A dalilin kane Complete Book By Jamila Samaila Yusuf

Author :  Jamila Samaila Yusuf Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 16

45K to 46.3K   out of 46.3K words

da kunna wutar dakin,ya juya yana kallonta.


Yace"amma kinsan banason ganin kukanki ko,kuma kinji abinda Mami tafada maki banda yawan tinani da 6ata rai ko?".


Zuhra tajuyo takalleshi,sai kuma batashi tausayi,yasa hannu yashare mata hawaye,fuskarshi cike da ladamar abinda yayi.


Yace"amma kinsan ko Hanan anan gidan tayi komai,Zuhra nasan idan kika tafi gida za'a kula da ke,amma nafison nakula da ke Zuhra kullun ina ganinki".


Zuhra tace"yaya Rafeeq fushinka yana tadamin hankali kayi haquri da maganar da nafada maka,kuma bazan sake maganar zuwana gida ba".


Yaya Rafeeq yace"my real wife,saboda haka nake qara sonki,i luv u to d square of infinity".


Ahaka sukayi baccinsu kike da so da kauna,hmm yaya Rafeeq kenan.


Hanan dukda irin yadda take tausayin Zuhra amma saida taji bataji dadin wannan lokacin ba,amma babu yadda ta'iya dole tayi haquri ahaka bacci yadauketa.



Washe gari dan dole Zuhra tatake badan komai da saidan yaya Rafeeq yana iya cewa anan zaiqara kwana dukda Hanan bazatace aah ba amma ai babu dadi.


Haka Zuhra taci gaba da rainun ciki har tabar laulayi,aka koma skul da yake suna 4 hundred level ne,cikinta nada wata 6 suka gama exam na 1st semester.



Zaune suke lafiya da Aunty Hanan,dan itama tasamu yadda takeso yanzu yaya Rafeeq yana kulata sosae fiye da da,tanajin dadin zama gidan sosae.



Duk abinda yakeso shine takeyi,dan itama tana kula da Zuhra sosae dan tagane zama lafiyarta agidan shine tazauna da Zuhra lafiya.



Kusan duk baya sati 1 sai Mami tazo gidan ganin Zuhra tare da yimata ya jiki.


Su Islam da Iman sungama A.B.U lafiya da yake suna gaban Zuhra da 1yr sakamokon abinda yafaru da ita.


Aka fara shire shiren saka masu rana wata 6.


Bayan su Zuhra sun kamala 2nd semester exams dinsu da sati 3,wani ranar juma'a tana kwance adaki ita da yaya Rafeeq matsanancin ciwon nakuda yakamata,tanata faman nishi yaya Rafeeq yatashi arude,yakira wayar Mami yafada masu,sannan yakira wayar Hanan babu 6ata lokaci sai gata cikin shirinta nazuwa asibiti.




Cikin daren nan suka tafi asibiti,acan suka tarar da Mami da Islam da Iman driver yakawosu.



Bayan andauki Zuhra cikin gadon daukar marassa lafiya akayi dakin haihuwa da ita.


Zuhra tasha wahala dan acan suka kwana,kowa sai addu'a yake Allah yasaketa lafiya.


yaya Rafeeq dan tausayin Zuhra hada kukanshi,Zuhra tasha wahala da saida marece sannan tahaihu har amfara shirin yimata c.s.


Abu kamar amafarki Nurse tayi masu albishir da tahaihu lafiya,amsamu twins babies,murna wurin dangi ba'a magana take yaya Rafeeq yayima Nurse kyautar kudi masu yawa,Mami kuwa yan hannun gold din dake hannunta takire tasakama Nurse din.



Nurse tayita godia,bayan kamar 1hr aka fito da jarirai farare tas da su mace da namiji.



kowa sai farin ciki yake,Islam tace"ai dama daganin wannan cikin yadda yayi girma kasan sai yan biyun".



Mami tace"Alhmdllh,Allah yaraya manasu".



Nurse tafito tace"ranka ya dade ku kwantar da hankalinku nan da 30mins zaku iya shiga kuganta".



Nanfa murna taqaru sosae.



Lafiya qlau Zuhra tahaihu babu wata matsala,bayan 2hrs aka sallamesu suka tafi gida.



Duk wanda yaga babies sai ace ai namijin da yaya Rafeeq yake kama macen kuwa Zuhra.


Hanan kuwa babu zama itama tana cikin farin ciki sosae.

Yaya Rafeeq yayi masu huduba da Umar da Maryam.



Da satin yadawo akasha biki wanda ba'a ta6a yiba dan shanu biyu da raguna hudu banda kaji da talo talo da aka yanka,anraba abubuwa kamar ba asan ciwon kudi ba,irinsu carpet,jikkuna,bedsheet,hijabai,cooler,alkur'anai da sauransu.


Ana kiran yaran da Sultan da Afra,kullun yaran suna wurin Aunty hanan dukda andauko Nannies guda biyu da zasu riqa kula da su.



Arziqi wurin yaya Rafeeq yafi da dan yanzu hada kamfanin atamfofi yake da shi a Ghana,ga kuma kamfaninshi na takalma da jakuna a thailand,ga kuma motoci da ake shigo mashi da su ana sayar mashi.




Tini yafara gina qaton gidanshi a g r a,katon gida mai dauke da part hudu,gidane na alfarma kuma namasu kudi masu jida kansu.



Ahaka bikinsu Islam yazo,akasha biki a gani nafada,lokacin su Sultan da Afra nada wata ukku sunyi wayau ga kyau,kamar Sultan harta 6aci da mahaifinsa,Afra kuma mahaifiyarta.




Haka taro yatashi lafiya qlau aka kai amare gidajensu,Islam ana kano aka ajiyeta,Iman kuma katsina.



Saida yaranta suka kusa iya yaye sannan suka fara service dinsu dayake acikin kano aka ajiyeta.


Ana cikin hakane Allah yaba Hanan ciki mai laulayin fitina dan dan dole yaya Rafeeq saida yabari tatafi gida,dan har cikin yayi qwari batajin dadi dukda anata zuwa asibiti.



Suna zuwa ganin akai akai,dan Sultan da Afra kamar gidan suke aisu kullun suna gidansu Hanan.



Bayan wasu watanni Allah yasauketa lafiya tahaifi diyarta mace wadda taci sunan Aysha,sunan Mummy kenan ana kiran baby da Farhat,yarinyar tana kama da Hanan sosae itama tana da kyau sosae.



Tini Zuhra ta manta da tayaye wasu yaranta,har ta kusa gama sevice dinta.


Amma yaya Rafeeq haryafara maganar wai babu wani labari dan shifa so yake gidan yacika da yara,Zuhra dai saidai tabishi da ido,abin mamaki kamar dai haihuwar babu wahala.


Ahaka Allah yabata ciki baifi wata hudu ba,Iman tahaihu suka dauki hanyar Katsuna ta dikko,tahaifi babyboy nanma asha taro baby yaci suna Aliyu suna kiranshi da Haidar.




Ahaka cikin Zuhra yatsufa,har lokacin haihuwarta yayi,bayan haihu da wata daya tasamu namiji yaci sunan Abba ana kiran baby da Khalipha suka tare a sabon gidansu.




Ba'a jimaba Islam tahaihu ita kuma baby girl tasamu mai suna Ayda.



Bayan Zuhra ta'anshi result dinta,yaya Rafeeq yafara shire shire yayesu yatafi da su England domin ci gaba da karatunshi da kuma na Zuhra zatayi Masters dinta acan,ga kuma su Sultan da Afra suma aka sakasu school tare da yaran turawa.




Rayuwa kenan,haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin jin dadi da kwanciyar hankali,kamar basu ta6a wani tashin hankali ba,Nigeria saidai suzo da yawo.


Bayan shekara biyar sun gama karatunsu da yaya Rafeeq turarawa sun daukeshi aiki a wata babbar jami'ar dake England zama yakamsu acan.



Wata shekara sunzo gida suna ahanyarsu tadawo gida driver yadaukosu airport nan sukaga wata almajira tanata faman bara jikinta duk quraje da yagaggun kaya da kuda sai faman binta sukeyi yaran sai faman janta sukeyi wai mayya mayya,adaidai inda danja tatsaida motarsu dan motoci biyune da daya tayi masu kadan,mota daya Zuhra da Hanan da Khalipha da Farouq na wajen Hanan da Suhaila tawurin Zuhra,dayar motar kuma Yaya Rafeeq da Afra da Sultan da Abiyad.




Matar tazo tana bara,Zuhra ce taji tausayinta taciro dubu biyar taba driver yabata,kamar daga sama matace takira sunan Hanan saikuma tafara kuka.


Dan Hanan bata wani ganeta ba,matar tace"Hanan baki ganeni ba?,ni ce fa Khubra,Khubra qawarki".



Hanan tayi salati tace"Khubra kice kika koma haka?".



Khubra tace"ni ce,banida lafiya Hanan kitaimaka min".


Tini motoci suka fara tafiya saboda ambada hannu,Hanan sanan tayima Mummy alqawarin itada Khubra har abada,kuma bazata karya wannan alkawarin ba,saidai taciro kudi masu yawa tamiqa mata hannunta na rawa ta'ansa kafin tayi magana har motarsu Hanan tayi gaba,nab Khubra tafadi tana kukan bakin ciki da ladama.



Yaya Rafeeq ne zaune cikin family dinshi porlour yaran duk sunbi sun hayeshi yana wasa da su.



Zuhra ce tafito tace"wa'annan yaran bakuji gaskiya".


Yaya Rafeeq yace"ni da nakeso Allah yaromin yara da yawa kinfasan yadda nakeson yara".


Ai Zuhra tace komai taqara gaba saboda tasan halinshi da son yaran kamar yadda yafada.



Rayuwarsu abin sha'awa cike da kwanciyar hankali,ga jin dadi sunje makka yafi sau nawa ga umara sunata zuwa,gashi kowace nada shoprite da kamfaninta.




Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin jin dadi,gashi ko wani lokacin cikin aikama iyayenshi da na matanshi abin arziqi tare da yan uwa da abokan arziki.




Arziki yaci uban nada dan yanzu yaya Rafeeq yasha kwana yayi kudi sosae yayi qiba daidai misali haka matanshi.



Yaranshi suna da tarbiya sosae ga kula da suke yamu tako'ina gasu kyawawa abinson kowa.





ALHMDLLH,INA GODIYA DA ALLAH DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI MAI SUNA ADALILIN KANE WANDA NI JAMILA SAMAILA YUSUF NABADA LABARI KUMA NARUBUTA.
08130193077










SAI KUJINI ASABON LITTAFINA MAI SUNA FURUCI NA NE!!!!!!!!!.




*REAL MISS J*🙋🏻‍♀😘

16 / 16