Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 23 / 27

lafia? Wardugu na tafiya yana sake sake a zuciyarsa, yakan tsinci kansa wani sakarai idan ya ganshi gaban wanda yake so a ransa yana cikin wani halin da ba zai iya fitar da shi ba, Motar ya bude ya shiga, a hankali ya juya fuskarsa gefensa ya ga ya lumshe ido tamkar mai barci, Motar ya tayar ya juya a hankali ya nufi saloon din da ya ajiye su Alhinayett Yana zuwa ya yi mata message cewar ta turo masa Agaishat, yana kofa, Ba tare da ta tambayi komai ba ta dubi Agaishat da aka gama yi mata tsararan kitso a kanta mai dan girma girma aka saka wani dan roba a karshen kitson dan kar ya warware , ta mugun yin kyau tace da ita ta je mota wardugu na kiranta, Duda gabanta ya fadi, aman sai ta dake ta mike tana tunannin lafia? Domin yace idan sun gama su yi tafiarsu, wani abu ya faru ne? Bata da amsar da ta fi ta fice a nitse tana mai jin faduwar gaba, Wardugu dake kallonta tunda ta fito, du takunta daya na kayar masa da gaban da bai san na meye ba, ya dai ajiye hakan a matsayin zai shige gaban abinda bai taba shiga ba, zai shiga rayuwarsu ba tare da izininsu ba, zai yi iya yinsa dan faranta ran amininsa, Kare mata kallo yake, a kasan zuciyarsa ya ayanna"""""meye na naci a kan bakar mace? Menene sirin Mu.azam?, Tana kara kusanto motar yana kara dubanta dan so yake sai ya karanto sirin a tare da ita, , Da yake ta gaban motar take nufo motar, kuma Wardugu ne ke tuka motar hakan ya saka idannuwanta sauka cikin nasa, manyan idannuwanta masu ruwan madara da bakin dake tsakiya mai girma wanda ke watso da hasken ruwa ruwa yana sheki , kallon nan mai shige da mai jin bacu shine kallon Agaishat wanda hakan ya samo asali da tun tana karama mahaifinta bata isa ta daga ido ta kale shi ba, sai ta saba da yin kalli a lumshe tamkar zata rufe idon aman kuma ta fi wanda ke kallo tar tar ganni domin wata kibiya ce ke jefo gannin nata har wajen inda ta yi niyar kallo, A hankali ta lumshe idannuwanta wa.inda ta yi niyar cire nata idannuwan a idannuwan Wardugu, domin kuwa tsai kallo na cikin ido sukaiwa juna wanda basu san da haka ba sai fa ta cire nata ya farka ya yi gagawar mayar da dubansa wajen Mu.azam dake jingine da kofar motar, Murya a dake ya ce" malan dan bani waje zan tatauna da yarinyar can, Sai a lokacin Mu.azam ya ga Agaishat ce ke karasowa wajen motarsu , a wannan lokacin har ta karaso sosai jikin motar tana jira a bude mata kanta a kasa, Mu.azam ya kali Wardugu , murya a raunane ya ce" war, kar ka yi min haka , me ta yi? Dan allah kar ka yi mata fada ko ka rikitata, na tuba , Wardugu ya tsare shi da ido yana mai jin wani tsoro a ransa da faduwar gaba, mutun ne shi tamkar kowa, dole abinda zai kayarwa kowa gaba ya kayar masa, sai dai ba zai taba nunawa ba, ba zai taba bari wani ya san halin jin tsoronsa ko faduwar gabansa ba, Da ido ya nunawa Mu.azam ya fice fa, Mu.azam ya turo baki ya bude motar ya fitar da kafa daya ya juyo fa haushi haushi ya ce" idan ka batawa abin kaunana rai , sai na tarar da wannan matar taka na nuna mata waye bos Mu.azam! Wardugu dai bai ce da shi komai ba har ya fita a motar ya tsaya yana kallonta kafin ya bude mata gidan bayan ta shiga motar jikinta a sanyaye ta gyara hijabinta ta kai dubanta Wajen Wardugu, Yana son magana da ita wanda zai fuskanceta, ya sani shi ya dace ya koma baya ko dan saboda gaban ana iya kallon su ta gaba du wanda zai fice, aman wani abu ya tsaya masa ya hana shi fita ya koma bayan motar, Dakewa ya yi , ya ce" dawo gaba. Agaishat dake duban gaban motar ta kai dubanta wajensa, a ranta fadi take" shi koda yaushe fuskarsa ba wani fara.a zai wani tantankewa yake yiwa mutane, to ni me na yi masa ? A hankali ya dago da kansa ya juyo fuskarsa dan bai ji ta motsa dan bin umarninsa ba, Kamar na dazu yanzun ma idannuwansu ne suka sarke da juna, a tare gabansu ya shiga luguden duka , Wannan karin Wardugu kasa cire idannuwansa ya yi a nata , tsai ya tsaya cikin kogin idannuwanta yana mai jinsa baki daya a cikin idon, Da sauri Agaishat ta janye kwayoyin idannuwan nata a nasa ta shiga kokarin bude motar hannayenta na rawa baki daya tana neman nutsuwarta na neman gagararta, Bude motar ta yi ta fita, shakar sansanyar iskar duniyar ta yi kafin ta juya da dukan kuzarinta ta bude gidan gaban ta shiga, Shi kam binta kawai yake da kallon da bai ya kureta da shi har haka ba, sam bai san yanai mata kallon da ya fice ka.ida a adinnance ba, A hankali ta ja ta rufe kofar, aman wannan karon ta gagara dubansa cikin ido kamar yanda shi ya tsareta da idannuwansa wa.inda ta rasa gane me yake kallo, Zuciyarta ke ingizata da ta dube shi, domin bayan ta dawo gaban ma ya yi shiru ne bai ce da ita komai ba, hakan ya saka a hankali ta kuma buda dara daran idannuwanta cikin nasa, Lumshe ido ya yi ya kuma budewa kan fuskarta, haka kawai ya ji baya iya yi mata magana tun karfi ko eani gatsai gatsai, ji yayi yana kokarin sanyaya muryarsa fiye da yanda yake yiwa kowa magana a duniya, girmanta, tausayinta ne ya ji a lokaci guda, yana jin kunyarta wace bai san ko ta meye ba, ya ajiye hakan kan dan tana abar kaunar amininsa, tabas zai ci gaba da jin haka a tare da ita balema idan ta aminta da zuciya daya zata kular masa da amininsa, Sangartar da muryarsa ya ci, marainiya ta zama a makogwaron sa, da kyar ya iya sarafata wajen fadin" *Kina son sa? Zaki rayu da shi?* Ajiyar zuciya ta sauke mai cike da ma.anoni, kanta ta sada a hankali ta ce" *shi ne zabina* Furucinta da faduwar gabansa ba zai tantance wane ya fi wani karfi wajen saka jinnin jikinsa gudu a karfin da ya zarce yanda yake, kirjinsa ke duka da sauri sauri inda ya ji hankalinsa ya tashi, ya rasa menene haka? Me ke faruwa da shi, Dakewa ya yi ya cire hular kansa yana dan alamun fifita da ita, bai daina kallon Agaishat ba, ya ce" zaki iya rayuwa da shi da zuciya daya? Ki so shi domin Allah? Zaki sadaukar da komai na rayuwarki wa shi? Dagowa ta yi ta tsurawa fuskar Wardugu ido, a hankali ta ce" *ka damu da amininka ko ka damu da amanarka?* Bai bata amsa ba, domin bai fahimceta ba, dan haka ta gyara zamanta ta ce" a gida, muna da Anna daya, du yaran gidan yan uwa ne, daga bakin ranar da Anna ta baiwa Ayya ni na zama yar Ayya, hakan na nufin ni kanwarka ce, baba tsofo yace idan iyaye ko yayu kai dangi baki daya zasu yiwa yarinya aure hankalinsu a tashe yake, su ne bincike kan waye mijin? Halaya da sauransu, su ne tabatarwa idan yarinyar na son sa ne domin Allah, kai dai a firgice suke, Dan Allah, *zaka zama yayana?* mai saurare na? Mai share kukana kamar yanda yayuna ke yi? Tunda ta fara labarin lebenta yake kallo tamkar mai koyon yaren da take magana da shi, a hankali ya ringa jinta a jikinsa har ta zagaye ilahirin jikinsa, wani irin nanauyan abu ya ringa ji wanda zaka ji shi ne idan kana son abu, ko dan uwanka ko wani na jikinka sosai , farat daya Wardugu ya ji ya yi kanwa daya kwalin kwal, jal, kwara , wace yake mararin samu, ya jima yana son samun kanwa daga mahaifiyarsa dan ya shagwabata , ya ririta ta, ya sangarta ta, ta fi yar shugaban kasa gata, a yau a yanzu ya aminta da bakuwarsu, ya ji ta zama jikinsu, zai iya cewa ya samu kanwa, zai kare mata duka cuta, zai iya yin fito na fito da koma waye kanta! Agaishat Agaishat kanwa ce a ransa wace yaje jinta tamkar jini daya suka fito, Ji ya yi zai iya sakewa ya yi hira da ita irin ta dan uwantaka, lokaci daya ta shiga kokonta idan ya aura mata mu.azam ya kyauta mata kuwa? Nan da nan zuciyarsa ta kwabe shi ta hanyar tunasar da shi ai komai na Allah ne , . A hankali ya dan jirga jikinsa bangarenta yana dubanta , ya dan saki fuskarsa ba laifi, dan karamin yatsarsa ya miko mata ya ce" zaki zama kanwata? Murmushi mai hade da dariya da farin ciki ta dan yi masa ta ki bashi hannun sai alamu da ta nuna zata hade hannayen nasu ita da shi , Shima murmushi ya sakar mata yana mai nuna alamun dimple dinta har biyu sun shige sosai, A hankali ta ce" yayana, Duda suna ne wanda kowa ke fada, karamin suna, sai da ya ji dadin abin, ya amsa mata da ido, Agaishatt ta ce" *ina son sa!*.................................... I.m back😕😕😕 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4️⃣3️⃣ 😕😊😊😊😊😊😊😊 A hankali murmushin fuskar nasa ya bace, shima ya yi kalar serius ya ce" kina son sa? Zaki aure shi? Agaishat ta dan kawar da kanta daga dubansa, ta ce" *eh zan aure shi,* Ajiyar zuciya ya sauke ya wauga bangaren Mu.azam, ya ga yana zaune kasan wata bishiya yana dadana wayar hannunsa, dubansa ya dawo wajen Agaishat, ya dan jima kafin ya ce" *Zan aura maki shi*, Agaishat bata ji wani yannayi na daban game da abinda wardugu ya fada kan aure da za.a yi mata, duda abu ne da take cike da murnar itama zata yi, aure da mutun kamar Mu.azam, itama zata yi rayuwar aure, aman zumudin da farin cikin ba wani can can ba , bata san dalili ba ko fargaba ne ya hanata jin madaukakin farin ciki kan lamarin? Murmushi ta sakar masa ta kai dubanta wajen Acn motar da ya gama kashe mata gabobin jiki dan mugun sanyin sa, Wardugu a hankali ya kai hannun sa wajen ky din motar zai kashe sai kuma ya bari, duban Agaishat ya yi ya ce" mu ga kitson yan matan Ayya? Ai kuwa ya washe baki tana zabga murmushi cike da farin cikin irin yanda ya sauko daga hararanta ya mayar da ita mutun gashi har ya damu da kitsonta take dubansa tana kokarin jan hijabin baya ta bude masa kitson tana fadin" Alhinayett ne tace kar a yi min kananuwa dan kar na wahala sosai, ka san me, kuncewa yake yi fa, Ayya ne taki yarda na daina kitson nan, kuncewa yake yi shi kadai.....ta karashe tana dan turo bakinta irin na shagwababun yaren nan, Murmushin da a yau ya kai sau hudu da ya yi du a gabanta ya kuma sakar mata yana duban kitson har ta rufe , bai san ta ina ba bai san lokacin ba sai ji ya yi ya ce" aa, ki yi ta yin kitson ki, yana yi maki kyau, Tsai ta yi tana dubansa, a ranta fadi take...da gaske ne ko kuwa? Me ke damunsa yake magangannu irin haka yau ne? Bata bashi amsa ba sai lumshe idannuwanta da ta yi ta bude motar tana fadin" Allah ya tsare ka, Da ido ya bita bayan ta bude motar inda yana kallo Mu.azam ya karaso wajenta da sauri yana alamun tambayoyi inda ya hangi ta sakarwa Mu.azam din murmushi bata ce komai ba, daga nan ta juya ta tafi cikin saloon din. Karasowa motar ya yi ya bude gidan gaba ya shiga ya tsare Wardugu da kallo, Wardugu ya tayar da motar ya juya akalarta zuwa gidan Ayya Tafiyar kurame ne suka yi har suka karasa gidan Ayya, suna tsayawa Wardugu ya daga karamar wayarsa ya danna number ya kara a kunne Ana dauka ya ce" ka cira min tiket biyu zuwa agadez yau. Yana gama fada ya katse kiran ya fita a motar shima ya bi bayan Mu.azam Yana shiga dakin Ayya ya zarce direct, yana zuwa ya tarar da ita tana ninke abin shinfidar da ta cire Kama mata ya yi suka ninke sannan ya gyara mata wanda ta shinfidar da kyau ya nemi waje ya zauna ya tsura mata ido, Bakinta ta tabe ta karasa inda yake zaune ta ce" menene? Murmushi ya yi mata yana dubanta ya ce" sai da wani abu d'a zai kali mahaifiyarsa kyakyawa Ayya? Kanta ta girgiza , ta ce" da ace uwar bata san halayen dan nata ba, me ke tafe da kai malan? Wardugu ya yi murmushi kafin yake yannayin magana mai mahinmanci, ya ce" na tambayeta idan tana son sa, amsarta ita ce" *Ina son sa, zan iya zaman aure da shi* , zan je na nema masa aurenta domin shima yana son ta, A hankali ta zauna tana mai yi masa wani irin duba, ta ce" baku da hankali ne? A me kuka dauki kalmar aure? Sai kace wani abin wasa? To ko yar zan baku ai sai da alwalin da zan gindayawa dokoki kan yata bale ni bamu wani yi magana da ita ba, aikin banza gagawar me kuke haka ne? To naki din! Kallonta kawai yake har ta dasa aya tana kawar da kai da yannayin haushi a fuskarta, Murmushi ya yi , a hankali ya ce" Ayya, aure ai tayashi ake ko? Sunnar mazon Allahn salalahu alaihi wa salam din kike cewa baki bada ba? Haba Ayyana, Yatsarta ta nuno masa ta ce" Wardugu ka kiyayeni, ni ban ce ba zan bada kwata kwata ba, aman yannayin yanda kuke maganar ne ya fara bani tsoro, meye na gagawa bayan kun san aikin shedan ce? Sannan yarinyar nan dai amana na dauko daga gidansu, idan wani abin ya sameta ba zan yafewa kaina ba! A hankali ya dawo kusa da Ayya ya zauna, hannunta ya kamo ya rike yana dubanta ya ce" abinda ke sakawa ana jan aure bincike, da halin rayuwa na yau da kulun, Mu.azam namu ne, mun san waye shi, sannan Allah ya hore mana abinda zamu kawo mu nemi auren ko nawa ne, Ayya, bana son mu zurfafa bincike ne, ina so ki yi min lamuni ki duba , ba zan saka kaina a maganar idan na san shirme ne, ba zan tarki tarbenta a haka da garage ba idan na san cutarwa ne wa amanarki, ina iya yiwa aminina alwali, kuma tare da shi zamu tafi namiji alwalin kansa ne, ki taya mu raya sunna da yar ki, kina da damar bibiyar rayuwarta da shi ...idan an yi maki abinda ba shi ba ki raba Ayya kam du jikinta ya yi sanyi, tana dunansa gabanta na faduwa tana ayana lale da kwakearan dalilin da ya saka Wardugu shiga wannan maganar auren, A hankali ta ce" menene? Me ke faruwa ne? Wardugu ya kara sada kansa yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa ya ce" alkhairi ne, ki taya mu. Can daman Ayya ba mai musa maganar wardugu bace, hakan ya sa ya yi gagawar shawo kanta kan zasu je garin su Agaishat neman aurenta wa iyayenta......, Bai bar dakin Ayya ba sai da ya tabatar da ya samu kanta ta bada amanarta da dukan yawunta, ta yi fatan alkhairi Haka ya fito ya tisa keyar Mu.azan dake cike da mamakin lamarin sukaiwa Ayya salama suka nufi aeroport dan tafia garin agadasawa su nufi timiya gari mai gawo 🙁 ........sowi kadan ne..... 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4️⃣4️⃣ Basu dauki tsahon lokaci a jirgi ba Allah ya sauke su lafia, Direct hotel suka nufa infa Wardugu ya yi kira kan q shirya masa mota da yan tsiraku sojoji zasu je kauyen Timiya, Sai bayan ya yi wanka ya mike saman bed ya danna wayarsa ya danawa hajia Walyn kira yana mai lumshe ido, Daga bangarenta ta daga tana duban agogon dake dakinta, hakimce take ta hada uban maltina tana son kwankwada tana tsoro, ance mata yana zubar da jaririn ciki wai, dan haka ta gyara zama da niyar sha sai ga kiran Wardugu, Dagawa ta yi gabanta na faduwa kar a je ya zo yana nemanta ne, Walyn........ya fada yana mai jan sunnan, Idannuwanta ta lumshe ta kwontar da kanta saman hannun kujerar tana sauraron yanda ya wani ja sunnan har tsakiyar kanta, Bakya neman mijinki wuni guda? Ki ji na ci abinci? Me ke damuna? Da wa na hadu? Karshema inda nake? Ko kin yarda da kanki har haka ne? Walyn ta yi murmushi ta ce" na yarda da kaina ne, Murmushin ya yi shima ya ce" baki da matsala, Kana ina? Ta jefo tambayar Wardugu ya daga kai yana karewa dakin kallo ya ce" ina hotel , a Garin Agadez. Me? Hotel? Agadez? Yaushe ka je? Me ka je yi? Kuma a hotel? Kai da wata yar iskar?, Idannuwanda ya lumshe, a hankali ya dora hannunsa na hagu saman kansa, shafawa yake yana lalabar kansa, shiru ya yi mata wanda hakan ya saka take ta kiran sunnansa da karfi tana fadin ka fada min da wata tsinaniyar kake hotel? Har ka bar gari da gari ka je garin agadez? Me ka je nema? Farin, kyan, ko gashin? Wanene bani da? Ka ban amsa Wardugu, A hankali ya katse kiran da wayar baki daya ya furzar da wata zazafar iska ta kai dubansa wajen Mu.azam da ya yi tsai cike da takaicin matar abokin nasa yana dubansa, mamakin irin rashin hankalin Walyn

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 23

WAReaders TGUpdates