Back to details

Bakace Book Compelet Sajida Nijar

Chapter 5 / 27

a washe gari wanda cikin ikon Allah sai da ya dauki awa shida kafin yake fitowa daga dakin tiyatar da ita shi ya hada zufa hakama masu kama masa wanda ba.a jima sosai ba aka gurgurota a gadon mararsa lafia aka kaita dakin da ake kontar da masu yoyon fitsari Jigum suke zaune suna mamakin wai asibiti ce haka, su kam tunda suka shigo garin a tsorace suke da yannayin tsarin gari, gini ne kala daban daban bene kai kasa na cin kudin masu kudin birni .... A hankali ta shiga bukar tana dube dube kafin take kallo shi, a kwonce yake , idannuwansa a rufe kamar marar lafia Da sauri ta karasa ta ce " Sofo? Firgigit ya buda idannuwansa ya sauke saman kanta, Kokarin tashi yake wanda da kyar abin tsufa ya samu ya zauna yana kallonta, murya na rawa irin ta tsufa ya ce" ina kika shiga? AGAISHAT zuciyata ta rikice na rashin gannin ki, na damu na kasa baci, kin ji har zazabi nake dan bana ganninki yata, ina kika je kwana biyu? Kin san ke nake gani ina jin dadi, kece mai daukana tamkar mahaifi, zo zo na ji me akai maki? Wa ya taba min ke ? Karasawa ta yi tana sakar masa murmushi ta kamo hannunsa ta damka masa goron da ta siyo masa tun wancen ranar, murya a nitse ta ce" mun fuskanci matsaloli ne a gida Sofo, aman yanzu alhamdulilah mun gode Allah, Su Anna sun tafi birni Sofo, muma watarana zamu je? Zaka tafi da ni nima na ga birni? Ajiyar zuciya ya yi jin ba abinda ya sameta na tashin hankali, ya lalubo karfen gurza goronsa ya mika mata ta mike ta darwaye ta dawo ta raba goron hudu ta maida hankali ta gurje masa shi tas ta mika masa ai kuwa ya hambuda yana tsotsa yana dan juya kai irin ya ji dadin goron Can ya ce" Birni garuruwa, A birnima akoy garin da dadi ne da shi sannan akoy wanda sam ba zaka so rayuwa ciki ba indai kai din bako ne Birni tana tatare da abubuwan firgitarwa, murane sun yiwa abin hawa irin mashin mota yarda, sun yarda da su suna halaka su Tagumi ta yi ta ce" suna halaka su kamar yaya? Ido ya dan zaro ya ce" zaki ga dan birni idan zai yi tafiyar da ba wata nisa ba, ba jeji ba, ba abin tsoro a hanya ba, dan tsabar sangarta da son jiki sai ya dare abin hawa abinsa ya tafi a dan kankanin lokaci in abin ya zo da karar kwana sai ya juyeka tamkar tuwon masara nan zigib ka mace shikennan sai kiyama Murmushi ta yi ta ce" toh ba kace ajali na tarda mutun du inda yake ba? Mutuwa ai kai ka fada min ba.a gudunta kuma ba.a boye mata, kuna Anna ta ce ita mutuwa lokaci ne idan lokacinka ya yi ba tsumi ba dabara zata daukeka ne ko waye kai ko me kake , kai ka ce min mutuwa mai yanke kauna, takan raba da da uwa, miji da mata, kuma kace min kowani bawa da ajalinsa a duniya Tsofo yama ta murmushi yana dan barin jikin nan na tsofafi ya dungure kanta ya ce" haka ne Agaishat, Mutuwa gaskiya ce, Allah ya sa mu cika da imani Ta amsa da amin...., ta ci gaba da fadin " ka ce a birni suna da wata kalar madara banda irin wannan tamu ta rakumi ko shanu? Ina so idan ka je birni ka kawo mini in kaiwa Anna ta sha ta ji itama Kansa ya girgiza kawai, domin ya lura yau du labari ne a kunshe a bakin Agaishat, wai shi zuwa birni, shi da a yanzu salarma baya iya zuwa masalaci kafafuwa sun kiya, ga tsufa me zai je nema birni? Sai dai idan har kadarar makwoncinsa a can wannan kuwa ya san ko ta wani hali Allah zai kai shi.............. Dago kanta ta yi ta ce " ka san me? Ya gorgiza kai alamar aa Ta ce" wankana sau biyu, su Mariama sun bani kaya suka saka na yi wanka Murmushi yake na jin dadi, bai taba yarda a duniya Allah na hada jinnin mutun da mutun haka kawai sai a kan yar yarinyar nan, Jinta yake tamkar jinninsa, sonta yake har bargonsa, baya son damuwarta, fatansa Allah ya bata miji na gari komai talaucinsa domin ba zata kasa ratuwa da talaka ba, a hakan rayuwarta ta ginu, gidansu ba laifi su ba talakawanan tukuf bane domin dadaya ne gidajensu ke zagaye a garin aman ita rayuwarta irin ta yayan talakawan nan tukuf ce masu wadatar zuciya, Tana ta zubar ta mike ta shiga dan totona dakin kamar yanda ta saba dan dudubawa da kyau ta kashe kunama, domin kunamu na cikin kasa bakaken nan wa.inda idan sukai cizo in ba.a yi gagawar shan magani ba dafin na saurin kashe mutun , sune a cikin kasar garin kamar me, yan garin sun iya rayuwa da su, domin sun san inda zasu same su sun iya kashe su tamkar yanda ake kashe cirnaku, Ta samu ta kashe wajen hudu ta cilar waje ta dauku tulu ta ce" sai na dawo Hannu ya daga mata yana murmushi ya ce" Allah ya tsare ki Yana kallonta har ta fice , ya samu kansa da zirarar hawaye, ya ce" ya Allah baka barin wani dan wani ya ji dadi, Allah ka sa , ka yarda, ka aminta , ka bani ikon gannin ta shiga hannu mai kyau kafin na koma gareka ....... *Niamey* Kan Anna kasa take tafiya domin bata son gannin irin yanda mutanen ke cuwa cuwa, a can kauye shiru ne, ba hayaniya , ba komai, sannan mutanen basu fi a kirga ba, hakan ya sa du idan ta fito daga dakin da Fatimata take koda dan ta leka ta ga safiya ce rana ne ko dare ne? Sai ta rikice Ji ta yi ta ci karo da mutun, da sauri ta dago dan bayar da hakuri sai dai me, gani ta yi ya zaro idannuwansa yana kallonta, a hankali ya nunota da yatsarsa sai dai wani abin ya ce masa Haba docter, haba docter, wacen koda jikin manyanta ya kamata ba zata koma haka ba, kuma ita batuba ce ba buzuwa ba, wannan kuwa buzuwa ce ta sha bakaken kayanta, kai bama zai yiwu ace ita bace, Da sauri ya ce" yi hakuri baiwar Allah Bata san ta ina ta iya hausa ba, bata san ya aka yi ta ce" Ba komai yi hakuri kaima Gaba ya yi yana dan waiwayenta, shi dai rabinsa da wancen dama familynta tunda aka hana masa aurenta, tun suna saurayi da budurwa, muryar wancen da wannan ba daya ba, sannan kai ka daina tunani kan matar nan mai yiwuwa matar aure ce Da sauri ya kawar da maganar a ransa ya nufi office dinsa yana dafe kansa a fili ya furta" ya dace na ajiye aikin nan, na jima ina fama har jikin tsufa ya zo.... Tunda ta koma dakin ta yi shiru tana tunani, Gaishat ce ta salame sallah ta juyo tana kallon maman nata ta ce" Anna me ke damunki ne?? Anna ta dan yi jim ta dago ta ce" wani yare na yi yanzu Gaishat, wanni mutun na kade ya min yare na bashi amsa tartar tamkar na iya yaren Da mamaki Gaishat ta taso ta zauna kusa da ita ta ce" me kuka ce????????? 🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫 Na *SAJIDA* *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣2⃣ Cikin yaren buzanci Anna ta maimaita mata abinda suka ce Da mamaki take kara kallon Anna ta ce" kuma baki san sunnan yaren ba? Anna ta girgiza kai, da yannayin damuwa a fuskarta ta ce" ban sani ba, kuma da dukan alama ba yaren faransanci bane domin likita ya yi ta yinsa a gabana ba wani fahimta nake ba, sannan ba yaren nan da muke ji wajen masu siyar da abinci a garinnan bane wato Zabarmanci, wannan yaren shima daban yake Gaishat ta mike tana kallon ledar fitsarin fatimata ta ga bata cika ba ta ce" Anna, ko mu koma wajen mutumen ku kara yin yaren? Anna ko haka na da nasaba da asalinki? Nan da nan Anna ta ji ranta ya baci, asalinta? Kennan dai yayanta ba zasu daina daga mata hankali da wannan kalmar ba, rai a bace ta ce" ina ruwanki da asalina Gaishat? Ina ruwanki? Tana gama fada ta fice a dakin don ji take zuciyarta sai tukuki take mata na bacin rai Da kallo Gaishat ta rakata, haka ne, komai irin dadin da kake ciki da Annarsu in dai ka yi gigin neman sannin wacece ita? Zata fatatakeka ne ko waye kai komai kusancinka da ita, Ajiyar zuciya ta sauke ta karasa kusa da Fatimata da yanzu masha Allah sosai take samun sauki dinkinta ana kula da ita sosai, likitan karshe ne , du niger ta wannan fannin da shi muke takama! A yannayin nishadi ta fito a gidansu, Abanta ya santalo Amarya yar bariki, irin a nuna masa ana son yayansa har Bak'A bata kyamata tana bata abinci bayan ya cashewa maryama kudaden da ta yi rantsuwar ba za.a shiga da matar ba sai ya bada su ......Algabitt dai na rakashewa fa amarya , yayansa na gefe suna rayuwarsu , inda bak'a ta dan samu inci na kwana biyu a gidansu domin bashi da lokacin wulakantata yana malake da amarya yan uwanta kuwa sosai suka dan sasauta mata tsanar da sukai mata Yar waka take da yaren buzanci tana saka sunnanta a ciki, fadi take" ni bak'a yau wa zai so ni? Bak'a nake wa zai rabe ni? Yar bak'a haka ne sunana! Dala biyar babu mai kaunata, Ta yi dariya ta ce" ni ko a baiwa an rasa mai siyana a kauye da birni, Agaishat kij cika muni....ta fadawa kanta sai kuma ta yi murmushi tana girgiza kai kawai Algabittt, yar firit din yarinyar da ya auro ta furta kai tsaye Shi kuwa da yake saman gadon karagarsa ya yi dadaya ya kallota ya amsata da um? Tasowa ta yi tana juyi uwa bishiya ta karaso tana nuna masa gidan manta na shafawa ta ce" ka san yanzu muma a kauye mun yi ido, yarinyar nan jikanyar mai siyar da fura nake kawance da ita, ita na baiwa kudina ta siyo min wannan man, Na ga fatar Agaishat ta dameka, baka son yarinyar dan bakinta, ni kuwa na hango kyakyawar yarinya ce ta karshe kawai bakin ne ya yi mata yawa, dan haka ga shawara wace in dai ka yarda ka takurata ta yi a hankali zata dawo farar mace itama mu siyar mu samu kudinmu mu yi tafiyarmu birni mu je mu rakashe mu hau mota mu saka gilashi mu dangwali kaji Wata zabura ya yi daga konce yana kallonta, irin maganar ta fara shigarsa, ya fara aminta da shawarar amaryar tasa Kara jujuya masa ido ta yi ta mika masa ta ce" ka ga bude ka gani, ai dai ka san wannan uban farin da na kara ba nawa bane wanda har kake son samun irina ............. ka yi mini ciki na haifa maka mai kyau ko? To sai fa wannan, ka bada na je na kai mata a siyo mata ta shashafa ka ga yanda bak'arka zata dawo yar dagwasssssss Murmushi ya sakar mata ya jawota jikinsa ya ce" na yarda, in dai ta dawo fara sai in baki ki kai a siyo dan ubanta sai ta shafa ko bata so Dan ture shi ta yi tana jin haushi a ranta, dan jaraba sai ya kama ya jajagulata shi ba wani nisa yake yi da lamarin ba du ya hargitsa mata tunani ya barta, haba ta yi aure ta bar jarumin maza saurayinta, aman yau sai ta gayato sho gidan nan Dan dukan kirjinsa ta yi ta ce" ina so wani dan uwana ya zo mu wuni tare yau Algabiiiiitttttt Ta fada tana jan sunnan Da ido ya tsareta, wai itama nan ta iya bariki, murmushi ya yi, shi dai burinsa ta dauki ciki fa? Ina ruwansa inma 2a zqi dane mata ruwan ciki, shi dai in ta yi cikin ta haifar masa kace komin jaraba ya rike abinsa ko a shekara goma ne ya saida ya kara kama daloli, shi kam haihuwar yaya mata ta yi masa rana ( wani abu zai baku mamaki a lamarin nan, irin yanda Algabitt baya kishin matarsa? To bara ku ji readers , ban ce duka buzaye ba, ba zan ce duka ba domin mahaifina buzu ne dan tsananin kulle da yake yiwa matansa ko gidan mutuwa da ta shafi gidansu zasu je shi ke kai su da kansa ba direba ba kuma ya tsaya su fito rufrufruf uwa matan ninja baka gannin komai na jikinsa ko.ina a rufe ruf ba damar ganninsu komai kusancinka da su, sai dai kuma akoy buzayen da basu san darajar matansu ba, sam basa kishin matansu, sai su ga matarsu kwonce saman bed da kato su fice abinsu ko a kwalar rigarsu, baya hana suma in an jima su taketa abinsu doki ce dan haka suke zaune da ita ba wani abin ba! Gaskiya ce a fadeta🤷🏻‍♀) Murmushi Algabit ya yi mata ya matsota sosai cikin yannayin rada ya ce" ke , kar ki damu da fada mini fan yan uwanki maza zasu zo, in dai zaki zauna da ni ki haifa mini mata masu kyau? To na baki dama! Ai kuwa da murna ta rungumeshi ta shiga bashi kulawa daidai daukar hankalin tsufansa 🤦‍♀ Wannan kennan ................................................ A hankali ya jona wayar abinda zai dafa masa ruwan zafin dan ya kada madara ya sha Komawa ya yi jikin bed ya zauna ya shiga karanta messages din Walyn, daya bayan daya, Na farkon farkon du yannayin ranta a bace ne, harda baya jin kunyar a ce matarsa guda ta kwana a cell? Toh garin niamey ya dauka, ita yanzu kunyar zuwa auren da zata hadu da mata take, a jejefeta da habaici ya nuna ita ba kowa bace a fadin duniya Sai daga baya kuma ta fara nuna wai ina ya je ne? Ya haka zai yi tafiya bai yi mata salama ba? Ina ya tafi? Sai daga karshe ta sauko sosai ta yi ta turo masa alamun kuka da nuna ta yi missing dinsa yana ina ne? Tana son ganninsa ta yi missing dinsa Murmushi ya yi a fili ya ce" Hajia Walyn matar Wardugu, Walyn mai zamani, Girgiza kai ya yi, kai shi kansa ya sani da ace wani saunan namiji ne da tuni Walyn sai yanda ta yi da shi, kuma ba boka ba malan! Wayarsa ya kunna wace take kiransa, ya cireta a liste noire (Black list) ya kwonta yana sauraron ruwan zafin na karar ya dafu aman ya yi masa banza, tunani yake, wai shi shugaban revel zai yiwa haka? Ya fada masa gashinnan zuwa aman ya ki zuwa? Har ya je ya yi ta zaman jiransa wai sai daga baya ya yi masa message cewa ba zai samu zuwa ba,? Ya sani sarai waye shi aman ai shima ya san waye shi! In ba dan tsufansa ba da sai ta tafka masa ashar din da zai gigita! Wayarsa ce ta shiga kara , irin kukan bindiga ratatatttatatatatatattatatatatatatattatatatatatatatatatatatatatat Muka hannunsa ya yi ya dauko yana karanta sunnan mai kiran Sai da ta tsinke aka sake kira kafin ya daga bai yi magana ba Oga, bako ne muka yi, ahi kadai yake tafe cikin duhun nan, ya zo ta hanyar boye , ragar wajen nan ta shaida zuwansa domin ta kama masa hannun shine ya fito yana fada Kai waye ya zo? Wardugu ya katse shi da kakausar murya Murya na rawa ya ce" Shugaban Revel! Wardugu ya lumshe idannuwansa, a nitse ya ce" ku shigo da shi fallon farko, ku juya Da toh suka amsa suna masu mamakin mai gidansu, yana nufin daga shi sai shi zai ganna da wannan hatsabibin mutumen? Lale Wardugu bashi da tsoro, baya dar, baya tsoron uban kowa! Kwonciyarsa ya yi bayan ya ji wa ke jiransa, Can cikin tunaninsa wayar ta kuma daukan kuka, Da haushi haushi ya mike ya daga da kakausar muryar nasa ya ce" Hello! Wardu.........ta fada cikin sanyin murya Tsai ya yi bai amsata ba Kuka ta fashe da shi ta ce" tu me manque (i miss you) Ajiyar zuciya ya sauke a takaice ya ce" ki bi Nuger airlines gobe ina Agadez hotel din sojoji ki sauka nan ko bana nan ki je dakina Yana gama fada ya kashe kiran yana shafa gefen fuskarsa da sajensa DOGON wando ya dora saman gajeran ya saka riga fara kar ta ririke damatsunansa ya fito ya nufi fallon da aka sauke bakon dare (🤣) Yana zuwa ya shigo kai tsaye, Mutumen dake zaune ya sha rawani ya hakimce cikin shiga ta kamala mai daukaka darajar dan adam ya dago ya tsaida kallonsa kan Wardugu, a tarihin rayuwarsa dole ya sako wannan yaro, domin shi ne mutun na uku da ya ajiye shi jira Murya a kausashe ya ce" Wardugu ba.a tsayar da ni jira Shima Wardugu kai tsaye ya ce" *Rhissa agbula* ba.a ajiyeni jira! Murmushi Rhissa ya yi, ya mike tsaye suka gaisa irin gaisuwar musulunci suka baiwa juna hannu suna yiwa juna salama Wardugu ya ce" ya zaka zo wajena ni daya bayan ka san ya dace a tatauna da kai a bainar nasi kowa na da magana da kai harda mai zuwa da maganar shugaban kasarka Rhissa ya ce" shugaban kasarka dai, ka san ni ba nawa ba! Sannan ni kaima da na aminta ganninka dan na fafata da kai na yarda tsaurin kanka zai je da nawa, bana musanyar yawu da matsoraci, ba.a daukana a tv haka kyauta sai kace wani sakarai! Wardugu ya girgiza kai ya ce" ya ake ciki? Wa ke son tayarwa kasata hankali? Ina suke? Menene abubuwan yakinsu? Ana jitajitar kune kuka dawo bayan kun daina aiki a

Share this story

Bakace Book Compelet Sajida Nijar - Chapter 5

WAReaders TGUpdates