Idan Kaya Ya Gaji Book 2 Hausa Novels Compelet by Badiat.doc

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 25

57K to 60K   out of 73.4K words

iya kashema mace kuWi ba tare da ana ban gishiri in baka manda ba. To a gidanmu babu tausayi, babu duban ?an?anta komai mu muke yima kanmu da zaran yaro ya kai shekaru bakwai to kuma shikenan magana ta ?are nauyin kanshi ya ratayane a wuyanshi, inya fita ya nemo ruwanshi, in ma bai nemo ba cikinshi. Akan Khalid nake jin zan sallama kaina dan ya riga daya sace mun zuchiya harda kuma kwaWayin abun duniya gaskiya sabida kana gidanmu dole ka nemi kuWi.
Washegari sai bakwai na safe ni dai na samu na tashi nayi sallar asuba.
Rakiya na zaune tana kallon Rahama da take yayyaga kaji tana kasawa a tire.
A guje Rahama ta fice a Wakinmu taje bakin magudana tamkar zata amayar da hanjin cikinta tai ta she?a Amai.
Shikenan itama dai nasan ciki ta kwaso duk da ba wannan bane karo na farko ba.
"Mitsiyaciyar yarinyarnan yaushe yaushe aka zubar mata da ciki amman har ta kuma kwaso wani ciki ni Rakiya duk wuyar da tasha"
Tana gama faWin haka ta yin?ura ta mi?e tana tura cikinta gaba ta fice.
Baki na taSe batun yin ciki da zubar dashi a gidannan ba komai bane mun saba da ji tun bamu kai haka ba.
Bazan iya ?irga Adama da Layuza sau nawa suka yi ciki aka zubar ba. Uzairu zuchiyata ne yaci gaba da rarraba namannan, na mi?a mishi ledata ya kwashe da dariya.
"Su Lolo kuma me aka samo mana?"
Hararar wasa nayi mishi tare da cewa.
Wai me ka Waukeni ne my Heart?"
Salatin Maigogul muka jiyo a tsakar gida a guje na fice na bar su a ciki.
"Me zan gani wai duwawu ya mutu ya bar zani?" Cewar Maigogul
Yana tsaye ya Wau wanka tamkar wani hamshakin mai kuWin gaske, komai na jikinshi mai tsadar gaske ne ga gogul da kullum yake manne a idanunshi dan bama gaye hakkinshi. Bakinshi kullum yana taunar cingam tamkar tsohuwar karuwa"
"Me kuwa zaka gani? Ciki tayo mu kuma a haka zamu ?are kenan a sintirin zuwa kemis karSo maganin zubar da ciki. Ka kasa sauke nauyin da Allah ya Waura maka damu da yaran duk ka barma duniya mu"
Da tsawa yace
"Ke Rakiya yi mun shiru jarababbiyar mata wacce ta zamemun tsiya. Ina da yara farare tsula_tsula irin wannan zan dafasu ne in sha kome kike so? Ah ni shikenan talauci da buga bugar rayuwa ya dakushemun ?uruciyata da kyawuna sai su in dakushe musu? Da sannu ha?onmu zai cimma ruwa zasu auri hamsha?an masu dashi na ?asarnan. Ke waye yayi miki ciki nace dan ubanki Isuhu?"
Ya dubi Rahama yana zazzare idanu"
"Alhaji Audu ne yayi mun?"
"Kinsan gidanshi ince dai ko, ko wajen aikinshi inda dai zamu iya zuwa mu sameshi?"
Kai ta gyaWa halamar ta sani.
Tabb Rahama ta taro rikici wallahi na sani.


To mutanene mun shiga waiwayen rayuwar lolo ta baya da sannu zaku ji dukkan abinda ya shige muku duhu
Son so fisabilillah.

Ina da Wan tsokaci kaWan akan masu zagin lolo, da masu ganin rashin kyautuwar hukuncin data Wauka na guduwa.
Shin kunsan menene cutar damuwa wanda a turance ake kiranta Deepretio?
Zan faiyace muku cutar zaku jita.
Allah yasa mu dace son so
Mrs Bukhari ce

IDAN KAYA YA GAJI..
GAMMO MA YA GAJI
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA BIYU
SHAFI NA GOMA SHA SHIDA



"wanke fuskarki maza ke da Lolo ku same ni a waje cicib yana jirana a mota dama"
Yana gama faWin haka ya fice yana saSa malum malum Winshi ga ?amshi yana zubawa.
"Allah ya kyauta halin Maigogul sai shi. Duk shi yake goyon bayanku kuke duk abinda kuke so.
Lolo Wakko mata mayafi maza ku je ni wallahi sha'anin zube_zuben cikinnan ya fita a kaina"
Baki na taSe na shige ciki na Wakko mayafina dana Rahama, sai wayata. Na cika naman kaza a bakina kafin na fito.
A wata ba?ar jibgegiyar mota mai numfashi muka samu su Maigogul a ciki shine a mazaunin direba sai Wan daudun abokinshi da sana'arsu Waya ba'a iya rabasu ko da yaushe tare suke.
Gidan baya muka shiga Maigogul ya ja motar muka bar unguwar.
Wayata ce ta shiga ruri tunda naga ba?uwar lamba nasan tabbas Khalid ne,da sauri na Waga wayar tare da sanyaya muryata sosai.
"Hello"
Na faWa muryar ?asa_kasa.
Jin muryarshi yasa na sake faWaWa murmushina.
"Sabuwa tun jiya kika baiwa zuchiyata aiki sai Webewa da kashewa take yi. Ban taSa samun macen data warce zuchiyata a kallo Waya ba sai ke"
Idanuna na kaWa wanda hakan dabi'atace da kuma wannan salon nake jan hankalin maza gareni.
In kuwa hakanne ashe dani dakai duk kanwar ja ce. Ni ko baccin kirki banyi ba. Kuma zuchiyata cike take fal da zumunWin sake sanyaka a idanuna ko zata rage nauyin da tayi. A takaice ina fatan kana cikin ?oshin lafiya?"
Murmushi yayi tare da sake nanata sunana.
"Sabuwa kenan. Zan dai kasance cikin ?oshin lafiyane kaWai inna ganni tare dake. Wannan fararen idanun da in kikai fari kike tafiya da zuchiyata su kaWai idanuna suke son gani. Yaya za'ayi in ganki, zaki iya zuwa wannan hotel Win da muka haWu jiya ina kwance a Waki mai lamba sifili tamanin da biyu"
Sake far nayi da idanuna nace.
Ehh tom yanzu dai bana gida mun fita da Babanmu da yayata sai dai fitar bata daWewa bace ka bani lokaci zan zo in sameka."
Ajjiyar zuchiya naji ya sauke take na lumshe idanuna a zahirin gaskiya nima a matse nake in ?one dan dama tuni a tafashe nake, na fahimci Khalid lamarinshi ba mai sau?i bane shima.
"Zan tanadi ruwan zafi, harma da farfesu da shayi mai zafi duka. Ina jiranki zan bar miki ?ofar a buWe da kinzo ki shigo kawai"
Da wannan muka yi sallama na sauke wayata.
Maigogul ne naga yana murmushi yana jijjiga kanshi. Cicib kuma sai waye wayenshi yake yi. Rahama kuma tayi lamo a kujera sai nuna ma Maigogul hanya take yi.
Ji nake da ace nasan Khalid zai mun tayin zuwa inda yake da bazan taSa biyo su Maigogul ba.
"Ga gidannan Maigogul"
Hannunta ya juyo ya kalla ?aton gidan samane mai get. Dariya yayi yace.
"Hmm Lolo shiga kice ana sallama da Alhaji Audu maza. Ke kuma ki fito mu jingina a jikin mota mu jirasu"
?alle murfin motar nayi na isa ?ofar gidan da mamaki ina tura ?ofar naga ta buWe babu sakata.
Gidan ?atone na gasken_gaske sosai ga motoci biyu a wajen da aka tanada na musamman domin su babban falon gidan na nufa. ?ofar a rufe take saida naita bugawa sai ga wata da gani mai aiki ce.
"Lafiya wa kike nema?"
Saida na harareta nace.
Lafiyarce ta kawo haka. Matar gidan kuma fa tana ciki ne?"
"Tana ciki wa zance mata?"
Ba kowa zaki ce mata ba, kice dai tayi ba?i ne tare muke da mahaifina"
Jin na ambaci haka yasa ta saki fuska tare da shigewa ciki.
Ba'a jima ba Hajiyar ta iso ga kyau ga iya wanka iyakar ganin wanda ya samu rabo.
"Baiwar Allah daga ina?"
Daga Zai. Alhaji Audu Mahaifina yazo nema yana waje"
Nan take ta haWe girar sama data ?asa, sai cewa tayi.
"Hanne! Hanne!!"
Ta kira ?ar aikin nata, da sauri ta fito.
"Je ki le?a waje ko zaki ga mahaifin wannan yarinyar kizo ki faWa mun. Ba karen hauka bane ya cijeni ba da zuke?iyar budurwa zata zo neman mijina in kuma haWasu dashi ba"
Hanne ta wuce aiken da uwargijiyarta tayi mata, ni da'ita muka shiga kallon juna ita nata na karantar yanayinane. Ni kuma nawa na tunanin inda maza zasu ajjiye kwaWayi nake yi. Duk yadda muke da kyau matar Alhaji Audu ta fimu kyau haske kaWai zamu nuna mata. Ni da na Wauka in namiji ya auri mace kyakkyawa ire_irenmu wanke hannu ka taSa shikenan bu?atarshi ta biya? Ashe bayan tiya akwai wata cacar fa kenan. Hmm matan gida akwai gagarumin aiki wurjanjan a gabanku. Dawowar Hanne ne yasa Hajiya ta Wauke idanta a kaina.
"Hajiya da gaske ne. Mahaifinta yana waje yana jiranta"
Ajjiyar zuchiya ta sauke, kana tayi ciki da sauri. Ba'afi mintuna uku ba sai ga goga naku ya fito cike da kamala da haiba a ido ciki fal fasi?anci.
Sai kallona yake yi nasan dai bazai wuci kamannina da Rahama yake kallo ba.
Saida muka fita yaga Rahama da su Maigogul sai yayi turus, tare da saurin rufo get Win gidanshi.
"Rahama lafiya, su waWannan Win waye su daa zaku zo mun har gida kusa ai kirana?"
?asa_?asa yake magana tare da waige_waige yaga ko jama'a zasu zo wucewa su gammu.
"Ni ne mahaifin Rahama nazo ne muyi magana akan Wanka dake cikin Rahama tabbataccen mara mutunci ?aton banza harma da hofi. A haka dai kamar na Allah"
Da sauri ya iso kusa da Maigogul.
"Baba dan ALLAH kaimun rai inada manyan yara mutuncinane zai zube in Maganar ta fito. Wallahi bansan tana da ciki ba."
Maigogul yace.
"To yaya kake so ayo kenan Dattijon biri? Dan wallahi ni ba ?aramin aikina bane yanzu in haWo kan jama'ar layinnan kab Winsu in labarta musu abinda ake ciki ba. Muyi tunSele a wajennan mu bafa komai bane. Ya zaka keSe da yarinya kace baka san haka zata iya faruwa ba sabida iskanci. Kaji mun Wan abu ta kazan..
"In babu damuwa mu haWu a ges house Wina mu tattauna a tsanake muga yadda zamu bulloma lamarin ayi ha?uri Baba a rufa asiri duka. Bani account number Winka in baku na mai a dai yi ha?uri a rufa mun asiri. Akan rufin asirina zan iya baku ko nawa ne. Rahama ki saka baki Baba yayi ha?uri. "
Baki Maigogul ya washe ni da Rahama sai kallon kallo aka barmu dashi. Cicib yace.
"To inane ges house Win naka yake da yamma sai mu zo ayo magana ayita ta ?are kai waye bazawara da jaka?"
Bai bashi amsaba dan yana kwashe account number Maigogul a wayarshi shi kuma yana karanto mishi sai da ya gama jerasu ya danna iyakar sifilin da yasan dole ya sanyaya ran Maigogul kana yace.
"Ita Rahama zatai muku jagora" Sai da cicib ya daki tsakiyan jallabiyar jikinshi da hannunshi kana yace
"Acan kuke haWuwa kenan? To ai shikenan"
Ya ?arashe yana fari gami da gyara kallabin dake kanshi.
"Alhaji kuWi sun shigo duk yadda kace haka za'ayi da Rahama dani duk abinda kace muyi shi zamu yi."
Murmushin mugunta Alhaji Yayi ya share zufar da ada ta tsattsafo mishi ya dubi Maigogul yace.
"Shikenan da yamma misalin ?arfe biyar ina jiranku"
Da wannan mukayi sallama muka shiga mota, shi kuma ya koma ciki.
Ni ina Allah _Allah muje gida in je wajen ?ar Shuwa. Rahama kuma sai mita take yima Maigogul shi kuma da Cicib sai zageta ta uwa ta uba suke yi."
A ?ofar gida Maigogul ya sauke mu bai ko shiga gidanba yace muje shi sai ya dawo.
"Maigogul kuWin da aka bayar baka bani ko sisiba..."
Ai kafin Rahama ta ?arashe magana ya yi mata da?uwa.
"Kinci gidanku Rahama. Ai kinsan koma yayane dole zan yafuta muku wani abun ke da Rakiya ko? To amman ki bari da yamma zan zo in Waukeki in muka je muka dawo sai azo ayi kasafin kuWin baki Waya. Wannan karon dai kin samu mai mai?o ba irin wancan fa?irin yaron talakan banza ba. Ni kam saina dawo"
Baki na taSe nayi wucewata gidansu ?ar Shuwa na barsu nan.
Mama tana tsakar gida tana wanke_wanke ?ar Shuwa kuma tana zaune sai shafa hoda take yi, ?anwarta kuma tana duba girki a murhu.
Mama sannu da gida"
Dariya tayi tace.
"Iyayen yawo kenan. Ai tunda naga Shuwa tana shafa hoda nasan yau dai sai an ganku bakwa gajiya ku kam"
Dariya kawai nayi naje kusa da Aminiya na zauna.
Aminiya albishirinki Khalid fa yana Hotel yana jirana ke yau ina cikin murna"
Hannu ta mi?o mun muka kashe.
"Kinga kwalliyarnan da nake rangaWawa? Fita zamu yi da Sagiru nima wai zai kaini in siya kayan da zan sa gobe na birthday. Naje gidanku sau uku baki dawo ba. Naje na tarar Amina babu lafiya"
Baki na keSe nace.
Bar bani labarin ciwo. Muddin suna kwaso cikin shege ai ba zasu yi rabo da ciwo ba.
?awata kice kema kin gama birkita Sagir Win naki?"
Dariya muka saka.
"Ke kinga yadda yake marairaice mun a waya kuwa? Kun sanni babu dama kuma damace a garemu zagewa nayi na dinga buWe bandir bandir na kalaman soyayya ina shiryasu a zuchiyarshi. Ke dai me kike so ni in Wakko miki a wajen shopping Win""
Yauwa turare nake so mai kyau ki Wakko mun. Bani da turare ragowar Humrar da kika bani ita zan shafe a jikina tas. Bari in tashi ke gara ke kinyi wanka ma."
Saida na mi?e tsaye nace da'ita.
To ni me kike so in kawo miki in mun fita?"
Mi?ewa tayi tsaye.
"Muje gidan naku kayanki zan saka wannan lace Win dai"
Rankayawa muka yi zamu fita.
"Shuwa baki bamu kuWin yaji da man ba"
Hannu ta cusa a rigar Mama ta mika ma Mama Wari biyar muka fice.
Gaza muka tarar a tsakar gidan yana wankin kayan sawarshi ga MP a gefenshi yana jin wakar ?an tauri. Rakiya kuma tana bakin ?ofa an kawo mata wasu labulaye tana gani.
Ga Hauwa a bakin murhu ta gangama tukunyar ruwan zafi Amina kuma tana kwance magashiyan a kan tabarma kusa da Wakinsu
Babu wanda muka kula ?ar Shuwa ta shige Wakinmu ni kuma na kandami ruwa a bokiti na Wauki sosona da sabuluna a kan tagar Wakinmu nayi banWakinmu da sauri.
Ban jima ba na fito wanka
Gaga gaga nayi brush shi wannan har yafi wankan nawa daWewa.
Na shiga Waki na tadda ?ar Shuwa ta saka kayana tana waya. A gaggauce na shafa mai ina ?o?arin saka siket na atampa Yar Shuwa ta sauke wayarta a kunnenta
"Ke ni kam na wuce yana bakin layinnan. Duk yadda ake ciki zamu yi waya"
A guje ta fice.
Rahama ta hararemu harda tsaki, ni dai ban bi ta kanta ba saida nasa kayana tsab na zauna zaman kwalliya, shima Wauri zama na musamman nayi mishi ga kitsona na ?ari har gadon bayana nayi kyau sosai jikin atampat kalan sararin samaniyane ( sky blue) da kuma ba?in bulu ( blue Black) na samu Wankunnena da sar?a ba?a?e na saka, ina dai da gyale ba?in Blue takalmine dai sai Halima ce take dashi. Gaban akwatin Maigogul naje na saci turare na feshe jikina dashi. Ina kan fesawa ne wayata tayi ruri.
"Ke Lolo ana kiranki kiyi hanzari"
Cewar Rahama dake kwance. Da sauri na iso inda wayar take Khalid ne yake kirana ba shiri na Wauki wayar tare da karawa a kunnena.
"Baby gani a ?ofar layinku maza ki fito ni na gaji da jiranki a Wakin hotel ne shine na biyo ki"
Kash dan ALLAH ka Wan shigo ciki Zaka ga wani gida mai jan buhu ka tsaya daidai ?ofar gidan zan fito"
Murmushi yayi wanda saida naji wani abun ya tsikaramun.
"Girmanki ai ya wuce haka. Bama sai kin haWani da Allah ba. Tuni harna shigo layinma ki tsaya a tsanake kiyi mun kwalliyar da tabbas zaki ?arasa ruguza kuzarina. Inason kwalliya inason mace mai gashi"
Farfar nayi da idanuna kawai nace.
"Shikenan sai na fito"
Ina faWin haka na ajjiye wayar.
Rahama dan ALLAH nayi kyau. Ko kina ganin a cikin kayana akwai wanda suka fi wannan kyau in saka? Sabon saurayi nayi mai mota yazo ya Waukeni zamu fita."
"Kinyi kyau. Amman da zaki saka wannan doguwar rigar taki ta yadinnan cottin zaifi wannan yi miki kyau kinsan jan kala yana Waukar farin mutum. Shi yasa ni kaya in babu ja a jiki bana sawa.
Rakiya ce ta shigo.
"Ahh tabarakallah Allah nagode maka daga Bani kyautar yara tsala_tsala haka. Lolo sai ina kuma? Baki ga yadda kikai kyau ba?"
Ina kan zakulo material Win da Rahama tace nace.
Wallahi dama zanje siyayya da saurayinane Rakiya. Yauwa Rakiya wannan doguwar rigar tawa ta yadi ko kinsan ina take jannan?"
"Ai kamar ?ar Shuwa rannan ta aiko ?anwarta na bata bata dawo dashi ba. Ai kayan jikinki ma yayi. Ba atampar ankon bikin da kukayi bane sati biyu da suka wuce ba? Kar ki canja jeki a haka farar mace ai bata bukatar wani kwalliya mai yawa. Matso in gyara miki Waurin"
Matsowa nayi ta gyara mun tai ta yi mun adda'ar tsari.
"A shigo mana da kayan daWi. Inta kama ma sai kice bari ki Wauki katan na taliya ko buhun shinkafa in shagon siyayya kuka je. Kinga ma daWe muna dafawa."
Tana gama faWin haka na suri takalmin Halima uwar masifa nasa na fuce.
"Ni Rahama baki faWa mun yadda kuka yi da uban naki ba. Ina ma wai kuka je ne?"
Daga haka ban kuma jinta ba.
Tun daga zauren gidanmu muka haWa idanu da Khalid yana sanye cikin yadin boyel na maza fari sol ga wata jar dara a kanshi wacce ta ?arama kyanshi kyau. Wani irin kallo da Khalid yayi mun ha?i?a ya ?ara ninka mun sonshi a zuchiyata sosai.
Murfin motar na Salle na shiga.
?amshi da sanyi suka ratsani. Sama yayi da gilashin motar ya nutsu yanata kallona sama da ?asa. ?ur idanunshi suka tsaya a wushiryar dake ?irjina. Ya Wago ya karema tsakiyar idanuna kallo.
"Sabuwa wallahi tunda nake ban taSa haWuwa da macen da ta warce zuchiyata lokaci guda ba sai a kanki. Ina da ?an mata manya waWanda suka fiki shekaru, amman ke a rana Waya kika sukurkutamun zuchiyata. Ke kinga yanda kika yi wani irin mugun kyau kuwa? Wato farar mace duniya ce"
Murmushi nayi tare da fari da fararen idanuna masu kama da madara.
Sake lumewa yayi a kujera ya sake shiga wani irin yanayi. Ina iya karantar soyayyata a idanun Khalid da ma gangar jikinshi."
?aran wayatace ta katse mun zaren waiwayena.

Sabuwa:.

Idanuna na lumshe da suke mun wani irin yaji da raWaWi.
Wayar ma ni bansan inda take ba, kaina wani irin mugun saramun yake yi.
Mi?ewa nayi na mayar da rigata mayafina a hannu, na suri jakata.
Narantse da Allah a wannan lokacin bansan a wanne hali nake ba. Abun mamaki kayan mayen da nasha sun?i su rage mun damuwa yadda ya kamata. Harna sauka na wuce dogon falo bansan ina zani ba. Sabida bana cikin hayyacina. Jina nake bani da maraba da matacciya wallahi. Ko ma?iyina bazan mishi fatan ya shiga irin halin dana shiga ba. Kuma bana mishi fatan ya kamu da ciwon damuwa.
Duk masu ganin rashin kyautawata baron gidan Babangida ni nayi musu Uziri tunda sun kasa gane ba'a cikin hayyacina nake ba. Harma wasu suka kirani da jaka akan Babangida.
Sai tsintsar kaina nayi a ckin club Win dake ?asan hotel Win.
Jirine ya Webeni na zauna a wata doguwar kujera daSas.
Dariya kaWai naji inayi irinta zararru sai kawai na jingina bayana a jikin wannan kujerar, bana

20 / 25