Idan Kaya Ya Gaji Book 2 Hausa Novels Compelet by Badiat.doc

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 25

39K to 42K   out of 73.4K words

bashi ikon ji.
Nannauyan ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya Wauki wayar sai dai harshanshi sai yaji sun sar?e ya kasa magana.
Zare wayar yayi a kunnenshi kawai ya tattare wannan kayan ya mayar ledarsu, ya haWa d takaddunshi jikinshi a mugun mace ya fita
Mrs Bukhari
Sai mun tara gobe

IDAN KAYA YA GAJI...
GAMMO MA YA GAJI
LITTAFI NA BIYU
SHAFI NA SHA ?AYA
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


(BANA JIN DA?IN YADDA MUTANE DA YAWA SUKE MUN DM SUNA TAMBAYATA SHIN DA GASKE NAKE YI LABARIN SABUWA YA FARU A GASKE. ALAL HAKI?A DUK SANDA NACI KARO DA WANNAN TAMBAYAR INA MATU?AR JIN BABU DA?I DOMIN HAKAN YANA NUFIN MAI TAMBAYAR YANA TANTAMAR ?ARYACE KAWAI NAKE YI. KO KUMA INA CEWA LABARIN GASKIYA NE DA WATA MANUFA.
KU SANI BABU RIBAR DA ZANCI DAN NAYI MUKU ?ARYA.
SHIN BAKU TA?A JIN UBANDA YAYI ?IYARSHI CIKI TA HAIHU BANE? AI LABARIN YAFI NA SU SABUWA MUNI TUNDA MAIGOGUL BAI TA?A JIN SHA'AWAR YARANSHI BA.
WALLAHI BILLAHI NASAN GIDAJE DA YAWA DA SUKA FI GIDANSU SABUWA KAZANTA.
SANNAN KU SANI DUK LITTATTAFAINA LABARAINE DA SUKA FARU A ZAHIRI KI AMINCE KO KADA KI AMINCE WANNAN YA DANGANTA DA YANAYIN YADDA KIKE ?AUKAN ABU.
AMMAN TABBAS LABARIN SABUWA LABARINE NA GASKE. NAGODE SOSAI DA SOYAYYA ALLAH YA BAR ?AUNA)

SABUWA TACE IN MI?A MATA SA?ONTA GA DUK ?AUKACIN MASOYANTA.

IYABO MA TACE TANA BIBIYAR WANNAN LABARIN KUMA TANA TAUSAYIN SABUWA SOSAI.
( IYABO MAI RAYA SUNNAH A GARKEN SHANU TSUNTSUN SOYAYYA BA. TA HAMMA BADA KANKI A SARE, AMINIYA A WAJEN UWANI TA BALBALIN, CINYAR SA MAGANIN MAI HA?AMA BA>?#?>?#?)





Yana fitowa ?an AcaSa ya soma bambamin faWa akan sai an ?ara mishi kuWi shi wallahi shi tallahi bazai yarda ba.
"Zan ?ara maka ko nawa kake so muje ka kaini kotun cikin gari"
Ya faWa cikin wata nutsuwar da shi kanshi baisan yana da'ita ba.
Yana zaune a AcaSa amman tunaninshi yana wajen Sabuwa da kayan dake ledar hannunshi.
"Khalid Allah dai ya tsine maka albarka. Dake kai tantirin Wan iskane hankalinka kwance kake mu'amala da matar wani, harda kawo mata tsarabar kayan karuwai. To mijinta ka siyo ma ta saka mishi, ko ko A_a ka siyo ne dan a saka maka ka kalla kaji daWi?"
Duk wannan m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aganganun a cikin zuchiyarshi yake yinshi. Kanshi ne ya sara mishi take wani jiri da zazzaSi ya sakko mishi. Babu shiri ya soma ambaton Allah
Amman zuchiyarshi sam ta?i nutsuwa, in bansa tunzurashi da zuchiyarshi take yi bata komai. Har hango sabuwa yake yi a Wakin hotel a gaban Khalid da wannan rigar baccin a jikinta.
"Malam anya kuwa kana da hankali ka duba nafi minti uku ina cewa mun iso amman babu um babu um_um."
Sai lokacin Babangida ya fahimci dashi fa ake Magana, Wago kan da yayi yaga lauyanshi da Kawu Manga a gaban AcaSar.
"Ashsha Babangida jikin naka ne ya kuma tashi ne, da ganin yanayinka kana cikin matsanancin ciwo."
"Kawu mai girma ma kuwa. Ku taya ni da adda'a kawai ita nafi bu?ata ba lallai bane in warke daga cutar da zuchiyata da tunanina suka kamu dashi ba"
"KuWina dubu biyu waye wai zai bani ne?"
Cewar ?an AcaSa da aka ?ureshi har zuwa bango.
Dubu biyu Kawu Manga ya ciro aka sallami mai acaSa ya wuce su kuma suka rankaya izuwa Chamba.
A ciki ya tadda Alhaji Abubakar Baban bola tare da lauyanshi da Wanshi, sai al?ali dake kujerarshi a zaune.
Bayan sun samu waje sun zauna al?ali yace.
"Babangida inaso inji daga bakinka shin da gaske kamfanin da kake ri?e dashi babu ko sisin kwabonka a ciki, naka juya kuWinne da yarjejeniyar raba riba?"
"Hakane mai shari'a babu jayayya ga duk abinda Alhaji Abubakar Baban bola ya faWa. Nayi mishi laifi ina neman afuwa a sassauta mun"
Anan dai aka ?ar?are magana da kissafe_lissafe a ta?aice da nera million goma kacal Babangida ya tsira shima a hakan ba ?aramin adalci akayi mishi ba. Shari'ar dake a chamba ce kuma akwai sanayya sannan Babu jayayya ko musu a take aka gama komai Babangida ya sanya hannu shi da lauyanshi, haka ma Alhaji Abubakar Baban bola ya sanya hannunshi shi da Wanshi da lauyanshi. Batun bama Babangida million goma kuma yace a i mishi alfarma zuwa wani lokacin zai bayar da haka aka rufe case Win kwata_kwata.
Suna fitowa sai ga kiran malama Babba ya shigo wayar Kawu Manga. ?agawarshi ke da wuya Malama Babba tace in suna tare da Babangida su tawo su sameta a gidan Wawo yanzunnan.
"To shikenan gamu nan. Amman lafiya naji muryarki haka a firgice?"
Malama Babba tace.
"Babangida hankalinshi bazai taSa kwanciya ba har sai yaga ba?in cikinshi yayi ajalina tukunna. Wallahi da zan iya ha?ura dashi kamar yadda Malam yayi dana huta"
Kawu Manga ya girgiza kai. Babangida Kuma ya sauke kanshi ?asa dan shi baisan kuma me ya kuma aikatawa ba.
"To ko Sumy ta kai Amir gidane danta fallasa asirina? A_a ai duk sharaWin data bani ban tsallake ko Waya ba bafa ita bace"
"Babangida muje gyatumarka na son ganinka yanzu. Barrister mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi "
Hannu Babangida yaba Barrister sukai musabaha kafin yabi Kawu Manga da wani irin sanyin jiki.
Yana bayan bespa Kawu Manga na tukasu tunaninshi kacokan yana wajen Sabuwa da tsarabar da take hannunshi har suka iso ?ofar gidan Wawo bai daina tunani ba.
"Sai ka shige mu je ai ko, sai wani sanyin jiki kake yi kamar gaske a haka kamar ba kaiba in ka kuntuka wata tsiyar sai mutum ga ri?e bakinshi mutumin banza."
Har suka shiga Kawu Manga faWa yake yi.
Matan Wawo suna tsakar gida suna aikace_aikacen mata na yau da kullum su Kawu Manga suka shigo.
Nan suka shiga rige_rigen gaishe da Kawu, yara da basa makaranta suka iso wajen Babansu a guje suka rirri?e mishi kafa
Murmushi Babangida ya dinga yi musu yana shafa musu kansu. Da ?yar iyayensu suka rabasu dashi, saida ya bada Wari biyu kuWin biskit, ya gaishe da matan yayan nashi kana ya shiga.
Da idanu yu suka bishi suna mamakin irin halayenshi a ido gashi dai mutum har mutum mai zubin kamala, hankali da tunani.
Da sallama suka shiga part Win da Malama Babba take ciki, ga wata yarinya tana shanya a igiyar dake Wan tsakar gidan da halama mai aiki ce Wawo ya Wakko.
Suna saka kai Babangida yayi tozali da Hamida da ?a?anta suna zaune dirshan a gaban Malama Babba "



SABUWA:.


Bus Winmu ta sauke mu a daidai bakin makarantar, haka nabi ayarin dalibai muka shiga cikin makarantar.
Mardiyya kaini ofishin shugaban makaranta"
Mardiyya ta shige gaba ina biye da'ita har ofishin.
Na shiga na tarar da wata uwa itama ta kawo ?orafi akan Walibai sun saka yaronta gaba da duka da tsangwama suna neman su burkita mishi tunaninshi.
"To Malama kiyi ha?uri sha'anin Walibai sai adda'a. Amman zamu sake saka idanu sosai akan shi Jamilun da mu'amalarshi da yara ?an uwanshi. Uhm kije gida kawai"
Mi?ewa tayi tare da cewa.
"Shikenan Malam nagode ina fatan ganin sauyi mu wuni lafiya."
Ta fita a hankali. Shugaban makaranta ya kalleni yace.
"Hajiya barka da zuwa menene ?orafinki, koko kin kawo yaro zai shiga makaranta ne?"
Yayi maganar da fara'a.
A_a ni mahaifiyar AWWa'u ce nazo ne naji ba'asin dukanshi da akayi irin wannan dukan sai kace ba uwa bace ta haifeshi ba"
Take ya gintse fuska, nima na Waure fuskata tamau.
"Uhm naga halama. Uhm Hajiya an kuwa baki labarin sata yayi aka dakeshi kuwa, sannan kuna da masaniyar sace_sacen da wannan yaron yake yi a wannan makarantar kuwa? In ba dan darajar kakansu ba ai da tuni mun koreshi dan gudun kada ya Sata ma yaran mutane tarbiyyarsu ta hanyar koyar dasu sata"
Yawu na haWiye muryata a kausashe, a dakushe a lokaci guda.
Malam dan yayi sata sai ai mishi irin dukan da akai mishi aka farfasa mishi jiki? Shin a matsayinka na uba kuma babban malami kai kana ganin irin wannan dukan hanyace ta horar da yaro ko hanyace ta sake fanWarar dashi. Ko tunaninka satarshi mu iyayenshi mu muka koyar dashi, ko kuwa mu muka Waurashi bisa gwadaben satar? Ka sani babu wata uwa da zata so Wanta ya kasance bana gari ba. A mafiya yawan lokuta duka ba mafita bane musamman ga yara ire_iren AWWa'u jawosu a jiki suka fi so da kuma nuna musu hanyar gaskiya tunda har gobe AWWa'u yaro ne ?arami kuma ina fatan Allah kar yasa ya girma da wannan halin. Kuma ku sani kuma da naku ?a?an suke a kimtse wallahi Allah ba dabararku bace."
Ina dasa aya na mi?e tare da zuge jakata na zaro nera dubu Waya na ajjiye akan teburinshi.
Ga kuWin da akace ya sata a mayar ma da yaron sannan a bashi ha?uri.
Kai kuma kune malamai ya dace ku taya mu tarbiyyar yarannan domin daku suka fi rayuwa a rana awa nawa mu iyayensu muke samu tare dasu, rabi da kwatan lokutansu naku ne. Ayi ha?uri kada a sake mishi duka irin wannan duk yadda zai lalace ha?i?a inason kayana."
Juyawa nayi na nufi ?ofa har na kusan ficewa naji shugaban makaranta yace.
"Hajiya!"
Juyiwa nayi na kalleshi. Jikinshi yayi laushi sosai, ni kuma zuchiyata tafasa kawai take yi.
"Ha?i?a na Wauki babban darasi a maganganunki na hikima. Na yaba da salon isar da sa?onki cikin ruwan sanyi kika dafa ni da ruwan jikina.
In sha ALLAH daga yau babu wani malami da zai sake dukan AWWa'u kan yayi sata. Koma me ya aikata zamu kira lambarki ko ta mahaifinshi dake jikin form mu sanar muku inma na zuwa ne sai ku zo.
Baya ga wannan halin na AWWa'u yaron bashi da matsalar komai. Gashi da ?wa?walwa, gashi da haza?a, kuma yarone mai tausayi, bugu da ?ari yana da son ?an uwanshi. Hajiya ai mana afuwa wallahi mun dakeshi ne ba dan mugunta ba, sai don gyaran tarbiyyar shi. Amman zuwanku yasa na fahimci ta inda mu kanmu muke da kuskure kuma zamu gyara"
Idanuna na lumshe kawai na gyaWa kaina tare da cewa.
Allah ya bamu ikon gyarawa.
Nayi maganarne haWe da sauke ajjiyar zuchiya irin na wanda ya samu sassauci a zuchiya.
Ban bi takan yaran ba na fice a makaranta. Ina tsallake ina jiran abun hawa sai naga mota ta tsaya a gabana. Gilashin motar aka zuge Khalid ne a cikin motar yana saye da fararen suit yayi kyau sosai. ?uri yayi mun da idanuwanshi, nima shi nake kallo ina jin wani abu a raina game dashi.
"Shiga mota in kai ki duk inda zaki je Sabuwa."
Da ka yi tafiyarka Khalid nagode sosai."
Murmushi yayi ya fito daga cikin motar ya iso gabana yana murmushi.
"Ai ban isa na barki anan wajen ba. Wai kinsan irin neman dana dinga miki ban sameki ba kuwa? Wallahi da kinsan irin halin dana shiga ta dalilin son sanin halin da kike ciki tun bayan rabuwarmu da kin tausaya mun. Ki daure muje in kai kii"
Jakata ya karSa ya buWe mun gaban mota na shiga, ya zagaya da hanzari ya shiga mazauninshi.
Idanuna a lumshe sanyin Ac na ratsani naji Khalid yace.
"Ga sigari ki sha ki rage nauyin zuchiya da ganin yanayinki kina cikin damuwar da tafi damuwar da kike cikinta a baya kafin in dawo cikin rayuwarki."
Sigarin na karSa na soma zu?a cikin salon ?warewa shi kuma ya ja mota ya seta ta a titi.
"Ina zaki je dama?"
Gidanmu zanje can zaka kaini"
Kai ya gyaWa yayi mun murmushi tare da cewa.
Menene abinda ya faru bayan rabuwarmu a wannan lokacin? Naso inji daga gareki nabi duk wata hanya amman ban sameki ba, wayarki bata shiga naje har layinku aka ce mun kun tashi dole haka na ha?ura. Kuma inata tunanin zaki neme ni ki sanar dani azzalumin mijinki ya sake ki nanma naji shiru"
Idanuna na lumshe, saida na zubar da haya?in dana zu?a tas kafin na bashi labarin abinda ya faru."
Labarin duk abinda ya faru na bashi tare da Waurawa da cewar.
Yanzu jira muke yi zaman kotu na biyu ya zagayo mu sake komawa kafinnan hannun nashi ya warke kamar yadda nauyan nashi ya bukata."
Murmushi Khalid yayi tare da sakin Wan wani ihu da yasani sakin baki da mamaki ina kallonshi.
Lafiya kake ihu?"
"Wannan labarin naki ai dole in yi ihu burina kice ya kusan cika na mallakarki halak malak ba tare da shamakin komai ba? Lallai zan saka himma a kan ginin da nake yi da na saka wasa amman yanzu dole in saka himma dan gidana da nake ciki bazai isheku ba."
Murmushi kawai nayi na girgiza kai tare da cije leSena kawai.
Akalar motar ya sauya zuwa wani titi daban.
Ina kuma zamu je, nifa ban shirya aikata komai ba asalima bazan sake aikata komai ba ko dan mutuncin yarana"
Kallona yayi da kyau ya nemi gefen hanya ya tsaya.
"Sabuwa wallahi sosai nake sonki ina mai tabbatar miki duk duniya babu Wanda zai soki rabin son da Khalid yake yi miki. Kada kiyi tunanin ko ina mu'amala da matan banza har yanzu kiji tsoro ko shakkar aurena. Ko Waya a halin yanzu bana mu'amala da ko wacce mace face ke, ke kuma kinfi kowa sanin rabin rayuwata ce ke, kada kiyi tunanin sabida jikinki nake sonki. Da gasken gaske sonki nake yi sosai."
Numfasawa yayi tare da ri?o hannayena biyu yana murzawa a hankali ni dai sama da kasa Allah bai bani ikon cewa dashi komai ba.
"Sabuwa nayi miki al?awarin zan baki farin ciki a aurenmu irin farin cikin da tuni kika yanke ?auna da samun shi. KHALID ne kaWai yasan mutuncinki."
?agowa nayi na dubeshi ha?i?a ga dai soyayya ?arara nakan iya karantata daga ?wayar idanun Khalid a zahirin gaskiya zuchiyata ko kusa ta?i gasgata Khalid da maganganunshi. Taya zai ga darajata bayan ni dashi muke ?etare katangar Babangida. In mu kai Aure bazai taSa samun nutsuwa da yarda dani ba wannan kam ya shuWe har gaba da abada in dai a wajen Khalid ne. Jibi irin zargi da ukubar da nake sha da Babangida yanzu haka akan zargi. Ina kuma ga na auri Khalid kai ina da sakel. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da cewa.
Allah yasa mu dace kai dai ka taya ni da adda'a bari dai auren nawa ya ?are tukunna. Amman inaso mu nesanta da juna sosai ni nayi maka al?awarin da zaran aurena ya mutu Khalid zan nemoka da kaina"
Na faWa tare da sauke kaina ?asa.
Acan ?asan zuchiyata ina son Khalid so mai tsanani fa ina dannewane domin aure da kuma darajar ?a?ana.
"Kina nufin ba zaki sanar dani inda kike ba, kuma ba zaki bani number wayarki ba ko me kike nufi. Sabuwa anya ba yaudarata kike son yi ba kuwa?"
Babu yaudara kasanni farin sani Khalid ni kaifi Waya ce. Da kaina zan nemo ka, ina son samun nutsuwar da zata bani damar mallakar kaina domin in samu ?arfin kashe wutar dake gabanane, mutuwar auren yafi komai wuya ka fahimceni dan ALLAH "
Hannuna ya saka tare da jingina bayanshi a kujerar da yake zaune ya lumshe idanunshi.
Gilashin motar na sauke na yar da sigarin dake hannuna na rufe gilashin, kafin na ba Khalid dukkan nutsuwata
Ha?uri na share fin minti biyar ina bashi kafin ya buWe idanunshi da sukai ja ya zuba mun su.
"Naji kuma na amince, ki ri?e amanar zuchiyar da ta daWe da yin sabo da ri?onki. Ki bani account number ki lokaci zuwa lokaci zan dinga tura miki kuWin da zaki dinga bu?atunki."
Dole na bashi account number na sannan ya harba motar zuwa titi, katafaren shagon siyayya ya shiga dani ya sai mun kayan ma?ulashe kafin ya sauke ni a bakin layinnu tare da sake jaddadamun girman al?awarin dana Waukarma kaina, da wannan mukai sallama da Khalid. Kai tsaye gidan da su Adama suka kama na nufa, Labbai na hango a bakin ?ofar Wakin nasu da ?aramin risho tana shirin kunnawa, ganina yasa ta washe bakinta.
"Ah Lolo kece da safe haka? Yanzu kuwa Maigogul ya fita daga gidannan baku haWu ba?"
Ina dariyar ya?e wanda yafi kuka ciwo nace.
Bamu haWu ba kuwa"
Shigewa ciki mu ka yi, Adama na kwance a tabarma sai shantaka bacci take yi.
Hiye ba shakka su Adama an samu waje bacci ma take yi har yanzu bata samu damar tashi ba. Da ace a gidanta ne ai da yanzu tana bakin murhu"
Dariya muka saka ni da Labbai. Dariyar ce tasa Adama ta buWe idanunta. Yamutse fuska tayi ta mi?e tana tsaki, cikin muryar bacci tace.
"Lolo yaushe kika zo?"
Kallon fuskarta nayi dama dama da kwalliya nace.
Naga fuskarki duk kwalliya ta dame"
Dariya tayi tace.
"Bari in wanko baki inzo ki sha labari ni dai nayi kamu ALLAH."
Bakina a sake har Adama ta fita. Labbai kuwa tana kwance a kasa tana dariyar mugunta dama halinta ne duk yadda akayi ba kamun arziki Adama tayi ba.
Sai da Labbai ta gama dariyarta harda birgima kana tace.
"Kafin tazo baki labarin bari in dafo mana taliyar yara, kinga muna ci muna hirar abun zaifi daWi."
Wata ?atuwar leda naga labbai ta buWe ta ciro indomi manya uku, da ?wai uku. Ni dai mamaki ne ya gama isata nama rasa tacewa.
Wayar Adama ce ta shiga ruri tana gefe na Wakko wayar nayi na duba naga an rubuta Alhaji Bilya. Kai na gyaWa kawai na ajjiye mata wayarta na ciro ice cream a ledar siyayyana dana Wakko babban roba dama dan mu sha dasu Labbai ne, Rakiya ma na dakko mata ?aramar roba da meat pie babba nasan tana son meat pie aikinta kenan ba da sallahun a tawo mata dashi. Adama ce ta shigo da sallama tana ganin kayan daWi ta shiga washe bakinta. 5 alive ta Wauka ta Salle ta sha_ta sha kafin ta sauke.
"Baki ji sanyin shi ba har maWigata wallahi kai Lolo Allah yasa a wannan karon mu shiga gidan da zamu huta."
Kafin in bata amsa Labbai ta shigo da faranti sha?e da indomi da daddaffen ?wai. Wayar Adama ce ta shiga ruri da sauri ta Wakko, da taga sunan sai naga ta washe bakinta. Labbai kuma nan ta shiga dariyar iskanci. Nima dai a wannan karon dariyar nake yi duk da bansan meke faruwa ba, amman kamar bazawari Adama tayi.
Tsahare ce ta shigo da sallamarta.
Ganin kayan ciye_ciye yasa ta hau washe baki.
"Na dawo a daidai ashe a daidai. Lolo ashe kinzo?"
Kaga manya manyan zawarawa ban jima da zuwa ba. Fita kika yi ne?"
"Wallahi a gidan ?awata na kwana ta haihu mijinta baya nan shine ma ya nemi alfarman inje in zauna da'ita. Yanzun ma kaya nazo zan Wiba zuwa bayan suna zan dawo"
Adama fa tana gefe

14 / 25