Sara Da Sassaka Hausa Book Complele

Author :  AYSHERCOOL Category :  Arewa Story

Chapter   19 / 19

54K to 56.8K   out of 56.8K words

An yi wani abu mai kama da arrow a gefen kan. Babban abin da ya sake jan hankalinta bai wuce sarƙar da take wuyansa ba, da ya zura ta a cikin rigarsa, amma saman chain ɗin ba za ta manta da shi ba, lokacin da ya zo tana Asibiti amma ya musa mata, ya ce ba shi ba ne. Gefensa wani matashin ne da za su iya yin tsawo ɗaya da shi, hatta askin kansu iri ɗaya ne, sai dai kowanne kamarsa daban. Sai dai ta tuna ranar da ta je sayen leda shagon Mamman da yamma ta gansu tare.
Kenan duk tsawon wannan lokacin da take ganinsa, wani abin ne shi daban ba abin da take tunani ba? Ashe Yaya Ismail ya fita gaskiya.
Tana nan kwance suka ƙarasa har gaban gadon take, sai dai tana kwance kamar an dasa ta, ta kasa komai. Suka ƙarasa suka kewaye gaban gadon take. Gani ta yi tamkar an canza shi, gaba ɗaya ya juye daga Mamman ɗin da ta sani, suka shaƙu, da suffarsa da kamaninsa sun koma wani abu na daban. Fuskarsa a tsuke tamkar bai san hanyar inda ake bi a yi dariya ba, babu alamar annuri, sai ɗan rarraba manyan idanunsa yake yi da suka ɗan kaɗa suka yi jawur, duk da idanunsa sun saba ba ta tsoro, amma sai ta ga gara lokacin da ta san shi a Mamman, babu alamar afuwa ko sassauci a cikin waɗannan idanuwan.
Wannan gashin na fuskarsa ma babu shi, fuskarsa tas take sai ɗan yarfin gashin baki kaɗan. A hankali take buɗe idonta tana lumshewa.
Ya riƙe ƙugunsa yana kallon drip ɗin da yake shiga jikinta ɗis-ɗis. "Kai Mega kamar haryanzu she's unconscious"

"Yeah" Ya faɗa a taƙaice, ya janyo side drower, ya ɗaukko file ya buɗe ya yi dube-dube, ya duba ya ɗauki ya biro, ya yi rubuce-rubuce a cikin file ɗin, ya mayar ya ajiye. Ya duba cikin kayan maganin da ke gurin, ya ɗauki wata allura, ya zuƙe ya fara zubawa a cikin drip ɗin.
Miƙa ta yi tana yamutsa fuska, jin yadda shigar ruwan, tare da allurar ya burkita mata jiki gaba ɗaya, ta ji wani irin raɗaɗi, ƙoƙarin tashi ta yi saboda yadda allurar ta gigita ta. Ya saka hannayensa ya danne ta. A hankali jikinta ya saki, bacci ya ɗauke ta.
Alfa ya ce "Mega, me ka ke yi mata haka kuma? Kar fa ta ƙarasa"

Mega ya ce "Shut up" Ya yi maganar yana ɗan zaro masa ido.

"An ƙi ɗin, ka san zuwa gobe in Allah ya kaimu Oga Musa za su zo, su ganta"

Ya kalli sauran sojojin da suka zo tare, ya yi musu alama da su fita. Bayan sun fita ya dubi inda Alina ke bacci ya ce "Ta na da magrine headache, tana cikin damuwa da kuma tsoro. Akwai buƙatar ta huta sosai ƙwaƙwalwarta ta samu nutsuwa. Sai ta zama stable ne za a iya samun bayanan da ake buƙata daga gare ta"

Ammar ya jinjina kai cike da gamsuwa.

"To yanzu what next?"

"Eh, zamu je gurin matar nan, ina son grabbing wasu abubuwan daga gare ta, ina buƙatar tattaunawa da ita"

Ammar ya yi shiru yana kallon Alina, ya kalli Mega ya ce "Omega, ka san tsabar soyayya kun fara kama da yarinyar nan?"

Tsaki Mega ya ja, ya saka ƙafarsa ɗaya, ya daki ta Ammar da ƙarfi tare da furta "You are not serious" Ammar ya biyo shi yana murmushi ya ce "Wallahi sai na rama"

*****

Laila na zaune a cikin cell, wani ɗan sanda ya buɗe ta ya ce ta fito. Ta tashi jiki a sanyaye ta fito.
Ɗan sandan jiya ne ya saka aka kawo mata kayanta ya dube ta ya ce "Kin ci sa'a, an bayar da umarnin gaggawa a sake ki, idan kin ga dama ki je ki ci gaba da iskanci. Ku ba 'ya'yan kowa ba amma kun fi kowa rashin mutunci. Kuma a nan da awa arba'in da takwas, ki koma ki yi video ki ba wa Honourable da sauran mutanen da ki ka kama sunansu, haƙuri ko kuma abin da zai biyo baya ba zai yi miki daɗi ba" Ba ta ce komai ba, ta karɓi jakarta za wayoyinta, ta fito reception, ta waiwaya ta kalli ɗan sandan ta ce "Na gode sosai Sir, abin da ya faru da ni ya ƙara mini ƙwarin gwiwar gwagwarmaya, ka gaya wa Honourable zan yi video na ba shi haƙuri. Ba zan sake ba 'ya'yan talakawa mun bar wa masu duniya su ci gaba da cin jahannama a cikinsu"

"Laaa" Ɗan sandan ya faɗa bakinsa a sake.

"Sir yarinyar nan fa ba ta daku ba"

"A'a ki je ga ki ga su nan ai, a banza za su illata rayuwarki, babu abin da aka isa a yi kuma, sauka lafiya"

Ɗaya ɗan sandan ya ce "Ikon Allah, gaba ɗaya fuskarta ta salihai ce"

ISP Sagir ya ce "Ta munafukai dai, ni na yi mamaki, daga sama fa aka bayar da umarnin sakinta"

Suka ci gaba da tattaunawa, Laila kuma ta tsare abin hawa ta tafi gida.

*****

Ɓangaren su Rahama kuwa, dawowar Sadauki inda ake tsare da su, ya ɗan sama musu sassauci, ana ba su Abinci an daina dukansu.
Tun da macijin nan ya sari Rahama, ba ta sake taka ƙafarta ba. Sai dai yau da ya dawo daga yawonsa, daga nesa da su kaɗan ya tsaya a kan babur, ya yi mata nuni da ta zo. Ta kalle shi ta kalli ƙafarta, ya sake yi mata alamar ta zo. A hankali ta yinƙura ta daddafa bishiya, ta miƙe ta tsaya ta ji ƙafafunta tamkar an ɗaura mata duwatsu.
"Ta ko da Bismillah, da sunan Allah" Ya yi maganar yana zuba mata ido, ta fara takawa a hankali cikin tsoro, yana zaune a kan babur ɗin yana kallonta. Ji take yi tamkar ta faɗi, amma ta daure ta ci gaba da takawa har ta je inda yake ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta.
"Yayi kyau,koma ki je ki zauna" Ta sake juyawa ta koma, har za ta zauna cikin ɗaga murya ya kira sunanta "Rahama"

Ta waiwayo. "Waa ɗoo" (Zo nan)

Ta sake dawowa, sai cukuikuye jikinta take yi a cikin babbar rigarsa da ya bata.

"Ya jikin naki?"

"Da sauƙi"

"Alhamdillah, ba wata matsalar?" Ta jinjina kai.

Ya ce "Ba ki da baki ne?"

"Babu matsala" Ta yi maganar tana sunkuyar da kai.

"Allahumma yashfiki, je ki zauna Allah ya sauwaƙe. Je ki ki zauna"

Ta amsa da Amin, ta juya za ta tafi.

"Ke zo nan" Ta waiwaya ta sake tsayawa.

"Duk abubuwan alkhairin da na yi miki, babu ɗaya da za ki iya cewa kin gode?"

"Na gode"

"Wuce ba na so" Ya yi maganar yana kafe babur ɗin sa ya sauka daga kai. Ita dai ba ta sake cewa komai ba, ta koma gurin zamanta ta zauna.

*****

Arewapen

Zaune suke su biyar a cikin office ɗin, kowannensu sanye da kaakinsa na aiki. Sun baje wani map a kan table su na dubawa.

Ɗaya ya numfasa ya ce "Haryanzu mr. President, da al'ummar ƙasa, su na jiran ji daga gare mu, duk da pressure da aka saka mana, dole ne mu yi amfani da hikimomi da dabaru, dan kar rayuwar yaran ta salwanta"

Suka amsa da gaskiya ne.

"Commadore Edward, za mu jira, ku duba mana exact gurin da yaran suke, mu kuma za mu shirya duk abin da yakamata. Duk wani abu da zamu yi, za mu yi shi ne within 8days, mu fitar da kyakyawan result"

Commadore Edward ya ce "Babu case, komai zai tafi yadda aka tsara, akwai yiwuwar su canza guri, muddin suka farga mu na neman inda suke. Amma gano inda suke ɗin shi ne babban target, ba wani abu"

Suka kammala tattaunawa, suka yi musabaha da juna, sannan suka naɗe map ɗin suka bar office ɗin.

*****
Laila ce ta yi sallama a gidansu, Da sauri Mama ta fito daga kitchen, cike da son tabattar da Lailan ce. Tana tozali da Laila kuma sai ta tsuke fuska. "Sun ga dama sun sako kin kenan?" Laila ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba.

"Yanzu kin ga sakamakon mai bijire wa maganar iyaye ko? Babu yadda ban yi da ke ki bar maganar nan ba, amma ki ka ƙi. Ke ba kowan kowa ba, ba ki da wani gata sai na Ubangiji, amma fitina ta yi miki yawa Laila. Ni dai lafiya na rabu da iyayena da mijina, balle na ce ko hakkinsu ne yake bibiyata ya sanya ba kya jin magana ko kaɗan.

Saddam da shigowarsa kenan, ya ce "Haba Mama dan Allah, daga dawowarta ki yi haƙuri ta huta ta ci abinci mana"

Mama ta juya kansa da faɗan "Ba zan bari ta huta ɗin ba, ni kwana biyu a jere hutawar na yi? Yanzu abin arziki ne a ce mace ta kwana a hannun 'yan sanda har kwana biyu, gurin 'yan sandan ma, sashen kula da manyan laifuk, ita ba kisan kai ba, ba fashi ba?"

Saddam ya yi wa Mama shiru, ya dubi Laila da take kuka, ya ce "Shigo ki zauna rabu da ita"

"Eh a rabu da ni mana, tun da ga mahaukaciya tana faɗa ko? Ku je ku yi abun da ku ka ga dama, babu mai kashe ni lokacina bai yi ba"

Saddam kuwa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ki yi haƙuri, ɓacin ran kin kwana biyu a gurin 'yan sanda ne ya sanya take yi miki faɗa, amma ki yi haƙuri. Ina fatan ba su yi miki komai ba dai ko?"

"Sun mare ni" Ta furta tana sake fashewa da kuka. Saddam ya yi shiru yana kallonta, wani abu ya tokare masa a ƙirji, idanunsa suka yi ja. Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Kar ki gaya mata an dake ki, ki yi haƙuri ni na fahimce ki, hakkinmu ne aka danne, shi ki ke fafutuka a kai, zan taya ki da yardar Allah ko ba za mu yi nasara ba, duk abin da ki ke nema, ki yi mini magana zan taimaka miki, amma ki daina kuka ki yi haƙuri" Ta jinjina kai tana share hawayen da yake gangarowa a kan fuskarta.

Ya miƙe tsaye ya ce "Bari na je gurin Umman su Bala, na karɓo miki ruwan zafi ki yi wanka, ki ƙyale Mama ta gama faɗanta ta huce" Jinjina masa kai kawai ta yi ya fice.
*****

Sannu a hankali suke ratsa tsakanin ofisoshin, har suka ɓulla can wani ɓangare da babu wadatattun ma'aikata a gurin.
"Alfa, tun da muka kawo mutumin nan fa, ba a sake bari mun gan shi ba"

Alfa ya ɗan sosa girarsa ya ce "I wonder, ina ta so na yi maganar amma dai na yi shiru, amma kamar na ji Oga Musa kan ya tafi yana cewa, za a canza masa guri, maybe ma a bar garin nan da shi gaba ɗaya"

Mega ya ja ya tsaya, ya ce "A bar nan garin da shu a kai shi ina?"

Alfa ya ɗage kafaɗa tare da faɗin"I don't know"

"Amma kana ganin ya dace a yi hakan, ba tare da mun ji komai ba, mussaman ni da na yi duk ƙoƙarin?"

"And someone is taking the credit of your work ba, so sad. Na tausaya maka Mega"

Abdallah ya ɗan yi shiru sannan ya numfasa ya ce "We shall see" Ya ƙarasa maganar ana buɗe musu wata ƙofa, da gurin yake ɗauke da duhu.

Mai tsaron gurin ya sara musu, sannan ya sake buɗe musu wata ƙofa, mai kama da ta fursinoni. Suka ajiye wayoyinsu a waje, da bindigoginsu, aka caje su. Mai cajesun ya damƙo wani abu a aljihun Alfa. Alfa ya zura hannu ya ɗaukko ƙaramin biro a jikinsa, aka karɓi biron aka ajiye, sannan suka shiga.

Tana zaune ta takure guri ɗaya, tamkar mai taɓin ƙwaƙwalwa, ta ɗago ta yi musu kallo ɗaya, ta mayar da kanta ƙasa ta sunkuyar.

Abdallah ya gyara zaman hular sojojin da ke kansa, ya ƙarasa gabanta ya durƙusa yana kallonta.
Sai dai ta sunkuyar da kanta, ta ƙi ɗagowa su haɗa ido.

"Nadiya ko?" Ya furta yana tsare ta da idanunsa.

Ta ɗago a hankali ta dube shi ta ce "Au ba ka ma tabattar da sunan nawa ba?"

Mega ya girgiza kaiya ce "A'a, ina son sake samun tabbaci daga bakinki ne. Ina son zan yi miki wasu tambayoyi ne, da nake buƙatar ki bani haɗin kai, ki yi mini cikakken bayani"

Ta yi murmushi tare da maimaita faɗin "Tambayoyi? Ni za ka yi wa tambayoyi na baka amsa? Shikenan ina jinka faɗi"

"Suwaye iyayen Alina na haƙiƙa?"

Ta yi shiru tana ɗan kaɗa kanta, sannan ta ɗago fuskarta ɗauke da murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarsa ta ce "Kai da uban gayyar yake hannunku, yaya za ku zo ku na tambayata?, ai shi ya fi kyautuwa ku je tambaya? Shi ne yake da amsar tambayar ba ni ba"

Mega ya tsuke fuska, saboda yadda ya fara ƙuluwa da murmushin da take yi, ya ce "Ke nake tambaya yanzu"

"Ba ka da ikon tambayarsa, saboda an killace shi an hana ka ganinsa ko? Haryanzu fa ba ma a yarda da kai ba, na cewar ka kama Kacalla Sumale ba. Sannan ba ka da tabbacin yana ina a halin yanzu. Na san ka fara jin kanka kai wani jarumi ne, saboda ka kama shi, tabbas ka cancanci jinjina na ɗan lokaci, dan babu wanda ya taɓa gano gaskiya da ka gano a cikin duhu, sai dai gaskiyar ta suɓuce a hannunka, kuma ita ma ta yi duhu ta sake ɓacewa ganinka a cikin duhun.
Wannan kuskuren da ka yi zai iya zama ajalinka, dan duk wanda ya gano shi, sai ya kawar da shi daga doron duniya, idan ba wanda ya yarjewa ya gano shi ba. Abu na gaba kuma muddin Kacalla na rayuwa a doron duniya, zai iya zubar da kowane irin jini, zai kashe kowane ne, domin Alina! Ka tafka babban kuskure mai muni da hatsari gare ka da rayuwarka" Gaba ɗaya suka yi shiru su na kallonta.

Ta jinjina kai ta ce "Ƙwarai, zai ci gaba da bibiyarka, zai yi farautarka babu dare babu rana, saboda ita. Kacalla Sumale ya shallake duk yadda ka ke tunani, yana da abin da baka tunani. Ni kaina a tsawon lokacin da na riƙe Alina da ina da hali, sai na ba ta guba na kashe ta, saboda tsananin kishin yadda yake ƙaunarta fiye da ransa. Sai dai ina kyautata zaton baƙin alhaki ne yake bibiyarsa, saboda iyayen Alina ne jini na farko da Isma'il ya fara zubarwa a Duniya da hannayensa!"

Tsit suka yi gaba ɗaya su na jin ta, tare da yin jarumtar ɓoye mamakinsu, mussaman ma Mega.

Alfa ya ce "Ke ban gane ba, iyayenta ne mutane na farko da ya fara kashewa, to ta yaya aka yi ya ɗauke ta ya riƙe ta? Suwaye iyayen nata? Sannan kema kuma wace ce? A ina sauran ahalinta suke?"

"Wannan tambayoyin duk shi ne zai ba ku amsar su. Abin da ba ka sani ba shi ne, Ismail ya san waye kai. Shi ne ya kashe Malam Ɗayyabu bayan da ya yi masa ƙarya. Bai yi maka komai bane ba, saboda gudun halin da Alina za ta iya shiga. Sannan ai ina aikinka a kansa ne kawai, tun da ka gama aiki a kansa babu buƙatar ka zurfafa a kan Alina babu ruwanka da ita.
Ka sani ya gama tsara komai, a kan matakin da zai iya ɗauka a kanka, bai kai ga aiwatarwa ba, ka riga shi motsawa. Ina mai baka tabbacin zai fita, dan Kacalla Sumale ba mutum ɗaya ba ne ba, mutane da dama masu burin cimma muradai daban-daban a cikin mutum guda, kuma muddin ka na yawo a doron ƙasa ko shi ko na cikinsa za su hallaka ka, saboda ka gano abin da duk wanda ya gano mutuwa yake yi.

Har ya buɗe baki zai yi magana, ya jiyo muryar mai tsaron Nadiya ya ce "Oga Mega time fa ya yi, kar a zo a kama mu, daga ni har ku mu shiga matsala"

Mega bai iya cewa uffan ba, ya miƙe tsaye,, Alfa kansa bakinsa tambayoyi ne a ciki, gaba ɗaya maganganun Nadiya sun ɗaure musu kai, amma haka suka yi waje suka bar gurin.

Mega ya dafa kafaɗar Mai tsaron ya ce "Thank you Nelson"

"Welcome sir" Ya yi maganar cikin girmamawa yana yi wa Mega murmushi.

Yadda yake tafiya yana dukan ƙasa da ƙafafuwansa, tamkar ƙasar ce ta yi masa laifi. Ba tare da ya sani ba, haka yake ta wani irin huci, tamkar zai shiɗe saboda tashin hankali.

Sai da suka ƙarasa office ɗin su Mega, Ammar ya rufe ƙofa ya dubi Abdallah ya ce "Mega wata sabuwa in ji 'yan caca, ka yarda da maganganun matar nan kuwa?"

Ya jinjina kai ya ce "Biri ya yi kama da mutum, but was fooled Alfa, meyasa tun da muka kawo shi, bamu sake ganinsa ba ko jin inda yake ba, aka hana mu ganinsa mussaman ma ni da muka yi aikin tare da sauran jami'an?"

Alfa ya ce "Yes tambaya ce mai ma'ana, amma ni ban ji na yarda da ita ba, amma ni abin da ya bani mamaki, meyasa ya kashe iyayen yarinyar? Me kuma ya sanya ya ɗauke ta ya riƙe, yake yi mata irin wannan mugun so? Kai Mega akwai maganganu da dama a bakin matar nan da suke buƙatar fashin baƙi. Suwaye mutanen da suke cikin Kacalla Sumalen, suwa yake yi wa aiki?...

Ayshercool
08081012143

19 / 19