Author : Reemah Category : Romantic Hausa Novels
koda motsa hannunsa ne, zirrr saiga hawaye na ɗigowa daga idonsa yana sauka akan paper. Suna cikin haka Jaybash yazo, halin dayaga abokinnasa acikine yabashi tsoro. Su Abby ma kowa yayi kansa ana tambayarsa menene, Isma'il ne yayi saurin karɓan papern dan karanta mene aciki daya sanya MJ kuka.
Tashin hankali wadda ba'a sa masa rana. Neehal da tariga tasan menene acikin papern ta durkushe awurin sai kuka. Ita kanta batasan ya hakan ta faru ba. Kuma wlh babu wadda ya taɓa nemanta sai mutum ɗaya "JAYBASH", kenan yana nufin Akeer yaron Jaybash ne ba na Mujahid ba. Ohhh God.
Suna ciki da haka likitoci suka fito da sauri suka sanar dasu news ɗin daya ƙara kiɗimar da duniyarsu. Akeer yace ga garinku nan. Jin wannan mummunan News din yasa Mujahid miƙewa yasaki wani irin kuka da gaba ɗaya saida mutane suka taru awurin suna kallon yadda babban matashi irinsa yake kuka kamar ƙaramin yaro. Da sauri Neehal ta taso ɗanta riƙe mijinnata ya daka mata tsawa da bai taɓa yi ba tun farkon haɗuwarsa yace mata "whyyy Neehal, whyyy? Menayi miki wadda na cancanci kinsakamun da wannan irin mummunan abun, nace menayi miki"?? Itama cikin kuka tace "dan Allah dear.."? Bata rufe baki ba Abby ya ɗauketa da wani irin gigitacciyar mari yace "kika kuma kiransa dear sai dai kisa haƙoran karfe abakinki dan saina rugurguza miki wadda kike dasu" durƙusawa tayi awurin tana kuka tace "dan Allah kuyafe mun, ba laifi na bane, Mujahid.."
Idonsa dayayi jaa zur yace "who's the Father? I said who's the damn Father "? Ɗago ido tayi ta kalli Jaybash daya matsa can gefe yana zuruzuru da ido, daka kalleshi kaga rashin gaskiya ƙarara a idonnasa. Mamy ta saki salati tace " amma Neehal kin cucemu, kin cuci rayuwar ɗana. Ki jira sakayyarki awurin Allah. Kai kuma Jay, idan mutum yanada aboki irinka gara ya gwammace ya zauna da makiyinsa tunda yasan kiyayya ce a tsakaninka da mutum ba abota ba. Kaje dakai da ita da gawan ɗanku, Allah ya isar mana".
Tsabar mamaki Mujahid ya kasa cewa komai, har Neehal da Jaybash suka bar asibitin bai bar kallonta ba, this is the most darkest day in his life. Kwata kwata soyayya batayi masa rana ba. He has totally lost trust in love.
Har yayi watanni uku gaba ɗaya ya canza ya rikide yakoma kamar ba Mujahid da kowa yasani ba mai yawan fara'a. Da wuya kaga yayi murmushi ko dariya, inko yayi hakan tona mugunta ne. Damuwar dayasawa ransa shine ya haddasa masa hypertension Kuma ya jefa shi cikin depression. He became so consumed to his self. Baya shiga cikin mutane, ya daina yarda da kowa idan ba family member ɗinsa ba. Tundaga ranan bai ƙara kallon wata mace ba da maganan soyayya, kallon mata yake dukansu haka suke, baida aboki. Shi yasa yanzu yasa aikinsa kaɗai a gabansa bai bawa kansa wani lokaci dazai zauna yayita tunani.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Back to story.
Sosai Innati ta tausaya wa Mujahid, ashe dai shima yasha ta arayuwa. Allah sarki bawan Allah, Allah ya kawo masa wacce zata rikeshi da amana.
Ina tsaye tun lokacin da Hajja tafara bawa Innati labari. Inata mamaki wai dama abaya can mugunnan na dariya ashe, lallai kam. Har imagination nakeyi yadda fuskarsa zata kasance idan da yana dariya. Ni kwata kwata bai wani bani tausayi ba, saima Allah ya ƙara nace azuciyata na wuce part din Mamy. Ɗaki na shiga nayi wanka sannan na yi Sallahn maghrib dan har an idar. Fitowa mukayi nida Raihanah zuwa farfaɗan gida wurin swimming pool wadda aka ƙawata wurin ruwan da wasu irin fitillu masu hasken gaske, wurin yayi kyau. Ga iska mai daɗin gaske yana kaɗawa ahankali. Zama mukayi nida ita muka sanya kafafu cikin ruwan muna wasa. Can Raihanah ta debi ruwan ta watsa mun afuska, nima nayi haka. Taƙara yi, ina kai hannu zan ɗebo wani naji kamar anjani cikin ruwa sai kawai ganina nayi aciki dumu dumu. Ga ruwan da zurfi bana wasa ba, Raihanah da itama bata iya fito ba tayi saurin miƙewa tayi cikin gida da gudu wai donta kira wani yazo ya ceceni.
Bubbuga hannu nakeyi a ruwan ina neman ceto, har gani nake kamar lahira tafara yi mun sallama. Gashi inata shaƙan ruwa kamar zan shiɗe. Babu kowa daya fito har kusan mintina biyu. Daga lokacin ban ƙara sanin inda nake ba. Sai ji nayi kawai gaba ɗaya na lume cikin ruwan ko kaina bashi asama.
Dawowarsa kenan daga masallaci, agajiye yake saboda saukan yamma yayi, har yazo zai shiga cikin gida yaga kamar kumfa ke tashi acikin ruwan swimming pool. Da sauri ya ƙarasa wurin, ya leka, ai kuwa sai gani yayi gashin macene ke rito asama gaba ɗaya gangan jikinta na cikin ruwan. Baisan lokacin daya tuɓe jallabiyarsa ba yarage dagashi sai dogon wando ya faɗa cikin ruwan. Alokacin daya fito da ita tariga ta sume. Hannu yasa ya ɗanne cikinta amma ko motsi batayi ba. Ya ƙara dannawa amma still bata motsa ba. Last option ɗin dayake dashi shine yayi mouth rescue.
Runtse ido yayi ya sa hannu yasa hannu ya rufe hancinta sannan ahankali yakai bakinsa kan nata yabata iska ta bakin cikin ƙwarewa. Wani irin numfashi taja sai tafara furzar da ruwan daga bakinta direct afuskarsa. Matsawa baya yayi yana yatsina fuska daidai su Mamy sun ƙaraso wurin itada Isma'il da Raihanah. Ganinta sukayi akwance aƙasa sai tari take yi. Da sauri Isma'il ya ƙaraso wurinta yasa hannu ya dagata cak kamar baby yayi cikin gida da ita, juyowa tayi awahalce tana kallonsa, yana tsugunne awurin bai miƙe ba shima itaɗin yake kallo da wani irin cold expression a fuskarsa. Murmushi Raihanah tayi tace " sannu Babban Yaya" harara ya hurga mata ya miƙe yana tsane gashin kansa daya jiƙe sharƙaf ya matse ya wuce yabarta awurin.
Yana shigowa yasamu Isma'il sai murza mata hannu yake tana kwance saman doguwar sofa sai numfashi take sama sama. Ko kallon gefensu baiyi ba ya wuce sama abunsa.
Ƙarfe tara ya sauko ƙasa ya tadda Mamy ne da Abby kaɗai a falon. Gaidasu yayi shima ya nemi wuri ya zauna yana kallon TV, coffee Mamy ta haɗa masa ta bashi don tasan shima ma'abocin shan sa ne kamar Abby. Hira yayi hira Mamy tace Abby " dear, gsky Yakamata afara shirin auren yarannan, kullum sai soyayya suke kamar zasu cinye junansu, gara kawai ayi musu auren idan yaso saitayi graduation agidansa" Abby dabaisan wa Mamy ke magana akai ba yace "wasu yara kenan"? Ƴar dariya Mamy tayi tace "dear kenan, Isma'il da Aneesa mana" Mujahid daya kai coffee bakinsa yana ƙurba baisan lokacin daya ƙware ba jin sunan wadda aka ambata....
Chakwakiya 🙆🙆🙆
Like
Comment
And Share 🙏🙏🙏
🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷
Reemah ✍️
PG 51_55
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Kallonsa Mamy da Abby sukayi cikeda mamaki, ya daga maganan auren kannennasa kawai zai shaƙe. Tari yake yi ba ƙaƙƙautawa har abun yafaraa basu tsoro Mamy tayi saurin kawo masa ruwa yasha. Abby Yana yi masa sannu. Har idonsa yayi jaa, saida abun ya lafa masa sannan Abby ya tambayeshi ko lafiya. Girgiza kai yayi ya sosa ƙeya yace "Abby kawai gani nake kamar ita yarinyar tayi ƙarama ace za'a yi mata aure tun yanzu. How old is she"? Tsaki Mamy taja tace "kaji Babana da wani shirme, to ni bari kaji na faɗa ma ina shekara 16 nayi aure kuma na haifeka ina 17, to saikace child abuse kenan iyayena sukayi? Kuma ba kai bane kacewa Amin zai auri Ameera, how old is Ameera ba 16 bace yanzu? Ɗan sosa ƙeya yayi cikeda kunya yace "Mamy her situation is different.." murmushi Abby yayi, idan ba karya zuciyarsa keyi masa ba kamar yaso ya gano wani abu a wurin Mujahid, amma dai bari yayi shiru ya zuba masa ido yaga gudun ruwansa.
Kwata kwata ma yaji zaman falon ya ishe shi, miƙewa yayi ya musu saida safe ya wuce ɗakinsa. Yana shiga falonsa ya rufe kofa yaja wani dogon tsaki kamar bakinsa zai manne da ƙofan ɗakinsa yace " fisabilillah just how old is that gurl dasu Mamy keso suyi mata aure. Ni banmaga laifinsu ba, shi Isma'il daya tsaya yana bibiyar ƴar karamar yarinya. Toh ni inama ruwana. Why should I bother myself, at least zata tafi zan huta da rashin kunyarta" wani abu azuciyarsa yace (MJ yaushe ta taɓa yi maka rashin kunya🤔) shrugging shoulder ɗinsa yayi ya wuce bedroom ɗinsa.
Koda dare kasa bacci yayi sai faman juye juye yake yi agadonnasa. To meyasa ma abun yadameshi. Dama yasani yabarta acikin swimming pool dinnan ne ta mutu kowa ya huta🙆🙆. Haka yayi tayi har Bacci ya ɗaukeshi. Da asuba daya tashi yayi mamakin daren jiya kwata kwata baiyi tunanin Neehal ba, chabbb aiki na gaba.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Nagama shiri kafin Raihanah, hijabina na hannu na kama gashina da ribbon nasa ta kitsa min jelar bayan na shafa masa mayuka masu ƙamshin gaske. Fitowa nayi rataye da school bag ɗina na fito falo. Babu kowa dan haka na wuce dinning zanyi breakfast. Serving kaina nayi Irish da fish pepper soup sai black tea na zauna zan fara ci kawai naji anyi sama da plate ɗin. Juyawa nayi na gansa akaina riƙe da plate ɗin abincina ya tsoma hannu aciki yana ci hankali kwance. Raina idan yayi dubu to ya ɓaci, wannan wani irin abu NE fisabilillah. Saikace abinci ya ƙare da bazai iya sa nasa ba, dana lura dai kawai yana neman magana ne na share shi na dau wani plate ɗin nakara serving kaina, ko kulashi banyi ba ya dau kofin Black tea ɗina yafara ƙurba, sip ɗaya yayi ya furzar dashi yace " kirage shan sugar, sugannan yayi yawa" ƙasa ƙasa nace " ai dama ba kai na haɗa mawa ba" ji nayi yace " how i wish I didn't save you from drowning in that swimming pool, yarinya sai shegen rashin kunya kamar tare aka haifoku" rai aɓace na miƙe na kalleshi nace " nidai banida rashin kunya tunda ba haka Innati ta koya mun ba. Ai idan Babba bai kama girmansa ba dolene ƙarami ya hau ya take" ban jira me zai ce ba kawai na dau jakata da hijabi nayi gaba har lokacin Raihanah bata fito ba.
Yana tsaye awurin ya daskare yama rasa mezaice, gyaɗa kai yayi yace "ungrateful human being, na ceceki amma ko godiya baki iya yi ba" Raihanah da fitowar ta kenan ta iske shi yana magana shi kaɗai tace "Babban Yaya wai dani kakeyi ne"? Wani uban harara ya watsa mata ya wuce, tabbas ko ba'a faɗa mata ba tasan dawa yake don kuwa ƙamshin turaren Aneesa na nan afalon har lokacin. Murmushi tayi tace "kar dai kar dai Babban Yaya ya fola, kai amma da wasannan yayi daɗin kallo".
Da yamma da muka tashi Ya Isma'il dakansa yazo ɗaukanmu. Bai wuce damu gida direct ba yakaimu cold stone yayita kwaso mana kayan maƙulashe nida Raihanah hardana Ameera. Damuka fito kuma ya ɗau wani hanya daban, munyi tafiya mai nesa kafin muka tsaya a wani babban shago inda naga anrubuta " Tecno", fitowa mukayi gaba ɗayanmu muka shiga cikin shagon. Babban shago ne wadda aka cikashi da wayoyi manya manya na zamani masu kyau da tsadan gaske. Na kasa rufe baki, sai ji nake inama na mallaki waya guda ai dana ji daɗi, nima nayita kashe hotuna yadda nake ganin Raihanah tana yi. Kamo hannuna Raihanah tayi muka bi bayan Ya Isma'il. Salesboy Ya Isma'il yayiwa magana naga yafara fidda wayoyi different designs Yana jerawa saman table ɗin. Kusan kala shida ya aje, kallona Ya Isma'il yayi da murmushi afuskarsa yace "sweetheart ki zaɓi wadda ya miki acikin wayoyinnan" baki sakato na tsaya ina kallonsa, ni yaushe nakeda hurumin na zaɓi abinda nakeso bayan ba haka aka sabar mun ba. Ai ni kawai duk abinda aka bani inaso ne, girgiza kai nayi nace "a'a Ya Isma'il kowanne ka ɗauka mun Allah inaso" danaga dai kamar ransa bai so haka ba kawai nasa hannu kan wata wayar wadda naga anrubuta "Camon 20 premier ", saida ya kara tabbatar cewa shiɗin nakeso kafin yabada katinsa aka zari kuɗin wayar. Anan akayi mun registern layi na MTN, da farinciki muka fito daga shagon ina washe baki, nima yau nayi waya. Ai ina zuwa gida zan nunawa Innati.
Muna isowa gida har anfara kiran Sallan maghrib dan mun jima awaje. Part ɗin Hajja na tafi inda duk na samesu afalo harda wannan arrogant man ɗin suna ɗan hira amma shi hankalinsa na kan system kamar kullum. Gaidasu mukayi nida Raihanah ko kallon gefensa banyi ba, ni tuni na warkar da kaina daga gaidashi tunda ba amsawa yake ba. Nunawa Innati sabuwar wayata nayi kuma na faɗa mata wadda ya siyomun. Hajja ma ta karɓi wayar ta duba duk sukasa albarka sannan sukace na ƙara yiwa Ya Isma'il godiya.
Raihanah dake tsaye agefen Innati ta saci kallon MJ, yayi wani kicin kicin da fuska sai jefa wa wayan harara yake kamar zai yi bindiga. Batasan lokacin da dariya ya kubce mata ba, bulusi, wlh kishi ne ƙarara a fuskar Babban Yaya. Kai amma Alhamdulillah, Finally ya faɗa tarkon son wata bayan shekara biyar. Suna haɗa ido tayi saurin juya kai tana kunshe kariyar da cinta aciki.
Da daddare, bayan munyi shirin kwanciya har ma munyi addu'a naji vibration ɗin wayata. Dubawa nayi naga " My love" asaman screen ɗin, murmushi nayi na amsa kiran. Cikeda soyayyar juna muke waya. Itako Raihanah sai dariya take, akwai matches agidan Abby, wa da ƙani suna son mace ɗaya ya abun zai kasance kenan.
"Sweetheart, gobe insha Allah zanyi tafiya zuwa wani taron mu na sojoji. Da na dawo zanyiwa Abby magana sai afara shirye shiryen aurenmu " wani kunya naji ya rufeni har na sa hannu na rufe fuskata kamar yana wurin. Allah ya kaimu kawai na iya cewa sannan muka yi sallama nayi addu'an bacci na kwanta.
Kamar yadda Ya Ismail ya faɗa, kwana biyar yayi a tafiyar da yace zaiyi. Yana dawowa ya sami Abby yayi masa magana. Nan Abby bai musa masa ba ya amince sannan yace shi da kansa zaije Adamawa ya nemawa Ya Isma'il ɗin auren Aneesa awurin Abba. Da ya faɗawa Mujahid maganar neman auren, duk da bai nuna ya damu ko kuma yanada wata matsala ba amma tabbas ranan sai da yaji kamar yasa hannu akai yayita ihu ko zaiji sauƙin abinda yake ji azuciyarsa.
Da Innati akayi shirin tafiya Adamawar harda Hajja. Da farko Mujahid baiso yabisu ba amma ganin idan yayi haka Abby bazaiji daɗi ba ya amince za'ayi tafiyar dashi. Tundaga ranan kuma ya fita aharkar Aneesa, ya daina tsangwamarta. Babban abinda yake yi masa zafi shine itama ba shiga harkar sa take yi ba, infact idana taganshi afalon Mamy ko Hajja saitayi kamar he's invisible. To meyasa yake jin zafin haka bayan shima he doesn't care about her.
Ranan Saturday da sassafe sukayi mota biyar uku na sojoji biyu na mutanin gida aka kama hanyar Adamawa. Gaba ɗaya mazajen gidan Abby, Mujahid, sultan, da ango Isma'il sune suka tafi. Sunyi shirin manyan kaya ba ƙaramin kyau sukayi ba. Innati tunda suka fara tafiya taji kwata kwata hankalinta ya kasa samun nutsuwa.
Ƙarfe ɗaya saura suka iso cikin garin Adamawa sannan aka kama hanyar unguwar dasu Abba ke zama. Tunda suka shigo cikin unguwar yara da matasa sai faman fitowa suke suna kallon wannan danƙararrun motocin ga kuma sojoji duk sun wani tamƙe fuska kowa na riƙeda bindiga ahannu. Suna shigowa layin gidansu Abba matan layin sai leƙowa suke daga katanga wasu kuma har fitowa sukayi waje anata kalle kalle, daka kalli motocin an kasan babban mutum ya shigo gari.
Agaban gidan Abba motocin sukayi parking. Tunda Hajja ta kalli Kofar gidan sai kawai ta fashe da kuka wiwi, Abby da Innati dake motar hankalinsu ya tashi suka fara yi mata tambaya, cikin kuka tace "Nadeen yanzu dama wannan gidan kike rayuwa har tsawon shekaru ashirin? Kalli irin kwangon gidannan fa wayyo ni Aneesatu, Allah ya isa tsakanina da mutanin dasuka jefaki cikin wannan halin. Yiyiyuyuiiiii" taƙara ƙara sautin kukanta, murmushi Abby yayi ya girgiza kai, Hajja rigima. Saida suka samu tayi shiru sannan aka buɗe musu Kofar motan suka fito.
Haire dillaliya makwabciyar Innati tunda ta kafe Innati da ido taji aranta tabbas akwai inda tasan matar nan, tayi mata bala'in kamada Hussaina matar Zaidu saidai wannan mai kuɗice kuma tafi Hussaina haske da murmurewa. Kamar kuwa innati tasan me take tunani tace "Haire baki ganeni bane? Nicefa Hussaina matar Zaidu" cikeda mamaki Haire tace "kai dan Allah wacce Hussaina, yaushe Hussaina tayi wannan arziƙin da har zata shiga cikin wannan danƙareriyar motar" Hajja ce ta tari numfashin Haire ta hanyar cewa "to itaɗin ce, idan baki yarda ba saiki ja bakinki kiyi shiru" tsit Haire tayi da bakinta suna ta kallon ikon Allah.
Yara ƴan matannan sai faman kallon samarin gidan Jenar suke suna sanyi su musamman MJ wadda yasha wankan danyan boyel yard honey colour baisa sanya hula ba amm gashin nan nasa yasha gyara ta musamman sai wani kyalli yake yi. Ango Isma'il bakinsa yakasa rufuwa, yau gashi a gidan surukanninsa.
Innati ce tayi gaba da sallama abakinta ta ƙusa kai cikin gidan. Gabanta ne yayi rassss ganin Goggo cikin wani irin yanayi sai ƙaƙarin amai take yi amma takasa, Abba na gefenta yana bubbuga bayanta sai faman sannu yake yi mata. Ɗagowa Goggo tayi tana kallon baƙuwar fuskar dake tsaye abakin ƙofa. Awahalce tace "baiwar Allah wakike nema"? Innati batasan lokacin data fashe da kuka ba da sauri ta ƙaraso wurin Goggo tace "Allah sarki rayuwa, Goggo yanzu kina nufin baki ganeni ba? Nice fa Hussaina" Goggo da Abba suka kalleta da kyau, ai kuwa itace. Iko sai Allah, Abba yace "Hussaina dan Allah ina kikaje. Yanaganki ke kaɗai ina ƴaƴana" bai gama rufe baki ba saiga Hajja da Abby sun shigo suma da sallama abakinsu. Da sauri Abba ya miƙe yana kallonsu, wannan dattijuwar tabbas tayi kamada Hussaina, toh amma shi