Author : Reemah Category : Romantic Hausa Novels
mata bull dog dinnan. Kai amma Mujahid dinnan professor ne a ɓangaren mugunta🙄🙄
Kusan minti biyu banji mutumin ya motsa ba, har na karashi kuka na banji yace na tashi ba. Ahankali na ɗaga kaina na zuba masa ido kamar wani naga sabon halitta. Lallai wannan gidan ƴan kyau ne. Shima sanye yake cikin kakin sojoji, kuma yana kamada Abby. Kamar yadda nake kallonsa shima haka yake kallona. Tamau naga ya haɗe fuskarsa ya fara kokarin mikewa. Da sauri na tashi daga jikinsa ina jan hanci nace "dan Allah kayi haquri,wani karene yabini" gyaɗa kai kawai yayi yace "ki kula" sannan ya fice a falon yana gyara kakinsa wadda ya matuqar amsar jikinsa. Murmushi nayi, wannan bawan Allahn ya haɗu. Gashi ba baƙi ba kuma ba fari ba, ƙirar jikinsa ya nuna cewa shi ɗin yana ɗaga karfe kamar dai wancan arrogant man ɗin. Sai yanzu ma nafara tuno wani abu, karennan saikace an aikoshi. To idan aikoshi akayi wanene wannan mugun da baya ƙaunata, wani zuciyar yace "mugun nanne mana" haba aiko ba'a faɗa mun ba nasan babu mai nufina da Sharhi sai shi. Yanzu inda karennan ya illata ni fa🥹
Muryan Mami naji abayana tace " takwarar Innati fatan dai babu abinda yasameki ko"? Juyowa nayi ina kallon ta, zaune take a cushion ga takarda ahannunta tana dubawa. Wani irin kunya naji ya kamani, yanzu haka ta kamani ina kalle mata yaro daga sama har ƙasa. Ban iya cewa uffam ba na juya da sauri na buɗe ƙofan nafito, cin karo nayi da faffaɗan ƙirjinsa yana tsaye agabana ya cusa hannayensa a cikin wandonsa. A mugun hankali na ɗaga ido na zuba masa kamar yadda shima ya zuba mun tasa. Ni kallon tsoro nakeyi masa shi kuma yana kallon a da tsantsar tsana wadda hakan ya gaza ɓoyuwa afuskarsa. Hannu yasa ya hanmaɗeni gefe yayi wucewarsa. Bayansa nabi da kallo kawai na girgiza kai, Allah dai yaso mutum babu abinda yasameni dana kai ƙara wurin Hajja.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
"Innati na shiga uku, yau sati biyu kenan banga period ɗina ba. Dan Allah babu komai ko"? Ameera ta tambayi Innati tanaji zuciyarta na tsinkewa. Kwana biyun nan ko Innati ta lura da yawan baccinta, kuma ga yawan kasala datake fama dashi, take zuciyar Innati yayi wani irin wawan bugu. Ya Allah yasa ba abinda take tunani bane. Ta ina zata fara inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun wannan shine abinda taketa furta wa.
Ƙoƙarin kwantar da hankalinta tayi dan itama Ameeran ta kwantar da nata, amma tabbas sai tayi da gaske kar abinda take zargi ya zamo gasky. Idan ko hakan ya tabbata ba ƙaramin cutar su wannan mutanin sukayi ba.
Ameera dai har yanzu ƙirjinta sai bugawa yake, ɓakonta bai taɓa tsallake kwanakinsa ba sai wannan karon. Mutaninnan sun bar mata tabon da harta koma ga Allah bazai taɓa gogewa ba, kullum saita kai ƙaransu wurin Allah, idan Innati tayi bacci kullum kwana take cikin kuka da mafarke mafarke.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Haka rayuwa ta cigaba da gudana agidan Goggo. Yau suci gobe kuma sai yadda hali yayi. Abun Abba kuwa tuni mahaifinta yabawa wani dama ya kawo sadaki. Ran Abba ba daɗi haka yake kallo budurwarsa zata auri wani duk asanadiyyar Hussaina.
Ko ina na gidan duku duku babu arzikin gyara. Ga kwanuka dake birjik atsakar gida wadda sukayi amfani dashi babu mai gyara musu gidan. Haka Goggo wani rana zata zauna tayita tunanin Innati tace Allah sarki da Hussaina na nan data gyara gidannan fes fes. Ai bakiga komai ba. Abba ko ba ƙaramin kewar ta yake ba, kullum fama yake da sha'awaratarsa amma kuma batanan. Duk saiyaji inama ace zata dawo, daya gyara tsakaninsu sunyi rayuwarsu cikin soyayya, dan wani irin soyayyar ta ne ya bijiro masa yanaji kamar zai fasa masa zuciya.
Pls like
And comment 🙏🙏
🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷
REEMAH ✍️
PG 36_40
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Kullum addu'a nake Allah ya haɗani da wannan kyakkyawan yaron Mamin. Ko hira muke da Raihanah sai nayita tambayarta ko yana nan, tun bata gane ba har tazo ta gane tana mun tsiya. Niko wani irin yanayi nakeji, wannan ake kira da soyayya? Daga ganin mutum shikenan sai na faɗa masa. Har sunansa saida ta faɗa mun, Ya Ismail. Kullum ina hanyan zuwa part ɗin Mami wai ko dan zan ganshi, amma abun haushin saidai nahaɗu da mutumin dabaya ƙaunata arayuwan nan. To wai shi baya aiki ne, kullum yana gida saikace namace. Kuma har yanzu idan na ganshi saina gaidashi amma baya amsawa,niko saikace mara zuciya bana fasa gaidashi aduk lokacin dana haɗu dashi.
Yau ina taya Baba Larai aiki a kitchen ɗin Hajja tasa naje babban lambun kayan miya a bayan part ɗin Hajja na tsinko mata ganyen ugu da alayyaho. Ina tafiya ina waka na shigo lambun. Har na fara tsinkawa naji mutum na waƙa abayana.
"As I dey look your eyes,
Shining like brightened star
Baby girl I don't mind
You go be my wife
When you down you can call on me
I'll be at your feet
Even if you slump
I will draw you up
Cos when I see you bumbum
I no dey hear caution
You sweet like Panadol
You dey cure my boredom
I say when I see your bumbum
Bumbumbum....."
Da sauri na juya dan ganin wanene wannan, ƙirjina ne ya buga ganin Amin tsaye abayana sai ƙare mun kallo yake yana lashe labbansa. Sosai naji raina ya ɓaci take zuciyata tayi baƙi ƙirin. Wannan iskancin nasa har kan masu aiki? Ehh lallai Raihanah tayi gasky da tace nayi taka tsantsan dashi.
Shiko Amin wani shu'umin murmushi yayi yace "haba baby gurl, why do you look scared. Nifa masoyinki ne. Zan baki duk wani jin daɗi na rayuwa dakike buqata, zan kashe miki kuɗi, zan kaiki ƙasashen waje" yacigaba da jero mata karyayyaki yana ƙara kusantota.
Sosai raina ya ɓaci, gashi lambun yayi nisa da cikin gida balle ko nayi ihu ajiyoni. Kwandon dake hannuna na ɗaga na nuna masa nace "wlh ko ka barni kona ƙwala maka wannan kwandon agoshi" ganin dai ba fasawa zaiyi ba nafara kiran sunayen Allah azuciyata. Sosai yake matsoni ina komawa baya harya kaini jikin bango, fuskata har wani ja ja yayi saboda irin haushin da nakeji. Hannu nasa na tunƙudeshi gefe da gudu nabar wurin hatta kwandon ma awurin na barshi. Sosai nake gudu bana kallon bayana saiji nake kamar yana bina.
Baiso ta tsere masa ba, wannan cute lips dinnata yaso ya ɗanɗana. Da alama dai yarinyar akwai wiyan sha'ani. Wani smirk yayi yace "you've escaped honey, not another day cos ain't giving you a chance to do that" hannunsa yasa saman wandonsa, tsabar jaraba har tayi wani ƙal🙈. Kwandon data bari ya ɗauko yayi part ɗin Hajja dashi.
Ina shigowa kitchen na ƙulle Kofar gam, Baba Larai daketa zaman jirana ta kalleni tace takwarar Hajja ina ganyen"? Saida na saita numfashina sannan na dago na kalleta, itama ni take kallo. To me zance mata, su yaran manya iyayensu na bala'in ji dasu, idan nace ga abinda Amin yayi mun anya baza'a hukunta niba. Wani ƙarya na ƙaƙaro nace "Baba, wani ƙaton maciji nagani rataye a ganyen ugun, shine naji tsoro na gudu, harta kwandon ma awurin nabarshi" da mamaki Baba Larai ke kallona alamar dai bata yarda ba, nace "Allah Baba, in baki yarda muje kigani"ganin na dage yasa Baba Larai cewa "toh ai shikenan, bari na kira ɗaya daga cikin mazajennan suje su tsinko mun" ajiyar zuciya nayi. Knocking mukaji aƙofar kitchen ɗin. Baba Larai ce ta buɗe ina leƙawa naga ko wanene idona ya sauka kan Amin dake riƙe da basket dana bari a lambu yana wani cin magani wa Baba Larai. Kulululu naji cikina yabada ƙara, wlh tsoron wannan mutumin nake dashi da sharrin dake tattare dashi.
Shigowa Amin yayi kitchen ɗin ya ajiye kwandon saman canta, har ya juya zai tafi saikuma ya juyo ya kalleni ya kashe mun ido ɗaya, tas akan idon Baba Larai daketsaye tana mamaki wai yau Amin ne a kitchen dakansa. Cabb. Bayan ya fice ta kalleni taga duk a tsorace nake, tace "takwarar Hajja meya haɗaki da Amin" bassss naji zuciyata ta buga, me zanyi da Amin inba Baba Larai ba. Bakina na rawa har idona ya fara tara hawaye nace "ba komai fa. Wlh babu komai Baba" gyaɗa kai tayi dan yadda taga tsoro a idanuna tasan tabbas gaskiya nake fadi, takowa tayi gabana takama kafaɗuna tace " karki damu. Kawai dai banson naga abinda zai cutar dake ne kuma naki faɗa miki, karki kuskura wani abu ya haɗaki da Amin, ko hanya karki bari ya haɗaku. Daso samu ne ma nace karki bari ko gaisuwa ya shiga tsakaninku, amma nasan bazaki iya ba dan haka ki lura kinji"? Gyaɗa kai nayi jiki asanyaye na fice daga kitchen ɗin.
Tabbas yazama dole na ja layi tsakanina da wannan bawan Allahn. Hajja na samu a falo tana zaune, shiko wannan basamuden yana kwance kan cushion din da Hajja take ya kwantar da kansa saman cinyarta tanayi masa tausa. Ko kallonsu banyi ba dan banida da wani sauran ƙwari ajikina nazo wucewa naji Hajja tace "takwara naji Larai tace wai kinga macici a lambu. Fatan dai babu abinda yasameki ko"? Shaf ma na mance cewa nayi wannan ƙaryar, idona na kan tulin gashinsa da Hajja ke masa tausa na gyaɗa kai kawai na wuce nawa ɗakin.
"Allah dai ya kyauta, toko menene ke damunta ta wani ɓata rai. Kodai bata jin daɗi ne" Hajja ta faɗa tana ƙoƙarin kama masa gashin da rubber ring. Juyowa yayi ya kalleta yace "wai meyasa kika damu da mara kunyar nan ne Hajja, saikace ba mai aiki ba, duk kinbi kin wani sake mata har hakan yasa take rainani" fasa ɗaura masa gashin Hajja tayi tace "waya faɗa maka itaɗin me aiki nane, Babana ka fita a idona na kulle. Naga kwata kwata kaki jinin yarinyar nan kamar kana ganin hanjin cikinta. Akanta fa sai mu bata da kai tammm" kasa cewa komai yayi yace "Allah ya huci zuciyar ki Hajja ta" Ameen tafaɗa tacigaba da ɗaura masa gashinnasa.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Ameera na assignment aɗaki Innati ta kirata akan tazo ta duba mata miyan dake wuta akitchen. Fitowa Ameera tayi daga ɗakin daga ita sai yar rigar kanti daidai guiwarta. Ido Innati ta zubawa ƴartata tana kallon ta, wani irin haske ta ƙara gashi idanunta sun wani cicciko kamar na babban mace. Harta nonuwanta sun ƙara tasawa fiyeda da yadda tasanta. Wai meke faruwa ne anya bazata kai yarinyar nan adubata a asibiti ba kuwa?
Ameera na shiga kitchen ɗin tabude tukunyan miyan dake wuta, wani irin haura mata kai ƙamshin miyan yayi take taji amai yazo mata, da gudu tafito daga kitchen ɗin tana rike baki tayi cikin daki. Innati harta fara Sallah aita yanke shi ta biyo Ameeran ciki, a bayi tasameta sai faman kwarara amai take kamar hanjin cikinta zasu fito. Habawa ai Innati take ta tabbatar da abinda take zargi. Mekuwa zatayi inba fashewa da kuka ba, tana kuka tana kiran Allah kusa. Shikenan mutaninnan sun cuceta sun cuci rayuwar ƴarta. Ameera na ganin Innati ta fashe da kuka ta wanke bakinta da sauri tataho wurin Innati ta rungumeta itama ta fashe da kukan duk da batasan menene ba.
Rungumeta Innati tayi tana cewa "Allah saiya saka miki Ameera, Allah bazai bar mutanin dasukayi miki abunnan ba saiya tona asirinsu. Allah saiya hukuntasu da mafi tsananin azaba" cikin kuka Ameera tace "Ameen Innati, wlh nima addu'ar danakeyi musu kenan" kamo fuskarta Innati tayi tace "bazamu zubar da cikin nan ba zaki haifoshi kuma zamu bashi tarbiyya yadda Allah da Manzonsa suka umurta" Ameera najin Innati ta ambato kalmar ciki taji komai nata ya tsaya cak, ci me? Ciki? Ajikinta. Kai inaaa hakan bamai yiwuwa bane, kallon Innati tayi tace "Innati ciki fa kikace" bata kuma sanin metake ciki ba bayan wannan tambayar datayiwa Innati sakamakon zubewa aƙasa datayi sumammiya.
Cikin kiɗima Innati tafara ƙoƙarin tashin Ameera tana kuka kamar anyi mata mutuwa. Tsoronta shine kar ƴarta ta faɗa cikin wani hali saboda wannan jarabawar da rayuwarta ta afka ciki. Ruwa ta samu ta ɗan yayyafa mata, wani irin dogon numfashi taja kafin ta sauke saikuma ta fashe da kuka tana duke duke kamar mahaukaciya tana cewa lallai saidai azubda wannan cikin dake jikinta ita bazata riƙe ba. Abun tausayi 🥹 🥹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Yau ina shigowa part ɗin Mami na tadda itada Raihanah Ya Sultan Mustapha da Ya Isma'il crush ɗina. Wani irin daɗi naji ya mamayeni a lokacin dana ƙyallara idona akansa. Kamar an yaga mun ruwan sanyi azuciyata haka naji. Shiko ko yasan da zuwana hankalinsa na kan wayarsa yana latsawa. Mamy ce tace "a'a takwarar Hajja shigo mana" sai asannan na lura da idon kowa kaina yake, kunya ne ya rufeni ankamani ina kalle mutumin dako yasan da zamata. Gaidasu nayi na nemi wuri na zauna kusada Raihanah wacce ke tsokanata ƙasa ƙasa nikuma ina share ta.
Satan kallon inda Ya Isma'il yake kwance nayi, direct naga shima ni ɗin yake kallo, da sauri na kauda ido inajin yadda zuciyarsa ke bugun tara tara. Can na ƙara ɗagowa na saci kallonsa, kamar ɗazu yanzu ma haka kallona yake. Ban iya sauke idona ba, sai shagala mukayi da kallon juna, wani irin killer smile ya sakar mun wadda yasani jin gaɓoɓina duk sun mutu, kunya ne ya kamani nayi saurin sauke idanuna ƙasa. Lallai wannan mutumin na musamman ne, komai nasa abun burgewa ne.
Ashe duk wannan nufin da akeyi akan idon Mamy, murmushi kawai tayi ta girgiza kai. Allah ya shirya yaran zamani watau ko kunya basuji har wani turawa juna signal suke. Uhmmm, su Isma'il Allah yayi, dama shine kawai duk cikin yaranta basu damu da soyayya ba, shi Mujahid yayi soyayya harda aure, shikuma Sultan wannan ba'a magana tunda budurwarsa ma sananniya ce agidan. Shine dai Isma'il wadda aiki kawai yasa agaba bai damu da komai ba. Kallon Aneesa tayi, sai wani duƙe kai takeyi ita adole kunya takeji.
Kasa zama nayi, duk najini atakure, idonsa ƙyar akaina yake. Duk wani motsin danayi a idanunsa yake, kamo hannun Raihanah nayi nace mata muje ɗaki akwai maganar dazamuyi, har mun tashi zamu tafi saiga Baba Larai tayi sallama akan Hajja na nemana.
Muna isowa part ɗin masani Hajja da wayarta ahannu sai kai komo take yi, ga samuwa kwance afuskarta. Tana ganina ta mika mun wayar tace " gashi nan mahaifiyarki ce ke so tayi magana dake, duk sainabi na damu yadda naji muryarta kamar ba lafiya ba" inajin haka babu zuciya ta tsinke, menene yasamesu. Allah yasa lafiya. Karɓan wayar nayi na kira Innati, bugu biyu ta dauka, a bayan wayar naji kamar muryar Ameera tana kuka, take hankalina ya ƙara tashi na tabbata cewa ba lafiya ba. Muryar Innati na rawa kamar itama tana shirin yin kukan tace "Jamma bazan iya ni kaɗai ba, zan iya karaya, muna buqatarki ataredamu. Allah ya jarabcemu babban jarabawa. Dan Allah kizo" ban iya cewa komai ba sakamakon hannuna daya fara rawa har bansan lokacin da wayar ta subuɗo daga hannuna zuwa ƙasa ba. Hajja dake tsaye tayi saurin ƙarasowa wurina tana tambayata menene. Hawaye kawai ke gangarowa daga idanuna,ganin haka yasa hankalin Hajja tashi.
Da ƙyar na iya buɗe baki nace "Hajja Innati na nemana. Gidanmu ba klau ba, inaji ajikina akwai abinda ya faru" itama Hajja cikin tashin tace "to ai baza'ayi haka ba. Yanzu bari in kira kamalu driver ya kaimu gidannaku tare" tana gama faɗin haka tasa Baba Larai ta kira drivern, sukuma suka shirya. Har lokacin da suka shiga mota zuwa gidannasu kirjin Aneesa keta bugun uku uku. To meya faru ne wai agidan, ko dai Abba yazo inda su Innati suke ne yayi musu barazana. Ita kwata kwata ma bata kawowa Ameera batun ciki ba.
Suna isowa gaban estate ɗin aka yi saurin buɗe musu ƙofa dan sojojin dake gadin wurin sun shaidasu. Tun kafin driver yagama faka motar Aneesa tayi sairin buɗe kofar motan ta fice da gudu har Hajja na kiranta amma batajiba.
Ina ƙarasowa gaban part ɗinmu na bude kofar falon na shiga nama mace wani abu wai shi sallama. Abinda nagani shine ya ƙara tada mun hankali har yasa nakasa motsa wa. Innati na ƙoƙarin kama Ameera amma sai buge buge takeyi kamar tababbiya. Me ke faruwa ne wai. Ameera na ganina ta mike da gudu tazo ta rungumeni tana ƙara rushewa da sabon kuka. Nima rungumeta nayi na fashe da kukan duk da bansan kukanta na menene ba.
Sallama Hajja tayi ta shigo falon, dake Innati tabawa falon baya shiyasa bataga wanene ya shigo ba. Har Hajja ta ƙarasa shigowa falon sannan Aneesa ta rabu da Ameera tace "Innati ga Hajja tare mukazo"Hajja ta kafawa bayan Innati ido sai jira take matar ta juyo taganta. Innati ma take taji bugun zuciyarta ya canza tun kafin ma tajuyo, a wani irin slow ta juyo dan ganin wacece Hajja dinnan da Aneesa ke yawan maganarta.
Idon Innati na faɗawa cikinna Hajja taji komai ya tsaya mata cak. Hakan ma takasance agefen Hajja. Ameera ma takafe Hajja da ido tana kallon matar, wannan ai carbon copy ɗin Innati ce. Hajja data kasa motsawa, laɓɓan bakinta na rawa ta fara ambaton sunan Allah tanayi tana ƙarawa. A hankali tafara takowa inda Innati ke tsaye, tana zuwa tasa hannu ta ɗan karkata wuyan Innati gefe, taja da tulin gashin kanta,ta duba wani birthmark wadda Nadeen ɗinta data ɓace takeda shi. Wani wawan bugu zuciyar Hajja yayi a lokacin da yayi tozali da tabon wuyan Innati wadda sak irinna Nadeen ɗinta ne. Atake ta fashe da kuka tafara kiran Nadeen ahankali, tace "wlh Nadeen dina ce. Ke ce Nadeen? Ina kika shiga wannan shekarun naketa nemanki, dama da rabon zan ganki kafin nabar duniya. Alhamdulillah alhamdulillah Alhamdulillah lallai Allah kaine abun godiya. Yau naga ɗiyata dana yi shekaru da shekaru ina nema. Allah na gode na gode Nagode ya Allah". Innati kam kasa cewa komai tayi, tabbas babu makawa wannnan mahaifiyarta ce wadda taɗade tana addu'ar Allah yanuna mata ita tunda tasan ahannun marasa imani ta girma. Kuma kullum ana faɗa mata cewa