Rayuwar Aneesa complete Hausa Novels pdf Reemah.txt

Author :  Reemah Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 24

36K to 39K   out of 70.4K words

kwaɓe shi yace " MJ she's your brother's wife to be", iska mai zafi ya furzar daga bakinsa ya koma ya zauna agefen gadonsa ya dafe kai da hannu biyu. Allah kaɗai yasan halin daya shiga a sati biyunnan daya koma Abuja, aiki mai kyau ma ya gagareshi, he's lost. Yana ji kaman wani abu mai muhimmanci yana neman suɓuce masa. Tunanin ƴarinyar nan ya mamayeshi, ko wayarsa ya ɗauka kaman fuskarta yake gani a madadin hoton Neehal dake screen saver ɗinsa. Wayan ya ɗauko ya kunna, hoton Neehal dake kai ya cire sannan ya deleting hoton a gallery ɗinsa, ba kamar da da idan ya kalleta saiyaji kewarta duk ya addabe shi, amma yanzu daya kalleta sai yaji sani haushi ya kamashi. Jefar da wayan yayi ya miƙe ya shiga toilet.


Angama sa lalle lafiya, Ango da abokansa sunzo sunyi ɓarin kuɗade masu yawa. Isma'il ya kasa daina kallon amaryar tasa saboda tsananin kyau datayi, ga wani sihirtaccen ƙamshin dake fitowa daga jikinta wadda ke ƙara haukata shi har ji yake kamar kar yabar wurin. Sunyi hotuna masu kyau, sannan ya aje mata bundle din One thousand guda biyu wai incase akwai abinda zata yi tunda ba waya suke ba. Godiya tayi masa sosai suka ɗan sha love kafin ya tafi da tarin kewarta azuciyarsa🥹


Sai karfe huɗu MJ yaga daman fitowa. Tuni Raihanah ta shirya tana jiransa a corridor din part ɗinsa. Har yanzu fuskarsa a daure take alamar akwai damuwa acikinta. Amma haka ya daure suka fita shida Raihanan. Suna zuwa asibitin data faɗaasa tace lallai sai ya rakata. Da suka shiga aka debi jininta tace mai shima kawai yabayar da jininsa shima ayi masa test ɗin dan ya ƙara tabbatar da genotype ɗinsa. Sarai yasan rigiman Raihanah idan ya tashi, dan haka he had no choice but to give in. Yana fita ta kalli wannan nurse din dasuka haɗa baki da ita tace tanason ta ƙarbi result in the next 30 minutes. Haka kuwa akayi, a reception suka zauna hira har ƙarfe biyar sannan nurse ɗin ta kawo musu result. Bata bari yagani ba, shima kuma bai damu ba tunda dama can yariga yasan genotype ɗinsa.

Washe gari akayi shirin dinner. Ango ya cakare cikin light blue shadda ɗinsa mai tsananin kyau, inda amarya kuma tasha adon Black princess gown Mai adon stones. Sunyi kyau kamar asacesu agudu. Mutane sunata fitowa ana shiga motoci wasu har sun riga sun kai venue dazaayi dinnern. Sai kuma wadda zai kai amarya da ango wata danƙareriyar Gwagon ne Black colour na ango shida abokansa suma wadda sukayi to match ɗin motoci. Saiga layin Gwagons gida biyar a tsakiya motocin sojoji kuma guda huɗu, biyu a baya biyu a gaba. Isma'il yakasa sukani sai kai komo yake yana Allah Allah afidda masa amaryarsa su yi chalo.


Can saiga tawagan amarya sunyi layi suna jerowa ƴan ɗagwas ɗagwas dasu gwanin sha'awa. Tunda Isma'il ya ƙyallara idanunsa akan Aneesa ya riƙe numfashinsa yana ayyana irin haduwar datayi. Wani abokinsa Captain Sadik ya ɗan taɓashi yana yi masa zolaya yace "man take it easy, she's all yours fa nan da ƴan awanni" harara Isma'il yayi masa yacigaba da kallon sarauniyarsa har suka ƙaraso inda yake. Hannunsa ya miƙa mata, itakuma tsabar kunya takasa saka hannun nata cikin nashi tana ɗari ɗari. Kamar Raihanah zatayi bindiga tace"kaii Ya Isma'il, ai ka bari aɗaura igiyar tukunna. Inka taɓata yanzu ka taɓa haramun" bai tanka mata ba ya budewa Aneesa ƙofan baya tashiga shima ya zagaya ya shiga tasa side din. Ƙawayen amarya kuma suka shige sauran motocin abokan ango aka fara tafiya in convoy.


An iso meenahs event center Kano, wurin yayi bala'in haɗuwa sai jin sautin romantic music kake yana tashi softly aciki. Wurin ya cika maƙil da jama'a, wadda aka gayyatar da kuma wadda ba'a gayyata ba. Batareda ɓata lokaci ba Dj yasa waƙar "perfect by King promise" waƙan dake tashe ayanzu. A hankali ƙawaye da abokan ango suka fara takawa cikeda class, inda amarya da Ango ke bayansu suma suna ɗan bada steps ahankali. Bayan sun shigo suka zauna a inda a tanada musu sannan aka fara gabatar da abinda yakawosu.


Na kasa samun nutsuwa tunda nazauna akan kujerar nan sakamakon jin ido ajikina danaketaji. Waiwaye nafara yi, karaf idona ya sauka kan mutum dake zaune ta can gefenmu akan high table ya kafeni da shanyayyun idanunsa wadda sukayi bala'in rikicewa zuwa wani colour dani kaina ban sansu ba. Ban san lokacin da bakina ya furta Masha Allah ba, gaskiya wannan bawan Allahn ya haɗu iya haɗuwa. Ya kai duk abinda ake nema awurin namiji ga duk macen datasan metakeyi, haɗuwar tasa har kusan kamar yafi Ya Isma'il ma. Sanye yake cikin Light brown getzner mai simple ɗinki, an mai irin babban riga na zamaninnan ne mai guntun hannu. Kansa yana sanye da hular yarbawa irin wadda ake lanƙwasa gefe ɗaya same colour da kayan jikinsa, wutsiyar gashinsa na kwance akan wuyarsa, duk da spec mai duhun haske yasa bai hanani kallon idanunsa ba, sosai bani ƙirjina ya buga. It's so unusual irin kallonnan, kamar wani magnet ne ke jawo idanuna gareshi. Na kasa ɗauke idonnawa akansa, shima kuma haka. Wani gentle murmushi ya sakarmin wadda ban taɓa gani ba tunda nake dashi a gidan Abby, hakan ya ƙara fidda baiwar kyau da Allah yayi masa, two sided dimples dinsa suka ƙara fitowa da kyau, idan ba idona ne ke yaudarata ba da sai ince kamar fatar laɓɓansa yayi motsi alaman akwai abinda ya furta wadda kinda looks like "YOU LOOK GORGEOUS". Da sauri na kauda idona daga kansa na mayar kan su Raihanah daketa tiƙar rawansu a cikin fili ita da sauran ƙawayena na makaranta. Murmushi na ƙaƙaro amma sam bansan meyasa ƙirjina yaketa bugun tara tara ba.


Yadda Mujahid ya dage yana kallonta sai ka rantse bai masan abinda ake yi awurin ba, Sultan dake gefensa ya taɓashi har ya gaji amma ko gizau dan uwannasa baiyi ba, daya juya ya kalli inda Mujahid ke kallo yaga idonsa ƙyam akan Aneesa ne. Shi abunma ɗaure masa kai yake yi, to wai idan dama MJ yanasonta meyasa baiyi ƙoƙarin winning heart ɗinta ba yabari har Isma'il ya riga shi. Hmmm shidai saidai ya zuba ido, amma kam idan Aneesa ce tayi mai nesa saidai yadda Allah yayi da lamarinsa.

Da aka kira ango da amarya suyi rawa, MJ kamar zaiyi bindiga, yadda yaga Isma'il ya dora hannunsa saman ƙugunta suna rawa kamar ya tashi ya yi masa ɗan banzan duka. Mace mai sa ƴan uwa faɗa 🙆. Lallai yanzu he can assure himself cewa ya kamu da tsananin ƙaunar yarinyar nan, he's head over heels for her. Irin son dayake mata ma baijin yataba jin haka akan Neehal, kodan saboda Neehal itace ta fara nemansa da soyayya oho. Amma wannan kam ya kusa rasa nutsuwarsa akanta, duk abinda yagani aknmanta ayanzu yana affecting ɗinsa seriously. Yana kishinta kamar me. Bai iya zama awurin ba kawai ya miƙe ya fita, fizgar motarsa yayi kamar zai tashi sama da sauri securities ɗinsa suka bi bayansa. Yadda yake tuki atitin Kano su kansu masu gagara saida suka matsa masa. Yana tuki ne aguje amma kuma cikin sukuni yake yi. Yadda yake overtaking motoci kai ka rantse race yake yi irin na film din Fast and furious. Ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida lafy. Bai gama tsaida motan ba yafito yabar ƙofan motarma abuɗe. Ɗakinsa yashiga ya wuce direct saman dressing mirror ɗinsa yafara zubar da kayan dake kai kamar zaiyi hauka dan kawai kishin dake cinsa akirji. Wani irin naushi yakaiwa mirror ɗinsa take ya tarwatse, saiga jini nabin hannunsa tundaga yatsa har guiwan hannu. Bai damu da haka ba, ya zauna saman gado ya kama kansa da hannu biyu, yanaji yadda kannasa ke sarawa kamar zai tsage gida biyu.

Sultan ne da Raihanah suka shigo ɗakinnnasa aguje cikin tashin hankali. Ashe tun lokacin daya bar wurin suma suka bi bayansa tareda security. Yadda sukaga ɗan uwannasu, hakan yasa suka shiga tsananin damuwa. Raihanah ce ta kawo first aid box takamo hannunsa, baimasan sun shigo ba saida yaji an riƙe hannunsa. Kallon Raihanah yayi da jajayen idanunsa, ya maida kallonsa wurin Sultan yace "wtf are you guys doing here. Kuje can wurin dinner din ɗan uwanku mana. Damn it" Sultan yace " and you think we'll live you in this condition. Hauka mukeyi. Why do you want to hurt yourself Ya Mujahid. Shimafa Isma'il ƙaninka ne, what do you think will happen idan yagano cewa matar da zai aura kakeso har kake hurting kanka akanta"? Kallonsa yayi da jajayen idanunsa yace "what else should I fucking do, yes I'm in love with her amd I know she's he's fiance but still, zuciya batada ƙashi. Ku nema mun mafita" Raihanah ta tace "Ya Sultan, wlh Ya Mujahid yafi Ya Isma'il son Aneesa, ni naga hakan a idanunsa tun ba yau ba. He's madly in love with her, nima kaina I'm not in support of her getting married to Ya Isma'il " sosai Sultan yaƙara shiga tashin hankali, wannan wani irin abu ne, saikqce Isma'il ɗin ba ɗan uwansu bane, shimafa zuciyace mai bugawa a ƙirjinsa, ya zaiji idan ƴan uwansa suna ɓakin ciki da abinda zai sameshi ma Alkhairi, har ga Allah he's not in support. Cikin son ya kwantar wa MJ da hankali yace " Ya MJ, shawarata kawai shine ka yi addu'a, Allah kaɗai yasan mezai faru tsakanin yau da gobe. Idan Allah yayi itace matarka we have nothing to do about it. Amma Dan Allah inaso idan har Allah yayi Isma'il shine mijinta, to ka fawwalawa Allah komai. Shima yasan da zamanka kuma yasan yadda zaiyi dakai" daga haka kawai ya juya ya fice daga ɗakin. Saidai Raihanah tagama dressing masa hannu sannan ta kwashe komai ta fitar. Ita dai birninta kawai Babban Yaya ya mallaki Aneesa, kuma shine burinta Allah ma zai taimaka mata wurin tabbatar da hakan.


Sai ƙarfe goman dare aka tashi taron dinner. Bayan sun dawo gida kowa agajiye akayi wanka sannan suka bi lafiya gado. Aranan da wani irin zazzafan zazzaɓi Mujahid ya kwana. Harta mafarki saidai yayi wai gashinan an daura auren Isma'il da Aneesa, wai a masallaci ya dinga yi musu kuka yana cewa ba'a yi masa adalci ba😂.


Karfe sha ɗaya ne ɗaurin auren, dan haka tun ƙarfe tara su Abby suka gama shiri. Su Mamy anata zirga zirga abincin da za'a kai wurin daurin aure. Raihanah da sassafe ta gama shirya plan ɗinta. Ƙarfe tara da rabi taje part ɗin Abby da papper ahannunta babu wanda taganta. Duk da bugun da ƙirjinta keyi hakan baisa tayi ƙasa aguiwa ba. Fortunately kuwa tasamu babu kowa a falonsa, papper tagani ansa cikin envelope, da sauri ta ɗauka ta bude tana addu'ar Allah yasa abinda take tunani ne. Hamdala tayi ganin genotype result ɗin Isma'il ne da Aneesa, da sauri ta dau na Isma'il tasa na Mujahid data riko, sai sunan ango da amarya wadda aka rubuta a different papper wadda za'a bawa Imam mai ɗaurin aure, shima tayi saurin rubuta wani inda tasa sunan Mujahid da Aneesa instead of Isma'il. Tana gama haka ta yi addu'a sannan ta aje da sauri tafita apart ɗin , har zufan wahala ta haɗa tsabar rashin Gaskiya. Abby kuwa yana fitowa bai bude envelope din ba ya ɗauka yasa a aljuhu sannan suka fito sai masallaci.


Nan kuwa Aneesa tunda ta farka da safe takeji yadda zuciyarta keta bugun uku uku.har lokacin da ake yi mata makeup ma kasa natsuwa tayi. Sai duba time takeyi, duk bugun da agogo yakeyi tik tok tik tok ji take kamar da bugun zuciyarta yake tafiya. Ta rasa farin ciki take ciki ko kuma fargaba.


An cika a masallaci sosai, ba'a ɓata lokaci ba kuwa aka shiga masallacin. Bayan anyi duk wasu abubuwa, su Abba ansha kwalliya cikin babban riga sai faman washe haƙora yake tunda yaga Mujahid, shifa yariga ya gama sawa ransa har yanzu cewa MJ shinee angon. Balle kuma yadda yaga yasha kwalliyan farin shadda kamar angon kuwa.

Envelope din Abby ya ciro ya mikawa Imam, shiko limamin daya karanta yaga ai sunan wadda ke cikin result shine yake cikin paper da aka rubuta, yayi murmushi sannan yace akawo sadaki. Da sauri Isma'il ya ciro bundir ɗin fice hundred guda uku ya aje gaban Limami, ga shaidu ga komai da ake bukata. MJ ya rufe idanunsa gam babu irin addu'ar dabaiyi ba azuciyarsa, ji yake idan ya rasa wannan yarinyar tabbas zuciyarsa zata buga. So masifa ne🙆🥹

Cikin sukuni Limami yafara magana kamar haka "akan sadaki dubu ɗari uku, da kuma shaidu kamar yadda addini ya wajabtar, an ɗaura auren Aneesa Zaid Ibrahim da angonta Mujahid Abdulazeez Isa".....


Like
Comment
Share🙏🙏

🌷 RAYUWAR ANEESA 🌷


Reemah ✍️


PG 61_65

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Cikin sukuni Limami yafara magana kamar haka "akan sadaki dubu ɗari uku, da kuma shaidu kamar yadda addini ya wajabtar, an ɗaura auren Aneesa Zaid Ibrahim da angonta Mujahid Abdulazeez Isa", gaba ɗaya mutanin masallacin suka ɗago suna kallon imami banda Mujahid wadda ya ƙara runtse idanunsa gam bayaso ya buɗe yaga mafarki yake yi. Abba dasai washe haqora yake yana girgiza kai saboda ƴarsa ta auri shugaban EFCC Mujahid ABDULAZEEZ Isa. Abby ya kalli imami yace "Allah ya gafarci Malam, an samu matsala fa, ba Mujahid bane angon" da mamaki imami ya kalli Abby yace "subhanallah, toh ai gashi sunansa ne acikin wannan papern da kuma result ya akayi haka" da sauri Abby ya ƙarbi takardan ya duba, aikuwa sunan Mujahid ne toh amma ya akayi hakan ya faru, kuma wannan rubutun ai ba nasa bane, kamar canzawa akayi. Cikin tashin hankali Isma'il yace "Malam baza'a iya warware auren ba"? Girgiza kai imami yayi yace "sai dai kayi haquri amma aure yariga ya ɗauru, sai dai idan shi angon yaga daman ya saketa" gaba ɗaya masallaci ya amsa da sallallami daga bakin mutane. Wannan ga wata sabuwa inji ƴan caca. Abby ya kalli Mujahid da har yanzu kansa aɗuke yake ya kasa ɗagowa ya taɓashi cikeda ɓacin rai, don shi yariga ya gama ganin cewa shi ne yayi wannan abun. Ɗagowa MJ yayi, su kansu saida suka tsorata da halin dasuka ganshi aciki, idanunsa sun ƙanƙance sunyi jaaa kamar ma hawaye ne acikin idon. Abby da ransa yariga yagama ɓaci ya ce "me kake nufi damu, aure wasa ne? Hauka kakeyi da zaka ci amanan ƙaninka ka aure masa mata? Mujahid yaushe kazama haka, Ni zaka tozarta bainan jama'a" shi kansa MJ yakasa motsa lips ɗinsa, to be sanma mezaice ba. Gaba ɗaya wannan turn of faith din baisan ya akayi lamarin ya juya ba. Kallon Isma'il yayi wadda shima kallonsa yake idanunsa sunyi jaaa yana jan zuciya, ko bai faɗa ba idon Isma'il yanuna cewa shima ya yarda MJ yaci amanarsa. Juyowa yayi ya kalli Sultan dake gefensa yaga shima ya kafe shi dana mujiya, he's dead. Asanyaye yace " Abby wlh bansan ya akayi hakan ta faru ba. Kuma meyasa zan ci amanar ɗan uwana fisabilillah" bai gama rufe baki ba yaji Sultan yace "because you love her" sai kuma kaji Masallacin ya sake ɗaukewa da salati, wasu har sun fara ƙuskus. Shock yakama Abby da Isma'il, MJ yanason Aneesa? Yaushe hakan ta faru? Miƙewa Abby yayi azafafe ya kamo collar din MJ ya miƙar dashi tsaye yace "yau zan nuna maka cewa na isa dakai. Yanzu nakeso ka saki ma ƙaninka matarsa" ko gizau Mujahid bai yi ba, Abby ya ƙara jijjigashi gana maimaita kalmar ya saki Aneesa, amma still ko motsi bai yi ba kamar mutum mutumi haka yakoma. Ko ƙasa da sama zasu haɗe bazai saketa ba, dama Allah ne ya qaddara cewa itace matarsa, sannan wadda ya haɗa plan dinnan duk inda yaganshi ba ƙaramin gift zai bashi ba, kuma sai inda ƙarfinsa yaƙare wurin protecting dinsa. Ɗaukan mari kakeji tassss, gaba ɗaya saida masallacin ya ɗauka. Abby ne ya wankeshi da wannan marin yace " Are You a human or a devil. Bakada zuciya ne? Zaka kalli ɗan uwanka yashiga wani hali saboda tsabar son zuciya, yaushe ka zama haka Mujahid" Abba da kwata kwata abun ma ya ɗaure masa kai, yadda yaga yanayin Mujahid tabbas in za'a cire son kai wlh yaron yana ƙaunar Aneesa, take yaji tausayinsa ya kamashi. Miƙewa yayi ya cewa Abby " Alhaji kayi haquri, amma Ni tun ranan da akazo neman izinin ƴata Ni Mujahid naba mawa, don tun ranan danaganshi na kwaɗaitu da shine ya zama mijinta. Gaskiya idan baida niyyar sakinta kar ayi masa dole" fuuuu Isma'il ya wuce ya fita daga masallacin abokansa suka bi bayansa da gudun gaske. Kafin su iso wurinsa har ya shiga matarsa ya figeta aguje, cikin matsanancin Tashin hankali suma suka shiga nasu suka bishi.

Acikin masallaci kuwa, duk yadda za'ayi a tausasa zuciyan Abby amma hakan yaci tura, yace Abban Aneesa shima yaci amanarsu, ai Isma'il ne ɗansa daya nema masa auren Aneesa. Hawayen da MJ yaketa tarewa saboda kar girmansa ya zuba a idon dubban jama'a amma ya kasa, suuu sai gashi suna bin junansu ɗaya bayan ɗaya. He's never prayed for a day like this, ranan da zaiga tsananin ɓacin rai afuskar Abby saboda shi, amma he's also helpless,tsakani da Allah bazai iya sakin yarinyar nan ba. Ai dama can Allah yayi shine mijinta. Bakinsa na rawa ya kamo hannun Abby zaiyi magana, Abby ya buge masa hannunsa yace "meet me at home. We're not done with this" ya wuce yabarshi,durƙusawa yayi kan guiwowinsa kansa aƙasa, Imam ya taɓa kafaɗarsa yace "kayi haquri, wannan jarabawa ce, in Allah ya yarda zaka cinye ta da sakamako mai kyau. Idan kanason yarinyar nan, kada kabari arabaka da ita komai daren dadewa". Ahankali aka fara watsewa daga masallacin. Shine ƙarshe, asanyaye ya fito ya shiga motarsa driver yaja suka bar wurin.


Horn yake bugawa ba kakkautawa, cikin sauri wani soja ya buɗe masa kofar. Yana fitowa ya wuce direct part ɗin Hajja, ko kula da mutanen daketa ango ango baiyi

13 / 24