Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
ƙofar wani ɗan ɗakin langa-langa, da ke ƙofar wani gida, yana ɗinke takalmi. Ta na tsayawa, su na haɗa ido, ta ji wani irin abu a jikinta. Ya yi mata dabaibayi da manya-manyan idanunsa, da suka surka da kalar ja. A take ta hau tsuma, ta kwasa da gudu ta ƙarasa gida.
Daga cikin ɗakin Ismail ya ji Alina ta faɗo gidan ya ce "Yaya mene ne haka za ki faɗo gida haka da gudu kamar an sako shanuwa?"
Cikin fargaba ta ce "Ni wallahi Yaya wannan mutumin kullum sai na gan shi, tsoro yake bani"
Ba shiri ya fito daga ɗakin fuska a murtuke yana faɗin "Waye shi, me ya yi miki?"
Tana ɗan rarraba ido ta ce "Bai yi mini komai ba, tsoronsa kawai nake ji, kuma kusan kullum sai na gan shi"
"Mu je na ji dalilin da ya sanya yake tsorata ki" Ya yi maganar yana zura takalmansa a fusace.
Anty Nadiya ta ce "Haba masoyi, kamar ba ka san shirirtar Alina ba, ban da shirirta ya za a yi haka kurum kawai ta din ga jin tsoron mutum, ka san ta saba irin wannan rashin kan gadon, kar ka je ta saka ka ji kunya."
Sai kuma ya ɗan sassauta tsuke fuskar da ya yi, ya dubi Alina ya ce "Babu ruwanki da shi, muddin ya yi miki wani abu na rashin kyautawa, kawai ki gaya mini" ta jinjina kai, sannan ta nufi ɗakinta.
Kwanaki biyu a jere, Alina duk lokacin da za ta fita, za ta ga mutumin nan, a ƙofar shagon nan, yana gyaran takalmi. Ta din ga ƙoƙarin koyawa kanta rashin jin tsoronsa, amma ta kasa mussaman idan ta tuna idanunsa, muddin suka haɗu suka haɗa ido, sai gabanta ya yi mummunar faɗuwa gaba ɗaya sai ta rikice.
In dai za ta fita har addu'a take yi, Allah ya sa kar ta haɗu da shi.
Cikin sa'a yau har ta je makarantar boko, ta je islamiyya ta dawo ba ta gan shi ba, sai da aka taso daga makarantar dare sannan ta gan shi a ƙofar makarantar su. Sosai abin ya fara damunta, ga shi tana tsoron jarabar Yaya, da sai ta sake gaya masa. Ta lura gaba ɗaya yanzu mutumin a layinsu ya tare, da safe zuwa azahar ya yi gyaran takalmi zuwa yamma ta ga ya kasa wani abin daban.
A daren ranar ma dai da gudun ta shiga gida, ta laɓe a bayan ƙofa ta daidaita nutsuwarta, sannan ta shiga cikin gidan, dan haka babu wanda ya gane halin da take ciki.
Da safe kuwa tamkar ta ce "Ba za ta je makarantar bokon ba, ko ta ce Yaya ya rakata. Yau ma sai da ta makara sannan ta fita, amma kamar yadda ta yi tsammani, yana jikin gidan da yake kallon nasu, ya zubo wa ƙofar gidan su ido kamar mai jiran tsammanni.
Babu shiri ta koma cikin gidan, tana ɓata fuska da rarraba ido.
Yaya ya ce "Wai me yake damunki ne? Kin makara fa mene ne haka ne?"
Kawai ta fara hawaye "Wallahi Yaya mutumin nan kullum sai na gan shi, tsoro nake ji, na fara tunanin ko gamo na yi ma nikaɗai nake ganinsa, ni tsoro nake ji"
Cikin rashin fahimta ya ce "Gamo kuma? Wai wane ne? Wane mutumin ne?"
Nan Alina ta sake yi masa bayani, tun ranar da ta fara ganinsa.
Tamkar zai dake ta ya ce "Kuma shi ne baki gaya mini ba, uban waye mu je ki nuna mini shi"
Anty Nadiya ta ce "A'a Masoyi, ka tsaya a bi a hankali"
"Ba ruwanki" ya yi maganar yana kallon Nadiya a hasale.
Ya tasa Alina a gaba suka fita.
Ko da suka fita, suka tarar da shi a zaune, yana ta kokowa da wani takalmi zai yi masa round ya gyara shi. Yaya Ismail bai jira komai ba, ya yi fatali da kayan gayarn takalimin matashin, ya damƙi kafaɗarsa ya tashe shi tsaye.
"Malam waye kai? Meye haɗinka da yarinyar nan ka ke bibiyarta?" Ya yi maganar yana nuna masa Alina.
Ya kalli Yaya ya kalli hannunsa da ya riƙe shi, ya juya yana kallon Alina da ta yi tsuru-tsuru, tana rarraba ido kamar a ce kyat ta gudu.
"Waye kai malam?" Yaya ya ƙara maganar cikin ɗaga murya, yana ƙara riƙe kwalar mutunin.
"Wallahi ni ba kowa ba ne, kuma ba bin ta nake yi ba" Ya amsa da wata dakakkiyar murya, mai cike da nutsuwa da kamala, tamkar ba daga gangar jikinsa mai ɗauke da wannan yamutsatsun kayan maganar ta fito ba.
"Ƙarya ka ke yi, kusan sati biyu kenan, tana maganar wani yana bin ta, mene ne alaƙarka da ita, idan ma wani abin ne a ranka, ko mugun nufi ne da kai a kan yarinyar nan, wallahi wani abin ya same ta, sai ka zubar da hawaye a kan matakin da zan ɗauka a kanka na gaya maka"
Jiki a sanyaye ya ce "Ka yi haƙuri dan Allah, wallahi ni babu abin da zan yi mata" Ya yi maganar yana ɗaga hannunsa alamar saranda.
Tuni mutane suka fara taruwa, suna tambayar ba'asin abin da ya faru. Maigidan da mutumin yake zaune a ɗakin langa-langar da ke ƙofar gidansa, ya fito yana tambayar hayaniyar me ake yi, aka taru a ƙofar gidansa haka?
Yaya Ismail ya ce "Rana tsaka mun ga mutum yana kwana a ƙofar gidanka, ba tare da mun san waye ba, yana bin Alina, bamu san daga ina yake ba, wallahi aka yi mata wani abin daga kai har shi ba za ku ji daɗi ba. Dan mummunan mataki zan ɗauka a kanku baki ɗaya"
A rikice mutumin ya kalli matashin mai gyaran takalmi ya ce "Me ka yi mata, meyasa ka ke bin ta?"
A rikice ya ce "Wallahi ba bin ta nake yi ba, hanya ce kawai take biyo da ni, sai ta yi zaton bin ta nake yi, amma ba bin ta nake yi ba, ni wucewa kawai nake yi"
Mutumin ya sassauta muryarsa ta ce "Kana ji malam Isma'il, dan Allah ka yi haƙuri, wannan da ka ke gani, almajiri ne kawai ya ɗan zo ci rani ne, aka roƙi na ba shi dakin nan na masu gadina tun da babu kowa, ya zauna tun da yanzu ba ni da masu gadi, kan ya samu gurin zama, amma ina da yaƙinin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba. Ɗalibin Alqur'ani ne"
Yaya Ismail ya sakar masa wuya, yana zazzare ido, tare da yi masa wani irin mugun kallo.
Yana sakinsa matashin ya durƙusa yana tattaro kayan gyaran takalminsa, da Isma'il ya yi fatali da su. Gaba ɗaya sai jikin Alina ya yi sanyi, ta yi dana sanin gaya wa Yaya Ismail, ba ta ji daɗin yadda ya ɗauki abun da zafi har haka ba. Sai ta ga kamar mutumin ya muzanta da yawa.
Ya ce "Gara dai da na yi magana, tun da mu bamu san wane iri bane kawai ka kawo shi ka ajiye, babu bayani. Wallahi duk abin da ya faru ba zan lamunta ba"
Alhaji Sadi ya ce "Da yardar Allah babu ma wani abu da zai faru sai alkhairi, in sha Allah"
Ismail yadube ta ya ce "Wuce muje" ya riƙe hannunta suka yi gaba, ta waiwaya ta ga maƙwabcin nasu na yi wa mai gyaran takalmin magana, yayin da shi kuma yake ƙarasa harhaɗa kayan sa da Yaya Ismail ya watsar, Ya ɗago suka haɗa ido ita , ta yi saurin kawar da kanta suka shiga gida.
MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN.
Ayshercool
08081012143
AMANA KAYAN MATAN
Ingantattun magungunan mata 'yan sokoto.
Ina kuke manyan mata, mata ƴan ƙwalisa, ba muna mata ba. Ku zo maza ku garzayo mun zo muku da babbar harka ta ingantattun magungunan na mata. Ina macen da take son burge mai gidanta? Ina wadda take son zama shalele a wurin mijinta? Ina macen dake son zama ƴar gata a wurin Oga? Ina wadda take son mijinta ya yi alfahari da ita, kullum yana riritata kamar ƙwai? Ina macen da ta samu matsalar ƙaruwa a wurin haihuwa? Ina wadda sanyi ya yi mata yawa ta buɗe? Ina macen da take da ƙarancin ni'ima a jikinta? Ina wadda take jin zafi a wurin saduwa? Hajiya kin taɓa amfani da maganin da zai matse ki ya mayar dake tamkar buduwa? Ko har yanzu kina nan a buɗe kamar bakin gari? To muna masu farin cikin sanar daku mun zo muku da ingantattun magungunan gyaran jiki na mata masu kyau da inganci kamar su..
Gumbar madara
Gumbar mata
Gumbar aya
Gumbar chaku
Gumbar dake saukar da ni'ima
Gumabar taƙadari
Gumbar riɗi
Gumbar dabino
Gumbar uku alkhairi
Kazar amare
Jijjiɓen saniya
Tabaje
Tsimi
Rikita mai gida
Jigidar tada sha'awa
Ruwan boom ruwan daɗi kenan
Ɗan matse
Karya gado
Maganin sanyi
Zumar ƙarin ni'ima
Zumar rage ƙiba
Zumar ƙarin ƙiba
Zumar riɗi
Mai zamani
Emergency powder
Tarhama
Kafi budurwa
Sabon budurci
Alfijir
Gamzaki
Garin dahuwar nama
Sabaya
Miskin ɗahara
Da dai sauran su. Namu ba irin na su bane, bamu fito ba sai da muka shirya, muka tabbatar da kwaliti da inganci kayanmu. Ƴar uwa gyara shi ne mace, aka ce ko kina da kyau ki ƙara da wanka, ina matan dake cewa ba sa shan kayan mata iya fruit kawai suke sha? To ku sani ko wane allazi da amanun sa, aikin fruit daban, aikin waƴan nan daban. Hajiyata ki saki jiki kawai ki zo musa labule, a gwangwaje ki da kayan da zaki rikita my house da su. Ki susuta shi, ya zamana duk inda yake kina maƙale a cikin ƙalbinsa. Matuƙar kika yi amfani da kayanmu, ina mai tabbatar miki da ba boka, ba malam za ki mallaki mijinki ciki ruwan sanyi, sai yadda kika yi da shi. Ga mai buƙatar kayanmu zai iya tuntuɓar waƴan nan lambobin 08163516796 ko 08081012143 muna aika saƙon mu a ko'ina.
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
SARA DA SASSAƘA
AYSHERCOOL
BRIGHT PENS
YOTA 002
Arewapen ayshercool
Page 3
Da sauri ya sunkuyar da kansa, sai dai saƙon da ya aika mata ta idanunsa, sun yi tasiri jikinta ya yi sanyi, har ta ɗan rasa nutsuwarta. Da sauri ya tashi ya kwashi kayan aikinsa da ya tattare, ya shige ɗakin da yake kwana ya rufo ƙofar.
Gaba ɗaya sai Alina ta ji babu daɗi, a ce babba kamar wannan, Yaya Ismail ya yi masa tijara a gaban mutane, har sai da fuskarsa ta nuna yanayi na damuwa, sai ta ji sam ba ta ji daɗi ba, har ta ji dama ba ta gaya wa yayan ba.
*****
Ramata na tsugunne, tana ta aikin wanki, yayin da Juma ke ƙoƙarin tuƙa tuwo, Baffa ya yi sallama. Suka amsa masa gaba ɗaya. Ramata ta yinƙura ta tashi ta je ta karɓi kayan hannunsa.
Juma ta kalle shi ta ce "Sannu da zuwa"
"Yauwwa sannu da gida"
Bayan Ramata ta ajiye kayan ta ce "Baffa sannu da zuwa"
Baffa ya ce "Yauwwa Ramatuna autar Baffa, Ubangiji Allah ya raya mini ke, ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare"
"Amin Baffana" Ta yi maganar cikin murmushi.
Juma ta ce "Nima Allah ba mantawa ya yi da ni ba, da bai bani haihuwa ba, da kullum sai ka saka Ramata a gaba ka na ce mata 'yar auta, domin ka goranta mini"
Baffa ya kalle ta ya ɗan ɓata fuska ya ce "Haba Juma ya za a yi na yi miki gori ma, ke ce dai ki ke tunanin haka, amma ni ban yi miki gori ba" Juma ta tsuke fuska tare da yi masa banza.
Bayan ya zauna a kan tabarma ya buɗe ɗaya daga cikin ledojin da ya zo da su ya ce "Ramatu, ga man shafawa da man wanke baki, da sauran abubuwa na shirye-shiryen komawarki makaranta na fara sayo miki, sati mai kamawa za ki koma ko?"
Cikin farinciki ta ce "Eh Baffana. Baffa kana yi mini addu'a ko? An kafe jarrabawarmu fa"
Baffa ya ce "Ba nima na gaya miki na ji a radiyo, an sako jarrabawar ba? Ai Allah ba zai kunyata mu ba Ramata, in sha Allah sai kin zama abar alfahari da kwatance a garin nan"
Ramata ta ce "Allah ya amince Baffa. Amma Baffa zan ci gaba da karatun kuwa?"
Baffa ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ramata zan so hakan, domin shi ne cikon burina. Amma kina kallon tambarin da aka yi mana a garin nan, saboda karatun da ki ke yi. Ni na san ko iya haka ki ka tsaya Alhamdillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Amma idan Allah ya kawo damar ki yi karatun, ko bayan raina ne, zan bar wasiyya a abin da na bari, a ware wanda za a biya miki, ki ci gaba da karatu, ko ma ni ma ware da kaina.
Juma ta juyo ta zuba masa ido, daga bisani ta taɓe baki ta ce "Taɓɗi abin na yi ne ashe"
Ba su kula ta ba, Baffa ya sake cewa "Ramata ga wannan saiwoyin, ki dafa su da kyau, gobe in Allah ya kaimu zan je duba mara lafiya"
Ramata ta yinƙura ta tashi tana faɗin "To Baffa"
*****
Alina ce ta shigo da sallama, ta ɗora da cewa "Anty na dawo"
"To sannu da zuwa, ya makarantar?"
Alina ta amsa da "Lafiya ƙalau, Yaya bai dawo ba?"
"Ban da abin ki Alina, dama yana da ƙa'idar lokacin dawowa ne? Amma dai ɗazu ogansa ya kira shi, zai je ya dubo masa wasu kaya, ya ce idan bai dawo ba, mu rufe ƙofa wataƙila sai Allah ya kaimu gobe"
Alina ta ɓata fuska ta ce "Ni wannan ogan nasa ya fiye matsala, ni ba na son wannan aiken da yake yi masa"
Nadiya ta yi murmushi ta ce "Kin fiye rigima ke kuma ba. Alina shi ne babban yaronsa, duk sauran cin amanarsa suke yi. Kuma idan bai je aiken ba da me zamu rayu, tun da a ƙarƙashinsa yake nema"
Jiki a sanyaye Alina ta ce "Antynmu tafiye-tafiyen nan ne da yake yi fa ba na so"
Cikin mamaki Nadiya ta ce "Saboda me?"
"Ba na son bin manyan hanyoyin nan, ba na son ya yi hatsari"
Da sauri Nadiya ta ce "A'uzubillah, wace irin magana ce haka Alina?"
Tuni idanun Alina suka cika da hawaye ta ce "Kullum ya yi tafiya hankalina ba ya kwanciya sai ya dawo, ina jin tsoron ya yi hatsari wataran a hanya. Duk ranar da aka ce babu ke ko Yayana a duniya ya zan yi?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska. "Na san dole hakan za ta faru watarana, amma b a na fatan ku riga ni barin duniyar nan, Allah ya sanya zamu daɗe tare"
Nadiya ta ce "Alina, shi ajali ba sai na kan titi ko na cikin ɗaki ba, yana iya faruwa a kan kowa, sai dai mu yi addu'ar Allah ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare da juna, kamar yadda ki ke fara. Bari a yi sallar magariba, sai na kira miki shi ki ji muryarsa" Alina ta jinjina kai tana share hawayen fuskarta. Ta nufi ɗakinta Nadiya ta bi ta da kallo, har ta shige, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ci gaba da abin da take yi.
Washegari da yamma, Yaya Ismail ya dawo gida, Alina ta rirriƙe shi tana murna har da hawaye. Nadiya ta ba shi labarin abin da Alina ta yi jiya, da ta dawo ta tarar baya nan.
Ya kalli Alina, cike da matsananciyar ƙaunarta ya ce "Ƙanwata, da gaske ki na tsoron na mutu na bar ki?" Ta jinjina masa kai cikin damuwa.
"Aikin gama ya gama, mutuwa dole ce Auta"
Cikin kuka Alina ta ce "Dan Allah ka daina faɗa ba na so, dan Allah ka gaya wa oganka ya daina yawan aikenka guri mai nisa ƙanwarka tsoro take ji"
Rungume Alina ya yi yana murmushi tare da rarrashinta. "Babu abin da zai faru sai alkhairi, idan na zauna da ya ya zan kula da ku? Ki yi haƙuri ki din ga yi mini addu'a kin ji ko?"
Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta ta ce "Bari na je na shirya, na gaya wa Anty zan je sayo cardboard paper, zan yi assignment"
Ya ce "To a dawo lafiya, ta baki kuɗi ko na ƙara miki?"
"Ƙara mini" Ta yi maganar tana miƙa masa hannu. Ya yi dariya ya zura hannunsa a aljihu, ya ciro ɗari biyar ya bata.
Bayan fitar Alina, ya dubi Nadiya ya ce "Masoyiyya ya dai?"
"Alina fa yanzu ba yarinya ba ce ba, lokaci kaɗan ya rage ta shiga shekara goma sha biyar" Ta yi maganar tana tsuke fuska.
Cikin rashin fahimta ya ce "To meyafaru?"
Nadiya ta ce "Ina maganar rungume ta da ka ke yi, wannan ba dai-dai ba ne ba, ba abu ne da ya dace ba"
Ya ƙare mata kallo ya ce "To abin ya motsa kenan, shaiɗan zai yi miki kururuwa"
Ta girgiza kai ta ce "Shaiɗan bai yi mini kururuwa ba, ina dai gudun kai ya yi maka ne"
Ya shafa sumar kansa ya dube ta ya ce "Nadiya, ƙa'idar ba za ta canza ba, a kan Alina, zan iya lalata komai ciki har da ƙa'idar, shi kansa shaiɗai ɗin ya san na fi ƙarfin ya yi mini kururwa a kan Alina. Alina ƙaddarata ce, kuma jarrabawata. Kin san bawa ba ya gujewa ƙaddararsa, a ƙoƙarin gujewa ƙaddarar mutum ka iya halaka ba ki ɗaya. Dan haka dole ki yi haƙuri ko domin gudun halaka. Nadiya ta dube shi cikin ƙunar rai, amma ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba.
Kasancewar ba a daɗe da idar da sallar la'asar ba, rana ba ta gama yin sanyi ba, balle masu zaman majalissa su fara bin dakali da tebura su na zama.
Alina na fitowa hanya, ta tarar da shi a tsaye a bakin titi, hannunsa rungume da bagco yana ƙoƙarin tsallakawa, su na yin ido huɗu, cikin azama ya yinƙura zai tsallaka titi, dan yanzu kamar tsoron ganinta ma yake yi tun da Isma'il ya tijara shi a gaban mutane. Yana ƙoƙarin tsallakawa wani matashi ya taho a kan babur da gudu, ya buge shi. Take ya faɗi, bagco hannunsa ma ta faɗi, yalo ne fal a cikin bagcon, aikuwa ya watse a ƙasa, a kan ƙaramin titin cikin unguwar. Matashin da ya buge shi kuma, ya ja baburinsa ya zura da gudu, ba tare da ya tsaya ba
Da sauri Alina ta bi yalon da gudu, ta fara tsintowa, tana sakawa a hijjabinta, saboda yadda suke ƙoƙarin shiga kwata. Sai da ta tsince su tsaf, sannan ta nufo inda yake, a ɗan tsorace ta ce "Sannu" sau ɗaya ya kalle ta, ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Ta ɗauki buhun, ta tattare ta zuba masa a ciki. Ta sake cewa "Sun ɓaci da ƙasa sai dai ka wanke. Still ya yi shiru bai