Sara Da Sassaka Hausa Book Complele

Author :  AYSHERCOOL Category :  Arewa Story

Chapter   8 / 19

21K to 24K   out of 56.8K words

sunana na gaskiya ba, sunana na gaskiya Fatima".

Ya ɗan yi turus yana kallonta, fuskarsa ɗauke da murmushi.

"Ya na ga kana murmushi?"

"Sunan Innata ne da nake matuƙar so, duk da ba ita ta haife ni ba"

Alina ta yi dariya ta ce "Ashe kai ɗana ne, to ɗan albarka zan din ga ce maka"

Jinjina kai kawai ya yi, yana murmushi, ita kuma ta shiga gida. Murmushi ta ɗan din ga yi, da ta tuna saboda ita ya je makarantar su, saboda ya haska mata hanya. Da ta tuna abin da Yayanta ya yi masa sai ta ji babu daɗi, kasancewar yanzu ta fahimci yana da kirki, kawai dai ɗabi'unsa ne wasu lokutan kamar mara gaskiya.

Mamman kuwa bayan ya shiga ɗakinsa, ya zare rigar jikinsa, ya gyara shimfiɗarsa, ya fito da indomie a leda, ya zazzage a wani kwano, ya cinye ya sha ruwa. Ya ɗaga ƙasan 'yar katifar da ke ɗakin, ya din ga kallon ƙasan katifar sannan ya mayar da katifar ya gyara ya kwanta yana ɗan yin miƙa.
Ya ciro wayarsa daga gefen katifarsa, ya tura wasu code zuwa ga wata lamba. Ya juya ya kwanta.

*****

YELWA

Baffa ne ya yi zuguum yana sauraren radion da ke gabansa, yanayin fuskarsa ya nuna ruɗewa da tsoro.
Ya numfasa ya ce "Juma"

"Na'am" Ta amsa tana tattara hankalinta a kansa.

"Ki na jin wata masifa ko?"

"A ina?"

"A radion nan da nake ji"

Ta girgiza kai ta ce "Me aka ce?"

"Faɗan manoma da Makiyaya a can wani yanki, an yanka manoma yankan rago su kusan goma sha biyu da sunan ɗaukar fansa"

Juma ta waro ido ta ce "Yankawa kuma?"

"Wallahi yankawa, ga shi ina ji a radio"

"Innalillahi, yanzu Jauro sai a yanka mutum, kuma da wuƙa aka yanka su ko da me?"

Baffa ya ce "Ina zan sani, abin da dai suka ce kenan. Wallahi abin nan yana bani tsoro. Mu ma kusan irin wannan rikicin muke fuskanta tsawon shekaru, ina tsoron ya rikiɗe ya zama wani abu daban."

Juma ta ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi da yardar Allah"

Baffa ya jinjina kai ya ce "Haka nake fata, amma haryanzu ina haƙurƙurtar da samarinmu, a kan lallai sai sun ɗauki fansar abin da aka yi mana. Ke dai Allah ya kyauta kawai".

*****

Rahama ce ke zaune a bakin kwanarsu, tana kallon 'yan hostel ɗinsu, sun sha kwalliya su na ta raye-raye kasancewar weekends ce. Sun saka bokitai da jarakuna su na ta kaɗe-kaɗe. Littafi ne a hannunta amma tana kallon littafin tana kallonsu, saboda abin da suke yi ɗin yana saka ta nishaɗi.

"Yelwa, kin noƙe kina wani murmushi, taso ki taka"

Cewar wata senior ɗin ta.

Rahama ta hau dariya tana girgiza kai.

Ruƙayya  ta ce "Idan Rahama ta yi rawa, na yi alƙawarin bayar da kyautar sadine gwangwani goma wallahi" Shewa suka hau yi, Rahama kuwa rufe fuska ta hau yi tana dariya.

"Ai wallahi Ruƙayya kin san sadine ɗin nan ba zai ciwu ba, in dai sai Rahama ta yi rawa za a ci shi. Ita a makiyayan ma ma irin na 1980s ɗin nan ne."

Suka din ga tsokanar Rahama, ƙarshe ta bar musu Hostel ɗin. Naja ce ta biyo bayanta tana faɗin "Yaya Rahama" Rahama ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am Nana".
"Dan Assignment ne da ni, na kasa ko za ki koya mini"
Rahama ta ce "Me zai hana na koya miki, wanne subject ne?"

Naja ta ce "Your favourite Maths"

Rahama ta ce "Mu je Library, sai mu yi a can" Naja ta jinjina kai, ta karɓi litattafan hannun Rahama suka tafi. Boarding kenan, gidan ka zo na zo, amma duk ƙin ka da mutane haka zaka haɗu da wanda za ku rayu tare tamkar yan gida ɗaya.
Duk da akwai ƙalubale, amma ana koyon darussan rayuwa.

*****

"Assalamu alaikum. Salamu alaikum" Cikin bacci yake jin 'yar muryar na yi masa sallama. Da kyar ya iya motsawa, ya tashi ya saka rigarsa, ya buɗe ƙofar. Da idanunsa ta fara tozali, ta ɗan ja da baya a tsorace.
"Ahh, ka yi haƙuri, ban san bacci ka ke yi ba, da dam..dama takalimina na kawo, yi haƙuri." Ya miƙa mata hannunsa yana tsare ta da ido. Jikinta na ɗan rawa ta miƙa masa takalaman nata.
Ya fito tare da kayan aikinsa, sai dai yau ta ga fuskarsa a tsuke sosai da sosai. Ta lura da yadda yake aikin yau a hankali sosai da sosai.

So take ta tambaye shi ko lafiya, amma ta kasa sai satar kallonsa da take yi. Gani ta yi ya tsaya cak da wanke takalmin, yana ɗan rintse idanunsa.

"Meyafaru?" Ta faɗa a ɗan rikice tana kallonsa.

Da hannunsa ya nuna mata cikinsa, ya tashi, ya ajiye komai a gurin, ya koma ɗakinsa. Jikinta na rawa ta tashi ta tafi gida. A kitchen ta samu Nadiya tana aikin girki. Cikin damuwa ta ce "Antynmu idan ki na da maganin ciwon ciki ki bani zan ba wa Mamman cikinsa ne yake ciwo"

Nadiya ta tsaya ta ce "Waye hakan?"

"Mai gyaran takalmi"

"To  ba shi da lafiya, to Allah ya ba shi lafiya, duba jakar magungunan ki gani idan akwai" jikin Alina na rawa ta shiga ɗakin Anty, tana duba jakar da suke ajiye magunguna, ta dubo maganin ciwon ciki. Ta fito tana faɗin "Anty na samu, amma akwai sauran kunu? Kin ga ba zai sha magani bai ci komai ba"

Nadiya ta ce "Eh gaskiya ne, amma dai da yayanki na ajiyewa kunun, kin san zai iya nema da rana ya ce zai sha"

Cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Antynmu ki kawo a ba shi, sai ki cewa Yayan kununan ya ƙare.

Nadiya ta ce "To Alina, a ba shi Allah ya sauwwaƙe, ya sanya kaffara"

Ta tsiyaye kunun gyaɗar a kofi mai murfi, ta yi waje da sauri. Nadiya ba ta kawo komai a ranta ba, saboda sanin halin Alina. Wasu lokutan a hanya za ta tsinto almajiri, ta kawo shi gida ta ce sai a ba shi Abinci ko ta ce sai Isma'il ya ba shi kuɗi. Duk da rashin mu'amala da ita da samarin unguwar ba sa yi, amma tana shiri da alamajirai sosai da sosai. Saboda tana son bayar da abu.

Cike da wauta da ƙuruciya, Alina ta faɗa ɗakin Mamma, ba tare da sallama ko neman izini ba. Da wani irin mugun zafin nama, ya saka filo akan wani abu ya rufe. Idanunta ba su kai ga tantance mata abin da ta gani ba, ya rufe da fulon.

Ta ɗan sororo amma ta basar ta miƙa masa kofin kunun ta ce "Ga kunu sai ka sha, sai ka sha maganin. Tsigar jikinsa duk ta tashi, saboda azabar ciwo har wani gumi ne yake tsatsafo masa ta kan karan hancinsa. Ya saka hannu ya karɓi kofin. Kunun  da zafinsa ya kafa kai ya din ga zuƙarsa. Bai shanye ba, ya miƙa mata hannunsa, ta saka masa maganin ya ɓalle ya haɗiye ba tare da ko ya haɗa da ruwa ba.
Ta tsaya cike da rashin sanin abin yi tana jera masa sannu. Bai amsa mata ba, sai yatsun ƙafarsa da ta ga yana ta lanƙwasawa, alamar yana cikin matsanancin ciwo.
Ya juyo da fuskarsa a hankali, duk gumi ya tsatstsafo masa, wasu irin jijiyoyi sun shata a goshinsa raɗa-raɗa, sai idanunsa da suka yi jawur.
"Je ki" Ya furta da kyar. Maimakon ta fita sai ta tsaya tana kallonsa, ganin kamar zai fita hayyacinsa.

"Ki fita!" Ya yi magana cikin tsawa, yana nuna mata hanyar fita. saboda rikicewa ba ta san yadda aka yi ta ganta a waje ba. Ta kwashe takalmanta ta nufi gida a tsorace.

Nadiya ta ce "Alina yanzu nake shirin fita na ga ko lafiya, ki ka daɗe, kin san fa fita zan yi, zan je Asibiti"

Alina ta ce "Lafiya ƙalau, sai kin dawo" Ta shige ɗaki. Nadiya ta bi Alina da kallo tana mamakin meya tsorata ta haka, ba ta sake magana ba ta fita. Cike da tausayawa Alina take tuno yanayin da ta bar shi a ciki, amma da tuna tsawar da ya yi mata, sai ranta ya ɓaci gaba ɗaya, ta ji haushi ba kaɗan ba"
Sai dai ba ta daina tantama da zuciyarta ba a kan abin da ta gani a ɗakin nasa ba. Idan ba gizo idonta ya yi mata a kamar dai bindiga ta gani a ɗakin ya saka pillow ya rufe. Sai dai ta ƙi yarda da hakan ta gani, ta basar ta ci gaba da kokwanton ba bindiga ta gani ba.

Sai dai hakan bai hana ta lokaci-lokaci ta din ga leƙa ƙofar gida ba, ta ga ko za ta hango ya fito ba.

*****

Kacalla ne tsaye a cikin dokar daji, tare da Sadauki, gabansu wani buhu ne a ajiye.
Ya dafa kafaɗar Sadauki yana kallon idonsa.
"Sadauki amanar kacalla"
ya yi murmushi ya ce "Allah ya taimaki Uban ɗakina"

"Ka ga dai yadda lamari ya kaya, na yarda da kai na san ba za a samu kowace irin matsala ba da yardar Allah. Ka je ka ƙarasa shirya komai da mutanenka, duk abin da ake ciki, mu yi waya."

Sadauki ya ce "An gama shugabana, ka yi layar zana, ka bi ta gabasa zan Kudu da kayan, ka saka a gyara mana hanya"

"Shikenan babu damuwa, Allah ya tsare"

"Amin" ya saɓa buhun nan a kafaɗarsa ya yi gaba.

*****

ALINA

wunin ranar ba ta sake ganin gilmawarsa ba, abin ya din ga damunta, ta din ga tunanin ko yaya yake.
Monday da ta fito makaranta, ta tarar da ɗakinsa a rufe, amma bai saka mukulli ba.
Har guri ta samu ta ɗan tsaya, ta gani ko zai fito, amma shiru ta gaji ta tafi, dan sai da ta makara ma.

*****

YELWA

Baffa ne yake tafe sannu a hankali, yaje ya bawa wani yaro maganin maciji, saboda maciji ya sare shi a ƙafa, ya duba ya ga wani mara lafiya da ya yi wa ɗorin karaya, daga nan ya biya kasuwa, ya ɗan yi sayayya ya nufo gida.
Yana ta sauri, ya ji ana yi masa sannu da zuwa, ya tsaya ya waiwaya ya ga wane ne, kawai ya ga Saleh. Baffa ya yi shiru bai ce komai ba, ya sa kai zai ci gaba da tafiya.
"Ba za ka amsa sannu da zuwan nawa ba? Babu faɗa mai ya kawo gaba?"

Baffa ya tsaya, ya kalle shi ya ce "Ɗan samari, ina gama ka da Allah, idan ka san shi. Kana kuma tsoron sa, ka fita daga harkata" Ya yi maganar idanunsa suna yi ja, muryarsa na rawa.

"Baba tun da Allah ya haɗa mu zaman guri ɗaya, ai haraka ta zame mana dole. Abin da zai iya cutar da kai na gano, na ce bari na sauke hakkin maƙwabtaka"

Baffa ya tsaya cikin rashin fahimta yana kallon Saleh. "Duk da lokaci ya so ya ƙure, amma ina tausayawa yadda ƙaddara ke bin ahalinku, mussaman ma kai.
Duk da Ramata ba ta gari, amma kana iya ɗaukar mataki."

Baffa ya ce "Ramatan kuma me ta yi muku, yarinyar da tana makaranta ma?"

"Tana soyayya da ɗan uwana Bukar, wanda ka sani na sani, babu ga maciji a tsakaninmu da ku, duk abin da ya faru ka kuka da 'yarka, na gaya maka ne ka yi wa tufkar hanci, kar ita ma ka rasa ta"

Cikin mamaki Baffa yake kallon Saleh, sai dai ya gaza cewa komai, sai bin sa da yake yi da ido baki buɗe cikin mamaki. Sam bai ji maganganun Saleh sun shige shi ba. Yarinyar da ba ta garin ma, ga ta da gudun magana yaushe za ta je ta yi wannan katoɓarar. Kawai ya sanya wa zuciyarsa ƙarya Saleh yake yi.

*****

Bayan kwana biyu.

An taso 'yan makarantar su Alina, Hafsa ta ce "Ke na sato mana littafi, yau zan karance shi cikin dare in sha Allah"

Alina ta ce "Haba dai ya sunansa?"

Hafsa ta ɗan yi shiru ta ce "Na manta, amma dai zan karanta mana"

"To shikenan, sauran gobe in Allah ya kaimu, ki ƙi ba ni labarin. Allah dai ya sa an zuba soyayya a ciki"

Hafsa ta yi dariya ta ce "Ai da ganin bangon littafin ma, ke dai ki jira, zan karance mana shi, shi kuma mu ji me aka yi a cikin sa"

Alina ta ce "Kin san littafi idan da soyayya a ciki, subhanallah har wani nishaɗi yake sakawa."

Hafsa ta gyaɗa kai ta ce "Ina ta ƙoƙarin ganin na sake da yaya Hafiz ɗin nan, nima mu din ga soyayyar nan na kasa, kunya ma nake ji wallahi"

Alina ta kwaɓe baki ta ce "Ke kenan, da aka bawa damar ki yi soyayyar ma, ni duk wanda ya ce yana sona zagi yake sha a gurin Yaya ya kore shi, wai ni yarinya ce. Idan aka ganni zata ake babba ce ni"

Hafsa ta ce "Kuma ga maza na sonki, amma wataƙila sai kin yi candy zai bari"

"Mhmm ai ni na zubawa sarautar Allah ido ne ma, na bar Yaya da halinsa"

Tun da Alina suka fito daga makaranta, take ankare da yana bin su a baya, amma ta basar, suke ta hira da Hafsa. Amma a ƙasan zuciyarta, ta ji daɗin ganinsa da alamar ya warke. Suka yi sallama da Hafsa ta bi hanyar gidansu, Alina ma ta bi tata hanyar.

"'yar ƙwalisa" Ya yi maganar yana ɗan ƙara sauri.

Sauri ta ƙara ita ma, ta ƙi ko waiwayowa, ta basar da shi.

"Alina" ya kira sunanta. Ta tsaya tana zumɓura baki, ta  waiwaya kai tana kallonsa.

"An taso?" Ya yi maganar yana kallonta. Ta yi shiru tana kawar da kanta gefe.

Ya sake cewa "Amm dama zan ce miki na gode ne"

"Da aka yi me?" Ta yi maganar tana tattaro jarumtar kallon idonsa amma abu ya gagara.

Ya ɗan ja numfashi ya ce "Maganin ciwon ciki, da kuma Abinci da ki ka bani"

Ɗan murguɗa baki ta yi ta ce "Daka yi mini tsawar" Ta yi maganar tana tura baki.

Ya ɗan rungume hannayensa ya ce "Ohh zafin ciwo ne fa, kuma ina jin tsoron kar a zargi wani abu, mussaman yayanki, na san ya ganki a ɗakina zai iya yi mini duka ma"

Idanunta ta ɗaga tana ƙare masa kallo, sai dai ba ta kalli idonsa ba, ta tura baki ta ce "Tun da abin alkhairi na yi maka, sai ka gaya mini a hankali ai. Amma ka yi mini tsawa. Kuma ni ba na son a yi mini tsawa, sai da na tsorata"

Ya yi shiru yana kallonta.
Ba tare da ta kalle shi ba a shagwaɓe ta ce "ka bani haƙuri to"

Ya yi turus yana kallon 'yar abar da da kaɗan ta fi ƙugunsa, tana iƙirarin ya bata haƙuri, kuma yanayin fuskarta ya nuna da gaske take abin da take faɗa har zuciyarta...

Ayshercool
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
Sai shaidar biya ta 08081012143

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

SARA DA SASSAƘA...

YOTA /002

P7

Ganin ya ƙi magana yana ƙare mata kallo, ya sanya ta yi gaba ta bar shi a gurin, Tana ƙunƙuni, da mita ƙasa-ƙasa.

Bai san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, ganin tsagwaron ƙarfin hali irin nata.

*****

PRESIDENTIAL RESIDENCE.

Garin ya yi shiru, ba a iya jin motsin komai, tamkar babu halitta mai numfashi a gurin. Sannu a hankali yake kaiwa yana komowa a cikin katafaren ofishin. Ya koma ya dafa kan kujera yana juya ta a hankali da hannunsa.
Ya kalli agogon office ɗin, ƙarfe uku saura mintuna goma. Yana sauke idanunsa, aka buɗe ƙofar ofishin aka shigo.

"Halilu ka ƙaraso?" Ya yi maganar yana ajiyar zuciya.

Cikin girmamawa kamar ya dungura ya ce "Yes sir na ƙaraso, a yi mini afuwa, ina fatan ban ɓata maka lokaci ba?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a. Bismillah zauna"

Halilu ya ja kujera ya zauna, yana daga tsaye ya tura wa Halilu jarida ya ce "Ina fatan ka ga wannan, na san ma wataƙila ka riga ni gani?"

Halilu ya ja jaridar ya fara dubawa. Ya shafi goshinsa, da yake jin kansa na yi masa wani irin ciwo. "Da na san abin da zan tarar kenan a ƙasar, da ko a mafarki ban nemi mulki ba. Tun bayan rantsar da ni, babu abin da na cimmawa mai muhimmanci sai ma koma baya da na fara fuskanta a ƙasar. Wannan case ɗin shi ne na uku da ya faru a tsukin kwanakin nan, dole mu yi wa tufkar hanci, kafin lamuran su fi haka ƙazanta. Wancan yankin na yamma satar mai ya ta'azzara, gabas kuma rikicin manoma da Makiyaya, da rikicin ƙabilanci. Gobe in Allah ya kaimu ka tara manema labarai, ka sanar musu na ƙoƙarin ɗaukar matakan inganta tsaro, ka dai san abin da yakamata ka yi a kai. Sannan a shirya mini zama da shugabannin rundinonin tsaro, gobe da misalin ƙarfe tara na dare. Za kuma mu naɗa wakilai su je ta'aziyya gurin da abin ya shafa"

Halilu ya numfasa ya ce "Shikenan sir, za a gabatar da duk abin da ka ce, na bar ka lafiya"

Jinjina kai kawai ya yi cikin ƙarfin hali.

*****

Tana zaune a kan kujera, ta ɗora wayarta a kan ƙaramin table ɗin gabanta, tana kallon paper gabanta, da ta yi rubuce-rubuce a jiki, tana rehearsal.

Ta bayanta ya ƙaraso yaka leƙa paper, ya ja guntun tsaki ya ce 'Yar wahala, ke dai kin ga ta kanki Laila" Ya yi maganar yana dungure mata kai.

Ta ɗago tana murguɗa baki ta ce "Ba ruwanka da ni, na gaya maka ka fita daga sabga ta"

"Da ruwana da ke, ke ba ki san yanzu haushinki nake ji ba, kamar na shaƙe ki na huta"

"To sai ka kashe ni ka huta ai"

Mama ce a gefe, a kwance a kan fulo hannunta riƙe da counter, ta ɗago tana faɗin "Sadam ba ruwanka da ita dan Allah, ka ƙyale ta"

"Mama ke ki ke goya mata baya dama, kiri-ƙiri yarinyar nan, ɗan aikin nan da ta samu, ɗan abin da ake ba ta yana taimakawa, amma saboda baƙin hali, ta ja an kore ta, ta dawo wahala wai content creation. Ko uban wa ya gaya mata ɗan jarida yana ɗaukan side ya shiga siyasa oho mata"

Laila ta ce "Ni fa ba siyasa na shiga ba, tun da an kore ni, i decided to take another decision. Dama can ina content ɗina. Beside yanzu na samu cikakkiyar dama na yi abin da nake so, a hankali zan yi building pages ɗina na fara samun kuɗi"

Sadam ya yi tsaki ya ce "Aikin banza ƙiba a kunne, comment section ɗin ki ban da zaginki ma babu abin da suke yi"

"Duk da haka ba zan gaji ba, masu yaba mini sun fi masu zagin yawa. Sannan masu zagin ma taimakona su ke yi gurin pushing ayyukana. Ni fa na gama gane ka. Kuma ina

8 / 19