Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
tana hararsa.
"'Yar ƙwalisa, ya aka yi ne, ya jikin?" Ta murguɗa baki ta yi shiru.
Ya fito daga cikin kantin, ya zauna a gefenta a kan bencin da yake ciki.
"Me na yi miki ne?"
"Sau ɗaya ka zo duba ni, baka sake nema na ba?" Ta yi maganar tana tura baki.
Ya yi murmushi ya ce "Ki yi haƙuri, tsoron yayanki nake ji, kin san ba ya son alaƙata da ke, amma kina raina na damu sosai da sosai, kamar na cire miki ciwon".
"Ba wani nan" Ta yi maganar tana zumɓura baki.
"Da gaske nake 'yan matan Yaya"
Ta ɗan ɗago ta saci kallonsa, ya kashe mata ido, kawai ta hau dariya. Shi ma ya yi dariyar. Ya ce "Kin rame sosai, me yake saka miki ciwon kai haka?"
Ta gyaɗa kai ta ce "Nima ban sani ba, tun ina ƙarama, wani Likita dai ya ce Magrine headache sunan shi. Ka san ranar da ka zo duba ni ɗin nan, bayan ka tafi...
Ya katse ta da cewa "Waye ya zo duba kin?"
"Kai mana, lokacin da ina Asibiti fa"
Ya girgiza kai ya ce "A'a ban zo ba"
Ta yi saroro ta ce "Ka zo mana, na manta kalar kayan da ka saka, amma ka manta ka zo. Har ka kawo mini yoghurt"
"Ta yaya zan zo bayan yayanki yana yi mini kashedi a kanki"
Cikin mamaki Alina ta kalle shi, ta ɗan dafa kanta ta ce "To mafarki na yi kenan? Har ka ɗaga ni zaune fa, lokacin Antynmu ta je sayo mini magani"
Ya ce "Anya kin gama warkewa kuwa, ko dai a koma Asibitin nan? Gaskiya mafarki ne, yanzu me zan ɗaukko miki da za ki ci?"
Ta girgiza kai ta kasa cewa komai, saboda mamakin da ya cika ta.
Ta tashi tsaye ta ce "Ni ba na son cin komai, ga wannan" Ta yi maganar tana ba shi leda.
Ya saka hannu ya karɓa yana faɗin "Me na samu?" Ya buɗe ledar ya fito da abin da yake ciki.
Hankici ta saƙa mai kyan gaske, ta saƙa shi fari da ja, ta rubuta Ɗan albarka, sai kuma hular sanyi ita ma ta rubuta ɗan albarka a jiki. Sai uban ƙamshi suke yi. Sosai yake murmushi, ya ɗago ya kalle ta, ya tsare ta da idnaunsa, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "'Yar ƙwalisa, wannan duk nawa ne?"
Ta ce "Eh, ka din ga canza hula, tun da na ga kullum da hula ka ke zama, ko ka na da sanƙo ne?" Ta yi maganar tana dariya.
Kawai ya yi wata 'yar gajeriyar dariya, jin abin da ta faɗa. Ya cire hular kansa, kansa cike da suma ya ce "Ba ni da sanƙo, ina dai saka hular ne ina rufe kaina"
"Eh na gani ka bani gyaɗa zan koma gida na yi bacci, magungunan nan bacci suke saka ni, duk su kashe mini jiki"
Ya miƙe ya ɗaukko bokitin gyaɗar ya ce "Ɗauki iya wadda za ta ishe ki"
Ta ɗauki ƙulli biyu ta ce "Wannan ta isa"
Ya kalli kantin, ya dube ta ya ce "Sai kuma me zan baki?"
Ta girgiza kai ta ce "Wannan ta ishe ni"
"Kai 'yan matan, na rasa me zan ce miki ne ma gaba ɗaya, amma na gode sosai da sosai Lina, Thank you in ji turawa. Nima yakamata ki din ga koya mini turancin nan"
Ta ce "To shikenan, zan din ga koya maka, amma ka daina wannan godiyar ta yi yawa. Ai ba zan biya ka ɗawainiyar da ka ke yi da ni ba"
Ya saki murmushi ga ta yarinya sai manyance, da iya tsara magana.
Ya ɗan lumshe idanunsa, yana nazartar fuskarta. "Ke ki ke ɗawainiya da ni ai, ki bani abinci, ki taya ni hira, ga kyauta kin bani, kuma... Sai kuma ya yi shiru.
Ta ɗaga kai suka haɗa ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa.
"Sai ka ce na baka wata duniya, ai ba yawa,na gode nima" Ta fice daga kantin, tana tafiya a hankali. Ya zura mata ido, har ta ɓacewa ganinsa.
*****
"Sadauki"
"Allah ya taimaki Madugu"
"An gama saita komai?"
"Na gama Madugu, umarninka kawai muke jira"
"To ku jira ni daga yanzu zuwa kowane lokaci, ku saurare ni, ina jiran a gama gyara mana hanya ne, saboda ba a son kuskure a aikin, sama ta ka zamu kai mamayar"
Sadauki ya ce "Allah ya bar Kacalla Sumale, kai mu ke saurare"
"Good"
*****
Sosai ya zuba wa kayan da Alina ta ba shi ido, yana murmushi.
Ya din ga jujjuya hular, ta saƙu sosai da sosai, sai ƙamshin turare take yi, ga handkachief ɗin ma ya yi kyau sosai, har beza ta yi masa da wani abu mai ƙyalƙali. Ya kai hancinsa ya shaƙi ƙamshin turaren da suke yi, irin wanda take yi ne. Ya yi murmushin gefen baki, ya haɗe su a guri ɗaya, ya ɗaga ƙasan kayansa ya saka su.
*****
YELWA
Tarin makiyaya ne maza, dattawa da matasa, su na zazzaune, a kan wata ƙatuwar tabarma, su na tattaunawa.
Moddibo da ya kasance shi ne jagora a ɓangren makiyayan garin, ya yi gyaran murya yana magana "To tunatarwa ce dai da muka saba yi duk shekara, yanzu ma ga mu mun zo da ita.
Mun san wasu za su dawo da dabbobi gida, wasu kuma za su fita da su. To ga kuma labarai marasa daɗi da muke samu, ga kuma rigimgimun cikin garin nan. Saboda haka nake roƙonku, duk inda za ku je, ku kasance mutanen kirki, duk inda ku ke ku wakilan makiyaya ne, makiyayi kuma ba a san shi da tashin hankali da neman rigima ba. Domin girman Allah ku kula da dabbobi, kar su shiga su yi wa kowa ɓarna. Sannan wanda za a bari a gari, kuma ina roƙon waɗanda za a bari a gida, kowa ya kula da dabbobinsa, kar ya bari su shiga gonar wani su yi ɓarna.
Hausawa sun ce; kowa ya kwana lafiya shi ya so. Kun san mutanen nan sun fi ƙarfinmu ta kowacce fuska, tsokanarsu ko neman rigima da su, ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba. Mu na sane da tabon da yake zukatanmu, na cutarwa da suke yi mana, da har abada ba zamu warke ba, dan haka kowa ya kula dan Allah"
Duk suka amsa masa da In sha Allah. "Ko akwai mai magana"
Baffa ya ɗaga hannu, Modibbo ya ce "Mu na saurarenka Jibo"
Baffa ya miƙe ya ce "To 'yan uwana Assalamu alaikum, ni ɗorawa zan yi abin da ka faɗa. Mu na jin yadda al'amuran rikicin manoma da makiyaya ke komawa wani abu daban. Duk ma'abocin jin radio, ko wanda yake shiga birni, na san yana da labarin hakan. Saboda haka nake sake roƙonmu mu ƙara kulawa sosai, dan kamar jira suke yi wani abin ya haɗo mu ma su far mana. Sannan duk wani abu da muka gani baƙo da bamu yarda da shi ba, mu sanar da junanmu...
Ɗan uwan Baffa ya ce "Dan Allah Modibbo, idan an gama taron nan mu tafi, ya tashi sai iyayi yake yi mana. Koma mene ne ba ɗanka ne yaje ya tsokane su ba, ya ƙara tayar mana da tsohuwar gabar nan ba, da bai je inda 'yarsu take ba, ai da abin bai ƙara tsauri ba."
Wani a gefe ya ce "Gaskiya ne, yo mutumin da bai iya kula da gidansa ba, ya ɗauki yarsa ya kai wata uwa duniya ne, zai wani tashi yana mana surutu da sunan shawara?"
Sai jikin Baffa ya yi sanyi. Maddibo ya tsuke fuska ya ce "Jatau, Iro meye haka? Iro da aka kashe mana, ai ba Jibo kawai aka yi wa ba, mu aka yi wa. Kisan gillar da aka yi masa zuriyar makiyaya aka yi wa. Kuma ba domin mu na son zaman lafiya ba sai mun bi kadin jinin iro. Batun kai Ramata birni wannan abu ne da shi ya shafa. Mu na jinka Jibo ci gaba da magana"
Baffa ya girgiza kai, fuskarsa ɗauke da murmushin ƙarfin hali, ya ce "Ahh dama shikenan maganar tawa, na gode" Ya nemi guri ya zauna yana yaƙe.
****
"Vice"
"Ranka ya daɗe"
Ya yi taku biyu da sanda a hannunsa, ya nemi guri ya zauna, ya ɗaga idanunsa, ya saka a cikin na kan Kangiwa.
"Na san ka san faɗin tashin da muka yi, muka kawo ku kan mulki ko?"
"Na sani Allah ya baka yawan rai"
"Masu iya magana sun ce, ɗan halal baya manta alkhairi, sai dai farawa da bismillah, Kankiya yana ƙoƙarin nuna mana, an tura motar zai bule mu da hayaƙi, ba tare da sanin direban da yake tuƙin motar namu ne ba. Tun da ya nuna zai mana butulci, ba zai yi mana biyayya ba, zamu yi masa yaren da zai gane. Idan ka amince ka bamu haɗin kai ɗari bisa ɗari, zamu mayar da shi fanko, ka jagoranci ƙasar, zuwa lokacin zaɓe mu hankaɗe shi, kai mu ɗora ka."
Cikin mamaki yake kallon Makama, murya na ɗan rawa ya ce "Ta yaya hakan zai faru ranka ya daɗe?"
"Wannan aikinmu ne, kai dai ka zama mai biyayya kawai, idan ba haka ba daga kai har shi, zaku rasa zamu nemo wanda za mu tsayar, dan ba za ku yi tazarce ba, dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan ka shirya ka amince, zamu hargitse ƙasar kai kuma ka ji da sauran...
Ayshercool
08081012143
AMANA KAYAN MATAN
Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara
Gumbar mata
Gumbar aya
Gumbar chaku
Gumbar dake saukar da ni'ima
Gumabar taƙadari
Gumbar riɗi
Gumbar dabino
Gumbar uku alkhairi
Kazar amare
Jijjiɓen saniya
Tabaje
Tsimi
Rikita mai gida
Jigidar tada sha'awa
Ruwan boom ruwan daɗi kenan
Ɗan matse
Karya gado
Maganin sanyi
Zumar ƙarin ni'ima
Zumar rage ƙiba
Zumar ƙarin ƙiba
Zumar riɗi
Mai zamani
Emergency powder
Tarhama
Kafi budurwa
Sabon budurci
Alfijir
Gamzaki
Garin dahuwar nama
Sabaya
Miskin ɗahara
Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
SARA DA SASSAƘA...
YOTA 002
P10
AYSHERCOOL
Kangiwa ya yi shiru yana lissafa maganganun a cikin zuciyarsa.
Ya jinjina kai a hankali ya ce "Shikenan, zan je na yi shawara"
"Ina saurarenka"
Kangiwa ya tashi sumi-sumi ya fice.
Ya zuba lemo a kofin gabansa, ya ɗago kofin ya kai bakinsa yana zuƙa a hankali, yana jujjuya lemon a kofin yana kallon katafariyar talabijin din da ke cikin ɗakin.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya ɗauke ta a gefensa, ya kalli lambar bai santa ba, ya dai ɗaga ya kai kunnensa ya yi shiru bai yi magana ba.
Jin an yi shiru ya sanya shi cewa "Waye a kan layi?"
"Kacalla Sumale"
Da sauri ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Yaya ake ciki ne? Mu na ta nemanka a waya ba mu samu ba, kai fa muke jira"
"Ba na gaggawa a aikina, yaƙin sunƙuru ka ce a yi, dan haka kar ka shigar mini aiki." Cikin mamaki mutumin ya buɗe baki, jin yadda baƙauyen ɗan ta'adda yake yi masa magana gatse-gatse.
"Ba zan ci gaba da ƙaddamar da hari ko ta ina ba, nima aikina lissafi nake yi. Na kira ka ne na jaddada maka na kuma ja maka kunne, kar ka kuskura ka saɓa yarjejeniyar mu. Kuma ka ce za ka kula da ɓangaren kwaɗin nan, idan aka kashe mini mutane, ko aka kama wani zan yi fyaɗar 'ya'yan kaɗanya ne, har iyakar da bai kamata ba sai na ci. Kuma wannan kwantiragin, ko a mutu ko a yi rai ne, ka tabattar ka kula da ɓangarenka. Idan da wani abu, ko kana nema na, ka tuntuɓi Sadauki... Ƙit ya kashe wayarsa.
*****
"Masoyiyya" Ismail ya kira Nadiya.
"Masoyi"
"Jikina yana bani wani abu"
Cikin rashin fahimta ta ce "Wani abu me kenan?"
"Haryanzu ina mamakin wanda ya biya kuɗin Asibitin Alina kuma da sunana, wannan ya tabattar mini da akwai wani abu a ƙasa"
Nadiya ta ajiye ninkin kayan da take yi, ta dube shi ta ce "Nima dai abin ya ɗaure mini kai, sai dai bana tunanin akwai wanda zai din ga bibiyarmu, saboda me ma to za a bibiye mu, ni nafi tunanin ko mistake aka samu"
Ya yi dariya ya ce "Mistake? Ba kuskure ba ne, wani abu ake ƙoƙarin gaya mini da hakan. Ina tunanin Alina na yin sauka, zamu bar garin nan, shi ma dan na ga yadda ta ƙallaffa ranta a kan saukar Alqur'anin ne. Kawai ina jin akwai matsala zamanmu a nan"
Nadiya ta ce "Amma duk shekarun da muka yi, ba a samu matsala ba, sai a wannan karon? Ina zamu koma?"
Ya ce "Alina, Saboda Alina dole mu bar garin nan, da daga ni sai ke ne, babu inda za mu je, tun da bamu takawa kowa ba, ba kuma mu zubarwa kowa ba a garin nan. Amma ba na son duk wani abu da zai kawowa ƙwaƙwalwarta cikas, kin san me nake nufi ai"
Nadiya ta numfasa tare da sauke numfashi.
Ya sake numfasawa ya ce "Wai me mutuniyar ta saƙa ne, da ulun da ta addaba mini sai na sayo mata?"
"Ina na san mata, ka san idan ta ga dama ta yi saƙar ta sayar, ko ta kyautar. Dan kai ta gado a ungo"
Ya yi guntuwar dariya ya ce "Ta saƙa wa Mamman hula ta ba shi, ya saka ta yaje masallaci da ita. Abin da nake gudu ya faru, amma zan ɗau mataki na ƙarshe a kai"
Da sauri Nadiya ta ce "A'a masoyi, kar ka...
"Shhhh" Ya katse ta yana zare mata ido, tare da tsuke fuska tamkar bai san yadda ake dariya ba.
*****
Daga nesa kaɗan yake tsaye, yana hango ƙofar gidan Malam Ɗayyabu, da rumfar almajiransa aka shimfiɗa tabarmi ake zaman makokin rasuwarsa.
Duk wanda yakamata ya tambaya, da binciken da yakmata ya yi, amma babu wani gamsashen dalilin rasuwar malamin, kowa yana faɗin ya kwanta bacci lafiya kalau, aka wayi gari da gawarsa.!
Alina ce a tsaye, hannunta riƙe da takalmanta na makaranta, tana tsaye a bakin shagon yana ta sallamar mutane.
Ya yi ƙoƙarin sallamarta, amma ta ce masa ya gama tukuna.
Kasancewar yamma ce, ana ta zuwa sayayya.
"Nifa na gaji da tsayuwa" Ta yi maganar tana tsuke fuska.
"To ai ke ki ka ce na sallame su, bari na ƙarasa ranki ya daɗe"
Ya sallami kowa, ya fito yana gyara zaman hularsa da ta saƙa masa. Ya saka hannu zai karɓi takalman, ta janye abin ta, ta ɓoye a bayanta.
"Meyafaru kuma?" Ya yi maganar yana kallon ta.
Ta harare shi, ta kawar da kanta gefe.
"Subhanallah me na yi?"
"Ka sallami kowa ka ƙi kula ni, kuma kana sallamar su, kana yin murmushi" Ta ƙarasa maganar tana kawar da kanta gefe fuskarta ɗauke da damuwa.
Ya yi dariya ya ce "Ni ne nake murmushin? Rigima dai ki ke ji, amma ban da ke kin ga ina yi wa wani murmushi? Ai ba na dariya murmushin ma ke kawai nake yi wa"
Ta ɗago kanta suka yi ido huɗu, kawai ta hau dariya, wanda hakan ya sanya shi ma ya yi guntuwar dariyar.
"Ɗan albarka"
"Na'am 'yar ƙwalisa"
"Yaushe za ka cire gashin nan na fuskarka ne? Ina son na ga fuskarka sosai da sosai"
Mamman ya shafa fuskarsa ya ce "Yanzu ba kya ganin fuskartawa?"
"Eh mana, gashi ya fi yawa, idan ka aske sai ka fi kyau"
Ya jinjina kai ya ce "Ai abin da Mumsy take so shi nake so, zan aske ki ganni sosai"
Ta kalle shi ta ce "Mumsy, amma dai Mamman ka yi karatun boko?"
Ya girgiza kai ya ce "Ai ba sai mutum yaje boko ba zai san wani abin ba, amma bari na din ga ce miki Inna"
"Ni wallahi ba Inna ba ce" Ta yi maganar tana dariya. Ya karɓi takalmanta, tana zaune ya goge su ya yi musu mai.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya ciro wayar ya kalla, ya kalle ta sannan ya ɗaga ya yi sallama.
Ba ta san me ake ce masa a wayar ba, ta ɗaga takalminta tana kallo, ta ga ya sauke wayar a hankali, fuskarsa babu walwala.
"Ya dai meyafaru? Ko jikin Innar ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Maƙwabtan ƙauyenmu ne, aka yi rikici da manoma, da maharba, an karkashe mutane"
Cikin razana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ubangiji Allah ya taƙaita. Ko za ka je gidan to ka gani?"
Jiki a sanyaye ya ce "Sai abin da Allah ya yi"
"A'a gara ka je, irin wannan kuskuren Yaya ya yi. Ya ce mu garinmu rikicin manoma da makiyaya ake yi, ba su ɗau abin serious ba, sai da ya yi yawan da muka rasa iyayenmu, kuma aka kori wanda suka rage daga garin. Shi ne su suka taho nan, ya ce mukaɗai muka rage a gidanmu. Kafin mu zo nan a gidan su Antynmu muka zauna, har ya aure ta, ita ma aka yi ta rikici a garinsu, aka kashe musu yan uwa muka taho nan. Duk an ƙarar da danginmu, daga Allah sai yaya muke da shi." Ta yi maganar tana sanya tafukan hannayenta, ta rufe fuskarta tana fashewa da matsanancin kuka.
Ya yi shiru yana nazarinta, ya jinjina kai, sannan ya yi ƙasa da muryarsa.
"Ki yi haƙuri