Rayuwar Aneesa complete Hausa Novels pdf Reemah.txt

Author :  Reemah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 24

24K to 27K   out of 70.4K words

itaɗin ƴar tsuntuwa ce. Hawayen farinciki ne ya fara gangarowa daga idanunsu gaba ɗaya, cikin begen juna Hajja da Innati suka rungume juna suna cigaba da kukansu.

Na da Ameera duk muka tsaya muna kallon wani babban iko wadda Allah kaɗai keda ita. Kenan mu ɗin jikokin gidan Isa Mainoma. Hannu Hajja ta miko mana mu biyun tayi mana alama da muzo wurinsu, da murmushi mai kamada kuka mukazo tahaɗa damu ta rungume akirjinta. Hajja baki ya kasa rufuwa sai furta kalmar godiya take abakinta. Bayan komai ya lafa duk suka zauna saman carpet dake malale a falon Hajja sai kallon Innati take tana murmushi. Turawa sunce blood is thicker than water, gashi dai banda kama tun kafin suga junansu amma zuciyoyinsu yariga ya basu cewa sunsan juna. Wayarta ta ciro ajaka ta dialling numbern Abby. Bugu biyu Abby ya ɗauka tun kafin yayi sallama Hajja ta tari numfashinsa tace "Ɗan Isa ka kasa nemo mun ƴata, to gashi ni da kaina na samota. Allah ya nuna min ita da kaina. Sai anjima" bata bari Abby yayi magana ba kittt ta kashe wayar. Kallon Aneesa tayi ta ce "takwara ashe dai keɗin jikata ce, Allah sarki shi yasa najiki daban azuciyata na ɗaukeki a matsayi ɗaya dasu Raihanah. Taho nan mai kamada Nadeen " taƙarashe maganar tana mikowa Ameera hannu alaman tazo. Cikin sanyin jiki taƙaraso wurin Hajjar, sai kuma takara fashewa da kuka. Sai asannan kuma hankalinsu Hajja da Aneesa yadawo kan cewa ai akwai abinda yafaru dayasa su zuwa gidan. Kallon Innati tayi tace "Nadeen mai ya sameta. Ɗan Isa yabani labarinki da komai. Kuma inshallah ƙarshen wahalarku kenan arayuwa. Saina tabbata kun samu jin daɗi wadda baku taɓa tsammani ba. Yanzu dai zaku shirya dan tareda ku zamu koma gida bazan barku anan ba" cikin kuka Ameera tace "Hajja babu inda zani. Bazan iya fita na kalli mutane ba. Gani zanyi kamar kowa zaina kallona da abun kunyar dake jikina. Bazan iya ba"


Kallon Innati nayi naga kanta aƙasa, to me suke boye mana ne. Hajja tace "Nadeen menene yake damunta, ku faɗa mana mana, duk kunbi kunsa hankalina ya tashi haba dan Allah " ɗagowa Innati tayi naga idanunta sun juya kala zuwa jaa tace "Hajja Ameera na ɗauke da juna biyu ne" salallami Hajja tafara tana maimaitawa. Nikam daskarewa nayi naji gumi duk ya rufeni na kasa koda ɗaga yatsana ne. La haula waka quwwata illa billah. Allahumma ajirnee fee musibaty wa akhlifnee Khairan minha. Hasbunallahu wa ni'mal wakeel. Ciki? Ameera nada ciki? Babu babban jarabawar daya kai wannan girma a rayuwar budurwa. Shikenan an gama da rayuwarta.


Ganin hankalin kowa atashe yake yasa Hajja danna nata tashin hankalin sanya kwantar musu da nasu. Kamo hannun Ameera tayi cikeda kulawa tace " karki damu. In every disappointment there's surely a blessing. Wannan cikin tabbas disappointment ne amatsayinki na budurwa, amma kuma ɗan dake cikinki bi'znillah alkhairi ne dashi mai ɗunbin yawa. Bazaki depressing kanki akan abinda bakida laifi akai ba, tabbas maganan mutane zaiyi yawa amma inaso kiyi kokari ki tsohe kunninki kar ki taɓa yarda maganan mutane yayi tasiri akanki. Ai Allah ba azzalumin bawa bane, kuma yana sane dake. We shall overcome this together" wannan nasihar ta Hajja ba ƙaramin kwantar musu da hankali yayi ba. Haka sukayi ta ɗan taba hira wadda kusan gaba ɗaya akan rayuwarsu tabaya ne. Watau duniyannan,komai kudinka baka isa ne ka hana wani abu yasami wani naka ba. Idan ba haka ba, duk da kuɗi da kuma dukiya da Allah yabawa su Hajja hakan bai hana ƴarta ta sha gwagwarmayar rayuwa ba. 🥹🥹🥹

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

"Yes Please do check that out and keep me updated about all that's ongoing at the headquarters. Kitt ya kashe wayar sannan ya maida hankalinsa kan abinda yake yi a system dinsa. Ɗan gajeren wando ne abokinsa da riga armless irin mai tsayi dinnan. Isma'il ne ya fito shima sanye yake da kananan kaya kamar na danuwansa. Yau fuskar cike take da annuri ba kamar kullum dayake cin magani ba.

Kallonsu Mujahid yayi yace "soja ƙanin mutuwa. Ana ganinku jiki ke rawa" ƴar dariya Isma'il yayi wadda ya bayyana zallan kamarsa d Mujahid saidai Mujahid yafi shi haske sosai. Ɗan jimmmm Isma'il yayi kamar da magana abakinsa saikuma yace " bros, how do you see wannan yarinyar ta wurin Hajja" kallonsu Mujahid yayi yace bangane ba wacce yarinya kake magana akai, murmushi Isma'il yayi yace "that beautiful girl dake zama da Hajja" kwata kwata MJ yamance da wacce yarinya Ismail ke magana akai saida yayi masa kwatancen ta, wani irin dariya ya fashe dashi harda kyalkyalwa ya tafa hannu yace "lallai Isma'il, badai so kake kace mun yarinya mara kunyar nan kake crushing akanta ba. Cabb, dama dai ka cire wannan filthy tunanin akanka. Yarinyar nan samm batayi deserving soyayyarka ba, she's a maid fa for crying out loud. Mai aikin Hajja ce. Mezakayi da ita bayan ga mata dayawa a waje masu qualification sai wacce ka zaɓa, come on Man" sosai wannan maganar ta MJ ya taɓa Isma'il amma ya dake yace "bros kenan. Ai baka saniba, ni cikin spec ɗina na macen danakeso na aura, banason wacce idonta ya buɗe ba. Nafison na auri wacce ni da kaina zan koya mata abubuwa da kaina. Zan ɗorata a tafarkin danakeso tacigaba. So all that you mentioned is just a world of fantasy" wannan karon ma dariya MJ yayi yace "lallai yaro ashe da bazaka taɓa sanin menene soyayya arayuwarka ba. Jeka ka auri ƴar ƙauye wacce zatazo ta hura wutan icce akitchen ɗin da akwai gas. Kai baka ga rayuwata da Neehal ba, she was the perfect one for me. Babu abinda na koya mata saima wanda ni ta ɗorani akai. I missed those days, ban taɓa tunanin rabuwa tsakaninmu ba amma gashi" sai kuma yanayin fuskarsa ya canza. Girgiza kai Isma'il yayi, yasan idan Mujahid yafara hira akan Neehal to ba'a ƙarewa ta daɗi. Gara kawai ya canza salon hirannasu dan shi kansa ya tsani labarin Neehal dama komai daya danganceta, asanadiyyarta ɗan uwansa ya kamu da cutar hypertension harya jefa kansa cikin depression wadda ya haddasa masa tsanan mata da kuma trusting ɗinsu ma gaba ɗaya.

Shikam MJ tunda yayi shiru ya faɗa duniyan tunani. Ganin haka yasa Isma'il canza hiran zuwana politics da kuma abubuwan daya shafi wuraren aikinsu. Wayar Mujahid ne yayi ƙara, ɗagawa yayi da sallama abakinsa. Abby a ɗayan bangaren da bakinsa ya kasa rufuwa yace " Babana Alhamdulillah, Hajja ta haɗu da Aunt dinka. Allah ya bayyana mun ƙanwata Mujahid. Yanzu dai dan Allah kayi ƙoƙari a tracking ɗin wayar Hajja Dan taƙi ta faɗa mun inda suke". Cikin ladabi MJ ya amsa wa babansa sannan ya kashe wayar. Fuskarsa ɗauke da tsadadden murmushi ya faɗawa Isma'il abinda yafaru. Hamadala shima yayi sannan suka fara tracking wayar Hajja a system ɗin MUJAHID. Bayan sun gano inda take suka kira Abby suka sanar dashi. Sosai Abby yayi mamaki dan wannan ai estate dinsa ne, dama ƴar uwarsa na zama a estate dinsa all this while shine bai sani ba. Batareda ɓata lokaci ba ya tara sojojinsa mota uku suka tafi estate dinnasa dake can GRA Nassarawa, Kano.

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Wani kwalin exotic ne ahannunsa ga kuma allura aɗayan hannunsa dayake injecting zuwa kwalin exotic din da murmushin mugunta a fuskarsa. Bayan ya gama ya jijjiga kwalin sosai ya maida shi fridge ɗin kitchen ɗin Hajja ya rufe. So much excitement on his face 😈. Akwai abinda Amin ke shirya wa amma Allah yafi shi.

Cikin takunsa na ƙasaita ya fito daga kitchen ɗin yana gyara hannun rigarsa. Bayan ya fice Baba Larai ta fito daga wani lungu na falon tana sakin ajiyar zuciya. Da alama dai taga abinda yayi a kitchen ɗin, hankali tashe ta wuce kitchen ta buɗe fridge. Ba lallai sai wadda ya shirya wa plan dinnan abun zai sama ba, hala ma aje kuma Hajja tasha ko kuma wani daban. Da sauri ta ciro kwalin exotic din ta buɗe ta zazzage shi tass a cikin sink area sannan ta dauko wani kwali daban a store ta maida shi fridge ta rufe.


🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Mamy na ninke kaya Abby ya kirata akan tafaɗawa kowa ya hallara afalon Hajja gasunan zuwa za'ayi taro na musamman ne. Mamy bata kawowa ranta komai ba duk da ba kasafai haka Hajja ke tarasu gaba dayansu ba saimun wani abu na musamman ne ya faru. Kiran Ammi tayi awaya ta sanar da ita abinda Abby ya faɗa. Batareda ɓata lokaci ba matan da ƴaƴansu gaba ɗaya aka hadu gaba ɗaya kowa na tunanin to kome yafaru da Hajja ta nemi su haɗu?


Cikeda farinciki Hajja tafito daga mota hannunta cikin na jikokinnata. Abby Kuma ya riƙe hannun Innati suna tafiya cikeda walwala. Da sallama abakinsu suka shigo falon, Abby da Innati ne agaba sai Hajja dasu Aneesa suna biye dasu.

Amin dake zaune shida Sultan akan two seater yana latsa wayarsa baima lura da shigowarsu Abby ba. Su Mamy dasu MJ kowa ya kafa idonsa kan Innati ana kallon ta. Sosai suka zuba mata ido farinciki ƙall afuskokinsu. Sallama Hajja tayi itama ta shigo da ƴan matanta.


MJ daya ƙyallara idanunsa kan Aneesa lokaci guda yaji gabansa ya faɗi, me hakan ke nufi. Nooo its not possible. Babu yadda za'ayi mai aiki tazama cousin sister ɗinsa. Impossible.

Ameera gaba ɗaya sai taji wani irin tsoro ya shige ta at once. Musamman dataga kusan rabin falon kattin maza ne masu jida jini ajika. Wannan fargaban saitaji yadawo mata sabo dal. Hannun Hajja ta ƙara riƙewa kam har hakan yasa Hajja juyowa ta kalleta. Sosai taga yanayin fuskarta ya canza zuwa tsoro. Ƙarasa shigowa falon sukayi gaba ɗayansu. Ahankali Ameera Kebin kowannensu da ido har idonta yakai kan Amin wadda alokacin shima ya ɗago ya kalleta idanunsu ya sarƙe cikin na juna. Rugugugugugugub. Cikin kiɗima Amin ya miƙe tsaye yama mance cewa bashi kaɗai bane a falon, "kkkkkkeeee, Ke?? Mekikeyi anan?.....


Kakara kakakakak 🙆🙆🙆 ana bala'i agidan Jenar.


Pls manage🙏

Like
Comment
And share🙏🙏🙏

🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷


Reemah ✍️


PG 41_45

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Ganin yadda Amin yabi ya rikice upon ganin Ameera yasa hankalin kowa dawowa kansa. Sai wani sambatu yake kamar mara gaskiya. Ameera kam kasa riƙe firgicin datake ciki tayi ta fara nunashi da hannu bakinta na rawa hawaye na gangarowa daga idanunta tace "SHINE, WLH SHINE,INNATI SHINE YAYI MUN FYADE" kuuuuuuu cikin Amin ya ɗauwani sauti wadda Sultan dake gefensa kansa saida yaji. Cikin tsananin ɓacin rai MJ da Isma'il suka miƙe suka hada baki wurin faɗin "MENE, FYADE"? Take kafafun Amin suka kasa daukansa,ji yayi idan ya ƙara minti ɗaya a tsaye tabbas zasu iya gaza ɗaukan nauyinsa. Cikin aro jarumta yafara magana yana stammering yace "mmmme ne? Fyaɗe? Bani bane wlh ƙarya takeyi, ni ban santa ba" dunƙule hannu Isma'il yayi azafafe ya kaiwa Amin wawan naushi abaki wadda yasa gefen bakinsa fashewa. Mamy da Ammi mezasuyi inba kuka ba. Raihanah da Mustapha kam sai murmushi suke, yau Allah ya tona asirin Amin.

Miƙewa Amin yayi yafara kukan munafirci yana cewa "wlh bani bane. I don't know what she's talking about" bai gama rufe baki ba MJ yaƙara daukeshi da wata zazzafan mari both right and left cheeks ɗinsa. Abby daya kasa koda motsawa ne a hankali yayi ƙoƙarin saita kansa har ya tako inda Amin ke tsaye, collar rigarsa ya riƙe yafara jijjigashi yana faɗin "Amin why, why Amin. Meyasa duk cikin ƴaƴana kaine kawai ka zabi ka zubar mun da mutunci a idon jama'a. Mene ka nema wadda banyi maka ba. Son abun duniya dakuma son mata yakaika ga aikata babban laifi wadda Allah ya tsinewa duk wadda ya aikata wannan laifin. Yanzu mene ribarka nayin haka. Yanzu koda yarinyar nan ba jininka bace kenan dakana tunanin kaci banza. Toh bari kaji wlh Allah ma bazai barka ba. Kuma nima ba zan Barka ba, insha Allah sai na ɗau mataki. Daga yau ko kuɗi za'a baka ka kalli wata mace awaje da filthy tunani aranka bazakayi ba. Mujahid kuyi mun maganinsa"

Kamar kuwa jira MJ da Isma'il suke, Abby na sakinsa suka kamashi sukayi ta jibgarsa, idan wannan yayi ya gaji sai ya jefawa wannan, sun maidashi kamar punching bag. Ammi sai kuka amma takasa hanasu dukan ɗannata. Ai daidai sukeyi, yakamata ahukuntasa daidai da laifinsu. Kallon Ameera tayi taga duk yadda yarinyar tabi ta rikice sai kuka itama takeyi. Sosai yarinyar tabata tausayi, yar karamar yarinya Amin ya lalata mata ta rayuwa da future ɗinta.

Saida suka tabbata sunyi masa jina jina sannan MJ yakamo collar ɗinsa ya jawosa har gaban Ameera ya yardashi agaban ƙafafunta, da sauri takoma baya tana kama hannun ƴar uwarta. "Beg for her forgiveness Now" MUJAHID ya faɗa cikin kausashshiyar murya, da sauri Amin ya kamo ƙafanta yana kuka yace "dan Allah kiyafemun, wlh bazan ƙara ba. Na tuba nabi Allah" babu wadda yaji tausayinsa afalon saidai mahaifiyarsa wacce itama kuka takeyi kamar harda ita aka jibga. Zuciyar mahaifiya daban take🥹

Jansa Isma'il yayi ya wurgoshi tsakar falon sannan kowa ya zauna aka sashi a tsakiya. Innati dai ta kasa cewa komai sai ɓarin hawaye datakeyi. Allah kenan, ashe dai ba'a kan ƴarta yafara ba, gashi kamuwar Allah sai ya faɗa akan ƙanwarsa duk da baisan cewa itaɗin ƙanwarsa bace.

Ajiyar zuciya Hajja tayi tace "gaskiya mun haɗu da babban jarabawa, munada bara gurbi a cikinmu wadda shine ɓata gari. Haƙiƙa Allah ba azzalumin kowa bane. Kuma ance "kama tudinu tudaan" duk abinda kayi inma Alkhairi ko sharri kaima sai anyi maka. Toh gashi Allah ya nuna mana, Amin tun ba'a je ko ina ba sai gashinan akan ƙanwarka Allah ya ramawa sauran innocent girls din daka dinga yiwa wannan abun. Kuma kasnii bafa Allah yabarka ahaka bane, kayi mata tsiyataku kaida abokanka kana tunanin cewa ai itaɗin ba komai bace. Allah yasa da asirinka ya tonu bainan jama'a, mene yakai haka kunya. Ƙannenka da yayyinka all are ashamed of you. Gashinan dai asanadiyyar wannan abun, abinda ba'a fata yafaru. Yanzu haka yarinyar nan tana ɗaukeda gudan jininka acikinta. Kaga ko there's no two way about it, Allah ya riga ya haɗa ƙaddararku" dammmmm Amin yaji azuciyarsa, me Hajja take nufi da Allah ya riga ya haɗa ƙaddararsu. "dan gidanku you're gonna get married to her whether you like or not. Babu yadda ka iya it's not up to you saidai in inta tace batada niyyar aurenka"MJ yafaɗa yanaji kamar ya miƙe yacigaba dayiwa Amin ɗin shegen duka dan har wani ciza lebe yake tsabar fushin dake cinsa aciki.


Wani irin kururuwa Amin yayi yafara kuka kamar ƙaramin yaro yace "Babban Yaya bazan iya aurenta ba. She's not a virgin fa. Wlh bazan iya.." bai rufe baki ba Abby ya ɗaukeshi da wawan mari sau uku, har idonsa ya kumbura yayi jaa abun aji tausayinsa kuma abun takaici.

Girgiza kai nayi ina ayyana irin rashin kunya na Amin, agaban iyaye da yayyi yake cewa bazai iya aurenta ba she's not a virgin, wane ya karɓi virginity ɗin nata da har ya iya buɗe baki yayi maganan banza. Ji nake kamar na ɗauko muciya nayita raɗa masa akai. Ni dukan ma da akayi masa wlh aganina kaɗan ne dahar yakeda bakin dazaiyi maganan banza. Kai amma anyi asara anan, kuma inshallah Ameera bazata taɓa auren wannan mazinacin ba. Ji nayi na ƙara tsanan wannan arrogant man ɗin saboda shiyakeso yayi haɗin da bai dace ba.


Cikin kuka Ammi tace " Amin saifa ka aureta idan har mu mun isa dakai. Dama wakakeso ya aure maka ita bayan komai da hannunka ka aikata. Karkasa nayi maka baki wadda zai bika har makwancinka, shashashan banza kawai. Allah ya shiryeka idan har kaiɗin mai shiryuwa ne.

Ameera dake kan matso hawayen takaici tace "Ni dai ba zan aure shi ba. Mugu ne azzalumi kuma dan iska. Na gwammace na zauna haka ba aure har ƙarƙen rayuwata idan har dashi zan zauna. Na tsaneshi na tsaneshi kamar mutuwata"

Abby zaiyi magana hajja ta dakatar dashi ta hanyar faɗin"a'a ɗan Isa. Yarinyar tagama magana, tunda tace bataso to shikenan basai an tursasata ba. Shi kuma Amin shima nawane dan haka bazanyi masa mummunan baki ba. Allah ya shiryeshi yasa ya gane. Wannan taro danaso ayishi cikin farinciki amma sai gashi ran kowa aɓace yake dan haka babu wani jimawa dazamuyi. To yara da iyaye ga ƴata Nadeen wadda nayi shekara talatin da huɗu ina nemanta sakamakon wasu mugayen mutane da aka haɗa baki dasu wurin saceta. Munyi neman duniyarnan amma muka kasa gano inda ƴata take, Allah yau ya bayyana mun ita da ƴaƴanta watau jikokina. Allah yayi muku albarka. Mujahid ashe dai ƴar aikin ƙanwarka ce ta jini, yanzu dai sai a rage kiyayyar da cin zalin da akeyi mata"

MJ dake wani cin magani ya kalli Aneesa yaga kanta aƙasa yake. Ƙasa ƙasa ya buga mata wani uwar harara kamar zai ciro idon waje. Abby dake lura dashi yayi wani murmushi ya girgiza kai. Yara kenan, ance mugun ƙiyayya na iya juyawa mugun soyayya . Ko me Allah zaiyi nan gaba shi kaɗai yabarwa kansa sani.

Miƙewa Ammi tayi tazo har gaban Innati ta tsuguna kamar me neman gafara ta haɗe hannayenta wuri ɗaya tafara neman yafiyar Innati akan abinda Amin yayiwa ƴarta, cikin dakiya da juriya Innati tayi maza takamo hannunta ta miƙar da ita tsaye tace "haba dan Allah Antyna, Ni nariga na yafe masa. Ai ƴaƴan duka namu ne. Saidai muce Allah ya shirya kuma Allah ya kiyaye gaba" da farinciki duk suka amsa Ameen. Cikin sanyin jiki kowa ya miƙe yayi part ɗinsa. Raihanah takamo hannun Aneesa da Ameera zuwa part ɗin Mamy sai washe baki takeyi, yau itama zaman kaɗaici yaƙare. Ashe dai tanada cousins mate ɗinta, gaskiya tadaina kwana aɗaki ita kaɗai daga yau.

Amin kawai aka bari da MJ afalon Hajja, ya durkushe awurin ya kasa miƙewa. Sai hawaye yakeyi yana danasanin abinda ya aikata. Ashe dama talala Allah keyi masa ya ɗauka kamar priviledge dinsa ne kawai yasa yake shanawarsa. Gaskiya daga yau zai fita harkan

9 / 24