakki fa fara sol wanke hannu ka taSa"
Rakiya ki dena Waga murya na jiyo muryar Layuza a tsakar gida "
?asa Rakiya tayi da muryar.
"Ai Qamriyya ce yau za'a kawo sadakinta da kayan Aure, wani ba?auyen zai kwasa."
Baki duk muka taSe.
"Ni ba wannan ba Rakiya sakina Baban yara yayi fa in faWa miki har saki biyu. To kinsan a baya saki Waya ya taSa yi mun.
Yau kwana goma cib da sakin da na saka rigimar sai dai in zauna inyi zaman ?a?ana wallahi yau dai a guje da bulala ya rakoni, kun ganni sai makwabta ne suka bani takalmi da mayafi.
Nazo na tarar anata rikici da mijin Labbai "
Ni dai take kaina ya hautsine hawan jinina ya tashi sabida damuwa.
"Hmmm ai Shikenan ke da Labbai duk auren naku dai ya tsinke. Ga dai filin tsakar Wakinnan du ya ishemu, ga wannan mitsiyaciyar itama Auren nata take so ta kaso. Duk ku dawo kuzo mu zauna ciwon zuchiya yai ajalina ga ba?in cikin Maigogul ga naku."
Tana faWan haka ta sau kukan da nayi imani sabida aurenane da zan kashe ba dan mutuwar auren Labbai da Adama ba.
"Rakiya ki dena kuka kada su Hauwa su jiyoki burinsu a kullum bai wuce su gammu a ?asa ba"
"Ke dallah su gammu a ?asan mana ai babu da abinda Hauwa ta isa goranta mun babu iriyar ?ar iskar da bata dashi a Wakinta.
Sama ne ya le?o Wakin Rakiya kina ciki, Adama Sabuwa kune a gidan?"
"Ahh Sama ai kai zamu tambaya kaine a gidan, wai Sama ina ka shige ne?"
Cewar Adama kenan.
Shigowa yayi da ?ar ledar kayanshi ya nemi waje ya zauna. Duk yabi ya lalace
"Ina can kasashen inyamurai neman kuWi Adama. In ka biye ta gidannan da rikicin gidan ina mai tabbatar miki likkafanin da inka mutu da tabarmar da za'a saka daga ?arshe nema za'ayi a rasa in dai gidannan ne.
Ya kuke ya yaran naku?"
Duk muka amsa mishi da lafiya, Rakiya kuwa tagumi tayi.
"Wai lafiya kuwa?"
Kafin a bashi amsa saiga Hauwa ta buWe labule.
"Wai yau muryar wa nake ji kamar Sama'ila dama kana duniyarnan. Yaushe da rabon mu saka a idanunmu?"
Kai ya Wan sosa.
"Wallahi Hauwa balaguro kawai nayi. Na shiga duniya neman kuWi"
HaSa ta ri?e tace.
"Kuma wacce sana'ar ka kama Sama?"
Harara Rakiya ta zabga mata harda jan tsaki.
"Bige_bige ne duk abinda na kama yi nake yi. Amman kamar dai lokacin kirsimeti ina zaga garuruwan inyamurai ina tallen balambalo" Sai da Hauwa tayi dariya kafin tace.
"Ai yafi maka zaman banzan.
Kaga ?aninka ma mijin Layuza ya kaishi shagonshi dake kasuwa yana taya shi aiki."
Sama yace"
"Wai ma'aru kike nufi shine aka saka a kasuwa. Yaron da ko Sera bai kaishi sata ba? Kai Hauwa nifa ina tsoron kada yaje ya kuntaka mishi sata azo ana raba hali"
Ai nan Hauwa ta shiga zage_zage haka ta saki labule.
Sama kuma ya suri ledar kayanshi yakai Wakinsu na langa_langa yayi ficewarshi. Yana wa?e_wa?e. Shi sabida tsabar shaye_shaye bama saka shi a lissafi dan ba kullum yake da hankali ba. Wataran ma

4 / 25