Rayuwar Aneesa complete Hausa Novels pdf Reemah.txt

Author :  Reemah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   5 / 24

12K to 15K   out of 70.4K words

nida kaine" hannunsa na rawa haka ya riƙe stool dinnan bai bari ya fado ba.

Abunka da tsohon jinin army, zama Abby yayi ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana kallon ɗannasa. Amin na ganin wasa mahaifinsa keyi, saidai yaga ya shafe awa ɗaya curr Abby bai motsa ba kuma idanunsa ƙyam akansa. Wani irin zufa ya haɗa ga fitsari daya matseshi kamar zai fasa masa mara. Duk wani motsi da Abby na lura dashi amma bai ce komai ba, yau yanaso ne idan jikinsa ya faɗa masa gobe babu inda zashi.


Saida ya ɗau awa biyu da rabi, by this time Amin kuka yake harda majina yana roƙon Abby yayi haquri, hannunsa rawa yake gashi Abby na rikeda dorina yaƙi barinsa ya aje stool ɗin. Jin kukansa yasa Ammi fitowa daga ɗakinta, ko damunta abun baiyi ba dan wai ana hukunta Amin, dama kullum addu'ar ta kenan Allah ya hadashi da Mahaifinsa. Amin na ganin Ammi ya saki wani kukan yace "Ammi kibawa Abby haquri, wlh bazan ƙara ba. Na tuba" bai ƙarasa ba Abby yace "nabi tuba da gudu ba wando, ko kayi shiru ko ka kwana awurinnan ahaka kuma kasan zan aika, nonsense kawai" tsit yayi baice komai ba. Stool ɗin Abby ya cire yace masa ya miƙe ya bashi wuri. Kasa sauke hannunsa yayi saboda wani irin tsami dayayi ya ƙame wuri ɗaya, yana kuka yana haurawa sama har ya kai bakin ɗakinsa ya shige. Kallon ƙofan dakin Abby yayi ya girgiza kai yace "Allah ya shirya".


🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Muna kwance saman katifa dake malale aƙasan dakin, nida Ameera muna kwance saman kirjin innati tana shafa kanmu, can na ɗago kaina na kalli Innati nace "Innati yanzu bazamu koma Adamawa ba"? Ajiyar zuciya Innati tayi" toh Aneesa yau ko mun koma garinnan wa mukedashi, gara muzauna anan mu gina rayuwarmu daga tushe inda babu wadda ya shaida mu. Addu'a nake ma kada Allah ya ƙara nuna mun koda mai kamada wannan ahalin" bakina bai iya shiru ba saida na ƙara cewa "toh Innati wai ina ahalinki suke, kullum idan muka tambayeki sai ki share maganar" wannan karon kam Innati kasa cewa komai tayi, ita ma ai batasan inda ahalinnata suke ba. Baba Mariya uwar goyonta dai tace mata itadin ƴar tsuntuwa ce kuma su kansu basusan inda ahalinta suke ba. Idan Allah yayi zasu haɗu toh idan kuma ba haka ba Allah ya zaba musu mafi alkhairi arayuwarsu itada ƴaƴanta.

Suna cikin tunaninnan Ameera tace "Ya Aneesa ranan da ina dawowa gida da yamma naga wasu motoci masu kyau sun jero akan titi, wai naji wasu mutane suna cewa ai shine shugaban inda ake kama manya manyan ɓarayin ƙasa, bakiganshi ba wlh, kamar Balarabe fari sosai kuma kyakkyawa, kinsan gashinsa ma tsayi dashi har saida ya tufke shi. Amma fa baya dariya idanunsa karr akan titi ko kallon gefensa bayayi. Da alama baida fara'a ko kaɗan" tsaki Aneesa taja tace "Innati dan Allah ki cewa yarinyar nan tayi shiru, kina wani bani labari saikace nace miki ina so naji. Toh ni bari kiji farin namiji kwata kwata bashi a lissafina, kuma banason namijin daya cika kyau, duk da bansan shi ba kuma bansan ko zan taba haduwa dashi ba amma haka kawai naji banayinshi tunda ya cika kyau.....🙆🙆


Like
Comment
And share fisabilillah 🙏 🙏🙏

🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷


Reemah ✍️


PG 21_25


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Mainoma Mansion

Ƙarfe ukun dare yadda MJ yaga rana haka yaga dare, zazzabine bana wasa ba ya rufeshi, gashi ya haɗa uban zufa amma kuma yana cikin bargo sai rawan sanyi yake. Kamar cikin hallucination (zafin ciwo) yake kiran "Neehal, Neehal, Neehal", can kuma sai jikinsa ya sake, kansa kuma ya sara lokaci guda. Cikeda son karfafa kansa ya mike ya jingina bayansa da headboard din gadonsa, pillow ɗinsa ya ɗauka ya runguma akirjinsa yana sakin ajiyar zuciya kamar wadda yayi tseren gudu da wani. This is his greatest nightmare that nobody knows up until today. Shi kaɗai yasan meke damunsa, amma Allah kaɗai yasan mafuta. Kunna side lamp din gadon yayi ya mike yana tangarda adaddafe yakai ƙofan bathroom dinsa ya shiga. Tubewa yayi dagashi sai wandonsa na Bacci three quarter ya kunna wa kansa shower ɗin ruwan sanyi, hannunsa bibbiyu adafe da bango. Ruwan na dukan fatar jikinsa yana jinshi har cikin ƙashinsa, yakai ten minutes ahaka sannan ya kashe showern ya tuɓe wandon yaɗora towel. Alwala yayi ya sanya jallabiya milk colour ya fito. Still ba ƙaramin ciwo kannasa keyi masa ba, sallaya ya shimfida ya fara sallan nafila duk azaune saboda jikinsa ba ƙwari. Bai yi ƙasa aguiwa ba, bayan ya idar yafara tilawan Al Kur'ani har yaji anfara kiran Sallan asuba. Ganin dai har yanzu jikinsa bawani ƙwari ne sosai dashi ba kawai ya yi sallan anan ɗakinnnasa. Yana idarwa bacci ya fara fuzgarsa, miƙewa yayi ya koma kan gadonsa ya kashe wutan daƙin. Minti kaɗan bacci yayi awon gaba dashi.


🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Karfe takwas na safe Hajja tafito falo ta zauna saman cushion dinta na alfarma, taci kwalliyan leshi maroon colour wadda ya ƙara fitar da zallan hasken fatarta na buzaye, an kafa wannan dankwalin one side ita adole ta dage tayi ɗauri me kyau kenan. Falon ƙal ƙal dashi ko ina sai tashin ƙamshin turaren wuta yake. Mai aikinta ne ta fito daga kitchen da tray ahannunta wadda yaji kayan alfarma na karin kumallo, tun daga nesa take zabgawa Hajja wani uban harara kamar zata balle idon waje. Tana ajewa saman center table ta juya zata tafi taji Hajja ta kira sunanta tace "ke ladidi, wa kika aje dazai serving ɗina" kamar wata sa'arta wacce aka kira da Ladidi tajuya tana cunno katon bakinta gaba,cikin zallan rashin ɗa'a tace "to ke Hajja bakida hannune da kullum saina zuba miki abinci, ku masu kuɗinnan..." Bata rufe baki ba sakamakon wani irin mari dataji an ɗauketa dashi wadda yasata zubewa aƙasa warwas gefen bakinta na fidda jini. Yana tsaye yasha wankan ƙananan kaya riga da wando three quarter farare masu kyau sai tashin ƙamshi yake, fuskarnan amurtuƙe babu ko annuri, amma da kallonsa kasan yaɗanyi rama saboda zazzabin dayayi jiya da daddare. Tun kafin Ladidi ta miƙe yaƙara sa ƙafa ya mauje bakin yarinya. Sandan da Hajja ke dogara wa ya dauka ya dinga ƙwala mata aduk wani gefen ɗaya samu ajikinta sai ji kake ƙwal ƙwal yana dukan ƙashin kafarta dana hannu. Hajja dake zaune sai dariya take tiƙawa kamar anyi mata bushara da aljanna. Sosai ransa ya ɓaci da attitude din da mai aikin tanunawa kakarsa.

Dan ganin kansa ya ƙyaleta sannan yasa sojoji sukayi waje da ita bayan yabata saƙon sallama daga aiki. Zama yayi kusada Hajja ya kama kansa hannu bibbiyu yanaji kamar zai tsage gida biyu. Kannasa Hajja takama tace "Babana lafiya kuwa. Tun jiya ban ganka ba, yau kuwa kazo kamar baka da lafiya. Menene" girgiza kai yayi alamun babu komai. Kwanciya yayi ya mike kansa akan cinyarta, voice dinsa so low yace "Hajja kisa Abby ya canza miki mai aiki, kuma ban yarda aƙara kawo miki wata mara kunya ba" murmushi Hajja tayi, shiyasa duk cikin jikokin ta suka fi shaƙuwa da Mujahid, yafi su nuna mata kulawa kodan itace ta raineshi.

Abincin dake gabanta ta ɗeba a plate sannan ta miƙar dashi tace lallai sai yaci, duk da baida wani appetite amma tunda yasamu kakartasa tana shagwaba shi yasa ya zauna tana bashi abaki, bayan yayi sosai ta ɗauko maganin ciwon kai taɓashi yasha. Wunin ranan a part din Goggo yayi, sallah kawai ke fitar dashi.

Da yamma da Abby yazo wurinta ta sanar dashi ta kori mai aikinta acanzo mata wata. Bai yi mamakin haka ba tunda ɗan gaban goshinta nagari sai duk abinda yafaɗa. To yanzu a ina zai samowa Hajja mai aiki, wani tunani ne ya faɗo masa shikaɗai yayi murmushi.


🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Washe gari da karfe goma,mun gama ƴan ayyukan da baza'a rasa ba, Innati ta girka mana yar jalop din taliyar Hausa ƴar murji mukaci, muna cikin hira mukaji siren din sojoji alamar babbansu ya shigo. Da sauri na miƙe zuwa window na leƙa, aikuwa irin motar mutumin nan ne daya taimaka mana, da sauri na dawo na zauna nace "Innati shine wlh, Allah yasa mu haɗu dashi sai nayi masa godiyan taimakon mu dayayi. Ashe dai har yanzu akwai na Allah a duniya. Ban gama rufe baki ba naji kwankwasa aƙofar part din namu. Cikeda mamaki muke kallon juna, hijabi na na sanya na mike naje wurin kofar na bude. Yana tsaye sai sakin murmushi yake fuskarsa kamar gonar auduga. Yau kam babu kakin sojoji ajikinsa manyan kaya ne kaftan riga da wando. Dattakonsa ya kara bayyana sai wani haske da kyalli yake. Daga bayana naji Innati na cewa "Jamma wanene"? To wa zance mata, ban gama rufe baki ba naji mutumin yace "wani bawan Allah ne" wuff Innati ta miƙe jin muryan mutumin daya taimaki rayuwarsu. Ameera na kwance bisa carpet itama tayi saurin mikewa ta zauna.

Abby kuwa jiyake kamar yazo gidan wani nasa, jin muryan Innati ba ƙaramin daɗi yayi masa ba. Itada ƴaƴanta sunyi matuƙar burgesa.

Ina tsaye kamar me jiran umurni naji Innati tace "Jamma basu hanya su shigo mana, kin tsaya abakin kofa saikace matar soja" Abby yayi murmushi yace "a'a wannan matar Babban mutum ce ba soja ba" cikin rashin fahimtar abinda ya faɗa na matsa gefe ina sosa kaina kamar mai ƙwarƙwata.

Zama Abby yayi kan carpet ya tankwashe ƙafarsa kamar wadda zaici tuwo. Innati duk ta rasa dame zata tarbesu dan babu komai agidan. Kallon mutumin yayi yace "ƴata zoki zauna akwai maganar danake so muyi daku ne", bayan na zauna ya kallemubɗaya bayan ɗaya yacewa Innati "dan Allah idan bazaku damu ba ina so naji labarin ku. Bazai yi kyau na aje mutane agida haka kawai bayan kuma bansan daga ina kuke ba" gyaɗa kai Innati tayi, saida ta ɗau kusan mintina biyu sannan tafara magana kamar mai shirin yin kuka. Gaba daya labarinmu tabawa wannan bawan Allahn,harda rashin imanin da aka aikatawa Ameera.

Jikinsa ne yayi sanyi sosai har kwalla ya zubar, irin rashin imaninnan a wannan zamanin, saikace wasu bayi. Tun yaushe aka daina irin rashin imanin nan na gidan miji, shi a tunaninsa yanzu mata idonsu ya beɗe da zasu iya ɗaukan mataki akan tauye musu hakki da mazajensu keyi. Take yaji wani irin tausayinsu ya mamaye zuciyarsa. Duk yadda zaiyi saiya inganta rayuwar wannan bayin Allahn, saiya sanya su farin cikin dahar su mutu bazasuu mance ba.


Kallon Aneesa yayi yace "ƴata zaki yarda kibini gidana ki zauna tareda mahaifiyata amatsayin abokiyar fira"? Wani irin dammm naji zuciyata ta bada, zama agidan sojoji cab din janjan, ba'a haife kamata koba, bazan bari inje nafara shan horo hannun wannan marasa imanin ba kaiii. Kamar kuwa yasan abinda nake tunani yace "kar ki damu indai sojojina ne, bazasuu shiga hurumin ki ba matsayin kema baki shiga tasu ba" kallon Innati yayi yace "baiwar Allah ina neman alfarmar kibani ƴarki na kaita gidana, mahaifiyata tana buqatar wacce zatana taimaka mata da wasu abubuwan saboda halin tsufa.

Kamar Innati bazatayi magana ba, har addu'a nake Allah yasa tace bata amince ba. Itako Innati gani take idan taki barayi masa adalci ba, ai wadda ya taimake ka shima yaci kayi masa wani Alkhairi matsayin bai fi ƙarfinka ba. Abby ma addu'a yake Allah yasa ta yarda, ajiyar zuciya Innati tayi tace "badamuwa Alhaji, na amince. Allah yasa hakan shi yafi Alkhairi" hamdala Abby yayi yace "Nagode sosai sosai ƙanwata" wani irin dammm zuciyar Innati yayi, ƙanwata kuma, saikuma ta tuna kila yafaɗa ne kawai batareda wata ma'ana ba.

Nikam na cika fammm kamar wacce aka activating da yeast, tsakani da Allah ni banaso naje ko ina, yanzu duk daddaɗan labaran da Innati ke bamu kullum zauna wuce ni saidai suyi hira itada Ameera, gaskiya ƙwararta za'ayi. Haɗa ido mukayi da Innati ta harareni alamar ko na sake fuska ko in gamu da fushinta.

Kallon agogon Abby yayi,akwai inda zai tafi karya makara yacewa innati ahado mun kayana saimu tafi tare. Kamani Innati tayi muka shiga ɗaki Ameera ma tabi bayanmu, muna shigowa na fashe da kuka ina bubbuga ƙafata aƙasa ni alambaram babu inda zani, rungumeni innati tayi tana rarrashina harna samu nayi shiru, sosai tayi mun nasiha saikace wacce za'akai gidan miji. Bamu ɓata lokaci ba muka fito hannuna cikinna Ameera dake matso kwalla itama.

Bayan nayi sallama dasu, bawan Allahn yace wa Innati gobe da yardar Allah zai aiko aje ayiwa Ameera registration na makaranta saita fara zuwa. Kuma ya bata maƙudan kudade masu tsoka yace asiya kayan abinci da na sawa. Atake naji ɓacin raina ya kau, farin ciki ya mamaye ni. Gaskiya wannan mutumin saƙo ne daga Allah.

Muna fitowa, mota ɗaya muka shiga dashi. Mutanin wurin sunata leƙowa, to wai su wannan wasu mutanene da Jenar ya kawo gidan ya aje sai wani tarairaya akeyi musu. Wasu dasukayi shekara a estate dinnan koda bakin ƙofarsu Jenar bai taɓa zuwa ba amma su wannan mutanin jiya jiya kawai gashi dakansa ya tako har inda suke.

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Muna tafiya amota sai kallon hanya nake, gaskiya Kano ta haɗu, irin wannan titin kamar ba'a Nigeria ba, wanan ka bace agarin saidai ayi wanin ka kuma. Wani dogon titi naga mun ɓullo, bamu jima ba naga anyi parking gaban wani tangamemem gate mai uban tsayi bama a ganin gidan dake ciki daga waje. Sojoji guda uku ne suka buɗe gate ɗin tsabar girmansa. Baki awangale nake kallon fulawowin dasukayi mana sannu da zuwa kaloli daban daban sai tashin ƙamshi sukeyi gwanin sha'awa. Ga wani wuri da aka zagaye da bangon ragaraga, su agwagi suna shawagi acikin wani kwamin ruwa mai hasken gaske, agwaginma ban taɓa ganin irinsu ba, ko tabon datti babu ajikinsu farare tas tas dasu, ga wasu ɗawisu guda uku suna kwance masu kyan gaske,guda ɗaya kuma yana tsaye ya buɗe fukafukinsa masu kaloli dayawa. Abubuwa dayawa nagani wasu ma bansan sunayensu ba.

Muna wuce wurin naƙara ganin wani wuri kuma shikuma an mamayeshi da glass ne, ashe lambu ne na kayan itatuwa masu kyau wayyo Allah. Tsakiyan wurin naga wani abu kamar tulu amma a tsaye ne ruwa na zubowa, ga wasu kujeru anjera agefe da gefen wurin na shan iska. Harma hangoni awurin na zauna inacin ayaba da lemu kai kuɗi yayi arayuwa jama'a.


Toni wai har yanzu tafiyan bai isa bane, kodai nan gidan gona ne, banga gidaje ba har yanzu. Ina juyowa ɗayan gefen kawai naga abinda yasani kasa rufe bakina. Ginine ƙaton gaske atsakiya mai hawa biyu wadda gaba ɗayansa glass ne gaban gidan. Wannan tulun da nace nagani ɗazu abaya ashe ma karami ne, wannan wani baban tulunne shima atsaye yake sai kwararo ruwa yake shaaa. Gefe da gefen ginin kuma suma part part ne na gidan sama suma amma basu kai na tsakiyan girma ba. Wannan kodai tafiyan damukayi bacci nayi bansani ba har muka ƙetare zuwa kasan waje, dan bazan taɓa yarda cewa wannan aƙasa Najeriya take ba. To idan kasa Najeriya take, mu da a ina muka zauna, kenan adaji muke rayuwa da ashe.

Masu aiki ne keta shawagi a tsakar gidan, duk suna sanye da uniform, ga sojoji suma sai kai kawo suke da manya manyan bindigogi ahannunsu. Makwat na haɗiye wani yawu ɗaya tsaya abakina yaƙi wucewa,ai ina ganin yau dana shiga gidannan to bana ƙara fitowa dan karma nahada hanya da samudawannan.


Agaban wannan tangamemen gini motocin suka faka lokaci guda. Bude mana kofa akayi, na fito ta ɗayan gefen inata kalle lalle sai juya wuya nake kamar zan ɓallata. Hatta kasan danake tsaye akai ba ciminti bane, wani irin tile ne mai hasken gaske ƙal ƙal kamar ba'a takawa. Nayi nisa akalle kalle naji ankirani, juyawa nayi naga bawan Allahn ne yayi magana, murmushi nayi nabi bayansa muka fara tafiya. Da sallama abakina muka shigo wani ƙaton falo dayaji kayan duniya na alfarma, ko ina sai tashin ƙamshin turaren wuta yake, ga kuma sanyin wani na'ura na turawa (Ac). Babu kowa a falon sai TV dake aiki, tangamemen TVn nake kallo wadda kusan ya cinye rabin bangon.


Zama nayi kasan tiles din dan tsoro nake kada na zauna saman carpet ace nayi datti dashi. Kunsan masu kuɗinnan da kyankyamin talakawa.

Abby ne ya haura sama ɗakin Hajja dan sanar da ita cewa ya samo mata mai aiki. Tsohuwar tana zaune bakin gadonta tana ninke kayanta da aka kawo daga wurin wanki tunda babu maiyi mata. Ganin ɗannata yasa ta aje kayan, zama Abby yayi kusada ita yace "Hajjata na samo miki abokiyar fira" cikeda murna Hajja tace "dan Allah, har ansamo wata kenan. Allah dai yasa ba halinta ɗaya da wannan hegiya mai zubin sandan raken ba"😂. Miƙewa tayi ta ɗau sandarta Abby ya kamo hannunta suka fito tare.


Ina nan zaune aƙasa, duk mutanin dasuka fito sai sun kalleni sun ƙara, da har tunani nake kodai kashine ajikina aketa kallona, duk sainaji na tsargu na fara kame kame. Wani irin sanyi nake ji kamar ina cikin ƙanƙara, abunka da bansansaba ba.

Har su Hajja suka sauko idanunta nakan yarinyar dake zaune, sotake tag fuskarta amma yarinyar ta duƙe kanta aƙasa. Zama tayi kan cushion tace " baiwar Allah ke kam meyasa zaki zauna aƙasa, hala dai daga ƙauye kika fito, idan ba haka ba ga carpet kika gwammace ki zauna aƙasa"? Ɗagowa nayi na kalli inda matar ke zaune, daram daram daram naji azuciyata, nafara ambaton sunan Allah ina yi ina ƙarawa. Wlhi babu abinda matar ta rage Innatina dashi saidai kawai ta nuna mata tsufa. Komai na su iri ɗaya sak, hasken fatar duk da wannan kam kuɗi sun zaunu dan haka ta fi innati haske shima ɗin ba sosai ba. Yanayin fuskarsu iri ɗaya, yalwan gashin kan innati sak irinna matar saboda ya fito ta ƙasan danƙwalinta kuma yanada tsawo har gadon bayanta. Hancinsu, kai komai ma kawai iri ɗaya ne. Meke faruwa? Na tambayi kaina acikin azuciyata.

Hajja itama ta

5 / 24