Author : Jamila Samaila Yusuf Category : Romantic Hausa Novels
ranta yaso ba.
Zuhra tace"excuss me"tatashi tafi.
Yaya Rafeeq yabita da kallo,Hanan wani farin cikine yakamata tasan koba komae ta6atama Zuhra rae.
Part dinta takoma tashiga bedroom dinta bisa gado tazauna tarasa me ke mata dadi hawaye sae fatan zuba suke daga cikin dara daran idanuwanta wanda yanzu sunkoma jajaye sbd tsabar kukan da takeyi tare da kishi daya tirnike mata zuciya.
Ita bata ta6a tinanin tana kishin yaya Rafeeq kamar hakaba.
Ashe haka so yake?,gsky ina matukar son yaya Rafeeq dan bbu macen da tata6a son wani namiji kamar yadda nakeson shi ,haka Zuhra tafadi cikin zuciyarta.
Yaya Rafeeq yalura da irin yanayin da Zuhra tashiga hankalinshi yatashi sosae gashi kuma Hanan tazo tatsareshi da solon soyayyarta.
Yasamu yyi mata dibara yajanyeta daga jikinshi.
Yatashi tsaye zai fita,cikin kissa Hanan tace"my man ina zuwa kuma?"
Yaya Rafeeq yace"zanje part din Zuhra"sbd kowa yasan Rafeeq mutun ne wanda baida kwana kwana arayuwarshi kuma bayayin qarya arayuwarshi.
Batare da yaji abinda zata fadaba yafita yabarta nan zaune.
Yana fita Hanan tayi murmushi tace"hmm aidai nasan taji haushi,kuma wlhy takaicina shizai kasheki Zuhra"tare dayin tsoki mtssss.
Zuhra tanajin anshigo part dinta tatashi daga bisa gado tashiga bathroom tasan yaya Rafeeq ne amma yanzu batason ganinshi.
Yana ganin bata porlour yashiga bedroom dinta,yana pushing din kofar bathroom din yajita a datse.
Yasan tana ciki,dan haka yakoma gefen gadon yazauna yana jiranta,yyi 10mins azaune amma bbu ko motsinta aciki.
Ya'isa kusa da kofar yafara knocking,amma Zuhra tayi mashi shiru kamar batanan.
Wane gefen zuciyarta yace yanzu idan baki fitaba zaiyi tinanin wani abune qwara kawai kin fita.
Zuhra tawanke fuskarta sannan tabude kofar tafito yana tsaye bakin qofar tara6ashi tawuce,yaya Rafeeq yabita da kallon mamaki sbd yakaranci kome atare da ita.
Zuhra tayi tako biyar sannan tatsaya tare da juya mashi baya.
Yaya Rafeeq yasanyaya murya yace"lfy my queen?, me ke faruwa?"
Zuhra wani takaici yaqara cusa mata cikin zuciyarta wannan mutumin yaraina min hankali yana nufin baisan abinda yayimin ba?.
Ji tayi yarungumeta tabayanta,yanayi mata dariya,Zuhra tafara kokofar qwace kanta amma takasa.
Yakai bakinshi saitin kunnanta cikin siririyar murya yace"ashe ana kishina,lalle ni Rafeeq inada sa'a sosae"
Zuhra taraqa daure fuska tace"oh dariyama nabaka kenan?"
Da sauri yasaketa yakoma gabanta kneels dinshi aqasa yace"a'ah gimbiyata kuka nake"yafara qaqalo hawayen dole waishe adole kuka yake ba dariyaba.
Zuhra takoma bakin gado tazauna,kneels dinshi yaja har ya'isa inda take zauna yadaura tafikan hannayenshi bisa cinyarta sannan yada kai yana kallon kyakykyawar fuskarta.
Yace"ae tinda nayi kuka sae'a baryin fushi dani kada zuciyana yabuga"
Cikin mamaki Zuhra najuyowa tare da kallon fuskarshi kamar da wasa taga hawaye kyakykyawar fuskarshi.
Zuhra taware ido tace"yayana wasafa nake maka,dan Allah kayi haquri"
Yaya Rafeeq yyi murmushi tare da kissing din lips dinta,yana mai kallon cikin idanuwanta yace"ina sonki Zuhra"
Rungumeta yyi sosae ajikinsa,sannan yace"saena fadima Mami sonki yana wahalar da ni Zuhra"
Zuhra taware ido tare da dagowa daga jikinshi fuskarta dauke da murmushi tace"kada kafadima Mami,zan yima sona warning da rabu da mijina yahuta"
Yyi murmushi yace"ae banaso yarabu da ni my queen"
Zuhra tamaida kanta bisa jikinshi tare da qara rungumeshi tace"ina sonka fiye da yadda nakeson kaina yaya Rafeeq"
Da sauri yadagota fuskarshi dauke da farin ciki yace"da gaske ina sona?"
Cikin wata murya mai kashe jiki wadda ita kanta batasan ta'iyataba tace"sosae ma my prince"
Ae tini yaya Rafeeq yafara zagaye bedroom din cikin farin ciki yana murna tare da fadin i'm lucky.
Zuhra mamaki yabata tare da dariya yaya Rafeeq yakoma mata tamkar wani yaro.
Dahaka yyita lallashinta tar tasaki ranta,sannan yakama hnnunta suka koma part dinshi,ahaka sukayi breakfast dinsu cikin jin dadi saedae Hanan idan tafakaici idon yaya Rafeeq taga baya kallonta saeta watsama Zuhra harara(ni Miss j nace"aikin banza daqquwa cikin babbar riga😜😏)................
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
```Wannan page din nakine qawata takaina,nagode da kulawarki agareni``` *NAFEESA SADA MASHI* ```.Allah yabar zuminci..```
_Allah yakawo miji nagari musha biki💃🏻💃🏻💃🏻....._
*145-150*
Hanan tana mamakin irin yadda Dr. Rafeeq yake nuna kulawarshi akan Zuhra,har take tambayar kanta,ashe yaya Rafeeq ya'iya kula da mace har haka?.
Mutumin da idan suka samu matsala saedae ita tabishi tabashi haquri,amma yau shike lallabar wata mace.
Bbu yadda ta'iya dole tayi haquri da irin rayuwar yaya Rafeeq,wane 6angare na zuciyarta yace gsky bazan iyaba.
Haka suka kamalla breakfast dinsu zuciyar Hanan cike da tinani daban2.
Misalin 9:30pm lokacin Zuhra tayi shirin kwanciya baccine cike da idanuwanta,tadade da fara bacci yaya Rafeeq yashigo bedroom dinta tare da shirin bacci.
Fuskarta da taji anata faman shafawa shine yatasheta daga baccin da take.
Ahankali tabude kyawawan idanuwanta,suna hada ido yyi mata sanyayayyen murmushi,itama murmushin tamaida mashi.
Ahankali take magana tace"yaya Rafeeq bakayi bacci ba?"
Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"ae bacci nazoyi yanzu,taso muyi sallah"
Batayi mashi gardama ba tatashi tayi alwala sannan sukayi sallah.
Bayan yadafa kanta tare da yin addi'o'i sannan yafito masu da gasashshir kaza manya guda biyu tare da madara mai sanyi haka sukaci abinsu cikin kwanciyar hankali.
Bayan sungama yadauketa yadaurata bisa gado.
Yyi switch off din light sannan yahau lafiyayyen bed dinsu yakwanta tare da jawo Zuhra jikinshi.
Kimanin 11:55pm lokacin basusan inda kansu yakeba,hasken da yagauraye bedroom din shiyaba Zuhra damar dawowa daga duniyar da take,Hanan ce tsaye abakin kofa tatsira masu idanuwa fuskar dauke da bakin ciki da tashin hankali.
Gaban Zuhra ne yyi mummunan faduwa ganin Hanan tayi saurin lullu6e jikinta da blanket sbd jikinta bbu komae.
Zuhra tace"subhanallahi,innalillahi wa'inna ilaihiraju'un"
Hanan tace"dole kifadi haka makira,munafuka"
Yaya Rafeeq dake kusa da ita yaqara jawuta jikinshi yana magana qasa2.
Zuhra tatasheshi daga bacci,daqer yasamu yabude idanuwanshi.
Zuhra tace"yaya Rafeeq ga Aunty hanan tazo"
Dasauri yabude idanuwanshi,koda yaga Hanan atsaye tsakiyar room din sae ya'ida wartsakewa.
Hanan tace"yaya Rafeeq inason yin magana da kai ne"
Yaya Rafeeq ranshi a6ace yace"wai ke wace irin wawiyace Hanan?"
Hanan tace"kamar ya dae?"
Yace"banda rashin tinani irin naki meye nazuwa nan ciki kamar yanzu?"
Hanan tace"ae shiyasa nace maka kafito porlour muyi magana"
Yace"ina tare da matana bazan fita nabartaba ko miye fadeshi anan"
Hanan tace"gsky yaya Rafeeq baka yimin adalci kafasan wannan kwanana ne amma kashigo nan,kuma sannan miyasa zaka biyota har part din kodan ni baka qaunata ne?"
Yaya Rafeeq ranshi yaqara baci yace"kinga yanzu banida lokacinki dan haka fita"
Zuhra na ganin ikon Allah,batasan dalilin da yasa Aunty hanan keson ganin tsiraicinta ba wannan ae rashin tinani ne.
Hanan taturo mashi baki tare da gyara tsayuwa alamar bazata tafiba.
Yaya Rafeeq yafara qoqarin saukowa dag bisa bed din,ai kafin kace mi,tini Hanan tabar part din Zuhra sbd tasan idan yakamata bazai mata saukiba.
Yyi tsaki yace"marar kunyar qarya aeda kintsaya yakashe wutar room din sannan yakoma yakwanta tare da jawo Zuhra jikinshi.
Yafara bata haquri tare da lallashinta kamar wata baby,Zuhra saeda tayima Aunty hanan Allah ya'isa data tashi yaya Rafeeq daga bacci sbd ba qaramar wahala taciba cikin daren nan.
4am yatashi yyi wanka baikoma bacci ba yaci gaba da nafilfili yanata yima Allah godia daya hadashi da Zuhra tare da saka mata albarka kuma Allah yabasu zama lfy.
Da lokacin sallar asuba yyi,shima yyi sallah sannan yafara kartun al'qur'ani mai girma.
Zuhra bata tashi bacciba sae 9am,dama yana zaune kusa da ita,shine yataimaka mata yakaita bathroom yyi mata wanka har tayi sallah sannan takoma takwanta.
Tausayinta ne yakamashi sosae,sbd yadda take tafiya gashi kuma batajin dadin jikinta.
Saeda yyi kwana biyu a room din Zuhra,yaya Rafeeq ne yatsara masu adadin kwanan da kowace zata riqayi tana aiki,kwana biyu biyu.
Hanan batayi musuba sbd taga fuskarshi bbu alamar wasa.
Aunty hanan ce tafara ansar girki,amma kowace zata dafa abinda takesu a kitchen dinta shiyasa aka samu saukin rigima.
Tarabu dajin hayanir Aunty hanan kwana biyu sbd duk abinda zai hadata da ita basonshi takeyiba,ba ciki zuwa part dinshi tayiba idan ba ita takeda aikiba saedai idan yaji shiru yazo part dinta.
Sati biyu da aurensu yaya Rafeeq yakaisu gidansu domin su gaishe da Mami da Abba,Mami taji ddin zuwansu domin acan suka wuni,Mami tayaba da tarbiyar Zuhra sosae sbd tana baka'in jin kunyar Mami harbata yarda su hada ido.
Ashe su Islam sunkoma school suna preparing din fara exams..
Da marece sukayima Mami da Abba sallama suka tafi,sunsamu kyautar kudi wurin Mami da Abba,sukayi godia sannan suka tafi.
Wani babban BAUQUE ne yabiya dasu,kowace tashiga taza6o tsadaddun englishwear masu kyau sosae............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:22] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
_DEDICATED TO_ *MARYAM AYUBA MAI RUWA & HAJ. MARYAM DAN LADI KANAWA.....*
```Ina alfahari da ku,Allah yabar zuminci,yakawo miji nagari musha biki💃🏻💃🏻💃🏻...```
*Ana tare🤝.....*
*150-155*
Suka dawo gida lfy,ranar Aunty hanan ce keda girki,da dare yyi yaya Rafeeq yaje yyima Zuhra sallama sannan yatafi.
Hanan ce kwance bisa gado a part dinta taci ado tare da wata yar qaramar riga iyakar cinyar sae faman qamshi tare.
Hanan kenan,wai ita jiran Dr. Rafeeq yatake yazo yasameta a part dinta.
Har 11:30pm bbu Rafeeq bbu alamarshi ranta yyi mummunan 6aci,tashi tayi tanufi part dinshi ran 6ace.
Tana shiga cikin bedroom dinshi,har yyi switch off din light,Hanan tahangoshi bisa lafiyayyen bed dinshi yana bacci hankalinshi kwance.
Rantane yaqara bacci,cikin zuciyarta takefadin,inacan ina jiranka kai kuma kananan kana bacci kadaukeni jobless.
Kusa da kanshi ta'isa tana turo baki tatashe shi,bayan yyi addu'ar tashi daga bacci yatashi zaune yana harararta.
Yace"lfy zaki tasheni ina bacci na,aidayake kinsaba dama"
Hanan tace"gsky yaya Rafeeq abinda kikeyimin acikin gidannan yyi yawa,ya za'ayi inacan ina jiranka kai kuma kananan kana bacci"
Tsoki yyi mata sannan yace"be frank, fadi abinda zaki fada"
Hanan tace"yaya Rafeeq yanzu nasan baka qaunata,Zuhra gatanan duk ranar girkinta part dinta kke tarar da ita amma ni kwata2 bakason zuwa inda nake"
Yaya Rafeeq yace"kin banta abinda kika fadamin ne akan part dinki?,toni banmanta ba,kuma maganar zuwa part din Zuhra da nake bbu ruwanki aciki,dan haka kisan abinyi kuma kada kisake tashina daga bacci akan maganarki marar manufa"
Yajuya yakwanta,Hanan takoma part dinta ranta a6ace,daren nan taci kuka ahaka tayi bacci.
Bayan wata daya da bikinsu,yaya Rafeeq yakai kowace gidansu tawuni.
Mama tayima Zuhra nasiha sosae akan zaman aure tare da biyayya da zama lfy.
Hanan kuwa bbu irin kuka batayima Mummy ba tare da fada mata wai yaya Rafeeq yana wulaqantata akan Zuhra,Mummy bata nuna mata ranta ya6acib saedae tayimata fada,tace may be bakiyi mashi biyayya kamar Zuhra.
Mummy tace"Hanan dole saikin koyi haquri da ladabi,kuma duk abinda yakeso yazamto kema kinaso ahakane zaku zauna lfy"
Mummy tayima Hanan nasiha sosae,har bayan magrib sannan yadaukosu tare da gaisawa da sirikanshi.
Shoprite yabiya dasu kowace taza6i abinda takeso,sannan suka wuce gida.
Wani wulaqanci da Hanan taqaro shine idan ana biki ko suna acikin family dinsu yaya Rafeeq,zaibamu kudi kowace sayi abinda zatakai,amma Hanan sbd tanada kudi saeta linka abinda yabamu sau biyu cikin kudinta,takai kaya masu yawa kota qara da kudinta.
Wataranar sunday Khubra tazo gidansu Hanan,ba wani dadewa tayiba sbd akwai mutum dake jiranta a Zaria.
Hanan tafara ba Khubra lbrin halin da take ciki.
Khubra tace"yau zaki shiga school ne?,saemu yi planning din abinda zamuyi"
Hanan tace"nextweek zandawo aiki,zanshigo gidanki sae musan abinyi"
Hanan taraka Khubra har bakin mota nan suka tsaya sukaci gaba da zagin Zuhra,har yaya Rafeeq yazo inda zuke.
Yafahimci abinda suke nufi,koda suka juya suka ganshi sukayi tsuro2.
Yakallesu sosae sanan yace"Hanan kibita kutafi"
Khubra da Hanan suka zaro idanuwa suna kallonshi fuskarshi bbu alamar wasa,suka fara bashi haquri.
Tsoki yyi sannan yashiga cikin gida yaqyalesu atsaye.
Khubra tace"yanzu yadda za'ayi,kishiga gidan yyi haquri yarabu da ke"
Hanan tashiga cikin gidan jikinta har rawa yake,Khubra tatada motarta tashiga tatafi,tana qara nazarin yadda zasu billoma rayuwar Dr. Rafeeq.
Hanan kod tashiga part dinta bata sake fitowaba daman Zuhra keda aiki.
Shima baibi takanta dukda yana sane da ita amma yasan zata gama wasan 6uyar tazo inda yake idan buqarta tataso,zai bata mamaki fiye da baya.
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:23] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
_DEDICATED TO_*All members in Miss j🙋🏻😘hausnovels group...*
```I LUV U lodi lodi😘😘😘,Allah yabar zumunci🙏🏻...```
*155-160*
Bayan sati daya da faruwar kana.
Hanan tasamu yaya Rafeeq a part dinshi kimanin 10am.
Hanan takwantar da murya tare da bashi haquri akan abinda yafaru.
Yaya Rafeeq yadago kanshi daga bisa Laptop din dake amfani da ita.
Kallo daya yyi mata sannan yamaida kanshi bisa laptop sannan yace"bygon is bygon don't mind"
Hanan tayi murmushin jin dadi tace"thank you alot my man"
Yaci gaba da abinda yake,dama yaga alamar akwai abinda takeson fadi abakinta sedae yyi shiru baice da ita komae ba.
Hanan tace"dama yaya Rafeeq inaso muyi magana akan komawana aiki ne"
Yaya Rafeeq baice da ita komae ba,Hanan tasake cewa"inaso inkoma bakin aikina"
Yaya Rafeeq yace"Hanan,banyarda daki koma aikiba"
Hanan tatashi tsaye tace"me kke nufi Dr. Rafeeq?"
Yaya Rafeeq yace"ae tasan kinji abinda nafada idan bakijiba nace bazakiyi aikin ba Hanan"
Hanan tace"sbd mi,meye manufarka?"
Yaya Rafeeq yace"sbd inada ikon komae akanki"
Hanan taturo baki cike da tsiwa tace"ni gsky inason aikina"
Yaya Rafeeq yatashi tsaye yace"ke Hanan,kada kiyimin rashin kunya ina jina?,bbu abinda banyi maku kuma bbu abinda kuke nema agida,idan akwau kifadi"
Hanan tace"bbu,amma nidae inason aikina sbd dashi kaganni"
Yaya Rafeeq yace"tou kiza6a ko zaman aurenki ko aiki,dan ni bazan iya cigaba da zama dake kina aikiba"
Hawaye ne suka fara zuba daga cikin idanuwan Hanan tace"Dr. Rafeeq kana yimin abinda kaga dama kodan nice nakeson ka?"
Yaya Rafeeq yace"ni banyi maki wani maganar so ko rashin so ba Hanan,amma dae nace banason zuwanki aiki"
Hanan tagoge hawayen da suka zubi mata tace"yaya Rafeeq kodan Zuhra batayi karatuba ne?"
Yaya Rafeeq yace"Zuhra batayi karatuba,amma cikin wannan watan zata samu gurbin karatu a jami'ar bayaro"
Hanan tace"karatu kuma?"
Yace"eh karatu mana,tinda kin hanata zama a A.B.U,saeta dawo kusa da gida"
Hanan tace"ita tatafi school,ni kuma nazauna agida,wae me kadaukeni ne?"
Yakoma bisa kujera yazauna sannan yace"zaki iyaci gaba da aiki idan Hanan tagama karatu sae tayi aikin itama"
Hanan tace"sbd rashin adalci?"
Yaya Rafeeq yatashi tsaye yadaga hannunshi zai mareta sai kum yafasa,yanaya huci ranshi ya6aci sosae.
Yanuna da yatsa yace"Hanan bakinki yana son yimin rashin kunya kada kikuskura,kuma ke kika jama kanki sbd bakida adalci,duk ranar da hidima tatashi banda abinda nasiya maku saekinsa kudinki kin qara dukdan kinuna mata ke ma'aikaciya ce,shiyasa ita zatayi karatunta,amma kije kiyi shawara zaman aure ko aiki"
Haka Hanan tabar part dinshi tana kuka,Zuhra batasan wainar da ake toyawaba.
Aunty Hanan takira daddy awaya tafada mashi komae tana kuka,itadae Allah yasani tanson yaya Rafeeq batason abinda zae rabasu amma kuma tanason aikinta.
Daddy yabata haquri yace"tayi haquri shi yanzu baida iko da ita,kuma yasan idan yyima Rafeeq magana zaiyarda,saidai bayason yatakurama Rafeeq"
Yace"tayi haquri tazauna gidn mijinta tinda bata rasa komeba idan tanason wani abu tafada mashi"
Yaci gaba da lallabarta hrsukayi sallama,Hanan tayi kuka tagaji,koda takira wayar Mummy tafadi mata abinda yake faruwa itama haqurin tabata tare da lallashinta.
Tanemi layin Khubra bata samuba,haushi yakamata.
Tayi wurgi da wayar bisa gado takoma porlour tazauna zuciyarta cike da tinani.
Sati biyu kenan bata samun layin Khubra batasan dalili ba kuma bbu damar zuwa Zaria.
Dole tayi haquri tagaji da fushinta kuma suka shirya.
Bayan wata daya da faruwar haka,lokacin yaya Rafeeq yagama ma Zuhra komae na makaranta saedae yakawo mata admission din B.U.K ranar Zuhra tasha murna,tasanar da iyayenta awaya suma sunji dadi sosae.
Zuhra tafara zuwa school,driver ne yake kaita yadawo da ita kullun dayake yaya Rafeeq bayanan yakoma bakin aiki saedae kusan kullun sae yazo gida.
Bio/Chem ne take karantawa kamar yadda tafara a A.B.U,yaya Rafeeq yana samun kulawa sosae wurin matasansa,ba kamar Zuhra dan yanzu tasaba da mijinta sosae.
Hanan tanajin takaicin zuwan Zuhra school saedae bbu yadda ta'iya gashi bata samun layin aminiyarta,abin duniya yadameta.
Ranan aikin kowace yana qoqarin farantama ko wace acikinsu.
Bayan wata daya da fara zuwan Zuhra school,tadawo tatarar da Aunty Hanan kwance a mainporlour dinsu kwance ashe batada lfy yane.
Zuhra tana ganin yanayin da Hanan ke ciki duktabi tarude,takira wayar yaya Rafeeq tafada mashi,anyi sa'a yana hanya.
Yana dawowa suka tafi TWINS INTERNATIONAL HOSPITAL,asibitin Mami.
Bayan kwaje2 da likita yyi sakamon yanuna Hanan tana dauke da ciki 6weeks..
Murna wurin yaya Rafeeq da Zuhra ba'a magana haka suka dawo gida cikin farin ciki.
Hanan najin jiki sosae tausayi take basu sosae.
Saeda sukaga tasamu bacci sannan sukabar part dinta,part din yaya Rafeeq suka tafi.
Yaya Rafeeq yakamo hannun Zuhra tare da zaunarda ita bisa gado,kanshi yadaura bisa cinyarta kafin yadago fuskarshi yana kallon cikin idanuwanta,fuskar yashafa yana murmushi.
Yace"kema insha Allah nan bada jimawaba zaki samu"...............
*Miss j*🙋🏻😘
[1/9, 22:23] +234 813 019 3077: *🎀A DALILIN KANE🎀*
*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
_DEDICATED TO_ *SARAH ADIYYA,*```Allah yabar zumunci🤝🤝🤝....```
*160-165*
Zuhra tasa tafin hannunta tarufe fuskarta alamar taji kunya.
Yaya Rafeeq yyi murmushi yace"oh haryanzu anajin kunyana kenan"
Zuhra dae batace mashi komae ba.
Labarin cikin Aunty hanan yazagaye family dinsu gaba daya,murna ba'a magana wurin Mami da Mummy.
Bayan sati biyu yaya Rafeeq yyima kowace cikinsu kyautar motar qirar ANACONDER,driver kekai Zuhra school kafin ta'iya,kuma duk ranar weekend yaya Rafeeq ne yake koya mata driven.
Hanan bata cika fitaba yaya Rafeeq yahanata yahanata fita sbd rainon ciki.
Duk yadda yaya Rafeeq yakeqin akawo mashi masu aiki agida,saedai Mami taturo masu Asabe mai aiki,sbd Zuhra tana zuwa school yaya Rafeeq kuma yana zuwa wajen aikinsa,dole akawo wadda zatayi masu aikace2.
Zuhra datariga tasan halinshi narashin son abincin masu aiki saedae tana dawowa daga school tadaura mashi abinci kafin yadawo.
Hanan tanata rainon cikinta har cikin yatsufa,Mami tana zuwa dubata sosae.
Gsky Zuhra tayi dacen iyayen miji da dangin miji basu nuna mata banbanci tsakaninta da Hanan ko kadan kodan sunsan halin Dr. Rafeeq oho,hadama bai bada fuskaba.
Tin lokacin da Aunty Hanan tasamu ciki yaya Rafeeq yana kula da ita sosae,Zuhra najin dadin hakan sbd itama matarshi ce.
Akullum addu'arshi Allah yabashi zuri'a tagari,Allah yaba Zuhra itama.
Haka itama Zuhra duk kulawar da tadace yanabata sosae,fiye da canbaya dan yakwantar mata da hankali.
Ana cikin haka su Zuhra suka fara exams karatu take sosae kuma yaya Rafeeq yana qara yimata explain din inda bata ganeba.
Wata ranar monday lokacin Zuhra tatafi school yaya Rafeeq kuma yaje zaria,Hanan ce zaune porlour bisa kujera tana kallon cikinta ya'isa haihuwa.
Ringing din wayarta tajiyo cikin bedroom dinta,takwada ma Asabe kira,da sauri ta'iso tana Aunty gani tare da durkusawa agabanta.
Hanan takalleta sama da qasa cikin masifa tace"sae yanzu kikaga damar zuwa kenan"
Asabe tasanyaya murya tare da kwantar da kai tace"kiyi haquri Aunty wlhy banjiba ne"
Hanan da daka mata tsawa tace"shut ur mouth up,wawiya phone dina zaki daukomin bisa side drower dina"
Asabe tatashi jikina rawa tare da bata haquri tatafi takawo mata wayar sannan takoma kitchen.
Hanan tana dubu missed calls taga sunan Mummy,fara'a tabayyana afuskarta tareda dialing call dinta.
Bugu ukku Mummy tadauka,Hanan tashagwabe fuskar kamar tana ganinta tafara yimata shagwaba.
Mummy tace"ya kikejin jikin naki?"
Hanan tace"Mummy lfy qlau,saedai wani lokacin inajin motsi aciki,amma yaya Rafeeq yacemin bbu komae"
Mummy tace"eh bbu matsala,Allah yaraba lfy,dama jiya ni da Alh.muke magana nace mashi zaki dawo gida kihaihu yace sae kinyarda da hakan"
Hanan tace"ni dae Mummy nafiso nazauna tare da mijina gsky"
Mummy tace"tou