Rayuwar Aneesa complete Hausa Novels pdf Reemah.txt

Author :  Reemah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 24

1 to 3K   out of 70.4K words

🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷


Reemah ✍️


Godiya🙏
Bismillahir Rahmanir Raheem
Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillahi Rabbil Alamin. Godiya ta tabbata ga Ubangiji Mai Rahma mai jinƙai. Rabbish rahlee sodree wayassir lee Ameer, wahlul uqdatan min lisanee yafqahu qaulee.


Masoyana mutanin aljanna, Allah dai ya bar mu tare. Banida abun faɗa sai dai nace Allah yabar min ku. Ina alfahari da ku sosai sosai🫰.

Gargadi🧏
Wannan littafin nawane, Ni na zauna na tsara labarin a yadda raina yaga dama. Banga amfanin wata ko wani ya kasa zama shima yayi amfani da basirar da Allah yayi masa ba, saidai ya zabi ya zauna ya bata lokaci wurin editing littafin wani ya juyashi zuwa nashi. Duk wani ko wata wadda yayi ko tayi mun haka, sakamakonsa yana wurin Allah. Akiyaye Please.

Tsarin labari✍️

Wannan littafin banyishi don cin zarafin kowa ba, kwata kwata ma ƙagaggen labari ne ba real life story bane. Don Allah duk wacce taga yayi kamada labarin da toh wannan kuma total coincidence ne, ina mai bada haquri.

Labarine wadda ya ƙunshi tsananin jaddada, cin amana, mugunta,dogon buri, abubuwan ban mamaki da nishadi,zazzafan kauna da soyayya😌😌.


Nice taku kullum Reemah, marubuciyar

MIJIN TACE
FARHAAN
yanzu kuma

RAYUWAR ANEESA....

# BETRAYAL
# COMEDY
# HOT LOVE
# ROMANCE

Happy Eid my loves❤️

PG 1_5

"Kan ubancan, ni yarinyar nan zata watsawa ruwan wanke wanke ajiki" Ni dai ina tsaye ko ƙala bance ba, nasan halin Abba sarai, karamin aikinsa ne ya rufeni da dukan tsiya. Cikin rawan murya nace "Abba kayi haquri, wlh bansan kana shigowa bane na watsa ruwa.." maganan danakeyi ne ya maƙale sakamakon wani irin gigitacciyar marin da Abbana ya sakar mun afuska har hakan yasa na zube akasa na kwala kaina da tukunyan tuwon Innati😂. Ko kallona Abba baiyi ba ya wuce cikin gidan abunsa yana zage zage. Da ƙyar na mike na zauna ina mulmula inda kaina ya bugu, abunka da mai arahan hawaye, take suka fara zubowa shaaa. Nidai na shiga uku, inda wani yau zai zo ya faɗamin cewa ba Abbana bane ya haifeni da wlh babu tantama zan yarda, jin kukana yasa Innati fitowa daga ɗan bayinmu dake tsakar gida wadda buhu kawai akasa aka ɗan rufe Kofar shiga, ganina datayi aƙasa caba caba cikin ruwan datti yasata isowa wurina da sauri tana kamani har na tashi akan kafata. Kamo hannuna tayi zuwa kan taburman dake malale a tsakar gida gaba daya ya fice hayyacinsa tsabar tsufa, zan iya cewa tunda aka haifeni har na taso naga wannan taburman da tsufanta, hala yana cikin kayan ɗakin Goggo (mahaifiyar Abba)😂.

Cikin sheshsheka nace "Innati nidai Allah na gaji da abinda Abba yake yi mun, saikace ƴar bare bana cikinsa ba, abu kaɗan duka duk jikina babu inda bai bar tabo ba, kalli kigani fa"nafaɗa ina nuna mata duk inda nasan akwai wata alama ta duka da Abba ya bari ajikina. Tsabar tsoron da Abba ya dasawa Innati akansa ya hanata cewa uffam, tasan sarai yana jinta shi yasa bata iya cemun komai ba sai haquri datake bani, ni kuma harga Allah nagaji da wannan haƙurin, aiko sarauniyar haƙuri itama tanada maƙura. Fitowa Abba yayi daga ɗaki dukkanmu dagani har Innati mukaja bakinmu mukayi shiru bamu ce komai ba, watso min kayansa dana ɓata da ruwan datti yayi yayi wucewarsa, ko ba'a faɗa mun ba nasan meyake nufi, to da me zan wanke kayan na shiga uku Ni JAMMA, Ni kaina na mance yaushe nayi wanka da sabulu balle nasan ina zanyi kashinta na wanke wa Abba kaya dashi.

Hawayen danake dannewa ne sukayi nasarar gangarowa, Innati babu abinda ke ƙaryata irin taga hawaye a idanuna,nice kawai mai bata ƙarfin guiwa, aduk lokacin da Abba yayiwa Innati duka, ni kaɗai takeda wadda ke iya rarrashinta. Dake saurin kuka nayi gadonsa ne daga wurin Innati, kasa bani haquri tayi itama kawai ta fashe da nata kukan tana rungume dani saman kirjinta. Sheshshekan kukanmu ne ya tasar da Goggo abaccinta. Fitinanniyar tsohuwa kenan, ko Abba albarka. Tun daga daƙi tafara sakin ashar tana zaginmu dagani har Innati. Jin haka yasa muka rarrashi kanmu mukayi shiru amma haka muka yini cikin ƙunan rai da rashin walwala kamar kullum.


Washe gari da sassafe na farka nagama duk wata aiki dazanyi danna samu naje islamiyya, shima rashin zuwa alokaci ba ƙaramin hukunci ne atattare dashi ba. Dake nasan babu batun karin kumallo yasa kawai na shirya cikin koɗaddun kayan makaranta na na ɗau jakata wadda akayishi da buhu na zuba littatafai na na fito daga ɗan kwangon ɗakina. Innati kawai na samu a tsakar gida tana wanke kayan Goggo. Sallama nayi mata nasa kai zan fita naji Goggo tayi ihun sunana wadda babu mai kirana da shi sai ita wato "Bahaguwa" bafa wai donni din Bahaguwa bace, ita kaɗai tasan ma'anar wannan sunan. Cikin ɗaure fuska na juya ina addu'a azuciyata Allah yasa ba aiki tsohuwar nan zata sani ba. Aikuwa kamar ta karanta abinda ke raina naga ta dunƙulo mun wata uwar ashar harda daƙuwa. Allah ya sani, badon komai na dage da zuwa islamiyya ba sai don yaƙi da jahilci amma wannan tsohuwar da ɗanta wato Abba makiyana ne akan haka, saidai idan zan saci idonsu na fice a gida zuwa makaranta, Amma muddin suka ganni tofa saidai na fasa zuwa.

Kallona Goggo tayi cikin halin ko in kula tace"dama dai kin huta da zuwa wannan makarantar amma nikam tausa zakiyi mun, na kwana da ciwon ƙafa" Allah ya kawo mun ƙarshen wannan tsohuwar, kamar na ƙwala ihu amma babu yadda na iya. Haka na zauna a ƙasa ta ɗora mun kafafunta wadda duk faso yagama cinye shi akan cinyata, inama ƙafan nada laushi dana ji dadin yin tausan amma gaba daya sai keta mun hannu yake. Wlh duk zanuwan gadon Goggo sun ɓaɓɓarke tsabar ƙaushin kafanta, Allah sarki ƙanwata Ameera, da tana nan kenan da itace zata yi daidai da Goggo, ba ƙaramin kwasa sukeyi da ita ba, har shakkar ta tsohuwar take idan tanaso tayi mata wani kulli kuma babu Abba a gida, amma muddin yana nan to sai inda ƙarfinta yaƙare. Wannan dalilin yasa Abba baiwa ƙaninsa Ameera amatsayin yar riko, saboda acewarsa tasa uwarsa agaba( to ya za'ayi bazata sa ta agaba ba, kaima ka takura wa uwarta🙄).

Ina nan zaune ina abu ɗaya har kusan awa ɗaya sannan Goggo ta ciro nera dari biyu a gefen zaninta ta jefa min tace " Ke Bahaguwa, maza miƙe kije ki sayo mun ƙosai na koko awurin innan Ladi kafin ɗana yadawo, nasan ya fice da yunwa tunda ba wani abinci uwartaki ta dafa masa ba" Goggo taƙarashe magana tana zabgawa Innati uban harara, ganin idonta baya kaina yasa nima hararanta ƙasa ƙasa ina murguɗa mata baki, kai kaman karas, wai Innati ce bata dafawa ɗanta abinci ba saikace shi ɗannata ya kawo ne aka ƙi dafawa. Ƙwafa nayi ƙasa ƙasa na mike ina cunno karamin bakina gaba, sai wani disco cikina yake kamar anbude gidan kiɗa a cikinta tsabar yunwa. Inama inna kawo kosannan Goggo ta ɗeba mana kaɗan nida Innati na.


Saida na shiga na canza kayan jikina zuwana aiki sannan na fito ina ƴar nasheed dina wadda malaminmu malam sabo yake yawan yi mana a islamiyya. Ina isowa na samu ana dambe, ankifarwa Innan Ladi kullun ƙosai gaba ɗaya aƙasa, saiga tsohuwa tasha ɗammara a tsukakken ƙugunta tana cewa lallai sai an biyata kuɗin kosanta😂😂, kasa riƙe dariya na nayi, aikuwa saida na dara. Kallon ikon Allah nake, wannan tsohuwa akwai ƙarfin hali, wadda fa ya kifar mata da kullunnan, naushi ɗaya idan yabata wlh saidai akaita gidanta na gaskiya tuyan ƙosai ya ƙare kenan😂. Nikam wannan batu ba ƙaramin daɗi yayi mun ba, wannan shine kamuwar Allah, nadai san babu wata mai tuyan ƙosai a wannan unguwar sai Innan Ladi, to kuma an kifar mata da kullu kenan yana nufin dagamu harsu Goggo da Abba zamu wuni cikin yunwa💃😂, dama nasan idan nakawo saidai su cinye su barmu da wanke musu kwanuka.

Harda ƴar rawata na juya nayi hanyar gida ina waƙa, sai da nazo dab da gida na canza fuskata alamar damuwa, ina shiga na tadda Abba yana zaune shida Goggonsa suna hira, ko da nayi sallama Innati ce kawai ta amsa amma su Goggo sai kallon hannuna sukeyi suna jiran suga ledan ƙosansu. Ganin haka yasa naɗan kara ɓata fuskata na iso gabansu, cikin ladabi na tsuguna na gaida Abba, "ke Ni dallah bani abinda aka aikeki banason munafirci, gaisuwanki zanci dan ubanki"? Fadin Goggo, murmushi nayi araina na miƙa mata dunkulallen ɗari biyunta nace "Goggo babu ƙosai" Abba bai bari na gama explanation ba kawai ya kwaɗa mun Mari, cikin fushi Goggo ta ingiza shi ya ƙara mun, acewarta hala ma ban tafi wurin ƙosan ba tunda taga ban daɗe ba nadawo.


Har rana dagamu harsu babu wadda yasa komai abakinsa, nida Innati sai ɗurawa cikinmu ruwa muke wai ko dan ya riƙe mana ciki, daga ƙarshe ma ƙulle mana ciki ruwan yayi. Goggo ta zauna tayita sakin tsaki ita kaɗai, shiko Abba ficewarsa yayi, yasan yadda zai yi dakansa. Yar karamar wayar ta ƙirar Nokia irin mai Black and white dinnan ta fidda tasani na kira mata layin Baba Auwalu ƙanin Abba wadda ƙanwata Ameera ke wurinsa. Cikin zumudi kuwa nayi dialling number din nasa kodan zan samu naji Muryar ƴar ƙanwata. Bugu biyu ya dauka na mikawa Goggo, ko sallama babu tace "Auwalu shikenan kai kuma babu waiwayon uwarka dan kana wani gari, tun jiya rabona da abinci amma kai na tabbata yanzu haka cikinka acike yake dam, kai ko kanason albarka kuwa" cikin tsananin damuwa wadda muryarsa ne ya nuna hakan Baba Auwalu yace "Goggo ki gafarceni, wlh muma ko karin kumallo bamuyi ba, dama Hansatu ta sawa ƴar wurin Husseina tallan piya wata ne gashi kuma tun safe ja'irar yarinyar bata dawo ba balle ayi amfani da cinikin datayi ayi cefane dashi" jin haka yasa ƙirjina dana Innati bugawa muka juya muka kalli juna, tun safe fa, yanzu kusan ƙarfe ukun rana kenan. Allah dai yasa lafiya. Tsaki Goggo taja tace "wannan yaran nikam na rasa wani irin rashin Sa'a suka shigo mana ahali dashi, yanzu haka shegiyar ƙila tana can wurin yan wiwi suna aikata iskanci dasuka saba, dake iskancin ajinin dangin uwarsu take" tafada tana hararan Innati, duƙa kai Innati tayi hawaye na gangarowa daga idanunta, itadai duk ba wannan ba, Allah yasa ƴarta tana cikin koshin lafiya.


🌷🌷🌷🌷🌷

Abu kamar wasa har ƙarfe bakwai na yamma babu Ameera ba labarinta. Tun hankalin Baba Auwalu da matarsa Hansatu bai tashi ba, ganin almuru yayi kowani ɗan talla da ƴar talla sun jima da dawowa gida, basai hankalinsu yatashi ba, to ina yarinyar ta tafi. Bata taɓa kaiwa irin wannan lokacin ba. Bayan sallan isha'i, Baba Auwalu baiga tazama ba, tunda yaji har yanzu yar ɗan uwannasa bata dawo ba. Babban ɗansa isyaku da mabiyinsa Ibrahim ya kira suka bazama neman ta. Ga uban hadari daya haɗu, iska mai ƙarfi yanata kaɗawa. Babu inda basu duba cikin unguwar nan ba, harma da unguwar dake kusa dasu kuma sunyi tambaya babu wadda yagane yarinyar da suke magana akai. Har ƙarfe sha daƴan dare babu labarin Ameera, to mezaicewa ɗan uwansa. Alokacin ne iska yaƙara yin karfi, nan da nan kuwa aka kece da ruwan sama mai bala'in karfi kamar da bakin ƙwarya , fakewa Baba Auwalu yayi shida ƴaƴansa har ruwan yayi sauƙi, wuraren ƙarfe sha biyu da rabi suka dawo gida. Lokacin Hansatu har tayi bacci itada ƴar ta Halima kamar babu wani abinda ya faru. Awannan daren kasa bacci Baba Auwalu yayi, to ina wannan yarinyar tashiga ne. Allah kawai ya kawo mafita.

🌷🌷🌷🌷🌷

Yadda Innati taga rana haka taga dare, haka kawai taji zuciyarta nata bugun uku uku, wuraren ƙarfe ɗayan dare Abba yayi wani irin miƙa jin iska mai daɗi na shigarsa, ahankali ya lalube saman gadonsa ya taɓo Innati wadda ke hawayen zuci tana addu'a Allah yasa komai lafiya wannan irin bugu da zuciyarta keyi. Shikam ko ajikinsa, hannunsa yakai yafara shafa Innati ahankali yana ɗan numfarfashi, anzo wurin. Inhar Abba ya fara laluɓan Innati ahankali to yana cikin halin buqata ne, amma komai nasa zafi yake yi mata. Jin haka yasa Innati fashewa da kukan datake ta kokarin rikewa, kamar Abba ya kwaɗa mata Mari, shi duk atunaninsa Innati na kukan taɓata dayakeyi ne,amma bai san cewa damuwarta daban bane. Cikin kuka Innati tace "Abbansu dan Allah ka taimaka ka kira yaya Auwalu ko anga Ameera, wlh hankalina gaba ɗaya ya karkata wurinta, ji nake zuciyata tana ta bugun uku uku" doguwar tsaki Abba yaja yace "yanzu ke Hussaina tsabar rashin sanin kiman miji, ina nemanki ashimfiɗa na kikeyi mun maganar wata shegiyar yarinya, ke angaya maki shi Auwalun baida matane, kawai sai in fara kiranshi da tsakar darennan dake nima na zama mahaukaci irinki. Dallah ni idan zaki bani haqqina kawai kibani banason doguwar zance" yana gama fadin haka kawai yajawota da karfi yafara yi mata abubuwa wadda ko motsa ta bayayi,toh baiwar Allah hankalinta ba'a jikinta yake ba balle taji daɗin abinda yake yi, dake kuma dama tunda tayi aure da Abba batasan wani daɗin s*x ba saboda shi kansa kawai yasani, idan kuma ya biya nashi to nata kuma ko oho ne. Jin abinda yake mata kawai ta kwanta tabar masa jikinnata amma kwata kwata bata wani tanashi.


Ina kwance saman yar katifata wadda yagama jin wahala, ga cizon sauro duk ya addabe ni. Sai tunanin rayuwa nake, inama ace mu masu kuɗi ne kuma Abbanmu da kakanmu suna sonmu da babu abinda zai kai haka daɗi. Nifa a kullum tunanina bai wuce nayi kuɗi ba don gani nake kuɗi shine tushen komai, zai samar maka farin ciki aduk inda yake. Na riga na ayyanawa raina idan nayi kuɗi saina sayowa Innatina wannan haɗaɗɗiyar leshin damuka gani a kasuwa wani rana, sannan zan ƙarasa karatuna na sakandare tunda ayanzu dai na tsaya a haji na biyune aɓangaren sss, zanyi karatu nima inzama wata babba mai faɗa aji a wannan ƙasar tamu. Saina inganta rayuwar ƴan mata da zaurawa wadda ke fama da ƙuncin rayuwa. Ina so idan nayi karatu nazama lauya saboda na ƙwatowa Innatina ƴancinta ahannun Abba, ita kuma Goggo imma Allah yasa zansata agidan dazan gina, to daƙinta zai zamo ƙarami sosai wadda zata takure sosai acikinta kamar ƴar yari😂 Ni kaina danayi tunanin saida nayi dariya. Kullum kafin nayi bacci sainayi irin tunanukannan,shike ɗebe mun kewar ƴar uwarta Ameera, itace muke zama muyi wannan hiran da ita har tsakiyar dare kafin muyi bacci. ALLAH sarki koya take yanzu agidan Baba Auwalu, ko itama tana shan wahala ahannun matarsa Hansatu, dama nasan can ba sonmu take da Innatinmu ba. Ahaka naita tunanin rayuwa har bacci ɓarawo yayi nasaran saceni.


Wuraren ƙarfe huɗu na asuba akayi wani irin gigitacciyar tsawa, wadda yasani farkawa kamar acikin kunnena wannan tsawa ta sauka. Take naji wani irin tsoro ya kamani, ance ba'a alaƙanta mafarki da wani ma'ana, to amma yanzu mafarkin ƴar uwarta Ameera nayi, kuma mummunan mafarki ne,inaji tana ihun sunana dana innati tana cewa ataimaka mata zasu kasheta, daidai ina ƙoƙarin kama hannunta akayi wannan tsawar. To me hakan ke nufi, anya Ameera tana lafiya kuwa. Gashi banida waya balle na kira naji. Kasa samun natsuwa nayi, ƙirjina sai dukan tara tara yake yi, ganin zama dai bazai yi mun amfani ba tunda bacci ya washe kawai na mike na fito waje cikin ruwan saman, abakin ɗakina na tsaya ina tarar ruwa nayi alwala, tsorone dani kamar farar kura dan haka sharp sharp nayi alwala na shigo ɗakina. Duk na jiƙe sharƙaf dan haka na tuɓe kayana na ɗaura tsumman zanina na sanya hijabi na tada Sallah. Nafilfili na dinga jerowa, bayan na idar na fidda Qur'an dina nafara karatu cikin zazzaƙar muryata. Nikaina nasan inada zaƙin murya😌, mafi yawancin lokuta Ni akafi sawa a musabaƙah dan nice ɗalibar data fi kowacce ƙoƙari kuma ga daɗin murya. Ban koma bacci ba har saida nayi sallan asuba, dake har yanzu ana ɗan yayyafi yasa banyi tunanin fitowa waje ba.


🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Karfe takwas na safe yayiwa Baba Auwalu a gidan Radio dan sanarwa akan ɓatar yarinyar wurinsa koda wadda yaganta, yabada lambar wayarsa dana Abba. Koda ya fito bai koma gida ba, kwata kwata hankalinsa yaƙi kwanciya,lallai duk inda Ameera take to bata cikin ƙoshin lafiya. Wani zuciyar yace to ko dai yaje wurin polisawa yasasu a lamarin, wani zuciyan kuma yace masa yaje gida ya sanarwa matarsa tukunna. Haka kuwa yayi, yana sanar wa Hansatu tayi alambaran babu wani polisawan da za'a kira, barin kawai suci musu kuɗi azo kuma ba'a ga yarinyar ba. Gara kawai in akayi sanarwa akayi sanarwa kuma babu wadda yaganta toh hala kwananta ne ya ƙare dan haka sai kowa ya ɗau abinda Annabi ya dauka. Sosai furucinta yabashi mamaki, wannan inda ƴarsa Halima ce abunnan yasameta daya zai yi?

Wuraren ƙarfe ɗayan rana wasu yara suka shigo gidan Baba Auwalu suna ƙwala masa kira. Da da farko bai ɗauka kirannasu da gaske ba,dan sun saba kawai suyita ƙwalawa babba kira kamar sa'ansu. Can yaji mutanin angwa suna ihu. Da sauri yaɗora jallabiyarsa saman ɗan guntun wandonsa yafi to harabar gidannasa. Turus ya tsaya ganin jama'a maƙil agidansa kowa shi yake kallo, Hansatu da Halima duk suma sun fito, to meya kawo wannan mutanin kuma. Ɗaya daga cikin matasan dasuka shigo gidan yace "amma Allah saiya tambayeka Auwal,bazai barka haka ba. Wlh kun cutar da ƴar mutane, kun kasa riƙon amana. Yanzu inda ƴarku Halima ce ta shiga wannan halin a hannun wasu yazakuji. Kun muzgunawa rayuwar yarinya, kun sata zuwa talla gashi asanadinku yarinyar tayi rashin abu mafi muhimmanci a matsayinta na ƴa mace, turrrr daku wlh" duk Baba Auwalu bai gane me

1 / 24