Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
ce komai ba. Sai ta fara tunanin ko kurma ne. Sai kuma ta tuna ranar da Yayanta ya je yana yi masa faɗa a kanta ya yi magana.
Ta sake cewa "Ko ba zaka iya tashi ba?" Bai ɗago ba ya yinƙura a hankali ya tashi tsaye. Sai dai ya ji rauni a babban yatsansa na ƙafa farcen ya ɗago, sai zubar da jini yake yi. Da sauri ta yamutsa fuska saboda ba ta ƙaunar ganin jini, yanzu hankalinta zai tashi.
Ya miƙa hannu zai karɓi bagconsa, ta girgiza kai ta ce "Muje na kai maka" Bai sake magana ba, ya ɗaga ƙafarsa ya fara takawa a hankali. Da kyar yake taka ƙafar, saboda ya bugu, ga jini na zuba. Gaba ɗaya sai tausayinsa ya mamaye ta, da ta kalli ƙafar sai ta yamutsa fuska ta kawar da kanta gefe.
Tana tafe yana biye da ita, ta ja ta tsaya ta ce "Laa ka ga chemist ɗin Albarka ya fito, muje ya duba maka, ko jinin zai daina zuba kar jininka ya ƙare ko tetanus ta shiga ciwon, duk da kwalta ce ba ƙarfe ba. " Ta yi maganar tana nuna ƙofar shagon. Ya ɗan kalle ta, yadda take magana Allah ya hore mata iyayi. Daki-daki take maganar tana demonstration, dai 'yar siririyar muryarta mai kauɗi tamkar tsuntsuwa.
Kansa a ƙasa ya basar ya ce "Ba ni da kuɗi"
Ta ce "Mu je da kuɗi a gurina"
Bai sake cewa komai ba ya bi bayanta.
Da sallama ta shiga, mai chemist ɗin na ganinta ya hau murmushi. "Alinan Yaya, ina Yaya?"
Ta yi murmushi ta ce "Yaya yana gida. Dan Allah ka duba masa ƙafarasa babur ne ya buge shi, kuma ya gudu" Mai Chemist ya tashi yana faɗin Subhanallah.
Ya dudduba ciwon sannan ya wanke masa ciwon, ya yi masa allurai, da magunguna.
Alina ta ce "Nawa?"
"Dubu uku da ɗari biyu" ya bata amsa.
Ta waro ido ta ce "Danƙari, to ka sakawa Yaya a cikin lissafinsa"
Mai chemist ya ce "To amma ki yi masa bayani"
Ta ce "Zan yi masa in sha Allah"
Daga haka suka fito suka tafi, sai da suka je ƙofar ɗakin da yake zama, ya tsaya yana kallon kayansa da ke hannunta, bai ce ta ba shi sai kallonta da yake yi.
Ta miƙa masa ya karɓa, ta ce "Ko na kawo maka baho da ruwa ka wanke?" Ya jinjina mata kai.
"To bari na je gida" Ta ajiye kayan, ta nufi gidansu. Ƙasan zuciyarsa cike da fargaba, kuma sai gargaɗinsa zuciyarsa take yi, da tuna irin abin da yayanta ya yi masa, da kuma kashedin da ya yi masa a kanta.
Ba a yi mintuna biyar ba, sai ga ta ɗauke da baho ta shaƙe shi da ruwa a ciki. Yana tsaye yana kallonta, ta ɗauki yalon nan ta juye a bahon duk ta ɗauraye su, ta zuba masa a cikin bagcon sannan ta zubar da ruwan.
Ta yarfe bahon ta dube shi ta ce "Allah ya tsare gaba"
"Amin" Har za ta tafi ta ji ya ce "Na gode" ta tsaya ta waiwaya ta kalle shi, amma jikinta ya yi sanyi, saboda yadda ya tsare ta da manyan idanunsa. Jinjina kai kawai ta iya yi, ta nufi gida.
*****
Ramata na zaune da wayarta a hannunta, ta tattara hankalinta tana sauraren radio a cikin wayar. Tana zaune hannunta riƙe da biro da takarda, ga kuma fitila a ci balbal tana haska mata littafin gabanta.
Cak ta tsaya da rubutun, ta ƙara tattara hankalinta a kan sauraren bayanan da mutumin cikin radion yake yi, yadda turawa suka mamayi Afrika.
Yadda suka fara zuwa African ta jirgin ruwa, su kan zo gaɓar teku domin yin cinikayya a ƙarni na sha biyar. Su na kasuwancin zinare, hauren giwa da makamatansu. Daga baya aka fara cinikayyar bayi, mussaman tsakaninsu da sarakuna, yadda suke dibar mutane daga Afrika su tafi da su ƙasashen su, su yi musu bauta.
Daga bisani a ƙarni na 16 suka fara kafa sansanoninsu, da kawo coci-cocinsu, da Asibitoci da makarantu a Afrika. Suka daina tsayawa a gaɓar teku suka fara watsuwa a cikin ƙasashen Afrika.
Cinikayyar bayi da yarjejeniyar bogi, tsakaninsu da sarakunan Afirka, shi ya fara kawo rarrabuwar kawuna a Afrikan tare da kawo koma baya.
A ƙarni na 19 alif dubu ɗaya da tamanin da takwas, manyan ƙasashen nahiyar Turai suka yi taro, suka rarrabawa kansu ƙasashen Afirka ba tare da sanin ƙasashen Afrikan ba.
Ramata ta riƙe haɓa, jin an tafi talla. Ta dubi Baffa da yake gefenta yana sauraren radion shi ma.
"Taɓ Baffa"
"Na'am Ramata"
"Tabbas ba a taɓa cin gari har abada ba tare da ɗan gari ba. Ƙulafuci da son zuciyan sarakunan Afrika na ƙarnukan baya, na daga cikin dalilan da ya sanya muke cikin wahala haryanzu, kuma muke ƙarƙashin mulkin turawa ta wasu fuskokin"
Baffa ya yi murmushi ya ce "Ba an ce mun samu 'yanci ba? Kuma duk da haka mutanen wancan ƙarnukan ai sun fi na yanzu wadatar zuci ma da amana. Duk da ni ba wani gane kan wannan abubuwan nake yi ba"
Jiki a sanyaye ta ce "Baffa, duk da ba na nan abubuwan nan suka faru, na san Alƙawarurrukan da turawa suka yi musu, baya rasa nasaba da basu tarin dukiya, ko kuma wani abu da za su amfana ba tare da kallon makomar al'ummarsu ba. Ban da haka ya za ku din ga ɗaukar junanku ku na sayarwa mutanen da ba ma launin fatarku ɗaya ba, daga wani guri suka zo, ba ma yankinku ɗaya ba, alhalin su ba sa sayar muku da na su mutanen, tun a lokacin sun nu na ba su san ciwon kansu ba fa kenan?
Baffa ya kwashe da dariya, ya ce "Ramatu kenan. Ga shi nan sun dawo daga tallan ai, bari mu ci gaba da jin meyafaru"
"Assalamu alaikum " su ka ji an kwaɗa sallama.
Baffa ya amsa sannan ya kalli Ramata ya ce "Maza shiga ɗaki"
Ta tashi tsam ta shige ɗaki, Baffa ya sake cewa "Bismillah"
Tamkar korarre haka ya faɗo gidan, Baffa ya miƙe yana yi masa sannu da zuwa, ya nuna masa gefen tabarmar da yake kai domin ya zauna.
Yana zama Juma ta fito kanta da lulluɓi, ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa, sannan ya mayar da idonsa kan Baffa.
"Wato kai dai ba zaka taɓa hankali ba ko Jibo?"
Cikin rashin fahimta ya ce "Yaya lafiya kuwa?"
"Ka tambaye ni ko lafiya mana, to ba lau ba. Saboda tsabar ɗan kanka ne kai, mun haƙura mun zuba maka ido kana yadda ka ke so. Ban da rashin mafaɗi har dukiyarka zaka tattare idan ka mutu Ramata ta ci gaba da yahudanci ko? To baka isa ba wallahi. Babu wannan maganar na soke ta. 'ya ce dai tun da ba zaka aurar ta ba, mun zuba maka ido, a garin nan dai ka san babu mai auren ta. Ka ɗauke ta ka kai ta can wata uwa duniya ta yi kwana da kwanaki babu wanda ya san inda take da abin da take yi, babu wanda zai aure ta dan haka sai ka jiƙa ta ka sha"
Baffa ya kalli Juma, ta tsuke fuska tana kawar da kai. Ya girgiza kai ya ce "Yaya haryanzu ba ku fahimci manufata ba, ana ta samun ci gaba a duniya, mu mu na guri ɗaya duk a dalilin rashin ilimi. Ko mulkin kama karya da ikon da ake yi mana a garin Yelwa rashin ilimi ne ya haddasa mana shi."
"Ni rufe mini baki, 'yan bokon ba su ne suke kashe-kashe ba, suke mulkin ƙasar gaba ɗaya ba, wane zalunci ne su ba sa yi. Sau nawa ana kai ƙorafin abin da yake faruwa a garin nan, amma su ke goya musu baya. Wallahi idan baka yi wasa ba, yadda ka fifita yahudanci a kan aurar da Ramata, sai ka zubar da hawaye a dalilin bokon nan, sai ta zame muku masifa daga kai har ita"
Ras gaban Ramata ya faɗi, jin yadda ɗan uwan mahaifinta ke janyo musu jafa'i ga shi dattijo. Ta jingina da jikin katangar ƙasar da ke ɗakin, zuciyarta na bugawa da sauri.
Baffa ya ce "Ba za a yi haka ba in sha Allah, Alkhairi za ta zame mana baki ɗaya"
"Wannan kuma matsalarku ce" Ya tashi ya kaɗe rigarsa ya fice.
Baffa ya dubi Juma ya ce "Kin kyauta, na gode sosai da sosai" Ta tashi sumi-sumi ta wuce ɗaki tana ƙunƙuni.
****
Ko da Alina ta taso daga makarantar dare, ba ta ga mutuminta ba, ta yi ta tunanin ko ya ƙafarsa, ko ya warke? Haka ta yi ta saƙe-saƙe, har ta koma gida.
Daga nan sai da aka kwana biyu, sannan ta sake ganinsa.
Sai dai kan ta ƙarasa inda yake ta yi magana, ya shige ɗakinsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi.
*****
Danƙareriyar mota ce ƙirar higlander take ta zuba gudu, sai dai jikin motar babu lamba.
Yana zaune a bayan motar, fuskarsa a rufe da rawani, sai idanunsa kawai ake iya gani. Sai rarraba idanu yake lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma sai ya sunkuyar da kansa ƙasa yana duba agogon hannunsa.
Check point suka tarar a hanya, wanda tilas direban motar ya yi slow, ya ja ya tsaya.
Sojoji ne su uku a a check point ɗin, ya yin da wasu ke zaune a cikin mota, babban cikinsu ya ƙaraso, ya kalli direban ya ce "Daga ina?"
Direban ya amsa da "Maigida ne ya aike mu"
"Waye mai gida?"
"Lamba ɗaya"
A ɗan hasalae sojan ya ce "Malam ka yi mini bayani, daga ina kuma ina za ku je? Sannan suwa ka ɗaukko, ga motar ta ku babu lamba, kai ba ku da gaskiya."
A hankali ya sauke gilashin motar, ya yi wa sojan alama da ya ƙarasa. Ya ƙarasa daidai tagar yana son ganin fuskar mutumin.
"Kacalla Sumale, shugaban manyan ƙungiyoyin ta'addanci na yankin nan, da ku ke nema babu dare babu rana, shi ya aike ni. Manyanku sun saka a ɗaukko ni domin wata yarjejeniya" Ya yi maganar yana ƙare wa sojan kallo, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakykywar fuskarsa fari sol ta bayyana.
Ya sake duban sojan ya ce "Ka buɗe mini hanya zan wuce" Sojan ya ɗana bindigarsa yana ƙarewa fuskar matashin kallo. Shi ma matashin ya tsare shi da nasa idanunsa da suka da kalar ja.
Ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kan sojan ba, ya ciro wayarsa ya daddana, ya saka ta a hansfree.
Daga cikin wayar wata murya ta ce "Ya aka yi ne?"
"Ka janye mutanenku sun tsare mini hanya, ko kuma su riga rana faɗuwa" Waro ido sojan ya yi, jin muryar mai maganar, saboda duk wanda yake cikin battalion ɗin su, babu wanda bai san wannan muryar ba.
"Argungu are you with me?"
Cikin rawar murya ya ce "Yes Sir"
"Clear the road"
"But Sir"
"I said clear the road"
"Ok sir" Tamkar soko haka ya ja da baya a hankali, yana kallon motar. Ya yi wa sauran alama da hannunsa, suka buɗe hanya motar ta wuce.
*****
"Alina, wai bacci ki ke yi da la'asar ɗin nan?"
Alina ta amsa da "A'a idona biyu" ta fito tsakar gida ta ce "Saƙa nake yi, safa da hula zan saƙa idan ki ka haihu mu saka wa jaririyar"
Nadiya ta yi murmushi ta ce "Alina kenan. Kin ga gobe in Allah ya kaimu litinin ki zo ki kai wankin takaliminki, ga nawa ki haɗa da shi a yi mini round, na yi wa Yaya maganar ya manta"
Alina ta ce "To bari na saka hijjabina" Ta yi maganar tana ɗan yin hamma, sai kuma ta katse hammar da ta tuna mutumin nan da ko sunansa ba ta sani ba yana gyaran takalmi. Da sauri ta janyo hijjabin ta zura, ta ɗauki takalman ta fita.
Sai dai baya gurin da yake zama, dan haka ta je ƙofar ɗakin da yake kwana cikin tsoro, ta fara bugawa.
Har ta sare ta fara tunanin baya nan, kawai ta ga ya buɗe ƙofar, sai da ta razana ta ɗan ja da baya tana kallonsa. Ya ƙura mata ido, a ɗan rikice ta ce "Ahh da..da..dama gyaran takalmi na kawo maka" Ta yi maganar tana nuna masa takalman hannunta.
Ganin ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta sha jinin jikinta, tsoro ya ƙara bayyana a fuskarta. Kawai ta ga ya koma, ta tsaya sororo tana kallon ƙofar, har za ta juya ta tafi, ta ga ya sake buɗewa ya fito da kayan gyaran takalmin. Ta yi ajiyar zuciya ya samu guri ya zauna, ta gaya masa abin da zai yi wa takalman, sannan ta koma gefensa kan dakali ta zauna.
Ya duƙufa yana wanke takalmin, ya din ga jujjuya takalmin Alina, tomes na 'yan makaranta baƙi, mai tsadar gaske. Ta ɗan zuba masa ido, haka kurum ta ji tana son ta ga fuskarsa, amma ya tara uwar ƙasumba dogon hancinsa kawai ake iya ganewa sai manyan idanunsa da suka fi komai razana ta. Bayan haka ga wata uwar hula da yake sakawa a kansa ya rufe, ga uban kwalli da yake rambaɗawa a idonsa. Kayan jikinsa sun sha jiki, dark bluen yadi ne a jikinsa, amma ya koma sky blue saboda tsufa.
"Ciwonka ya warke?" Ta yi maganar ba tare da ta shirya ba.
"Ya warke" Ya faɗa a taƙaice.
"Allah ya ƙara sauƙi, ya kiyaye gaba"
"Amin" Yayi maganar yana ci gaba da abin da yake yi ba tare da ya ɗago ba.
Ya gama gyaran takalmin, ya wanke mata nata, sannan ya miƙo mata.
Ta karɓa ta ɗan yi murmushi ta ce "Kai ya naga takalmina ya koma sabo? Wannan ƙyallin ai sai na gano fuskata a ciki saboda kyau da sheƙin da yake yi" Ta yi maganar tana ɗaga takalmin tana kallonsa. Ga mamakinta sai ta ga ya ɗan kalle ta ya yi murmushi.
Ita ma murmushin ta sake yi sannan ta ce "Nawa ne?"
"A'a ki bar shi"
Alina ta ce "A'a ai sana'a ka ke yi, Yayana ya ce a duniya kar ka zalunci mai sana'ar hannu".
Ya ce "Idan kin kuma kawowa sai ki biya"
"To Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata, idan su na raye Allah ya ja kwanansu"
Ya amsa da "Amin na gode"
Ba ta kai ga tashi ba, sai ga Isma'il ya shigo layin a kan babur, idonsa na sauka a kansu, ya tsuke fuska kamar ya ga bala'i...
1k ne a telegram via 0069685771
Aisha Adam stanbic. Shaidar biya ta
08081012143
Ayshercool
08081012143.
AMANA KAYAN MATAN
Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara
Gumbar mata
Gumbar aya
Gumbar chaku
Gumbar dake saukar da ni'ima
Gumabar taƙadari
Gumbar riɗi
Gumbar dabino
Gumbar uku alkhairi
Kazar amare
Jijjiɓen saniya
Tabaje
Tsimi
Rikita mai gida
Jigidar tada sha'awa
Ruwan boom ruwan daɗi kenan
Ɗan matse
Karya gado
Maganin sanyi
Zumar ƙarin ni'ima
Zumar rage ƙiba
Zumar ƙarin ƙiba
Zumar riɗi
Mai zamani
Emergency powder
Tarhama
Kafi budurwa
Sabon budurci
Alfijir
Gamzaki
Garin dahuwar nama
Sabaya
Miskin ɗahara
Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
SARA DA SASSAƘA...
AYSHERCOOL
YOTA/002
BRIGHT PENS
P4
Bai kula su ba kawai ya wuce, Alina ta tashi ta ce "Sai anjima na gode"
Cikin fargaba ta shiga gida, ta tarar da Yaya Ismail a tsaye yana jiran isowarta.
Aikuwa ya tare ta da "Meye haɗinki da mutumin nan? kin kawo mini ƙara na je na tsawatar masa, yanzu kuma na ganki a gurinsa me ya kai ki gurinsa kuma?"
Alina ta nuna masa takalman hannunta A ɗan tsorace ta ce "Gyaran takalmi na kai masa, ni fa dama babu abin da yake yi mini Yaya, tsoronsa kawai nake ji da, kuma daga baya na gane mutum ne, shi ne na kai masa gyaran takalmanmu, nawa da na Anty"
Ya ce "To dai ki din ga kula da kyau, kuma ki din ga addu'a"
Alina ta jinjina kai, ta ajiye takalman.
*****
Yau Juma'a, da yamma liƙis Ramata ce sanye da ɗinkin riga da skirt na yadi, ta yi wa fuskarta ado da jam baki da kwalli, ta yi kyau. Ta tsaya dai-dai jikin wata bishiyar tsamiya, tana ɗan leƙe-leƙe.
Wanda ta gani yana tahowa ne, ya sanya ta tsuke fuska, gabanta ya tsananta faɗuwa, idanunta suka fara kaɗawa, ta ji tamkar ta juya ta zura da gudu. Tun daga nesa yake wage baki yana dariya cike da ƙeta, ya ƙaraso inda take tsaye, jikinsa sanye da kayan farauta, da karnuka su na bin sa, sai abokansa su biyu.
Ya ƙare mata kallo ya ce "Jikar makiyaya wannan kwalliyar fa?" Ta ƙara tsuke fuska tana jin yadda zuciyarta ta fara tafasa, ta haɗiye wani abu mai ɗaci a maƙogwaronta, tana kallonsa.
Hannu ya miƙo zai kai jikinta, cikin zafin nama, ta buge hannun ta ja da baya tana huci.
Ya sake kwashewa da dariya sannan ya ce "Kafiya da taurin kai tamkar mahaifinki Ramata. Daga nan shiyyarku na so shiga domin na ganki a bar ƙaunata, sai dai na taki sa'a na yi gamo da ke a nan. Ko akwai wanda ki ke jira ne?" Ta tsare shi da idanunta