Author : Reemah Category : Romantic Hausa Novels
hayaniya yayi yawa. Gaba ɗaya mutanin gidane afalon, nida Ameera ne kawai babu. Dake ita yanzu cikinta yayi girma dan haka yana ɗan bata wahalan fita ko ina.
Yana durƙushe kan carpet idanunsa aƙasa, ga Abby dayasashi agaba da faɗa, Hajja da Innati suna zaune kan cushion babu mai magana. Su Raihanah na hango can gefe itada Mustapha sun zuba min ido kamar zasu zaƙulo hanjin cikina. Ya Sultan ma haka, idanun kowa naga yadawo kaina har na fara tsarguwa. Asanyaye na ƙaraso cikin falon na zauna kusada Mamy, hannu tasa ta shafa dogon gashina tana tambayata babu abinda ke damuna dai ko. Girgiza kai nayi ina kallon shi yadda ya kife Kai aƙasa ya kasa ɗagowa.
Abby naji Yana cewa "Toh gashinan ta sauko, yanzu nakeso ka rubuta mata takardanta kabata agaban kowa, kuma Bayan haka inaso kaje Port Harcout ka roki ƙaninka ya dawo gidannan a ɗaura aurensa da Aneesa" yafaɗa yana jefa masa paper da biro. Sai yanzu yaɗago na samu na kalli ƙwayar idonsa, ya canza launi yazama wani irin jaa mai ban tsoro, hawaye na gangarowa daga idanun nasa. Haɗa ido mukayi, yadda yake kallona har cikin bargona nake jin kallon, ban iya jure wa ba kawai na kauda kai. Ina addu'a a zuciyarta Allah yasa ya rubuta min takardata, Allah yasani bazan iya rayuwar aure dashi ba.
Asanyaye ya ɗau papern har zai Fara rubutu naji Hajja tace "idan Mujahid ya rubutawa Aneesa saki, kusa aranku zamana agidannan yazo ƙarshe" da sauri duk muka juya muna kallon Hajja, mamaki ƙarara kwance afuskar Abby yace "Hajja, wani irin magana ne wannan fisabilillah, kiga halinda yarinyar nan take ciki. Ita ma fa ba sonsa take ba, dan meyasa za'a ɗora mata abinda batada niyya" kallona Hajja tayi tace "takwara kina don Mujahid ko kuma a'a, karkiji tsoron kowa. Nayi miki alƙawarin cewa idan kikace bakiso nida kaina zan sa ya rubuta miki takardanki", rasss naji zuciyata ta buga. A hankali na maida idanuna kansa, yadda yake kallona in a sympathetic way shiya sanya naji wani irin yanayi atare dani.
Sauke kaina nayi ƙasa, bansan ya zan kira wannan moment ɗin ba. Na dai san cewa bana son shi, to amma meyasa nakasa buɗe baki na faɗa musu hakan. Nayi iya ƙokarina wurin ganin cewa na girgiza kai tunda bakina na muzanta abinda raina keso, amma kuma sai naji kamar wuyan nawa an riƙe ta. Kusan mintina biyu falo ya ɗauki wani shiru, ana jiran aji mezan faɗa.
Hajja kuwa ganin haka yasa ta concluding cewa Aneesa tana don Mujahid. Kallon MJ yayi dake tsugune aƙasa, tace masa " Mujahid miƙe" kallonta sukayi suna jiran mezata ce, asanyaye ya miƙe still idanunsa na kan Aneesa da hawaye ke gangarowa daga kurmin idanunta tana amfani da ɗankwalinta tana sharewa. Abby kuwa sai jifansa yake da mummunan kallo. Hajja tace "kema takwara miƙe" da sauri na ɗago ina kallon ta, mekuma take so nayi yanzu. Miƙewa nayi ina kallon yatsun hannuna na kasa ɗagowa in kalli kowa Afalon. Ban farga ba sai ji nayi Hajja ta yafa mun mayafinta Wadda ya matching da kayan jikina, ta kamo hannuna sai ji nayi ta sanya shi cikin wani abu mai uban laushi. Sai da na ɗago naga cewa, hannunsa ne, kamar auduga haka hannun nasa keda taushi. Zuru zuru nayi da ido, me tsohuwar nan take shirin yi.
Sai ji nayi tace " daga wannan falon, babu inda zaka tsaya sai gidanka. Inaso ka tafi da matarka yanzunnan. Duk wadda yasan ban isa dashi ba ya gwada tsaida ku" gaba ɗaya ƴan falon suka juya suna kallon Hajja. Tuni hawaye ya fara Zarya a idanuna, zan ƙwace hannuna naji ya ƙara damƙe wa da kyau, Hajja takoma ta bayanmu sai tura mu take yi har takai bakin ƙofan falonta sannan ta rungumemu gaba ɗaya ta sanya mana albarka ta sakemu muka fice afalon, kit kit naji tasa key a ƙofarta.
Mun kai minti biyu ahaka, ban motsa ba shima kuma bai motsa ba, still hannuna na cikin nashi, mun kafe wuri ɗaya da ido babu ko kyaftawa, Ni da shi har yanzu cikin shock muke. Dama ance idan kaga kayi kuka to tashin Hankali bai kai ma ƙura bane, shine wannan case ɗin nawa. Hawayen ma kamar kafewa yayi, duk yadda nakeso nayi kukan amma na kasa.
Duk girman kansa, yau sai yaji ƴar yarinyar nan tayi masa wani irin kwarjini ta cika masa ido. Ga laushin hannunta dake fuzgarsa ya kasa taɓuka komai. Lallai Allah yabar masa Hajja, Allah ya ƙara mata nesan kwana, tayi masa abinda iyayensa karan kansu sun kasa yi masa. Ahankali ya juya ya kalleta inda yaga itama shi take kallo da cold expression afuskarta. Kamar eye competition haka suka tsaya suka kafe juna da ido ga hannunsa sakale acikin na juna, idan mutum ya kallesu zai rantse kallon love akeyi, nan kuwa ita kallon tsana da takaici take masa, shine dai kawai yake mata kallon ƙauna.
Kamar an tsikareta kawai ta ƙwace hannunta cikin nashi, tsoronsa da da takeji taji shima ya kau ta kalleshi tace "kana tunanin kaci galaba akaina ko? Kana tunanin ka rabani da masoyiyana kayi nasara akaina ko? Allah ma yasa mafarki kakeyi, wlh wlh kaji rantsuwan musulunci. Abinda matarka ta farko tayi maka nata nafila ne, tun wuri kayi abinda Abby ya faɗa ko kuma ka gwammace kida da rawa" yadda nake ta hayayyaki amma ga mamakina kamar ko ajikinsa, wannan kallon dai dayake jifana dashi bai canza ba, saima wani smirk 😏 danaga yayi yace "uhhh gurl, ban taɓa kuka akan mace ba, amma tundana fara akanki, just get ready to sign till death do us part with me. Ban fara sonki don na rabu dake ba, dan haka duk wani rigima dazakiyi i know the perfect way to handle you sweetheart " hannu nasa na toshe kunnina duka biyu, wannan kalmar so da kuma sweetheart dayake faɗa Kamar ranan mutuwata yake faɗa mun. Na tsaneshi, na tsaneshi da duk wani abinda ke raina. Hawayen dasuke maƙale ɗazu sune suka samu daman saukowa yanzu, wadda ba haka maso ba, banaso yaga gazawata ko kaɗan, badai dani yake wasan ba, zamu zuba dani dashi shege ka fasa.
Signal yayiwa ɗaya daga cikin securities ɗinsa, kan kace me saiga motoci guda biyar sun jera kansu alayi ɗaya. Kallon ta yayi ta tsaya ta cika fammm kamar wacce aka activating da yeast hawaye na zubowa daga idanunta. Murmushi yayi mai ƙayatarwa, batayi aune ba sai kawai ji tayi anyi sama da ita. Duk wani mutsu mutsu datakeyi bai sa ya aje ta ba, buɗe masa mota akayi ya direta aciki sannan ya zagaya shima ya shiga yanajin ransa ƙal. Bai dawo Abuja da farin ciki ba, gashi yanzu zai koma da farin ciki. Yana shiga aka tada motar sai kan hanya.
Baƙin ciki ya haɗu mun goma da ashirin, wato dan ya sameni yar ficika dani shine zaita ɗaukana ahannu kamar jaririya, wani abun ma samun wuri ke kawo shi, badon yaga fuskar ba da bai ɗaukeni ba amma ni nasan yadda zanyi maganinsa. Tsabar yadda naji raina a aharzuke, nama kasa yin hawayen kamar ɗazu, zuciyata tana tafarfasa inaji kamar zan yi bomb. Bakina na turo gaba kamar zai tokare driver dake tuki, ai yanzu na rantse shida ganin hawayena har abada. Ga wani ɗaci ɗaci dake taso min a maƙogwaro na na rabuwa da ƴan gida, kewar Innati da Ameera duk ya mamayeni, ko tunanin Hajja ban yi ba, tsohuwar nan ji nake itama na hadata da jikan nata in zauna a ruwan cikinsu ko zan samu sa'eeda.
Nidai kallon hanya nake yi, yadda mutane suka kafe motocin da ido abin takaici sai kace sunga shugaban ƙasa ne ke wucewa. Bansan lokacin da naja dogon tsaki ba, cikeda takaicin komai ma. ALLAH sarki Ya Isma'il, nakasa mance bawan Allah, yanzu shikenan na rasashi? Wannan tunanin shiyaso kawomin hawaye, amma dana tuna alƙwarin danayiwa kaina sai na cije.
A babban masallacin Niger state muka tsaya saboda lokacin Sallah yayi. Muna fitowa, biyu daga cikin sojojinsa suka take mun baya zuwa gefen mata, duk inda nayi suna biye dani saikace wata prisoner da ba'a so ta gudu, juyowa nayi na hararesu tun daga sama har ƙasa na zuba wani uban ashar, amma mutaninnan ko motsi basuyi ba kamar badasu nakeyi ba. Dan kaina na juya nacigaba da tafiya har wurin alwala, bayan na idar mashiga masallaci amma mutaninnan suna tsaye bakin Kofar shiga sun riƙe bindiga fuskarsu ba wasa.
Dake ƙasaru zanyi kawai na haɗa da la'sar gaba ɗaya nayi. Ina fitowa naga dai suna tsaye kamar ɗazu, ban bi ta kansu ba nayi wucewata suka bini abaya.
Awurin motar naga ya tsaya ya haɗe hannu a kirji ya zuba min wannan shanyayyun idanun nasa kamar mai cutar sikila, harara na watsa masa tundaga nesa har na ƙaraso wurin motar ban jira ya buɗe mun ba na bude da kaina na shiga.
Sai wuraren ƙarfe shida na yamma muka iso cikin garin Baba Tinubu. Baki hanci da ido duk sun kasa rufuwa ina kallon hadewar wannan gari. Ashe haka garin yake, haba ai Dole mutum ya mance da Allah yacigaba da zaluntar mutane, na juya na banka masa harara nacigaba da kallon motoci masu kyau dake shawagi a titin.
Asokoro🌷🌷🌷
Wani tangamemen Mansion 🏛️ ne mai girman gaske mai hawa biyu. Faɗin haɗuwar gidan ma kamar ɓata lokaci ne dan bayyana irin kyawunsa yana buqatar page guda ne. Horn suka fara inda gate ɗin dakansa ya fara wangale kansa batareda wani ya taɓashi ba. Masha Allah tabarakallah.
A hankali suke jerowa cikin gidan ɗaya bayan ɗaya har gaban ƙaton ginin. Bayan duk sun fito, sojoji biyu sukazo gaban motar da MJ yake sannan suka bude kofar sunayi masa sannu da zuwa. Hannu kawai ya ɗaga musu sannan ya zagaya ta ɗayan gefen inda Aneesa take. Tun kafin yasa hannu ya buɗe ta tunkude masa hannunshi tawuce gaba kamar dama can tasan gidan. Sai da tazo gaban entrance door nan ake rigiman, tayi tayi ta buɗe kofa, kofa yace sai ki buɗe mu gani.
Rigiman wannan ƴarinyar yana burgeshi, ta bayanta ya tsaya daidai wurin wani abu ajikin ƙofar kaman scanner ya scanning fuskarsa, sai yasa hannu daidai ƙugunta ya miƙar da ita saitin abun shima ya scanning fuskarta, kamar macece acikin Kofar sai ji tayi Kofar yayi magana yace "new owner approved" baki awangale ta tsaya tana kallo, itafa yanzu ta fara sarewa da lamarin bawan Allahn nan, wato shi ɗagata ko agaban uban waye ba matsalarsa bane. Ai shikenan tasan yadda zatayi tayi maganinsa.
Kiiiii kofar tabude ahankali. Wani sanyi da ƙamshi mai daɗi sune suka fara yi mun sallama. Kasa shiga nayi saboda abinda idonsa ya gane mun, ba falo bane, wani wurine kamar corridor, abango Kuma water fountain ne inda ruwan ke saukowa tundaga sama har ƙasa yana shiga wani ɗan kurmi Karami. Cikin bangon kuma kamar da glass akayi, kifaye kala kala masu kyau suna yawo acikin ruwan. Na ma mance cewa da kwai mutum abayana sai ji nayi yace "welcome home Mrs Mujahid, muje ciki da sauran kallo ai, kuma duk nakine" da sauri na juya bayana ina kallon da, tsayinsa daidai nawa, kamar fuskarmu zata haɗe wuri guda. Saurin ja da baya nayi ina jifansa da harara naja tsaki nabi wani ɗan hanya wadda nake tunanin nanne zai sadani da cikin gidan.
Nan ma Wani kallon ne sabo, kamar dai corridor dinnan, kusan rabin bangon falon glass ne wadda a cikinta akwai ruwa da kifaye masu kyau. Sama na kalla inda naga ceiling din samansa wani ƙaramin swimming pool ne, reflection din swimming pool din afalon sai yayi kamar muna ƙasan ruwane. Nidai Bature bazai kasheni da ƙaryan kire kire ba, yanzu fisabilillah kalli gidanmu na Adamawa, ahaka ma gara namu akan na wasu, muntane na kwana su tashi cikin yunwa amma ga wasu anan ji suke kamar duniyan ma nasu ne gaba daya.
Kar yaga kamar nidin ƴar ƙauyece kawai na saita kaina, na juya na kalli dogon benen da zai sadaka da second floor inda gaba ɗaya stairs din na glass ne ga wasu fitillu masu kyau suna haska benen. Ina tafiya inaji yadda idanunsa ke yawo ajikina musamman mazaunaina amma na matse na cigaba da tafiya har na haye sama. Jerin ƙofofi ne guda uku nagani, na tsakiyan zuciya ta bani na shiga. Da sallama na murɗa ƙofan na shiga, wani sanyi mai daɗi ne ya ratsani ga ƙamshi. Makeken bedroom ne dayaji furnitures na alfarma kamar na sarki. Komai na ɗakin shiny dark purple ne daga labulen har furnitures din. Ga wani makeken King sized bed irin mai circle dinnan gwanin sha'awa. Wannan dai bai mun kamada da kamar an taɓa anfani da Dakin ba, dan komai sabo ne bazaka ce an taɓa wani abu daga ciki ba. Saida na rufe Kofar sannan na ƙarasa shigowa ciki, mayafin kaina na warware na kunce ɗankwalina na zubar akan gado. Kofar danake tunanin nanne toilet na wuce na shiga.
Babban closet ne girma amma babu komai aciki, ga wurin takalma daban gana jewelries gakuma na kaya daban shima. Can gefe ne na hango wani kofa daban inda nafi tunanin nanne toilet. Addu'a a bakina na bude nashiga, Masha Allah komai yayi. Ga wani ƙatoton kwamin ruwa a tsakiyan toilet ɗin irin me cycle, nan kuma ta gaba wani tangamemen madubi ne da washing hand basin. Ga wardrobe na glass a gefenshi inda naga towels ne acikin kaloli daban-daban, ga kuma inda aka kewaye da glass wurin wanka kenan, yana dauke da different types of shower head, akwai wanda idan aka kunna ruwa kaɗan yake fitowa, akwai kuma wadda idan aka kunna ruwa normal ne ke fitowa sai kuma wadda zakaji ruwa shaaaa kamar ruwan sama yana fitowa, ga gefen ruwan sanyi gana zafi. Bakina ahangame duk saida nabi kowani lungu da sako na cikin bathroom ɗin kafin na tube kayana yarage dagamu sai pant da bra. Wardrobe ɗin da aka tanada na shampoo da sabulan wanka na buɗe na ciro wadda zan yi amfani dasu. Saidai na tsaya ruwa ya taru acikin bathtub din sannan na jefa shower bomb aciki, daya narke na cire sauran, shower gel da soft sponge na ɗauko sannan na shige cikin ruwan. Ajiyar zuciya na sauke, na kwantar da kaina ajikin tub din warm water dinnan yana shiga lungu da saƙo na jikina. Na dau lokaci dayawa sannan na fara cuda jikina da lallausan soson wanka ga sabulu mai ƙamshi.
Bayan nayi wanka na wanke kaina na dauro alwala, sannan na cire ɗaya daga cikin towels dake wardrobe dinnan. Iron towel mai rigan nanne, igiyansa ta gefe yake na daura, na dau karami na daura akai dan na samu ya tsane mun danshin ruwa dake kaina. Saida na tabbata na tsane jikina sannan na fito daga toilet ɗin da kayana dana cire ahannu.
Leda na hango saman gadon, ko ba'a faɗa mun ba nasan wadda ya aje shi. Harara na jefawa ledan, dagashi har mai shi suje su karata can bana buqatarsu. Sauri sauri na maida kayan jikina kar lokacin Sallah ya kure. Da mayafina nayi rolling na shinfida ɗankwalina aƙasan lallausan carpet mai gashi dake tsakar ɗakin na tada Sallah. Ina cikin sallah naji ya buɗe kofa, bai shigo ba ya tsaya abakin Kofar saida ya ƙare mun kallo son ransa sannan yaja kofar ahankali yatafi. Bayan na idar ina lazumi, naji irin disco da cikina keyi, tun safe banci abinci ba kamar wacce ke azumi. Kallon ledan dake kan gado nayi, ina hango takeaway dake ciki, dafe cikina nayi da ƙarfi ina haɗiye yawu, wani abu azuciyata na cewa " Aneesa babu kyau fushi da abinci" wani abu kuma na cewa " karfa kici, bakisan meyasa miki aciki ba", na kasa tantance abunda yakamata nayi, daga ƙarshe dai na making up mind Dina zanci abincin idan ma guba yasa aciki, gara na ci na mutu kozan huta da ganin mummunan fuskarsa😂😂. Warware mayafina nayi da rarrafo wurin abincin na dau ledan. Budewa nayi naga takeaway guda biyu ne sai strawberry milkshake da ruwan Cway aciki. Takeaway na farko stir fried pasta ne da grilled fish ɗayan kuma fruit salad ne. Pasta ɗin nafara ci, tunda nayi cokali ɗaya naji wani mugun daɗi ya mareni akumatu bansan lokacin dana fara hambula abuna ba. Tundana kafe kai cikin takeaway dinnan ban ɗago ba saida naga ƙarshen taliyar da kifin,sannan na balle murfin goran ruwa na kafa abakina. Saida najini saƙat sannan nayi gyatsa nayi hamdala. Dagowa dazanyi na ga mutum tsaye abakin ƙofa ya kalmasa hannu a kirji yana kallona cikeda nishaɗi afuskarsa. Kenan duk loman dana dinga yi a idonsa, amma mutuminnan ma ya mugun sameni. Cikeda borin kunya nayi ball da takeaway ɗin tareda strawberry milkshake daban sha ba. Miƙewa nayi na turo baki gaba ina hararansa kamar idona zai faɗi kasa. Murmushinsa mai bani haushi naga yayi ya ƙarasa shigowa dakin, gani nayi ya nufoni, da sauri nafara ja baya yana ƙara matsowa. Saida nakai bango naji dai babu inda zan iya zuwa kuma gashi faffadan kirjin nan nasa mai kama da flat screen TV yayi mun rumfa. Sosai ya matsoni sosai har ina iya jiyo saukan numfashinsa atsakiyar kaina. Ƙoƙari nake wurin hawa da saukan numfashi na saboda idan ba haka nayi ba, to duk hawan da ƙirjina yayi sai ya taɓa nasa kirjin. Kamar hakan baiyi masa ba, saida ya kara kusantoni da kyau wannan karon kam ƙirjinsa male male yake manne da ƙirjina. Wani irin nafara ji a jikina saboda yadda kirjin nasa ke gugan nawa. Aharzuke na buɗe baki zanyi magana naji ya sanya yatsansa manuni ya toshe mun baki dashi yace "shushhhhhh, bakinki yacika Surutu, ke baki gajiya ne"? Haka kawai na tsinci kaina dayin shiru kamar yadda ya umurceni. Handkerchief naga ya ciro daga aljihun wandonsa ya nufa bakina dashi, da sauri na juya kaina gefe. Banyi aune ba sai jin wani abu mai ɗumi a Kamatu na, pecking ɗina wannan mutumin yayi, mashiga uku ji Aneesatu takwarar Hajja, yagama dami wlh. Hawaye mai zafi nashi ya gangaro mun duk yadda nayi na taresu, juyowa