Author : Jamila Samaila Yusuf Category : Romantic Hausa Novels
take magana tace"wa yace kadauki wannan yar iskar yarinyar kayafi da ita?"
Ranshi yaqara baci fiye da da,sbd baisan dalilin dayasa duklokacin da Hanan tajefi Zuhra da wannan kalmar yake qara jin takaicinta ba.
Cikin zafin rai yake magana yace"ke wace irin marar tarbiyace?,aka koya maki sallama ba bare kuma gaishe da nagaba da ke ne?"
Cikin tsiwa tace"sae natambayo,kuma wlhy kana gab da jama yarinyar mutane bala'i"
Yaya Rafeeq yace"wlhy idan kika sake kika yima Zuhra wani abu,sai kinsani"
Hanan tace"saedai insani,wlhy indai akanka ne RAFEEQ"
Yace"magana ta dake taqarshe,duk ranar da kika sake kiran Zuhra da yar iska,zakiyi ladamar sanina,kuma kada nasake gani qazamin kiranki awayana"yyi tsoki yace jobless sannan yakashe wayar shi.
Ba qaramin takaici Hanan tashiga ba,wani bangare na zuciyarta tace kodae son yarinyar nan yake,afili tayi saurin cewa wlhy billahi RAFEEQ baka iyasa ba,kayi kadan kuma zakayi ladama.
Saekuma wani bangaren yace ya za'ayi kamar Dr. Rafeeq yaso wannan yarinyar?,saekuma tayi tinanin kawae da yarage mata hanya ne dan yana ganinta tare da qannanshi,amma shida ko qannanshi baya sakarma fuska mizai da wannan wawiyar,haka yita sake sakenta,amma bata yarda yanason Zuhra ba.
Tashi yyi yashiga bathroom yyi wanka sbd wani zafi daya taso masu dukda room din akwae a/c tana aiki.
Washe gari bayan Zuhra tayi wanka tashirya cikin wani material dinkin riga da siket mai zanen flower green tayi kyau sosae,Mama tace"tashirya taje tagaishe da Haj. Hadiza matar chairman,kafin lokacin tafiz yyi,Zuhra tafiddo hijabin milk tasaka tayima Mama sallama.
Baya Iman tagama exam dinta,Aunty Hanan tadauke saeda suka biya kaduna tadauko wasu takardunta sannan suka wuce Kano,bbu inda tayi parking sae gidansu,zuwa anjima sae ida kaisu gida.
Dama kuma ranar Mummy tadawo daga Cairo,Mummy taba zama school sosae saedai deputy provost shi yake gudanar da aiyikan cikin school din.
Bayan tayi parking aharabar gida suka fito,ma'aikata sae faman gaishe da ita suke amma ko kallon mutunci bbu atsakninsu,dama ita mutum ce wadda batason talaka,shiyasa lokuta da dama idan Mummy tagani tanayi maya fada,da anyi maya fada kuma sae kuka har tacema ba'a sonta tinda ba'ason abinda takeyi,dole Mummy talallabe ta tinda ita daya suka mallaka kamar rai.
Aporlour suka tarar da ita tana duba wasu takardu,Mummy taji dadin ganinsu sosae,bayan sungaishe da ita kamar yadda suka saba.
Mummy tace"amma Hanan kin kyauta min da kika kawomin su gida,ni da yarana amma sae nadade bangansu ba,ba kamar ke Islam"
Islam tayi murmushi tace"Mummy karatune yaboye ni ae"
Mummy tayi murmushi tace"ina fatan kunyi kokari a exams dinku,sbd wannan shekarar akwai provost award da zamu bayar"
Hanan tace"Mummy sunyi karatu sosae ae"
Mummy tace"wel,Allah yabada sa'a"
Suka ansa da ameen ya rabbi.
Hanan tatashi takoma kujerar da Mummy take tafara shagwaba wae yunwa takeji,Mummy tayi murmushi tace"wae wadda ake shirin yima aure itace batabar yimani shagwaba ba"
Su Islam da Iman sukayi dariya.
Hanan taqara shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace"Mummy ko nakira wayarshi baya dauka kuma bayason kulani"
Mummy tace"laifi kikayi mashi ko?"
Hanan tace"mummy bbu abinda fa nayi mashi"
Mummy tace"tou shikenan,zanyi bincike kuma zangano gsky"
Daddy ne yakira wayar mummy,bayan sungaisa yake tambyarta Hanan tadawo ko,mummy tace"ina tare da ita hadasu Islam da Iman"
Mummy taba Hanan wayar,bayan sungaisa Hanan tace"daddyna nayi fushi,shine kakira mummy baka kirani ba"
Daddy yace"am sorry nima inanan nakusa dawuwa"
Haka sukasha firarsu har saeda suka gaisa dasu Islam sannan sukayi sallama,suka yi wanka sannan sukaci abinci,da marece Hanan takaisu gida,Allah yasa har tagama zamanta Rafeeq baidawo ba.
Bayan sati biyu da dawowarsu gida,kullum basu da labari saena Zuhra dukda suna waya da ita,yanzu ko Mami tasan Zuhra sosae dukda bata taba ganinta ba amma tana ganinta ahoto cikin waya,taji yarinyar takwanta mata arae yadda taji yaranta suna labarinta tasan suna zaman mutunci sosae kuma sunshaqu da juna.
Islam tacema Mami gobe zasuje gidansu Zuhra,haka Mami tabasu kudi suje suyi shopping hadda Zuhra,komae guda ukku saka saya kuma iri daya saedae kala tabanbanta dayake kowa nada best colour dinshi,kuma sunsan kalar da takeso.
Washe gari suka shirya ado sukayi bana wasa ba,driver yakaisu,dama tafadi masu sunan unguwarsu,da suka isa suka kirata sae gata tafito,sunji dadin ganin junansu,sannan takaisu gida............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*I luv u all😘😘😘...*
*55- 60*
Islam da Iman sunyi mamakin muhallin da Zuhra take rayuwa sosae,sbd bazaka taba tinanin yarinya kyakykyawa irin Zuhra tana rayuwa anan ba,kuma sannan takama kanta a school karatunta tasa gaba.
Lokacin da sukazo Mama batanan tana gidan chairman,sae ita daya.
Dan qaramin gidane ginin kasa,bbu ko yabe,tare da qananan katangu,gidan daki biyu ne tal,shima ginin kasasae dan filin tsakar gida wanda bbu ko sitinti,a tsakar gida murhummu yake tasancewar bamu abinyin kitchen ko yar rumfar da zamu riqa sanwa kodan damina,sae ma kewayimmu wanda akiyi da langalanga bbu ko murfi,dakin mama sae na Babana,dakin mama nasaukesu,wanda bbu komae sae dan qaramin gado da karfe,da wata yar qaramar katifa,kujeru guda biyu wanda sun tsufa,sae wani tsohon carpet wanda mama tasamo gidan chairman.
Dama tinda sukace suna hanya,tasawo masu So6o da kunun aya a makwabtansu,dambun masara ne da mai da yaji mukayi,shi nazuba masu kuma sunci sosae sae santi sukeyi.
Suka bata kayan da Mami tace abata,Zuhra taji dadi sosae sbd acikin irin kayan su Iman suka sanyo nasu.
Suka shiga firarsu ta school,sbd baifi sati biyu sukoma school ba.
Suna cikin firarsu Mama tadawo gida,cikin girmamawa suka gaishe da ita,mama taji dadin ganin irin yaran da Zuhra take rayuwa da su,sbd tinda tagansu tasan natsatstsune,kuma sannan suna da tarbiya,dukda yanayin muhallin da suka iskesu baisa sunji qamarsu ba,shiyasa mama taji tana son yaran sosae.
Sae wajen qarfe 6pm sannan suka miqe zasu tafi,suna cikin sallama da mama,Baba yadawo dauke da huluna ahanninshi,Zuhra ta'ansa tare da yimashi sannu da zuwa.
Islam da Iman suka gaishe da shi cikin girmamawa,Mama tafada mashi cewa su Islam ne,Baba yayita sak masu albarka sannan suka fita.
Mama ce tarasa wane abu zata basu,sae tatina da wata kuka da bushashshiyar lu6ewar da aka kawo mata daga qauye,takira Zuhra tace gashi tabasu,sunyi godia sosae.
Zuhra tarakasu har kofar gida inda driver yyi parking,ji suke kamar karsu tafi sbd wani sonta da tausayinta,daqer sukayi sallama da juna suka shiga mota suka tafi.
Haka suka dawo gida cike da mamaki,koda sukaba Mami labarin rayuwar su Zuhra,Mami tatausaya masu sosae.
Yaya Rafeeq atsaye gaban mirror cikin shigar dogayen kaya,wata dakakkiyar shadda ce,tsadaddiya,ruwan toka sae shining take,yasaka huka da takalma bakake,yyi kyau sosae sae ni'imtatcen kanshinsa ke tashi.
Haka yafito porlour fuskarshi bbu walwala,Mami ce tasashi yaje yagaishe da Mummy yyima kuma daddy sannu da zuwa,yadawo daga Umara.
Mami nalura da yanayinshi sati biyu yadan rame,da alama yana cikin damuwa sosae,amma tasan bazai wuce akan saranar auren shi,kuma ita bbu yadda zatayi.
Yarar da Mami a kitchen tana hada coffee mate,tana ganinshi tayi murmushi tace"har kashirya kenan"tashafa fuskarshi tace my son kayi kyau.
Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"nagode Mami"
Mami tace"cikin kwanakin nan me ke damunka ne?,naga kadan rame"tana kallon cikin idanuwanshi yasan ansa takeson ji yanzu.
Yace"bbu komae Mami"
Mami tatausasa murya tace"kayi haquri,nasan maganar Hanan ce,nasan katakura kanka akan yi mana biyayya Rafeeq,muna matuqar farin ciki da Allah yabamu yaro mae biyayya kamar ka"
Yaya Rafeeq yyi murmushin karfin hali yace"bbu komae,Mami nayarda zan aureta amma ina buqatar dan wani lokaci"
Mami tace"naji,amma kana tinanin Alh.da iyayen Hanan zasu qara maka wani lokaci"
Yace"insha Allah bbu damuwa Mami,sae nadawo"
Mami tace"Allah yadawo dakai lfy,kagaishe min da Haj.fatima"
Bakar motace yashiga qirar corolla sabuwa fil,cikin isa da izza yake driving har ya'isa unguwarsu,unguwace ta masu kudin gaske.
Mai gadi yabude mashi katafaren gate yashiga,yyi parking din motarshi,yafito masu aiki suka shiga kawo gaisuwa shikuma yana ansa tare da basu yan nakashewa.
Kofar da zata sada shi da porlour yashiga,tare da sallama,bbu kowa porlour sae plasma dake manne a bango tanata faman aiki tare da karar a/c.
Bayan kamar minti ukku Mummy tafito daga bedroom dinta,tana ganinshi tayi murmushi tace"yau Rafeeq ne agidammu"
Yaya Rafeeq yyi murmushi,bayan sun zauna yagaishe da ita,cikin jin dadi ta'ansa.
Suka shiga hirarsu akan school tare irin award da za'aba students da irin decoration din da yakeso ayima dakin tarbar bakin.
Mummy tace"wae kwana biyu mi yahadaka da qanwar taka?nasan dae laifi ta'aikata"
Yaya Rafeeq yadan sosa kae sannan yace"bbu komae Mummy"
Mummy tayi murmushi irin nasu na manya tace"adai riqa haquri,Allah yadaidaita tsakanin ku"
Tatace tace bari infadima Alh.zuwanka,sannan tafita.
Bayan kamar minti goma saeta tare da Daddy,bayan sungaisa da daddy,mummy tatashi tafita.
Sukadan yi hirarsu sannan daddy yyi murmushi yace"ya zance sa biki kuma?"
Rafeeq yadan sosae qeya yyi shiru tare da sunkuyar da kai kasa.
Daddy yyi murmushi karo na biyu yace"my son ko akwai wata magana ne,ko miye kafadi mani,yadda nadauki Hanan haka nadauke ka har cikin zuciyata wlhy"
Tabbas yanada magana kuma yanajin kunya kamar yadda daddy yadauke bai dace ace yakawo mani uzuri ba amma dole ne yafadi kuma yanemi alfarma.
Yaya Rafeeq yace"dama daddy ina neman alfarma adan qaramin lokaci sbd wata hidima data taso mani"
Daddy yyi murmushi yace"dama akan wannan ne,ae bbu komae,kuma aduk lokacin da kke buqatar wani abu,kasanar da ni plz"
Yaya Rafeeq yyi godia sosae.
Hanan ce tashigo sanye da wanibmatsatstsen jeans da yar body hug takamata sosae,gashinta bbu ko hula tadaure shi da ribom a guri daya tamaida jelar baya,hannunta dauke da qaramin tray da lemon kwali da ruwan roba asama sae glass cups.
Cikin sallama tashigo tadaura tray din abisa centre table,sannan tazauna bisa kujerar da daddy yake zaune tayi mashi sannu da hutawa.
Daddy ya'ansa cikin sakin fuska sannan yace"Hanan bakiga yayanki yazo ba?"
Hanan tayi murmushi tasa tafin hannunta tarufe fuskarta tace"yaya Rafeeq sannu da zuwa"
Daddy yace"ae kema kinsan baki kyauta,ni bari naje inyi wanka tafin kugaisa"
Yatashi yafita.
Yana fita Hanan tadawo kujerar da ke kusa da Rafeeq tazauna,tana kollonshi amma shi tv yake kallo.
Cikin sanyin murya tace"yaya Rafeeq mi yasa bakason kallona,bakason kulani?"
Yyi kamar baijita ba saeda tasake maimaitawa karo na biyu,agajerce yace"laifin kine ae"
Da sauri tace"laifina kuma nami?,kafadamin wlhy zan gyara"
Yaya Rafeeq yace"ranar nan wa kika yima rashin kunya awaya?"
Hanan tace"wlhy dagayau nabari yaya Rafeeq,i'll not do it again"
Yamiqe tsaye sannan yace"matsalar ki ce Hanan"
Mummy tashigo sukayi sallama sannan yatafi gida.
Ahaka hutunsu yaqare suka koma school,daddy yyima Abba bayani sosae gameda zancen sa rana,Abba baiyima Rafeeq fada sosae ba haka suka haquri.
Wannan lokacin ma Alh.kabar shi yyima Zuhra koma da kudin da gwamnati taturo.
Bayan satu daya da komawarsu aka gama shirye2,angyara hall din sosae anyi decoration yyi kyau,ga baki daga wurare da dama mai girma provost tagayyato,sbd a foculty of science ba'a taba samun wanda yasamu point kamar hakaba.
Hall din cike da mayan yan siyasa da yan kusawa da professors da dai sauransu da kuma students gurinsu daban,su Dr. Rafeeq sune gaba gaba,su Islam da Iman ma sun halarci wurin da Zuhra tace bazata samu zuwaba,saeda su Islam suka matsa mata.
Aka gabatar da komae sannan aka fadi dalibar nada 4.89 point,kowa mamaki yake abinda ba'a taba samu ba.
Students da dama nata addu'ar Allah yasa ni ne.
Mai gabatarwa yace ba kowa bace overoller illa ZUHRA UMAR FAROUQ................
*Miss j*
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
```May ur adorable soul rest on perfect peace my lovely mum,i really missing u🙏🏻🙏🏻🙏🏻...```
*60-65*
Zuhra ji tayi gabanta na faduwa sbd bata ta6a tinanin sunanta za'a kira ba,kuma basu anshi result dinsu ba barema taga abinda taci.
Sae ta6i ketashi acikin hall din,kowa ya qosa yaga wannan jarumar.
Sae aka kira sunanta sau ukku,amma takasa tashi,su Islam sae fama suke da ita tatashi amma taqi.
Saeda suka matsa mata sannan tatashi tsaye amma takasa matsawa daga inda take
Yaya Rafeeq da yaga bata fito ba,ya miqe tsaye,yana yan dube2 can nesa da shi,yahango tayi tsaye,yana hada ido da ita yyi mata alama da tafito,ahankalin take tafiya har tahau kan step din dakin taron.
Jikinta sae shavering yake gashi yau bata liqab dinta ba,students,lecturers da baqi sai faman kallonta suke.
Hanan dake kusa da Dr. Rafeeq tini ranta yagama 6aci,bataso wawiyar yarinyar nan ce tasamu wa'annan kyautittikan ba,gashi taga Rafeeq ya tattara hankalinshi yamaida kanta.
Mai gabatarwa yaba Zuhra damar gabatar da kanta da irin farin cikin da take ciki acikin harshen turanci.
Hanan tanemi alfarma wurin mai gabatarwa akan yabata lokaci zataji Zuhra tambayoyi,da yake abin nasune bbu wani bata lokaci tafita gaban mutane tashiga jeroma Zuhra tambayoyi.
Cikin ikon Allah Zuhra bbu tambayar da bata ansaba,Hanan taqajin haushi sbd dama tayine dan taqure Zuhra(ni Miss j nace"hassada ga mai rabo taki ce).
Hanan takoma tazauna rae bbu dadi,Zuhra taburge mutane da dama,hatta provost dake cikin dakin taron saeda taji Zuhra tabirgeta.
Yan siyasa da masu fada aji,suka farayi mata kyaututyuka,cheque din kudade Zuhra tasamesu sosae.
Zuhra batada kowa a wurin yaya Rafeeq shiya zame mata tamkar yaya awurin,Hanan sbd takaici ba'a tashi taron da itaba.
Islam da Iman sunyi farin ciki sosae,kamar sune suka samu wa'annan kyaututtikan.
A.B.U tacika da labarin Zuhra Umar Farouq,maza da mata hada lecturers,dole Zuhra takoma saka liqab dinta sbd students da dama sukan tareta da sunan sanon yin friending da ita wasu ma cewa suke suna sonta.
Bayan kwana biyu dayin taron,akaba su Zuhra result dinsu,Islam da Iman suma sunyi koqari saedae basu kai Zuhra ba.
Suka tafi office din yaya Rafeeq domin su nuna masa,cikin sallama suka shiga,kamar kullum saeda yabasu umarni sannan suka shiga.
Aunty Hanan ce zaune bisa kujera,tana neman yimashi rashin kunya akan maganar da sukayi da daddy akan adaga sa ranar aurensu.
Tinda taga Zuhra ranta yaqara baci,sae yan harare2 takeyi,Zuhra kanta aqasa,Islam da Iman suka gaishe da shi cikin harshen turanci kamar yadda suka saba,sannan suka gaishe da Aunty Hanan.
Zuhra tagaishe da Dr. Rafeeq amma da mamaki bai ansaba,ranshi 6ace yace"ina liqab dinki?"
Zuhra bakinta na rawa tace"gayanan cikin shoulder bag dina"
Yaya Rafeeq yace"daukoshi kisaka"
Yadda ya daure fuska kamar bashi yyi maganar ba,Zuhra tafiddo liqab dinta tasaka.
Kallon tuhuma Hanan takeyima shi,tafin tace"me ye business dinka da saka liqabinta Dr. Rafeeq?"
Dr. Rafeeq yaqara daure fuksa gami da yimata wani kallon raini yace"nasaka da ke ne?"
Ganin maganar zatayi tsawo yasa bata qara magana ba,Islam da Iman suka fiddo results dinsu suka bashi yaduba,ya yaba masu sosae,sannan sukaba Aunty Hanan tagani.
Zuhra tamiqa mashi nata,yaduba tare da qara yaba mata,da Islam tamiqama Aunty Hanan result din Zuhra,tsoki tayi tare da hararar mai result din.
Su Islam sukayi mata sallama suka tafi hostel.
Ranar wata thursday Islam da Iman da Zuhra sukaje gidan yaya Rafeeq dake staff quaters.
Suka tarar da shi,bisa machine dinnan na motsa jiki,vesy ce da three quarter a jikinshi,vest din tajiqe da zufa harcikin gashin kanshi da fuskarshi.
Yana ganinsu yasauka suka gaisa,yashiga bedroom dinshi domin yawatsa ruwa.
Bayan kamar 15mins sukaji tsayawar mota a harabar gidan,ba'afi 5mins ba,Aunty Hanan tashigo,taci ado kamar zata occation,sanye take cikin wata doguwar riga ta alfarma tayi rolling da qaramin gyale sai kamshi take.
Bayan su Islam sungaishe da ita,ta tambayesu ina Dr. Rafeeq yake?,Iman tafada mata.
Lokacin data shiga har ya shirya nasaka kaya.
Kamar daga sama yaganta gabanshi,bbu ko sallama.
Yace"ke wace irin wawiyar yarinyace zaki shigimin bedroom bbu ko sallama?"
Cikin tsiwa tace"ba wannan tambayar nakeso kayiminba,wae miye tsakaninka da waccen karuwar yarinyar?"
Dr. Rafeeq ranshi yaqara baci yace"wlhy idan bakinki yaqara furta mata irin wannan kalmar sae nabaki mamaki"
Hanan tayi irin murmushinnan narainin wayau tace"wane mamaki zakabani bayan wanda kake bani yame da waccen mayyar....."
Kafin taqarasa maganar,tini yatsinka mata wani wawan mari.
Yace"tou bari kiji sonta nake,kuma itace matar da zan aura"
Hanan ji tayi kamar saukar aradu,ga mari ga tsinka jaka.
Tadafe fuska bakinta na rawa tace"ni kamara?,tou wlhy zaka gani,kuma saina rama"
Afusace ta'isa porlour kai tsaye wurin Zuhra tanufa,tafara tsinka mata mari,saeda tayi sau hudu,tana niyar qarama mata,cikin zafin nama yariqe mata hannu...........
*Miss j* 🙋🏻😘
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY &WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*65-70*
Yariqe mata hannu tare da ingiza gefe daya,ya nunata da yatsa,cikin kakkausar murya yace"ashe ke qaramar marar kunyace,ae nayi tinanin da kikace zaki rama,akaina din zaki rama,sbd fita kibarmin gidana"
Aunty hanan takalleshi tayi wani murmushin takaici sannan tanuna Zuhra da yatsa tace"zaki sani"tafi daga gidan afusace.
Zuhra batasan lokacin da tafashe kuka ba,ba itaba hatta hankalinsu Islam da Iman yatashi.
Islam da Iman suka fara yima Dr. Rafeeq kallon tuhuma,sunaso su tambayeshi me ke faruwa,amma yadda yanayin fuskarshi yake,sunajin tsoro.
Yaya Rafeeq yaqaraso inda Zuhra take zaune,ya sunkuyar da fuskarshi saetin fuskarta,ahankali yake magana cikin muryar lallashi.
Yace"i'm sry Zuhra,insha Allah bazan taba barin haka tafaro da keba"
Cikin muryar kuka Zuhra tace"plz yaya Rafeeq,kafadamin me ke faruwa,ni wlhy bbu abinda nayi mata,idan kuma wani laifin nayi mata wlhy bansan na'aikata ba,ina mai bata haquri akan ta sausauta tsanar da tayimin"
Yaya Rafeeq yadaura yatsanshi bisa lips dinshi,alamar tayi shiru yace"bbu wani laifin da kika aikata mata Zuhra"
Islam tace"yaya Rafeeq me ke faruwa ne?"
Yace"bbu komae,ku kwantar da hankalin ku"
Iman tace"yaya Rafeeq mi kayima Aunty hanan?"
Harararta yyi sannan yace"bita kitambayeta mana"
Ya juya wurin Zuhra yace"gobe insha Allah,zanje kano kuma zambiya inba su Baba cheque din da kika samu kuma inyi masu bayani"
Zuhra tashare hawayenta tace"nagode,Allah yasaka da alkairi"
Islam tace"yaya Rafeeq mu zamu tafi hotel"
Yace"ok,amma inaso kuyimin rakiya,Zuhra kishiga ciki,ki wanke fuskarki"
Bayan tagyara fuskarta,yadaukesu cikin mota suka fita,bbu inda suka tsaya sae garin kaduna,shoprite yakaisu kowace tazabi abinda takeso,yabiya,sannan yamaido su bakin hostel.
Aunty hanan tana fita bbu inda tazarce sae gidan wata qawarta mai suna,Khubra,tasan idan tatari Mummy da wannan zancen bbu abinda zatayi sbd mutuncin dake tsakaninta da Mami.
Aunty hanan tafadima Kubra duk abinda yafaru,Khubra tayi ashariya tace"hmm,lallai kura tayi lfy,Hanan duk kina ina kika bari wannan yarinyar tasace maki zuciyar wanda kikafi so?"
Hanan tace"hmm,Khubra kenan,kinfasan irin taurin kae na yaya Rafeeq"
Khubra tayi tsoki tace"amma wlhy kinbani kunya Hanan,duk irin kyau da Allah yyi maki ace cikin shekaru 13 kinkasa mallakarshi,kitina tin muna primary kike sonsa,ina gayunki na turkishi college yake?,har wata tazo tasace zuciyar sa"
Hanan tayi murmushi tare da share wasu zafafan hawaye da suka zuboma tace"ya za'ayi namallake shi,mutumin da dayaganni sae yabata rae,Khubra Allah yatsinema so,so bala'ine,Allah yajarabceni da son mutumin da yafi qarfin hankalina da tinanina"
Khubra tayi murmushi irin na yan bariki tace"ki kwantar da hankalin ki zan sakaki ahanya,yanzu kisan yadda kikayi zuwa gobe kisamo address din gidansu da unguwarsu da safe saemu fasa kawae"
Hanan tayi murmushi jin dadi tace"har naji sanyi wlhy,shiyasa nake sonki,kuma nazo wurinki,sbd nasan zaki daurani ahanya,ni yanzu bari intashi intafi,sbd yau Mumny zatabar kasar,zata samu kamar sati ukku bata dawoba"
Khubra tace"ywwa kinga zamuyi yadda mukeso kenan,tarko ne kala2 zamu hada mata saetaji dama batazo duniya ba"
Da haka sukayi sallama Hanan tatafi tanajin ddi.
Washe gari tinda safe Hanan tashirya tatafi cikin makaranta,deparyment dinsu Zuhra tanufa,lokacin lecturers basu zoba sae massengers,haka Hanan tashiga tasa massenger yagano mata file din Zuhra Umar Farouq,anan Hanan tasamu address din gidansu,takuma gano ashe gwamnati take daukar karantun Zuhra,Hanan tayi murmushin mugunta