Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
yana zaune a kan buzu, hannunsa riƙe da Alqur'ani bugun warsh, yana karantawa. Opposite ɗin sa wata irin ƙatuwar rumfa, shimfiɗe da tabarmi da alluna a jijjingine, almajirai sun tafi bara.
Sallama ya yi wa dattijon, ya nemi guri ya zauna a gefensa. Dattijon ya kai aya, sannan ya amsa sallamar suka gaisa.
Ya dubi dattijon ya ce "Malam Ɗayyabu ko?"
"Eh nine"
"Dan Allah tambaya na zo na yi maka, kai malamin Alqur'ani ne. Ma'abocin Alkur'ani kuwa za a same shi da gaskiya da tsoron Allah. Kuma yanayin dattakunka, ya sanya mini yarda da komai zai fito daga bakinka, gaskiya ce"
Malam Ɗayyabu ya jinjina kai ya ce "Wannan gaskiya ne, in sha Allah yadda ka kyautata mini zato, ina sanya ran gaya maka gaskiya da yardar Allah"
"Akwai wani matashi da ya tare a unguwarmu, ya ce shi ɗalibinka ne, ya yi sauka a hannunka, daga baya kuma ya sake dawowa garin nan, neman kuɗi. To ina son tabattar da hakan daga gare ka ne, saboda yana ɗan bibiyar 'yar uwata ne, ina tsoron wani abin da ba a so ko fata ya faru, na ga yakamata lallai na bibiya"
Malam Ɗayyabu ya ce "Wannan gaskiya ne, ka yi kyawun kai, mussaman zamanin nan da ya lalace. Amma ka ga tun ban fi shekara ashirin da biyar ba, nake harkar ɗalibai, dan haka wanne daga cikin ɗaliban nawa?"
Ya ce "Sunansa Mamman, ban san sunan garinsu ba, amma ga hotonsa".
Ya yi maganar yana ciro wayarsa ya ɗan daddana, ya miƙa wa malam Ɗayyabu. Hoton Mamman ne a zaune yana wankin takalmi, Alina na gefensa a kan dakali tana magana.
Malam Ɗayyabu ya karɓi wayar ya yi shiru yana kallon wayar, ya numfasa ya ce "Wannan ce yar uwar taka?"
"Ba a kanta mu ke magana ba malam, wannan mutumin da ya ce shi ɗalibinka ne, nake magana a kai"
Malam Ɗayyabu ya yi shiru ya zuba wa hoton ido.
"Malam ka yi magana mana" Ismail ya yi maganar yana kallonsa.
Malam Ɗayyabu ya ɗago kai yana kallon Isma'il.
Ismail ya ce "Ina ƙara tuna maka, ka dubi girman mai littafin da yake gabanka, ka gaya mini gaskiya"
"Ɗalibina ne" Ya yi maganar yana gwama numfashi.
Ismail ya yi shiru yana nazartar fuskar malamin.
"Ka tabattar ɗalibinka ne?" Ya jinjina masa kai yana ɗan zazzare ido.
"Idan akasin gaskiya ka gaya mini, mai Alqur'anin nan ba zai bar ka ba"
"Me zai sanya dattijo kamar ni, ya yi maka ƙarya, alhalin baka sanni ba ban kuma sanka ba? Mamman ɗalibina ne, sai dai ya sauke ya haddace, dan haka ya kai munzalin da zai zaɓi abin da yake so, kuma ina da yaƙinin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba"
Ismail ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne,na gode sosai da sosai Malam" Suka yi musabiha, ya tashi ya tafi. Yana tafiya jikin Malam Ɗayyabu ya yi sanyi, wani irin gumi ya fara tsatstsafo masa, ya kalli Alqur'anin da yake gabansa ya furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, da wani bakin zan nemi gafarar Allah"
'yar ƙaramar wayarsa da ke cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya ciro ta, yana kallon yadda kira yake shigowa babu suna kuma babu lamba.
Hannunsa na rawa ya kara wayar a kunnensa.
"Aikinka ya yi kyau, idan aikin naka ya ci gaba da kyau, shikenan ka tsira, idan kuma aka samu matsala salin alin zamu ɓatar da kai"....
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
*MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN*
*Masu nema daga farko, su duba cikin channel link ɗin nan*
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 09017242889
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
SARA DA SASSAƘA...
AYSHERCOOL
YOTA/002
Page 8
Sannu a hankali ya ajiye wayar, jikinsa na ci gaba da tsuma, ya tashi tsaye a hankali yana waige-waige, ya ga ko zai hango wani a gurin, da ko shi ne ya bayar da rahoton zuwan matashin, amma bai ga kowa ba. Zuciyarsa ta raya masa haɗin baki ne, ana sane aka turo shi, dan a gani ko zai faɗi wani abu ko ba zai faɗa ba. Ya sanya hannu ya ɗauki Alqur'aninsa ya tafi yana ta istigfari.
*****
Tana tsaye daga nesa da shagonsa kaɗan, ya buɗe ƙofar ya tsaya yana kallonta. Doguwar riga ta saka, da wani ɗan ƙaramin mayafi, hannunta riƙe da flask ɗin Abinci. Tun kan ta ƙarado, ƙamshin turaren da take yi, ya karaɗe ilahirin gurin. Ta saka jam baki a bakinta, idanunta kuma ta saka kwalli.
"Ɗan Albarka"
"Mmm 'yar ƙwalisa"
Ta yi murmushi ta ce "Bacci ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
"Me ki ka dafa mana ne yau?"
"Buɗe ka gani" Ta yi maganar tana miƙa masa flask ɗin Abincin, ya karɓa ya buɗe, ya ga tuwon shinkafa da miyar wake. Ta miƙa masa ledar hannunta ta ce "Ga zoɓo mai muslmin sanyi kuma"
"Na gode sosai 'yar ƙwalisa"
Cikin jin nauyinsa ta ce "Nima na gode, sai anjima"
Ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Ina kuma za ki je?"
"Zan je titi ne sayo wa Antynmu abu"
"'Yan mata mayafin nan ya yi ƙarami fa, ana ganin jikinki. Kuma ga shi kin yi kyau sosai da sosai"
Ta rufe fuska ta ce "Dan Allah ka daina bani kunya mana"
"Hmm ba kunya nake baki ba, gaskiya na faɗa, kuma mayafin nan ya yi kaɗan, ba ki san kin fara girma bane?"
Ji ta yi tamkar ta nutse saboda kunya da ta mamaye ta. Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Yanzu zan dawo fa" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓe.
"A dawo lafiya, na gode sosai da abinci" Ta juya ta tafi, ba tare da ta sake cewa komai ba.
Yana zaune bayan ya gama cin abincin, ya jiyo hayaniya a waje, sarai ya ɗauki muryar Isma'il sai bala'i yake yi, har ya basar saboda ya riga ya fuskanci Ismail masifaffe ne lamba ɗaya. Sai dai tuna cewa ba a jin kansa, idan ba Alina aka taɓa ba, ya sanya ya tashi da sauri ya leƙa.
Aikuwa kamar yadda ya yi tsammani, wani matashi yake yi wa hargowa, tun daga titi ya gano shi, ya bi Alina yana yi mata ɗan kira, ya biyo su a babur sai da suka shigo cikin layi, ya rutsa su yana zazzaga wa matashin bala'i. Tuni mutane suka taru su na ba wa Isma'il haƙuri. Alina kuwa yanayin fuskarta ya nuna rashin jin dadin tijarar da yake yi wa matashin, ga jama'a ya tara musu, sai ɗaga murya yake yi. Takaici ya sanya ta wuce gida ta bar su a gurin.
Da kyar aka ba shi haƙuri, matashin ya tafi.
Mamman ya girgiza kai kawai yana murmushin gefen baki.
Kamar guguwar baƙin hadarin kaka, haka Ismail ya shigo gidan yana ci gaba da bala'i.
"Wallahi Alina idan ba ki kiyaye ni a kan gayyar mazan nan da suke bibiyarki ba, a gabansu zan naɗa miki duka wallahi. Ke ba ki san halin da ƙasar nan ke ciki ba na rashin tsaro, kowa ba abin yarda ba ne, amma da yake kin fi kowa mutunci kowa sai ya biyo ki yana yi miki surutun banza kina washe baki, mara hankali kawai da ba ta san ciwon kanta ba"
"Yaya wallahi ban san shi ba, biyo ni kawai fa ya yi"
"Rufe mini baki ina magana kina magana" Yadda ya yi maganar cikin ƙaraji, ya sanya babu shiri, ta shige bayan Nadiya tana ɓuya.
"Ki ci gaba kar ki fasa. Wataran sai kin janyo mana abin da ya fi ƙarfinmu, ko tilasta mana komawa inda muka fito yadda mu ma za a kashemu kamar yadda aka kashe iyayenmu. Shi kansa wannan ɗan iskan da ki ka saki jiki da shi kamar ubanki, ki ka liƙe masa kallonki kawai nake yi. Gaba ɗaya mutumin nan da ganinsa ka san munafuki ne ba shi da gaskiya. Ƙirarsa da idonsa duk na miyagun mutane ne, babu ta inda ya siffantu da wani almajiri, amma kin liƙe masa, na rasa uwar da yake gaya miki. Amma za ki ga matakin da zan ɗauka a kanku"
Alina ta fashe da kuka, Nadiya ta rungume ta ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Ki daina kuka rabu da shi, ya yi faɗansa ya gama, kar ma ki sake kare kanki, ƙyale shi"
Bayan fitar Ismail Alina ta ce "Antynmu ni shikenan haka zan zauna, yaya ya korar mini ƙawaye, ya hana ni hulɗa da kowa? Kuma wallahi Mamman mutumin kirki ne, ai kema kin san ba zan je inda zan lalace ba, ai ina bin nasiharku ba zan baku kunya ba. Kuma ni ba saurayina bane"
"Na sani Alina, amma duk wanda zai so mu, ba zai kai yadda Yaya yake sonmu ba. Duk abin da yake yi, yana yi ne, domin ya bamu kariya kar wani abu ya cutar da mu, ki yi haƙuri wataran sai labari" Alina ta jinjina kai.
"Alina" Nadiya ta kira sunanta tana nazartarta.
"Na'am"
"Son Mamman ki ke yi ko?"
Alina ta ɗago da sauri ta ce "So kuma? Haba Antynmu, ni wallahi ba son shi nake yi ba, kina ganin mutuncin da yake yi mini, ni kawai dai mun saba ne. Yana da kirki kuma yana koya mini karatu"
Nadiya ta jinjina kai tare da yin murmushi ta ce "Shikenan tashi ki je"
Ismail kuwa yana dawowa daga sallar isha'i, ya manta da faɗan da ya yi wa Alina, sai da bai ganta a tsakar gida ba, ya tambayi Nadiya ta tuna masa ai ta yi bacci tun faɗan da ya yi mata.
Bayan kiran sallar asuba na farko, Mamman ya buɗe ƙofar ɗakinsa domin kama ruwa ya yi alwala, kawai ya yi tozali da Isma'il a tsaye kamar bayyanar aljan.
A tsorace ya ce "Lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Isma'il.
"Ba lafiya ba, gurinka na zo"
Ya ajiye butar hannunsa, ya ce "Allah ya sanya ba laifi na yi ba"
Ismail ya ce "Na je gurin mutumin da aka ce ka yi karatu a hannunsa, ya tabattar mini da kai ɗalibinsa ne, sai dai Haryanzu ni ban ji na yarda da kai ba. Amma na san komai girman gona akwai kunyar ƙarshe. Na fuskanci amfani da ƙarfi gurin raba ka da kanwata, zai iya zama cutarwa a gare ta, ka yi amfani da yaudara ka sanya kusanci tsakaninka da ita. Kuskure mafi girma da za ka yi shi ne fara soyayya da Alina, na kuma fuskanci idan ban yi da gaske ba abin da zai faru kenan. Ka sani akwai layin da idan ka ƙetara a kan Alina zan iya sadaukar da rayuwata na yi zaman prison na har abada saboda ita"
Mamman ya kalli Ismail ya yi murmushi ya ce "Ban san dalilin da ya sanya ka tsane ni har haka ba. Ni da Alina zaren ba kalar yadin bane ba, kawai mutumtaka ce a tsakaninmu. A ɓangarena na yi maka alƙawarin, kare martabar Alina, ba zan faɗa soyayya da ita ba, sai dai ban yi maka alƙawarin hana ta sona ba" Wani mugun kallo Ismail ya yi masa ta hasken fitilar solar gurin, ya yi ƙwafa ya juya ya bar gurin.
Gari ya fara haske, Ismail ya yi sallama a ƙofar ɗakin Alina, ta amsa masa murya ƙasa-ƙasa. Ya ɗaga labule ya shiga. Ta tashi zaune daga kwancen da take, ya zauna a gefen katifarta yana kallonta.
"Alina fushi ki ke da ni, ko gaisuwa ko?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a zan gaishe ka, tsoro nake ji, kar na je wani laifin na sake yi ne"
Ya ɗan jinjina kai, tare da kaɗa ƙafafuwansa da ya miƙe, ya ce "Ƙanwata, na san maybe kin yi fushi da Yaya, amma duk abin da Yaya yake yi, ƙoƙari yake bawa halittu mafi soyuwa a gare shi kariya, wato Fatima da Nadiya, a duniya yanzu ba ni da kamar ku, gurin baku kariya daga duk abin cutarwa, sai inda ƙarfina ya ƙare.
Ke yarinya ce Alina, haryanzu ba kya banbance mene ne daidai da akasin haka, kuma kina kan shekaru mafiya hatsari na ruɗin ƙuruciya, zuciyarki a buɗe take, duk abin da ya yi mata daɗi, ko ya burge ta, karɓa za ta yi. Shiyasa nake taka tsantsan gurin tantance miki aya da tsakuwa. Ni gaba ɗaya mutumin nan bai yi mini ba, yana da sifofin munafukai marasa gaskiya. Amma ba na son ɓata miki rai shiyasa nake ta saka muku ido. Ki yi haƙuri faɗan da na yi miki, amma ki yi a hankali kar ki kawo mana abin da zai kawo mana barazana ga kwanciyar hankalinmu."
Har ya yi magana ya gama, Alina ba ta ce uffan ba, ya tashi ya fita.
Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, ba ta son abin da za ta ɓata wa yayanta rai, amma gefe guda sun shaƙu da Mamman, rana tsaka ta daina kula shi ba ta kyauta ba. Ga shi gaba ɗaya cikin abin da bai fi wata ɗaya da satuttuka ba, suka yi wannan shaƙuwar.
*****
Ruƙayya ce ta ƙura wa Rahama ido, yadda take ta juya abu a kofi ta kasa sha.
"Rahama ya ne? Me yake damunki ne?"
Ta ɗago ido ta kalli Rukayya, ta sunkuyar da kanta.
"Ke kalle ni, mene ne?"
Ta girgiza kai alamar, babu komai.
"A'a da komai, mene ne?"
"Baffa bai zo ba, bai kuma kira kowa ba a gaya mini dalilin rashin zuwan nasa, a tsorace nake" Ta ƙarasa maganar hawaye na cika mata ido.
Ruƙayya ta ce "Haba Rahama, wataƙila wani abin ne ya hana shi zuwa, amma da yardar Allah zai zo"
Rahama ta ɗan rausayar da kai ta ce "Duk da ƙaunar makaranta da nake yi, a duk lokacin da na taho, hankalina a tashe yake. Saboda rashin sanin abin da yake faruwa a garinmu. Garinmu babu cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali".
Rukayya ta dafa kafaɗarta ta ce "Babu abin da yake faruwa sai alkhairi. Share hawayenki ki gama ci, ki zo mu je Clinic akwai marasa lafiya" Ta jinjina kai ta kammala abin da take yi suka bar Hostel ɗin.
A clinic ɗin suka tarar da wata ɗaliba da ƙofa ta ji wa rauni, zai yi mata ɗinki. Yana ganin Rahama ya hau murmushi ya ce "Ai yanzu nake saka ran na aika a nemo mini ke, na ga yau ban ganki ba"
Ruƙayya ta ce "Yaushe za ka ganta, tana can tana shagwaɓa, wai Baffa bai zo mata visiting ba, tun da yan gidanmu da suka zo mata dodanni ne"
Ya ɗan yi dariya ya ce "Ai ba a shiga tsakaninku, ina ga idan ki ka yi Candy sai kin jira Rahama"
"Wannan dole ne" Ta yi maganar tana dariya ta wuce ɗakunan da ake ajiye ɗalibai idan ba su da lafiya"
Rahama kuma a gefen Likitan ta zauna, tana ci gaba da yi masa tambayoyi kamar yadda ta saba.
*****
Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, yana tsaye a jikin tagar ɗakinsa, yana shan sigari, ya sha ta kai uku. Sannan ya dawo ya canza kayan jikinsa, zuwa shirt da dogon wando, ya samu wani mayafi, ya rufe fuskarsa, ya ɗaga ƙasan fulonsa, ya ɗauki abun da zai ɗauka, ya ɗau ƙaramar wayarsa, da wata wallet, ya rufe ɗakin ya fita.
Da safe Ismail na kallon Alina nata rawar jikin kai wa Mamman Abincin safe, wanda da wani abin ne ya nuna baya so, da tuni ta bar abin, amma nasihar da ya yi mata ba ta shige ta, dan bai ga alamar za ta ja baya da hulɗa da mutumin nan ba. Shi dai fargabarsa ɗaya kar Alina ta faɗa soyayya a shekarun ƙuruciya, mussaman da mutum irin wannan da haryanzu ya kasa nutsuwa da shi.
Ba ta fi mintuna uku da fita ba ta dawo, tana faɗin "Antynmu ga Abincin Mamman, baya nan ko ina ya tafi da sassafen nan, idan ya dawo ya ƙwanƙwasa miki ya karɓa, ko ki aika masa idan ɗan malam ya zo karɓar nasa" Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar jakarta.
"Yayanmu na tafi" Ya ɗaga kai ya kalle ta, ya yi shiru bai amsa ba.
Ta ɗan tsaya cak tana kallonsa, ta sake cewa "Yaya na tafi"
"Sai kin dawo" Ya furta a taƙaice, jiki a sanyaye, Alina ta fita. Sai ta ji gaba ɗaya duniyar ta yi mata babu daɗi, ganin fushi da damuwa ƙarara a fuskar Yayanta.
*****
Rahama na zaune a class ɗin su, kasancewar lokacin prep ne, tana zaune tana karanta wani littafi, da yake ƙunshe da yadda turawan mulkin mallaka suka mamayi Afrika, da sace musu wasu daga kayan tarihinsu, da kuma mallke musu kadarorinsu. Kawai ta din ga jin zafin abubuwan da suka gudanaz saboda yadda ta yi zurfi a karatun gani take kamar a gabanta abin ya faru.
"A Yelwa" da sauri ta ɗaga kai.
Prefect ɗin da ta kira sunanta ta ce "Ki je ofishin pc ana neman ki"
"Tom"
Ta amsa tana tattare litattafanta tana zuba wa a cikin jakarta, ta yinƙura ta tashi ta fita. Hannunta na cikin hijjabinta tana tafiya a hankali.
Muryar Baffa ta jiyo, su na magana da principal ɗin su. Da sauri ta ƙarasa cikin ofishin. Murmushinta ya gaza ɓoyuwa. Ta gaisa da Principal sannan Baffa ya fito suka keɓe.
"Baffa na zata ba za ka zo ba, hankalina a tashe na fara tunanin ko wani abin ne ya faru a gida"
Jikin Baffa a sanyaye ya girgiza kai ya ce "Babu abin da ya faru, sai dai tsoron faruwar tasa ne ya sanya na kasa zuwa ko ina."
Rahama cikin kaɗuwa ta ce "Baffa mene ne?"
"Ramata dama akwai wata alaƙa a tsakanin ki da yaran manoma ban sani ba?"
Ras gaban Ramata ya faɗi, ta hau tambayar kanta, ya aka yi Baffa ya sani, duk ɓoye-ɓoyen da take yi.
"Kin yi shiru Ramata, ke yanzu ba kya duba mana halin da muke ciki ko? Sai kin janyo ke kaɗai ɗin da ki ka rage mini, kema na rasa ki ko wata fitinar ta tashi ko?"
Ramata ta yi ajiyar zuciya, ta gyara zamanta ta ɗan kalli Baffa ta sunkuyar da kai ta ce "Baffa abin da ka faɗa ba ƙarya ba ne, Bukar ya daɗe yana bibiyata tun ƙawancen da nake yi da Hanne. Sai dai na saki jiki na