Rayuwar Aneesa complete Hausa Novels pdf Reemah.txt

Author :  Reemah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 24

39K to 42K   out of 70.4K words

ba. Suma sun sha mamakin ganinsa cikin wannan yanayi, shida Yakamata ace angansa cikin farin ciki amma kuma sai ɓacin rai yadawo dashi. Masu son jin kwakwaf suka shiga part din na Hajja dan jin meyasa Ango yadawo da wannan yanayin.

Ko sallama baiyi ba ya wuce zuwa ɗakin Innati inda anan akewa Aneesa shiri. Tariga tagama shirinta tsaf cikin atamfa mai kyan gaske tasha ɗauri Masha Allah. Sai ganin mutum kawai sukayi ya diro cikin daƙin rai aɓace. Raihanah dake yiwa Aneesa hoto tana ganin Isma'il a wannan yanayin tasan cewa burinta ya cika, amma sai ya bata tausayi. Hannun Aneesa Isma'il ya damke yace "taho mutafi" kallonsa tayi da mamaki, wai dama haka akeyi, ita ta ɗauka iyaye ne da ƙawaye zasu kaita Dakin mijinta, to meyasa nata zai zama different. Yadda taga ransa aɓace ba kamar yadda ta saba ganin shi ba shiyasata jin tsoro dan haka ta mike ta gyara mayafinta tafara binsa abaya. Su Raihanah da wata ƙawar Aneesa mai suna Anna Adam suka bi bayansu, yau ga wani abu suna kallo awurin Isma'il. Meta faru?


Suna fitowa fakon Hajja saiga Abby ma da mutanensa su Sultan sun shigo, yadda Abby yaga ran Isma'il aɓace ga kuma Aneesa daya riƙe hannunta yana janta kamar kayan wanki, Hajja ma ta sauko dan Abby ya kirata, gasu Innati duk suna falon. Turus yaja ya tsaya yace "Abby, yau duk abinda zai faru saidai ya faru. He's divorcing my wife right now" su Mamy duk kansu ya kulle, me ake magana akaine wai. Hajja tace "kai Isma'il bana son rashin kunya, meye haka kanata jan yarinya. Ai daga ɗaurin auren bazama kabari akai maka itaba saidai kajata kutafi? Zai yi magana sukaji sallaman MJ, Yana shigowa suka haɗa ido da Aneesa har saida yaji gabanta yayi wani irin mummunan faɗuwa, idonsa ya juya tamkar garwashin wuta, fuskarsa har ja ja yayi.

Raihanah na ganin yanayin Babban Yaya, har saida taji wani mugun fitsari yana neman ƙwato mata awando da sauri ta matse ƙafafunta tana haɗiye yawu ido yayi zuru zuru. Abby ya wurga masa harara tajuya ya kalli sauran mutanen falo wadda bakine yace "dan Allah inaso abamu space zamyi magana da iyalai na" batareda musu ba kuwa kowa ya fita sai ya rage mutanin gidanne kawai.

Zama sukayi gaba dayansu, Abby yafara magana " wani babban jarabawa ya aiko mana sai dai muce Allah yabamu ikon cinye ta..." Gaba ɗaya abinda yafaru masallaci ya kwashe ya faɗa musu. Isma'il dake zaune agefen Mamy sai jifan MJ yake da mummunan kallo, gaba ɗayansu suka sa salati suna jimamin wannan al'amari. Mamy cikin fushi tace " Ni dama nasan hakan zai faru. MUJAHID kabani kunya ban taɓa expecting haka daga gare ka ba. Yanzu ka zaɓi ka cutar da ɗan uwanka saboda son zuciya, tsakani da Allah ka kyauta kenan"? Kansa na ƙasa ya kasa dagowa, duk abinda zai faɗa ba lallai su yarda dashi ba, amma shikam duk abinda zai faru saidai ya faru amma bazai saketa ba. Juyin duniyannan akayi da MJ ya saketa amma fafir yaƙi motsawa kamar bashi awurin. Hajja da Innati sun kasa magana, to me zasuce, MJ da Isma'il duk nasune, idan akace Mujahid ya saketa kuma bayan yana sonta ai ba'ayi masa adalci ba, shi kuma Isma'il idan akace ya haqura bazai ji daɗi ba, kar hakan kuma ya kawo gaba tsakaninsu.


Tsananin tashin hankali Raihanah tashiga, yadda ta zaci abun zai zo da sauƙi ashe ba haka bane, Babban Yaya ya bata tausayi. Tabbas yanason Aneesa da ba haka ba da tuni ya saketa kamar yadda Mamy da Abby suka bashi umurni.


Mujahid ne ya fara lura da yadda Aneesa ta kafe wuri guda kamar mutum mutumi, sosai ya lura da yadda take zaune bata motsi. Hajja ce taɗan taɓa kafadarta sai ji kawai sukayi timmm ta zube aƙasan tiles ɗin falon. Isma'il ne ya fara miƙewa daga inda yake zaune sai MJ shima ya miƙe aguje duk sukayi kan Aneesa arude. MJ ne ya fara kaiwa wurinta kafin Isma'il, bai damu dasu Abby da kowa dake zaune awurin ba umm ya sungumeta yayi Dakin Hajja da ita, Isma'il yabi bayansa. Suna shiga ɗakin ya kwantar da ita akan gado ya zauna agefen gadon ya kamo hannunta cikeda kulawa yafara murzawa yana kiran sunanta ahankali, Isma'il dake tsaye abayansa kamar yayi bomb kawai ya juya ya fice aharzuke. Su Hajja dasu Mamy suka shigo Dakin suma hankalinsu yayi matuƙar tashi, Sultan ne ya dubata yaga ai komai normal me, kawai shock ne data shiga. MJ ya kasa sukuni sai kai koma yake abayansu Innati dasuka rufe Aneesa. Wani wawan kallo Abby ya watsa masa yace "kagani ko? Dama abinda kakeso kenan. Toh ai gashinan, idan kanaso ka rasata shima Isma'il ɗin ya rasata ai gatanan sai kuyita yi" bai jira cewarsa ba ya fita adakin. Mamy ma saida tayi nata bombomin duk abanza don MJ ko ƙala baice musu ba, kamar da dutse suke magana. Wannan attitude ɗin dayake nunawa ba ƙaramin ɓata musu rai yake yi ba. Haka dai suka fita adakin don Sultan yace tana buqatar hutu ne ba hayaniya ba.

Daga Hajja sai Raihanah dakuma Innati sai MJ daya ƙi fita adakin daka kalleshi saiya baka tausayi. Can ta fara motsi kamar zata farka da sauri ya haye saman gadon ya zauna kusada ita ya zubawa kyakyyawar fuskarta ido.


A hankali nake buɗe idona danaji sunyi mun wani irin nauyi, ga kaina dake sarawa dib dib dib, dana tuno abinda yasani cikin wannan halin naji kuka mai ƙarfin gaske ya kwace mun. Buɗe ido nayi na saukeshi kan fuskarsa yana kallona da wani abu a idanunsa kamar damuwa, sosai nashiga yin kuka harda jijjiga, Innati ganin haka itama ta hayo kan gadon tafara rarrashina, nikuma kamar ance naƙara sautin kukan, haka naketayi. Ban san lokacin daya jawoni ƙirjinsa ba nidai kawai jina nayi ajikin mutum ya rungumeni tsamm yana shafa gadon bayana. Aharzuke na fara kiciniyar kwatan kaina amma yaƙi bani daman yin haka. Hajja dake tsaye agefenmu tace masa ya sakeni ya fice adakin tana so tayi mun magana. Badon yaso ba haka ya sakeni yanata ƙare mun kallo har ya kai wurin ƙofa, ayadda nakejin zuciyata tana hauhawa tabbas a wannan lokacin da za'a bani wuka da babu abinda zai hana ban daɓa masa shi a kahon zuciyarsa ba, tsanansa ya ƙara huruwa sosai azuciyata.

Raihanah tabi bayansa da gudu tana fashewa da kuka, tabbas dolene taje ta faɗa abinda tayi kar ana ganin laifin ɗan uwanta. Ita ba haka taso al'amarin ya kasance ba amma tabbas ta tafka kuskure. Tana fita aɗakin taji anjawo hannunta zuwa wani gefe can kamar lungu. Mustapha ne yajawota, shima idanunsa sunyi jaaa alamar dai yasha kuka. Ta tsorata da yanayinsa badai yasan itace tayi wannan abun ba. Ƙasa ƙasa ya fara magana saboda kar kowa yajisu yace "why Reena? Meyasa kikayiwa Ya Isma'il haka? Kina tunanin babu wadda yaganki Right? To ni dinnan I saw you alokacin dakika canza result ɗin Ya Isma'il da kuma sunansa" itama ƙasa ƙasan tafara yi masa magana tace "plsss Mustapha karka faɗawa kowa, yanzu kazo ka rakani zanje wurin Ya MJ na faɗa masa cewa nice nayi wannan abun" a tsorace Mustapha yace " kaii, ke bakisan halinsa bane. Ai gara mu fadawa Abby than mu faɗawa Babban Yaya, a'a gaskiya kar muje" still bata yarda ba tace " nidai shi zan faɗa mawa. Ko ma mene zai faru saidai ya faru" tana gama faɗin haka tajuya tawuce, shima yabita abaya yana kiran sunanta. Basu tsaya ako ina ba sai gaban part ɗin MJ. Knocking tayi aƙofa, kusan mintina biyu amma shiru ba'a buɗe ba. Can dai suka ƙara kwankwasa kofar, saida yadau ƴan lokuta sannan ya buɗe kofar. Dagashi sai wandon getzner dinsa da farar singlet wadda ya ƙara fidda hasken fatarsa mai kyau da sheƙi. Gashin kansa kuma ya kunceshi ya barbaza a gefe da gefen kansa kamar mace. Fuskarsa dake dauke da cold expression yace "mekuke so" da gudu Raihanah ta ƙarasa jikinsa ta rungumeshi tana ƙara fashewa da wani kukan tana cewa "Babban Yaya I'm sorry, nayi maka laifi, Please ka yafemun" duk bai gane metake cewa ba, kuma bai rungumeta ba, shidai yana tsaye ne kamar dutse. Daya gaji da kukanta ya ɗago haɓarta dayayi gaja gaja da hawaye yace "it's alright, menene ya faru. Akwai abinda kika mun ne wadda ban sani ba" cikin kuka tace "nice na canza result dinnan na kuma canza sunan dake ciki" zaro ido waje yayi ya jawota da Mustapha cikin falonsa ya ƙulle Kofa kar wani yaji. Zaunar da ita yayi saman cushion ɗinsa yace "Reena why? Meyasa kika yi haka" share hawayenta tayi tace "saboda nasan kanasonta, that's why I wanted to help you" iska ya furzar daga bakinsa ya share mata hawaye yace "shikenan, kukan ya isa haka, but what you did was not right ko kaɗan, ya kike tunanin idan Abby yaji wannan maganan ai shima ransa bazai yi daɗi ba talkmore of Isma'il. Kinaso ki fice masa arai ko"? Da sauri ta girgiza kai tace "a'a Ya Mujahid, pls ka taimaka kar ka saki Aneesa, wlh na tabbata itama tana sonka. Saidai kawai ita har yanzu bata gane hakan ba" wannan furucin nata yayi masa daɗi, kenan ƴarinyar tana sonsa? To meyasa hakan bai nuna a idanunta ba, sai kuma ya tuna wannan unusual look ɗin data bashi alokacin da take hannun Isma'il daya saving ɗinta a swimming pool. Baisan lokacin da murmushi ya ƙubuce masa ba, dimples ɗinsa masu kyau suka lotsa ciki. Kallonsa galala Mustapha da Raihanah suka tsaya yi, to me kuma yasashi dariya. Gimtse fuskarsa yayi yace "yanzu dai, as your punishment Reena, keda kika haɗa auren ke zaki sa tasoni, and only if you promise me that, will I decide wether not to tell Abby" zaro ido waje tayi, shi Babban Yaya komai sai anyi masa ne? Soyayyarma itace zata sa Aneesa tayi masa? Cabb ɗin jan jan. Kallon Mustapha yayi yace "partner in crime, nasan dakai aka haɗa so you're also part of the punishment. Dariya sukayi gaba ɗaya suka rungume ɗan uwannasu. Tunani yafara ta yadda zai iya shawo kan iyayensa su haqura subar masa ita a matsayin matarsa.


Magana sosai Hajja tayiwa Aneesa, ta kuma sanar da ita cewa wannan shine qaddararta, dama Allah ya riga ya zana tun fil azal cewa Mujahid shine mijinta uban ƴaƴanta, don haka tayi haquri kawai karta yarda tayi abun dazai sa Abby ya tunzura yace lallai sai MJ ya saketa.


Duk wannan maganar da Hajja keyi, tamkar yana shiga ta wannan kunninne yana fita ta ɗayan, bata hangar zaman aure da wannan mutumin koda nan kusa ne, kwata kwata babu comparison tsakaninsu, personality ɗinsu Sam bai matching ba. Shi yanada rashin fara'a, kuma baya sakewa da mutane. Ba kamar Ya Isma'il wadda shi sam opposite ɗin dan uwansa yake, yanada fara'a yanada raha kuma yasan ta yadda zai bi da ita idan tana fushi dashi. Shiko wannan idan tayi fushi dashi ai saidai ya rufeta da dukan tsiya dama kuma halinsa ne. Suna cikin magana Baba Larai tashigo akan Aneesa tayi baƙo yana falon Hajja.


Kamar zanyi bullet, waye kuma yazo zai ƙara mun baƙin cikin danake ciki. Innati ce ta gyara mata ɗaurin ɗankwalinta taɗan gyara mata fuskarta yadda baza'a gane cewa tayi kuka ba, sannan ta ɗora mata mayafinta suka fito falonn tare. Abba ne zaune akan ɗaya daga cikin royal cushions din falon Hajja sai faman kalle kalle yake yana girgiza kai, yana ayyana irin kuɗi da aka kashe a wannan gida tun daga bakin gate. Idonsa ne ya sauka kan innati wadda take sanye da danƙareriyar less purple colour ɗinkin bubu wadda ya zauna mata ɗass ajiki, ga ƙunshinta ja ahannu yayi kyau sosai. Ƴar light makeup ne afuskarta amma ta haɗu ba wasa. Ya ma mance da abinda yakawosu gidan saboda kallon Innati, take yaji wani tsananin ƙaunarta ya ɗarsu azuciyarsa.

Tundana hango Abba zaune Afalon naji baƙin cikin dake zuciyata ta ninku. To ba dai yabada aurena ba, mekuma ya kawo shi wannan gidan. Kokuma yazo ne dan ya ƙara mun baƙin cikin danake ciki. Zama nayi a ƙasan cushion ɗin dake facing dinshi, kaina aƙasa na gaida shi ƙasa ƙasa kamar ansani dole. Innati ma ta gaida shi fuskarta babu yabo ba fallasa. Shi kuwa sai murmushi yake kamar zautacce yace "Masha Allah uwargida agidan Zaidun Goggo, Allah ya ƙara miki nesan kwana muyi rayuwa cikin soyayya". Kamar nasa hannu akai nayi ihu, badon Innati ta dafe Ni ba, da babu abinda zai hana na miƙe na koma ɗaki, dama kuma ga kaina dake kan ciwo har yanzu. Ganin Innati ta share shi kamar bada ita yayi ba, yasa ya gyara zamansa ya fuskance ni yafara magana " Aneesatu ƴar Baba, nasan kinada hankali, kuma kinada sanin Yakamata. Kinsan cewa babu abinda zai sameka a wannan rayuwar face abinda Allah ya qaddara maka. Kuma babu abinda zaka samu face Allah yayi wannan abun fa naka ne. Nasan tun kafin nazo anriga an sanar dake abinda ya faru a masallaci, dan haka ba wani doguwar magana zanyi ba. Inaso kisani, ni tun farkon ranar da aka zo neman aurenki, shi Mujahid shine dai zuciyata tayi na'am dashi, kuma tun a ranar shi naba aurenki. Kunga ko Allah ma yanaso shine ya zama angonki, shiyasa yabisu aranan da zasu zo Adamawa. Kiyi haquri, kiyi haquri, ki zauna da mijinki kiyi masa biyayya iya ƙoƙarinki. Kar ki taɓa muzguna masa dan kawai ba shine kika yi niyyar aure ba. Allah yasa mudace, kuma Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina sannan yabaku ƴaƴa na gari", kuka ne ya ci ƙarfina, sosai nake kuka Innati kuma tana shafa bayana alamar nayi shiru, nikuma kamar tana ƙara tunzurani haka na ƙara ɓare baki ina kuka na tashi da gudu na koma sama ɗakin Hajja.


Duk yadda za'ayi baƙi da suka zo biki kar su gane meke faruwa amma hakan ya faskara. Dake news kamar wild fire yake spreading kafin kasani ɗaɗɗaya ne acikin gidan Jenar basusan meke faruwa ba. Within short period of time aka fara watsewa, toh gaba ɗaya hankalin mutanen gidan babu shi akan baƙin da aka gayyato. Ƴan son jin kwa kwaf ne kawai suka rage suka ki tafiya.
Da daddare ko ina yayi tsit kamar ba gidan biki ba, kowa ya watse harda ƴan gulma dasuka ce su babu inda zasu.


Tunda rana da Isma'il ya fice agidan bai kuma dawowa ba, gidansa ma babu shi. Da Abby ya bincika kuma aka ce masa yakoma can wurin aikinsa a Port Harcout. Aranan kowa ya kwana cikin baƙin ciki, ba kamar Raihanah dake jin ranta sakai ba. Tunda de aikin gama ya gama ai lokaci kaɗan komai zai wuce.

Aɓangaren Ango da amarya kuma, shi MJ ya kwanta ya rungume filo akirjinsa yana tunanin ko wani hali amaryarsa take ciki. On the other hand kuma ga Mamy da Abby dake fushi dashi, ko ɗazu ma kin magana dashi sukayi, ga kuma Isma'il, bayaso relationship ɗinsu ya ɓaci saboda wannan abun. Juyi ya ƙarayi to the other side ya zubawa bed side lamp ido.

Kasa bacci nayi, abubuwa duk sun cunƙushe mun ma rasa yadda zanyi na warware su. Idan na tuno da fuskarsa sai naji wani baƙin ciki ya tokareni a maƙogwaro na. Wayata dake gefena na ɗauka na buɗe hoton Ya Isma'il lokacin dayana filin yaƙi da kakin sojoji ajikinsa. Dake Airforce ne, a background jirage ne irin na sojoji masu yawan gaske. Yayi kyau sosai, hoton na kafawa ido inaji kamar na shiga na rungumeshi konaji sauƙin wannan takaicin. Bansan iya lokacin dana ɗauka ahaka ba sai kawai duba agogo nayi naga ƙarfe 2:45AM, gashi idona garau yake babu alamun bacci acikinta, mikewa nayi na shiga toilet na dauro alwala sannan na fito ma yada Sallah. Bansan iya raka'o'in danayi ba amma har tafin ƙafafuna radadi suke yi mun. A sujjada kuwa kuka mai kyan gaske nakeyi ina kaiwa Allah ƙaran abubuwan da akayi mun, ban tashi ba saida naji hankalina ya ɗan kwanta, har sai lokacin wuraren 4:56AM babu baccin, dan haka na dauki Qur'an nafara tilawa har akayi sallan subh. Ina idarwa kuwa na ɓingire da bacci awurin.

Gudu nake cikin wani lambu mai kyau ina sanye da white floral gown gashin kaina dake sake agadon bayana iska sai ƙadamun ita yake. Daidai ƙarshen gonan ina gudu ina kallon bayana kawai naji nayi karo da mutum. Juyawa nayi da sauri ina haki, sanye yake cikin farin jeans da farin T-shirt hannunsa na sanye take da agogon Rolex mai kyau ga wani irin sassayan ƙamshin dake fita ajikinsa. A hankali na ɗago ina kallon fuskarsa, ɗauke take da kayataccen murmushi inda dimples ɗinsa suka ƙara yi masa kyau. Nima murmushin nake mayar masa. Hannunsa yasa aƙuguna ya jawoni jikinsa inda yake fuskantata sosai. Nikuma hannu nasa na sakalo bayan ƙeyarsa muna facing juna, rufe idona nayi ina kusanto bakina zuwa nashi, tun kan nakai shi ya rigani ta hanyar maida hannunsa daya bayan kaina ya haɗe bakinmu wuri ɗaya. Deep emotional kiss yafara bani Yana yawo da harshensa a lungun bakina,nikuma ina yawo da yatsuna cikin tulin gashin kansa...

Kamar an taɓani haka naji na miƙe wuffff ina dafe ƙirjina haɗi da salati abakina. Zufa duk ya wanke mun fuskana da jikina. Wannan wani irin mafarkine, kuma in rasa da wa zanyi saida wadda nafijin tsanansa azuciyata. Allah ya isa ban yafe ba wlh, Hannu nasa nafara goge lips ɗina kamar azahiri ya sumbace ni. Inayi inajin hawaye sharrr afuskata.

🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷


Reemah ✍️


PG 66_70


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Da safe ƙarfe bakwai inata jin hayaniya a falo. Da ƙyar na miƙe nashiga toilet nayi wanka sannan nafito na shirya cikin riga da skirt wrapper na atamfa, ko powder ban shafa ba kawai na yi simple ɗauri nafito. Turus na tsaya ina kallon mutanin dake falo, haba ashe shiyasa

14 / 24