Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 12 / 27

mamaki take mutane a cikin wannan allon suna ta magangannu suna komai abinsu, har bayan take lekawa wai ko zata gansu ta nan ta sha yiwa Ayya tambayar kuma yanzu idan suka fito fa? Yanzunma Ayya ta kuna mata wakokin dandali, kalo take tana ta sakin murmushi kumatunta na lotsawa dimple har biyu a fuskarta, wani wajen sai ta rufe fuska idan namiji ya fara rawa, sosai take dan gane hausar da suke tana kara koya ta nan, shi kuwa abin na birge shi, sannan ya yiwa Ayya tambayar wacece ita? Da french, ayyarma ta shiga kora masa bayanin komai.....ya sha mamaki, ya ji wani lamari a tare da yarinyar, yana son inganta rayuwarta...... Wannan kennan. Wardugu na zuwa ya ce" tashi mu je, Mu.azam ya mike ya bi bayansa suka nufi dakin Mu.azam din , Ayya ta yatsina fuska a ranta ta ayanna mai yiwuwa ya yi fushi๐Ÿคฃ. Suna shiga Wardugu ya ce" c'est bon, maintenant tu me dit la veritรฉ sur ce qui t'arrive ( ya isa, yanzu sai ka fada min abinda ke damunka!) Mu.azam ya tsare shi da kallo, a hankali ya zauna saman kujera yana kallon Wardugu, Wardugu ya karaso ya zauna shima, ya ce" ka san dai kana iya yiwa kowa karya banda ni! So ka fada min tun kafin na hasala Mu.azam, wata irin cuta ce wannan wanda baka taba yi a gabana ba ta zugeka haka? Me ya samu kasan gashinka ? Kana tunanin ban lura ba? To gashinan kasan gashinka a aske! Sai ka janyo sauran ka rufe, du ka zama wani iri? Ka duba fa ka gani wandon vest ne a jikinka ka dauko riga rose (pink) ka saka sai kace mace? Hannunka ba agogo, yannayinka na nuna kama tare da damuwar da ta fi karfin furucinka, ina hawa aiki karfe goma na dare, ka fada mani na juya! Mu.azan da wata irin murya ya ce" Cancer du cerveau ke damuna..... (cancer ta kai) Wani irin tsam Wardugu ya yi, ya kaste maganarsa a lokacin da bai shirya ba, Zurbat ya mike yana duban Mu.azam, hannayensa duka biyu ya saka ya dafe kansa, baya baya yake ja ya...... ๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ *BAK'A CE*๐Ÿซ๐Ÿซ๐Ÿซ Na *SAJIDA* *ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ____________________________________ *๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2๏ธโƒฃ4๏ธโƒฃ Wani irin tsam Wardugu ya yi ya katse maganarsa a lokacin da bai shirya ba, Zurbat ya mike, duban Mu.azam yake da wani irin kallo, hannayensa duka biyu ya kai saman kansa ya shiga yamutsa gashin kansa , baya baya ya shiga yi da kafafuwansa, bai fi taku hudu ba ya tsaya ya juya ya juyo, hanunsa ya jimke ya daki dayan da shi, A hargitse ya dawo wajen Mu.azam, so yake ya zauna aman ya kasa...... murya a cinkushe ya ce" yaushe, yaushe? Yaushe ka sani? Ya aka yi ka sani????? Mu.azam ya mike yana dan sakar masa murmushi yana kokarin ganin ya saka shi ya dan nutsu aman ya kasa kama shi, dan haka ya tsaya yana kallonsa ya ce" Wardugu, har na kai wajen da gashina baya zama fa, ya jima a jikina ciwon ....nima ina gannin alamu a matsayina na likita sai dai ina turewa na ki maida hankali, ya kai ni sai na suma na yi awani a sume, na daina shiga tiyata ba yau ba, ina zuwa asibiti ne dan kar imanina ya yi rauni, ina zuwa ne dan haduwa da wa.inda suka fi ni damuwa, ina yi mana adu.a a tare, Wardugu idan na jima a gabannan na kara shekara hudu a duniya,... "C'est faut!,(KARYA NE!) Wardugu ya fada tun karfi yana nuno Mu.azam da yatsarsa, Taku ya yi wajensa ya ce" idan kai ka fada, idanma wani sakaran likitan ya fada na fada karya kuke, karya ne Mu.azam, ku baku isa ku fadi abinda Allah ya boye ba, ba wani mahalukin da ya san ranar mutuwarsa , mutuwa bata shawara, bata fadi sai an ganta, mutuwa na zuwarwa bawa a lokacin da bai sani ba, sannan a lokacin da bai shirya ba domin a kulun bawa baya cikin shirinta, Wardugu ya yi shiru, gaba daya ji yake jikinsa ba karfi, a hankali ya kai kasa ya zauna nan kasa, waje guda ya tsurawa ido kafin ya ci gaba da fadin" sannan Allah kadai ya san gawar fari, ba wai dan wane bashi da lafia wane lafiarsa kalau za.a ce sai marar lafiar nan ya rigayi mai lafia rasuwa, Mu.azam da ya karaso , a hanakli ya duka ya dora hannayensa saman na Wardugu, murya a raunane ya ce" ban taba tunanin wani abin zai girgizaka haka ba Wardugu, menene a ciki? Ko dan abin ya shafeka ne baka so ka ji? Wardugu ka yi hakuri, ka daina tayar da hankalinka kan maganar nan, nima na fada maka ne dan na ji sanyi sannan na samu wanda ya san ciwona, Wardugu ka.... Bai tsamaci lamarin ba, sai jinsa ya yi jikin Wardugu, Wardugu da dan ya tsokane shi yake ce masa sai sun yi gaisiwar larabawa, yau gashi da kansa ya rungume shi, Murya a cunkushe wardugu ya ce" bana so bana so..... Kasa karasawa ya yi kuma ya saki Mu.azam ya mike ya fice da wani irin sauri ....... A hankali Mu.azam ya hade kansa da gwuiwarsa, , tabas mutuwa Aya ce, duk mai rai mamaci ne, tabas ba karamar ni.ima bane da Allah ya boyewa bayi ranar mutuwarsu, shi gashi, hasashe ne aka yi, likitoci sukai a kansa, rayuwar turai da za.a fada maka komai kwaro kwaro ne, sun kiyasta lokacin da suke gani zai kai a raye a doron kasa sun fada masa, wai basu fada masa rana da lokaci bama aman gashi du ya firgice ya fice a hayacinsa, Idannuwansa ya lumshe yana jin saukar zazafan hawayensa, zuciyarsa ce ta ci gaba da fada masa" ka zo kasar nan je dan ka kara ninninka ibadunka, ka kara yawaita sadaka da aikata abubuwan alkhairi, ka zo kasar nan ne dan ka samu ka raya sunnar ma.aiki idan Allah ya nufeka, mutuwa kowa yi zai yi Mu.azam, ka daina karaya ka yi hakuri har Allah ya yi ikonsa a kanka, Wayarsa ce ta dauki kuka ya kai dubansa wajen wayar ya mike daga tsugunnin nan ya daukota ya daga, Docter me ka yi kennan? Na zo wajen aiki na tarar da takardar barin aikin ka? Saboda ni kake son yin nesa da aikinka ko saboda na fada maka ka yi hakuri a yi maka aikin nan? ...... Kansa ya shafa yana sauraronta, masoyiyarsa wace ke nuna masa kauna, tana son Mu.azam tamkar nama daya na cikin miya, tana son kasancewa da shi, labarin rashin lafiarsa ya gigitata har itama ta kwonta, nan ne ta yi ta fadi tashi har ta gano ana iya yi masa aiki a cire wajen, aman aikin ne keda hatsari sosai, yana iya samun tabuwar tunaninsa, ko ya kasance ya shiga coma wace shigekan daga ita ba zai tashi ba, ko idan Allah ya aminta ya yi jinya sumul ya samu sauki aman shi ya kara kai da kasa ba zai harda a wani buda kansa ba a dawo kuna ba wani succes, MU.azam ya ce" Aisha, Aisha ta ce" ka dawo na roke ka, ka dawo tun kafin lokacin a iya yi maka aiki ya shige, Ki yi hakuri ki daina kirana Aisha, Mu.azam ya fada da sanyin murya, ya ci gaba da fadin" nawa kuka yiwa aikin? Nawa suka fita? Karshe dai du yawanci daga dakin aikin za.a fitar da su basu san inda kansu yake ba, zasu dawo kulun a jone da inji yana taimaka masu wajen numfashi, da na.urori masu basu abinci, da masu jan fitsari da masu karban kashin su, zasu dauki lokaci a wannan yannayin har ya kasance ko a cire masu na.urorin ko dare daya su tsaya sun daina aiki, su basu dauki kadara suka yi ta ibada suna shinfida a makwoncinsu na gaskiya ba, su basu san a inda suke tsakannin duniya da lahira ba, Aisha, Allah ya dora mani, ba zan kai labari ba! Ki yi hakuri...... Yana gama fadar haka ya katse kiran, Docter Aisha dake kai kawo tsakannin dakinta da falonta ta dafe kai ta fashe da kuka, yar balaraba kyakyawa da ita, a fili ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Mu.azam, in sha Allah zaka warke, sai mun rayu da kai Mu.azam....... (๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”๐Ÿ˜”) Bayan sati uku Ayya ce zaune tana nunawa Agaishat yanda ake gyara lale ja domin tana son kunsa mata ne, Bayan ta tankade shi lukui ta kawo mahanabiya ta zuba masa sannan ta zuba dan madaidaicin ruwa ta kwabe shi sosai ya yi shar da shi ta zuba dan ruwa gefe ta ajiye tana kallon Agaishat ta ce" yi ki wanke kafar mana Agaishat, kin ga yayanki Mu.azam ya ce zaku fita ku zaga gari , ni kuwa na fi so idan mun gama kunshin nan sai ku tafi.... Agaishat ta yi sauri ta shiga darwaye kafar nata ta cire ta dauke ruwan ta kai ta zubar ta dawo ta dauki abin goge kafar ta gogoge ruwan kafin take zama ta tankwashe kafafiwanta Ayya ta shiga daura mata iskwace tana fadin"ki lura dan gobe ki daura abinki kin ji Yar Ayya, Agaishat ta gyada kai tana murmushi, a kowani lokaci a kowani yannayi ta tsinci kanta tunda ta sauke kafarta a gidan Ayya sai iyayenta da yan uwanta da baba sofo sun fado a ranta, bale yanzu Wardugu kansa da yake yawan hararata a farkp ya daina, shi dai baya shiga lamarinta aman baya hana wani shiga, Alhinayettt ma tana lekowa wani sa.in idan Wardugu na gidan su sha hira da yaren buzanci domin tana jin dadin jin yaren raurau ana hira da ita ba wani kyama, sosai Alhinayettt ke dan gwada mata wasu abubuwan, da hikima take nuna mata wasu yan al.adun yan birni sannan Mu.azam na mugumugun sakata a jiki, yana sakar mata fuska fiye da tunanin mai karatu, idan ta kali kayayakinta, suturun da suke malakinta a yanzu, sai ta ji hawaye na neman zubo mata, tunaninta me yan uwanta suke sakawa a yanzu? Wani hali suke ciki? Jiya i yau ne ki Baba ya canza halayensa? Sai dai takan bi su da adu.a kawai, itace kadai abinda take iya yi masu a yanzu, kuma tanaiwa iyayen rikonta adu.ar gamawa da duniya lafia, ba.a wani sakata makarantar boko ba domin shekarunta sun tafi shekara goma sha takwas har ta kusa cike sha tara, aman a gida Ayya na koya mata abinda ya sawaka sai karatun islamiya da ta kara zurfafawa sosai tana kara neman ilimin adininta. Ayya na gama daura mata kunshin ta mike tana leka windows, mamaki take irin yanda yanzu wardugu ya ajiye kafarsa a gidan, duda ta san amininsa na nan dole za yana yawan zuwa aman abin na bata mamaki, bai jima da fita ba fa aman har ya dawo, sannan yanzu basa fada da mu.azam akasin da da sai ta shiga tsakani ko ta gindaya masa doka kan Mu.azam din kafin yake barinsa ya huta, yanzu kuwa bini bini ya shigo ya haye wajen Mu.azam su yi ta hirar da ita bata san ko ta meye ba, yanzun ma tsaye suke su uku, da yar jajar nan Alhinayettt sai hira suke suna dariya, Rufe windows din ta yi ta juya ta fice ta bar Agaishat na zaune tana jira ya bushe ta wanke kamar yanda Ayya ta fada Bayan kunshin Agaishat ya bushe, ta mike ta saka takalminta silifas ta yi bayi, Wanke kunshin ta yi, jan kunshi yayi jajajir, ga mamakinta ya fito sosai a fatarta har ya haska mata fatar kafar da hanayen, Da sha.awa take kallon kunshin ya yi kyau a idannuwanta, Ta dauki lokaci a bayi domin sai da rmta yi wanka ta fito ta je bakin madubi tana goge gaban goshinta inda ruwa ya taba kannanuwan kitson da Ayya ta dage akai mata wa.inda sai warwarewa suke dan kansu , Turarukanta ta zauna ta shafa na madara masu sanyin kanshi, ta shafa mai kadan a jikinta, Kwali ta dauka tana adu.a domin har yanzu ta kasa sabawa da saka shi da dadi sai ta yi ta fama, bayan ta saka ta caje girarta, ta dauki wani jan baki mai ruwan lebe wanda Ayya ta fada mata kadan za tana shafawa a lebenta na kasa, Hakan kuwa ta yi ta shafa kadan kafin take tsurawa madubin ido, tunda ta zo garin nan ka.ida ne a wuni sai Ayya ta tsareta yin wanka sau biyu wataran har sau uku, idan kuwa ta yi wanka dole ne ta zauna ta kula da du wata gaba ta jikinta, tun tana kallon haka a wani iri har ya kasance idan bata yin ba itama bata jin dadi, sannan ta yarda da mutun sai da gyara, wannan mugun bakin da take gani a jikinta a ruwan wanka ta ga yana sauka daga jikinta, tsabar rashin wanka na kirki ne da kuma karin bakin turkidi(tufafin buzaye), yanzu fatarta ta kasance bak'a mai haske, irin bakin nan mai kyau mai birgewa, ga gyara yana kara samu yau da kulun, har santsi santsi take ji fatar tata ta fara yi mata, Mikewa ta yi dai ta shiga fitar da riga da siket din da Ayya ta rataya jikin abin turaren wuta tun da safe kan su zata saka, Wani ni.imtacen kanshi suke na turaren tubawa, A hankali ta saka slipe (pant) dinta, an ta kasa saka breziyar domin har yanzu bata iya aiki da ita ba, kai ita bata ma sonta ne , Kayan nan ta saka sket da riga, sun amsheta sun mata cicif a jikinta dinkin zamani , Tsaye take tana kallon lufayar da Ayya ta bata, ta nuna mata ta koya mata daurawa sai dai bata iya ba har yanzu (daura lufaya sai a slow), Gashin kanta kawai ta sakawa ribom ta saka yar bakar hular da Ayya ta hada mata da kayan ta luluba Lufayar ta fice da takalman a hannayenta dan Ayya ta nada mata da kanta, Alhinayettt karfe nawa ne zaki je wajen auren? , Agaishat ta tsinci muryar Wardugu da bata da siri tana tambayar Alhinayettt dake zaune tsakiyarsu Ayya kuwa na wajen table din diner tana gyara shirin da mai aikinta ta yi mata domin bai mata ba! A hankali ta sauko, ta karaso tana hangen yanda Mu.azan ke sakar mata murmushi, Karasawa ta yi sosai kafin take gaisar da su a jimila ta hanyar fadin" Ina kwanan ku, Alhinayett ta amsata tana yaba kunshinta da harshen buzanci wanda Wardugu ya ji me take fada ya yatsina fuskarsa yana girgiza kai. Mu.azam ya kai dubansa wajen agogo ya maido wajenta ya ce" Agaishana, yanzu ne safiya, duba karanto min karfe nawa ne? Na ga ko kin gane yanda na koya maki, Ai kuwa ta juya wajen agogo ta shiga nunawa da hannayenta tana irgawa tana faman fada masa lokacin Ayya ta karaso ta kama hannunta ta ce" a bar y'a na gama shiryata, ita da bata yi safiyar zuwa wajen namiji ba ai ba lale ne ta gane safiya ce ko rana ko yama ! Ayya ta karasa tana murguda baki irin na tsofafin nan masu rigima ta kai dubanta kan Alhinayettt, wato dai da Alhinayettt ake, Wardugu ya mike ya karasa wajen Ayya, ya kasance sun saka Ayya a tsakiya shi da Agaishat wace hannunta ke cikin na Ayya tana so ta warware mata Lufayar nan ta nada mata, Sosai ya so rage muryarsa, sosai ya yo yaki da muryarsa ya ce" kin ce baki tsufa ba? Da yaren tubanci, Juyowa ta yi ta murguda masa baki ta ce" eh da saurana, Wani tsadaden murmushi ya sakar mata yana dan juya kansa, ya kamo dayan hannun nata cikin nasa ya ce" kin san du duniya ba a yi ba ba kuma za.a yi ba macen da zan so kamar mahaifiyata ko? Ta kawar da kanta bata bashi amsa ba, ya ce" in dai kina irin abin nan sai in fara tunanin na bani Ayyana ta fara tsufa, Hannunta ta warce ta dungure kansa kamar yanda takan yi idan ya hasalata ta ce" ni ba wani tsufa ko rashin tsufa bane, ina jin haushin irin yanda kuka dauki al.adar yahudawa kuka mayar naku, tun da safe take gidan nan Wardugu ya ce" Mu.azam ya gayace mu baki daya mu raka shi ya ga gari, Ayya ta yi tsam tana kallon sa, Mu.azam ya gayace ku? Wardugu ya gyada mata kai, Hannunta ta kai wajen wuyansa ta taba wai ta ji da zafi, Kalau ta ji wuyansa, ta saki ta dafe habarta da mamaki, ta ce" yaushe mage da bera suka fara shan innuwa daya har shawararsu ta fara zama daya? Me ke damunku? Shirin naku kuma ya fara bani tsoro, Wardugu ya saki hannun nata yana murmushi ya karasa ya ce" ku fice mu je ta fito idan an gama shiryata, kai yama zaka hada mana fita da karamar yarinya? Yanzu fa dole ka saka mutun ya rike bakinsa gaban yara! Mu.azam dake biye da shi yana dariya Alhinayettt kuwa da naci ta zauna sai da Ayya ta nadawa Agaishat ta saka takalminta plat, suka kamo hanya Agaishat ta mugun yi mata kyau a idannuwanta, sai ta fito kamar wata chocolate color din balaraba, ta hade ta yi wani sihirtacen kyau Haka suka karaso suka bude bayan suma suka shiga, ita dai Agaishat kanta a kasa, irin kalon da mu.azam ke jifanta da shi ke bata kunya, sai ta rasa me ya sa yake irin kallon nan,? Alhinayettt ta mika hannu ta dauko wayar Wardugu ta dawo ta shiga nunawa Agaishat hotuna suna dariya, Wardugu ya ce" ina muka nufa oga? Mu.azam ya ce" ka kai mu Bienvenu a Wardugu place, Wardugu ya taka wani wawan birki, ya kalo shi ya ce" wasa kake? Mu.azam ya ce " aa can nake son zuwa, yana mai hade rai shima ya mayar da dubansa gefen titi (BIENVENU a Wardugu place, waje ne da mahifin Wardugu ya buda da sunnansa tun suna tare suna

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 12

WAReaders TGUpdates