Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
masu cewa kuɗi ake ba ni, nake kare gwamanti. Ni babu wanda ya bani kuɗi na kare gwamanati, hasali ma ba a san da zamana ba.
Son da nake yi wa shugaban ƙasa ya faro ne, silar sunansa ɗaya mahaifina marigayi DSP Faruk Kankiya. Wanda ya rasa rayuwarsa shekarun baya, bayan artabunsa da 'yan fashi, wanda wani case ne daban. Tun Mr. President yana riƙe muƙami a matakin jiha nake son sa, Saboda son da nake yi wa mahaifina aka kashe shi, kuma 'yan fashin da ya kama aka sake su.
Har Mr. President ya zama shugaban ƙasa, ina bibiyar lamarin siyasar sa, ina son shi, yana burge ni, kuma halayensa sun yi kama da mahaifina a wasu ɓangarorin.
Ba zan iya daina son sa da ba shi goyon baya ba, son zuciya ɗabi'ar zuciya ce, ba zan iya kushe shi dan na faranta muku ba. A ƙarshe ina baku haƙurin, duk wanda baya son abin da nake yi ya yi haƙuri, ya daina following ɗina, roƙona ɗaya ku daina zagin Abbana dan baya raye. Mr. President kuma har abada bana fatan ko shi ko muƙarabbansa, wani ya maganta mini sisinsa ba na buƙata. Shugaba ne da nake wa kallon Uba, zan yi masa addu'a Allah ya yi riƙo da hannayensa kuma zan ci gaba da goyon bayansa ɗari bisa ɗari".
Mama na wanke-wanke a tsakar gida, ta ji ana ta ƙwala sallama a ƙofar gida.
"Waye?" Ta yi maganar tana kallon hanyar soro.
"Bala ne"
"Shigo" Ta amsa tana ɗauraye plate ɗin hannunta.
Ya shigo yana sake sallama ta amsa masa tana faɗin "Dama kai ne ka maƙale a waje ka na kwaɗa sallama?"
"Wallahi kuwa, mutuniyar fa?"
"Ta je karɓo caji"
Ya zauna a kan tabarmar da ke shimfiɗe, ya ce "Bari na jira ta"
Su na cikin hira, Laila ta dawo, tana ganinsa ta yi murmushi ta ce "Balansy"
Ya ɗan tsuke fuska ya ce "Dalla zauna, mai abin haushi" Ta tsuke fuska ta ce "Me na yi?"
"Videon da ki ka wallafa ɗazu mana, uban wa ya aike ki? Ina ruwanki da wasu masu Comment da zagi, ko dai ki rama zagin ko ki ƙyale su"
Ta sake ɓata fuska ta ce "Ni ba zan zama 'yar balaja'u na din ga zage-zage ba"
Bala ya ce "Ina ruwanki da wani balaja'au in dai za ki samu kuɗaɗenki? Next week akwai yiwuwar dollar ta ƙara tashi, sai ki cire kuɗinki"
Ta yi murmushi ta ce "Kai ka ce ina cikin alkhairi, nawa zan samu?"
"Kusan dubu ɗari da hamsin a ƙiyasi, sai dai yadda ta kaya. Ke ba wannan ba, na ji wai-wai, shugaban ƙasa zai zo garin nan, jajen abin da ya faru na ɓatan matan nan, idan hakan ta tabatta dole ki halarci gurin nan, duk yadda za mu yi, ko hoto ki yi da shi"
Ta waro ido ta ce "Dan Allah? Ni ba sai na yi hoto da shi ba, ko ganinsa kawai na yi"
Mama da ke kitchen ta ce "Bala me ka ke ƙulla mata, ba dai wata tsiyar za ka saka ta kuma aikatawa ba ko? Kun yi ƙulle-ƙullen da sai da ta rasa aikinta, yanzu kana kitsa mata wani abin, ni dai kar ku janyo abin da za a zo har gida a same mu, mu shiga uku ina lallaɓa rayuwata"
Bala ya ce "Hajiya Mama ba za ki gane ba, idan Allah ya ɗaga likkafar Laila, sai kin manta duk wata wahala fa, za ki sarara"
Sadam ya fito daga ɗakinsa, fuskarsa duk alamun bacci ya ce "Maƙaryaci, wace likkafa kullum cikin wahala ku ke, ba kwa samun ko sisi, sai ma kuka da baƙin ciki da take kwasa"
Bala ya ce "To ina ruwanka? Duk ranar da Allah ya sanya ta fashe mana, muka sha kwana zaka sha mamaki. Mu na nan zamu fara wallafa ayyukanmu a jaridarmu mai zaman kanta ta online".
Saddam ya yi tsaki ya ce "Jaridar bugaggu ba"
Bala ya ce "Laila, kar gwiwar ki ta yi sanyi, za mu ba su mamaki da yardar Allah"
Ta yi murmushi ta ce "Ba zan gajiya ba, ba kuma zan sare ba in sha Allah"
*****
Can a daji kuwa, Rahama tana yashe a ƙasa, su maharan ba su bari an taɓa ta ba, kuma ba su taɓa ta ba.
Ɗaya ne daga cikinsu ya saka ƙafarsa yana taka tata. A hankali ta motsa, ta buɗe idanunta da suka yi mat nauyi, sai dai ta ji kanta kamar ba nata ba. Ga shi ba ta gani sosai sai dishi-dishi. Ya yin da ƙafar da maciji ya sare ta, take jin ta tamkar ba a jikinta take yi ba. Ga jikinta sanyi ƙalau.
Ganin ta motsa ya sanya ya durƙusa a kanta yana kallonta. Ta kalle shi da kyar, amma ta kasa motsi. Ya yi wani irin murmushi yana lashe laɓɓansa, ya miƙa hannunsa jikinta yana faɗin "Ashe dai da sauranki ba ki yi mushe ba?" Ya yi maganar yana neman ɗage mata riga a gaban mutane. Tafasar da zuciyarta ke yi, ya bata wani irin ƙwarin gwiwa da niyyar ta hankaɗe shi, amma tana ɗaga hannunta ya koma ya faɗi.
"A'a Halliru, kar ka yi wa yarinyar nan wani abu, kar Sadauki ya zo ya yi mana hauka"
"Shhh" Ya yi maganar yana kallon Salisu, da fuskarsa ke bayyanar da tsoro.
"Ba zai yiwu a bawa kura ajiyar nama a hana ta ɗanɗanawa ba" Ya yi maganar yana ɗago Rahama, yana kallonta cikin murmushi.
"Kai ba fa zai yiwu ba, idan na gama sai mu ƙarasa ta, mu ce saran macijin ne ya kashe ta kawai" Ya yi maganar idanunsa na yin ja, jikinsa na rawa, saboda sosai yake ƙarewa jikinta kallo, mussaman da kullum cikin takurewa take.
Ayshercool
08081012143
Mun kusa Kammala free pages.
1k ne a telegram via 0069685771
Aisha Adam stanbic
Sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira sai an kammala 1500 za su biya.
AMANA KAYAN MATAN
Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara
Gumbar mata
Gumbar aya
Gumbar chaku
Gumbar dake saukar da ni'ima
Gumabar taƙadari
Gumbar riɗi
Gumbar dabino
Gumbar uku alkhairi
Kazar amare
Jijjiɓen saniya
Tabaje
Tsimi
Rikita mai gida
Jigidar tada sha'awa
Ruwan boom ruwan daɗi kenan
Ɗan matse
Karya gado
Maganin sanyi
Zumar ƙarin ni'ima
Zumar rage ƙiba
Zumar ƙarin ƙiba
Zumar riɗi
Mai zamani
Emergency powder
Tarhama
Kafi budurwa
Sabon budurci
Alfijir
Gamzaki
Garin dahuwar nama
Sabaya
Miskin ɗahara
Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
*ALBISHIR ALBISHIR ALBISHIR*
*Jama'a Albishirinku, mun sake shirya tsaf domin kawo muku advance class, na koyar da sana'oi da muka yi firts batch, ga mu mun dawo domin kawo second batch, wanda zai kasance Advance class a kan na farko da muka gabatar*
*Ki na son fara sana'a, kin rasa yadda za ki yi? Ko kuma jarinki ne kaɗan kin rasa wace sana'ar za ki yi? To wannan classes ɗin naku ne, ku garzayo ku yi rijista domin kar a yi tafiyar nan babu ku. Daga sana'oin da za a koyar sun haɗa da;*
1. Graphic design
2. Magungunan mata
3. Sabaya
4. Turaren wuta
5. Fara
6. Candies
7. Skin care products
8. Importation
9. Snacks
10. Yoghurt
11. Oil perfumes
12. Bead work
13. Hair cream/oil
14. Dabarun kiwon kaji
15. Huluna
16. Spice's
17. Dabarun sana'ar kayan kitchen
18. Noma a zamanance
19. Dabarun kasuwanci
Dama ƙarin wasu, ga masu buƙatar sanin yadda tsarin yake kai tsaye su tuntuɓi wannan lambobin.
08081012143
07037977211
08069611181
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
SARA DA SASSAƘA
YOTA 002
AYSHERCOOL
Page 14
Cikin sauri Sabi'u ya saki Rahama ya tashi, saboda jin ƙarar babur a bayansu, ba tare da jin sautin tahowarsa ba.
Ya sauka daga kan babur ɗin, sauran 'yan bindigar suka nufo shi, su na yi masa barka da zuwa, ya miƙa musu bindigarsa suka karɓa.
Ya ƙarasa inda Ramata ke yashe kamar abin banza, ya saka hannunsa ya ɗago ta zaune. Ya kalli leɓenta ya bushe, jikinta sanyi ƙalau. Sai motsa hannunta take yi, tana ƙoƙarin kare jikinta.
Ya dubi ɗaya daga wanda suka zo tare, ya ce "Ba ni abin nan" Ya ƙaraso ya miƙa masa wata 'yar ƙaramar kwalba. Ya kwance ta ya ɗaga bakin Rahama ya zuba mata abin da yake cikin kwalbar. Mintuna kaɗan ya ɗaga ta zaune, aikuwa ta fara sheƙo amai babu ƙaƙƙautawa, ta galabaita sosai, sai da ya fuskanci ta gama sannan ya ja ta ya jinginar da ita a jikin bishiya. Sai haki take yi tana sauke numfashi.
"Kina jikar makiyaya, ya aka yi ba ki sha maganin dafin maciji ba?" Ta yi shiru tana bin sa da kallo a galabaice.
Ya kalli inda ƙafar da macijin ya sare ta, ya fara kumbura. Ya ciro wata aska ya tsaga gurin, ya tsare ta da idanunsa, da idan ta kalli idon nan nasa da ya sha farin kwalli sai tsoro ya kama ta. Ya durƙusa ya kafa bakinsa a dai-dai gurin. Ji ta yi tamkar yana fizgar wani abu a cikin jikinta. Wani irin wahalallen kuka ta din ga yi jikinta na karkarwa, tamkar za ta shiɗe. Ya ɗago ya buɗe kwalbar da ya bata magani a ciki, ya zuba abin da yake cikin bakinsa. Abun baƙi ƙirin babu kyawun gani.
Ya dube ta ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah macijin zai kawo kansa, za ki ga hukuncin da zan yanke masa. Ya yi maganar yana goge mata gumin da ya tsatstsafo a goshinta. Ya ciro hiramin da yake rufe fuskarsa da shi, ya yagi wani sashi a jiki, ya kama ƙafar saman gurin da ya cije ta ya ɗaure.
Ya sa aka kawo masa ruwa, ya ba ta ta sha, ta rage tana daga zaune ta yi alwala, ta yi sallar asuba a haka a yadda take zaune.
Yana tsugune a gefenta, ta idar aka ba ta waina a cikin leda fal da ƙuli-ƙuli, ta riƙe wainar a hannunta, ta ɗaga kai tana kallon sauran 'yan uwanta da suke tsare tare, sannan ta kalli Sadauki.
"Nasu abincin yana hanya, idan ba ki ci naki ba, maganin da ki ka sha zai iya halaka ki"
Hannunta na rawa, ta gutsiri wainar, sai dai ta riƙe a hannunta, tana sinne kai ta kasa ci. Ya yi murmushi ya matsa gefe ya kawar da kansa daga kallonta, sannu a hankali ta fara kai wa bakinta tana ci, tamkar tana cin magani.
Sadauki ya ɗan waiwaya ya ce "Sabi'u zo ka karɓi kwalbar nan, ka ajiye mini zan yi aikinta na kama macijin nan" Ya yi maganar yana miƙa masa kwalbar da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma ya zura a cikin Aljihunsa.
Sabi'u ya ƙaraso ya kawo hannu zai karɓi kwalbar. Sadauki ya janye kwalbar, Sabi'u ya sake ƙarasawa zai karɓa, amma Sadauki ya fito da ɗaya hannun nasa riƙe da bindiga ƙirar pistol ya harbe shi har lahira. A take da yawa daga cikin ɗaliban suka saka ihu cike da tsoro. Jikin Rahama kuma ya hau rawa ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi saboda jinin sai dai ya ɓata mata fuska. Idanunta da suka yo waje suka ƙara bayyanar da tashin hankalin da ta shiga. Sadauki ya ɗan tsura mata ido, ganin yadda numfashinta ke kai komo a ƙirjinta.
Ya sake ciro hiraminsa ya kamo fuskarta, ya fara goge mata jinin yana faɗin "Yi haƙuri na tsorata ki ko? Ya aka yi jinin makiyaya ta kasance cikin matsorata ne? Mu fa ba matsarota bane ba a sammunda tsoro ba" Ya yi maganar yana ci gaba da goge mata fuskarta.
Ya sakar mata murmushi ya ce "Kar ki yi mini mummunar fahimta fa, ni mutumin kirki ne" Ita kuwa ba ma ta gama iya tantance a wani yanayin take ciki ba, balle ta fahimci me yake faɗa. Sai da ya gama goge mata jinin sannan ya miƙe tsaye, ya murtuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba ya ce "Wannan shi ne abin da zai biyo bayan duk wani wanda ya yi yinƙurin aikata halin ɗan taure a tsakanin yaran nan. Kai Gulafa, ku je ku binne shi, kai kuma je ku ƙarasa aikin da na saka ku ku yi mini, saboda zan din ga zagayowa ba tare da na sanar muku ba.
Ya kalli sauran 'yan matan ya ce "Ku kuma ku kwantar da hankalinku, na gaya muku babu wanda za mu cutar" Ya saka hannunsa ya cire babbar rigar yadin da take jikinsa, ya durƙusa ya saka wa Rahama da har a lokacin jikinta bai daina rawa ba. Ba ta iya motsawa ba har ya gama saka mata, shi ma kuma bai sake ce mata komai ba. Ya nufi baburinsa ya hau, suka miƙa masa bindigarsa ya karɓa ya tafi.
*****
Laila ce a zaune, ta duƙufa a kan wayarta, hannunta ɗaya riƙe da biro da takarda tana rubuce-rubuce.
Mama ta shigo ɗakin ta tsaya a kanta ta dube ta cike da takaici ta ce "Wai Laila uban me ki ke yi ne a kan wayar nan?"
Laila ta yi miƙa ta ce "Mama aiki nake yi"
"Aikin banza ba, awa ashirin da huɗu, kullum idonki a kan waya, ina jin wani likita na magana a radio, ya ce ba da jimawa ba idanun matasan yanzu duk zai mutu, saboda azabar kallon waya."
Laila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Bincike nake yi ne, neman kuɗi nake yi da wayar nan Mama, dan Allah ki bani dubu ɗaya zan je wata unguwa ne"
Mama ta dube ta sheƙeƙe ta ce "Shegiyar wayar taki da ki ke wuni a kanta, ki ke neman kuɗin da ita, ba ta kawo miki dubu ɗayar da zaki yi yawon ba"
Laila ta yi murmushi ta ce "Hajiya Mama kenan, bari na yi wanka na je Cafe ɗin su Saddam, na san ko ya gama yi mini gori zai bani"
"Tsaya tukuna ma ina za ki je?"
Laila ta hau murmushi ta ce "Ba daɗewa zan yi ba, zuwa zan yi na dawo"
"Tambayarki na yi, ina za ki je?"
Laila ta ci gaba da murmushi ta ce "Mamansy, kin san ba zan je inda zan ɗaukko miki magana ba"
"To wallahi idan ba ki gaya mini ba, ba za ki fita ba"
Ta ɗan sunkuyar da kanta, jiki a sanyaye ta ce "Mama zan koma batun filinmu ne, ina ci gaba da bibiya, idan ba za su yi mana adalci ba, akwai yiwuwar na wallafa rubutu a kan lamarin"
Mama ta nemi guri ta zauna ta dube ta ta ce "Laila, na san an cutar da ku. Wannan filin shi ne abin da muka tsira da shi da wannan gidan, tun da an yi ƙarfa-ƙarfa a kan filin nan ki yi haƙuri kawai. Tun da mun tsira da gidan nan shikenan. Kin ga ɗan uwanki da na ba shi baki ya haƙura, to kema ki bar wa Allah kawai"
Laila ta sunkuyar da kanta, sannan ta ɗago kanta idonta duk hawaye ta ce "Mama shikaɗai fa muka tsira da shi, kina gani hakkin babanmu abokansa suka ci abin da suka ga dama, suka bamu wanda suka ga dama. Kuma filin da aka saya mana tsawon lokaci, mu na saka ran mu na da kadara mai tsada a ajiye, rana tsaka gwamnati ta ƙwace an bamu diyyar da bata kai rabin kuɗin kadararmu ba. Kuma an saya mana wani filin shi ma wasu su mallake su ce nasu ne, mu zuba ido"
"Laila ya za mu yi tun da sun fi ƙarfinmu? Da aka ƙwace filayen mun daina rayuwa ne? Muka rasa mahaifinku ma balle wani fili, mu bar wa Allah kawai. Albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da Alqur'ani filaye idan mu na raye sai dai ku bawa wani kyautar su ma, mu bar wa Allah kawai"
Ba haka Laila ta so ba, amma gudun ɗaga wa Mama hankali, ya sanya ta jinjina kai ta nuna mata cewar komai ya wuce.
*****
Ɓangaren Alina, abubuwa sun ƙara rikice mata, yadda ta kai ba ta iya sarrafa kanta sosai. Hankalin Nadiya ya tashi sosai, dan Alina ta kwanta rashin lafiya, saboda damuwa wannan ciwon kan ya tayar mata. Ga shi a duk lokacin da ta yi yinƙurin gaya wa Nadiya abin da ya faru, sai ta ji ba za ta iya ba, gani take yi kowa sai ya zarge ta da laifin faruwar komai dalilinta, dan babu irin kashedi da jan kunnen da Yaya bai yi mata ba a kan Mamman.
Tun safe Alina ke kallon Nadiya daga kwance, tana harhaɗa musu kayansu a bagco.
Ta dubi Alina cikin kulawa ta ce "Sannu ƙanwar Yaya"
Alina ta jinjina kai ta ce "Anty ina zamu ne, na ga kina haɗa kaya?"
"Tafiya zamu yi" Ta bata amsa.
"Ina za mu je?"
"Garin nan zamu bari"
Cikin rashin fahimta Alina ta ce "Mu je ina? Idan yayan ya dawo kuma fa?"
Nadiya ta ce "Alina kin fiye tambaya, ki zuba ido za ki gani, ci gaba da zamanmu a nan ba shi da wani amfani, Yaya kuma duk inda muka shiga, in dai ya dawo zai neme mu"
Alina ta sake cewa "Ta yaya zai san ina muka tafi, ko kin san inda yake ne?"
"Alina, ki kwanta