Rayuwar Aneesa complete Hausa Novels pdf Reemah.txt

Author :  Reemah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 24

66K to 69K   out of 70.4K words

Akeer duk da yaso yaron kaman me. But this little Angel right here is different, jinta yake har cikin jininsa. Rubguneta yayi tsam akirjinsa yana sumbatar goshinta.

Labarin aihuwa ya kai wasu Hajja har Kano cikin minti kaɗan. Duk aka fara shiri za'a zo ganin baby. Jirgi guda na Abby sukayi aka jibgosu a birnin tarayya. Aneesa sai buɗe idonta tayi taga Innatinta azaune akusada ita. Saida tabi kowannensu da kallo ta dawo kan Innati saita fashe da kuka tana neman yafiyar mahaifiyarta tana cewa ashe haka aihuwa yake, dan Allah ta yafe mata. Shafa kanta Innati tayi tace mata Allah yayi mata albarka. Babyn wacce ke hannun MJ ya kafe matarsa da ido ya miƙowa Innati ta ajewa Aneesa saman kirjinta. Wani irin soyayyar yarinyar take ji har cikin ƙashin bargon huhun naman jikinta 😂. Kwanasu ɗaya a asibiti aka sallamosu gida.


Last page dropping tomorrow inshallah 🥹🥹

🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷

REEMAH ✍️


PG 96_100

Last page.

Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga

Mom Sani
Ashanty
Eeshert Maijama'a
Zeinab
Noor ɗin Zeinab😂
Khadijat Musa
Maryam
Sa'adatu Aliyu Musa
Aisha Abdullahi
Maimahaman Kagana
Mmn Minal
Queen Halery
Hadiza Alkali
Mrs Abdulkarim
Dama sauran Fans din RAYUWAR ANEESA wadda ban ambato sunansu ba.

Ina godiya sosai da sosai akan goyon baya da kuka bani wurin kammala wannan littafin lafiya. Sharhinku, addu'o'inku da kuma ƙaunar da kuka nuna mun supersedes all🥺. Ina alfahari da ku ako ina. Ina sonku fisabilillah 🙏. Allah yabar zumunci, yahaɗa mu cikin aminci a Darussalam. Nagode Nagode Nagode sosai sosai🙏♥️. I love y'all 🥹🥹🫰


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Ranan suna Baby girl taci sunan Haseena. Baban jego yayi ƙoƙari sosai, babu wadda ya rasa ci yarasa sha, ga sovenirs iri iri sai hamdala. Aneesa kam ba'a magana, tayi fes fes, wanka kala kala photographers har sun gaji da ɗaukan hotuna.

Washe garin taro basu suka farka daga baccin gajiya ba sai wuraren sha ɗaya. Dake anan Abuja akayi sunan, dan haka Ammi ce ta zauna da Aneesa take yi mata wankan jego. Su Mamy da su Hajja aranan suna jirgin su ya ɗaga da daddare.

Aneesa na cikin bacci taji Haseena ta tswala ihu inyaaaa, a firgice ta farka ashe wai wanka Ammi keyi mata, ina irin ɗaga yaro da ake yi sama ayita jijjigashi, da gudu MJ ya shigo Ɗakin har yana cin tuntubi, ganin anjuya masa kan yarinya ƙasa Ammi ta riƙe kafafunta ana jijjigata yayi saurin shigowa ya karɓi yarinyarsa ya rataya a kafaɗa. Haɓa Ammi ta riƙe tana kallonsa tace "yau naga ikon Allah. Mujahid meye haka, ka bani yarinya na shiryata banson iskanci" ƙara matse yarinyar yayi aƙirjinsa ya ɗau towel ɗinta ya rufeta yace "haba Ammi, ƴar yarinyar nan ake juya mata kai ƙasa, in jini ya dawo kanta kuma fa" Aneesa na zaune akan gado ta riƙe kumatu tana kallon draman Ammi da ɗanta, shi kuwa ya haqiqance baza'a ƙara yiwa ƴar sa haka ba. Ran Ammi ya ɓaci ta miƙe ta haɗa bawon wankan da komai ta fitar dashi aɗakin tana ta zalzale masifa amma MJ na tsaye ƙyam ya rungume ƴarsa sai zabgawa Aneesa harara yake kai kace itace tayiwa ƴarinyar haka. Turo baki gaba tayi tace "to Yaya ni sai faman hararata kakeyi saikace ni nayi maka laifi" haɗe fuska yayi yace " yanzu tsakani da Allah, yarinyar nan guda nawa take, kina kallo ake jefa mun ƴa asama saikace paper" miƙewa tayi ta gyara riganta ta shiga toilet dan watsa ruwa, tana jinsa yanata faman masifa yana sakin tsaki time to time. Har tayi wanka ta fito, tasameshi yana damben sa wa baby pampers, dariya ya kamata sosai ganin yadda yajuya gaba baya ya wani ci serious irin shi ya iya dinnan. Itako bby sai hurga ƙafa takeyi asama ta kasa zama wuri ɗaya sai kuka take. Daya gaji ya miƙe yana haɗa fuska ya kalli Aneesa yace "gatanan ai, tun abinda Ammi tayi mata yasa ta kasa yin shiru, ni kizo kibawa yarinya nono ko zata yi shiru" murmushi tayi ta ƙaraso ta ɗauki Haseena tasata saman cinyarta ta buɗe towel din ta tafara shayar da yarinyar. Yana tsaye yana kallonsu cikeda burgewa, har yarinyar tafara bacci sannan tacireta ta ƙarasa mata shirin.


Yau Abby yayi baƙi daga Adamawa, Governor ne da kansa yazo ziyara, dake shida Abby classmates ne a secondary school, His Excellency Muhammad Waziri. A babban falon Abby wadda ba kullum ake budewa ba sai idan anyi baƙi na musamman, anan aka buɗe aka gyara tsaf tsaf aka barbade da turare. Tunda safe da Abby ya faɗawa su Innati zai yi baki, itada su Mamy suka shiga kitchen sunata shirya abinci kala kala. Da misalin ƙarfe ɗayan rana suka iso gidan, motoci ne har motoci, gana sojoji gana bodyguards zai Kuma na shi Babban baƙon dakansa. Baza'a kira shi da dattijo ba saboda yanada sauran ƙarfi ajikinsa, kuma kana kallon sa kaga ma'abocin daga ƙarfe hala tun yana yarintarsa. Fari ne amma ba cancan ba, Fulanin asali kyakyyawa, ga tsayi. Abby na tsaye abakin ƙofan motansa yana jiran fitowar abokinsa. Ana buɗe masa motan ya fito suka rungume juna da Abby suna bubbuga bayan juna, Abby yace "sannu da zuwa baban tuzurai. Kaide Moha ALLAH ya nuna min ranan aurenka. Gani nan harda jikoki amma kai ko inyaaaa babu, dan Allah kafada mun yadda kake rayuwar babu mace atare da kai" murmushi His Excellency yayi ya shafa ƙeyarsa ƙasa ƙasa yace "lemon tsami da azumi sune suke taimako na" dariya Abby yayi suka tafa hannu kaman wasu samari. Ƙarasowa sukayi cikin falon suna wasa da dariya.

Masu aiki ne suka fara aikin jero kayan motsa baki, ga kuloli na abinci kala kala. A plate ɗaya akayi serving ɗinsu, suna ci suna warwaso yadda dai classmates keyi lokacin nan na secondary school. Bayan sunci sukaje sukayi sallah sannan suka dawo. Abby yace bari yaje ya kirasu Hajja da sauran mutanin gida su zo agaisa.

Afalon Hajja yasamesu dukkansu suna hira. Innati taci wankan abaya ne beige colour wadda ya karbi fatar jikinta dayayi lugui. Kiransu Abby yayi akan suzo agaisa da His Excellency, ɗankwalin abayarta ta yafa akai, jelan gashinta na yawo a bayanta, Hajja da Mamy na gaba itama ta biyo bayansu. Da sallama abakinsu suka shiga falon, Yana gishingide da cushion, Yana ganin Hajja ya miƙe da sauri ya sauko ƙasa ya rusuna cikin ladabi ya gaida ita. Mamy ma ta gaida shi, sai yanzu ya kalli Innati dake gefen Mamy, aransa yace "Masha Allah tabarakallah, what a beauty" yadda Abby yaga abokinnasa ya kafawa ƴar uwarsa ido yayi murmushi kawai. Itako Innati ranta fes ta gaida shi, basu jima ba suka fita afalon yarage Abby da abokinsa. Ɗan sosa ƙeya His Excellency yayi yace "Abdul, wannan mai maroon abayar ƙanwar Hajja ce, naga suna bala'in kama"( note shi bai san cewa Abdul nada ƙanwa ba) girgiza kai Abby yayi ya ciza Apple ɗinsa yace "kai Malam ƙanwata ce fa, wadda muka shekara muna nema" haɓa His Excellency ya riƙe yace "haba, kai Masha Allah, wallahi ta fika kyau nesa ba kusa ba" harara Abby yayi masa yace "Malam abini ahankali, ni ne nan waliyyinta, tunda suka shigo falonnan na harbo jirginka. Ayi mun ladabi ko nabawa wani, kasan zan aika" shafa ƙeyarsa yayi wadda babu ko alaman furfura yace "haba wa, Ni na isa. Ai kai Yanzu Yaya zan riƙa ce ma. Allah yaja zamaninka yayanmu, Allah yabar mana kai yayanmu, kai Yaya Allah yayi maka me Nice 🙂 " wani wawan dariya Abby yayi yace "shegen miya, da baka dawo hanya ba'ai, yanzu dai kace nine nafi kyau idan ba haka ba, cire aranka kawai" da sauri His Excellency yace "habawa, ina taga kyawunka ai kai ƙarshe ne yaya, kambulusi" azuciyarsa yace "Allah ko rabin kyawunta baka gani ba"😂. Kafin arufe shafinnan saida Abby ya amince zai yiwa Innati magana akan abokinnasa. Idan aurennan ya tabbata sai yafi kowa jin daɗi, saboda Muhammad mutum ne har mutum, alokacin duk cikin ajinsu babu mai kokarin shi, kuma yanada hankali ga sanin Yakamata.

Bayan tafiyar His Excellency, Abby yayiwa Innati magana da daddare, kunya ya kamata, wai maza basuda ta ido, shikenan daga ganin mutum sau ɗaya sai kace kafaɗa sonshi. Bawai dan kuɗinsa ko kyawunsa ba, a'a, tana fargaban ta ƙara jefa kanta a wani rayuwar kunci na aure, gara tayita zama da mahaifiyarta tana kula da ita har su rabu lafiya, tayi renon jikokinta. Saida Hajja tasa baki amaganan sannan Innati ta sallamawa ranta kawai ta yarda kuma tayi addu'ar Allah yasa shine mafi alkhairi. A daren ranan Abby ya kira His Excellency ya sanar dashi abinda ake ciki. Farin ciki kamar zai kashe bawan Allah, Abby bai ɓoye masa komai ba na cewa Innati ta taɓa aure harda yara, kuma yace yaji ya yarda zai aureta ahakan.

Cikin satin aka sa ranar aurensu nan da wata ɗaya curr. Kamar bikin farko, haka Hajja ta dinga jigilan kuɗade tasa masu gyara sukazo aka fara yiwa Innati. Duk yadda tayi da Hajja amma tsohuwar taki tace "a'a Nadeen, aurenki na farko banyi abinda ya dace ba, aurenki na biyu wallahi sai na kai maqura" haka dai ta haqura ta ƙyaleta.


Gidan amare da angwaye ba'a cewa komai, kowa yana zaune da matarsa lafiya. Habiba na can tana renon matashin cikinta, itakam tagode babu wani laulayi mai zafi saidai yawan Bacci. Ba kamar Ummu sulaim ɗin Sultan ba, baiwar Allah duk tabi ta rame saboda wahalar da cikin ke bata, dake cikinta bai kai na Habiba a watanni ba. Mazajen kam an dage kowa na kula da matarsa daidai gwargwado, Ya Isma'il soyayya iya soyayya babu kama hannun yaro, yadda yakeji da matarsa bazama kace yataɓa soyayya da wata mace kafin ta ba.


Amin da Ameera sai yadda Allah yayi kawai. Daga ita harshi an rasa wanene gwara awurin soyayya. Suna kulada juna yadda ya dace. Aadil yana wata bakwai akayi masa ciki, aranan da Ameera tagane cewa cikine da ita, tayi ƙaramar hauka. Ita atataf saidai azubar da cikin, bata shirya ɗaukanwa Aadil ƙani ko ƙanwa ba. Cewa take yaron bazai yi lafiya ba, shi kuwa Amin shima ya nace yana son abunsa babu abinda za'ayi. Da ƙyar yasamu ta haqura, kuma tacigaba da shayar da Aadil ɗin. Yanzu haka tana hundred level kenan a buk inda Amin ma yake, tana karantar Biochemistry. Cikinta yanzu yana wata huɗu kenan harya fara tasowa. Ƴan mata har kishi suke da ita, ga haɗadden motar da Amin ke kawowa school idan ya faka agaban faculty dinta zai fito ya buɗe mata ƙofa sannan ya karbi jakanta,bazai fito ba sai ya tabbata yakaita lecture theatre ɗinsu. Da yamma idan ya riga ya tashi haka zai jira harta gama ya ɗaukota suwuce gidan Mamy su ɗauko Aadil sannan su wuce gida.


Rayuwa kullum sai ƙara tsanani takewa Abba da Goggo, sunje Kano amma haka baba Auwalu yashafa tozali a idonsa yaci musu mutunci kamar ba ɗan uwansa da mahaifiyarsa ba. Koran kare yayi musu yace babu inda zasu zauna agidansa. Haka sunaji suna gani suka koma Adamawa, yanzu a wani ƙwangon gida suke zama. Duk sun zama abun tausayi, shi Abba wani kwararraben wheelbarrow yasamu yana turawa a kasuwa, idan mutum yayi siyayya kuma kayan sunyi masa yawa, Abba zai karɓa ya sa a wheelbarrow dinsa ya tura har inda mutumin zai shiga adaidaita sahu. Itakuma Goggo gishiri take saidawa, idan tasiya packet guda ɗaya saiyayi kaman sati ɗaya Kafin ya ƙare. Tayiwa Baba Auwalu tsinuwa yafi bakin kwando, ta mance cewa abinda kayiwa ɗan wani sai ɗanka yayi maka kokuma ayiwa ɗanka. Gashi yanzu rayuwa ta juya, Innati na cikin daula su kuma suna cikin ƙunci. Allah kenan, Ya Allah aduk halin damuke ciki kar ka sa muyiwa na ƙasa damu mugunta, kar mu cutar kuma kar acutar damu da ƴaƴanmu🙏


Ana bikin Innati saura kwana goma Su Aneesa sukayi arba'in. Aranan duk suka tattara daga ita har Ammi zasu dawo Kano sai bayan biki, zuciyan mazane kawai yasa Mujahid baiyi kuka ba. Ammi ce ta tsaya masa awuya lallai saidai su taho gida da Aneesa, babu yadda ya iya haka ya yarda. Yanzu haka yana zaune da Haseena ahannu yana kallon yadda Aneesa ke kai komo tana shirya musu kayansu a akwati. Saida tagama tajuyo ta kalleshi taga wani irin mayataccen kallon dayake binta dashi. Kashe masa ido ɗaya tayi tayi murmushi tace "Ya MJ menene" haɗa fuska yayi yace "sai yaushene zan cancanci acanza mun wannan tsamammen sunan na Ya MJ, ko sau ɗaya baki taɓa kirana da wani pet name mai daɗi ba, yanzu kikayi wasa sai na hana ku wannan tafiyan sai ana gobe bikin mutafi tare" dariya tayi, tasan ƙaramin aikinsa ne kuwa yanzu ya hanata tafiyan. Matsowa kusada shi tayi ta karɓi Haseena ta aje saman gado tayi kujera da cinyarsa, hannu tasa ta saƙalo ƙeyarsa da kyau suna kallon juna. Kiss tamanna masa agoshi tace "haba Baby Boy, abun bai kai haka bafa. I'm sorry bazan ƙara ba kaji"? Ashagwaɓe yace "to Ni dai baby, Allah nayi kewarki, tun yaushe banji ɗumin matata ba, duk Ammi tabi ta takura mana. Yanzu kuma ina murna kinyi arba'in zan samu na rage zafi kawai za'a taso da wani kabli da ba'adi " sauri tayi ta haɗe bakinsu wuri Daya, kamar jira yake yafara bata hot kiss har wani karkace wuya yake yana kama gefen kanta da kyau, cikin fitar hayyaci ya buge zip ɗinta ƙasa ya sauke riganta, boobs dinta dake acike yakaiwa damƙa yana matsasu yadda yakamata. Ba'ajin komai sai sautin numfashinsu dake fita sauri sauri, tabbas idan mutum ya tsaya abakin kofa tas zaiji. Kansa yacusa atsakanin boobs dinnata yana basu kisses, tunda ta aihu baiji duminsu ba sai yau. Hook ɗin bra ɗinta yasa hannu ya ɓalle, sai gasu muraran abayyane, kamar jariri haka ya sa bakinsa aguda ɗaya yafara bata good sucking ahankali. Cije leɓe tayi bataso tayi ihu amma tabbas badan Ammi ba irin ihun dazata saki sai gidan ya amsa. Kullum complain take cewa idan Haseena tana shan nono zafi yake mata, amma meyasa da MJ yasa bakinsa akai wani irin daɗi taji har ƙwaƙwalwata, ƙara damƙe kansa tayi da kyau tana banƙaro masa kirjin. Shi kuwa an dage sai zuƙowa yake yana lumshe ido, cire masa baki tayi awannan ta mayar masa da ɗayan, har wani riƙe masa shi tayi irin yadda uwa ke riƙewa yaronta idan tana shayar dashi.

Ganin bazai iya jurewa ba akasalance ya miƙe da ita ajikinsa ya wuce wurin ƙofa yasa key sannan ya dawo dakin. Su kansu idan aka tambaye su ya akayi kayansu yabar jikinsu har rantsuwa zasuyi suce basu saniba. Ɗaukanta yayi suka shiga toilet dan karma ajisu, sun mulmula juna yadda ya kamata saidai basuyi penetration ba. Sun kai kusan awa a toilet suna juya kansu sannan sukayi wanka tare suka fito. Har wani murmushin jin daɗi yake, dakansa ya shiryata cikin leshi doguwar riga mai fadin wuya. Tana riƙeda da Haseena shikuma yaja akwatin suka fito. Afalo suka sami Ammi tana zaman jiransu. Fitowa sukayi suka shiga mota sai airport, basu jima ba jirginsu ya ɗaga. Haka MJ ya dawo gida da dimbin kewar iyalinsa.



Bawani event akayi da bikinba. Iya walima kawai akayi. Saida ana gobe ɗaurin aure kafin su MJ, da Isma'il suka diro agari. Gida ya cika maƙil da jama'a. Ameera da Aneesa suna makale da mamansu, wai yau sune mahaifiyarsu zata ƙara aure Allah sarki. Har tausayin mahaifinsu ya kamasu. ALLAH kaɗai yasan a wani hali yake ciki. Koma menene ai mahaifinsu ne, kuma sun daɗe da yafe masa abinda yayi musu shida mahaifiyarsa.

Washe gari juma'a, dubban jama'a suka sheda ɗaurin auren Nadeen Isa Mainoma da angonta Governor Muhammad Waziri of Adamawa state. Bikin ɗaya girgiza Media, babu wadda ya taɓa tunanin Governor ɗin Adamawa baida mata sai yau da labari ya dinga yawo akan cewa farkon aurensa kenan. Yakasa rufe baki, sai baza babban rigansa yake yana gaida jama'a.

Can gida ma ancika dam. Matan Governors na arewacin Nigeria ɗaɗɗaya ne kawai basu halarci bikin ba. Kowa yaga Mamy sai ya kyasa, Allah sarki daga matar Zaidu yanzu ta koma matan Governor wato First Lady ɗin Adamawa Yola.

Su Aneesa da su Ameera da sauran matan yaran gidan Jenar anko sukayi na wani tsadadden cutton lace black mai adon duwatsu, baby Haseena da Aadil suma sunsha kwalliya cikin kayan yara na kanti masu kyau sai zuba ƙamshi suke.

Bayan mazajen sun dawo daga ɗaurin aure, duk suka fito harda Hajja da Innati Amarya tasha kyau cikin leshi ga alkyabba an ɗaura mata asama, banda matar Governor yanzu matar Yarima ce, dan angonnata shine babban yaron Sarkin Adamawa kuma dagashi ba ƙari. Atsakiya suka sata ga His Excellency agefenta sai sauran yaran gidan Jenar gaba ɗaya da matansu, ga Hajja gasu Mamy ga kuma Abby. Amin na riƙeda Aadil, MJ Kuma yana riƙeda Haseena, kowa ya tsaya kusada matarsa akayi babban round na group picture. Kyawun hoton ba'a magana. Jama'a duk sun tsaya suma da wayoyinsu suna daukan hoton wannan ahali mai cikeda kamala da kuma farin ciki. Angama taro lafiya lau, duk an watse saura mutane kadanne wadda suma gobe ko jini duk zasu koma gidajensu. Aranan Innati adakin Hajja ta kwana, sun jima suna hira kafin suka kwanta Innati tasa kanta asaman ƙirjin mamanta tanaji kamar karta tafi.


Washe gari da sassafe aka fara shirin kai Amarya. His Excellency na garin Kano bai koma ba yanace ƙememe sai tareda amaryarsa zai tafi. Hardasu Aneesa a ƴan rakiyan amarya. An shirya Innati cikin lafaya aka ɗora Mata alkyabba daban bana jiya ba, na yau harya ninka na jiya haduwa da kyau. Motoci sunyi jeri awaje suna jiran fitowar amarya, Ameera da Aneesa suna gefen Innati sun rirrike mata hannu, sun bar ƴaƴansu dasu Mamy da Ammi wadda suma dasu za'ayi tafiya. Motar dake tsakiya aka sa Innati Ameera da Aneesa suka shiga, su uku ne kawai amotan sauran mutane suka jera kansu a sauran motocin.

Jirage guda uku private Jet aka

23 / 24