Author : Reemah Category : Romantic Hausa Novels
da shida hannunta na rikeda wani jariri fari sol mai bala'in kamada ita. Ahankali yasa hannu ya shafahoton yanajin wani irin radadi azuciyasa. To mene ma amfanin rataya wannan hoton tunda bata tareda shi kuma? He misses her so much it hurts, ta zama wani bangare ajikinsa wadda duk yadda zai yi ya cireta yakasa. Labbansa na rawa ahankali yafurta "Hayaaty". Ganin zai ƙara shiga halin dayake shiga aduk lokacin daya kalli hotonta kuma abinda ya faru abaya yana dawo masa ƙwaƙwalwa kawai yasa ya rufe hoton ya juya zuwa king-sized bed dinsa. Kwanciyar rufda ciki yayi ya kulle idanunsa kamar mai bacci amma kuma ba bacci yake ba, wani siririn hawaye ne ya fara gangarowa daga kurmin idanunnasa. Toh fa Babban Yaya da kuka kuma?🤔
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Tafiya muke acikin unguwa bamusan inda muka dosa ba tunda wannan ba garinmu bane. Da ƙyar Ameera ke iya takawa hakan yasa Innati tsugunawa tace ta haye bayanta. Duk inda muka ɓullo idon mutane na kanmu, kamar dai kowa yasan abinda yasami Ameeran, wasu har nunata suke da yatsa. Ikon Allah, mutane ba tausayi.
Har muka fito titi inda motoci suke wucewa. Can dai naji ina, wani irin juyi cikina keyi alamun yunwa, rabona da abinci mai kyau na mance.
Wani wuri muka samu inda ake saida abinci na ƴan talakoki, anan Innati tace muje muci abinci. Nikam har yanzu Innati bata daina kasheni da mamaki ba,a ina tasamo wannan kuɗin. Shinkafa fara da miya sai pure water, yadda muke cin abincin dagani har Ameera har saidai mutane suka juya suna kallon mu. Ameera ce ta ƙware tsabar rusan abinci. Tana shan ruwa taci gaba daga inda ta tsaya har kerma jikinta keyi, sosai tabani tausayi.
Muna zaune mukaji gunjin motoci sun faso kai cikin harabar wurin, bamu gama tunani ba sai ga wasu jiga jigen sojoji sun sauko daga cikin motocin, da kaɗan ban saki fitsari ba, wani irin tsoro ne ya rufeni lokaci guda. To mekuma ya kawo wannan mutaninnan, Allah dai yasa ba laifi mukayi ba. Abun bai kara bani tsoro ba saida naga wasu sojojin sun shigo da gudun gaske kowanne rikeda bindiga ahannunsu sunyi layi su goma, biyar a gefen dama biyar a gefen hagu suka daga bindigarsu sai paaaa kakeji. Ameera dake gefenmu take ta saki fitsari a wandonta,Ni kaina riƙe kaina nake. Ba ƙaramin tsoron sojoji nake ba, musamman tunda ba ganinsu nake ba agarinmu. Wai nikam me zai kaini inda sojoji suke ko a mafarki inaa.
Wani dankareren mota ne ya sawo kai cikin wurin, bansan sunan motar ba amma dai nasan duk yadda akayi motar akwai kuɗi sosai. Soja daya ne ya buɗe motar, kusan minti biyu kafin wani kafa mai sanye da kakin sojoji ya fito, har mutumin ya ƙarasa fitowa bamu daina kallon wurin ba. Wani hadadden magidanci ne fari amma kuma ya manyan ta. Kakin sojoji ne ajikinsa wadda ba ƙaramin amsarsa yayi ba, sojojin nan sukayi masa salute 🫡 kamar dai yadda sukeyi idan wani babba ya iso wuri..
Gefenmu naji wasu matasa suna cewa "Jenar Abdulazeez Isa Mainoma kenan, mazan fama. Gsky duk wadda sukazo wurin nan yau kamar dai mu mun taki Sa'a, Allah ya kawo mana karshen wahala da yardarsa" juyowa nayi na kalli wadda aka kira da Jenar din, gaskiya kuɗi yayi arayuwa, kalli yadda jikinsa ke wani sheki kamar ba tsoho ba, akanme nima bazanso nayi kuɗinan ba.
Gaba ɗaya mutanin suka miƙe ganin haka yasa muma muka mike, kowa yafara sara masa, muma ɗin haka mukayi. Ahankali yafara takowa inda muke tsaye, Innati ta kalleni nima na kalleta, mekuma yasa yake zuwa wurin mu. Bamu gama tunani ba har mutumin ya iso wurin mu, makwat na hadiye yawu ina zaro ido waje.
Abby da ya kafe su Innati da ido musamman ita innatin, meyasa zuciyarsa ke fuzgarsa zuwa garesu, kodai saboda shirin dayagani ajikinsu ne wadda ya nuna su ɗin mabukata ne sosai. Da murmushi afuskarsa ya kalli Aneesa wacce aƙalla zatayi shekarar ƴar autarsa Raihanah, inba idonsa ne ke ƙaryatasa ba zai iya cewa gaba ɗayan su su ukun Innati, Aneesa da Ameera suna Kamada Hajja....
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Gogho abun duniya ya ishe ta sai faman sakin tsaki takeyi akai akai. Abba dake ɓare mata lemu yakalleta yace "Goggo menene lafiya kuwa"? Ajiyar zuciya tayi tace "haka kawai naji gidan ba daɗi tunda Hussaina ta tafi. Yanzu wazaina mana bauta, kadaisan babu abinda zan iya yi da kaina." Yatsina fuska Abba yayi yace "ahap Goggo karki damu kanki, Ni dinnan akwai wasu kudaden dana adana gobe gobe nan zan kai gidansu Abu zan biya sadaki, dama mahaifinta yace ni kaɗai suke jira ayi a ɗaura auren" hamdala Goggo tayi tace "ashe dai abun ya matso Allah, to haka akeso". Miƙewa Abba yayi yace "bari indauko kudaden mu kirga tare mu tabbata sun cika" da sauri Abba ya shiga ɗakinnnasa ya lalube jakan kudinsa daga kasan gado. Har wani zakadi yakeyi ya buɗe jakan, yana budewa yaga abinda idanunsa suka kafe wuri ɗaya ya kasa koda motsi ne🤣🤣🤣🤣🤣.......
Like
Comment
Share fisabilillah 🙏
🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷
Reemah ✍️
PG 16_20
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Har wani zakadi yakeyi ya buɗe jakan, yana budewa yaga abinda idanunsa suka kafe wuri ɗaya ya kasa koda motsi ne. Wani iska mai sanyi ne yaji ya buge shi, lokaci guda yaji kamar an dauke duk wani kuzari ajikinsa. Suuu ya tafi kamar zai faɗi, adaddafe ya zauna saman gadonsa ya shafe fuskarsa. Goggo dake zaune awaje taji shiru kamar anyi ruwa an dauke tafara kiran sunansa, jin shiru bai amsa ba yasa ta mike ta buɗe labulen ɗakinnnasa, Abba na zaune akan gado ya kafe wuri ɗaya da ido babu ko kyaftawa, yama rasa ko ihu zai kurma ko kuma salati zai yi ko kuka. Hussaina ta cuce rayuwarsa tagama dashi. Goggo tayi masa kiran duniyannan amma ko ajikinsa. Kamar me tsoro tasa hannu tadan taɓashi, afurgice ya ɗago ya kalleta, bakinsa na rawa yace "Goggo Hussaina ta gama dani, ta gama da rayuwata itada ƴarta sun gudu da kuɗaɗena, na shiga uku" kamar Goggo bata ji meyace ba sanadiyyar wani tsuuuu dataji cikinta yabada, mene? Mene? Mene? Hussaina ta sace kuɗi ta gudu, shikenan nasu ya ƙare, ta ina zasu fara yanzu.
Bata iya cewa komai ba kawai ta mike asukwane tayi waje ta ɗau buta da gudu tayi bayi sakamakon ruɗewar da cikinta yayi lokaci ɗaya sai gudawa kawai takeyi ba kakkautawa🤣🤣🤣🤣. Toh yanzu ina ma zasu fara nemanta bayan ta kai kusan awa uku da barin gidannan. Amma ta cuce rayuwarsu. Ance kamuwar Allah yafi na mutum, wannan kuɗin da Innati ta ɗauke nata ne halak malak, sai dai ma ace Abba ne ya hanata haqqinta. Uban goyonta wadda shine ya aurar da ita ya bata ɗan gona madaidaici, amma Abba ya saida gonan harma yafara cin kuɗin, duk tunaninsa duk abinda yakeyi Innati batada wayau ne shiyasa batace komai ba amma baisan tarashi kawai take ba. Gashi yau Allah ya ɗorata akansa har ta samu ta damƙi haqqinta bata bar gidan hannu wofi ba.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Abby dake kallonsu Aneesa kamar akwai inda ya sansu kawai yaji tausayin bayin Allahn ya kamashi lokaci guda, musamman yadda yaga fuskar Ameera duk akumbure kamar anyi mata duka. Innati ma jitayi kamar akwai inda ta sanshi, amma tamance a ina ne.
Cikin muryan tausayi yace "bayin Allah, daga ina kuke, me kukeyi anan" kowa kuma sai mamaki ya kamashi, meyasa duk cikin dunbin mutanin dake wurin bai iya yiwa kowa magana ba sai wannan almajiran. Innati ce tayi magana tace "daga Adamawa yallaɓai" gyada kai yayi yace "kunada zama ananne ko kuma akwai inda zaku daganan"? Yaƙara jefo musu tambayan, kamar me jira da sauri nace "wlh babu inda muka sani agarinnan, kuma bamuda kowa. Bamusan ko ina agarinnan ba, gash..." Ban gama magana ba naji Innati ta buge bakina tana hararana alamar inyi shiru,, cunno baki nayi gaba kamar zanyi kuka. Murmushi Abby yayi, yadda tayi ɗin sak yadda Raihanarsa takeyi idan tana shagwaba.
Juyowa yayi ya kalli wani soja acikin sojojinsa yace" ina so akai mutaninnan sabon estate dina dana ginawa marasa ƙarfi, abasu apartment guda su zauna aciki, abasu duk wani abinda suke buqata. I'll get back to them in the meantime inshallah". Da sauri Innati tace "a'a yallaɓai, wlh daka bari. Bazamu rasa wurin kwana ba da izinin Allah" kamar nayi ihu, meyasa Innati takeyin hakane wai don Allah, yanzu Allah ya kawo mana mataimaki amma tana cewa a'a, tsakani da Allah ita kanta tasan karya takewa kanta, babu inda zasu zauna agarinnan saidai in a gindin gada zasu na kwana. Abby daya gane cewa mutanin atsorace suke dashi yace "i insist, kar ku damu. Sojojina suke gadin wurin. Babu abinda zai sameku, dan Allah ku kwantar da hankalinku", badon Innati taso ba ta yarda. Harta Bill dinku damukaci abinci shine ya biya mana.
Mutanin wurin kowa ya fara kuskus, wasu suna cewa kullum suna Zarya awannan wurin amma Jenar bai musu Alkhairi ba sai mu damuka zo yau yau. Ya ɗau lokaci sosai awurin yana ta rabawa mutane kuɗi, wasu kuma matasa ne wadda sukeda takardun karatu duk sun haɗo sun kawo masa.
Ɗaya daga cikin motan sojojin akasa muka shiga, duk mun Kame kanmu wuri ɗaya inda Innati ta kankamemu ajikinta kamar za'a rabamu. Munyi tafiya mai ɗan nesa kafin muka iso bakin wani gate mai girman gaske inda sojoji ne masu gadin dana gani suna zaune ga bindigarsu agefensu. Suna ganin motan mu suka tashi suka wangale mana gate ɗin gidan, wurine mai girman gaske sashe sashe sunfi aƙirga yan madaidata masu kyau daidai misali.
Gaban wani sashe sojojin suka tsaida motarsu sannan sukasa muka fito. Muna fitowa suka miƙawa Innati makullen gidan sannan suka ce mana anjima za'a kawo mana kayan amfani. Bakina kin rufuwa yayi, Allah kenan. Mun fito batareda tunanin yau yau dinnan Allah zai kawo mana mafita ba amma gashi. Anbamu gida kyauta halak malak batareda munsha wahala ba. Godiya Innati tayi musu. Saida mukaga tafiyarsu sannan tasa makullin tabude ƙofan gidan. Da sallama abakinmu muka shiga, ɗan ƙaramin falo ne wadda babu komai acikinsa sai ɗan ƙaramin carpet wadda ke malale aƙasa. Can gefen falon kuma kofofi ne guda biyu, saida muka shiga ko ina muka bubbude muka duba, Alhamdulillah gidane wadda mu awurin mu kamar aljanna aka bamu in za'a hadashi da inda muka baro.
Dake akwai ruwa a ko ina babu ruwanmu da wani fita debo ruwa akai. Da ruwan sanyi muka yi wanka gaba ɗayanmu. Saida muka biya sallolin da ake binmu kafin muka zauna muna fuskantar Ameera nida Innati. Sai yanzu muka samu daman kebancewa dagamu sai mu, kafin Innati tayi wani magana kawai Ameera tafashe da kuka tana faɗin "Innati sun cuceni, sun gama da rayuwata. Wlh har duniya ta naɗe bazan taba yafe musu ba" yadda take sambatu kamar wacce ke ƙoƙarin zarewa saitabamu tausayi. Wani sabon shafin kukan muka buɗe muna rerawa gaba ɗayanmu. Mun jima sannan Innati tayi ƙoƙarin rarrashinmu, saida ta tabbata hankalinmu ya kwanta sannan tacewa Ameera"kin sansu ne? Kin san inda sukeda zama? Kin shaida fuskokinsu?" Da sauri ta girgiza kai alamar a'a tace "bansansu ba Innati, amma yaran masu kuɗi ne dan acikin wani mota suka zo mai girman gaske su uku. Ɗayan cikinsu dogone kuma yanada jiki kuma ba fari bane. Cikin su ukun ma Innati shine kawai yayi mun fyaɗe, sauran sun tayashi rike Ni ne saboda kokuwan ceton raina danayi" share hawaye nayi nace "ɗaukan ki sukayi amota"? Gyaɗa kai tayi tace "sun shaƙa mun wani abune mai ƙarfin gaske ahanci na , daganan ban sake sanin inda nake ba. Sai farkawa nayi naganin a wani hadadden daki, shi wannan mutumin shina fara gani dagashi sai gajeren wando. Innati har duka saida sukayi mun kalli" tafada tana nuna mana shatin bulalai ajikinta wadda ya nuna kamar da igiyan madauri wandon maza akayi(belt). Wannan rashin imani har ina. Dan kawai yarinya ta fito neman kuɗi sai wasu yan iska su ɗauketa su keta mata haddi, wlh Allah ya isa. Munci kuka mun godewa Allah, kuma mun barsu da Allah tunda bazamu iya dasu ba, amma aisu basufi ƙarfin wadda ya halicce su ba.
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Yana tsaye gaban makeken bathroom mirror dinsa, ƙugunsa daureda towel iya guiwa. Abs dinsa sun wani fito radau radau saman lafaffen cikinsa sun haɗe da vline dinsa, gashin kansa dake da bala'in yawa kamar mace ya kwanta saman ƙafaɗarsa yana digan ruwa, golden brown sharp eyes ɗinsa na dauke da wani cold expression wadda bazaka iya tantace halin dayake ciki ba. Hannunsa hands akimbo yana ƙarewa ƙirar jikinnasa kallo. He looked so sexy🙈🙈. Yau shekarunsa uku kenan babu Neehal ɗinsa ataredashi, it feels like a dream. Yarasa meyasa yakasa cireta aransa,kodan saboda itace first love ɗinsa? Lallai Neehal ɗinsa tadabance, sai an tara mata ɗari za'a samo guda daya wacce ta yi kusa da ita a kyau. Itace kawai jarumar macen data iya ɗaukan nauyinsa harna tsawon lokaci. Babu mace, he repeats babu macen dazata iya da buqatunsa har yau baiganta ba. Shiyasa kawai he prefers to overwork himself dan ya cire wannan tunanin azuciyarsa, gara yayita zama ahaka har Allah ya ɗau ransa. Bazai taɓa iya trusting wata mace aduniyar nan ba, the heartbreak he has undergone is enough for him. Women are cheaters🤔inji Mujahid fa bani na faɗa ba.
Hand dryer ya ɗauka yafara busar da gashin kannasa wadda ke fidda wani irin ƙamshi mai daɗin gaske na oils. Bayan ya gama ya wuce makeken closet dinsa,gefen kayan bacci dake shaƙe da different brands din kayan bacci masu tsadan gaske. Komai nasa cikin miskilanci yake yinshi, wani riga da wando na cotton yard honey colour ya fitar da takalmin su irinna yawon ɗaki mai laushinnan ya dauko sannan yadawo cikin dakin. Bayan ya gama sawa ya tsaya gaban mirror din ya ɗau turarensa na Oud Al-layl na maza ya feshe jikinsa gaba ɗaya. Gashin kansa kuma ya tufke wuri ɗaya da ɗan ƙaramin rubber band, ba ƙaramin fidda masa zallan kyawunsa style dinnan yayi ba. Shi kansa saida ya gyaɗa kai irin "this is it" dinnan kafin ya juya ya koma wurin study table dinsa. Wayarsa ƙirar Samsung Z flip ya ɗauka yafara duba emails da aka turo masa. System dinsa da shima same Company ne da wayarsa ya buɗe, yana danna power button hoton matannan ta ɗazu ya ƙara bayyana. Amma wannan karon ita kadaice, tana sanye da Arabian gown babu dankwali akanta, kannata yasha kitso ƙanana tana murmushi hannunta daukeda jan fure aka ɗauketa hoton, ba ƙaramin kyau tayi ba. Saida yadauki lokaci yana kallonta sannan yacigaba da abinda yake.
Wayarsa ne yafara ƙara, sunan "Abby" ya bayyana akan screen ɗin. Daukawa yayi ya amsa da sallama cikin ladabi, Abby aɗayan gefen yace " haba Babana, kazo tunda rana amma bamu haɗu ba. Abincin ka ma duk adaki kaci. Kana lafiya daiko"? Yatsina fuska yayi murya ƙasa ƙasa yace "Yes Dad, ina Lafiya" badon Abby ya yarda ba kawai ya ce "shikenan, yanzu dai tunda dare yayi mubari sai gobe mu haɗu ko"? Gyaɗa kai yayi kamar mahaifinnasa na ganinsa,kit ya kashe wayar bai jira ance komai ba.
Wani irin murɗawa yaji cikinsa yayi daidai maransa, saiga mutuminku na matse ƙafa wuri ɗaya, can kuma ya mirgina ya faɗa saman guiwowinsa yana dafe da cikinsa, nan da nan ya haɗa zufa. Da ƙyar ya iya rarrafawa da guiwa zuwa inda fridge yake ya ciro goran ruwa, ya koma wurin side drawer din gadonsa ya ciro magani ya haɗiye yana maida numfashi. Guiwansa na ƙasa rabin jikinsa na kan gado ya kwanta saman hannunsa guda, dayan kuma still yana cikinsa. Rufe ido yayi kusan two minutes can kuma kawai saiya fashe da wani irin kuka kaman ƙaramin yaro. Sosai yake kukannan kamar ba Mujahid ɗan Jenar Abdulazeez ba. Har wani sheshsheka yakeyi,bakinsa na rawa yafara furta "Neehal why, why did you do this to me. Why would you go away from me when I needed you the most, why"? Saikuma ya ƙara fashewa da sabon kukan. Atake wani irin zazzaɓi ya rufeshi, jikinsa yahau kakkarwa yana rawan sanyi. Da ƙyar ya haura gadonsa ya jawo lallausan duvet ya rufe jikinsa ya kashe wutan dakin gaba ɗaya. Sorry Babban Yaya 🥹🥹
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Karfe goma daidai ya dinga buga horn abakin gate ɗin gidannasu. Sojojin dake gate suka wangale masa ita ya danno hancin motarsa da wani irin gudu kiiii. Sports car ne mai kyan gaske yellow color. Fitowa yayi ya ƙulle motar yana cigaba da rera waƙansa yana kaɗa kai kamar ƙadangare. An gama yawon dare kenan sai yanzu aka ga daman dawowa gida. Amin ba ƙaramin mayen mata bane, shidai abarsa da wannan, bai taɓa koda ɗandana wani abu wai shi giya ba. Tafiya yake cikin izza har ya iso bakin apartment ɗinsu, baima lura da motan MJ dake pake a tsakar gidan ba sai yanzu. Kansa yayi wani irin sarawa lokaci guda. Dama Babban Yaya na gari shine yakai wannan time ɗin bai dawo gida, shikenan kashinsa ya bushe. Gobe sai ya yabawa aya zakinta. Kamar wadda aka zarewa laƙa ajiki ya buɗe ƙofan falon Ammi ya shiga. Babu kowa an kashe komai na falon. Hasken wayarsa ya kunna cikin sanɗa yafara haurawa stairs, bai ankara ba kawai yaji yaci karo da mutum.
Har zai kurma ihu Abby yayi saurin mauje masa bakin da bayan hannunsa, collar din rigarsa yakama yajawoshi har ƙasan Babban falon sannan ya kunna wuta. Amin na ganin Abby yafara salati, wai meke faruwa ne yau. Dama Abby ma yadawo gari, inna lillahi. Zama Abby yayi kan sofa yace "yau dinnan ni da kaine agidannan Amin. Dama bakasan ya ake bawa sojoji horo ba yau zan koya maka, oya kneel down and raise your hands up" kamar zaiyi kuka haka babu musu ya tsuguna yayi abinda aka umurce shi. Wani ƙaton stool Abby ya dauka ya ɗora masa saman hannunsa dake sama sannan yace "karka kuskura ka sake abunnan ya fado ƙasa idan ba haka ba