Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
ba shi dama ne, ba domin komai ba, sai dan na san wacece wadda ake zargin Ironmu a kanta, na tattara hujjar da zan bi hakkinsa" Ta ƙarasa maganar tana kallon Baffa.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ramata yaushe ki ka koyi baƙin taurin kai haka? Ni da nake ubansa na haƙura na fauwwala wa Allah, ke da ba ke ki ka haifar mini shi ba, ki dage sai kin ɗauki mataki, a gurin wa za ki ɗauki matakin? Ramata kar ki ɓata mini rai , ki yi abin da za ki janyo mana tashin hankali, ba zan iya kirga iya tashin hankali da barazanar da na gani a rayuwata a zamana a garin nan ba, yakamata na huta haka"
Rahama ta yi shiru tana goge hawaye, saboda yadda komai yake dawo mata tun daga cikin kwanyarta har zuwa cikin idanunta. Baffa ya koma yi mata nasiha, ya bata abin da ya riƙo mata ya tashi ya tafi.
Gudun kar hankalin malamansu ya dawo kanta, a zo ana tambayarta lafiya, ko su zata kukan tafiyar Baffa take yi, su yi mata faɗa, dan haka ta goge hawayenta ta tashi ta tafi. Sai dai da aka tashi daga prep, ta kai kayan kwanarsu ta ajiye, ta tafi keɓanttacen guri ta zauna tana tunani.
Tabbas tana son bin jinin ɗan uwanta, amma ta fuskanci yanayin shari'a a ƙasar nan ka na buƙatar ilimi, kuɗi da kuma hanya, idan ba haka ba wahalar banza za ka yi ta sha, idan ba Allah ya tarfawa garinka nono ba. Mussaman ita da ga ƙarancin shekaru kuma ba ta da tabbacin samun cikakken haɗin kan mutanen garin, kowa cewa zai yi babu ruwansa saboda tsoron manoma da ake ji a garin.
*****
Yana riƙe da leda a hannunsa, yana ƙoƙarin shiga layin, ya ga daidaita sahu na ƙoƙarin fitowa, da Alina a ciki a kwance a jikin Nadiya. Da sauri ya tare a daidaita sahun ya riƙe ƙarfen yana kallon Nadiya ya ce "Lafiya kuwa?"
Nadiya ta ce "Alina ce babu lafiya za mu je Asibiti"
A ɗan rikice ya ce "Subhanallah, Asibiti kuma meya same ta"
Cikin basarwa Nadiya ta ce "Tana da ciwon kai mai tsanani ne, mai Napep mu je, kar ta ci gaba da galabaita" Mai baburin ya ja suka tafi. Mamman ya tsaya yana bin adaidaita sahun da kallo, da tunanin ina yayanta za su tafi Asibiti sukaɗai? Kuma kwanaki uku kan ya yi balaguron da ya yi, lafiyarta ƙalau.
Wayarsa ya ɗaukko mai madannai, ya daddana, sannan ya ƙarasa shagonsa ya shiga.
Ya gama abin da zai yi ya fito ya zauna a bakin hanya, ko zai ga dawowarsu, amma bai gani ba, dan ya yi mamaki a yadda yake da Alina, babu yadda za a yi ya yi magana ba ta ɗago ba.
Wata maƙwabciyarsu, da take jikin gidansu Alina, ya gani ta fito daga layin, ta riƙo kwando da kwanukan Abinci. Ya tashi ya ƙarasa, suka gaisa. Ya ce "Dan Allah Asibiti za ki jegurin su Alina?"
Ta ce "Eh zan kai musu Abinci ne"
Cikin damuwa ya ce "Subhanallah, wane Asibitin ne?"
"Bright ne, a can suke kwanciya idan ba su da lafiya"
"Dan Allah kar ki ce na dame ki, dama tana yawan rashin lafiya ne?"
Maman Hanan ta ce "Gaskiya dai dan kwana biyu ma Alina ta yi lafiya, amma tana da yawan rashin lafiya"
Ya jinjina kai ya ce "Shikenan na gode sosai"
Alina na kwance a kan gadon Asibiti, Idanunta a lumshe, ɗakin an kashe fitila, saboda ba ta son haske, idan ciwon kan ya tayar mata.
"'Yar ƙwalisa" Ya kira ta a hankali.
A hankali ta motsa ta buɗe idanunta a saboda hasken fitilarsa da ya haske mata fuska. Sai dai idonta ya yi ja sosai.
"Sannu" Ya furta yana ƙasa da muryarsa. Ta mayar da idanunta ta lumshe, ta ce "Ina ka tafi babu sallama, nake ta neman ka?" Ta yi maganar cike da kasala da rashin ƙwarin jiki.
"Na je gida ne, kin san Innata ba ta da cikakkiyar lafiya ita ma."
Ta jinjina masa kai kawai.
Cikin tausasawa ya ce "Me yake yi miki ciwo ne?" Ta ɗaga hannunta a hankali, ta nuna masa kanta. Kawai ta ga ya saka hannu yana share mata gumin da yake tsatstsafowa a goshinta. Ta buɗe idanunta tana kallon fuskarsa ta hasken fitilar wayarsa. Ji ta yi zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri, har numfashinta ya fara fita da sauri.
Idanunsa da suke ba ta tsoro ya tsare ta da su. Ga kusancin da yake tsakaninsu, wani irin ƙamshi jikinsa yake fitarwa mai kwantar da hankali. Hakan ya ƙara sanya mata kasala da wasi-wasi.
"Yaya Mamman" Bai amsa ba sai kallonta da yake yi.
"Ƙamshin turare ka ke da ƙaurin wani abu, kamar... Sai kuma ta yi shiru."
Ya ɗan ja dogon hancinsa, ya basar, ya ce "Tashi zaune ki ci abin da na kawo miki" Kafin ta yinƙura ya riga ta ya ɗaga ta zaune.
"Wayyo Allah kaina, ka yi mini a hankali mana, zai rabe biyu" Ta yi maganar muryarta na rawa.
Ya jinginar da ita, sai dai gaba ɗaya a tsorace take, idan ban da Yaya babu wani namiji da ya taɓa gangancin kai hannunsa jikinta, ko da kuwa samun kusanci da ita ne. Bayan rashin ƙwarin jiki da take fama, wani irin yanayi take ji a jikinta da ya ƙara kashe mata jiki fiye da da.
Ya janyo ledar da ya zo da ita, ya fito da yoghurt, ya fito da fruit, ya ce "Wanne za ki ci?" Tsura masa ido ta yi, tana tsoron kar wani ya shigo ya gan su a haka, saboda yadda yake zaune daf da ita, gaba ɗaya a tsorace take. Ta zuba wa wuyansa ido, idan ba gizo idanunta suke yi mata ba, sarƙa ce a wuyansa, sai dai ba ta fitowa sosai, tana cikin rigarsa, tana son ta yi magana amma ta kasa.
Ya ci gaba da bin ta da kallo, da mamakin abun da yake gani a tare da ita.
Ya buɗe robar yoghurt ɗin ya ce "Na baki a baki ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. Laɓɓansa take kallo a hankali, kamar yau an canzo shi gaba ɗaya. Idan su na magana bai fiye son su din ga haɗa ido ba, kuma yana ƙoƙarin kiyaye duk wani abu da zai sanya ko hannunta ya taɓa, ko zama ta yi yana nesa da ita, amma yau kamar zai rungume ta. Ba haka ba hatta muryarsa tamkar an canza ta. Muryar ta ƙara buɗewa, kuma babu alamun wasa a cikin muryar tasa.
Babu tsammanni su ka ji an buɗe ƙofar ɗakin gaba ɗaya.
AMANA KAYAN MATAN
Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara
Gumbar mata
Gumbar aya
Gumbar chaku
Gumbar dake saukar da ni'ima
Gumabar taƙadari
Gumbar riɗi
Gumbar dabino
Gumbar uku alkhairi
Kazar amare
Jijjiɓen saniya
Tabaje
Tsimi
Rikita mai gida
Jigidar tada sha'awa
Ruwan boom ruwan daɗi kenan
Ɗan matse
Karya gado
Maganin sanyi
Zumar ƙarin ni'ima
Zumar rage ƙiba
Zumar ƙarin ƙiba
Zumar riɗi
Mai zamani
Emergency powder
Tarhama
Kafi budurwa
Sabon budurci
Alfijir
Gamzaki
Garin dahuwar nama
Sabaya
Miskin ɗahara
Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
SARA DA SASSAƘA...
Ayshercool
YOTA/002
P9
Aka kunna fitilar ɗakin, da sauri Alina ta rufe idanunta, saboda ba ta son haske idan tana wannan ciwon kan.
Nurse ce ta ƙaraso tana turo trolley. Ta ce "Yi haƙuri Alina, zan ba ki magani ne"
Ta gaida Mamman ya amsa, ya sake duban Alina ya ce "Kar ɓi ki sha kafin ta baki maganin"
Ta girgiza kai ba tare da ta ɗago kanta ba, ta ce "Ina Anty ta tafi?"
Nurse ɗin ta ce "Ta je sayo miki magani, ba a samunsa a nan haka"
Ya sake tausasa muryarsa ya ce "'yar ƙwalisa daure ki sha ko kaɗan ne"
Ya yi maganar yana ajiye mata a kan cinyarta. Idanunta a rufe ta fara laluben cokalin dan ta sha. Ya ɗebo ya kai bakinta. A hankali take karɓa, amma idonta a rufe. Kaɗan ta sha ta ce ta ƙoshi amai take ji, ba za ta iya ci gaba da sha ba. Nurse ta kama hannunta, ta buɗe cannula ta fara yi mata allura. Alina ta kawar da kanta gefe ta rintse idonta, saboda yadda ba ta son allura. Ya fakaici idonta, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro sirinji, ya kalli Nurse ɗin da idonsa, ta koma gefe ya kama hannun Alina, cire sirinjin da ta saka mata, ya saka wanda ya ciro a aljihunsa ya fara yi mata. A gigice ta buɗe idonta ta kalle shi.
Sai dai ba ta yi magana ba, jikinta ya saki ta fara bacci, a hankali ya gama zuba ruwan allurar a jikinta, sannan ya gyara mata kwanciyarta, ya kalli Nurse ɗin ya ɗaga mata babban yatsansa alamar jinjina.
Sannan ya yi mata alama da ta tafi. Ta juya da trolley ɗin ta fice. Ya ciro babbar waya a aljihunsa, ya ɗauki hotunan Alina.
Ya kwashe sauran kayan ya fice ya bar ɗakin da sauri.
Ba a yi mintuna goma da fitarsa ba, Nadiya ta shigo ɗakin, ta ƙarasa gaban gadon Alina tana faɗin. "Fatima, haryanzu ba ki tashi ba?" Ta yi maganar tana dafa goshin Alina.
Ta ajiye magungunan da ta sayo, sannan ta ciro wayarta da ke ta ringing.
"Hello masoyi"
"Na'am ya jikin nata?"
"Jiki Alhamdillah, tana ta bacci, ka san ƙa'ida sai ta yi kwana biyu tana fama"
"Na kusa shigowa garin ai nan da awa biyu in sha Allah"
"Wai dawowa zaka yi da gaske? Aikin fa"
Ismail ya ce "Kin san hankalina ba zai kwanta ba, ba na son ciwon kan nan da take yi, na kusa shigowa in sha Allah. Kin samu magungunan kuwa?"
"Eh na samo su, amma da kyar aka bani su, wai ba a sayar da su barkatai"
"To Alhamdillah, da ta tashi a bata ta sha, kuma su yi mata duk abin da yakamata, su tattara mini bills ina dawowa zan bayar, dan bana tunanin akwai isassun kuɗi a file ɗinmu"
Nadiya ta jinjina kai tana faɗin "Ai ka san ko babu ko sisi, za su yi mana duk abin da yakamata, sai ka ƙaraso"
Ya amsa da "To shikenan" Ya katse wayar.
*****
Tun da Baffa ya zo, Rahama ta rasa nutsuwarta gaba ɗaya, kanta har wani ciwo yake yi mata. Tabbas babban dalilin da ya sanya ta karɓi soyayyar Bukar, amfani da shi ne ta gano haƙiƙanin wace ce wadda aka tozarta mata ɗan uwa saboda ita. Amma daga baya ta fahimci kamar shi ma bai san wace ce ba, sai dai kyawawan ɗabi'unsa ya sanya ta saki jiki da shi, har take jin ta fara sonsa. Ta sake tuna maganganun da Saleh ya gaya mata. Ji ta yi tana son ta haɗu da Hanne ko ta halin ƙaƙa. Litattafan da suke gabanta ma, sai ta ture su a gefe, ta nemi guri ta kwanta saboda ba ta jin dadin komai.
Sai dai tana ɗarsa batun son Bukar a zuciyarta, sai mutumin nan ya bujiro mata, ya mamaye ko ina.
*****
Mariya na zaune tana goge uniform ɗin ta na Islamiyya.
Mama ta dube ta ta ce "Mariya, dan Allah idan kin je, ki ba wa malam haƙuri, in sha Allah a satin nan za ki kai kuɗin makarantar ya ƙara haƙuri"
"Tom zan gaya masa in sha Allah"
Hafsa ta shigo ɗakin da sallama tana cire hijjabinta.
Mama ta amsa ta dube ta ta ce "Yaya?"
"Na fita kenan Yaya ya kira ni, ya sako mini dubu uku, ya ce mu yi haƙuri mu lallaɓa, ya je wa Naja visiting shekaranjiya ba kuɗi a hannunsa"
Mama ta ce "Hafsa ba dai gaya masa ki ka yi cewa bamu da komai a gidan ba?"
"Haba Mama kema kin san ba zan gaya masa ba. Dama ba son zuwa gurin Kawu Babballen nan nake yi ba, da an taɓa shi shi ma cewa zai yi ba shi da shi, mu je yaya ya bamu"
Mariya ta ce "Ya ma haɗa ka da masifa ma"
Mama ta ce "Allah sarki yaron kirki, Ubangiji Allah ya tsare mana shi, ya yi masa jagora. Allah dai ya saka masa da alkhairi. Mariya kan ki tafi makarantar nan karɓo mana gari kowa ya sha, mu cancana kuɗin"
"To Mama" Haka ta ci gaba da yi musu addu'a da fatan, Allah ya haɗa mata kan su.
Miƙa ya ɗan yi, idanunsa jawur saboda gajiya, ya cire bindigarsa ya ajiye yana duba wayarsa.
"Haris yane? Ka zo mu je cin abinci, rana ta yi fa"
"Oga Suleiman ka je kawai, bacci nake ji ne"
"Kai Haris, bacci a yanzu, shikenan bari na je"
Haris yana jin yadda cikinsa yake ƙugi, saboda yunwar da yake ji, amma ya rage kayan jikinsa ya nemi guri ya kwanta.
*****
Alina ce ta yi shiru tana tunanin da gaske Mamman ya zo, ko kuwa mafarki ta yi? Cikin kulawa Yaya yake ta jera mata sannu cike da kulawa.
Ta jinjina masa kai, tana ƙara riƙe hannunsa a cikin nata.
"Sannu Alinan Yaya, Ubangiji Allah ya yaye miki wannan ciwon kai, ya yi miki maganinsa"
Suka amsa da Amin.
"To yanzu ya ki ke ji?"
Ta ɗan yi shiru ta ce "Kan ya daina ciwo, ni yanzu mu tafi gida kawai" Ta yi maganar da sigar magiya.
Ismail ya ce "A'a ki yi haƙuri ya ƙara sakinki tukuna"
Ta kwaɓe fuska ta ce "Yaya gobe in Allah ya kaimu Asabar, idan ba a ji karatuna ba, makina zai iya yin ƙasa a cire ni daga cikin yan sauka"
Nadiya ta ce "Alina ai larura tana gaban komai, ki bari dai mu gani"
Ta shagwaɓe tana yi musu magiya.
Ismail ya ce "Ina ganin hakan za a yi, tun da haka take so. Bari na je na ji nawa ku ka ci"
Nadiya ta ce "To shikenan"
Ya fito reception, suka gaggaisa da ma'aikatan, kasancewar sun san shi sosai, patient ɗin su ne, mussaman saboda yawan rashin lafiyar Alina.
Ya ce "Hajiya duba mini file ɗinmu, nawa ku ke bi na, nawa Alina ta ci?"
Aka ciro file, ya sake cewa "Ina ga wancan karon bai fi dubu uku ce ta yi saura a file ɗin ba"
Matar ta ɗaukko file ta duba, ta kalli Ismail ta ce "Ai ba a binku ko sisi, kun biya"
Ismail ya ce "Hajiya ya idon ne? Duba dubu uku ce a cikin file ɗin, sun kawo Alina kwanansu biyu yau. Ki ga nawa suka ci na saka muku yanzu" Ya yi maganar yana daddana wayar hannunsa.
"Da gaske fa nake, an biya har da canjin dubu talatin a file ɗin." Ya kalle ta, ya ja file ɗin gabansa ya fara dubawa. Shekaranjiya ranar da aka kai Alina Asibiti aka saka kuɗi dubu saba'in a file ɗin, kuma da sunansa a saka. Ya yi shiru.
Ya kira Nadiya a waya, ya ce ta zo reception. Ba a jima ba sai ga ta ta iso.
"Masoyiyya, waye ya biya kuɗin Asibitin Alina?"
Nadiya ta ce "A'a ba a biya ba"
Ya ce "To zo ki ga"
Ta ƙarasa ta kalli file ɗin, ta ce "Gaskiya ba su biya ba"
Aka kira wayar wanda ya yi duty ranar, ya ce ta POS kawai ya ga transfer, ya ga sunan Isma'il a jiki, da narration, dan haka ya yi setting bills ɗin.
Ismail ya yi shiru yana tunani, bai sake cewa komai ba, ya ce Nadiya ta haɗa kayanta su tafi.
*****
Babbar mace ce, za ta shekara Arba'in da uku, ta sha kwalliya, ta fito katafaren falonta, ta yi turus ta ɗan tsaya tana kallonsa.
"Baba Mai Kano saukar yaushe?"
"Ko na koma ne?" Ya yi maganar yana ɗan kallonta.
Ta gyara zaman gilashin fuskarta, ta ce "Wane mutum inji mutuwa, barka da sauka"
Bai amsa ba ya nufi fridge, ya buɗe ya ɗauko coc mai sanyi, ya ɗauki glass cup, a saman fridge ɗin, ya zuba ya sha. Ya dawo falo ya zauna. Ya dube ta ya ce "To kina lafiya?"
"Mmm ba gani kana gani ba, Alhamdillah na godewa Allah"
"Ya jikinki fa?"
Ta yi murmushi ta ce "Alhamdillah"
"Allah abin godiya. Amm na ce duk takardunki masu muhimmanci su na nan a ajiye inda na sansu ko?"
"Eh me za a yi?" Ya miƙe tsaye ya ce "Abu nake nema"
Ta dube shi ta ce "Me za ka yi ne?" ya yi gaba cikin hanzari ba tare da ya ce komai ba.
"Mai Kano me za ka yi ne wai? Kai ba ka zo gurin mutum ba, a yi ta maka magana ka mayar da mutum iska, ba za ka amsa ba"
Ya shige bedroom ɗin ta, wardrobe ya buɗe, ya din ga duddubawa ya ciro wata takarda, ya din ga kallon takardar a tsanake, daga bisani ya tashi ya mayar da wardrobe ɗin, ya fito falon ya tarar da ita a zaune, da remote a hannunta, tana canza tasha.
"Sai anjima" Ya furta yana nufar hanyar fita.
"Ina fatan baka hargitse mini ɗaki ba?"
"Ki saka a gyara miki" Ya yi waje da sauri.
BAYAN KWANA HUƊU.
Tun daga nesa ya zuba mata ido, har ta shigo cikin kantin nasa.
Guri ta samu ta tsaya