Author : Reemah Category : Romantic Hausa Novels
ta shiga kitchen ɗin, sharp sharp ta dafa ruwan shayi ta zuba a flask sannan ta yi mayo egg sandwich ta ɗora saman tray ta fito. Har ta haura bata hadu da kowa ba. Da sallama abakinta ta shiga, zaune tasameshi yana aiki a system ɗinsa, aje trayn tayi saman center table. Aje system ɗinsa yayi ya sauko ƙasa ya tanƙwashe kafafu yasa itama ta zauna kamar jiya suna facing junansu. Sandwich ɗin ya serving a plate, ya haɗa tea a glass cup ɗaya. Shida kansa yake bata, intaci shima saiya ci gwanin sha'awa. Yau kam ta cire kunya ta narki sandwich ɗin da kyau. Bayan sun gama ci kuma, shida kansa ya kwashe plate ɗin yasata agaba suka fito, ake plate ɗin yayi a kitchen duka wuce party ɗin Hajja. Anan suka samu anata hira, kusan kowa na falon. Habiba ce keta faman basu labarai suna kyakyatawa. Yau da sauƙi, Aneesa bata wani ɓata rai dataga Habiba ba. Saima zama dasukayi suna ta hira abunsu. Hajja ta kalli MJ tace " Babana, yaushe zaka koma gida da matarka. Banason yawan zuwa hutunnan dakake musamman yanzu dakakeda mata. Isma'il yace gobe zasu koma sai in andawo shirye shiryen aurensa, kai ma kawai ku tattara gobe kowa ya koma wurin aikinsa " Aneesa jitayi kamar ta nitse aƙasa, yanzu mutane da gidansu shine za'a na koransu wai sukoma can wata uwa duniya. Raihanah ta saci kallon MJ, sai taga kamar shi abun ma daɗi yayi masa, ta maida idonta kan Aneesa taga yadda ta haɗe giran sama da ƙasa. Haka sukaci gaba da hira har lokacin Sallan zuhr.
Washe gari, Isma'il da Habiba suka shirya komawa Port Harcout, inda Mamy da Ammi suka yi mata sha tara na arziki. Sai ƙarfe tara suka kama hanya. Aneesa tana sane da MJ ya dinga haɗa kayansa, itakuwa ko akwatin ma bata fitar ba, har ya gama taga ya ɗau wayarsa yayi danne danne ya aje. Minti kaɗan sai aka kwankwasa kofar falonsa, budewa yayi saiga Raihanah da kayan Aneesa ahannu kamar zatayi gudun hijira. Tunda ta haɗa ido da Aneesa wadda ta cika tayi famm ai bata sake kallonta ba, karɓan kayan yayi ya rufo kofa. Miƙewa tayi ta fashe da kukan shagwaba harda bubbuga kafa aƙasa. Murmushi yayi ko kulata baiyi ba saida ya gama haɗa kayan tas cikin wani akwati, sannan ya juyo zuwa gare ta, har yanzu kukan takeyi da hawaye caba caba. Abun har ya bashi tsoro, ba dai har yanzu tana kan bakanta bane na cewa saidai ya rabu da ita.
Takowa yayi inda take ya jawota jikinsa ya runguma da kyau, lamo tayi tana kan kukan ahankali. Shafa gashinta yayi yace " bakiso ki tafine "? Girgiza kai tayi tana ajiyar zuciya tace " Ni dai kawai kawai kasa aƙwaso maka kayana. Kuma harda bra ɗina aciki fa" saikuma ta ƙara fashewa da kuka, ikon Allah. Yanzu dama saboda bra ɗinta dake cikin kayan shine yasata kuka. Kamar zai yi dariya saiya riƙe karya jawowa kansa wani abun daban. Saida ya ɓata lokaci wurin rarrashinta sannan ta yi shiru tanata faman turo baki gaba. Shiryawa sukayi, tana ganin ya ɗauki turare zai fesa tayi saurin hanashi tana toshe hanci, da mamaki ya tambayeta Meya faru, sai cewa tayi "wlh wannan turarennaka warin kashi yake mun" mamaki yahanashi magana sai kawai uhmmmm yace ya aje turaren ya fasa sawa. Bayan sun kammala shiri suka fito saƙale da hannun juna. Afarfadan gida suka samu mutanin gida basu koma ciki ba dan su Isma'il basu daɗe da wucewa ba. Sallama sukayi dasu, amma kafin su tafi saida Aneesa tayi kuka Hajja da Ammi sukayi aikin rarrashi, Innati kuwa jitake kamar ta kwakkwaɗeta, yarinya sai son shagwaɓan tsiya yadda kasan itace last born. Aadil na hannun babansa yana ta faman zazzare ido yana tsotsan hannunsa, karɓansa Aneesa tayi tanaji inana abata shi Sutafi tare. Kamar yaron yagane, shima tunda ya shiga hannunta yaƙi komawa hannun babansa. Ameera ce ta karɓeshi tana rarrashinsa kafin yayi shiru. Batareda ɓata lokaci ba suka shiga mota sai airport, suna isowa minti kaɗan jirgin su ya ɗaga zuwa birnin tarayya.
Wani babban gida Abby ya siyawa Amin acan Hotoro, anata gyare-gyare komai saida akasa sabo dal. Can gida kuma gyara Ameera take sha as per sabuwar Amarya, lefe kuwa tuni Mamy ta gama haɗawa dozen ɗaya. Aranan da Aadil ya cika arba'in aranan suka paka zuwa sabon gidansu. Gidane haɗadde ɗan dede four bedroom bungalow. Daren ranan Amin ya antayo da ledodi guda biyu. Sallan nafila sukayi tare suka ƙara godewa Allah, gasassun kaji ne irin gashi mai romo romonnan da exotic mai sanyi ya fitar yayi serving ɗinsu. Aadil da tuni yayi bacci bayan mamansa tayi masa wanka ta shiryashi cikin kayan baccinsa yana cradle.
Aranan saida Amin ya kashe ranan garin Kano gaba ɗayansu bai bar ko ɗaya ba. ALLAH yasa babu mai gadi balle wani bayansu a gidan, zabga ihu yadingayi yana kiran sunan Mamy da Ammi kai harda sunan Aneesa saida ya kira, tunda yake sex da mata awake bai taɓa jin irin ƙololuwan daɗi irinna yau ba (bambancin haram da halal kenan), Ameera tasha wuya iya wuya amma haka ta daure dan ta faranta masa, shi da kansa yayi mata wanka suka tsarkake jikinsu sannan suka kwanta, Aadil kuwa tunda ya farka saboda ihun da ubansa keyi haka ya koma baccin wahala tunda yaga babu sarki sai Allah bayan ya gama shan kukansa.
Su Isma'il suna komawa Port Harcout a satin su Abby suka tafi dashi da abokansa dan neman auren Habiba, ƴan gidan sunyi murna kaman me. Ansa biki nan da wata biyu, inda za'a haɗasu da Sultan da budurwarsa Ummu Sulaim. Habiba baki ya kasa rufuwa, tuni labari ya zaga ƙawayenta, sai faman nuna musu hoton angonnata takeyi sukuma suna ƙyasawa.
Tunda suka dawo Abuja babu abinda ya taɓa shiga tsakaninsu na auratayya, saidai babu damuwa tana kula dashi yadda ya kamata. Amma abun mamakin shine, bai isa yasa turare taki ba, ko turaren wutan datake sawa aɗakinta da gidan gaba ɗaya ta daina sawa wai warin kashi yake mata. Aneesa takai point ɗin da idan tayi abinci saidai tafito can wurin ɗakin maigadi tazauna taci, cewa take bata iya cin abinci acikin gidanta yanayi mata wari zatayi amai. Abun harya fara damun MJ, wani irin hanci ne da ita, kowa hancinsa normal amma ita kamar ta aljannu ne da ita, komai mai ƙamshi tace ita wari yake yi mata.
Gashi har yau kalmar nan ta "I LOVE YOU" takasa furta masa. Wani plan ya haɗa dan ya gwadata. Yau weekend Dan haka yana gida throughout. Tana zaune tana kallo ya shigo bayan ya dawo daga masallaci sallan azahar. Abakin ƙofa ya tsaya ya buɗe mata hannu alamar tazo, miƙewa tayi babu musu tafara takowa zuwa wurinsa, amma kafin ta kai sai jin mutum tayi aƙasa timmm ya faɗi babu alamar motsi atattare dashi. Ihu ta saki tana ƙwalawa sojojin gidan kira, da gudu suka shigo suna ganin Ogansu aƙasa sukayi saurin sungumeshi zuwa cushion. Ɗaya daga cikinsu ya kira doctor yayi masa bayani. Tana zaune tana kuka ta riƙe hannunsa kamar zata ɓallashi tana jijjigashi amma bai tashi ba. Doctor ya iso ya zauna kusada shi inda yajuwa Aneesa baya bata ganin fuskar MJ. A hankali MJ ya buɗe idanunsa ya kalli doctor ya kashe masa ido ɗaya, sojojinsa dake tsaye suna kallon wannan drama sukayi ƙoƙarin matse dariyansu, juyawa sukayi suka fita a falon yarage daga Aneesa sai Doctor da MJ. Juyowa doctor yayi ya kalli Aneesa yace "Madam, rabon da ki cewa mijinki i love you tun yaushe"? xaro ido waje tayi ta dafe ƙirji tace "i love you Kuma, Meya haɗa ciwonsa da i love you Doctor " ɗan ɓata rai doctor yayi yace "haba ai Dole ciwonsa ya tashi. Mutum nada ciwon hawan jini dayake buqatar ana ce masa i love you akai akai shine kika ƙyaleshi har tsawon lokacinnan baki ce masa ba"? 🙆 Hawaye na gangarowa a idanunta innocently ta matso kusada shi ta kamo hannunsa ahankali ta buɗe baki tace "Ya MJ katashi, wlh ina sonka sosai sosai. I love you, I love you I love you I love you " ta dinga maimaitawa kamar karatu, murmushi Doctor yayi, lallai ya yarda da wani malami yace mata wawaye ne, gashi da ƙarya kaɗan aka tono abinda ke zuciyarta. MJ kuwa Allah ne kawai yasoshi bai tonawa kansa asiri ba saboda daɗin daya mamayeshi. Kamar mai ciwon gaske a hankali ya fara motsi da hannunsa dake riƙe cikin nata, buɗe idonsa yayi ya ƙara lumshewa ya buɗe su tas akanta, rungumeshi tayi tana sakin kuka, da gudu doctor ya ɗau akwatin aikinsa yabar falon yana dariya. Shi kuwa MJ daɗi iya daɗi, hannu yasa ya zagaye bayanta yana bubbuga wa ahankali. Da ƙyar ya samu tayi shiru awurin har Bacci ya ɗauketa ahaka. Kwantar da ita yayi a ɗaki shima ya kwanta kusada ita ya jawota jikinsa shima yayi baccin.
Tunda suka dawo gida Goggo take fushi da Abba. Gashi babu abinci agidan kina misƙala zarratin. Duk kuɗaɗen da Abby yabawa Abba tas ya cinye su a kayan marmari shida Goggo. Goggo duk sai tabi ta kwaɓe a sati guda, wannan jikin datayi lokacin tana gidan Innati duk ya zube tas, takoma yadda take ada. Abba kuwa babu aikin fari balle na baƙi, tabbas yanzu kam ya yarda cewa haqqin matarsa na bibiyansa. Ana nan ana nan wani rana wani mutum mai suna Alhaji Bobo yazo gidan da safen Allah lokacin suna karin kumallo da garin kwaki a tsakar gida. Jin sallamarsa yasa Abba miƙewa da gudu ya shiga ɗaki yana cewa Goggo tace masa baya gida. Wasu zaratan maza ne suka shigo su uku cikin zafin nama suka fara tarwatsa tukwanen dake tsakar gidan suna ball dasu, salati Goggo tayi ta miƙe tana neman taimako wai ƴan fashi sun shigo masu gida. Alhaji Bobo yashigo Rai aɓace yace "Malama kiyi mana shiru, kuma kicewa macucin ɗanki ya fito waje, idan kuwa ba hakaba sainasa anyi raga raga da sauran haƙoran dake bakinki. Cikeda tsoro Goggo ta ƙwala ihu tace "Zaidu kafito, kanaji kana gani za'a hallaka mamanka amma kana ɓoye aɗaki ɗannan" ɗaya daga cikin samarin ne suka shiga ɗakin da Goggo ke kallo azafafe ya hurgo Abba waje. Rikeshi sukayi su biyu Alhaji Bobo ya kids masa mari akumatu yace "Zaidu ina takardun filaye na dana baka saƙo ka kaiwa gidan sanata? Ko ka fitar mun dasu koka sa ran zamanka acikin gidannan ya ƙare" fitsari na neman ƙwacewa Abba a wando ya yi saurin matse ƙafa yace " Alhaji kayi haquri, kaɗan bani lokaci. Wlh wani ɗan ƙwangila na saida mawa, amma inajin ya shigo gari zan je na yi ƙoƙarin amso maka takardunka " tsawa ya daka masa yace "kar ka maidani wawa Zaidu. Daga gidan ɗan kwangilan nake kafin nazo nan. Tuni angama gine gine a filaye na, ka siyar masa da filayena a matsayin naka bayan kasa a canza sunana zuwa naka. Kai omale ku kira masu bull dozer dinnan ayi daga raga da gidannan kar komai ya tsira. Sunaji suna gani masu bull dozer suka zo, aka fatattakesu waje, cikin abinda baifi minti arba'in ba aka yi ƙasa da gidansu Goggo. Mutanin anguwa sun fito sun tsatssaya suna kallon wannan ikon Allah. Goggo kuwa sai birgima take akan yashin gidan tana kuka har zaninta ya kwance saura patarinta tsamamme da baya samun wanki. Mai garine ya tausaya musu yace su zauna agidansa zuwa gobe sai suka ma hanya zuwa koma inane zasu. Washe gari Abba yace su shirya sukoma Kano zuwa gidan Baba Auwalu. Hmmm
Ranan Monday itada kanta ta shiryashi cikin three pieces suit mai kyau, amma duk wankannan kememe taki yasa turare, sai faman manne mata yake (su MJ ansami abun da akeso), da ƙyar ta ɓanɓareshi ajikinta ya tafi aiki. Ahaka ma bai wani jima ba yadawo gida. Yanayin yadda taganshi sai ya tuno mata da lokacin first night ɗinsu. Yadawone idanunsa wani iri. Tana kula dashi kamar tsoro yake ya tambayeta kar tace a'a, itakuwa data gane taje tayi wanka ta shirya cikin bumshot da half vest irin mai botura agabansa ko bra batasa ba ta ɗora hijab akai. Aɗakinsa ta sameshi ya fito daga toilet dagashi sai gajeren wando. Kallonta yayi idanunsa aƙanƙance ya marairaice fuska ya buɗe mata hannunsa. Da gudu ta cire hijabi ɗinta ta ƙarado gareshi, kusan suman tsaye yayi a lokacin data cire hijabi, yadda boobs ɗinta ke up and down shine ya kashe masa tunani. Baiyi sune ba sai ji kawai yayi ta haɗe bakinsu wuri ɗaya azafafe take bashi hot kisses. Dama kuwa jira yake shima ya kama kanta da kyau ya karkace yana maida mata martani. Komai zafi zafi sukeyinshi, tunaninsu da kayansu duk yabar jikinsu batareda sun saki ba, irin foreplay ɗin dasukayi har Aneesa ta mance irin azabar daya gana mata a lokacin farko. Lokacin data dawo hayyacinta kuwa tuni MJ yayi nisa a duniyar ta bayan yayi addu'a, babu wani maraba da lokacin farkonacan sai dai wannan karon tayi iya ƙoƙarinta wurin ganin batayi masa magiya ba, hakan kuwa itama ya taimaka mata, dan inda batayi haka ba, zai yi amfani da force ayanda yake bayaji baya gani. Zunduma ihu yake son ransa itakuwa kamar gawasau hawaye da kukan zuci, bai tashi sarara mata ba saida ya gwada duk wata style daya sani akanta. Irin ambaliyar dayayi mata kuma, ita kanta tasan cewa ya daɗe yana haquri da rashinta akusadashi. Mirginawa gefe yayi yana maida numfashi, saida yaji ƙarfi sosai ajikinsa sannan ya mike ya wuce toilet ya haɗa ruwan zafi a tub, dawowa yayi ya sungumeta zuwa toilet din. Sosai ya gasata kuma wannan karon batayi masa irin kiciniyar datayi wancan lokacin ba. Wanka sukayi ya fito da ita ahannu sai faman zuba masa shagwaɓa take yana biye mata.
Ahaka rayuwa taci gaba da tafiya, cikin tsantsan soyayyar juna da kulawa. Basu kara zuwa Kano ba sai lokacin cikinsu Isma'il. Anyi taro sosai nagani nafada, kuma an ɗaura aure lafiya an kaiwa kowa amaryarsa inda Isma'il shi zai koma can Port Harcout da amaryarsa amma zasuna zuwa gida akai akai. Ummu sulaim din Doctor Sultan kuma anan Kano gidansu yake. Kowa yana ji da matarsa suna kashe love yadda Yakamata. Aadil yayi wayo inda yanzu zama yake yi, ga Amin daya zama maƙale mata awurin Ameera. Ya koma makarantarsa itama ta koma Tata. Haka da safe zasu shirya sai su kawo Aadil gida wurin Ammi, sai ya kaita makaranta daganan shima ya wuce tasa makarantar. Kowa saida ya sheda nutsuwar Amin. Hatta VC ɗinsu dayayi masa wulaƙanci duk yanzu an shirya yazama obedient. Yanzu haka yana final year ɗinsa, Ameera Kuma tana SS 3 kenan zasu rubuta WAEC.
Tun bayan bikin su Isma'il dasuka dawo gida ya lura da yawan ƙananan ciwo datakeyi akai akai. Har yasa baya zuwa aiki shi kadai saidai suke tare, ita aikinta bacci kawai a office dinsa. Idan yayi baƙi kuma saidai abuɗe musu wani office daban saboda kar adameta. Da yamma kuma kafin sukoma gida to ƙa'ida ne suke cold stone asiya ice cream kala kala. Abun mamaki kafin washe gari tas ta shanye su. Bai taɓa lura da cewa tunda tadawo gidansa ko sau ɗaya bata taɓa yin period ba tunda shi kullum cikin shan zuma yake. Ga wani kyau data ƙara tayi fresh Masha Allah.
Kusan wata biyar kenan da dawowarta Abuja. Tana zaune tana shan ice cream yadda ta saba, ta buɗe saman rigarta tabar ciki awaje, saukowa yake daga kan bene. Tundaga nesa ya hango yadda cikinta ya taso yayi kummm dashi, har yana cin tuntubi ya ƙaraso wurinta da gudu ya durƙusa aƙasa yasa hannu akan cikin, kamar jiraa cikin yake taji wani shafi pain adaidai inda hannunsa ya taɓa kamar an buga mata abu awurin har saida ta saki ƙara. Kallon ta MJ yayi yace "sweetheart rabon da kiga period ɗinki tun yaushe "? Sai yanzu ma ta tuna da wani abu wai shi period, kan uba. Aikuwa ta nace tun yaushe tayi period, badai wani cuta ne da ita ba. Rau rau tayi da ido zatayi kuka da sauri MJ ya hanata, yasan halin sarai idan tafara kuka to wani aikine daban rarrashinta. Kwantar mata da hankali yayi ya ce anjima zai siyo mata pt ta gwada. Bai jima ba kuwa ya fita yaje yasiyo yakawo, amma acan pharmacy aka ce masa yabari sai gobe da sassafe fitsarin farko saita gwada dashi. Da asussuba ya tashe ta tana cikin baccinta mai daɗi ga namomin kaza agabanta tana yagawa, kuka tasa mishi wai yayi mata bukulu yasa naman kazan ya gudu. Aneesa akwai abun dariya. Dakansa yayi mata gwajin, tare suka tsaya sun kafe pt da ido suna jiran ganin sakamako. Positive ya nuna musu wani irin ihu sukayi su biyun a toilet, da sauri ya ɗagata sama yana murna. Itama haka, Finally zata haifi babyn kanta kuma da mutumin da take tsananin sonsa fiye da kowa. Har hawayen farinciki yayi yana murna.
After three months.
Tana ture zungumemen cikinta akitchen tana aiki a hankali, ƙafafunta duka biyu sun kumbura suntum. Ga wani budewa data ƙarayi kamar wata mama, hips dinnan bajam kenan, boobs kam ba'a magana. Breakfast tray ɗinsa ta riƙe ahannu zata fitar falo, tanasa ƙafa wajen kitchen taji ƙafan ya riƙe gam yaƙi motsawa. Cikinta da bayanta ya riƙe, sake trayn tayi aƙasa tana dafa bango wai wash wash take tana cize leɓe. Saukowarsa kenan yaji ƙaran zubewan abu aƙasa, da sauri ya karaso wurinta inda yaga tana murƙususu. Cikin fitar hayyaci ya sungumeta sai waje yana ihun abuɗe musu gate da sauri. Sun iso asibiti babu bata lokaci aka kaita labour room
Allah yakawo mata cikin sauƙi, shiganta da aihuwarta duk baikai minti goma ba. Tsaleliyar budurwa ta haifo kyakyyawa mai Kamada Mujahid.
Nurses sun gyara ta da babyn, tana bacci aka kawo wa MJ ɗiyarsa. Har hawaye take a lokacin daya riƙe little princess ɗinsa ahannu, sai yanzu ya yarda blood is thicker than water. Kwata kwata baiyi irin connection dinnan ba alokacin da Neehal ta haifo