Author : Jamila Samaila Yusuf Category : Romantic Hausa Novels
bata ta6a tinanin ya'iya dariya kamar haka ba.
Ahankali yatako inda kusa bed din shima yahau bisa yazauna kusa da ita yana kallonta.
Murya qasa2 yace"kin kusa taramin jama'a,ashe haka kike da tsoro"
Zuhra cikin zuciyarta tace kakusa samin hawan jini amma afili sae tashagwa6e fuska taci gaba da kuka.
Tini yarude yafara tambayarta,Zuhra lfy?,me ke damunki ne?,nine ko toyi haquri.
Yafara qoqarin goge mata hawayenta,ji sukayi ambanko qofa da sauri,gaba dayansu hankalinsu yakoma gurinta.
Hanan ce,atsaye fuskarta bbu alamar fara'a sae cika take tana batsewa.
Yaya Rafeeq yasauko daga bisa gado yataka har inda take tsaye.
Yace"lfy dae kika shigo mana bbu ko sallama?"
Hanan tace"yaya Rafeeq me kike anan?"
Ranshine yaqara 6aci yayi mata tsawa yace"ina tambayarki kina tambayana?,tou wurin matata nazo ko kinmanta da ita matata ce?"
Hanan tini hawaye suka fara zubo mata tace"ni kuma awane matsayi nake awurinka kenan?"
Yace"wannan kuma ansar na wurinki"
Hanan tayi murmushin takaici tace"tou shikenan nagode"tajuya tafita.
Zuhra bataji dadin abinda yyi ba dukda itama tanada laifi miye nashigo mani bedroom bbu ko sallama bare neman izini.
Zuhra tasauko daga bisa gadon takoma porlour tazauna,batare da tayi mashi magana ba.
Yaya Rafeeq yabita porlour yazauna kusa da ita yana fuskantar fuskarta yace"me kuma yafaru ne?"
Zuhra sanyaya tace"yaya Rafeeq abinda kayi bai daceba,dole Aunty Hanan zataji bbu ddi, amma dan Allah kayi haquri idan ranka ya6aci"
Yaya Rafeeq yace"kamar ya kenan?"
Zuhra tace"bawae ina nufin wani abu ba,amma yaya Rafeeq yakamata itama kaje part dinta kaduba halin da take ciki"
Yaya Rafeeq yatsaya yana kallonta,yarinya qarama amma tasan abinda yadace.
Yyi murmushi yace"ina jinki my wife"
Zuhra tace"kuma kaga itace babba part dinta yakamata kaje yau,dan Allah kaje kaga halin da take ciki yanzu naga ranta a6ace yake"
Yaya Rafeeq yace"tou shikenan,insha Allahu zanje yanzu,kuma inaso ciki abinci"yamiqa mata daya daga cikin lodojin ya'ajiye bisa centre table.
Yasa hannu yasha fuskarta sannan yyi mata murmushi sukayi sallama da juna,Zuhra tabishi tarufe part dinta.
Koda yashiga part dinta bata porlour yanufi bedroom dinta kwance take bisa gado kamar meyin bacci.
Yashiga tare da sallama,amma bata ansa ba.
Hanan tatashi zaune ranta a6ace dajin muryarta tasha kuka tagaji bakinta har rawa yake.
Tace"mi yakawoka part dina?,kafita banason ganinka Dr. Rafeeq kakoma wurin wadda kafiso,sae yanzu nagane nayi babban kuskuren aurenka wlhy"
Mamaki yabayyana afuskarshi yace"Hanan ni kike fadima irin wa'annan maganganun?,tou wlhy bazan dauka ba kuma kinsan waye Rafeeq zan kamaki ahannuna Hanan,saekin raina kanki"
Hanan batace komae sbd tsabar takaici.
Yace"abincinki na porlour idan kinga dama sae kici"
Kamar jira take yagama magana tace"banaci kakai mata tahada"
Yace"kina iya zubarwa"yafita ranshi abace.
Part dinshi yatafi sbd bayason yahana Zuhra bacci yau yasan agajiye take,zuciyarshi cike da takaicin magamnganun da Hanan tafadi mashi,amma zataji kuka da idanuwanta akan wannan maganar.
Hanan itama takasa bacci tasan yau da ita yaya Rafeeq zai kwanta,Allah yasa dae kada nazamo sanadiyyar tashin ciwonshi.
Wayarta talalubo da niyyar kiran aminiyarta Khubra domin tabata shawara,sae wata zuciyar tace kiyi haqurin gari yawaye mana.
Bbu yadda ta'iya dole tahaqura amma fa batayi bacci ba sbd tinanin yaya Rafeeq tanason shi tana kaunarshi kuma batason bata mashi rae,amma zancen gsky bazata juri wulaqancin shiba.
Hanan bata iyacin abincin ba hasalima bata buda taga mike cikin ledarba.tasaka cikin freedge sannan tatafi daniyyar takwanta,amma takasa bacci tarasa mike damunta,toilet tashiga tadauro alwala tafara nafilfili har aka fara kiran sallar asalati.................
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*125-130*
Haka gari yawaye zuciyar cike da tinanin laifin data aikata ma Dr. Rafeeq,dukda itama bae yi mata dai2 ba.
Da asuba yaya Rafeeq yashigo da niyyar yatada Zuhra,yayi switch on din light,kwance take bisa lafiyayyen gadonta baccinta take cikin kwanciyar hankali.
Ahankali yake tafiya harya'isa bakin gadon,yaje saitin fuskarta sannan yadurqusa,kalllon kyakykyawar fuskarta yakeyi tare da murmushi.
Cikin zuciyarshi yake fadin Zuhra banaso natakura maki,ina sonki sosae,kamar yarda yakeson kaina.
Hannunshi yadaura bisa kyakykyawar fuskarta mai santsi kamar fatar jariri,har yakai cikin gashin kanta mai tsawo da taushi ga kamshi yaji gyara.
Shafa gashin yake harya soma fita hayyacinshi.
Da sauri tabude idanuwanta fuskarta cike da tsoro,sbd al'amarin yafara bata tsoro.
Suna hada ido yyi murmushi yace"sarkin tsoro nine mijinki"
Zuhra tace"yaya Rafeeq harkatashi,ya Aunty Hanan?"
Yadan yamutsa fuska yace"eh nazo kuma natada ke,lokacin sallah yyi"
Yamiqe tsaye yana fadin kitashi fa kada nadawo natarar da ke kina bacci.
Tashi tayi tare da dauro alwala tafara gabatar da sallah tare da nafilfili.
9am Zuhra tagama shiri cikin wani tsadadden material pink colour tayi kyau sosae,make-up tayi wadda taqara fitar mata d madarar kyanta.
Zaune take porlour tana kallo komae neat sae kamshi ke tashi tako'ina.
Yaya Rafeeq ne yashigo cikin shigar qananan kaya,riga blue da jeans black fuskarshi dauke da fara'a sakamakon ganin kyakykyawar matarshi da yyi.
Gashin kanshi yaji qara yanata shining ga kuma qamshi,yaqara wani kyau mai daukar hankalin duk wata mace.
Yaqaraso har bisa kujerar da take zaune shima ya zauna,yana kallonta.
Kafin tayi magana yace"my wife kinyimin kyau sosae fa,gsky nayi dacen mata"
Zuhra tayi murmushi tace"yayana katashi lfy?"
Yadan nisa yace"lfy amma ba lau ba"
Zuhra taware ido tace"lfy dae yaya Rafeeq me ke faruwa?"
Yaya Rafeeq yace"tinaninki ne yahanani bacci da kamar nadawo sae nayi tinanin kada natakura maki"
Zuhra tace"tinanina kuwa yaya Rafeeq kana tare da Aunty hanan,kadae kawae kana zolayana"
Bayason sanar da ita abinda yafaru dole yacanja maganar.
Hannunta yariqe yahada da nashi yana kallon cikin idanuwanta yace"Zuhra da gaske ne,kwana nayi ina tinaninki"
Zuhra tayi murmushi tace"nima haka yaya Rafeeq"
Kallonta yake cikin mamaki yace"Zuhra da gaske kindamu da ni?"
Qarar qaraurawa sukaji,da alama sunada baqo.
Zuhra tace"bari naje naga waye"tare da tashi tanufi bakin kofa.
Tana budewa taga wata mata hannunta dauke da basket tare da wata leda ahannunta,wacce bazata wuce shekara arba'in da wani abu ba,Zuhra tagaishe da ita tare da bata umarni tashigo.
Yaya Rafeeq yana ganinta yasaki fuska,bayan sungaisa tace gashi inji Mami tace akawo maku.
Haka yaya Rafeeq yyi mata kyautar kudi yasallameta tayi masu addu'a tare da fatan zama lfy sannan tatafi.
Zuhra tace"wae yaya Rafeeq yaushe su Iman zasuzo ne wlhy nati tinanin sune shiyasa nayi saurin bude gida,jiya bbu yadda banyiba sukwana anan amma suka gudu"
Yaya Rafeeq yadan harareta cikin wasa yace"a ina zasu kwana?"
Zuhra tace"anan mana yayana"
Yace"mijinki na gidan zakice wasu suzo sukwana"
Zuhra tashagwabe fuska tace"abinda tafiya kayi kabarni kuma kasan inajin tsoro"
Yyi murmushi yace"tou yau zantayaki kwana tinda tsoro kikeji"
Zuhra taware ido tace"a'ah rufamin asiri,Aunty Hanan nagidan,yanzu kayima Aunty hanan magana sae muje part dinta muyi breakfast"
Yace"muje part dina sae tazo muhadu acan"
Yaya Rafeeq yadauki kwando daya Zuhra tadauki leda suka tafi part dinshi,saeda Zuhra jera masu komae bisa dinningtable sannan ya'umarceta da takira Hanan.
Bbu yadda ta'iya dukda tsoron da takeji haka tabi umarninsa tatafi gabanta nafaduwa.
Yyi alqawarin kozain qara zuwa part din Hanan sae idan laluri amma hakanan bazae shigaba.
Zuhra tashiga part din Hanan,bbu kowa aporlour sae plasma dake manne da bango da keta fatan aiki.
Zuhra tafara sallama cikin zazzaqar muryarta,bayan kamar 7mins Hanan ce tafito cikin shigar qananan kaya batako ansa sallamarba,fuskarta cike da bala'i...................
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*130-135*
Zuhra tasanyaya murya tace"Aunty hanan kintashi lfy?"
Hanan tawatsa mata harara tace"da bantashi ba zaki ganni ne?,me yakawo ki part dina munafika?"
Zuhra bata nuna mata ranta ya6aciba tace"yaya Rafeeq ne yace kizo muyi breakfast"
Hanan tace"bazan zoba,kinje kinyima Dr. Rafeeq asiri sae yadda kikayi da shi tou wlhy zaki gane kurenki"
Zuhra tafara zubar da hawaye tace"wlhy Aunty Hanan banyi ma kowa asiri"kafin tarufe baki tini Hanan tasharara mata mari.
Hanan tace"kuma wlhy sae kinbar Dr. Rafeeq kamar yadda kika baro cikin uwarki,fita kibarmin room dina tinkafin nasauya maki wannan aljanar fuskar naki"
Zuhra da gudu batar part din Aunty hanan tana kuka,part dinta takoma tafada bisa lafiyayyen bed dinta taci gaba da kuka mai bantausayi.
Ita tarasa abinda yake mata dadi.
Jitayi andafa bayanta,arazane tajuyo tare da kallon wanda yadafata yaya Rafeeq ne,fuskarshi kice da tambayoyi da dama.
Zuhra tadan juya tagoge hawayen dake fuskarta sannan tajuyo fuskarta dauke da murmushin karfin hali.
Yace"lfy?,me ke faruwa?"yaqagu da yaji ansar da zatabashi.
Zuhra tace"yaya Rafeeq kajini shiru ko,nazone natarar da ankirani awaya"
Yakada kae alamar bai yadda ba yace"me kikema kuka Zuhra?,fadamin gsky"
Zuhra tace"kaina ne yakemin ciwo"
Yace"me yasamu fuskarki?"tare da shafa fuskarta.
Marin da Hanan tayi matane har jini yakwanta awurin abu ga farar fata.
Zuhra bakinta na rawa tace"bigewa nayi yanzu"
Yace"kinje part din Hanan ne?"
Zuhra tace"eh naje tana zuwa"
Sae tacanja maganar tace"yayana yaushe su Islam zasuzo ne?"
Yyi murmushi yace"sae ranar da kika rinqa fadima mijinki gsky Zuhra"
Yajuya da niyyar yafita,sbd baiji dadiba.
Da sauri Zuhra tasha gabanshi tace"dan Allah yaya Rafeeq kada kayi fushi da ni"idanuwanta suna zubar da hawaye.
Yyi murmushi karo nabiyu sannan yasa yatsanshi yagoge mata hawaye yace"Zuhra bata tafan ranar da zanyi fushi da ke,kibar saurin zubarmin da hawayenki masu tsadar gaske"
Yyi kissing din goshinta tare da shafa gashin kanta sannan yace"muje muyi breakfast,inaso inje gida idan kungama"
Zuhra tace"kazomin da su Islam plz"
Yyi murmushin dake qara mashi kyau yace"yadda kikace my queen"
Zuhra tayi murmushi,yakama hannunta suka tafi part dinshi.
Hanan abin duniya yadameta yaya Rafeeq din data dade tana so da kauna gashi tin yanzu yafara fushi da ita.
Zaune take bisa bed dinta tayi tagumi tana tinanin meye mafita.
Wayarta tadauka tafara neman layin Khubra cikin sa'a bugu ukku tadauka.
Khubra tace"amaryar Dr. Rafeeq ae banyi tsammanin ganin kirankiba yanzu"
Hanan tace"sbd mi?"
Khubra tace"kina tare da mutumin naki,me ake damu kuma,ae naso ace inzama quda domin ganin wannan ranar"
Hanan tatabe baki tace"hmm,Khubra kenan"
Khubra tace"ban gane wani Khubra kenan ba"
Hanan tace"dakinsan bakin cikin daya cusa min dasaikin jajantamin har kimin kuka"
Khubra tagyara kwanciya tace"shaqamin mana aminiyata"
Hanan tana kuka takwashe komae tafada mata taba boye mata komae ba.
Khubra tayi tsoki tace"amma wlhy Hanan kinbani mamaki,dikda iliminki kike aikata wannan shashancin,kimmin faduwar toto aruwa"
Hanan tace"haba Khubra bisa gado fa nashiga nagansu shi da ita"
Khubra tace"tou me yakaiki part dinta?,banda dama kinaso kiganuma kanki,kuma wae har kika buda baki kika ce mashi kada yasake shigo maki room dinki,kinsan irin zuciyarshi yyi fushi da room dinki kenan"
Hanan tace"eh kuma hakane,yanzu yazanyi ne"
Khubra tayi murmushin da ita daya tasan mi take nufi tace"kinga inaso yau da daddare kije part dinshi kibashi haquri,kuma kada kisake kifito hakanan,aedae kingane,kuma kizanja zamanki da shi tare da Zuhra"
Hanan tace"sbd mi?"
Khubra tace"duk ranar da muka hadu zan sanar da ke"
Hanan tace"yaushe zaki shigo ne"
Khubra tace"yanzu dae muna Abuja ni da Alhaji,amma nextweek zamu dawo"
Hanan tace"hmm aminiyata kenan,dakin bani shawara sae nabi amma ke bakison shawarana"
Khubra tace"hmm ae bazaki ganeba ne,saedae munhadu"
Sukayi sallama da juna.
Shi yariqa bata abaki har taqoshi,Zuhra tana mamakin irin so da kulawar da yaya Rafeeq yake bata,Dr. Rafeeq din data sani wanda take jima tsoro kuma baya dariya,mutum mae tsadar gaske yau shine yake nuna mata so haka.
Gabantane yyi mumunan faduwa sakamokon tuno furucin Aunty hanan da tayi,itadae tasan tana dumuwa da damuwarshi kuma tanason ganinshi akusa da ita,tanason ganin kyakykyawar fuskarshi tare da murmushinsa mai tsadar gaske,wanda ba kowace mace bace take ganin irinshi.
Bayan sungama yyi wanka yashirya lokacin Zuhra tana part dinta.
Yafito cikin dakakkiyar shadda ruwan qasa tare da babbar riga yasaka hula ruwan kasa da takalma yadaura agogonshi na gold yaqara feshe jikinsa da turaruka designers,yyi kyau sosae na ban mamaki.
Part din Zuhra yashiga lokacin itama tashirya cikin wata gojuwar riga qirar bahrain,blueblack tasha ado,tayi mata kyau sosae,gashin kanta yaji qara sae qamshi yake fuskarta tadauki make-up.
Dasauri isa inda take tare da rungumeta yana fadin my queen zaki rudani fa.
Yace"kinyimin kyau kada kibari kowa yaga wannan kwalliyar sbd ni daya keda ita my queen"
Zuhra tace"nimafa da inada dama bazan bari kafita"
Yaware ido yace"sbd mi?"
Zuhra tashagwabe tace"nasan mata zasuyita kallommin kai"
Yyi murmushi yace"lalle ana kishina sosae kuma nagode"
Saeda sukasha kauna sannan tarakashi harabar gidan wurinda aka tanada dan ajiye motoci suka tafi,itace tazaba masa motar da zai shiga sannan yatafi.
Koda yaje gida yyi sa'a Abba na gidan,bayan yagaishe da su,Abba yashiga yi mashi nasiha akan yyi adalci atsakanin amanar da aka damqa mashi tare da addu'ar sumun zama lfy.
Da jima sosae agidan,har bayan la'asar sannan yatafi gida,Islam da Iman basunan suna gidan Mummy ita taturo driver yadaukesu.
Haka yakoma gida batare dasu Islam ba,yana zuwa gida Zuhra tatambayeshi su Islam,yafada mata abinda Mami tace.
Zuhra tace"ina tarasu ne,amma duk ranar da sukazo sae sunyimin 1month agidannan"
Yace"suda zasu koma school,ana shire2 fara exams"
Zuhra tace"yawwa idan akayi hutu,sae suyishi anan"
Tadan tsaya alamar tinani,yatambayeta abinda takema tinani amma tace bbu komae.
Zuhra tafiddo masu abincin ranar da aka kawo masu sukaci,hankalinsu kwance.
Da dare yyi dole yyima Zuhra sallama sbd bayason tagane halinda suke ciki shiga Hanan,amma daga yau shikenan zai yanke hukunci.
Itama Zuhra batace dashi komae ba sbd ita tayi tinanin Aunty hanan a part dinshi take kwana,amma tanajin kishin mijinta.
Yazo yyi mata sallama sannan yatafi part dinshi.
Haka yakwanta zuciyarshi cike da mafarkin Zuhra tare da tinanin daga yau yabar kwana shi daya.
Ahaka bacci yadaukeshi,ahankali tabude kofar tashigo sanye take cikin waya yar qaramar riga wadda da kadan tazo cinyarta,rigar ruwan sararin samaniya batada nauyi,sae faman qamshi take,kanta bbu kallabi tabazo gashinta har gadon baya,tayi switch on din light tini haske yagauraye bedroom din,Hanan kenan.
Tinda aka bude kofar yatashi saedae bae nuna alamun yatashinba,saeda yaji ana qara tinkaro inda yake kwance sannan yatashi zaune yana kallonta cikin bacin rae..............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*135-140*
Hanan tana ganin haka tazo har bakin gadonshi sannan tadurkusa tafara kuka tare da bashi haquri.
Juya mata baya yyi sannan yakwanta kamar yanayin bacci.
Amma ba bacci yakeyiba ji yake kamar ana zuba mashi wani abu cikin brain dinshi,sbd shi mutum ne wanda bayason kuka ko kadan.
Tayi kamar 15mins tana kuka kafin yyi mata magana.
Cikin muryar kuka Hanan tace"dan Allah yaya Rafeeq kayi haquri,kayafemin wlhy bazan juri zama dakai kana fushi da niba"
Bbu yadda ya'iya dole yyi mata magana kodan tatafi tabarshi da abinda yake damunshi wato tinanin Zuhra.
Ba tare daya kalletaba yace"shikenan komae yawuce amma fa bazan sake shiga part dinkiba Hanan saedae kiyi haquri".
Tasan halinshi sarai,dama tasamu yyi mata magana,tanata tinanin yadda zata shawo kan mutumin nata.
Sae kawae wata zuciyar tace kici gaba da kuka,may be yasaurare ki.
Bata matsa inda take durkusheba taci gaba da kuka domin tajawo hankalinshi gareta.
Kukanta duk yabi yadaga mashi hankali zaune yatashi yana kallonta,takaici ya'isheshi,sae tausayinta yakamashi.
Yace"me kuma akayi ne Hanan?,kinfasan yanzu dare yyi amma kinzauna sae dagamin hankali kike"
Hanan dae tarasa tacewa,tashi kuma tanajin kunyar tasake cewa wani abu kada yaganota.
Yace"kinga Hanan dan Allah idan bazaki yimin shiruba kifita hakanan"tare da juya mata baya yyi kwanciyarshi.
Bayan kamar 5mins tana tinanin yyi bacci tatashi ahankali tahau bisa gadon tare da kwantawa abayanshi.
Duk abinda takeyi yana jinta,wani 6angare na zuciyarshi yace kada kawulaqanta Hanan sbd tanuna tana sonka tana qaunarka tin kafin tamallaki hankalinta,kuma itama tanada hakki akanka kamar yadda Zuhra take da hakki,akwai ranar da Allah zae tambayeka.
Bbu yadda ya'iya Hanan matarshi ce,juyowa yyi yana kallonta tare da kashe beside drower lamp din dake kusa da kanshi.
Hannunshi yadaura bisa kanta yafara shafar gashin kanta,Hanan ji tayi kamar amafarki,saeda tata6a jikinshi sannan tasan ba mafarki takeyi ba.
Hanan tace"dan Allah yaya Rafeeq kayafemin bazan iya gafartama ma kainaba idan bana zaune da kae lfy"
Ahankali yake magana yace"zan yafe maki amma kitabbatar da bazaki sake aikata wani abu marar kyau akan kowaba,ina nufin Zuhra,Zuhra tanason ki dukda irin abinda kika aikata mata"
Hanan tace"i'll not repeat it again Insha Allah"
Yaya Rafeeq yace"Allah yasa da gaske kike Hanan"
Hanan tace"da gske ne mana yaya Rafeeq,ina sonka sosae"taqara shigemashi ajikinshi.
Yaya Rafeeq yace"nima ina sonki"
Dukda room din ba wani haske ke akwai sosaeba saeda Hanan tadago idanuwanta tana kallonshi bakinta har rawa yake tace"yaya Rafeeq da gaskene kana sona?"
Yaya Rafeeq yace"ina sonki mana amma abinda kike aikatawa ne banaso Hanan"
Hanan tace"nabari ae my husband"
Dr. Rafeeq yaba Hanan mamaki sosae duk yadda tadaukeshi yawuce nan 6angaren soyayya,wannan dare Hanan tasha wahala sosae,Dr. Rafeeq yyi sa'ar samun Hanan amatsayin virgin,yyi farin ciki sosae kuma wannan shiya nuna mashi tsantsar son da Hanan take yimashi tindaga Nursery school har zuwa masters dinta da tayi bata wulaqantar da kantaba ga wani tana riqe da mutuncinta har Allah yakawosu wannan lokacin.
Da asuba bayan yyi wanka yyi sallah,sannan yatasheta tare da temaka mata tayi wanka itama tayi sallah sannan suka koma suka kwanta.
Harya kwanta yatashi yafita,Hanan tajin lokacin da yatashi amma bacci yaci qarfinta sbd da dare bata samu wani baccin kirkiba taci gaba da baccinta.
Part din Zuhra yanufa hannunshi dauke da keys din part dinta,yabude yashiga,yana shiga yatarar da ita tana tana karatun al'qur'ani mai girma, yyi murmushi sanan yaqarasa kusada ita yazauna.
Tanakai aya tadago dara daren idanuwanta tana kallonshi fuskarta dauke da murmushi tace"yaya Rafeeq kuntashi lfy?,ya Aunty Hanan?"
Yyi murmushi tare da shafar fuskarta sannana yyi kissing din goshinta yace"tabani saqo nabaki"
Zuhra taware ido fuskarta cike da mamaki tace"Aunty hanan din?"
Yace"eh mana,ita my wife"
Zuhra tace"tou wane irin saqo ne my prince?"
Yyi murmushi yace"sae zuwa anjima zan baki"
Zuhra tayi murmushi tace"Allah yakaimu lfy"ita bata fahimci abinda yake nufiba.
Yace"ameen by wife,bari natafi kiqarasa karatunki,sae zuwa anjima"yamiqe tsaye yatafi,Zuhra tabi bayanshi da kallo tan murmushi,saeda yafita sannan taci gaba da karatunta.
Koda yakoma part dinshi yahau bisa gado tini Hanan tamance duniyar da take tayi nisa sosae wurin bacci,yakashe fitila tare da jawota jikinshi sukaci gaba da bacci cikin kwanciyar hankali.
Da gari yawaye,bayan yyi wanka yashirya lokacin ita bata tashi bacci ba,kananan kayane kijinshi yyi kyau sosae,sae tsadadden kamshinshi ke tashi.
Wajen 9:30am Mami ta'aiko masu breakfast dinsu kamar kullum, lokacin Zuhra tagama shiri cikin wani english wears pink nd white sunyi mata kyau sosae,kuma sunkama jikinta,gashin kanta yaji gyara tadaure da ribom pink yasaka yan kunne white tayi kyau sosae tafeshe jikinta da turaruka tare humra masu dadin qamshi.
Fuskarta tadauki make-up tayi kyau sosae,kayan breakfast din tadauka tanufi part din yaya Rafeeq da su.
Zaune yake porlour yana kallon tashar bbc london,yana ganinta yatashi yatarota,fuskarshi dauke da jin dadin ganinta.
Yanata yabon kyan da tayi,Zuhra taje tajera masu bisa dinningtable sannan tadawo tazaune dan nesa da shi.
Sunata firarsu cikin farin ciki,yace"gsky my queen kinyimin kyau sosae,kada ki'ida rudani da salon gayunki"
Zuhra tayi murmushi tace"yaya Rafeeq yamata ayima Aunty hanan magana tafito muyi break kada yyi sanyi"
Kafin yaya Rafeeq yyi magana Hanan tafito daga cikin bedroom dinshi,jikinta sanye yake cikin wannan qaramar rigar tajiya wadda da kadan tazo cinyarta kanta bbu ko kallabi,bbu inda tatsaya sae bisa jikin yaya Rafeeq,Zuhra tana ganin ikon Allah............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*140-145*
Kallo daya Zuhra tayi mata takauda fuskarta tadaure tace"Aunty Hanan kina lfy?"
Hanan batare da takalleta ba tace"lfy"dan kada yaya Rafeeq yyi tinanin wani abu shiyasa ta'ansa badan