A dalilin kane Complete Book By Jamila Samaila Yusuf

Author :  Jamila Samaila Yusuf Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 16

42K to 45K   out of 46.3K words

illama itace take qara qarfafama yaya Rafeeq gwaiwa ajan auren.


Mami dama tadad'e da fahimtar halin Zuhra mutuniyar kirki ce,kuma tasamu tarbiya tindaga gidansu.



Nanfa kowa yashiga yabon halinta,Abba yayi farin ciki sosae dajin irin halin matar d'anshi guda daya tilo namiji kuma wanda yafiso.



Kowa ya qara sonta tare da ganin girmanta da kuma qara d'aukaka martabar iyayenta.



Ana saura kwana ukku aurin aure,Abba ne yahad'a lefe dozen biyu,d'aya aka kai gidansu Hanan,dayan ko na Zuhra ne,kuma komae iri daya ne saidai color yabanbanta.


Mami ma tayi masu akwati guda biyar biyar,sannan ga kuma wanda yaya Rafeeq yayi masu.


Yaya Rafeeq yarasa me zaiyima Zuhra arayuwa,yayi mata kyautar mota JAGUAR XF 2018 fara sul,tare da saka mata albarka da tarin kalamai masu dad'i wanda yaqara tabbatar mata da lallai yaya Rafeeq yana qaunarta fiye da kansa.



Kudine yabata miliyan d'aya yace tayi hidimar biki,idan kuma tana buqatar qari ya cheque yabata yace tarubuta ko nawatakeso zaiyi waya akawo mata.



Gidansu amarya ma biki akeyi babu kama hannun yaro kamar wata budurwa wanda zatayi sabon aure.



Daga gidansu amarya aka hada masu dinner a wani katafaren hall na manyan mutane masuji da kansu,amarya taji gyara tasha dilka harwani yellow takeyi,daqer Zuhra tasamu ango yahalarci taron amma ita bata samu zuwaba saboda batajin dad'in jikinta sosae.



Zuhra ce tahada masu kamu a wani babban hall na masu kud'i,abinci ne na turawa sai wanda kakeso lemuna,snacks da dao sauran kayan tand'e tand'e dana more rayuwa.



Kowa sai yabama Zuhra yake akan qoqarinta,hakanan dai take hidimarta amma batajin dad'in jikinta,tin jiya da daddare yaya Rafeeq yaketa tambayar me yake damunta amma tace ita lafiyarta qlau fa,dan dole yarabu da ita badan yayarda ba.



Haka aka d'aura auren Hanan da yaya Rafeeq,d'aurin auren da yatara manyan mutane,yan siyasa,yan kasuwa,masu fada aji da malamai da sauran yan uwa da abokan arziki,anatayi masu fatan alkairi.



Hanan tana zaune gaban Mummy da Aunty Saudat qanwar Mummy da mama sa'a yayar Daddy anayi mata fad'a wata sabuwar number ce tadame da kira.



Mummy tayi mamaki saidai bata nunama ko komae ba,saida aka gama fadan Hanan tashiga bedroom din Daddy domin ta'ansa waya.



Hmmmm,Khubra ce,tauraruwa mai wutsiya kenan,Hanan tad'auka suka gaisa.


Khubra tace"naji labarin rashin lafiyarki da rassuwar Sultan ga kuma bikinki anayi,ban samu zuwaba saboda kinsan Mummy batason ganina da ke Hanan,amma ina mai baki haquri".


Hanan tace"haba Khubra wannan ba hujja bane,aiko a wayane kin nemeni har afad'i maki rassuwar yarona amma kiyi shiru?".


Khubra tayi murmushin irin na gogaggun yan bariki tace"hmmm, ai baikatama kiga laifina ba Hanan,laifin kishiyarki Zuhra zaki gani saboda malamina yafad'amin itace tayima Sultan asiri yamutu,dan haka kada ki yadda,Allah yabaki damane domin kiga bayan Zuhra,ki bima yaronki haqqinshi".


Hanan tace"Khubra kina nufin Zuhra ce takashemin Sultan d'ina..............."


Ganin Mummy datayi atsaye kusa da ita shine yasa maganarta tamaqale bata samu damar fitowa ba.


Mummy tayi murmushin takaici tace"hmmm da kyau Hanan,kicemin ga inda nake tifqa anayimin warwara,ga wadda take qara baki tarbiya ko?".


Hanan hannunta na rawa tini takashe wayar,tarasa bakin magana tinin tafara kuka.


Mummy tace"kukan name nene kuma?,Hanan idan har kikace tarbiyar da wannan shed'aniyar ta baki itace zaki d'auka,toh kitina wannan itace damarki taqarshe a gidan Rafeeq wlhy duk abinda yabiyo baya babu hannummu aciki ni da mahaifinki domin zan fad'a masa komai".


Hanan cikin muryar kuka tace"wayyo Allah na Mummy na wlhy natuba,babu ni babu Khubra har abada,ku yafemin dan Allah".


Mummy tace"Hanan tin kina university narabaki da yarinyar nan amma ashe nice kika d'auka mutuniyar banza baki rabuda da itaba,yarinyar da take aikata manyan laifika,tabi maza tabi mata,Hanan bazan zargekiba amma baki kyauta minba".



Hanan hannunta na rawa tazare layinta takarya agaban Mummy,sai faman zubar da hawaye take.


Mummy tadafa kafad'arta tace"Hanan keba musulma bace?,baki yadda da qaddara ba?,baki yadda Allah ne mai kashewa ya kuma raya ba?".



cikin muryar kuka Hanan tace"nayarda Mummy".


Mummy tace"toh Allah shine wanda yarabaki da Sultan ba Zuhra ba,ki ajiye maganar waccen jahilar,kuma boka jihiline Hanan,inason fad'i maki gaskiya Zuhra tana sonki,tana qaunarki,nason d'anki,tanason ki Rafeeq,tanason farin cikinku,tanason yan uwanki da iyayenki,ita yarinyar kirki ce kuma mai tarbiya,daga qarshe inaso kiyi koyi da kyawawan halinta idan har kinason zama lafiya,kada kinuna mata abu marar kyau saboda tana sonki sosae".



Hanan tace"Mummy insha Allahu nad'auki maganarki kuma ina da Khubra har abada,ki yafemin,wlhy ban ta6a aikata wani mummunan abuba kamar yadda Khubra take aikatawa".



Mummy tace"toh Allah yayi maki albarka,kije kizauna da mijinki da abokiyar zamanki lafiya kuma da zuciya d'aya,yanzu kije iyayenki na jiranki zasu kaiki gidan mijinki".



Hanan tasha kuka tafin tatafi,daqer aka rabata da Mummy sai kace wata qaramar yarinya.


Tin daga lokacin Hanan tayi alqawarin babu ina ba Khubra hargaba da abada kuma tad'auki qaddara akan mutuwar Sultan,da kuma zama da mijinta tare da Zuhra da zuciya d'aya.


Babban al'amari,tin bayan sallar la'asar du abinda Zuhra taci saiya dawo ga kuma wani ciwon kai da take fama da shi,amma babu wanda tafad'i mawa.


Duk da su Islam da Iman nata faman yi mata surutu akan me ke damunta,saidai tace babu komae batajin magana ne.


Aka kai amarya gidan mijinta,bayan sallar insha kuwa yawatse,gidan shiru dan Zuhra tana part dinta kwance biya kujera 3seater saboda abinda yake damunta.


Yaya Rafeeq yana gidan Abba,Mami da Abba sunafa faman yimashi nasiha tare da nuna mashi yanayin rayuwa da kuma haquri.


Abba yace"Alhmdllh yau dai Allah yanuna mana abinda muka dad'e munason gani,toh Rafeeq ga Hanan a gidanka,kayi adalci atsakaninsu,kasan dai halin da Hanan take ciki,ko ince ciwon da yake tare da ita,toh ka kula sosae,idan har kazama sanadin tashin ciwon Hanan bazan yafemaka ba,yarinyar nan tana sonka tana qaunarka kuma ba rasa masoya tayiba hakanan abin Allah,Allah yanufeta da sonka,idan har katadama Hanan ciwonta kagama kunyatani a idon duniya saboda iyayen yarinyar nan suna da kawaici sosae, kuma son gamamin komae tinda suka nunamin suna son abinda nahaifa,bawai ina nufin kafifita Hanan akan Zuhra ba,aah banaso awulaqanta kowa acikinsu,kuzauna lafiya,hakan zaisa hankalina yakwanta inyi farin ciki ko bayan raina,Allah yayi maku albarka,yabaku zuri'a tagari".


Mami ta'ansa da ameen ya rabbi.


Mami tace"toh,duk abinda zan fad'a mahaifinka yarigani Rafeeq,hakika Zuhra yarinyar kirkice samun irinta sai antuna dan haka kariqesu da kyau,itama Hanan idan tanada wasu halaye wa'anda bakaso,zaka iya gyarata cikin hikima,da haka hartazama kamar kowa,banaso wani abu marar dad'i yafaru atsakaninku,Allah yarufa asiri,ya albarkaceku ya kuma baku sa'a"


Suka ansa da ameen.


Abba yace"yanzu saika tashi katafi gida dare nayi.


yaya Rafeeq yayi godia tare da fad'in insha Allah yayi alqawarin adalci,atayashi da addu'a Allah yahad'a kansu.


yaya Rafeeq baibar gidanba sai wurin 9:30pm.


Suka rakashi har wurin mota hadasu Islam da Iman sannan sukayi mashi addu'ar asuba tagari.





Yabiya wani supermarket yayi shopping dinduk abinda yake buqata sannan yatafi gida.


Ango yasha qamshi,yasha farar shadda fara qar tare da babbar riga,wadda tayi aiki irin na yan ghana,ya qara kyau da kwarjini.



Hannunshi d'auke da manyan ledoji guda biyu,part din Zuhra tafara shiga yatarar da ita kwance biya kujera.


Yayi sallama amma bata ansaba yasan bacci takeyi,a fili yace"oh my God,my wife abisa kujera kike bacci kuma?".

Ya isa wurinta da niyyar yad'auketa yakaita bedroom dinta bisa gado.


Fuskarta yafara shafawa mai tarin taushi tamkar fatar jariri sabuwar haihuwa,ahankali tabude kyawawan idanuwanta kamasu shining kamar zaiba.


Suna had'a ido tayi mashi murmushi,shima murmushin yamaida mata tare da kissing goshinta.


Zuhra tace"yaya Rafeeq nayi tinanin kunyi bacci fa".


yace"ya zanyi inyi bacci batare da naga wannan kyakykyawar fuskar takiba,yanzu nadawo daga gidansu Mami".


Tace"ina abokan naka?"


Yayi murmushi yace"ko auren farko ban yarda abokai sukayimin rakiya ba bare kuma nabiyu,yanzu haka kece zaki rakani ai".


Zuhra tace"ni kuma yaya Rafeeq?".


Yace"taso mujema,ni naga kindan fad'a Zuhra kuma kinqi kifad'amin abinda yake damunki".


Zuhra tayi murmushin qarfin hali tace"kai dai ke ganin haka amma ni babu abinda yake damuna".



Tatashi suka tafi part din Hanan,har ciki bedroom dinta sua shiga saboda bata porlour.


Zaune take tsakiyar gado,dakin yayi kyau sosae,sai Zuhra taga komae na part din Hanan iri dayane da kayan da yaya Rafeeq yacanza mata,color ne kawai yabanbanta,kayan part din Hanan komae purple tin daga porlour dinta har bedroom da kitchen,ita kuma Zuhra komae pinks colour ne nata.


Tana ganin kafin ta'ansa sallama tayi masu kyakykyawan murmushi tare da ansa sallamarsu.



Suka zauna yaya Hanan tagaishe da yaya Rafeeq babu yabo ba fallasa ya'ansa,Zuhra tagaishe da ita tare da yimata sannu da zuwa,cikin kulawa Hanan ta'ansa.


Yaya Rafeeq ne yayi masu nasihohi akan zama lafiya da kuma bin umarni da order,yayi masu bayani sosae akan zaman mataye na mazan Allah(s a w),daga qarshe yace yana fatan zasuyi koyi da su.


Yace"ga dinner dinsu nan Hanan,tajera masu a dinning area,babu 6ata lokaci Hanan tatashi,a part dinta sukaci abinci,pizza ne da tsire da lemuna da wani cake mai shegen dad'i,sai kuma wasu manya donut wanda sukaji kayan had'i,da fresh milk da dai sauransu.


Bayan sungama sukad'an fara fira,har 10:45pm,Zuhra tace"idan nabiye maku bazanyi bacci ba yau dan haka nabarku lafiya".


Tamiqe zata tafi,Hanan tace"kai Zuhra badai har kinfajin bacci ba?".


Zuhra tace"wlhy Aunty Hanan bacci nakeji,bari intafi inkwanta".

Yaya Rafeeq,Aunty Hana,
Ina maku fatan alkairi,
Asuba tagari.


Yaya Rafeeq ai bari murakaki mana,yatashi tsaye,Hanan ma tatashi suka fita.


Dama Zuhra nata ganin jiri,daurewa kawai take,saboda batason sugane wani abu dan hankalin yaya Rafeeq zai tashi sosae,qarshe wannan daren nasu ya6aci.



har cikin bedroom dinta suka kaita,yaya Rafeeq ne yakwantar da ita,yanada niyyar lullu6eta sai amai,duk yabi yarud'e yaqara rungumeta ajikinshi,hankalinshi yatashi sosae duk yabi yarud'e.


Gaba d'aya kayan jikinshi sun 6aci amma baidamu ba,yaqara rungumeta ajikinshi kamar wadda za'a qwace mashi ita.


Yadda Zuhra keyin aman dile duk wanda yagani yarud'e,sai abin yayi m Hanan yanayin irin yadda Sultan yariqayi agida kafin sutafi asibiti aranar da zai mutu.


Itama Hanan tarud'e sosae,yaya Rafeeq yace"Hanan tafi part dina kidauka car keys mutafi asibiti.


Da gudu Hanan tafita har tinti6e takeyi,kafi tadawo yaya Rafeeq yacanza ma Zuhra riga,sannan yacire babbar rigar da ke jikinshi.



Yadauketa yafita da ita,a porlour yaci karo da Hanan,suka tafi harabar gida sai asibiti.



Allah dai yakaisu lafiya dan irin gudun da yakeyi,Hanan ce rungume da Zuhra a baya,shikuma yana driving.



Suna zuwa asibiti emergency aka ansheta,akayi cikin wanda room da ita,drip aka fara saka mata,sanna aka shiga dubata.


Yaya Rafeeq ko zama baiyiba haka itama Hanan takasa zama,tausayin Zuhra yakamashi dama yasan daganinta batajin dad'i,Allah kadai yasan irin yadda takeji.



Saidai Hanan taga Yaya Rafeeq yana zubar da hawaye kamar wata mace,tinda take bata ta6a ganin kukan yaya Rafeeq ba,ko mutuwar Sultan baiyi kuka ba,wannan wane irin sone yaya Rafeeq yakeyima Zuhra?.


Lalle Zuhra tayi sa'a arayuwa,ko kuma ince halintane yaja mata wannan martabar.


Idanuwan yaya Rafeeq sunyi yajur kamar garwashi,gashi cikinsu babu wanda yazo da wayarshi bari afad'i a gida.


Bayan 2hrs Doctor yafito tare da sauke farin glass din dake fuskarshi fuskarshi babu annuri da walwala,gaban Yaya Rafeeq ya yanke yafad'i.


Hatta Hanan saida taji hankalinta yayi mugun tashi,itama har kuka saida tayi dan tausayi gashi kuma angon nata sai zubar da hawaye yake.



Doctor yakalli yaya Rafeeq cikin tausayawa yace"kasame ni a office yanzu"...........................









*Real Miss j*🙋🏻‍♀😘
[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*



*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*



*250-255*



Hankalin yaya Rafeeq yaqara tashi,Hanan dake zaune tatashi tsaye.


Yaya Rafeeq zuface fara keto masa duk da irin A/C dake cikin asibitin.


Yaya Rafeeq yabi bayan Dr. Hashim,har zuwa office.


Zaune yake agaban Dr. Hashim bisa kujera.


Yaya Rafeeq addu'a kawai yake,Allah yasa Zuhra tasamu lafiya kamar yadda take abaya.


Dr. Hashim yayi gyaren murya yace"ranka ya dade matar tana dauke da juna biyu na tsawon 6months,congratulations".


Yaya Rafeeq yace"Dr. ya jikin matana yake?".


Dr. Hashim yace"kada kadamu ranka ya dade,insha Allah zuwa gobe zaku koma gida".



Yaya Rafeeq yayi ajiyar zuciya mai qarfi yace"Alhmdllh,hankalina ya kwanta sosae".


Dr. Yace"lalle kanaji da wannan matar taka sosae".


Yaya Rafeeq yace"Dr. Hashim kenan,ina sonta fiye da tinanin mai tinani,yanzu zamu iya shiga muganta?".


Dr. Yace"eh zaku iya shiga,amma fa zatakai zuwa 5:30am bata farkaba cuz alluran da akayi mata,Allah yabata lafiya".



Yaya Rafeeq yace"ameen ya rabbi,muna godia".


Sukayi sallama da Dr. yatashi yafita.


Tinda yabar Hanan ko zama bata sake yiba,saboda hankalinta atashe yake.


Anan yatarar da ita cikin farin ciki,Hanan tana ganinshi itama tayi murmushi tasan da alamar nasara.


Yaya Rafeeq yaqaraso ina take tsaye,Hanan tace"yaya Rafeeq ya jikin Zuhra?".


Yaya Rafeeq yace"Alhmdllh Hanan,Zuhra tana d'auke da juna biyu,Allah sarki,ashe ina da rabon ganin yaron Zuhra?".


Hanan tace"Alhmdllh Allah yaraba lafiya".


Yaya Rafeeq yace"ameen ya Allah,yanzu mushiga muganta".


Hanan tabi bayan shi har suka isa bakin qofar shiga room din,yaya Rafeeq ne yamurd'a qofar sannan yashiga tare da sallama,Hanan na biye da shi.


Kwance take bisa gado,tanata baccinta,cikin kwanaki kad'an tad'an fad'a,tausayinta yaqara kama shi.


Yazauna agefe gadon,Hanan na zaune bisa kujerar da ke kusa da gadon.


Kyakykyawar fuskarta yake kallo,yasa hannunshi na dama yafara shafar fuskarta da keda taushi kamar fatar jariri sabon haihuwa.


Wani masifaffen kishi yatasoma Hanan,ji take kamar ta'anshi car key tatafi gida dan dai dare yayi sosae,babu yadda ta'iya dole tarintse idanuwanta tana neman tsari daga shaidan.


Basu dade ba sukajiyo kiran sallar asuba,yaya Rafeeq yatashi yashiga toilet yadauro alwala sannan yatafi masallaci.


Bayan yatafi itama Hanan tayo alwala tayafa mayafinta tare da kabbara sallah.


Yaya Rafeea yana dawowa,yaga dai Zuhra bata farka yacema Hanan zaije yafadama su Mami.



Hanan tace''adawo lafiya".



Hanan ta'isa bakin gadon Zuhra tazauna zuciyarta cike da tinani iri daban daban akan Zuhra.


Hakika tasan tana kishin yaya Rafeeq,kuma tana sonshi sosae fiye da komae,batayi niyyar had'ashi da kowa ba,amma babu yadda ta'iya idan tanason zamanta lafiya tare da shi to dolene tazauna da Zuhra lafiya,saboda ba itaba hatta iyayenshi sunsan yanason Zuhra fiye da komae.



Dan dole taba zuciyarta haquri tare da addu'ar Allah yabasu zama lafiya,ya karesu daga sharrin mutun da aljan.


Tabbas Zuhra yarinyar kirkice bata nufina da komae sai alkairi toh dammi natsaneta,wannan duk sharrin shaidan ne tare da sharrin Khubra,Allah karagemin wannan kishin da yake damuna nazauna da Zuhra tamkar qanwata ciki daya.


Wannan tinanin shine tayitayi har Allah yayima Zuhra farkawa.


Ahankali Zuhra tadafa hannunta muryar asanyaye tace"Aunty Hanan tinanin me kikeyi haka".


Fuskar Zuhra kice da damuwa.


Firgigi tadawo cikin hayyacinta tace"Zuhra kintashi?,ya jikin naki?,bari nayima Doctor magana,ina zuwa yanzu".


kafin Zuhra tayi magana har Hanan tafita,tausayin Hanan yakama Zuhra,cikin zuciyarta take fad'in badai anan Aunty Hanan takwana ba.



Babu 6ata lokaci Hanan tadawo da Doctor,fuskarshi d'auke da fara'a yashigo tare da sallama,Hanan na biye da shi.


Bayan Zuhra tagaishe da shi ya'ansa,tare da yimata ya jiki,yashiga dubata.


Jikinta da sauki sosae,yatambayeta ya takejin jikin nata,Zuhra tace"lafiya qlau saidai rashin qwarin jikin".


yace"kada kidamu zaki samu lafiya insha Allah".


Yakalli Hanan yace"zuwa anjima za'azo abata breakfast dinta tare da magani,Allah yabata lafiya,Ina Rafeeq yajene?".



Hanan tace"yaje yadawo yanzu insha Allah".


yace"ok,shikenan".sannan yafita.


Hanan tadawo tazauna kusa da ita tace"ya jikin naki?".


Zuhra tace"nasamu sauki Aunty Hanan,amma kinyi qoqari da kika kwana awurin nan nagode Allah yabaki lada".



Hanan tayi murmushi tace"ameen,ai tare da shi muke yaje gidan Mami yadawo".


Zuhra tayi murmushi tace"Allah yadawo da shi lafiya".


Bayan sungaisa da Mami da Abba nan ne yake fad'a masu abinda ke faruwa,duk sukabi suka rud'e hadasu Islam da Iman da suka tashi bacci ba shiri sunyi cirko cirko.


Tare da Mami yataho asibitin tin cikin motor Mami taketa faman mashi fad'a dan tinlokacin da zasu tafi asibitin da ankira amfad'a masu,ambar yarinya kamar bata akowa.



Saidai yaya Rafeeq yayita bata haquri dan yaga ranta ya6aci sosai.


Suna zuwa suka tarar da Zuhra tafarka,har tana iya magana lafiya lau.



Bayan tagaishe da Mami,Mami ta'ansa tare da yimata ya jiki cikin kulawa tare da tausayawa.



Wata Nurse ce tashigo tare da wani dan keke naturawa wanda yake dauke da kayan break da kuma magunguna.



Cikin toilet din akwai sabon brush da maclearn,bayan tayo brush,lokacin Nurse din tagama had'a tea,da niyyar ita zata bata.


yaya Rafeef ne yace"kibar zanbata".


Nurse din tayi murmushi tace toh tare da komawa gefe.


Yaya Rafeeq ne yabata tea din da hannunta tare da cheaps da soyayyen kwai,bata wani ci sosae ba,dukda Mami tasa baki.



Bayan yagama batane,Mami tace"yanzu katafi da Hanan gida domin tashirya,kaima saika shirya,sannan kutahoma da Zuhra da kayanta da zata shirya".



Badan ranshi yasoba hakanan yatafi yabar Zuhra,haka yatafi da Hanan gida akabar Mami.



Mami ce taci gaba da kula da Zuhra tare da tattalinta kamar mahaifiyarta,Mami sai nan nan take da Zuhra kamar ba sirikarta ba.


Hakika Zuhra najin dadi tare da godema Allah daya hadata da Mami,saboda tinda Allah yahadata da yaya Rafeeq bazata iya cewa ga abinda Mami tayi bata marar kyau ba,tsakaninta da ahalin Mami da Abba sai godia tare da fatan alkairi.


Lokacin da Doctor yadawo qara duba Zuhra,nan yakeyima Mami murnar akan cikin Zuhra,itama Zuhra anan takejin abinda ke faruwa,Mami tashiga nuna farin ciki tare da godia ga Allah,ita kuma Zuhra banda kunya babu abinda takeji dan ji take kamar tagudu.



Bai wani 6ata lokaciba sai gashi yadawo,tare da iyayen fruits da juice da chocolate da dai sauransu.



Bai dade da dawowa ba saiga su,Islam da Iman driver yakawosu tare basket manya guda biyu ta abinci,nan fa Mami tatsare Zuhra akan saitaci abinci.


peppe chicken ne tazuba mata tare da soyayyen irish da source.

Zuhra tana faraci tayi da gudu toilet,yaya Rafeeq yabita amai kawai takeyi babu qaqqautawa,saida tagama sannan suka dawo.



Babu abinda takeso sai tea da cheaps shikenan abincinta.


Wajen 11am saiga Mummy tazo ganin Zuhra tare da abinci kala kala da fruits da ruwan roba,tatausayama Zuhra sosae,anan tazauna har lokacin da aka sallamesu suka tafi gida.


Saboda kawai irin na Mama cewa sukayi tinda Mami tana tare da Zuhra basai sunzo ba dan itama uwace zatayi komae.



Mami taji dadin da irin kalaman iyayen Zuhra,sun bata girmanta sosae.


Babu irin gatan da Mami batayima Zuhra ba,lalle Zuhra mai sa'a ce.



Sai bayan sallar isha'i sannan Mami da su Islam suka tafi gida.


Dan Yaya Rafeeq da Hanan anan suma suka wuni.

Saida lokacin kwanciya yayi,yaya Rafeeq yabi Hanan har part dinta yace"tayi haquri yakwanta agurin Zuhra tinda batada lafiya.


Hanan dukda bataji dadi ba saidai tadanne tace mashi babu komae,Allah yabata lafiya.


Zuhra har bacci yafara daukarta taji alamar mutun yashigo bedroom dinta,da sauri tabude idanuwanta wa'anda suke cike da bacci,yaya Rafeeq ne tagani yana qoqarin rufe d'aki.



Fuskarshi cike da murmushi yace"maman twins ko akwai abinda kike buqata?".


Zuhra tayi murmushi tace"babu abinda nake buqata mijina,saidai katafi kakwanta da Aunty na".


Yaya Rafeeq yaqaraso kusa da ita yazauna gefen gado yana kallon cikin idanuwanta yace"tasan baki da lafiya kuma tahaqura inkwana anan ko zaki buqaci wani abu".




Zuhra taji tausayin Aunty Hanan sosae,fuskarta cike da tausayin Hanan tace"yaya Rafeeq zamana anan kamar zan takura maku,kaga Aunty Hanan tana buqatar kulawarka,ina son intafi gida ko zaku samu damar cin amarcinku".


Da ranshi ya6aci baici da ita komai ba saidai yakwanta kawai tare da kashe beside lamb din dake kusa da shi.


Hankalin Zuhra yatashi tasan fushi yayi,ahankali tamatso inda yake tare da kiran sunanshi.


Tace"yaya Rafeeq lafiya?".


Baiyi mata magana ba,ranta babu dadi saidai taji hawaye suna zuba bisa fuskarta.

Dajin yadda take mayar da numfashi yasan kuka takeyi,da sauri yatashi zaune tare

15 / 16