A dalilin kane Complete Book By Jamila Samaila Yusuf

Author :  Jamila Samaila Yusuf Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 16

30K to 33K   out of 46.3K words

ita tare da hudu da takalma baqaqe sae fatan qamshi yake,yyi kyau sosae.

Kallon yanayinta kawae yyi yasan tana cikin fargabar haduwa da shi.

Bakinta na rawa tagaishe da shi.


Yasamu wuri yazauna sannan ya'ansa tare da yimata nuni da kujerar da ke kusa da shi tare da umarnin ta zauna.

Islam tazauna tana mai cigaba da addu'a.

Kallon daya yyi mata yace"me kikayima kuka?"

Gabanta yyi mummunan faduwa cikin zuciyarta tace ashe haryanzu kananan da halinka na bin qoqwanto,afili tace"bbu komae idonane kemin ciwo"

Yyi murmushi yace"hmm yaushe kika fara qarya Islam?"


Tasan halinshi sarai shiyasa nayi niyyar fadin gsky,Aunty hanan ce tashiga tana dauke da Sultan.

Tazauna kusa da mijinta tanason gano abinda ake ciki,Islam takawo hannu zata anshi Sultan,yaya Rafeeq yyi mata tsawa yace"badake nake magana bane?"

Tini hawaye sunci gaba gaba daga cikin idanuwanta.

Aunty hanan tace"haba yaya Rafeeq wannan ai saika ida tsoratar da ita wlhy,kasan Islam da tsoro wlhy duk abinda tasan xa'ayi mata fada batayinshi"

Yaya Rafeeq yace"dake nake magana ne?"

Aunty hanan tahusata ranta ya6aci sbd taga take taken mutumin nan yanason disgreace dinta agaban kowa.


Aunty hanan tace"bakayi magana da ita amma ai tinda tanuna taji tsoro saeka rabu da ita hakanan,shiyasa basason zuwa gidannan sbd takura wlhy"

Fuuu tatashi tafita tare da Sultan.

Yaya Rafeeq yabita da kallon mamaki yaishe yarinyar nan tarainani ina fada tana fada.

Ranshi yaqara baci,yace"tashi kije kishirya i've been waiting for u since,don't waste my tym plz"


Islam tatashi tafita,yaci gaba da tinanin Hanan amma zaiyi lokacinta nan bada jimawaba.

Zuhra ce tashigo cikin shirinta na boyel lace red mai flower blank yyi kyau sosae,simple make-up tayi sbd tasan fita zasuji,tasakagyale black da shoes nd bag tayi kyau sosae,Zuhra kenan.


Bayan 15mins Islam tashigo tare da sallama,bayan sungaisa da Zuhra bbu 6ata lokaci suka tafi.

Cikin mota yaya Rafeeq yyima Islam nasiha sosae sbd yasan tanada hankali kuma tasan abinda takeyi.


Ahaka suka isa shoprite duk abinda suke buqata shi suka dauka,baiyi mgnar Hanan ba sbd yasan fushi tayi.

Haka suka da dawo gida hankalinsu kwance.


Bayan 2months hutu yaqare Islam da Iman suka koma skul Zuhra ma haka.


Wata ranar monday yaya Rafeeq tana Zaria,Zuhra tana skul,Hanan takira Asabe ta'aiketa shoprite tayi mata shopping din baby food tare da gargadin Asabe akan kada tabari kowa yasani,da yake Asabe ba wani isasshen boko tayiba sae Hanan tarubuta mata abinda takeso.

Hanan tasa driver yakaita.

Bbu 6ata lokaci abinki ga aikin kudi aka dawo mata da abinda tabuqata.

Hanan tabuda wardrop tasa,watan Sultan ukku tafara bashi madara hankalince batako bashi nono baifi tabashi sau daya ba.


Hanan kenan sarkin kafiya,gashi dama bawani jituwa take sosae da mijin nata ba yau shiri gobe fada idan kuma yashareta abin duniya yadameta taje tana bashi haquri har Zuhra tagane mata saedae bbu ruwanta da lamarinta.


Bayan Zuhra tadawo daga skul tayi wanka tashirya ranar itace take da aiki,zaune take porlour din yaya Rafeeq tana kallo,Aunty hanan ce tashigo da Sultan cikin keken baby.


Bbu ko sallam tashigo ganin yaya Rafeeq baya porlour.


Zuhra tana ganinsu tayi murmushi tana ga Sultan ga Sultan.


Fuska ayatsine Hanan tajuyo tana kallonta cikin rainin wayau tace"dalla tufemin baki ubanwa yafada maki sunanshi Sultan munafuka?"

Wato ke munafuka ance ansa sunan mai dattin hula shine kikejin ddi to sunan mahaifina nasakama baby na amma zaki iya kiranshi da Areef idan kinga dama"tayi tsoki tafita tare da jan keken baby.

Abin duniya yadamu Zuhra shin tarasa me zatayi kuka da ihu?.

Batasan lokacin da taji hawaye suna zuba afuskarta ba,dan kada yaya Rafeeq yasan halinda take ciki tatashi tanufi part dinta.


Saidae aikin gama yagama yaya Rafeeq yagama jin komae sbd yafito wanka yana shiryawa.


Part Hanan yanufa da niyyar yyi mata rashin mutunci bude qofar bedroom dinta keda wuya yyi ido hudu da Hanan tanaba Sultan madara a feeder................






*Miss j🙋😘*
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*




*200-205*



*K*allon tuhuma yake mata cike da 6acin rae,fuskarshi bbu annuri kamar bai ta6a yin murmushi ba.

Tini hankalin Hanan yatashi tsoro da fargaba suka bayyana afuskarta,hakika tanajin shakkar yaya Rafeeq especially yanzu daya kamata tana aikata laifi,wanda yamaida babban laifi agurinsa.


Hmm,Hanan kenan,amma irin qarfin zuciya nata sai tanuna kamar bbu abinda yake faruwa.


Murmushi tayi sannan ta'ajiye feeder tare da kwantar da Sultan bisa gado,tasowa tayi tana tafiya mai janhankali ta'isa har inda yake tsaye.

Hanan tace"lfy kayi tsaye anan yaya Rafeeq?,kazo muzauna mana kaga Sultan sae kallonka yake yaga daddy dinsa"


Haushi yaqara kamashi waishi Hanan zata rainama hankali,tana neman mayar da shi shashasha kamar yadda yadauketa?.


Hanan tace"munje part dinka bakanan ni da Sultan,yanzu kadawo ne?"


Yaya Rafeeq yace"me kikeba Sultan?"tambayar da jehomata kenan.


Hanan tace"madara ne"


Yace"wa yabaki izinin ba yarona madara?"


Hanan tace"kaga yaya Rafeeq,kafa dameni da tambaya,daga naba yarona madara kamar nabashi poison"


Baisan lokacin daya sharara mata mari ba yace"ni kike fadima wannan maganar cike da rashin sanin abinda zaifito daga bakinki?"


Ji tayi wutar nepa dinta yadauke,numfashinta yadauke na'yan dakiku tare da ganin walqiya ta wuccin gadi,hannunta tasa tadafe kuncinta tana mai zubar da hawaye.

Tace"ni kamara Dr. Rafeeq?"


Yace"ammare ki wawiya dake,sai insaka doka kikarya min ina matsayin mai gidannan"


Hanan ranta ya6aci tace"dokokin Allah nawa aka karya bare kuma taka?"


Ranyi yyi mummunan 6aci yace"kije gida nasake ki saki daya,kuma inaso kisani idan yarona yasamu matsala akan madarar da kika bashi wlhy sai nayi shari'a dake jahila"

Hanan cikin mamaki tace"kasake ni kace?"

Yace"bana buqatar sakeyin wani magana mai tsawo dan haka kita kibarmin gidana"


Hanan tace"zantafi amma kasani bazan tafi da yaronka ba sbd badashi nazoba"


Yace"idan kinga dama kina iya barinshi gidan mahaifinsa sbd mahaifinsa baice bazai iya kula da yaronshi ba"yana gama fadin haka yafita yabar mata part dinta.



Tinda yafita take kuka ahaka tasa wasu abubuwan da zata buqata cikin wata travelling bag medium batabi takan Sultan ba tadauki key din motarta wanda daddy akawo mata tare da travelling bag dinta tafita.


Driving take nafitar hankali ahaka tafita gate din gidan,mai gadi da masu aikin gidan sai faman kallonta suke hankalinsu tashe.


Akan titi ma Allah dae yatsare ta ta'isa gida lfy.


Tinda mai gadi yabude mata gate tashiga take kuka ko parking din motar batayi ba hakanan tafito tashiga cikin gidan.


Bbu kowa a porlour sae plasma daketa fatan aiki ita daya,batayi tinanin Mummy tana gida ba dan haka takwanta bisa doguwar kujera taci gaba da kuka dataga bayi tanufi room dinta wannan take zaune lokacin tana gida.


Cikin room dintama kuka take wiwi bbu kama hannun yaro.


Larai ce mai aiki daga zuwan Hanan da halin da take ciki tanufi room din Mummy domin tasanar da ita.

Zaune take gaban Laptop dinta tana faman dubawa,knocking din da tayi anayi mata shine yadakatar da ita,tare da bada umarnin shigowa,Larai ce tashigo tare da sallama,bayan Mummy ta'ansa cikin sakin fuska kamar yadda tasaba,sannan tasanar da ita zuwan Aunty hanan,cikin mamaki Mummy tanufi room din Hanan.


Ganin halin da 'yarta take ciki,hankalinta yatashi sosae,cikin rashin kuzari take tafiya harta'isa bakin gadon dan ko Hanan bataji tafiyarta ba saedae taji andafa mata kafada.


Hanan tana juyowa taga Mummy tarungumeta taci gaba da kuka mai cinrai,Mummy taqara rudewa tace"Hanan lfy?,me ke faruwa?"


Cikin dishashshiyar murya tace"Mummy nashiga ukku yaya Rafeeq baya sona,yasakeni Mummy"


Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un abinda yafito daga bakin Mummy kenan sannan tace"me yafaru ne Hanan?,wannan wane irin tashin hankaline?"


Hanan tace"Mummy mutuwa zanyi idan yaya Rafeeq baya sona"


Mummy tace"bazaki mutuba kuma mijinki yana sonki Hanan,yanzu ina Sultan?"


Hanan tace"yanacan gidanshi yarabani da yarona Mummy"



Mummy taci gaba da lallashinta amma Hanan kamar ana qara tinzirata,zuciyar Mummy cike da tinanin abinda yahadasu amma tasan halin Hanan sarai sannan tasan halin Rafeeq,tarasa ta'ina zata fara.



************


Yana komawa part dinshi bisa gado yafada zuciyarshi cike da tinanin abinda ya'aikata batare da shawarar iyayenshi ba,yanzu baisan abinda zai biyo bayaba dole ran iyayenshi ya6aci shikuma yana tsoron hakan.


Zuhra ce tashigo bedroom din tare da sallama sannan tazauna gefen gadon tana kallonshi.


Mamakine yakamata ganin irin yanayin da yake ciki wanda bata ta6a ganin hakan ba.

Ahankali tasan hannunta tafara shafar sajen fuskarshi cikin murya mai kama da rad'a take tambayarshi me ke damunshi?.


Yadaura hannunshi bisa nata dake kan fuskarshi yace"Zuhra nayi babban laifi wanda sae yanzu nake tinanin irin 6acin ran da su Abba zasu shiga idan suka sani"

Zuhra tace"subhanallah,mijina wane laifine ka'aikata haka?,me ke faruwa?,kuma dazan shigo naji kukan Sultan inaji Aunty hanan tana wanka dan Allah kaje kadaukomin shi"

Baitsaya 6ata lokaci ba yanufi part din Hanan kwance yake bisa gado shi daya yaci kukanshi har yagaji,wani tsanarta yaqaraji cikin zuciyarsa sbd kukan da yaron yyi ina laifin takaimashi yaronshi inyaso saeta tafi tabashi gida.

Haka yadawo dauke da Sultan ahannunsa,Zuhra ta'anshe shi taci gaba da lalla6arshi cikin sa'a bayan minti goma yyi bacci.


Zuhra takwantar da shi,tace"yayana kasanar da ni plz"

Yace"Zuhra nasaki Hanan"

Zuhra tayi salati hawaye suka fara qoqarin zubo mata.


Yace"nasaki Hanan batare da sanin iyayena ba"..........................





*Miss j*🙋😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*



*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
_{United we stand nd successed}_



*210-215*




*Z*uhra tace"ya salam,yaya Rafeeq kaje kadawo da ita kafin su sani,sai kaje kabasu haquri"


Yaya Rafeeq yace"Zuhra banajin zan iya zama da Hanan cikin wannan lokacin gsky"

Zuhra tace"haba yayana nafasan kai mai tausayine da haquri,dan Allah kaci gaba da haquri damu,itama zata gyara insha Allah"


Kukan Sultan ne yadakatar da ita akan maganar da take,da sauri tashiga bedroom din shi.


Tare da Sultan tashigo yanata faman kuka bbu ko tsagaitawa.


Zuhra taci gaba da lallashinsa amma kamar tana qara tinzirashi,yaya Rafeeq ya'anshe shi shima yashiga lallabarshi amma abanza.


Gaba dayansu hankalinsu yatashi,sun kasa ko zama sai faman zagaye porlour suke.


Sunkai 1hr ahaka amma bbu sauki,abin duniya yadamesu.


Yaya Rafeeq yace"bari kawae nakaishi gida wurin Mami daganan nafada masu abinda yafaru kuma nabasu haquri".


Zuhra tace"toh yayana Allah yatsare hanya"

Itace tarakashi har harabar gidan,yashiga mota,saeda taga fitarshi sannan tadawo cikin gida.


Part dinshi tashiga domin tagyara amma abin duniya yadameta jikinta bbu qwari.

************

Daqer tasamu tayi wanka dukda Mummy tanata faman lallabarta ko abincin kirki bataciba shima dan taga Mummy tatashi hankalinta shiyasa taci.


Zaune take porlour tayi tagumi abin duniya yadameta,Mummy ce tafito porlour tana ganin yanayin da Hanan take ciki jikinta yyi sanyi,ahankali taqaraso kusa da ita tazauna tare da dafata.


Da sauri tajuyo sakamokon jinda tayi andafata,tana ganin Mummy wasu sabbin hawaye suka zubo mata.


Mummy tasanyaya murya tace"Hanan,dan Allah kirage wannan damuwar"

Hanan taci gaba da kuka bata iya cewa komae ba.

Mummy tace"oh Hanan cigaba kikayi da kukan?"

Hanan tace"Mummy idan banyi kuka ba me zanyi arayuwana,yarabani da yarona,Mummy inason yaya Rafeeq amma shi bayasona bansan me yasaba"


Mummy tace"kiyi haquri Hanan,kuma maganar Sultan yanzu zanje innemi alfarmar abamushi,amma inaso kikwantar da hankalinki,kinji 'yata"

Hanan tace"toh Mummy"

Mummy tashiga cikin bedroom dinta tashirya cikin wani tsadadden lace milk tayi kyau sosae,sannan tadauki mayafinta tafito porlour bayan talalla6i Hanan sannan tayi mata sallama tafita.


Bisa hannun kujera takifa kanta taci gaba da kukanta daga qarshe takoma cikin bedroom dinta.


Da kanta take driving zuciyarta cike da tinani kala2,batasan yadda zata billoma Alhaji ba da wannan zancen gashi dama baya qasar.


Ahaka ta'isa gidan,bayan tayi parking din motarta aharabar gidan,cikin sallama tashiga main porlour dinsu.


Zuhra ce zaune aporlour tayi tagumi,bataji sallamar Mummy ba sbd tayi nisa cikin tinani.

Saida Mummy tayi sallama sau ukku sannan ta'ansa.


Zuhra taqaqaro murmushi tare da yimata sannu da zuwa.

Cikin fara'a Mummy ta'ansa,tare da samun wuri tazauna.

Zuhra tafita tadawo da ruwan roba da lemun kwali tare da glass cup guda biyu zubama Mummy.


Zuhra tagaishe da ita cikin girmamawa,Mummy ta'ansa sannan tadan kurbi ruwan dan kada Zuhra taga ko wani abu ne.


Mummy tace"Rafeeq yana nan ko?"

Zuhra tace"bayanan Mummy"

Mummy tace"toh shikenan bari intafi sae anjima"

Zuhra tace"toh Mummy kigaida gida"

Mummy tashiga mota da niyya tafiya gida amma tana jin komawa gida batare da Sultan ba irin halin da Hanan zata shiga.


Sae wani sashe na zuciyarta yace tatafi gidansu Rafeeq,haka kau akayi takarkata hancin motarta zuwa unguwarsu Haj. Maryam.


*************


Yaya Rafeeq yana shiga gidan zuciyarshi cike da fargaba,cikin sa'a lokacin Mami bata dade da dawowa daga wurin aiki ba.

Bayan yagaishe da Mami,Mami tana yima Sultan wasa tace"toh anfara yawo da shi ne shi daya"

Yaya Rafeeq yace"aah Mami"


Mami tadubeshi tace"ina Hanan din?"

Rafeeq yaduqar da kanshi qasa yace"Mami tana gidansu"


Mami tace"kamar ya tana gidansu Rafeeq?"


Rafeeq yace"Mami munsamu matsala da ita ne"

Mami tace"Rafeeq wane irin matsalane wanda agida bazaku iya shiryawaba har yakaiga tatafi gidansu?"

Rafeeq yace"Mami kugafarce ni amma nasaki Hanan"

Mami tace"subhanallah,Rafeeq kasan abinda kake fada kuwa?"


Abba ne yashigo da alama daga masallaci yake,suna ganinshi sukayi cirko2 suna kallonshi.

Bayan sunyi mashi sannu da zuwa,yazauna,yaya Rafeeq yagaishe da shi.


Abba ya'anshi Sultan yanayi mashi wasa yace"lfy Rafeeq naganka hankalinka tashe?"

Yaya Rafeeq bakinshi yana rawa yace"lfy la......"

Mami tace"inafa lfy Alhaji,wani tashin hankali da yaron nan yazomin da shi"

Abba yace"me ke faruwa ne?"


Mami tayi shiru,Abba yyima Rafeeq tsawa kai bakaji nane?"


Rafeeq yasadda kanshi qasa yace"Abba dan Allah kugafarce ni,nayi wani babban kuskure batare da shawarar ku ba,nasaki Hanan dazu"

Abba yyi salati yace"abinda kayimin kenan Rafeeq,amanar da aka bamuce kayima haka?"

Mummy ke tashigo porlour tare da sallama,fuskarta dauke da fara'a kamar yadda tasaba zuwa gida.

Mami da Abba suka ansa,ji yyi kamar yanutse cikin qasa sbd baisan yanajin kunyar Mummy ba sae yanzu,kasa dago kai yyi yakalleta.

Duk wanda yake kusa da Mummy yasan tanason Rafeeq sosae kamar yarta data haifa,kuma ko wurin aikinsu kowa yasani,shiyasa yakejin kunyarta sosae...............






*Miss j*🙋😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*


*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
_{United we stand nd success}_


*215-220*



Ganin Mummy yatasa hankalin Abba da Mami tashi bare uwa uba Rafeeq.

Mummy kenan,kamar yadda tasaba shigowa gidan cikin fara'a yauma haka tashigo,cikin rashin nuna damuwarta haka suka gaisa da su Abba..


Mami tace"Haj. Aysha bamuji ddin abinda yafaruba amma dan Allah ayi haquri,halin yaran yau sai addu'a"

Abba yarasa tacewa tinda suka gaisa da Mummy baiyi magana ba.

Mummy tace"haba Haj. Maryam ai nasan halin Rafeeq nasan kuma halin Hanan,nasan wani babban laifi zata aikata mashi,ai naji labarin irin zaman da suke,ko kadan Hanan bata da biyayya"


Rafeeq tinda yagaishe da Mummy kanshi aqasa yake har yanzu ko motsin kirki yakasa yi.


Mami tace"ae Haj. Aysha ba haka yakamata yyi ba ko kadan bai kyauta ba,shima baza'a rasa nashi laifin ba"


Mummy tace"ai qara yyi mata hankali may be tagyara halinta bataga yadda abokiyar zamanta take ba yarinya qarama amma da halin manya,amma dan Allah alfarmar da nake nema abamu Sultan mutafi da shi"


Abba yace"ni abin yadaure min kai,Rafeeq ne zaiyi irin wannan babban hukuncin batare da shawara na ba,ina jin kunyarku sosae Aysha,da wane ido zan dubi Alh. Lawal?"


Mummy tace"dan Allah ina roqon ku kada kutadama Rafeeq hankali sbd kunsan yanada heart attack already"


Mami tamiqama Mummy Sultan haryayi bacci,bata wani jima sosae ba tatashi tatafi gida.


Mummy nafita Abba yatashi ya shiga part dinshi,Mami tabi bayanshi sbd taga ranshi yabaci sosae,akabar Rafeeq zaune tsakiyar porlour yanata faman zubar da hawaye.

Zaune suke cikin wani madaidaicin porlour wanda yaji kayan more rayuwa da tsadaddun kujeru na zamani.


Mami tace"Alhaji, lalle Rafeeq ya aikata babban kuskure amma ayi haquri maganar haj Aysha abin dubawa ce yakamata mubinciki abinda yahadasu tare da yima Rafeeq uzuri sakamokon lalurar da yake da ita kada muxamo sanadiyyar tayar damashi da ciwon shi"


Abba yace"ya kikeso nayi da mahaifin yarinyar nan yadauki amanar yarsa yabamu,yarinyar na tana matuqar son yaronnan amma shi har yanzu bayasonta,narasa dalili why!!!?"

Mami tace"Rafeeq yanason Hanan tinda har tahaihu da shi Alhaji,babban matsalar shi,kasan yadda Rafeeq yatashi bayason raini,ita kuma Hanan batada ladabi batason zaman lfy,Islam tabani labarin komae kamar yadda sukaba Haj. Aysha"


Abba yakalli Mami yace"kinga Maryam ni yanxu inada abinyi plz"yatashi yabata wuri.


Bbu yadda Mami ta'iya dole tatashi tafita sbd tasan halin Abba man of policy ne baya sauya magana.


Jikinta bbu qwari tafito,tana fito taga Rafeeq cikin porlour kamar yadda tabarshi.

Hankalinta yaqara tashi,da sauri ta'isa wurinshi tana kallon cikin idanuwanshi sunqara ja kamar jini yakwanta..

Mami takama hannunshi suka shiga bedroom dinta da shi,Mami tazauna bakin gado yaya Rafeeq yazauna bisa carpet.


Mami tace"Rafeeq mahaifinka yyi fushi,nasara tayadda zan 6ullo mashi,nima kaina banji ddin abinda ka'aikata ba"

Rafeeq bakinshi na rawa yace"Mami nima nasan abinda na'aikata ba dai2 bane,amma rainane ya6aci kuyafemin dan Allah"

Mami tace"Rafeeq nariga nayafe maka amma kada kasake aikata irin wannan bbu kyau"


Rafeeq yace"yanzu ya zaniyi da Abba?"


Mami tadafa kanshi tace"insha Allah zanyi qoqarin nashawo kanshi,amma kada kasama kanka damuwa banaso ciwonka yatashi,kuma kakiyaye banaso irin haka tasake faruwa"

Rafeeq yace"insha Allah Mami"

Bayan wani lokaci yatafi gida.

*********

Tinda Mummy takoma gida da Sultan,Hanan tabude sabon shafin kuka,Mummy tarasa yadda zatayi da ita dukda irin rarrashinta da takeyi.

Gashi haryanzu takasa fadima mahaifin Hanan halin da ake ciki.

Mummy tace"Hanan idan ganin yaron ne bakiso zan maidashi wurin mahaifinshi,nayi tinanin idan nakawo maki yaon nan hankalinki zai kwanta"

Hanan tace"Mummy wlhy narasa yadda zanyi,inaso incire yaya Rafeeq cikin rayuwata amma nakasayin hakan"

Mummy tace"addu'a zakici gaba dayi Hanan kuma nima inayi maku addu'a"

Mummy tasa Larai tayima Sultan wanka aka shirya mashi sae bacci yadauke shi.


Bayan sallar isha'i,Daddy yakira Mummy awaya anan ne take fada mashi abinda yafaru tsakanin Hanan da Rafeeq.

Daddy baiji dadin abinda yafuba amma bbu yadda ya'iya,Mummy tayi mashi bayanin irin zaman da sukeyi Hanan batason zama lfy da shi da kuma abiyar zamanta,sannan yafahimta.


Bayan wata daya ds faruwar hakan,ba Rafeeq bbu labarinsa kullum Hanan tanata sa idon ganinshi amma shiru.

Ahaka Daddy yadawo daga thailand shima yyi mata fada sosae,kuma sannan ba wani shiga harkarta yakeba sbd tayi hankali.

Zaman gidan ba wani yima Hanan ddi yakeba,sbd bbu wanda yake sakar mata fuska cikin iyayenta har qara Mummy,amma Daddy daga gaisuwarta da yake ansawa,bbu abinda yake mata amma yana daukar Sultan yyita yimashi wasa.

Koda Abba yazo wurin Daddy bashi haquri,daddy bainuna komae ba,yace ai yyi dai2 dayayi mata haka,zanyi tayi hankali.

Rafeeq kullum sae yaje wurin Abba yabashi yahaquri amma bayako kallonshi,haka Mami da tayi mashi maganar Rafeeq saiya tashi yabata wuri.


Saida Mami tafadima Alh. Lawal halin da ake ciki sannan fa Daddy yasamu Abba yyi mashi magana sannan yyi haquri.


Yanzu hankalin Rafeeq yakwanta sosae bbu wani abu dayake damun Rafeeq yashi zamansu lfy shi da Zuhra dinshi.

Kusan kullum sai ankawo mashi Sultan har gida yagani.

Hanan dai taga abin bayi,wataranar monday Hanan tashirya wai itama zatabi Mummy zaria,sbd Mummy tacema daddy 1week zatayi a skul sbd sunada wani meeting da zasuyi.


Hakanan dai daddy ya yadda suka tafi,Hanan ko dadi takeji zataga yaya Rafeeq...............


*Ina sauraron comment dinku followers din wannan buk,nasan zakuce wane irin so ne Hanan takeyima Dr.Rareeq??...*

*Miss j*🙋😘
*🎀ADALILIN KANE🎀*



*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*


*EDIT BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*




*230-235*





Bayan sun fito, Zuhra tace "su taso suje suci abunci".


Islam kunya ta Kama ta sosae, ji take kamar tace ta k'oshi, to tasan halin 'yan kayansu, tana cewa ta k'oshi zai fara hararar ta.


Iman ko ajiki nta, ai dama so take yaji, cikin zuciyar ta take

11 / 16