Author : AYSHERCOOL Category : Arewa Story
tsira ba, ni wane tabbaci nake da shi zan tsira?"
"Ke dalla yi wa mutane shiru da wannan falsafar banzar taki. Ba nan ki ke zama kina video kina goyon bayan gwamnatin ba. Dalla tashi ki ɗora mana tuwo"
Mama ta ce "Kai dakata mini, Laila na da gaskiya. Duk inda iyaye da yan uwan yaran nan suke, hankalinsu a tashe yake. Ubangiji Allah ya tseratar da su cikin Aminci. Ni kaina abin ya tsaye mini. Har da yarinyar wata class mate ɗinmu aka sace wallahi abin gwanin ban tausayi. Tare muka yi islamiyya da ita"
Sadam ya ɓata fuska ya ce "Ahh lallai aiki ya ganku, gara na fita tun wuri na nemi abin da zan ci, tun da naga alamar zaman makoki zaku yi yau, ba za ku dafa abinci ku bani ba"
*****
Tamkar marasa amfani, haka suke hantarar ɗaliban.
Su na jere a zazzaune, ana raba musu buredi a wulaƙance, mai rabon buredin ya miƙa wa Ramata. Ta miƙa hannu za ta karɓi buredin, ya haɗa da hannunta ya riƙe yana ƙare mata kallo. Jikinta ya yi sanyi ya hau rawa, ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta. Amma cike da rashin ɗa'a ya fara shafa hannun nata da ɗaya hannun nasa, har zuwa damtsenta. Jikinta ya hau rawa cike da tsoro tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ya tsare ta da ido da baƙar fuskarsa yana sauke numfashi.
"Kai kar fa ka kuskura ka yi abin da ba shikenan ba, kar ka ja mana tashin hankali" cewar na kusa da shi, da suke raba buredin tare.
Ya yi murmushi tare da sakar mata hannunta, yana yi mata murmushi.
A hankali Rahama ta yi ajiyar zuciya, dan tsoro ne ya shige ta, ta zata wani abin zai yi mata.
Ƙarar sautin kusantowar babura ce ta cika gurin, gaba ɗaya suka zuba wa inda suke jiyo sautin ido. Su goma sha biyu ne suka zo a kan babura kowannensu riƙe da miyagun makamai.
Idan da sabo, ya ci a ce Rahama ta saba da ganin tashin hankali, amma a wannan karon ma sai da tsoro ya shige ta, ganin uban bindigun da suke hannun maharan kamar za su yaƙin duniya.
Cikin girmamawa suke gaishe shi, ya din ga jinjina musu kai, ya din ga ƙarewa 'yan matan kallo, ya tsayar da idanunsa a kan Rahama. Ya yi shiru yana ƙara ƙura mata ido, tamkar mai son hango wani a kan fuskarta.
Sai dai ita ma ta ɗan tsura masa ido, ba ta kai ga janye idanunta ba, ya tako a hankali nufo ta, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa ta daina kallonsa. Ya ƙarasa ya tsuguna a gabanta yana kuma ƙare mata kallo, tun zuwansu ya lura da yadda take ta kare jikinta da hannunta.
"Kalle ni" Ya faɗa cikin kakkausar murya.
Tamkar zuciyarta za ta faso ƙirjinta ta fito, saboda luguden da take yi, haka ta ɗago idanunta da kyar ta kalle shi. Ta mayar da kanta ta sunkuyar.
"Kin sanni ne?" Ta girgiza kai a hankali.
Ya saka hannu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Da gaske? Kalle ni dai, na ga kina kallona kamar kin sanni ko?" Ya yi maganar yana murmushi.
Ta sake girgiza masa kai tana sunkuyar da kanta ƙasa, ba tare da ta kalle shi ba.
"A jam fullo?" (Ke Bafulatana ce?"
Ta jinjina kai alamar eh.
""ko honɗun wuro njahaa?" (Daga wani gari ki ke?"
"Yelwa" Ta faɗa a tsorace.
Ya waro ido tare da yin murmushi ya ce "Daga Yelwa aka kai ki makarantar kwana? gaskiya ne, lallai makiyayan Yelwa sun waye, an samu gagarumin ci gaba Sannu ko, ku kwantar da hankalinku babu abin da za mu yi muku, za ku koma gida lafiya in sha Allah, za mu ajiye ku ne nan da wani ɗan lokaci, domin cikar muaradanmu da na iyayen gidanmu. Da mun kammala za mu sake ku. Kun kafa tarihi a duniya, ɗalibai na farko da aka yi garkuwa da su. Ya yi maganar yana murmushi.
Ba tare da ta san ita yake kallo ba, ta sake ɗagowa ta kalle shi, fari ne sai dai ba tas ba, idanunsa sun sha farin kwalli rabajau, yanayin fuskarsa da yadda yake magana, ba ka ce ko kwari da baka zai iya ɗauka ba, balle bindiga.
"Za ki ce wani abu ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. Ta girgiza kai da sauri tana sake sunkuyar da kanta.
"Ya sunanki?"
"Rahma" Ta furta kamar mai raɗa cikin tsoro.
"Ramata" Ya furta yana guntun murmushi, ya miƙe tsaye ta kalle shi da mamakin jin yadda ya faɗi sunan da ake gaya mata a gida, Alhalin ita ba ta san shi ba, ba kuma ta taɓa ganinsa ba...
Ayshercool
08081012143
1k ne a telegram
0069685771
Aisha Adam stanbic
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g
More pages available at Arewapen.
SARA DA SASSAƘA...
AYSHERCOOL
YOTA/002
BRIGHT PENS
13
Murmushi ya yi ganin yadda alamun mamaki suka bayyana a fuskarta baki ɗaya, a lokaci ɗaya.
*****
Fuskar Ummi ɗauke da matsananciyar damuwa take kallon Ruƙayya, tana kwance a gadon Asibiti sai dai ba ta magana. Sai dai Likitoci sun tabattar wa su Ummi cewar, tsoro ne kawai da razani suke damunta. Haka suka karɓo ta suka tafi da ita, da niyyar su canza mata Asibiti, zuwa na kusa da su can cikin gari.
Babu yadda Ammar bai yi ba, ya samu release ya je gida, ya ji halin da ake ciki game da Ruƙayya amma aka hana shi, sai dai su yi waya ya ji ya jikinta, saboda su na daji ma a lokacin.
*****
Nadiya ta takura wa Alina a kan lallai sai ta koma makaranta, dan idan Yaya ya dawo, ya tarara ta jingine zuwa makaranta, sai ya yi mata faɗa.
Ko da ta shirya ta je makarantar ma, jikinta duk a sanyaye yake, malamai da ɗalibai su na ta yi mata jajen ɓatan yayanta.
Hafsa ta yi ta rarrashinta tana bata haƙuri, ji ta yi kamar ta gaya mata haƙiƙanin abin da ya faru, amma tamkar wadda aka asirce ta kasa furta mata komai.
Haka ta je Islamiyya ma, tana tafe tana jan ƙafarta jikinta a sanyaye. Ta jiyo muryarsa "'yan mata" Kamar ta yi banza ta tafi sai kuma ta tsaya cak. Ya ƙaraso yana faɗin "Alhamdillah, kin koma makaranta kenan? Ai hakan ne ya dace zama a gidan damuwa zai ci gaba da saka ki"
Ta ɗago idanunta ta zuba masa, tare da haɗiye wani abu mai ɗaci, idanunta ya cika da hawaye.
"Lafiya mene ne kuma?" Ta yi shiru tana bawa hawayen idanunta damar zubowa.
Jiki a sanyaye ya ce "Ki na ji 'yan mata, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri ki ci gaba da addu'a in sha Allah zai dawo cikin ƙoshin lafiya da aminci"
"Yaushe? Zuwa yaushe zaka dawo mini da shi?"
Ya yi saroro yana kallonta. "Ka gaya mini yaushe za ka dawo da shi? Na ganka fa, na ga komai, amma na kasa gayawa kowa, ina ta kallonka in ga ko za ka dawo da shi, amma ka ƙi. Na san kai da Yaya ba kwa jituwa amma abin da ka yi ya yi tsauri"
"Me ki ke nufi?"
"Na ganka, na gani, a kan idona ka ɗaure shi kai da wasu ku ka tafi da shi Da daddare ranar na dawo daga makarantar dare. Ta can baya na zagayo ina tsaye a bakin lungun can, na ganka. Dan Allah Mamman dan darajar iyayenka ka dawo mini da yayana dan Allah" Ya waiwaya layin ya ga babu kowa, ya sassauta murya ya ce "Ni fa ban gane me ki ke nufi ba"
"Ka sani wallahi ka sani, kai ka ɗaure Yaya da igiya ku ka tafi da shi" Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba ni ba ne ba, dan ranar da ki ke magana bana garin nan, na je gurin Inna"
"Kai fa ma'abocin karanta Alqur'ani ne, bai kamata ka yi ƙarya ba, dan Allah dan Annabi ka dawo mini da shi"
"Amm ina ga ki je gida kawai, wataƙila damuwa ce ta yi miki yawa ki kr irin wannan tunanin, amma gaskiya ba ni ki ka gani ba." Ya wuce ta ya bar ta a tsaye a gurin.
Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ƙarasa gida, ko da ta je gidan ta tarar Nadiya ta fita, dan haka ta samu cikakkiyar damar yin kuka.
*****
"Haƙiƙa mu na yabawa yadda mr. President yake ta ƙoƙarin ganin yaran nan sun kuɓuta, mun san ayyuka sun yi maka yawa, kuma duk wani abu da ka ke yi, domin al'immarka ka ke yin su. Amma Allah wadai da fadarka ta yi da sace ɗalibai, ta bakin mai magana da yawunka ta yi kaɗan. Ko ba ka je da kanka ba, ka rarrashi al'ummarka mussaman iyayen waɗanda aka sace ɗin nan, za su ji daɗi, komai ƙanƙantar abin da zaka gaya musu kuwa za su ji daɗi domin kai uba ne ga kowa. Please ka ce wani abu ko babu yawa, za mu ji daɗi"
A hankali ya ja ajiyar zuciya, bayan kammala kallon videon da ta wallafa, gaba ɗaya ƙasar ta ruɗe, ko ta ina bring back our girls ake posting.
Ji ya yi ya samu ƙwarin gwiwa da kalamanta, ko da maganarsa ba za ta yi tasiri ba, akwai buƙatar ya yi magana da bakinsa, ba a ji iya ta bakin mai magana da yawunsa ba.
Halilu ne ya shigo ofishin, hannunsa riƙe da takardu. Cikin matuƙar girmamawa, suka gaisa. Bayan an yi masa iznin zama, ya dubi Kankiya ya ce "Mr. President, tafiyarka taron kasashe masu arzikin man fetur fa jibi ne, ina yi maka tuni duk da na ga ka yi busy da yawa."
"Na soke tafiyar"
Da sauri Halilu ya dube shi ya ce "Mr. President ka soke kuma?"
"Eh, hankalina na kan batun yaran nan, ba zan iya komai ba"
"Haka ne, amma akwai buƙatar ko wakilci a naɗa ka tura"
"Babu buƙata, mutanen nan hawan ƙawara suke yi mana kawai, wannan shekarar ba zamu halarci taron ba, hanyoyi da yarjejeniyoyin da za su durƙusar da mu, su azurta kansu kawai suke yi"
"Amma Your excellency, ƙin halartar zaman, ya saɓa da yarjejeniyar da tsohuwar gwamnati ta saka hannu, kafin karɓar bashin biliyoyin da aka yi a shekarun baya, za su iya hukunta mu, ta hanyar janye mana wani tallafin, ko kuma sanya mana takunkumin da zai durƙusar da tattalin arzikinmu ma baki ɗaya"
Ya ɗan yi shiru yana matsa yatunsa, ya dubi Halilu ya ce "Ina buƙatar zama da shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa. Ina buƙatar bincikar yadda aka gudanar da wannan maƙudan kuɗaɗen, da ainihin kwafin yarjejeniyar basussukan da aka karɓa. Dan yanzu haka ma, ƙasar ba za ta tafi ba sai an ciyo wani bashin, kuɗaɗen da suke asusun ƙasar nan, ko jihohi goma ba zai riƙe ba"
Halilu ya risuna ya ce "In sha Allah, za a yi yadda ka ce, amma mr. President ka sake nazari a kan batun taron nan" Kai kawai ya jinjina. Bayan fitar Halilu ya sake ɗaukko wayarsa yana dubawa.
Comments ne na rashin kyautawa, da cin zarafi aka cika Laila da shi. Cin mutumci har da iyayenta, cin mutunci mai matuƙar muni ga ita da iyayenta, ban da ƙazafi da kushe mata halitta a ƙoƙarinta na bawa gwamnatinsa kariya.
A hankali ya dafe goshinsa yana ɗan murzawa a hankali. Yana tunanin meya kamata ya yi.
*****
YELWA
Duk da dakiya da juriya irin ta Baffan Rahama, sai da ya yi wata irin muguwar rama, dan ko lokacin da aka kashe masa ɗa, bai shiga mummunan tashin hankali kamar yanzu ba. Ko Abinci baya iya ci, baya iya bacci, 'yar kasuwar da yake ɗan zuwa ma ya daina saboda matsananciyar damuwa da kuma tashin hankali.
Tashin hankali da damuwa da yake ciki, bai hana jama'ar garin zunɗensa ba, har da masu yi masa dariya da Allah ya ƙara.
Hanne na zaune a ɗakinta, tana saƙar mafici, Bukar ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. Ta ɗaga kai ta bi shi da kallo tana mamakin me ya faru.
"Hanne, kin san me yake faruwa kuwa?"
Ta girgiza kai tana tsare shi da ido, tana jiran ƙarin bayani.
"Su Ramata aka sace s makarantar boko"
"Kamar ya ya aka sace su? Ta ya za a sace mutum? Ko dai ba ka ji dai-dai ba ne?"
Bukar ya tsuke fuska ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Da gaske nake an sace su Ramata a makaranta, ba a ma san inda suke ba"
Hanne ta dafe ƙirji tana nanata "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin abu ne? Allah sarki Baban Ramata, anya akwai wanda Allah ya taɓa jarabta a garin nan kamar sa? Amma ni ta yaya za a ce an sace mutum"
Cikin damuwa Bukar ya ce "To nima dai haka na ji"
"Gaskiya zan je gidan nasu, zan sake tambayar Baffan"
"A'a babu ruwana, kin san a ƙarƙashin takunkumi ki ke, kuma a gan ki a gidansu Ramata?"
Hanne da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Wallahi ko za su kashe ni sai na je, har Duniya ta naɗe Ramata da ahalinsu su na bin mu gagarumin bashi, ba zan iya jurewa ba sai na je"
*****
Sosai ɗaya daga cikin masu tsaron su Rahama, yake ƙoƙarin kai musu farmaki. Da ƙoƙarin fito da zalamarsa a fili a kansu.
Duk dare haka ake ɗaure musu ƙafafuwa, domin kar ma a samu mai yinƙurin guduwa.
Idanun Rahama biyu, tana rarraba su a cikin duhu, ta ji wani abu mai sanyi, yana bin ƙafarta. Ta ɗan motsa ƙafarta a hankali, ta ji abin ya daina bin ta. Wata irin ƙara ta saki, bayan jin wani irin raɗaɗi ya ratsa ƙwaurinta zuwa cikin ƙwaƙwalwarta ta gigice.
Cikin hanzari masu tsaronsu, suka yo kanta su na haskata da fitila, su na yi mata tsawa. Tuni gumi ya wanke ta, sai dai kafin su yi magana suka hangi wani irin ƙaton baƙin maciji ya bar gurin.
Su ka haska ƙafar Rahama, ga shaidar gurin da ya cije ta, jikinta sai wata irin tsuma yake yi.
Da yawa daga cikin ɗaliban, har da wanda suka fara bacci, duk su ka zubo mata ido, su na yi mata sannu. Ya yin da tsoro ya shige su, kar ya kuma cizon wani.
"Dare ne yanzu babu abin da za mu iya yi, zuwa da safe a sanar da sadauki" cewar ɗaya daga cikinsu.
Babu wanda ya damu ya ba ta wani taimakon gaggawa, kawai suka koma mazauninsu, suka bar ta. Rahama kuwa ji take yi tamkar ranta ne zai bar gangar jikinta, saboda azaba da raɗaɗin da yake ratsa ta.
Duk yadda ta so gwada jarumta sai ta kasa, ta fara kuka mai sauti, mai nuna tsantsar azaba da galabaita.
"Ke ki rufe mana baki, ko mu ƙarasa ki" Ya yi mata tsawa.
Sai dai ba ma ta fahimtar abin da yake faɗa, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, jikinta ya din ga karkarwa. Gaba ɗaya hankalin ɗaliban ya tashi wasu suka fara kuka.
Dukansu suka fara yi, da kan bindigogi su na taka su da ƙafa, tare da yi musu barazanar harbi, hakan ya tilasta musu jan bakinsu su yi shiru.
Jin Rahama ba ta da niyyar yin shiru, ya sanya ɗayan sanya bakin bindiga ya buga mata a kanta, hakan ya sanya ta sulalewa a gurin.
*****
Ta na daga kwance a kan gadon Asibiti, duk ta rame ta yi zuru-zuru, cikin damuwa Ummi ta riƙo hannunta ta numfasa ta ce "Ruƙayya, haryanzu jikin naki? Yakamata a sallame mu zuwa gida"
"Tsoro nake ji ne" Ta yi maganar cikin rauni, tana fashewa da kuka.
"You are safe dear, gida zamu koma babu wanda zai biyo ki gida ya cutar da ke, in sha Allah. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki yi ta addu'a.
"Ummi an tafi da Rahama fa. Kuma harbi suka harbe securitynmu" Ta yi maganar tsoro na bayyana a muryarta.
Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah za ta dawo cikin aminci." Ta yi maganar tana shafa kanta da sigar rarrashi.
*****
Safiyar Lahadi yana zaune a cikin ɗakinsa, yana daddana wayarsa, ya ji alamar motsi a bakin ƙofa, ya ɗan yi shiru yaga alamar motsi a gurin.
"Waye a nan?" Ya yi maganar yana kallon ƙofar, tare da zura hannunsa ƙarƙashin pillownsa.
Ɗaga labulen ta yi ta shiga, ya yi saroro yana kallonta.
"Lafiya kuwa? Me ki ka zo yi ɗakina da sassafiyar nan Alina, sai kin saka a zarge mu?" Ya yi maganar yana ƙarewa kumburarriyar fuskarta ido. Allah ya wadata Alina da manyan idanuwa, sai dai sun rine sun yi jawur kamar an zuba mata kala.
Gani ya yi ta durƙusa a kan ƙafafuwanta, ta haɗa hannayenta biyu, hawaye na rige-rigen zubowa daga idanunta ta ja numfashi da kyar ta ce "Dan girman Allah, dan son da ka ke yi wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ka taimaka ka gaya mini ina ka kai mini Yaya? Ka san ba mu da kowa sai Allah sai shi, ban san yadda zan rayu babu shi ba, shi ne komai nawa. Dan Allah ka gaya mini inda yake, na kasa gaya wa kowa abin da ya faru, dan Allah dan Annabi ka dawo mana da shi, ka yi haƙuri dan ma wani laifin ya yi maka ka yafe masa dan Allah"
"Alina" Ya kira sunanta yana tsare ta da ido. Ta ɗaga kanta tana kallonsa.
"Sau nawa zan gaya miki cewar ni ba ni bane ba ki yarda? In ɗauki yayanki na kai shi ina?"
"Wallahi kai ne, na ganka da idanuna, kai ne ba wani ba. Dan Allah Mamman ka taimake ni ka dawo da shi. Ba wanda zan gaya wa na ga abin da ya faru, dan Allah ka taimaka. A duniya bayan Allah da ma'aiki ba ni da kowa sai Yayana ka duba rayuwata da maraicina dan Allah"
Wani irin motsi ya din ga ji a ƙasan zuciyarsa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga kai komo, lissafi na neman ƙwace masa, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita ya ce "Zo ki tafi, zan fita"
Jiki a sanyaye ta taso, ta sake nufarsa, amma ya murtuke fuska ya ce "Ki fita ki bani guri" Ta girgiza masa kai tana haɗa hannayenta tana kuka, ya kawar da kansa daga kallonta yana nuna mata hanyar fita. Wani irin tsoro ya mamaye ta, ta fita tana jan ƙafarta a hankali tana kuka mai sauti.
*****
Yanayin fuskar Laila ne ɗauke da damuwa, da alama ta sha kuka ne sosai da sosai.
Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara da sallama, kamar yadda ta saba a dukkanin videos ɗin ta.
"Na ga alamar posting ɗina na ƙarshe a kan mr. President, bai yi wa da yawan mutane daɗi ba. Na ci zagi da ni da iyayena, da masu ce mini karuwa, da