Author : Jamila Samaila Yusuf Category : Romantic Hausa Novels
sannan tatafi.
Tadauki motarta bbu inda tsaya sae gidan Khubra,cikin shiri tatarar da ita,suka kama hanya zuwa kano.
Lokacin da suka isa unguwarsu Zuhra,suka tsaya suna tambayar wani yaro gidansu Zuhra,suna cikin magana da yaron saega mlm umar yafito daga gida bisa dan kekensa,yaron yanuna mlm umar yace yawwa ga Babanta can yafito daga gidan can ne gidansu,suka sallami yaron.
Khubra tayi murmushi tace"munxo asa'a kenan,muje kibigeshi da mota"
Hanan taja mota da gudu,suka isa inda mlm umar yake sannan Hanan tayi mashi wata muguwar banka.............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
```I luv my fans😘😘😘...```
*70-75*
Mlm umar yafadi ko motsawa baiyi ba,wata matace tarugo aguje tayo wajenshi tare da kiran taimako amma kuma cikin rashin sa'a unguwar bbu mutane sosae kasancewar safiya ce,yaron da su Hanan sukayima tambaya shima yarugo.
Matar tace yaron Ali ruga gida kafadima maman Zuhra idan bata tafi gidan wanke2 ba.
Yaron yatashi aguje tatafi,duk abinnan da ake su Khubra na cikin mota sinqi fitowa.
Hanan tayi tsoki tace"ashema uwarta yar wanke2 ce"
Khubra tace"tada motar mutafi tinda munui abinda yakawo mu"
Hanan tatada mota suka tafi,suna taji dadi.
A zaria road wajen flyover Dr. Rafeeq yaga kamar Hanan acikin mota,tana ta tafi itada wata suna dariya,sae kuma yyi tinanin me zatayi kano acikin safiyar nan.
Yaya Rafeeq yyita sauri sbd yasamu Baba agida kada yamakara ace yatafi kasuwa.
Yaya Rafeeq yana shiga unguwar yaga taron mutane sunyi cirko2 awaje,kuma shidae baiga abin kallo ba.
Yaje kofar gidan yyi parking din motarshi,yafara qoqarin kiran wani yaro yayi mashi sallma da Baba.
Nan yaron ke fada mashi ae Baba Ummaru,yanzu aka tafi kaishi asibiti.
Yaya Rafeeq gabanshi yafadi yace"dama baida lfy ne?"
Yaron yace"a'ah,hadari sukayi yanzu,shida wasu masu mota"
Yaya Rafeeq hankalinshi yaqara tashi yace"tou nagode"
Dr. Rafeeq yamatsa kusa da wani matashin yaro yatambayeshi ko yasan asitibitin da aka kai Baba,matashin nan yafadi mashi,Dr. Rafeeq yashiga mota yabi bayansu.
Lokacin da ya'isa asibiti har ankaishi emergency ana neman jini,anan yahadu da Mama,tare da shi akayi komae yyi paying.
Zuhra tinda gari yawaye takejin jikinta bbu ddi,tana cikin damuwa,hatta Islam da Iman sun fahimci hakan,koda suka tambayeta mike damunta,tace wlhy itama bata sani ba.
Hakan suka tafi lecture,da yake lecture din Aunty Hanan ce,kafin lokacin yyi harsun isa venue sbd tana iya hana Zuhra shiga.
Lokacin da suka isa venue din bbu kowa sune farkon zuwa,suka fiddo textbook dinsu suka fara dubawa.
Bayan 1hr students suka taru a venue,yar mulkin saeda taqara 45mins sannan tashiga lecture hall din.
Tinda Aunty Hanan tashigo Zuhra tattara hankalinta tamaida gaban whiteboard din venue din.
Hankalin Aunty Hana yana wurin Zuhra jira kawae take taga tayi wani qaramin laifi taci mata zarafi.
Aunty Hanan dataga Zuhra batada niyyar yimata laifi,saeta qara daure fuska tasata tatashi tsaye agaban jama'a.
Aunty Hanan tagyara tsayuwa tace"ke baqauyiya yinanin me kike?"
Hankalin kowa yakoma kan Zuhra da aka kira da baqauyiya.
Islam da Iman hankalinsu yaqara tashi dama tinda safe da sukaga Zuhra cikin damuwa suma duk hankalinsu atashe yake.
Hanan tagyara tsayuwa taci gaba da cewa"ko kina tinanin gidan mazan da kikaje kika kwana jiyane?,amma dae wlhy kinci amanar gwamnati tayi maki abinda iyayenki suka kasa yi maki,sbd tadauki nauyin karatunki,iyayenki suna gida suna wanke wanke a gidajen jama'a,amma ke kinanan kina bin maza,wlhy kinyi asara kuma kincuci gwamnati,kuma sannan hukumar makaranta takamaki da laifin son wani lecture wai shi Dr. Rafeeq kuma sannan kina bibiyarshi har gidanshi,tou bari kiji nan bada jimawaba asirinki tare da wannan cikin shegen da kike dauke da shi zaku tattara kibar makarantar nan tinda bata Ummaru mai wankin huluna bace,danhaka fita kibarmin aji,fasiqa kawae"
Zuhra jikinta na kerma har bata ganin gabanta bata samu ko damar daukar shaulderbag dinta ba tafita,Islam da Iman kuka kawae suke kamar ransu zae fita,wannan wane irin cin zarafi ne?,kodan taga iyayen Zuhra basu da kudine?.
Zuhra tinkafin tasamu nafef take kuka mutane sae kallonta suke wasu na tambayar kansu mi akayi mata?.
Dr. Rafeeq yyi duk abinda ake buqata sannan yaba Mama bandir din 500,koza'a buqaci wani abu,baibar asibitin ba saeda Abba yakiqashi da kanshi,dama shi yace yazo kano.
Dr. Rafeeq na zuwa gida yatarar da Abba,lokacin Mami na wurin aiki,Abba yace"maza kahada kayanka yanzu zaka tafi England,ma'aikatan kamfani na na takalma dake qasar nuna neman yimin asara,jiya anyi maka biza jirgin 1pm zaka bi,gashi yanzu har 12:15pm"
Yaya Rafeeq hankalinshi yaqara tashi yanaso yyima Abba maganar aikinshi amma baitaba yin musu da Abba ba.
Abba yafahimci abinda yake cikin zuciyar dan nashi,Abba yadafa kafadarshi yace"kada kadamu my son,munyi magana da Haj.fatima(provost) kuma tace bbu damuwa"
Ba wannan ne kawae damuwar Dr.Rafeeq,yana tinanin halin da Baba yake ciki sannan ga kuma Zuhra.
Bbu yadda ya'iya dole yahaqa kayanshi,ko sallama baisamu yyi da Mami ba bare kuma su mlm Umar da baisan inda kanshi yakeba ,driver yakaishi airport jirginsu yadaga.
Daga ranar Zuhra bata qara shiga lecture din Aunty Hanan ba,makaranta kuma wata surutun Zuhra yatsaya kowa yasan labarin yarinya mai qoqari wadda tabata wayonta,har takae Zuhra bata fita saeda liqab dinta.
Kwana biyu da su Islam da Iman sukayi waya da Mami take fadi masu Rafeeq yyi tafiya zuwa England.
Da Hanan taga kwana biyu tarabu da ganin Dr. Rafeeq,tadauki hanya zuwa kano,koda take gidansu Mami ke fadi mata yyi tafiya.
Haka tataho tana murna bbu inda tawuce sae gidan qawarta Khubra,ga dama tasamu suka fara tinanin tuggun da zasu hada mata wanda za'a koreta daga makarantar.........
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*75-80*
Khubra yar jihar Niger ce,lokacin da Hanan tayi first degree dinta a ABU,suka hadu,Khubra tayi ciki ne aka koreta daga school da taje gida iyayenta suka koreta,tadawo zaria da zama tana dan taba barikinta.
Tinsuna makaranta Khubra tari tasan Hanan bata kula namiji,sbd son da takema Dr. Rafeeq,amma iyayen Hanan basusan tana tare da Khubra ba.
Khubra tayi murmushi wanda ita daya tasan mi take nufi tace"Hanan wae ke bazaki iya rabuwa da Dr. Rafeeq dinnan ba,ki shigo cikin harkarmu,yadda Allah yyimaki irin wannan kyau,namiji sae wanda kika za6a"
Hanan tayi murmushi tace"Khubra banajin zan iya hada rayuwana da wani da namiji ba yaya Rafeeq ba,shi daya nakeso akanshi nakoyi so,kuma nasan so,kema ina yi maki addu'a da kiyi aure,Khubra zakifi kyau a dakin mijinki....."
Khubra tabata rae tace"dakata Hanan,ba wa'azi zaki yimin ba,nasan komae akan rayuwa da kuma abinda yadace dani,inaso inba iyayena mamaki,nayi alqawarin da sae nakai masu abinda basuso a gida"
Hanan tace"Khubra kada kiyi haka plz kidawo cikin hankalinki"
Khubra ranta ya baci sosae tace"kinga Hanan,ya'isa haka,yanzu aikin da yarage nakine akan Zuhra"
Hanan tace"kinga ni sae anjima,tinda baki daukar shawara"
Hanan tafita afusace bbu ko sallama.
Bayan sati daya da rabuwar Hanan da Khubra,Zuhra sundawo daga lecture,wata yar kusa da room dinsu,take fada masu anliqa sunan Zuhra Umar Faruoq a notice board.
Sunyi mamaki sosae sannan suka rakata har departmemt dinsu,bayan yan mintina Zuhra tafito tana kuka kamar ranta zae fita.
Iman da Islam suka rude dama kuma basu iya shiga tashin hankali ba duk saesu rude.
Islam tace"Zuhra lfy?,me ke faruwa?"
Zuhra tamiqama Islam takardar da ke hannunta,Islam na dubawa tafashe da kuka,tafara salati.
Iman ta'anshi takardar taduba ranta bace tace"wlhy qaryane,wannan sharrine"
Iman taja hannunsu suka shiga Hostel,ranar haka suka kwana kuka,Zuhra data tina abinda aka rubuta cikin takardar wae ankoreta tana dauke da ciki,sae taji kamar tayi hauka.
Washe gari tinda safe,Zuhra tayi parkin ita gida zata tafi,Islam da Iman sukace suma bazasu tsayana gida zasu tafi.
Bbu yadda Zuhra batayiba da su tsaya suyi karatunsu,Islam tace"Zuhra duk abinda yasameki yasamemu,wlhy ji nake kamar yar uwata akayima wannan sharrin kuma ba laifin kowa bane laifin Mummy(provost)ne takasa zama cikin makaranta yaubata wannan kasa gobe bata caccan kasa"
Zuhra tace"a'ah ba haka bane Islam,anyimin hakane sbd ana ganin iyayena basu da komae......"kuka mae bantausayi taci gaba da yi.
Ranar cikinsu bbu wanda yakwana cikin makaranta,Islam tayi masu shatar mota,aka kai kowa qofar gida.
Zuhra tana shiga gida ta tarar da bbu kowa agidan,ta ajiye kayanta,tasamu wuri tazauna tana tinanin abin duniya,tarasa me ke damunta yunwa takeji ko mi,tajima da dawowa bbu wanda yadawo tayi tinanin Mama tana gidan chairman,Baba na kasuwa,gashi bbu credit a wayarta bare takira.
Wayarta tafara ringing,tana dubawa taga sabuwar number,Zuhra tashare wasu zafafan hawaye da suka zubo mata tare da daukar wayar takara a kunne.
Dariya taji anyi sannan akace da Mrs Rafeeq kke magana,wato Hanan Lawal Umar,na kiraki ne domin in sheda maki wannan shine warning na qarshe da zanyi maki akan mijina,wlhy akanshi zan iya yin komae,kinga yanxu kin rasa karatunki a banxa,yanxu sae aje asibiti ayi jinyar mai dattin hula,taja dogon tsoki takashe wayarta.
Zuhra da tazama kamar gunki,ji take kamar zuciyarta zata buga sbd tashin hankali,yanzu nan Hanan ce keda hannu cikin korarta tare da itama mafificin qazafi,duk a dalilin yaya Rafeeq.
Tana zargin yana sona ne?,kamar yaya Rafeeq me zaiyi da ni,aiko yace yana sona bazan yarda ba,anyimin qazamin sharri an cimin mutunci cikin taron jama'a duk sbd kae.
Kamar an tsikareta tamiqe tsaya sakamokon tina kalmar da Hanan tafadi,to ko da gaske Baba yana asibiti ne?.
Zumbir tamiqe dama ko hijabin jikinta bata cireba,tashiga maqwabta,anan ake sheda mata ae wasu yammata ne sukazo neman gidanku sannan suka tureshi cikin ganganci sannan basuko kalli inda yake ba,suka tada motarsu suka tafi.
Zuhra tatambayi asibitin da aka kaishi,hankalinta tashe kamar mahaukaciya tanufi asibitin...........
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*80-85*
Nafef tashiga amma gani take kamar ba tafiya yakeyi ba,ahaka suka shiga asibiti.
Zuhra tatambayi room number din da Baba yake dama kuma amfada mata.
Tana shiga room din,tatarar da Baba kwance bisa gado,da alama barchi yake.
Bbu kowa dakin sae shidaya amma da alama akwai mutum cikin toilet din dake cikin room din.
Zuhra ko zama bata samu tayiba,sae faman kuka take,yanxu nan Hanan ce sanadiyyar kwanciyar Baba asibiti.
Mama ce tafito daga toilet cikin tashin hankali take kallon Zuhra,sakamakon idanuwanta da suka kunbura fuskarta tayi jajir sbd tsabar kuka abu ga farar fata.
Mama taqarasa kusada Zuhra takama hannumta tare da zaunar da ita bisa kujera,mama tazauna gefen gado,tana fuskantar Zuhra.
Cikin muryar lallashi Mama tace"haba Zuhra,wannan kukan ai yyi yawa,kuma ae yasamu sauki tinda har likita yyi maganar sallamarmu"
Mama tasa hannu tashare mata hawayenta tace"shiyasa naqi sanar da ke,sbd nasan halin da zaki shiga,gashi yanxu duk kamarki tasauya,yaron kirkin nan yasanar da ke ko?"
Zuhra tace"Mama waye yaron kirki?"
Mama tace"yayan su Islam mana"
Gaban Zuhra saeda yafadi sakamokon sunanshi da Mama ke qoqarin fadi wasu zafafan hawaye suka qara zubo mata.
Mama tace"hmm,ae nasan shine zae sanar da ke,sbd wurinshi kawae zakiji,ae yaron kirkine kuma yana da tausayi,kinga komae na asibitin nan shine yyi sannan yabani kudi masu yawa,wae idan wata hidima tataso"
Hankalin Zuhra yaqara tashi tana tinanin me yasa yaya Rafeeq yake yima iyayenta hidima,tana tsoron Aunty Hanan tasani.
Babane yafarka daga barchi,da taga jikinshi da sauki sae hankalinta yadan kwanta.
Shima dayaga halin da Zuhra take ciki saeya fara lallabarta yana cewa haba Zuhra abinda nasamu sauqi sosae,kiyi haquri kibar kuka.
Mama ce tahada mata tea,cikin kayan da aka sawoma Baba,saeda Mama ta lallabeta sannan tasha.
Islam da Iman suna isa gida,lokacin Mami tana wurin aiki,Abba kuma bayanan.
Bbu kowa gidan sae masu aiki,ma aikata suka shiga jera masu abinda da lemuka kala kala,amma bbu wani abin kirki da sukaci,ko wace jikinta bbu kwari.
Bayan sunyi wanka sunshirya,suka fara neman layin Zuhra,cikin rashin sa'a tana shiga amma ba'a dauka,tamance wayar a gida,sukayita kira har sauran charge din dake wayar yaqare dama bbu wani charge sosae.
Da suka riqa sukaji akashe dole suka haqura.
Da marece Mami na dawowa,tacika da mamaki sakamokon ganin su Islam da tayi,Mami bayan singaisa Mami tace"wannan wane irin weekend ne yau tuesday?"
Islam tace"Mami ba weekend muka zoba,dawowa gida mukayi"
Mami tace"wat?,ban fahimci me kuke nufi ba"
Iman ta kwashe labarin sharrin da akayima Zuhra tafadima Mami.
Mami tashiga rudani tana tinanin,wannan wani irin abune mutum baiyi laifiba za'ace yyi ne.
Mami tace"yanzu ku kuna ganin sharri aka yimata?"
Su Islam suka fara rantsuwa akan sharri akayima Zuhra.
Mami tace"yanzu kuzo kuhada kayanku,ku koma shool sbd idan Abbanku yadawo bazaku kwashe da kyau ba,ba kuba harni abin saiya shafeni"
Islam da Iman suka fara kuka,Mami tashiga lallabarsu tace idan Haj. Fateema(provost)tadawo zasuyi bincike.
Sunsan halin Abba sose dole suka hada kayansu driver yamaidasu school badan ransu yaso ba.
Mami tashiga rudanu game da lamarin Zuhra,sbd itadae yarinyar takwanta mata arae.
HAnan ce taje tahada baki da vice provost akan zata bashi maqudan kudi tare da duk lokacin da yake neman alfarma wurin Mummy insha Allah zatayi yadda zatayi yasamu abinda yake buqata,dasa hannunshi akayima Zuhra sharri aka koreta.
Haka Zuhra tariqa jerangiya asibiti tana kwana gidan maqabtansu,Mama takwana asibitin,har aka sallamesu asibiti,ita tamance da wata waya,kuma su Islam sae nemanta suke.
Hanan tazo gidansu yaya Rafeeq ta tarar da Abba da Mami aporlour tafara kukan munafinci,anan tasheda ma su Abba cewa,yaya Rafeeq yana wulaqanta ta,wae yanzu kuma wata yarinya yakeso wadda ak kora amakaranta sakamokon tana dauke da ciki.
Ran Abba yabaci sosae,yace idan har ni nahaifeshi tou zai yawo mamu marar tarbiya acikin zuri'armu ba,bari yadawo dani yake magana,nizai mayar mutumin banza.
Haka Abba yaci gaba da fadanshi,Mami talallabi Hanan tayi shiru,tagama yininta sannan tatafi gida.
Bayan sati daya da sallamo Baba asibiti jikinshi yadawo normal,Baba yace"yakamata Zuhra takoma makaranta tinda yasamu lfy"
Mama tace"Zuhra maganar mahaifinki gsky ne,yakamata ki koma kada ayi abubuwa bakinan"
Zuhra tafara sabon kuka tana tinanin maganar da zata fadima iyayenta,saeda sukayi kamar zasu daketa sannan tafadi masu,korarta akayi amma wlhy qarya ake mata.
Hankalin kowa yatashi Baba baiyi maganaba ya umarceta da tadauko hijabinta sutafi asibiti,saeda sukaje likita yatabbatar mashi da bata dauke da ciki sannan yadan samu sauki.
Suna dawowa gida Baba yatashi gidan Alh. Kabir domin yasheda mashi matsalar da tataso,amma Alh. Kabir yashema ma Baba ce ae tin satin da yawuce aka sanar da gwamnati laifin da ta'aikata yanzu haka tafidda hannunta akan karatun Zuhra,dan haka mlm Umar kada nasake ganinka a kofar gidana,hatta matarka da takeyin mana wanke wanke na haramta mata shiga gidana daga yau.
Haka Baba yadawo jiki bbu qwari,bayan kwana hudu da faruwar haka Zuhra ta ida zuzucewa tafita hayyacin tabi tarame sbd damuwa.
Satin Dr. Rafeeq ukku a England yadawo gida Nigeria,cikin sa'a yakwantar da rigimar da akeyi akamfanin..............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:21] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
```Ina miqa godia agareku masoyana,ina ganin comment dinku kuma yana qara encouraging dina,ina qaunar ku lodi lodi😘....```
*85-90*
Dr. Rafeeq yadawo gida cike da son ganin abubuwa da dama,family dinshi sunyi farin cikin dawowarshi sosae.
Da marece lokacin yyi wanka yaci abinci,yashirya da nufin yaje gidansu Zuhra,yagaishe da su Baba daganan yabasu kyaituttukan da Zuhra tasamu.
Dr. Rafeeq yaje yatarar da Mami a porlour yasheda mata cewa zai fita.
Mami tace"inason magana da kae idan kadawo,kadin mahaifinku yadawo"
Dr. Rafeeq yace"ok,ae bazan jima sosae ba"
Sukayi sallama da Mami yafita.
Danqareriyar motarshi yashiga kirar RANGE ROVER 2017,omo colour,yanayin shigar da yyi tayi mashi kyau sosae,bbu inda yatsaya sae kofar gidansu Zuhra.
Yasa akayi mashi sallama da Baba,cikin sa'a lokacin mlm Umar yadawo gida cin abincin rana.
Baba na fita yaga yaya Rafeeq,yaji dadin ganinshi sosae kuma dama yanason yi mashi godia akan abin arziqin da yyi masu.
Baba ya'umarceshi da sushiga ciki.
Tinda Zuhra taji tsayuwar mota aqofar gidansu,ranta yabata yaya Rafeeq ne,dan haka bbu shiri takoma cikin daki da sauri tasan Baba cewa zaiyi yashigo cikin gida.
Suna shigo cikin gidan Baba yakirani inkawo masu tabarma,ji nayi dama ace bana gidan sbd banason ganinshi yanzu.
Bbu yadda tana iya dole nasaka hijabina tare da daukar tabarma nafi nafito.
Tinda tafita yake kallonta,kamar bae ta6a ganinta ba,wani dadi yakeji aranshi sakamokon ganinta amma yyi mamakin ganinta a gida.
Kamshi tirarenshi yabi yacika mana gida,har ji nake gabana na faduwa sbd gani nake kamar Aunty Hanan na biye da shi abaya,kada taga yazo gidammu tace kuma wurina yazo.
Bayan nagama shinfida tabarma na gaishe da shi sannan nashiga daki,nayi quri kamar munafika gashi kuma Mama tashiga maqobta dubiya.
Yaya Rafeeq yashiga yima Babana bayanin abinda nasamu da yawan kudin,Babana yyi mamaki sosae,sannan yyima yaya Rafeeq godia.
Banajin abinda suke tattaunawa sosae sbd ba akusa da dakin suke ba,sae yanzu natina banba yaya Rafeeq ruwaba,yashi banida kudi hannuna,sae natina da wata naira ishirin da Mama ta'ajiye,nayi tinanin kuma ae bazai iya shan pure water ba,shida keshan ruwan roba,nakoma nayi zamana.
Bayan wasu mintina naji Baba yana kirana,na'ansa tare da tashi nafito.
Bayan na durkusa nace Baba gani.
Baba yace"kuma Zuhra ba'a kawoma baqon ko ruwa?"
Shidae baice komae ba,natashi nadauki naira ishirin dinnan nafita.
Naje nasawo awani gida kusa da namu,nadurqusa na'ajiye bakar ledar purewater agabanshi,sae naji yace min sannu da qoqari.
Bansan lokacin da nadago fuskata nakalleshi ba,gabana saeda yaqara faduwa karo na biyu sbd wani asirtaccen haske da idanuwanshi suka qara,gaba daya yaqara wani haske fatar jikinshi taqara murjewa tayi fresh,sajen fuskarshi dake qara mashi kyau da gashin kanshi sunqara baki sae shining suke,daqer nasamu tinanin na yadawo natashi jiki bbu qwari nashiga daki dan ko sannunshi ban ansaba.
Yyi awa daya agidan duk nabi natakura nakosa yatafi,
Bayan sunyi sallama da Baba yatafi,Baba ya'umarceni da infita inkira Mama gidan da taje dubiya,nasaka hijabina nafita.
Cikin mamaki inafita naga mutum zaune acikin mota,yana ganina yabude mota yafito,naqara inda yake dan nasan ganina yasa yafito.
Yaya Rafeeq yace"inganni har yanzu bantafiba ko?,dama ke nake jira Zuhra"
Zuhra taware ido cikin tsoro tace"yaya Rafeeq lfy dae ko?"
Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"matsoraciya lfy qalau,weekend kika dawo kika baro qawayen naki?"
Zuhra tagirgiza kae hawaye suka zubo daga cikin odanuwanta tace"a'ah,ba weekend nadawoba"
Kallon tuhuma yake mata kafin yace"lfy?,me ke faruwa ne?"
Cikin muryar kuka tace"dama...,ankoroni ne"
Cikin muryar mamaki yace"wat?,kamar ya ankore ki?,laifin me kikayi ne?"
Zuhra taci gaba da kuka tace"wae ance inadauke da cikine"kukanta yaqaru.
Yaya Rafeeq arazane yamaimaita abinda tafada.
Zuhra tace"wlhy yaya Rafeeq ba gaskiya bane,bani dauke da ciki wlhy"
Hankalinshi yatashi qarara zufa tafara keto mashi,idanuwanshi suka koma kamar yaji,yace"Zuhra nasan bazaki iyaka kai kanki ba wlhy,fadamin raping dinki akayi ne?,waye ya yaudare ki?"
Hankalin Zuhra yaqara tashi ga tsorota da tayi sakamokon yanayinshi daya sauya,cikin tsoro take magana tace"wlhy yaya Rafeeq ni ba yar iska bace,wlhy sharri akayi min"
Wa yyi maki qazafi Zuhra? tambayar da yyi mata kenan.
Zuhra bakinta na rawa sbd ita har bayan idon Aunty Hanan tsoronta takeji,tace"Aunty Hanan ce,wae tana zargin kana sona,ita takirani tafadamin itace tayimin haka sbd kae"
Taci gaba da kuka.
Ranshi abace yace"dama na zargi Hanan,Zuhra maganar Hanan ba wasa bane"
Zuhra taci gaba da kuk tayi tinanin yana nufin yayard tanada cikin.
Yaci gaba da cewa"tasan yadda nake sonki kau?,Zuhra ina sonki, ina qaunarki"
Zuhra batasan lokacin da tayi shiruba,cikin tsoro tafara ja da baya,saeda tajin jingina da bangon gidansu.
Da taga yana qoqarin matsowa kusa da ita,da gudu tashiga gida,tana kuka.
Ranshi yabaci sosae abinda Hanan tayima Zuhra,ga Zuhra