🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* NA SAKE ZUWA DA SABON TSARI, SABUWAR TAFIYA, SABON AL.AMARI........ NI CE YAR MUTAN NIGER NA KAWO MAKU SABON NVL DINA WANDA A KASATA NAKE MAI TAKEN *BAK'A CE* bak'a ce na dauke da darusan rayuwa, dole ya nishadantar, ya baku mamaki, ya saka ku tunani..... *BAK'A CE* zai zo da kadan daga cikin al.adun yarena *BUZANCI* da kuma *TUBANCI* ..........ku biyo ni ku sha labarin *BAK'A CE* TALLAH TALLAH TALLAH *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣ *WANI YANKI NE CAN WAJEN AGADEZ CIKIN JAMHURIYAR NIGER mai sunna TIMIYA*, inda buzaye ne ke rayuwa a garin indai ka ga bakuwar fata to lale bako ne ya zo kuma juyawa zai yi , A kauyen nan basu da ruwan pampo sai fan take, wuta bata kai can ba , Gari ne mai tarin ni.ima , albarkar noma garake , sannan mota bata shiga domin can cikin sahara ne sai dai a hau rakumi a samu a shiga cikin Timiya Yan mata ne laye su hudu, Cikin ukun nan kowace ta kala tamkar ka lasheta dan kyau da daukan hankali sun sha digo digonsu na buzaye da katanga , sai daya a gefensu wace kanta ke sade kasa jikinta na dan rawa rawa hanayenta kawai ake ganni bakin kirin da yafen mayafinta na turkudi (tufafin buzaye ) Shigowa wani datijo ya yi yana dan dukawa dan tsayi ne da shi, da hannunsa yake yiwa mutanen dake bayansa nuni da su shigo domin bashida hausar kirki a bakinsa Yana dago kansa ya hangota a cikinsu, ya juyo da dan sauri ya ga mazan nan har sun zauna Rai bace ya nufi dakinsu wajen uwar yaran wato matarsa yana zuwa ya daga hannunsa ya dungurewa yar datijuwar kai ransa bace cikin yaren buzanci ya ce" ban hane ki turo min da wannan bakar yar taki ba? Na aurar da yaya hudu saura uku na cire wannan bakar a yayana, na sha fada maki ni a danginmu ba baki aman kika tashi kika haifo min baka? Na yi na yi ki fada min gaskiyar waye ubanta kin ce ni? Kuma dan bakin ciki an samu elhazawa masu son auren yaren kin tunkudo (turo) mini da ita ko? Bata ce komai ba sai sada kai da ta yi, har ya gama babatunsa ya juya Yana komawa ya damki hannunta ya jata kiiiii suna shiga ya hankadata ta tafi tagataga ta duke nan kusa da gadon karagar mahaifiyarta kanta sade, ya aibatata sosai kafin ya juya ya koma wajen bakinsa Kanta sade hawaye ya ziraro mata, ta dago a hankali ta kali mahaifiyarta da idannuwanta ke rufe ruf tana jin yanda zuciyarta ke suya Murya a raunane ta ce" *ANNA* (wato mama) Bata bude idannuwanta ba, bata amsata ba Ta dan jima a haka kafin take mikewa ta dage rufar da ta yi tana kallon mahaifiyarta da wani irin yannayi, a gaskiya a jikin wannan matashiyar budurwa banda idannuwanta ba wani abu mai hasken fari domin kuwa tana da baki ga kuma tufafinta mai rinar da fata ne wato turkudi Mamanta ta dago ta bude ido a karo na farko, murya shake cikin yaren buzanci ta ce" kal ki ce komi, ki yi hakuri kawai A hankali ta juya dan ruwa gidan baba tsoho.... Ku biyo ni garina, *TIMIYA* domin a Niger nake.... ......taku har kulun YAR MUTAN NIGERSAJIDA 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2⃣ A hankali take tafiya tana dan rabewa, da ta hango gugun yara sai ta labe har sai sun fice idan kuwa wasa ne suke dole sai dai ta canza hanya domin irin wulakancin da mahaifinta da wasu a cikin yan uwanta ya sanya har jama.ar garin ke wulakantata suma suna dubanta daban cikinsu.... A hankali ta karyo kwanar runfar baba tsoho Sanda take dan karasawa domin bata son haduwa da almajiransa tun bama Ali ba wanda ya so hada shi da ita ya ci mata mutunci yayi mata kwakwaran kashedi na koda wasa kar ta yarda ta nuna tana son sa domin shi dama ya shigo garin Timiya ne dan ya samu buzuwa fara ya aura..to tun daga lokacin sauran almajiran ke tsokanarta suna fadin ta Aliyu *BAK'A* zaune yake cikin bukarsa, rawani ne a fuskarsa kwaurin hannun sa da na kafarsa ake gani , hakan zai nuna maka tsohon mutun ne, domin fatarsa du ta yi yaba haka gashin dake kwaurinsa du sun yi fari sol sol da su Waje daya kawai yake kallo, a zuciyarsa kuwa ya afka tunanin yau ina ta yi? Ya aka yi bata zo ta dauki karatu da safe ba? Bata da kawa, bata da wani mai rabata a jikinsa, mahaifiyarta kanta bata mugun sake mata dan tana tsananin tsoron mijinta a kan yarinyar Shi kam yana cike da zulunmin abinda ya sa bata zo ba A hankali ta daga kasarin dakin ta yi masa salama Murmushi ne ya subuce masa yana kallonta kafin ya amsa salamarta karasawa ta yi tana dan tatare tataren dakin ta kai dubanta wajensa, cike da kaunar tsohon sannan idan tana tare da shi takan ji ta wani iri, bata jin tsoronsa sai soyayarsa, tsohon shi ne kawai mai yi mata murmushi a duniya, Dan murmushi ta sakar masa ta ce" SOFO (wato tsoho) Shima murmushin ya yi, ya dan nunota da yatsarsa, Ta karasa ta duka kasa ta ce" ta gode (gaisuwa kennan) Turkudin kanta ya shafa a hankali kafin ya ce" Alharasssss Mikewa ta yi ta gama tatare masa dakin ta dauko tsintsiyar kabar da ta yi da kanta dan share dakins ta shashare ko.ina ta dan dage kasarin ta dauki tulun ruwansa ta fice Murmushi ya yi, ya bi ta da kallo....a kasan zuciyarsa ya ayanna" Allah ya nuna min farin cikin ki kafin na koma gareshi Tafe take da tulunta cikin nutsuwa, tana zuwa ta duka wajen diban ruwan , wani dan kewaye ne aka yi shi ba rijiya ba, shi ba teku ba shi dai ruwan ana jayo masu shi ne, sannan kalar ruwan jajajir ne sai kanshin laka , akoy ruwa masu kyau sai dai idan ta yarda ta je wajen sai dai ta dawo ba ruwan ba tulun domin du yawancin yan matan garin can suke zuwa dibo ruwa su kuwa sun ki jinnin ganninta a wajen Sai da ta cika tulun ta mike ta gyara bakin zaninta da kyau ta daga ta dora saman kanta Yanda ta bar shi zaune haka ta dawo ta tarar da shi Ta nemi wajen Tulun ta ajiye tana dubansa cikin yaren buzanci ta ce" baka gajiya da kallon waje guda? Bai bata amsa ba sai mika mata allonta da yayi yana nuna mata wajen zama A hankali ta zauna ya ci gaba da koya mata karatu wanda sosai ta nisa kuma shine malaminta tunda ta san shi Suna gama karatun ya ce" menene tambayarki ta yau? Ta yi tsai tana kallonsa, can ta nisa ta ce" sofo, shin mutun mai bakar fata laifi ya yi aka halice shi baki? Da sauri ya kallota, ganni ya yi kanta a sade, tana faman murza hannayenta .....yarinyar akoy zurfin ciki sosai aman wani lokacin sai ta fadi dan abinda ke ranta domin tana gannin abubuwa masu firgitarwa a rayuwarta Hannunsa ya daga, murya a sanyaye ya ce" ko daya mutun baki da fari du daya ne a wajen Allah Dara daran fararan idannuwanta ta dago ta sauke kan nasa da sukai dan ja sannan du sun yi yaba irin na tsohon mutun, hawayen da ya taru a idannuwanta ta yi iya kokarinta ta mayar da su , daga haka bata kara komai ba, bata bari ta yu kuka ba ta mike tsam ta fice ba tare da ta kara kalma daya ba Ajiyar zuciya ya sauke, yana tir da halayen Agali, Agali bashi da hankali da tunani, dan kawai Allah ya yi yarinya an haifeta bak'a cikin y'ayanka sai ta zama abin kyama abin kyankyami abin wulakantawa? Ita ta halici kanta ne? Ta jima tana tafiya kafin ta karaso gidan iya mai siyar da nono Har kasa ta duka tana gaisheta Iya ta amsata kafin take cewa" kin ga nonon nan yana yi min wuya, ban san me yasa idan kin dauka cinikinki baya fice dala dari da ashirin .....sai dai ki maido mini shi haka du an motsa shi sannan in baki salama ni kam yau ki yi hakuri na sararma masu zuwa gida sara, kinga daman tausayin ki yake saka ni na baki dan ki samu dan kudin kashewa Kanta a kasa ta ce" ki yi Hakuri iya, zan kara kaimi wajen siyarwan ki zuba min kadan yanda zan iya siyarwa Kanta ta girgiza ta mike ta dauki kwarya ta zuba mata nono dan madaidaici ta mika mata, ita Allah yana ganni dan tana jin tausayin yarinyar ne aman tana da masu siyan nononta a hannu a hannu domin shannunta suna da yawa Dauka ta yi ta fice a gidan, tana tafe tana jin wata irin juwa na daukanta, bata karya ba, bata ci komai ba sai yanzu ta tuna Ajiyar zuciya ta sauke ta samu gu ta dan rakube ta daga kanta sama ta afka tunani Mu je zuwa ci kin labarin *BAK'A CE* 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3⃣ Suna tafiya ya shigo dakin, Yanda ya barta tunda ya dungure mata kai haka ya tarar da ita Ransa bace ya nunota da yatsarsa ya ce" ke, A hankali ta dago kanta ta sauke kansa tana kallon sa Y.ayana biyu sun samu miji yan albarkana Wani abu ta hadiye a makogwaronta, a hankali ta ce" wannan karon wa ka siyarwa yaran? Da mamaki yake kallon ta, mayar masa da magana ne ta yi? Shi? Da izgili ya karasa kusa da ita ya nunata ya ce" ke balagazar mace, ke har kin isa ki dube ni ki fda min cewar ni ina siyar da yara? A me kika dauke ni kennan? Matsiyaci? To bara na tuna maki a gidannan daidai da sansannin ( tabar buzaye) da zaki gumtsa sai kin taba tawa ba zaki iya siya ba dan bakya saye bakya saidawa zaune kike dabar ta.kar duwawu komai sai an yi maki, To yaranna sun samu mazaje sun yi min kyakyawan tayi! Kuma na fada maki idan har na aurar da yaran nan gaba daya ki kuka da kanki ke da yarki dan kuwa ba zai yiwu ya kasance ina ciyar da yar da ban yarda cewa tawa bace bama Har ya gama bata kara tofawa ba , ya juya ya fice a dakin A hankali ta zauna kusa da mahaifiyarsu, itama farinta har daukan ido yake, Hannunta ta kamo ta rike gam ta ce" zan so ki fada mana tarihinmu kafin muma mu tafi kamar su aunty a daina jin labarin mu, ba labari ba aike ba wani motsi.....Allah kadai ya san halin da suke ciki idan suna raye! Ba yace auren wata biyu kawai zan yi, idan na cika wata biyu na kwaso masa kudade na dawo ko ya sake ni ko bai sake ni ba sarki zai hana shi shigowa garin ........ ki daure ki fada mana tarihin rayuwarmu Anna (mama) Su waye mu? Ina ne asalin asalin mu? Su waye dangin mu? Bamu da kowa ne sai mu da ku? Idan muna da mai ya sa ba wanda ya taba zuwa inda muke? Ina son sani ANNA Jajayen idannuwanta ta sauke kan *Gaishat*, wai ita nan mai damar ce domin ita bata hantarar Bak'A, sannan tana kamanta bin iyayen su ba kamar sauran ba Kwace hannunta ta yi ta hade rai ta yi mata nuni da kofa Ta san kan zancen dan haka ta mike ta fice daga dakin Kallonta yake tunda ya kirayeta ta zo turakarsa tana zuwa ta tube du wani abin da sunnansa sutura a jikinta, ta tsaya masa a gabansa wato gashi ka yi ka gama na koma Kansa ya girgiza kafin yake tsareta da idonsa, ya juyar da kansa ya kuma kallota Can ya ce" Nadia, haka zamu yi ta rayuwa? Ke ba zaki taba saukowa ki bani kulawar da nake bukata ba? Saurin zubewa ta yi kasa ta ce" ka yi hakuri Uban gidana, ban san zan bata ranka ba kar ka hada ni da Ba (Aba) Idannuwansa ya lumshe, a gaskiya Allah ya jarabe shi da matsanancin son yarinyar, Yarinyar ce ko a cikin bugaje (buzaye) ta fita daban, ta hadu iya haduwa ko ba wanka Nadia mai kyau ce, dalilin haka ya amshi tayin aurenta da Ba dinta ya yi masa bisa sharudan kawar da ido da toshe kunnuwa kan karansa da za.a kawo a cikin garin kan yanda yana tafiyar da rayuwar gidansa, aman ya kasa samun nutsuwa da ita........ya kasance komai zatai masa tana yi ne dan tsoro ba dan soyaya ba A hankali ya dagota ya jata zuwa ainahin turakar domin yanda yake kwakwarta shi kansa mamaki yake, yanzu dai shekara biyar da aurensu bayanta ma ya kara auren mace biyu ya saki gudar aman har yanzu ta kasa fice masa a rai a kulun yana mai jin zumudin kasancewa da ita.....aman ita ta kasa kontar da hankalinta ko dan matsayinsa na sarkin garin ta murza mulkinta aa tana rabe rabe ne a gidan mijinta Nadia kennan babar yar *BA* Ke kin san nawa ne million daya? Jika dari dari har goma fa, an ce Gaishat har million goma sha hudu mutumin ya bada kudin aurenta, Ke ki rufe min bakin ki, ke fa haka birge ki yake ko? Kina ganni yanda yake aurar da yayan nasa daga sun tafi shikennan ba labari, kudin ya zo bai yi masa anfannin komai ba, daga an kwana biyu ya kashe sai kuma ya fara harin wata a cikin y'ayan nasa, ai sun kusa karewa zamu ga kuma idan wada ya tsanar zai yi shelar ya siyar Mahaifiyarsu da ta shigo da Buzu (salaya) a hannunta ta kale su ta ce" ke Amina, ki tashi maza ku je ku yi sallah, wannan maganar kun cika yinta bayan kun san ya zama abin gasa a garin nan, sai kun jaza min abinda ya fi karfina ko? Kuma da hakan bata faruwa da ku dan Ba din ku bai yarda da hakan ba, ku kun fi kowa sanni gidajen da basa haka basu fi a kirga a garinnan ba aman zaku zauna mamakin kwaya daya? Kowa ya yi da kyau kai nasa! Ku mike ku bace min a wajen nan kar ku yarda maganar nan naku ta yi tsayi ya zo ya tsige mu baki daya domin ku kun san waye shi ! Sumui sumui suka fice dan zuwa yin alwallah su gabatar da sallah Sai yama sosai ta kamo hanyar gida, Tana tafe ne tana dan jin dadin yannayin garin domin sanyin yama ya fara busawa sosai ita kuwa gwanar son sanyi ce sosai Ba ita ta kai gidan iya mai nono ba sai kusan magariba, ta kai mata cinikin inda iyar ta bata dala ashirin da biyar ta yi godiya ta mike Har ta kusa fita iya ta kirayeta ta dawo Ta ce" kin ga , ga abinci nan ki dauka ki ci mana ni na ci na rage, sauran ki yi min halin naki sai na tabatar kina kyankyamina ne na san irin matakin da zan dauka Fanata ce ta fito daga daki, kmar kulun cikin mahaukacin gayu mai gigitar da jama.ar garin ....Fanata dai y'a ce a wajen yar uwar iya wace ke aure a cikin garin agadez, mahaifin fanata Babarbare ne shi ya sa sunnanta ya fita daban , A da fannata ta kasance ita ba fara kar ba ita ba baka ba duda mahaifiyarta farar buzuwa ce, Aman kasancewarta a can cikin birni, da taraya da kawaye ya saka take shafa mai wanda ya mugun karbarta ta yi fari kar kar kar harma ta fi maman nata farin, Fannata akoy kyau ga iya daukan wanka Tana son garin timiya a rayuwarta domin gari ne mai cike da ni.ima Tunda ta fito take kallonta da mamaki, Dubanta ta mayar wajen Iya ta ce" iya, yarinyar nan mai maki tallah ce ta girma haka? Iya ta ce" eh ita dai ce Fannata ta yatsina fuska ta ce" to aman har yanzu sunnan da ake kiran nata da shi ne? Wato *BAK'A*? iya ta amsata da kai Fannata ta kallo wajenta ta kuma kallon iya ta ce" menene sunnanta na gaskiya ne ita wai? Iya ta kalli Bak'a, ta kalli Fannata, ta ce" sunnan Hajia ne da ita, karfi da yaji Ba dinta ya mayar da sunnanta Bak'a har ake mata kiranye da haka Da mamaki Fannata ta karasa kusa da ita tana kallonta, Yarinyar fa nata wani tsararan kyau, boyeyen kyau, duda mugun bakinta ga bakin turkudi na bugajen kauye🙈🤣, ga dati da take fama da shi, aman ita tana hango wani al.amari a tatare da yarinyar, to aman me zai hana ta shafa mai itama? A sanninta ba bakon lamari bane buzu farinma ya shafa mai, kai ba buzu ba yanzu abin ya zama larabawama mai suke karawa shi yasa zaka gan su wani farfarfar da su sunna daukan ido, ba sai dan duniya ke shafa mai a duniyarmu ba, mun dauki mai mun mayar da shi abin kmgyaran fata, ra.ayi ne shafa shi idan ka shafa ba mai yi maka kallon dan duniya a karkarar mu Abimcinta take ci kanta a sade tana ji yanda Fannata ke aikin tambaya a kanta, tsoro take kar a je mugun kyankyaminta kamar yanda mutanen garin ke yi ya saka take son sannin ko ita wacece dan ta kara samun damar ci mata mutunci, hakan ya sa take sauri dan ta gama cin abincinta ta kara gaba , so take ta
Gidan littattafan Hausa na zamani
AN